yana kaɗa ƙafa, hannunsa ɗaya yana riƙe da waya, ɗaya kuma kan shisha, yana ta fesar da hayaƙi.
"Hello" sautin muryar mace ya fito daga cikin wayar.
Ya ce "Hello, how far?"
Ta amsa da "Ya aka yi?"
"Mun yi magana da tsoho, ashe kin gano in da yarinyar nan take?"
"Eh, na gano, sai dai sun ce ba za su karɓi kuɗi ba, hakkinsu suke nema, dan haka sai ka san yadda zaka yi"
Yayi murmushi ya ce "Ki san yadda za ki yi dai, ai kin san dolenki ki ɓoye laifin nan ma, kamar yadda ki ka saba".
Cikin takaici ta ce "Ka ce dole?"
"Ƙwarai dole, idan asirinmu ya tonu ai kema naki ya tonu, yanzu wane matakin ki ka ɗauka?".
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Yadda na lura, takamaimai, ba su san waye kai ba, daga ita bar babarta, dan haka zan je gidan ita Antyn taka, a bamu adress ɗin maigadin da suka kaita Asibiti lokacin da abun ya faru, duk da Yallaɓai ya gaya mini, an sallame shi daga aiki, amma dole za mu yi framing ɗin sa da laifin, in case wani zai tayar da maganar, sai mu ce mai laifin ya shiga hannu, abun da nake ƙoƙarin yi kenan"
Ya kwashe da wata irin dariya ya ce "Daɗi na da ke akwai brain, anyway ina ne gidan su yarinyar, she needs to learn a lesson, da ita da babarta da ɗan jaridar da ya saka zancen".
Da sauri ta ce "Kar ka kuskura, ba zaka ɓata mini aiki ba, na gaya maka ba su san kai waye ba, idan kuma ka yi wani yinƙuri, da ya samar da wata ɓaraka babu ruwana a ciki na gaya maka"
Abdul ya ce "Na ji, ina son ganin yarinyar ne kawai"
"Abdul, ina da abubuwan yi da yawa a gabana"
"Naja'atu, kar ki katse mini waya, ki bani adress ɗin yarinyar".
Kashe wayar ta yi, tare da jan tsaki, ta cigaba da rubuce-rubucenta.
Nabila sai wajen sha ɗaya saura na dare, sannan ta ɗan dawo dai-dai, sai a lokacin ta samu ta yi wanka, a cikin ɗakinta ta tsaya tana kallon cikinta, da ciwonta, da haryanzu yake yi mata zafi.
A haka ta lallaɓa, tayi shafe-shafen skin routine ɗin ta, ta fita kitchen ta haɗo tea, ta dafa indomie, ta koma ɗakinta, ta saka wayar Viper a caji.
Ta ɗauki wayarta ta tarar da tarin missed calls ɗin Nasir, ta kira shi ta saka wayar a hansfree, tare da kashingiɗa.
Ya ɗaga tare da yin sallama, ta amsa masa a hankali.
"Arfa ko ki neme ni, ki ji ya na sauka ko?"
A shagwaɓe ta ce "Am sorry, i got a little accident ne, a asibiti na wuni"
A ɗan rikice ya ce "Subhanallah, garin yaya meyafaru?"
"Don't mind, akwai labari ne"
"Wane irin labari? Amma dai kina lafiya ko?"
Tayi murmushi ta ce "Gashi muna magana da kai, lafiya ƙalau nake, ka ce Viper daga prison aka sake shi ko? Laifin me yayi aka kama shi?"
Nasir ya ce "Ohhh my God, meyasa ki ka damu da lamarin nan ne har haka Arfa?"
"Ni ka amsa mini Please"
Ya ce "Yeah, amma ya shiga prsion, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, shigarsa na ƙarshe ne, ya ɗan daɗe, kuma da alama laifin da ya yi babba ne, sai dai ba wannan ne a gabana ba, kama shi nake son yi.
Akwai jami'anmu suna yawo a farin kaya, suna neman bayanai a kansa"
"Ka daina wahalar da kanka, na samo maka abubuwan da za su sauƙaƙa maka komai"
Ƙasa-ƙasa yayi da murya ya ce "What do you mean? Ba na son wasa fa".
Ɗan shiru ta yi, ta tabattar idan ta gaya masa gaskiya a yanzu, ba gwaninta za ta yi masa ba, dan muddin ta gaya masa ta san in da yake, zai ce ta je wurin ƴan daba, zaneta zai yi, kuma sai ya gaya wa Abba ta shiga uku.
Dan haka ta ce "Da gaske nake, na je wurin wata client ɗin mu, a unguwar da yake, na samo labari, yana da yaransa da suke ƙananan dilallan tabar wiwi, amma ba su san in da yake ba, wai akwai wani guda ɗaya a tal'udu, yana sayar da katin waya bayan magariba, amma ƙwayoyi yake sayarwa, ya san in da yake".
Ya ce "Look arfa, ba na son wasa, daga zuwa unguwar wurin client, har ki ka samu wannan rahotannin?"
"Haba DSP, kar ka manta ni ma fa ma'aikaciya ce, wallahi ba ƙarya nake yi ba, daga majiya mai ƙarfi na ji labarin, na je wurin kuma na ga mutumin yana zaman sayar da katin wayar, idan baka yarda ba, idan ka dawo da kanka ka bincika"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "No, ba sai na dawo ba, zan aika a bincika mini, ina fatan baki gaya wa kowa ba?"
"No, babu wanda na gayawa"
Nasir ya ce "Good, amma kar ki kuskura ki yi wani abu, da zaki saka kanki a cikin hatsari kin ji ko?"
Nabila ta ce "To, idan ka dawo zan baka wani abu mai muhimmancin da zai taimaka maka, amma sai idan zaka yi mini alƙawarin ba zaka dake ni ba, ko ka yi mini faɗa" tayi maganar tana kallon wayar Viper.
"Menene abun?"
"Sai ka dawo tukuna zan gaya maka, take care"
"Shikenan, Allah ya kaimu na dawo ɗin, ki kwanta ki huta"
"Ok bye-bye" ta kashe wayar ta ajiye, ta ɗauki ta Viper, da ta yi caji, ta kunna ta.
Ta kai wayar hancinta ta sinsuna, ga warin sigari tana yi, ga ƙamshin turare.
Ta fara shige-shige a wayar.
Cikin call log ɗin sa ta duba, ga lambobi nan, sai dai duk kiransa ake yi ba ya kira, sai jerin private number da ake kiransa da ita.
Ta duba cikin messages ɗin sa, babu komai a ciki, sai dai a cikin drafts ɗin sa, yayi saving ɗin wasu kwanakin wata.
Tayi shiru tana tunanin yadda ta ɗaukko wayar ta sa, lokacin da take tattare kayan jakarta, da ta buɗe idonta ta gansu a tarwatse, ta ga wayar a gefe, ta haɗa da ita tana sane.
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani laifi ka yi aka kama ka, sannan aka sake ka, ba bisa ƙa'ida ba? Shi yafi cancanta ma in mayar da hankali in binciko, yadda ana kama ka, zan yi raising case ɗin nima, a hukunta waɗanda suka sake ka" tayi maganar tana sake mayar da wayar ta sa caji.
"Ko ban ce na san in da ka ke ba, wayarka zata bawa jami'an tsaron damar nuna in da ka ke".
Ta mayar da kwanukan kitchen, ta dawo ɗakin ta rufe ƙofarta ta kashe fitila za ta kwanta, sai dai tana kashe fitilar, sai ta ga kamar Viper ne a tsaye a gabanta, saura ƙiris ta kurma ihu, ta kunna fitilar tana zazzare ido, tana cigaba da ƙarewa ɗakin kallo, zuciyarta na saƙa mata ko ya biyo ta.
Da ƙyar ta nufi gadonta ta kwanta, gabanta na faɗuwa, ba tare da ta kashe fitilar ba.
Zumbur ta kuma tashi zaune, ta ɗauki wayar ta sa, ta sakata a cikin wardrobe ɗin ta, ta rufe ta ta dawo ta kwanta tana rarraba ido.
Sai dai fa fafur ta kasa bacci, tsoro ya baibayeta, mussaman idan ta tuna ya ce idan suka sake haɗuwa sai ya kashe ta, sai yanzu ma ta fara tunanin da yaya zata miƙa wayar nan ga DSP Nasir, dan dolen dole sai ya tuhume ta, to idan ya tuhume ta wace amsar za ta bashi? Yaya aka yi wayar ɗan daba ta zo wurinta?.
Sai kuma ta koma tunanin, yaya iyayensa suke ji, sun haifi ɗa ya zame wa mutane masifa a gari?.
Tsananin zurfin da tayi a cikin tunani, ya sanya, wani ɓarawon bacci, ya yi awon gaba da ita, sai dai baccin bai je ko ina ba, ta din ga jin numfashi a fuskarta.
A hankali ta buɗe idanunta, jin saukar numfashi a fuskarta, sai dai me, tayi tozali da fuskar Viper, ya kafeta da manyan idanunsa da suka yi jawur, dogon karan hancinsa yana taɓa nata, ko ƙiftawa ba ya yi.
A firgice ta yi ihu, ta faɗo daga kan gadon, jikinta na wata irin kyarma, tana jejjera numfashi, sai dai ta buge wurin ciwonta, dan har ya fara zubar da jini.
Sai da ta ɗago ta sake kallon gadon, sannan ta ga ashe filo ne yake taɓa mata hanci, sai ta ga kamar Viper.
Ta rintse idanunta tana addu'a, tare da dafe gefen cikinta da yake ta yi mata zafi.
Ɓangaren sumayya ma hakan take, dan kasa bacci tayi, dan ita kwanciyar ma gagararta ta yi, tayi dana sanin sha'awar fara aikin jarida, wace irin masifa ce haka tana zaman zamanta, ana neman mayar da ita ƴar ta'adda, saboda an fi ƙarfin ta.
Alwala ta yi, ta tayar da salla, ta din ga addu'a, tana fatan Ubangiji Allah ya tsare su daga sharrin honorable Indabo, mussaman Nabila da ba ta san wainar da ake toyawa ba, gashi a yau kawai an yi wasa da rayuwarta, ba tare da ta san hakan ba, nan gaba ba ta san me za su yi mata ba, kuma ta san muddin ta gaya wa Nabila, akwai ƙura dan za ta iya aikata abun da zai sanadin su rasa rayuwarsu gaba ɗaya.
Sai dai tana ta tunanin wace hanya Nabila ta bi ta ga Viper, tun da ta ce sun haɗu to lallai sun haɗu ɗin, hatsabibancin Nabila da taurin kanta, har tsoro yake ba ta. Tun da ta ƙududi aniyar yin sunan nan, idan ba wuƙa ta gani a maƙogwaronta ba, babu lallai ta haƙura.
Honorable Ma'aruf ne a tsaye yana ta zazzagawa Abdul masifa kamar zai ari baki, shi kuma sai cika yake yana batsewa yana harare-harare.
"Na fara gajiya da rashin mutuncinka Abdul, na gaji, gashi a banza ka nemo magana a wurin ƴar matsiyata, sun ƙi yadda a haɗa kai da su, a binne taiyar da ka shuka, dole sai na ɗau mataki a kai. In the next couple of years, kai zaka tsaya takarar deputy governor a garin nan, kamar yadda muka yi yarjejeniya da party, kafin na shiga, amma sai shashanci ka ke yi, so ka ke yi sai lokacin ya yi ƴan adawa, su ɓata mana shiri, na gaji da zubar da jini, saboda rashin hankalinka da wautarka, na ce ka yi aure ka ƙi, daga shaye-shaye sai neman mata, idan ma zaka yi yakamata ka san abun da ka ke ciki"
Abdul ya numfasa ya ce "Ka yi haƙuri, ni yakamata na goge wannan ɓarnar da kaina, ka karɓar mini address ɗin yarinyar, zan san abun yi"
"A baka ka je ka kuma yi wa mutane wani shirmen ko?"
Ya girgiza kai ya ce "No, na yi maka alƙawarin ba wani shirmen zan yi ba, zan goge komai ne kawai"
"Ɓace ka bani wuri" yayi maganar yana hakin baloƙoƙon da ya yi.
Nabila fa abu ya zame mata ga ƙoshi, ga kuma kwanan yunwa, wayar Viper ta zame mata larura, ta rasa yadda za ta yi.
Da safe Abba ya ce ta zauna a gida ta huta, saboda jikinta, amma ta ce masa ita ta ji sauƙi, fita za ta yi, da kansa ya ɗauke ta a mota, ya tafi kaita wurin aikin, suna tafe yana yi mata nasihohin da ya saba yi mata, amma da za a yankata, ba zata iya faɗar me yake cewa ba.
A gate suka haɗu da Director, yana ganin major kamar zai dungura, saboda risunawa cikin girmamawa, ya gaida major.
Ya amsa masa cikin girmamawa yana tambayarsa aiki.
Director ya amsa da "Aiki Alhamdilillah, yau kuma da kanka ka kawo ta?"
Major ya ce "To ya na iya, ƴar gudaliyata babu lafiya, kuma ta dage sai ta fito aiki. Ina fatan dai yanzu tana mayar da ka?"
Director yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, ta rage shiririta, tana aiki sosai ranar Alhamis ma za ta fita trial ita ce incharge of case ɗin"
Major ya ce "Masha Allah, idan ki ka yi wining, akwai special gift" Tayi murmushi kawai ta sauka daga motar, dan ba wani ganewa take yi ba.
A wurin aikin ma, jin ta ta din ga yi tamkar wadda ta shekara tana amai da gudawa, gaba ɗaya gaɓoɓinta a sage suke, da ta motsa, sai ta ga kamar za ta ga Viper a gabanta.
Layin Nasir ta kira, tayi sa'a ya ɗaga ya ce "Ya aka yi kuma?"
"Ka aika a bincika maka maganar mutumin nan ne?"
"Ki kwantar da hankalinki mana, ina sane zan aika".
"Ai kar ka zo ka ce ƙarya nake yi ne"
"Haba dai ni na isa ma"
"Yaya"
Ya amsa da "Na'am barrister Nabila maitama".
"Wane laifi Viper yayi na ƙarshe ne, aka rufe shi?"
"Ban gani ba a cikin record ɗin sa, waɗanda na gani dai, kawai rigima ce da mutane, da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi da kuma dillancin su".
"Wace kotu da wace kotu aka taɓa kai shi?".
"Arfa ban sani ba wallahi, wai menene akwai matsala ne?"
Ta kashingiɗa ta ce "No, babu wani abu sai anjima"
Ta kashe wayar ta ajiye, ta tashi ta tafi office ɗin Barrister Habib.
Bayan ta yi sallama, ya amsa mata, yana ƙura mata ido, har ta ƙarasa ta zauna.
Kai tsaye ya ce "Menene matsalar?"
Ta ce "Na yi kama da mai matsala ne?"
"Eh mana, yau ba kwalliya, ba ƙwalisa ba biscuit, ba sweet a hannu, duk yau dai sai a hankali"
Tayi murmushi ta ce "Barrister ka bani dariya, saka mini ido ka ke yi kenan, ka san jiya a asibiti na wuni, shiyasa ban zo ba jiya"
"Eyya, ai na zata mulkin ne ya motsa, ki ka ƙi zuwa, tun da ke ba tuhumarki ake yi ba, ba kya laifi"
Sake sunkuyar da kai ta yi tana murmushi.
Shi ma murmushin ya yi ya ce "Ina jin ki, meyafaru, dan ba kya zuwa office ɗin nan sai da dalili"
Ta gyara zamanta ta ce "Barrister, na san ka san wani ɗan daba da ake nema ko? Aminu Viper"
Yayi mata ƙuri da ido yana kallonta.
"Dama wani labari na ji, wai wani laifi ya yi aka kai shi prison, kuma kawai sai aka sake shi ba bisa ƙa'ida ba, gashi sai ɓarna yake yi a gari" sai kuma ta yi shiru.
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ina jin ki"
"To shi ne, sonake na san wani laifin ya yi, ban sani ba dan Allah ko zaka bincika mini, a wace kotun aka yi masa shari'a"
"Meyasa ki ke son sani?"
"Eh, sonake idan an kama shi, na bibiyi shari'ar da za ayi masa, kuma na binciki meyasa aka sake shi da"
Wata ƴar dariya ya yi ya ce "Nabila kwanan nan na ga you are so much serious, amma kin san hakan kamar tarar aradu da ka ne ko? Amma let's see how far you can go, zan bincika miki in sha Allah, nan da 3days zan neme ki"
"Na gode sosai babban yaya, Allah ya ƙare ka, na gode sosai da sosai"
Yayi murmushi tare da jinjina mata da hannunsa ya ce "Ki huta little barrister "
***
Can gidan su rahama kuwa, ta samu bacci, mamanta na tsakar gida tana ta shara, kasancewar ta mace mai son tsafta, jin motsi a bayanta, ya sanya ta waiwaya domin ta ga abun da yake faruwa.
Matasa ne su uku, zabga-zabga cikin shigar banza a tsakiyar tsakar gidan.
A tsorace ta ce "Lafiya kuwa? Meyafaru?"
Ya ƙarewa gidan kallo ya ce "Dama a nan ku ke rayuwa, ƙasƙantattun matsiyata, amma har ki ke fatan ganin an kai ni kotu an karɓowa ƴar ki hakkinta? Har wani hakki ne da ita? Talaka yana da wani hakki ne ko ƴanci?"
Cikin rawar baki ta ce "Waye kai malam?"
"Na yi miki kama da malam? Ni na yi wa ƴar ki fyaɗe, da ki ka tafi nema mata hakkinta?".
Sakin tsintsiyar ta yi, tana kallonsa, a ƙalla zai kai shekaru talatin da takwas, kallon idonsa ta yi babu mutunci ko imani a cikin su.
"Yanzu kai ka iya samun ƙwarin gwiwar zuwa gabana, ka gaya mini ka yi wa ƴa ta fyaɗe? Bayan ka turo mini waccan bayahudiyar ta yaudaremu, ba ta yi nasara ba, shi ne ka zo gabana ka gaya mini ka keta wa ƴa ta haddi?"
Ya fara takowa gabanta ya ce "Yes, na zo na ƙara kashe ƙishirwa ta ne, sannan in yaba wa baiwar Allah da Allah ya yi wa ƴar ki, kin iya haihuwa"
Yayi maganar yana wata irin dariya, a fuskar maman rahama, da tuni idonta ya fara zubar da hawaye.
Ya saka hannu ya riƙe ɗan kwalin kanta, haɗe da gashin kanta, ya tsuke fuska ya ce "Kin san ko ni waye, da ki ka saka na tako ƙafata wannan ƙazamin kucakin ƙauyen"
Ihu ta saki, saboda zafi.
Salim ya ce "Kai Abdul wannan yawa ne fa, ba wurinta mu ka zo ba fa"
"Bar ni Salim, duk da hausawa sun ce abun cikin ƙwai, ya fi ƙwai daɗi, what if na wajen ƙwan ya fi?" Yayi maganar yana riƙe rigarta.
Salim ya ce "No, kar ka yi haka, akuyanci kenan ai, dan Allah ka bari"
Abdul zai yi magana, suka yi ido huɗu da rahama, a tsaye a ƙofar ɗakin su, tana kallonsa.
Ayshercool
08081012143
15
🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*
*Ina masu buƙatar sayen nagartattun kayan magungunan mata, wanda babu cuta ko algus a ciki, ku yi joining link ɗin nan, domin samun nagartattun magungunan mata*
https://chat.whatsapp.com/BLqFsnlyNf0B483RhoWq8v
15
A take ya hankaɗe uwar a gefe, ya yi wa ramma wani irin miskilin murmushi, ya nufe ta yana wata irin tafiya, irin ta riƙaƙƙun ƴan iska ya ce
"Hi baby girl, long time almost 2months kenan fa ko?"
Hawaye ne ya fara bin fuskar ramma, jikinta ya hau rawa.
Ya sanya hannu ya dafa jikin bango, yana ƙare mata kallo ya shafi sumarsa ya ce "To ya ki ke, kin warke?"
Shiru ta yi ta sunkuyar da kai, tana tuna waccan ranar, da irin yadda ya keta mata haddi cike da zalunci.
Ya ce "Ohh, wai waccan ranar ce haryanzu ba ki manta ba ki ke kuka? Ya wuce ai wancan, kin bar ni da tsananin kewarki, duk ruwan da na sha komai sanyin sa, ya daina kashe mini ƙishirwa".
Ya kai hannu ya ɗago fuskarta, ya shafi hawayen da suke ta ambaliya a kan fuskarta.
Yinƙurawa mamanta ta yi da sauri, tana kururuwa ta ce "Kar ka taɓa mini ƴa, mugu azzalumi, wai babu wanda zai kawo mini ɗauki ne?"
Ya kalli su Salim ya ce "Ku saka mini matar nan a silent"
Haka suka rirriƙeta, suka ɗaure mata baki, suka shaƙa mata wani abu, a take jikinta yayi laƙwas.
Ya sake kallon ramma ya ce "An ce akwai unborn ɗi na a cikin ki ko? da gaske za ki haife shi kuma?"
Cikin kuka ta ce "Ban yafe maka ba, ka lalata mini rayuwa, ban sanka ban taɓa ganinka ba, ka biyo ni gida kana wulaƙanta mini uwa, dan bamu da kuɗi, Allah ya saka mini" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfin ta.
Salim ya sunkuyar da kai ya yi shiru, haka nan ya ji abun yayi masa wani iri a zuciyarsa, sauran matan da suke lalata da su, suke kai kan su, wannan kuma yarinya ce ƙarama.
Dariya ya yi ya ce "Dan kin ce baki yafe ba, ba zai hana ni shiga aljanna ba, kun ƙuduri aniyar neman hakkinku, duk da an yi muku tayin kuɗi kun ƙi, zan nuna muku ƙarfi da izzar kuɗi a ƙasar nan".
Ya danƙi hannun ramma, da jikinta ya ɗauki zafi sosai.
Tana ihu tana kiran mama, ya ja ta suka fice daga gidan, suka sakata a mota suka tafi da ita.
*****
Ɗan mama ne ya shiga ɗakin Viper, ya tarar da shi yana ta sintiri a ɗakin.
"Ka daɗe ka yi ƙarko uban gidana"
Viper ya tsaya cak, yana jiran ya ji me zai ce.
"Na yi aikin da ka saka ni, ya tafi yadda yakamata "
Ya kaɗa kai tare da yi masa alamar ya ƙaraso.
"Ina labarin malam lawan?"
"Kamar dai yadda ka ce, an kula da komai, sai dai babu wanda ya sake zuwa, gashi yanzu yana yawo a cikin unguwa".
"Madaki fa?"
"Shi ma kamar dai yadda ka sani, Honorable indabo yake yi wa aiki yanzu".
"Ina buƙatar isassun kayan aiki, a kwanakin nan zan dirar masa, mu ɓalla ƙarfe, sai dai mu yi mutuwar kasko, ayi wadda za ayi".
"Ba yanzu ba" suka ji muryar Walid.
Suka mayar da hankalinsu kan sa.
Walid ya ce "Viper da sauran lokaci, kai ka san madaki ba haka kurum yake daba ba, da zai kasu cikin sauƙi, da tuni mun kawar maka da shi, ka ɗan saurara tukuna"
A hasale ya ce "Ba zan saurara ɗin ba tukuna"
"Viper!"
Ciki ƙaraji ya ce "Walid ka ƙyale ni"
Walid ya girgiza kai ya ce "Da zan iya, da tuni na yi, mutumin nan ya fi ƙarfinmu ko ta ina, idan ka yi amfani da zuciya wallahi ba zamu yi nasara ba, ka bari mu bi komai a hankali mu lissafa, yadda ko mutuwar kasko ce mu yi"
Cikin ƙaraji ya ce "Ba zan jira ba, na gaji, na gaya maka na gaji. Na so bin komai a hankali, meyasa ka kawo mini yarinyar saboda me? ka san ka ƙara tunzara zuciyata yaya ka ke so na yi, so ka ke sai na haukace tukuna? Kalli yadda na koma walid, kalle ni, abun da nake ta ƙoƙarin dannewa ka fama mini, dan me zaka kawo mini wannan yarinyar sannan ka ce na nutsu how? Ta ɗauki wayata ta tafi, ka na da tabbacin hannun wa wayata za ta shiga? Idan aka tashi kama ni, kana da tabbacin su waye za su kama ni, idan na ƙare a haka ban aikata abun da nake ƙuduri ba fa? Ko dai ka nemo duk in da yarinyar nan take na kasheta, ko kuma a yau ba sai gobe ba, sai na yi gaba da gaba da madaki ko na kashe shi ko ya kashe ni, amma kafin nan sai na fara gaba da gaba da wancan dabban" tuni gumi ya tsatsttsafo masa, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, kafofin gashinsa ya bubbuɗe.
Walid ya taka gabansa a hankali, cike da shirin ko ta kwana, dan ya san ƙarshenta sai ya ba shi gwale-gwale, ko ya mangare shi.
Ya shammace shi, ya soka masa sirinji a damtsensa, kasancewar jikinsa babu riga, ya fara yi masa allura, sannan ya fara yi masa magana.
Walid ya ce "Na san na yi laifi, amma ka bari na gyara laifina da kaina, na san abun da ka ke ji ɗan uwa, ba kai kaɗai ka ke ji ba Al'amin"
Viper ya zubawa walid ido, ya rasa me zai yi, yana tsaye ya kashe masa jiki, ba zai iya komai ba, kasa tsayuwar yayi, ya tafi zai faɗi walid ya riƙe shi ya kwantar, ɗan mama kuwa dama tuni ya arce, dan yana tsoron a shaƙe shi.
Barrister Naja'atu ce zaune a katafaren ofishin ta, tamkar na matar gwamna, yana ɗauke da duk wani kayan alatu da ake buƙata.
Sannu a hankali take shafa screen ɗin wayarta, daga bisani ta saka wayar a kunnenta.
"Honorable, ka isa Abujan ne?".
Ya amsa da "Eh ma sauka"
"Ok, yaya maganar yarinyar nan da Abdul ya yi raping?"
"Yes, he handle the case himself, yayi maganin abun".
Ta ce "Ok, ina fatan ka ja masa kunne, kar ya je ya aikata wani shirmen da ba zamu iya gyarawa ba".
Ya ce "No, kar ki damu, zai yi abun da ya dace".
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, dama ina tsoron ya yi wani shirmen ne, amma tun da ka ce haka, shikenan"
Ta katse wayar, ta mayar da hankalinta kan sakatariyarta da ta shigo.
Cikin gyatsine ta ce "Ke kuma ya aka yi?"
"Kin yi baƙi ne ma"
"Suwaye?"
"Eh to, da alama dai ƙorafi suka kawo, ke suke.....
"Ke bani da lokaci, ayyuka sun yi mini yawa, su ganki ko wani daban, hutawa nake buƙata, wannan jaraba a uzzurawa rayuwarka, london zan wuce ma ni this week na je na huta. Ki fita ki je ki sallame su" ta juya jiki a sanyaye ta bar office ɗin.
Salim ya kalli Abdul da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana shan giya a cikin wine cup ya ce "To wai yanzu ya zaka yi da yarinyar nan da ka kawo ka ajiye, Ga abun da aka tsara, kai kuma ga abun da ka yi?"
Ya ɗan girgiza giyar a cikin kofin sannan ya ce "Gani na yi za ta ci bulus idan ta tafi a haka, sai na gama moreta zan aikata kawai"
"Amma ba ka ganin, hakan zai iya kawo matsala, yanzu ko a nan gaba?"
Ya girgiza kai ya ce "Ba wata matsala, na ɗan lokaci ne, zan gama abun da zan yi da ita, zaka iya tafiya ma kawai"
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan"
Sannu a hankali ta buɗe idonta, ta din ga gani dishi-dishi, ta kasa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 121