wani irin ihu da Viper yayi, sai da wasu suka fara gudu, ya daki katakon gabansa da ƙafarsa ya ce "Ƙarya ne, jauhar tana nan a raye, gobe zata haihu, matata bata mutu ba"
Da ƙyar aka danne shi, Alƙali ya aika shi gidan prison, tare da ɗage shari'ar.
Haka ya cigaba da buge-buge, tamkar zai jefar da motar gidan yarin, sai da suka sumar da shi, sannan suka samu nutsuwa.
Tun daga wannan ihun, bai sake magana ba, ba cin abinci, sai dai zai yi salla kawai.
Har aka yi zama na biyu a kotu, bai ce uffan ba, duk wasu hujjoji Bunkure ce ta samar da su, lawyern gwamanti gabatarwa kawai yake yi.
Sai dai juyin duniya, ya yi magana, yaƙi yi.
Bunkure ta je gaban Al'amin ta tsaya ta ce "Amsa ɗaya kawai kotu take buƙata daga bakinka, kai ka kashe matarka jauhar?"
Ya ƙura mata rinannun idanunsa, ta din ga yi masa wani irin kallo, mai cike da rainin wayo.
Ya jinjina mata kai alamar eh.
A nan suka buƙaci a ƙarƙare shari'ar, ba tare da wata huɓɓasa ba, lawyern Al'amin, ya ce ya yarda da duk abubuwan da masu gabatar da ƙara suka gabatar. Daga haka aka sake ɗaga shari'ar zuwa wata guda.
Wata gudan da sai da ya shafe shekaru biyar a prison, ba a cigaba da shari'ar ba, ba kuma a sallame shi ba.
Kullum burinsa shi ne ya farka daga mafarkin nan da yake yi, shi dai ya san matarsa na raye, ba ya cin abinci baya iya bacci, ya koma tamkar mahaukaci.
Sai dai lokaci zuwa lokaci yana yi musu ihu, da kiran matarsa, ya kan kira sunan madaki da Indabo.
Lokaci lokaci, ya kan ga aiken abinci, hakan ya sanya ya ƙara sakankancewa jauhar ce ke yi masa aike, bai sake ganin wani yazo wurinsa ba, tsawon shekaru biyar ɗin nan.
Rana tsaka aka ce masa ya fita ya tafi gida an sallame shi.
A ƙofar prison ɗin ya tsaya, yana tuna lokacin da ta zo tafiya da shi, lokacin da aka rufe shi, aka ce an kama shi da cocaine.
Bai tsaya ko ina ba, sai unguwarsu, da ƙafa ya taka ya tafi, amma ya tarar da gate ɗin a rufe.
Sai yayi tunanin ta koma gida ne, dan haka sai ya fara tafiya gidansu, dan tabattar wa.
Gidansu ya fara zuwa, rahila da yaranta, gaba ɗaya suka dare, suka gudu ɗaki tana ihu ta ce "Ka fita ka kore shi, gashi can an sako shi, Allah wadaran yan siyasa, sun sako masifa da annoba, wanda bai san halacci ba".
Abbu ya fito ya kalli Al'amin, ya koma kamar wani mahaukaci, a gigice ya nufo Abbu ya ce "Abbu, ina jauhar? Ta haihu ne? Ina abun da ta haifa?"
Abbu ya ja da baya ya ce "Kar ka matso kusa da ni, Jauhar tana gidan uwarka da ubanka, dama ka gaya mini zaka kasheta, kuma ka cika alƙawarin ka Al'amin, na gode da muguwar sakayyar da ka yi mini, da ɓata mana sunan zuriya. Ka fita babu ni babu kai, ka nemi wani uban bani ba, na sallamawa duniya kai, ba zan cigaba da rasa makusantana, mutanen da nake ƙauna ba saboda kai, ka je na yafeka a duniya"
"Na ji na yadda, amma ina jauhar? Sun ce idan na ba su abun da suke so, zasu kai ni in da take"
"Sai dai ka bita kabari ka ɗauki ɗan naka, mara mutunci, ka fita ka bar mini gida, bana ƙaunarka bana ƙaunar ganinka"
"Ba zai yiwu ba, wallahi sai kun fito mini da matata" ya juya ya fita da gudu, ya tafi dabar su, incomplete building ɗin da suke zaman shaye-shaye.
Su Walid suna ganinsa, suka rirriƙe shi suna kuka, ya watsar da su ƙasa, ya ce "Walid, ina jauhar? Na san ta haihu ko?"
Walid ya tashi tsaye ya ce "Viper ka nutsu mana, ya aka sako ka ne? Ba yadda bamu yi ba, a ƙarasa shari'arka mu ɗaukaka ƙara aka ƙi"
"Dalla ina tambayar ku, ina jauhar, ko ta koma gidansu, ku bani kaya na canza na je wurinta, na san hanata ganina aka yi"
Hawaye na zuba a idon liti ya ce "Viper, Ƴar madara fa ba ta raye, ta rasu"
Al'amin yana zuwa nan a maganar, yayi shiru, yayi fatali da kayan gabansa, ya fara wani irin haki, yana nema ya kurma ihu.
Nabila tana kuka, ta toshe masa baki tana girgiza masa kai.
Ya saka hannu, ya cire hannunta daga bakinsa ya ce "Ban cancanci na haukace ba? Ban cancanci na nemi fansa ko ta wane hali ba kenan?"
Nabila ta girgiza masa kai, kuka ya hanata magana.
"Na kashe matata, ni na kashe jauhar ɗina, halittar da ta nuna mini tsantsar so da ƙauna"
"Ba kai ka kasheta ba"
Cikin tsawa ya ce "Ni ne, ni na kasheta. Meyasa da Abbu ya ce mini zai yi mini aure, na ce zan kasheta, ya ce mini Allah ya taimaka? Meyasa na kasa tuba na daina bangar siyasa da daba, a lokacin da zabra take ta ankarar da ni illarta, mai yasa sakamakon laifina ya faɗa kan matata?"
"Astagfirullah, Viper kar ka yi saɓo"
"Meyasa ban karɓi ƙaddarata ba tun da farko, na furta idan aka yi mini aure zan kasheta? Meyasa na jinkirta barin aikata laifi, sai da na rasa mutane masu muhimmanci a sanadin daba da shaye-shaye. Daba da bangar siyasa ta yi mini mummunan tabo, na kasa zubar da hawaye ko sau ɗaya tsawon shekarun nan, meyasa ba zan haukace na huta ba.
Ina son matata, laifina ya shafe ta, ba ta ji ba bata gani ba, na kasa yadda ta mutu, haryanzu ina ganinta ina ganin ɗana a jikinta. Ko ban ɗauki fansa ba, ina fatan na haukace, ko na bita na huta. Ina ma jauhar ba ta sanni ba, da yanzu tana nan tana rayuwa cikin farin ciki, bani da sa'a ko kaɗan a rayuwata, duk wanda na saka sonsa a raina, sai Daba da bangar siyasa tayi masa illa"
Huci yake yi, idanunsa suka rine zuwa ja mai ban tsoro.
Ta sake mayar da hannunta bakinsa, ta rufe masa, tana kuka ta fara furta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Astagfirullah wa atubuilaihi"
A hankali ya fara maimaitawa shi ma, jikinsa na kyarma, kamar wanda ake kaɗawa gangi.
Nabila ta ce "Ka yi i ajiyar zuciyan da kake dannewa" ya kama ɗaya hannun nata, ya ɗora saitin zuciyarsa, yana wani irin haki, wani irin bugu zuciyarsa take yi mai ban tsoro.
A take ya saki wata irin nannauyar ajiyar zuciya, tare da hawayen da suka maƙale a tsakiyar zuciyarsa tsawon shekaru shida!
Ayshercool
08081012143
58
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Cikin matsanancin tashin hankali, Nabila tana kuka ta ce "Viper zuciyarka fa, dan Allah ka nutsu zata daina aiki, idan ta cigaba da bugawa a haka, ka cigaba da istigfari da maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un" tayi maganar cikin damuwa, ƙara danna hannunta yayi a kan ƙirjinsa, yana wata irin shaƙuwa mai haɗe da haki, numfashin sa na fita sama-sama.
A jejjere zuciyarsa take bugawa da ƙarfin gaske.
Cikin tausayawa take kallon sa, Al'amin yana buƙatar kafaɗar da zai kwanta yayi kuka, babu wanda ya fuskanci ainihin matsalar sa, kowa ɗora masa laifi kawai yake yi, iftila'in da ya faɗa masa, kowa ya dare ya bar shi, sai abokansa duk da suna iya ƙoƙarin su a kansa, amma ba abun da yake buƙata suke yi masa ba.
Ji tayi ina ma tana da damar, da zata rungume shi, ta bashi dama yayi kuka yadda yake so, ko zai samu afuwa a zuciyarsa, tsawon shekaru shida, yana dakon baƙin ciki da damuwa, kuma ya kasa zubar da hawaye sai a wannan lokacin.
Haka yayi shiru ya sunkuyar da kai, sai dai bai saki hannunta ba, hawaye ne kawai yake zuba daga idonsa, taya shi take yi, sai dai ta rasa me ma zata kuma ce masa, a tsorace take da kar zuciyarsa ta buga.
A hankali ya saki hannunta, ya goge hawayen sa, ya tashi zumbur, ya tattare kayan ya mayar ɗakin, hatta kayan jauhar suna nan, lokaci lokaci, su Walid ne ke zuwa su karkaɗe gidan su share, dan idan ya bushi iska yana zuwa cikin dare, yayi ta tuna irin rayuwar da suka yi.
Yanzun ma yana shiga ɗakin, ƙwaƙwalwarsa ta nuna masa ita zaune a kan gado, tana shirin dutse, gefe ga boti a kusa da ita a kwance, ya mimmiƙe yana ta goge jikinsa.
Ta ɗago ta kalleshi tana murmushi ta ce "Manya gatan wasa, me ake so ne ake ta kallona? Ko fankar ce?" Tayi maganar tana kashe masa ido.
Gadon ya nufa da hanzari ya kai hannu ya riƙe ta, amma ya ga pillow ne kawai a wurin.
Ya dafe hannunsa a wurin, daga baya ya fito jiki a sanyaye ya ce "Mu tafi" Nabila ta saki niƙabinta tana ta kuka, suka nufi hanyar fita, ya gyara facemask ɗin sa suka fita.
Yana fita yaga wasu daga magidantan layin, a ɗan tsaitsaye, suka yi ido huɗu da malam lawan, ya zura da gudu ya shige gidansa, ya rufe ƙofa.
Ya danƙi hannun Nabila ya din ga sauri da ita, maimakon su bi titi, lunguna suka din ga bi, suna tafe yana haki, yana dafe ƙirjinsa.
A dai-dai wata kan kwana, ya saki hannunta, ya danƙo wani mutum da yake zaune yana jin radiyo, yana cin karas, zuwa wani lungu.
Nabila ta ce "Me yayi maka shi kuma?"
Ya zaro iraƙi a ƙugunsa, ya saita masa a maƙoshinsa, ya ce "Bani wayarka"
Jiki na rawa, ya ciro wayar, ya miƙa wa Viper.
"Ka janye mini mutanenka, zan yi walƙiyya, idan ba haka ba, zan yi maka rami a maƙoshinka"
Mutumin ya diririce, ya ce "Ban gane me ka ke nufi ba"
Ya ɗaga mutumin ya haɗa shi da bango da ƙarfi, ya ce "Ka janye mini mutanenku zan tafi, idan na kuma magana, hanjinka zan naɗo da wuƙar nan"
Mutumin ya ce "Ya aka yi ka gane ni, ka san identity ɗina?"
"Saboda tsohon mai laifi ne ni, ba yau na fara aikata laifi ba" yana ƙoƙarin zira hannu a aljihu Viper ya riga shi, ya ciro bindigar da take aljihun mutumin ya ce "Ka yi abun da na ce, ko na harbe ka"
A razane Nabila ta ce "Viper bindiga ce fa, dan Allah kar ka yi wani laifin mu shiga uku" bai kulata ba, ya sake saita mutumin da bindiga.
Ya saka wayar a kunnensa ya ce "Zaku iya tafiya, we missed the target" ya katse wayar ya ce "Sai ka bani bindigata na tafi"
Viper ya ce "Ɗaga hannunka, ka wuce mu je" ya tasa mutumin a gaba, tamkar ya kamo mai laifi, yana gana suna bin sa a baya, da ya motsa sai ya ji Viper ya ce "Idan ka waiwayo zan fasa kanka da bindigar nan" haka suka yi doguwar tafiya a haka, sai kuma ya ji shiru.
Ya waiwaya, ya neme su ya rasa, a rikice ya bi hanya, saboda bindigar sa da take hannun Viper.
Yana shan wata kwana, ya ga abokin aikins a tsaye da bindigar a hannunsa.
"Gata, tun da ya ritsaka nake biye da ku, a hanya ya yar da ita, suka yi wani wurin, nayi ƙoƙarin bin su, amma ban cim musu ba".
"Ohh shit, meyasa ba ka yi making wani move ba, wannan ai shirme ne kayi"
"No, kar ka gargaɗe mu a kan haka, ka ce sai abun da ka ce, kai ka ke son ka kama shi da kanka"
Ya fesar da iska ya ce "Kuma haka ne, amma gayen nan ya bani mamaki, na rasa ya aka yi ya gane ni a cikin fararen kaya.
Kaga fuskarsa?"
"A'a sir, fuskarsa a rufe take ai, ban ganshi ba, ni bayansa ma kawai na gani".
"Na so naga kammaninsa, ko wataran zamu sake haɗuwa, suma informer's ɗin banzaye, da ba su sanar da wuri ba. Yi shiru ga oga Nasir yana kiran waya"
Ya saka wayar a kunnensa ya ce "Hello sir"
"Ya ake ciki ne?"
"We miss the target sir"
Nasir ya ce "Kamar yaya?"
"Kafin mu je, ya bar unguwar, bamu tarar da shi ba"
Nasir ya numfasa ya ce "Shikenan, ku dawo mu haɗu a office, sai mu sake shiri"
"Ok sir" ya kalli abokin aikinsa ya ce "Mu je,ya ce mu koma office"
Viper kuwa wata hanyar ya bi, suka ɓulla can wata unguwar daban.
Sai dai suna tafe yana ta haki, yana haɗa hanya.
"Viper mu tsaya ka huta, kalli halin da kake ciki, ko mu samu wani asibiti a duba ka, kar numfashinka ya ɗauke" bai ko nuna ya san da shi take ba, sai da suka fita titi ya saki hannunta ya ce "Ki koma gida"
Cikin damuwa ta ce "To kai kuma fa?"
"Ki tafi nace" yayi maganar da kyar, kawai ya tare wani mai napep ya shige ya tafi.
Jiki a matuƙar sanyaye, ta koma chamber ta ɗauki motarta, ita kanta ta san ikon Allah ne ya kaita gida, amma kusan gaba ɗaya ba ta hayyacinta, tarin damuwa ce kawai cunkushe a ranta.
Ba ta san yar madara ba, ba ta taɓa ganinta ba, amma ƙarshen labarin ya tsaye mata a rai, da wayonta ba a taɓa yi mata mutuwar da ta gigita ta ta ji ta ba, sai dai jin wannan mutuwar ta gigita ta, ta ɗaga mata hankali. A cikin zuciyarta take jin ƙaunar matar da ba taɓa gani.
A wannan karon ma tayi kuka mai isarta, ga uwa uba, tausayin mai gayya mai aikn wato Al'amin, dan ita yar madara ta mutu ta huta, amma shi da blame ɗin ya dawo kansa, shi ne babban abun a tausayawa. Wayoyinta suka isheta da ringing, ta kashe su gaba ɗaya ta ajiye.
Ta din ga fatan Allah ya mayar da Viper maɓoyarsa lafiya, dan ta tsorata da mummunan yanayin da ya shiga.
Sannan haryanzu labarinsa da saura, ba duka bane ba, amma tana fargabar sake matsa masa son jin ƙarashen labarin, dan gudun kar ya sake shiga mawuyacin hali kamar yau.
Tana ta saƙe-saƙe, sumayya ta yi sallama, ƙasa-ƙasa ta amsa, sumayya ta shiga ɗakin tana mita. "Malama kin ce mini zaki zo, amma kin shanya ni, bayanai ne suke ta fitowa a kan mutuniyar ki, ina son ki gana da mutanen direct, na haɗa ku, amma ki ka ƙi zuwa"
Ji tayi Nabila tayi mata shiru, ta ce "Arfa meyafaru ne? Kamar kuka ki ka yi fa"
"Kuka nayi sumayya"
Cikin rashin fahimta ta ce "Kukan me kuma? Ko duk a kan shari'ar ne?"
"Sumayya komai ma, yakamata nayi kukan ne kawai"
"Arfa yakamata fa ace kin san kin girma, haba abu kaɗan sai kuka, ki din ga miƙa wa Allah lamuranki mana haba Arfa".
"Arfa, Arfa" suka jiyo muryar Nasir yana ƙwala mata kira.
Tayi shiru bata amsa ba, ya shigo ɗakin, ya tarar da ita a zaune, ta jingina da gado.
"Ina magana ki ka yi mini shiru?"
Ta ce "Kaina ne yake yi mini ciwo"
Sumayya ta ce "Yaya ina wuni?"
Ya amsa da "Lafiya ƙalau sumayya, ya aiki?"
"Alhamdilillah"
Ya sake mayar da idonsa kan Nabila ya ce "Waye mutumin da ya zo wurinki ɗazu a Office ɗin ki?"
Ta ɓata fuska ta ce "Na gaya maka client ɗina ne ai"
"A'a arfa, na tambayeki wani irin case ne zaki tsaya masa, kin ce is confidential ban san lokacin da muka fara ɓoyewa juna abun da ya shafe mu ya shafi aiki ba. Mutumin nan yayi kama da masu aikata miyagun laifuka, duk da ban ga fuskarsa ba"
Ta girgiza kai ta ce "Allah ya kiyashe ni hulɗa da masu aikata laifuka, sai dai ko da mai laifin ne, a matsayina na lawyer babu ruwana da laifin sa, zan bashi kariya ne kawai. A wurinku ne ku ke kama mai laifi, a wurin lawyer babu ruwansa da mai laifi ko akasin haka, client ɗinmu ne a gabanmu ba laifinsa ba".
Ya tsaya yayi shiru yana kallonta "Ban gane me ki ke nufi ba"
Tayi murmushi ta ce "Ba wani abu da nake nufi yaya, aikinku kamo mai laifi, mu kuma namu aikin binciko gaskiya komai ɗacinta"
Ya jinjina kai ya ce "I see, ɗazu informer's ɗin mu sun sanar da mu Viper ya je gidansa, da shi da wata da ba a san ko wacece ba, sai dai kan jami'anmu su je, ya bar unguwar" duk da ƙirjinta yayi dumm. Amma cikin iya siyasa ta ce "Ikon Allah, lallai wannan Viper akwai shu'umi, ya cika macijin gaske, wato lokacin da ya ga dama, sai ya baro raminsa ya fito shan iska, to Allah ya shirye shi. Amma ya batun abokinsa da kake bibiya?"
Nasir ya ce "Nothing much, ya daina zuwa unguwar ma kwata-kwata, abun har mamaki yake bani, da mun hari wani abu da muke son mu kama shi, sai abun ya kuɓuce mana, amma muna nan muna ƙoƙari"
Nabila ta ce "Gaskiya abun da mamaki, Allah ya yi jagora"
Ya amsa da "Amin, Sumayya ki din ga yi wa yar uwar nan taki faɗa, bata ji ko kaɗan tana neman zunguro mana sama da kara, kasadarta tayi yawa sosai"
Sumayya ta ce "Ana yi mata fa yaya, ka san halinta da kafiyar tsiya ne, amma zata daina in sha Allah"
Ya jinjina kai ya ce "Allah ya sa" bayan ya fita Sumayya ta ce "Arfa, waye yaya yake magana a kai, ina fatan dai ba wani mai laifin bane ba, ko kuma wani abun ki ke shirin ɗaukkowa ba"
Nabila ta kalleta ido cikin ido ta ce "Kina son na ce miki viper ne, ki je ki ji daɗin gaya wa waɗanda ki ke ba wa information a kaina?"
Gaban sumayya ya faɗi ta ce "Information a kan ki kuma?"
"Eh mana sumayya, ana bibiyata ta hanyarki, kina bibiyar duk activities ɗina kina sanar musu. To ki gaya wa ko suwaye suka saki, wallahi babu yadda suka iya da ni, gaba da gaba za su yi da ni, su karɓi abun da suke so daga wurina, ba wai su fake da ke ba kina ba su information a kaina ba"
"Nabila waye ya gaya miki haka?"
Nabila ta ce "Jira ki ke yi a gaya mini? Ni na ganoki, sai dai na kasa yadda saboda ƙauna ba ƙarya ce ba, kuma wanda ya gaya mini ba zai yi mini ƙarya ba, dan bai sanki ba, balle ya san alaƙarmu da ke. Please sumayya You can leave, ko ganinki ba na son yi wallahi" Sumayya ta ce "Nabila, ki tsaya mu fuskanci juna dan girman Allah"
"Babu wata fahimtar juna da ta rage tsakanina da mai fuska biyu, ni da gaske na yarda da ke, ba zan bari a cutar da ke ba, mussaman ayi amfani da ni a cutar da ke ba, amma ke gashi ana ƙoƙarin cutar da ni ta hanyar ki. Koma waye yake bibiyar tawa, ki ce masa ya fuskance ni ya gaya mini abun da nayi masa. Idan kuma a kan ayyukan da na saka a gaba ne, babu wani mahaluki da ya isa ya hana ni abun da nayi niyya, ki tashi ki tafi"
Sumayya ta miƙe tsaye, kawai ta ɗauki jakarta ta fita, tana tafe a hanya tana kuka, sam ba ta san da wasu kalamai za ta yi amfani ba, wurin fahimtar da Nabila ba, sai dai tayi mamakin gaske, a kan wanda ya gaya wa Nabila cewa ana bibiyar ta, da Nasir ne ya gaya mata, to da tabbas sai yayi zancen yanzu a gabanta, kuma sai ya tuhume ta, amma sai dai bai yi hakan ba.
Bayan tafiyar sumayya kuwa, Nabila ƙanƙame pillownta tayi, tamkar ta samu viper, ta cigaba da zubar da hawaye.
Viper kuwa a galabaice ya ƙarasa gidan da suke, gaba ɗaya nema yake ya fita hayyacinsa, haki kawai yake yi, zuciyarsa na cigaba da wannan matsanancin bugun.
Ɗan mama ne kawai a gidan, ya tashi ya riƙo Viper cikin tashin hankali, ya shiga da shi ɗaki, ya kwanta a kan katifarsa, ya cigaba da ajiyar zuciya, yana haki, ga wani abu da yaƙi gaba yaƙi baya a tsakiyar ƙirjinsa.
"Oga Viper, meyafaru ne? Baka da lafiya ne? Meyake damunka?" Ya jejjerawa Viper tambayoyin, amma babu guda ɗaya da ya iya amsa masa, ya lumshe idanunsa ya na ta sauke numfashi.
Cikin sauri, ɗan mama ya kira Walid a waya, ya sanar masa halin da Viper yake ciki.
Walid ya ce "Ka kula da shi, kar ka bari ya sake fita, gani nan zuwa"
***
Madaki ne zaune a cikin dokar daji, a gaban wani mutum da shi da yaronsa lakwari.
Ya miƙe ƙafarsa da ciwon jikinta yayi rami, mai zurfi, sai wani irin kore ruwa ne yake fitowa, wurin ciwon ya kumbura suntum babu kyawun gani ko kaɗan.
Mutumin ya ƙare wa ƙafar kallo sannan ya ce "Ya riga ya yi maka illa, tabbas yana da makarin asirinka, dan kuwa ya karya shi ɓara, wuƙa da kaifi, za su din ga tasiri a jikinka. Cikin tashin hankali da damuwa madaki ya ce "Yanzu babu wani abu da za ayi a kai, idan ya so a kuma bani wani asirin?".
"Gaskiya babu, yanzu dai magani zan baka, aje a haɗa shi da diddigar maƙera, ka yi kwana arba'in ana sakawa ciwon, sai ya warke sai kuma mu ga da abun da zamu ɗora".
Madaki ya yi shiru, saboda baƙin ciki, lokacin da aka bashi asirin, an tabattar masa da babu wani wanda yake da laƙanin karyewar asirin, sai shi wanda ya bashin, wanda yanzu ya mutu sai ɗan sa yanzu dan kuwa shi kansa ɗan ma bai san makarin asirin ba, dan haka sun yi mamakin yadda aka yi Viper ya samu.
Sun kamo hanyar dawowa kano, madaki ko iya magana baya yi, babu tunanin da yake yi, da ya wuce wani mataki zai ɗauka a kan Viper, dan kuwa karya asirin nan, dai-dai yake da karya alkadarinsa baki ɗaya.
Kiran P.A ne ya din ga shigowa wayar Madaki, sai da yayi da gaske sannan ya ɗaga, domin kuwa gaba ɗaya ransa a jagule yake saboda tashin hankali, da fargabar halin da zai shiga, idan aka fuskanci Alkadarinsa ya karye.
"Madaki, ina ka shiga ne, yau kwanaki kusan huɗu wayarka ba ta shiga, distinguish ya bayar da muhimmin aiki da kai kaɗai ne zaka iya yin sa"
Madaki ya yi ajiyar zuciya ya ce "Aikin menene?"
"Idan kana gari ka shigo"
Madaki ya ce "A'a, na ɗan yi wani balaguro ne"
"Duk in da ka ke ka dawo, honorable ya matsa a kan lallai a kama viper, yarinyar nan yake so a ɗaukko masa"
Madaki ya ce "Wace yarinyar kenan?"
"Wata lawyer ce, wadda na fara yi maka zancen nan"
Madaki yayi wani huci, ya ce "Bari na shigo garin, zan yi maka magana"
P.A ya ce "Wai madaki lafiya kuwa? Kamar ba ka da karsashi, meyake faruwa ne?"
"Basar ka ɗauke tunaninka a kan hakan, zan faso idan na shigo gari" ya katse kiran yayi shiru yana tunani, tabbas ta bakin Al'amin daga lokacin da suka ga ya daina yi musu amfani zasu watsar da shi.
***
Nabila ta kira layin Viper ya kai sau biyar, dan ta ji halin da yake ciki, amma ba a ɗagawa, har ta fitar da ran zai ɗaga ta ji an ɗaga wayar.
"Haba master, ka barni cikin zullumi da tunanin halin da kake ciki, ka ƙi ɗaga wayata".
"Walid ne"
"Oga walid, yana ina dan Allah?"
"Gashi muna ta fama, jiki ya rikice gaba ɗaya".
Cikin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wani abun ne ya same shi ne?"
"Ke zamu yi wa wannan tambayar, dan babu yadda bamu yi da shi ba, ya ce sai ya fita, wurinki zai zo, zai yi wani aiki, mun yi iya ƙoƙarin mu mu hana shi, amma ya ƙi saurarenmu, ko kin yi masa wani abu ne ki gaya mana dan Allah"
"Wallahi Allah kenan, ban yi masa komai ba, office ɗina ya zo ɗazu....
Walid ya katseta ya ce "Office kuma? Ya ce kiranki zai yi a waya ku haɗu"
"A'a zuwa yayi, yayi amfani da wayata da computer ta ta, daga nan ya ce zai ƙarasa mini labarin da ka fara bani, har gidansa muka je" ta yi wa walid bayanin yadda aka yi.
Walid ya ce "To ki tayamu addu'a, jiki ya rikice, ɗan sakewar da yayi kwana biyu, ta gushe ya koma yadda yake a da. Salla kawai yake yi a kwance tun da ya dawo, sai dafe ƙirjinsa yake yi yana haki".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Oga walid da ka ƙarasa mini labarin nan, duk da haka bata faru ba, da na san halin da zai shiga kenan, da ba zan takura masa ya gaya mini ba. Ubangiji Allah ya kawo masa mafita, Allah ya bashi lafiya, ba zai yiwu na fito yanzu ba, dan Allah ku
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 61 Chapter of 121