da murtala.
Saboda bayan kasancewar ta sananniya, tayi ƙoƙari wurin samar da sabbin shirye shirye masu ƙayatarwa, wanda za su tafi dai-dai da matasa da ma dattijai baki ɗaya. Wasu daga cikin abokan aikinta da ta baro a can, suka din ga yi mata magiyar suma ta samar musu gurbi a in da ta koma, suma su koma. Yanzu sumayya ba ta da fargabar ta samo rahoto, a kushe ace mata ba irinsa ake buƙata ba, saboda kawai bai yi dai-dai da abun da wasu suke son ji ba.
Ranar farko da suka gabatar da program ɗin ƙeƙe da ƙeƙe ita da Nabila, program ɗin ya yamutsa hazo, dan tayi sukuwa tayi zamiya, ta ƙarewa bunkure foundation ta tas da hukumar shari'a, tayi bayanin yadda shari'ar baba mai gadi ta kasance a kotu, tare da jaddada idan har da gaske dan al'umma suke ayyukansu, ya zama dole a bayyana ina ramma take, idan kuma da gaske tana asibiti, a bawa lauyoyi da ƴan jarida damar zuwa su ganota, kuma a kawo bayanin likita a kan abun da yake damunta zuwa lokacin da aka gaza ganinta a gaban kotu.
Hatta lauyan gwamanti ta din ga challenging ɗin sa, a yadda suka din ga taka doka yadda suke so.
Nan fa mutane suka din ga tururuwar kiran waya, wasu suna sharhi, ciki har da wani lauya mai zaman kansa, da ya kira waya, ya tofa albarkacin bakinsa tare da tabattar da akwai jabun lauyoyi da suke yi wa doka hawan ƙawara, a yi cuwa-cuwa a danne hakkin mai ƙaramin ƙarfi, a wanke yaran masu ido da kwalli, ire-iren foundations ɗin bunkure suna da yawa. Ya ƙara faɗaɗa bayanan da Nabila tayi, tare da fito da wasu abubuwa ma da ita hankalinta be kai, kai ba.
Nabila ta ji daɗin program ɗin sosai da sosai, dan kuwa ji tayi, zuciyarta ta rage raɗaɗi da baƙin cikin abun da aka yi musu a kotu.
Bayan kammala program ɗin, still cigaba da kiran wayar a aka yi, ƙarshe sai kashewa suka yi.
Sumayya ta ce "Mutuniyata kin yi bala'i fa"
Nabila ta ce "Ke ni ɗin ta wasa ce? Ai sai Najar bunkure ta zubar da hawaye, yanzu ta ƙarƙashin ƙasa zan yi analysis nawa ƙungiyar take samu na tallafi a wata, da kuma abun da ake spending wurin tallafwa mutanen da ake iƙirari. Ni ɗin fa ba ta wasa ce ba"
Sumayya ta ce "Ba wani ta wasa ko ba ta wasa ba, dole mu daga da Addu'a fa, Allah ya tsaremu Masoyiyya"
"Amin dai, amma yanzu meye abun yi?"
Sumayya ta ce "Eh to, kamar yadda ki ke tunanin kawo ƙarshen bunkure, ni kuma sonake na ci uban indabo, duk da ya fi ƙarfina, amma zai ga abun da 'yar matsiyata zata iya yi, dan wallahi sai na kusa girgizo shi daga kan kujerar nan"
Nabila ta kwashe da dariya ta ce "Me yayi miki ne, ki ke wannan alwashin?"
"Zagin cin zarafi yayi mini, lokacin da ya ce na din ga bibiyar masa ke, kin san na taɓa zuwa na bayar da wani rahoto, a kan cewa an ce an yi wani aiki a yankinsa, kuma da na je ban tarar an yi ba, kin ga abubuwan da aka yi mini a kan hakan? Program ɗin da zamu din ga yi da yaya murtala, irin su Indabo zamu din ga bankaɗawa asiri. Zamu faɗi abun da suke karɓa na consituency project duk wata, da kuma ayyukan da suka gabatar a watan, daga nan ya ragewa al'ummar yankin da ake wakilta, su yanke hukuncin da ya dace"
"Allah ya ƙara lafiya, ƴar gwagwarmaya amma shirin ya ƙayar da ni, Allah ya taimakemu ya ƙarfafi gwiwarmu masoyiyya. Abun mamaki shekarun baya bamu taɓa tunanin samun wannan damarmakin ba, sai dai mu yi ta dama dama"
"Haka lamarin Allah yake, yanzu ya ara mana damar da muka roƙa, ya rage namu mu yi abun da ya dace da ita"
"Haka ne, Allah ya taimake mu ya bamu sa'a" suka ce Amin.
Ko da ta koma gida, Walida ce ta fara tararta ta ce "Arfa, yanzu muka gama jin program ɗin ku, live ku ka yi shi, kina ta ɓarin maganganu ko tsoro ba kya ji"
Nabila ta ce "Walida, wanda bashi da gaskiya ai shi ne yake tsoron a faɗeta, bamu fara dan mu daina ba"
"Zaki ga baki fara dan ki daina ba, yaya ya shigo a ƙalla sau uku yana nemanki, ya kira wayarki ma, kin ƙi ki ɗaga"
"Duk a kan program ɗin da na yi"
Walida zata bata amsa ya shigo, fuskarsa babu annur ko kaɗan.
Ta tsaya tana kallonsa, ya ƙaraso gabanta ya kalleta ya ce "Arfa ba zaki taɓa yin hankali ba ko? Meyasa ki ke son yin wasa da rayuwar ki ne?"
"Dsp, rayuwa ta ka ce ai, nikaɗai nake abuna ai, shiyasa nake takatsantsan kar baya tawa rayuwar, na saka ta wani a hatsari"
"Zaki rufe mini baki, ko sai na kwaɗa miki mari, ni kike gaya wa ba kya saka rayuwar wani a hatsari? Duk tayar mana da hankalin da ki ke yi ba kya gani, yadda ki ke tayarwa da Abba hankali a shekarunsa ba wasa da rayuwarsa ba ce ba? To wallahi ba zaki kashe mana uba ba, muna da burin ganinsa a raye".
Aikuwa ta gyara tsayuwarta, ta haɗiye wani abu mai ɗacin gaske, ƙirjinta na yi mata zafi ta ce "Good, an zo wurin, kar na kashe muku uba, tun da ni ba nawa uban bane ko? To ku mayar da ni wurin nawa uban mana, meye na zama ana yi mini gori, how many years for now? kuna yi mini gori, kai ɗin ma da baka yi yau gashi ka fara, alhalin kun fi kowa sanin bani na zaɓi hakan ba, da da yadda zan yi, da tuni na bar muku gidanku, ku nuna mini hanyar gidan nawa uban mana"
Ta baya ya fizgota, ya ɗauketa da lafiyayyen mari.
Gigicewa tayi, jikinta ya hau rawa ta kalli Abba, da ransa yake a ɓace, fuskarsa babu annuri.
Ya riƙe hannunta, ya zazzaro mata ido ya ce "Me ki ka nema kika rasa? Me kike buƙata a rayuwar nan da ban yi miki ba da ki ke zancen mahaifinki, menene shi Nabila?"
Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta dafe kuncinta.
"Ki gaya mini, kafin na kasheki, me uban naki ya tsinanawa babarki ma, balle ke? Uban me ki ke nema a wurinsa?"
"Abba ka yi haƙuri, ba zan sake ba"
"Ba zan yi haƙurin ba, ki gaya mini ta ina na gaza, menene ba na yi miki"
Mama da jin hargowar su ya sanya ta fito ta tarar da su, ta ce "Mhmm, ai tsintacciyar mage ba ta taɓa yin mage major, kuma gurbin ido ba ido bane ba, muna nan da kai wataran sai ta saka ka zubar da hawaye"
Nasir ya ƙarasa ya ce "Abba dan Allah ka yi haƙuri, ba zata sake ba in sha Allah, kar ka kuma dukanta"
"Shut up! Kai ma har da kai, ina yi maka kallon mai hankali ashe ba haka ba ne, ku kuke tunzurata take wannan zancen".
Ya ce "Ka yi haƙuri dai Abba, in sha Allah ba za a sake ba"
Ya saki hannunta ya fice daga gidan baki ɗaya.
Nabila kuwa da gudu ta ƙarasa ɗakinta tana kuka mai cin rai.
***
Ƙarfe sha ɗayan dare, liti yana ƙofar gidan su Al'amin, yana rarraba ido, babu yaron da zai aika cikin gidan, kowa ya watse.
Ya bubbuga gate ɗin gidan, ya koma gefe.
"Waye?"
"Nine"
Ya buɗe gate ɗin ya kalli liti ya ce "Ya aka yi?"
"Wurin Abbu nazo shi nake nema"
Jin muryar liti, ya sanya Abba gane jama'ar Viper ne, dan haka ya ce "Mai zamanin yana tsare ai, ka sani kake nemansa"
"Dan uwarka wurin mai zamani na ce maka na zo? Wurin mai gidan na zo, baka gane ni bane liti ne" yayi maganar yana cire facemask ɗin fuskarsa.
"Na gane ka, amma a kan me zaka zo nemansa, ka gaya mini na je na gaya masa"
Wata uwar shaƙa liti yayi masa, ya watso shi waje ya ce "Shege, kai ka isa in zo wurin maigida ka ce na gaya maka menene sa'anka ne ni, wallahi idan baka kiyayeni da abun da ya shafi mai zamani ba, sai na sassaraka na bar wa uwarka tabon daba, makira yar wuta" tamkar gidan ubansa, liti ya kutsa kai ya shiga gidan.
Ya tsaya a tsakar gidan yana kwaɗa sallama.
Rahila ce ta fito ta ce "Wane mara mutuncin ne haka a tsakar gidanmu, malam balaggagen gardi ka shigo mana gida".
"Ɗanki ne ya so na shigo, eh sarkin gida nake nema, an ce ya je gada biɗata, mu kuma tsakainmu da maƙyanƙyasanmu akwai amana, mussaman maƙyanƙyashin mai zamani, ai dattijonmu ne iya wuya, ace masa gani na amsa kira".
"Wace irin magana ce kake yi wannan, ni ban gane ba"
"Gana ce, kuma kin gane mai nake nufi, ki yi mini magana da mai gidan, ko na shiga na neme shi da kaina"
Abba ya shigo gidan yana zare ido, ya sake cewa liti "Ka zo ka fitar mana daga gida"
"Gidan ubanka ne ko na mai zamani? Idan gidan ubanka ne sai na fita, idan kuma gidan uban mai zamani ne nima gidanmu ne"
Rahila ta ce "Wane mai zamanin, ka tafi can ka neme shi, ka fice ka bar mana gida"
"Ke yar wuta ban saka da ke ba, baƙar sheɗaniya, idan baki nemi yafiyar mai zamani ba, wuta ɗaya zaki shiga da matar sheiɗan, kai ware ka yi mini magana da mai gidan" yayi maganar yana zaro makami.
Abbu kuwa bacci yake yi sosai, a cikin baccin ya jiyo muryar liti, kawai zuciyarsa ta raya masa Al'amin ne, ya zo da mutanensa.
Da sauri ya fito tsakar gida, yana tambayar ko lafiya.
Liti na ganin sa ya mayar da makamin, ya durƙusa ƙasa ya ce "Abbu barka da dare"
"Yauwwa barka, lafiya ka shigo mana gida a wannan daren?"
"Liti ne Abbu, an ce ka je namanmu, ko ni ko walid, shiyasa ban yi sanya ba, na ce bari na gangaro na amsa kira, duk da mu masu laifi ne, ya kyautu ace muna zuwa muna kawo gaisuwa"
Abbu ya ce "Ikon Allah, meye sunanka na gaskiya ne?"
Liti yayi murmushi ya ce "Bawan Allah nake ai sarkin gida, Abdallah ne"
"To ni Abdallahn zan ce, bisimillah shigo mu shiga daga ciki"
Rahila ta ce "Ya shiga ina? Makami ne fa a jikinsa, sai yayi maka illa, ya zaka shiga da shi makwancinka?"
Abbu bai kulata ba ya ce "Ƙaraso Abdallah"
Ya bi bayan Abbu, yana baza babbar rigar daya saka a kan ƙanan kayansa ya kalleta ya ce "Munafuka, haddsana mai raba ɗa da uba, idan baki yi wasa ba, tun a duniya sai kin tozarta"
Duk tsagerancin Al'amin baya saurarta balle ya zageta, amma liti sai ƙare mata zagi yake yi.
Abbu ya kalli liti ya ce "Abdallah, dan Allah ko ka san in da Al'amin yake? Tun da ya zo mini daga prison na kore shi, ban sake ganinsa ba, ina matuƙar kewarsa da son na ganshi, na san ku ne makusantan sa, ban sani ba ko kun san in da yake?"
Liti ya ce "Eh to, gaskiya ban san in da yake ba, amma dai muna haɗuwa"
Abbu ya ce "Ban gane ba"
Liti ya ce "A bar shi hakan da na faɗa, ban san in da yake ba, amma muna haɗuwa, kuma maganar gaskiya, yana fushi da kai, tun da aka ce yayi laifin nan baka bashi dama ko sau ɗaya ba, ka saurare shi"
"Wace damar zan bashi, na nema masa auren yarinya girma da arziki, amma ƙarshe yayi silar rayuwarta"
Liti ya kalle shi ya ce "Haryanzu ka yadda shi ne ya kashe yar madara?"
"Meyasa ba zan yadda ba, tun da ya furta mini, kuna gashi yana shaye-shaye"
Liti ya jinjina kai ya ce "Haka ne" ya tashi tsaye ya ce "Baka shirya ganin sa ba, maybe zuwa gaba kaɗan, amma wallahi mai zamani, Allah ne yayi da sauran kwanansa a gaba, dan ya kusa kashe kansa, ko mun lalace fa ku iyayenmu ne, bamu da sama da ku, duk son da mai zamani yake yi maka, ka fita daga zuciyar sa, ya daina maganarka ranar da na yi masa zancenka ce mini yayi shi yanzu ba shi da uba, kaga wannan ba dai-dai bane ba, alhalin ga wani ɗan kut.... Da yafi mai kora shafawa da shi da yan uwansa, suna zaune a gidan, mu kuma kun sallamawa duniya mu. Bari na ɓace, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ka cigaba da yi mana addu'a a duk in da muke, mai zamani zai samu yanci ya cigaba da gudanar da rayuwarsa kamar kowa, ba tare da yana ɓuya ba"
Abbu ya miƙe suka fito tsakar gida ya ce "Kayi mini wani taimako Abdallah, ka tayani kwantar masa da hankali kafin ranar da Allah zai saka na ganshi dan Allah"
"To in sha Allah"
Ya ɗaukko kuɗi ya bawa liti, liti ya ce "Meyasa zaka bani kuɗi, ni ba zan karɓa ba, ayi mana addu'a kawai, in sha Allah mai zamani ya kusa samun ƴanci" yana gama maganar ya fice.
***
Liti ne yake ta kallon Viper, ya numfasa ya ce "Mai zamani"
"Farin jakada" liti yayi dariya, ya ce "Rabon da ka gaya mini sunan nan har na manta, kwanan nan kamar kana jin raha, menene sirrin ne?"
Ya ce "Abubuwa da yawa, ƙwaƙwalwa ta ta samu nutsuwa a 'yan kwanakin nan, sannan na fara jin daɗin yadda nake wasa da hankalin maƙiyana, ka san sanyawa mutum tsoro yafi kowane horo wahala"
Walid ya ce "Ai mun gode Allah, da bayan tafiyar jauhar, Allah ya kawo mana Nabila rayuwar ka, haƙiƙa bayan ƴar madara ita ta ceto mana ƙwaƙwalwarka da tunaninka"
"Ba wani nan, da an yi magana ka fara sako maganar wannan makirar ba wani, ba uwar da ta tsinana masa"
"Wai anya liti idan aka bi salsala ba daga zuriyar fir'auna kake ba, kai wai baka yafiya ne"
"Ba zan yafe ba, kace ma nine fir'aunan kawai mana walid"
"A'a ni ban ce maka fir'auna ba, amma dai baka da zuciyar kirki"
"Ni rabu da ni, zan yi magana ka hana ni, zaka saka na manta"
Ya kalli Viper ya ce "Mai zamani, Abbu yaje rumfar sayar da shayi yana nemana ko ni ko walid" a take ɗan annurin fuskar Viper ya ɗauke.
Liti ya ɗora da cewa "Na ɗan yi yawo na nemi bayanai, kar na je ko wani set up ne, amma na fuskanci lafiya ƙalau ne, dan sai na ci uwar agolan nan na gidanku, da ya kawo mini wargi, mun haɗu da Abbu, ya ce mini yana son ya ganka, amma na ce ban san in da kake ba, akwai tarin nadama a tare da shi, dan Allah mai zamani ka sassauta, naka mahaifin ne kawai ya rage mana, mu yi haƙuri mu yafe masa, na tabattar masa da ka kusa yin 'yanci da yardar Allah"
"Bani da uba, nawa uban ma mun rasa shi, dama can ba ya ta tamu, dukkanmu marayu ne, da muke zaune a matsayin ƴan uwan juna, ko na yi ƴanci, ba zan sake zuwa in da yake ba, na bar shi da waɗanda yake so"
"A'a Viper, su fa iyaye komai za su yi, ba a fushi da su" harshensa ya zaro waje, ya ɗago sweazland ɗin da take gefensa, ba shiri liti ya tsuke bakinsa, yayi shiru ba dan ya rasa abun faɗa ba, sai dan sanin cewa yana sake magana sai ya saka masa ƙarfe.
Message ne ya shigo wayar Viper.
"An yi maka gargaɗi a kan yarinyar nan tun da farko, amma ka ƙi ji, yanzu ta zama rauninka, sai ka yi aiki tuƙuru, dan kare rayuwarta!.
***
Nabila ba ta san ya aka yi aka samu lambar wayarta ba, mutane suka din ga kiranta a waya, wasu na zaginta a kan program ɗin da ta gabatar, ta taɓa bunkure foundation, wasu na jinjina mata, tare da nuna mata goyon bayansu, da ta gaji kashe wayar ta yi gaba ɗaya.
Gaba ɗaya kewa da tunanin Viper, suka haɗu suka uzzurawa rayuwarta, tana ta ƙoƙarin basarwa amma abu yaya gagara kamar yadda dariya ta gagari kare.
Ta tsaya a gaban mudubi tan ƙarewa kanta kallo, bayan ta fito daga wanka, ta shiga ƙarewa kanta kallo, kyakykyawar farar fatarta sai sheƙi take yi.
Idanunta jawur, saboda kuka, gaba ɗaya haushin Nasir take ji, gaba ɗaya komai yayi mata zafi, ba ta jin daɗin komai.
Message ne ya shigo ƙaramar wayarta, "Mu haɗu a garden" ta zubawa notification ɗin ido, tayi wata irin ajiyar zuciya, kamar sanyi ta ji a ranta, da ganin saƙon nasa.
'Wai me nake yi haka ne? Ta tabatta son shi nake yi kenan? Wace irin ƙaddara ce haka?"
Ta lumshe idanunta, hawaye ya ziraro daga idaunta, abubuwa da yawa suna damunta, kuma babu wanda take burin ta gayawa sama da Al'amin, mutumin da bai damu da ita ba ko kaɗan.
Jiki a sanyaye ta shirya, ta saka kayanta, ta kawo facemask ta saka, ta fice.
Ko da ta je garden ɗin, ba ta tarar da shi ba, ta kira wayarsa amma ba ta shiga, haushi ya kamata, ranta ya ɓaci, dan da niyyar ta ganshi ta zo, haka kurum tayi ta ɗokin ta zo su haɗu.
Ta nemi wuri ta zauna cikin takaici, haushin kanta take ji, yadda ta faɗa soyayya cike da wawanci.
Ta ɗan jima a wurin a zaune, sannan ta tashi, ta ɗauki mota zata koma gida, ya kirata a waya.
Bai jira tayi magana ba, ya fara "Yayanki yana bin bayanki, nan da kilometer biyu, akwai wani gidan cin abinci, ki tsaya ki shiga" ya gama maganar ya katse.
Babu tunanin komai ko musu, ta cigaba da tafiya, sai dai ta din ga kallon mirror, amma bata ga alamar wani ita yake bi ba.
Ta tsaya a restaurant ɗin, ta shiga ta sake kiran wayarsa, bai ɗaga ba ya tura mata saƙo "In the next 10 minutes, ki koma motarki, ki samu wuri ki zauna ki jira"
"Wai dan Allah meyasa...... Katse wayar yayi, ba tare da ta gama maganar ba.
Ta nemi wuri ta zauna ranta a ɓace, mintuna goma na cika ta ga saƙonsa.
Ta tashi ta fita, ta ƙarewa harabar wurin kallo, amma ba ta ganshi ba, ta buɗe motar sai da ta zauna, kawai ta ganshi a cikin motar, da ihu zata kurma, amma tayi shiru, tana rarraba ido, ta rufe motar ta kalleshi ta ce "Ta ina ka shigo?"
"Ta ƙofa" ya bata amsa.
"Amma to meyasa kayi ta wahalar da ni?"
"Fita ki zagayo, zan ja motar" ta jinjina masa kai, ta fita ta zagaya, shi kuma ya koma mazaunin direba, ya bawa motar wuta, ya ja ta da uban gudu ya bar wurin.
"Ka tuƙa a hankali, tsoro nake ji" bai ce mata uffan ba, ya cigaba da fafara gudu, sai da ya cimma wani a kan babur, ya sanya hular kwano.
"Kin san wannan?" Ta girgiza kai alamar a'a.
"Kin tabatta?"
"Eh, ɗazu dai ka na ƙaraso nan, na wuce shi a kan titi"
Ya jinjina kai ya ce "Ke yake bi, kin wuce ni a mota, na ga yana binki, ina kyautata zaton ko dai yayanki, ko wani ne ya sa ya din ga binki"
Ta sauke numfashi ta jingina da jikin dai-dai lokacin da ya saka hannu a jikin seat ɗin, yana ƙoƙarin shiga wata kwana.
Tudun gashinta ta ɗor a kan hannunsa, ta lumshe ido, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa, jikinsa ne yayi wani irin sanyi, yayi saurin cire hannunsa, ya ƙarasa in da yake son su je.
Shi ma lambu ne wurin, amma babu kowa, sai sanyin bishiyun wurin, ta fuskanci yana son yanayi irin haka.
"Yaya ake ciki da case ɗin rahama, a ina ki ka tsaya?"
Kawai ta zuba masa ido, ya yi mata wani irin kyau, ma'abocin ƙanan kaya ne, shirt ce ajikinsa baƙa da zanen damusa a jiki, sai dogon wandon jeans, mamaki ma take yi, a in da yake samun kuɗin sayen kaya masu kyau.
Sai ƙamashin turaren florie yake yi, ya yi gyaran fuska, ya kuma yi saisaye, idanunsa sun rage wannan jan, alamu sun nuna ya ɗan tsagaita da shan miyagun ƙwayoyi.
"Malama ina magana kin yi shiru kina kallona"
"Yanzu rashin muhimmancina har ya kai na shiga wannan tashin hankalin, ka sani amma ka kasa nema na ko a waya, ka ce mini sannu, i almost lose my life fa, a yaya ka ɗauke ni ne? Bani da muhimmanci har haka a wurinka, haba dear, ni ka san ba zan taɓa yi maka haka ba, ina son rayuwarka, ina son ganin walwalarka da farincikin ka, ina son na maye maka gurbin jauhar, da wasa na ɗauki abun, amma ya zame mini gaske. Ka daina nuna mini halin ko in kula, bana jin daɗi ko kaɗan. Damuwa ce da ni a raina sosai, ina son wanda zan gaya wa ya saurare ni, wanda zai fahimci haƙiƙanin abun da nake ji"
"Ki shiga hankalinki, bana son wannan wasan da ki ke yi mini, da zarar aikina da ke ya kammala, kowa zai kama gabansa, ki daina yi mini irin wannan wasan, na gaji da yi miki kawaici, ba na so"
Cikin ƙarfin halin da rauninta ya hana ta aikata hakan, hawaye ya fara biyo kuncinta ta ce "Ba wasa nake yi maka ba, ƙaddara ce da na roƙawa kaina da bakina, ba wasa nake yi maka ba, da fari wasa nake yi, amma yanzu ya zame mini gaske, ban taɓa tunanin zan iya cewa wani namiji ina son shi ba, amma kai naga kamar nutsuwar ka ta kai na gaya maka"
Ya ce "A'a karki yaudari kanki, wace nutsuwa nake da ita?"
"Rauninka mutane kawai ke iya gani, ni kuma nagartarka nake gani, kamar kai ne zaka zama dai-dai da ƙaddarata"
Wani abu ya ji yana nema ya rinjayi zuciyarsa, mussman da ya fara ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila tana kuka.
Cikin ƙarfin hali, yayi ta'awizi ya kaurara muryarsa cikin tsare gida ya ce "Jauhar ɗaya ce, kuma na sameta ta suɓuce mini, babu wata mace da zata iya maye mini gurbinta, sanya wata macen a zuciyata tamkar cin amanar 'yar madara ne, a kanta na gama soyyaya, kuma na gama aure, dan haka kar ki ƙara yi mini wannan maganar, ki nemi wani ki aura, wanda iyayenki za su yi alfahari da ke da shi, jauhar ma ƙaddara ce ta saka aka bani ita"
Ta share hawayenta ta ce "Nabila mace ce mai aji, aji ma na gaske, ban taɓa mafarkin fara furtawa wani namiji ina son shi ba, raunin macen kenan, daga tausayi na faɗa sonka ban shirya ba, kai banda ƙaddara da haɗin Allah, me zai kai mace kamata yin kasada da rayuwata kamar wata wawuya ina nemanka ina zaman zamana?.
Sannan ka sani idan akwai macen da nagartarta zai hana a auri wata mace bayan wafatinta, to Sayyada Khadijah ce Allah ya ƙara mata yadda, kuma idan akwai macen da soyyayar da ake yi mata, zai hana ayi mata abokiyar zama, to sayyada Aisha ce radiyallahu anha.
Baka san wace damuwar ce a raina ba, ka zaɓi ka yi mini haka, ko baka so na, ba haka yakamata ka yi mini ba, bani mukullin motata na tafi" tayi maganar tana kuka tare da miƙa masa hannu.
Kallonta kawai yake yi, babu in da ta bar 'yar madara a kamanni, hatta kukan nan da take yi, jauhar kawai yake gani, sai dai Nabila ta fi jauhar murya, da kilewa kuma ita mafaɗaciya ce.
Loosing control ɗin sa ya kusa yi, da zuciyar sa take raya masa, ya rungumeta ya rarrasheta, sannan ya ji menene damuwarta, fizge mukullin motar tayi, ta ƙara gaba tana kuka.
Ayshercool
08081012143
67
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Cikin zafin nama ta juya tana kuka, ta nufi hanyar barin wurin, har ya ɗaga ƙafa da niyyar ya bi ta, sai kuma ya fasa, dan idan ya bita bai san me zai ce mata ba, yana kallonta ta hau motarta ta bar wurin.
Bashi da zaɓin da ya wuce shi ma ya bar wurin, sai dai ya tafi zuciyarsa cike da wasi-wasi, ko cikin duhu aka tara mata dubu, zai cire 'yar madararsa, amma haryanzu ya kasa gane dalilin da ya sanya Nabila take kama da jauhar, ba kuma wai kama sama-sama baz kamannin ne tamkar an raba kara biyu.
Ya cigaba da takawa a hankali ya bar wurin.
***
"Indabo ina fatan ka saurari program ɗin da wannan sheɗanun yaran suka gabatar, ka shirya ɗaukar mataki ne, ko kuma ni na ɗauka da kaina? Na gaya maka ba zan bari wahalata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 70 Chapter of 121