ba, ka yi koyi da wasu, ba ta wulaƙanta ɗan Adam da tana yi, da ba ta riƙe ka da amana da tausayawa ba. Ina sake roƙonka yafiya, da kuma fatan samun haɗin kanka, ka ƙarasa mini labarinka da kanka, ina sha'awar kasancewa wani ɓangare na labarin nan, mai ban tausayi da ratsa zuciya Viper, sai da safe" tun da ta fara maganar, ya sunkuyar da kai, ya saki sigarin da take hannunsa, ya sunkuyar da kai hannunsa yana rawa. Ta gama maganar ta katse wayar, amma ya kasa ajiye wayar.
Sai da liti ya dafa shi ya ce "Maza yane?" Ya ɗago idanunsa ya kalli liti.
"Kamar Muryar wannan shegiyar yarinyar na jiyo a wayar, duk Walid ne da wannan sheɗancin"
Ya cigaba da ƙurawa Liti ido, babu abun da yake fata, banda ya zubar da hawaye ko na mintuna biyar ne, amma ko na sakan ɗaya ya kasa tsawon shekarun nan.
Murya a sanyaye ya ce "Liti"
"Na'am mai zamani".
"Ina kewar jauhar sosai"
Walid da da yayi musu shiru, dan ya lura daga Viper har liti haushin sa suke ji, amma maganar da Viper yayi yanzu ta sanya jikinsa ya yi sanyi, tausayin Viper ya ƙara kama shi.
"Da yanzu yarona ya isa shiga makaranta, wataƙila ma ta kuma haifa mini wasu"
Walid ya taso, ya dawo gaban Al'amin, ya riƙe hannunsa ya ce "Ka ƙara haƙuri mai zamani".
"Zuwa yaushe? Ko na ɗauki fansa kamar yadda nake buri da fata, kashe kaina zan yi saboda ba ni da wata makoma, idan kuwa hakan ba zai samu ba, zan koma in da na fito na ƙarasa rayuwata".
"Dan Allah maza ka daina irin wannan maganganun, kana karya mana zuciya wallahi " liti yayi maganar cikin damuwa.
Viper ya girgiza kai ya ce "Ba zaka gane ba"
Kawai ya gyara ya kwanta, gaba ɗaya suka kewaye shi suna kallonsa.
Nabila kuwa kallon wayar ta cigaba da yi, ta ce "Allah ya bani nasara a kanka, ya bani ikon taimaka maka".
Kira ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta saka a kunnenta, ta yi sallama.
"Wa'alaikum Salam da 'yar ƙwalisa".
"Wa ke magana?"
Yayi murmushi ya ce "Bawan Allah ne"
"To, ai kowa ma bawan Allah ne, wanne daga ciki?"
Yayi gyaran murya ya ce "Wani case ne da ni, nake so a taimaka mini"
Nabila ta yi hamma ta ce "Office zaka zo, ba ta waya ba" ta katse kiran, dan a zatonta irin samarin nan, ne masu kiran wayar mata anyhow, duk da Muryar wannan ba ta yaro ba ce.
Wani nannauyan bacci, yayi awon gaba da ita wanda babu abun da take yi ban da mafarkin Viper, dan sai da ta kusa makara yau.
Kwanaki uku da zuwanta wurin su Viper, ba ta sake zuwa ba, she's very busy, tana ta off and down na tattara hujjoji, duk da ana ta taɗiyeta, duk in da za ta bi ta samo shaida, sai a rufe, sai da aka aike da dattijon nan gidan kaso.
Gashi sai tayi ta sintiri a hanata ganinsa.
Kamar uba da ɗa haka Walid yake ta lallaɓa Viper ya ci abinci, sai dai ya cakala ya bari, ba ya cin abinci.
Private numbrn nan da ake kiransa da ita ce, ta kira shi, wayar tana ta ringing liti ya ce "Maza ka ɗaga mana"
"Me zan ce?"
Walid ya ce "Ko ba ka da abun cewa, ka ɗaga kawai"
Ganin ba shi da niyyar ɗagawar, ya sanya Walid ya ɗaga ya sakata a hansfree.
"Aminu Viper, kwana biyu. Ashe ta dawo maka da wayar. Alamu sun nuna kwana biyu ka yi sanyi, Kodayake kai sai an sakankance ka ke ɓarna. Gargaɗi nake sake yi maka, ka nesanta yarinyar nan da ga gareka, za a iya cutar da kai ta hanyarta".
"Ni nake da ikon yanke hukuncin abun da yake daidai da rayuwata, babu wanda ya isa ya juya mini rayuwa yadda nake so, ka cigaba da ɓuya ko ka bayyana kanka, zan yi abun da nake ganin shi ne dai-dai da rayuwata.
Mutumin yayi murmushi ya ce "Aminu Viper, shikenan idan ka ƙi ji, ba zaka ƙi gani ba ai"
"Babu abun da ban gani ba, dan haka na shirya ganin koma menene" ya katse wayar.
Liti ya ce "Duk walid ne ya janyo komai, ni na san a rina, wannan yarinyar idonta kawai zaka kalla ka gane munafuka ce"
Kallon da Viper yayi masa ne, ya sanya shi yin shiru, Walid yayi dariya ya ce "Ayi dai mu gani, za a gane waye mai gaskiya tsakanina da ku".
Liti ya ce "Ba wata gaskiya da ka ke da ita, ka dakatar da mu daga making moves, wallahi mun kusa fita operation kwanan nan"
"Ku fita yaƙi ma ba operation ba"
Haka liti da Walid suka kusa yin faɗa.
Tun ana gobe Nabila zata je wurin Naja'atu Bunkure, suke waya da sumayya, take bata ƙwarin gwiwa, a kan za ta iya, kar ta ji tsoro.
Da safe sai da ta fara zuwa wurin aikinsu, ta samu barrister Habib, shi ma ya ƙara mata ƙwarin gwiwa, da yi mata fatan alkhairi.
Cikin ƙasaita take fiya a farfajiyar office ɗin, har ta ƙarasa, mutane ta tarar jingim. Wanda galibin su mata ne, suna jiran shiga wurin Barrister Naja'atu Bunkure.
Kai tsaye Nabila ta shiga wurin sakatariyarta, ta nuna mata ID card ɗin ta, nan da nan ta bawa Nabila wurin zama, na ciki na fitowa ta yi mata iso zuwa wurin Barrister Naja'atu.
Tun a hanya take maimaita "la hula wala ƙuwwata illa billa". Har ta shiga wurin Bunkure.
Tayi sallama, ba tare da ta ɗago ta kalli Nabila ba ta amsa mata, ta ƙarasa ta zauna ba tare da an yi mata umarnin hakan ba.
Kayan jikin Nabila kawai ta kalla, ta fuskanci ba kalar gajiyayyun da suke zuwa wurinta bane ba.
Ta gyara zaman gilashin fuskarta ta na kallon Nabila.
"Sannu da aiki ma" Nabila tayi maganar tana murmushi.
"Yauwwa sannu"
Nabila ta ɗaga mata id card ɗin ta ta ce "I am barrister Nabila Yusuf maitama"
Bunkure ta jinjina kai ta ce "You look familiar to me"
Nabila ta jinjina kai ta ce "Na yi mamaki ma, da ki ka iya tuna kamar kin sanni, saboda na san jama'ar ne da yawa. Ni abun da ki ka yi mini ba zan taɓa mantawa ba har abada"
Bunkure ta ce "Ohh really"
"Yeah and i have a promise to fulfil, a dalilin abun da ki ka yi mini"
Ta kashingiɗa da jikin kujerarta ta ce "That's very good, ina son mutane masu yarda da kansu, ba na buƙatar sanin me nayi miki, ko kuma wani alwashi ki ka yi ba, ga ki ga bunkure Allah ya ida nufi "
Nabila ta ce "Na ji daɗi da ki ka ce Allah, dan kuwa shi ne gaba da komai, na gode sosai barrister"
"Mentioned not"
Nabila ta gyara zamanta ta ce "Yauwwa, ba komai ne ya kawo ni ba, na zo ne a kan wani case, duk da ba mu haɗu a court ba, an kai wanda nake depending prison, amma ban ganki a court ba sai wakilanki"
Bunkure ta ƙarewa Nabila kallo, sannan ta ce "Wane case ki ke magana a kai?"
"Yarinya da aka yi wa fyaɗe, ki ka ce kin tsaya mata, ni ce lawyer wanda ake ƙara, na je wurin 'yan sanda ana ta yi mini yawo da hankali, ina son doctors report, kuma ina son zan ga yarinyar zan yi magana da ita".
Naja ta yi wa Nabila kallon baki da hankali sannan ta ce "Kin san a gaban wa ki ke?"
"I am barrister Nabila, ba ruwana da a gaban wa nake, ina neman hujja ne da zan kare client ɗina"
"Nawa suka baki, ki ka samu ƙwarin gwiwar yin wannan kasadar? Zan ninka miki, ki ajiye case ɗin, kafin ki kunyata a idon duniya "
"Watch your words, it can be use against you a kotu, kin san me nake nufi, you are also a lawyer"
"Who the hell are you?" Bunkure ta yi maganar tana tashi tsaye, Nabila ma ta tashi tana sake ɗaga mata id card ɗin ta "Sai da na fara gabatar miki da kaina, sannan na gaya miki meya kawo ni.
Ko dai ki bani abun da nake buƙata kawai, ko kuma na fasawa duniya wacece ke?"
"Ni ɗin? Yaushe ki ka yi grduating, da me ki ke taƙama ki ke jin karanki ya kai tsaikon da zaki tunkare ni kina gaya mini maganar da ki ka ga dama?"
Nabila ta girgiza kai ta ce "Cikin dukkanin girmamawa ta seniority a aiki, nake faɗar duk abin da nake magana a kai. You were my mentor before, abun da ki ka yi mini ya tabattar mini you are green snake under green grass. Keep your eyes open, Barrister bunkure, zan iya baki mamaki a lokacin da baki zata ba. Zan cigaba da bibiyar case ɗin ramma, da ƙoƙarin wanke wanda nake karewa har sai na yi exposing ainihin gaskiya ko da kuwa ita ce ajalina" tun da ta yi face to face da ita, ta ji duk wata fargaba da tsoron da take ji sun kau.
Ta ɗauki jakarta, ta fita daga office ɗin.
Tsaki Bunkure ta yi ta daki tebur, ta ɗauki wayarta, ta danna ta kara a kunnenta.
"Yauwwa barrister Kabir ya kake?"
"Lafiya ƙalau manyan ƙasa ya aikin?"
"Normal ne, wacece Nabila a ma'aikatanka?"
Ya ce "Lafiya kuwa? Ya aka yi ki ka santa?
"Wacece ita, a id card ɗin ta na ga a wurinka take aiki"
Ya ce "Barrister Nabila, a law firm ɗina take".
"Ta zubawa kanta fetur a jiki, tana kuri, idan na ƙyatta ashana, ba ita ba har kai, zaka ƙone ƙurmus ka ja mata kunne, ɓera ba ya taka rawa a gaban mage, ko da kuwa tana kan gargara ne"
Kabir ya ce "Subhanallah, me ta yi?"
"Ka bincike ta, ba na bari ayi mini kuskure biyu, ko yinƙurin yi aka yi, ina daƙile duk wani abu da zai kawo mini cikas".
Kabir ya ce "Na fahimta, ki yi haƙuri dan Allah zan yi magana da ita, zan kuma ja mata kunne" ta ajiye wayar tana tsaki.
Cike da annashuwa ta fito daga wurin, tare da jin kanta tamkar ta yi facing ɗin babban abun tsoronta.
Ta tsaya a gefen hanya, ta ciro wayarta, ta kira Viper, ya ɗaga sai dai bai yi magana ba.
"Hello, ya jiki? Na san ba zaka yi magana ba, dama so nake na ji ya jikinka, na so zuwa na ganka amma rana tayi sosai, zan je wani wuri ne, ka kula da kanka sosai" ta katse wayar, ji yayi tamkar ya aikata wani uban zunubi, ya din ga bin wayar da kallo, yana tunanin yarinyar nan tana da hankali kuwa?.
Gida ta tafi cikin matsanancin farinciki, duk da ba su kwasheta da daɗi ba ita da.
Gida ta tafi ta yi wanka, ta ɗauki wayarta ta kira sumayya, amma line busy.
Ta ajiye wayar ta kwanta tana bacci.
***
Shiru shiru Abdul bai je kiran iyayensa ba, yana nan yana fama da kansa, kuma ya hana duk abokansa zuwar masa gida.
Duk da Allah ya isa, da fatan mutuwa da ramma take yi masa, hakan ba ya hanata tausaya masa, idan ciwon ciki ya murɗe shi, har mamaki take yi da ya ce mata ulcer ce, dan ita ta ɗauka yunwa ce take kawo ulcer, yaran masu kuɗi ba sa yi.
Da daddare yana kwance a kan gado, tana zaune a ƙasa tana karanta wani novel na turanci, da ta ɗauka a falonsa, duk da ba wani ganewa take yi ba, amma yana ɗebe mata kewa.
Tana ji aka kira shi a waya, ya ce yana zuwa, ya tashi ya fita.
Bayan ya fita, ta ɗaukko pillow, ta ajiye a ƙasa ta cigaba da karatunta.
Hamma da take ta yi ba ƙaƙƙautawa ne ya sanya ta gane bacci take ji sosai, ta tashi za ta rufe ƙofar ɗakin, kasancewar ya bar key ɗin ta ciki, dan ciwon cikin nan da yake yi, ta samu sassauci daga akuyancinsa.
Sai dai ta buɗe ƙofar falon ba ya nan, ta fito ta wuce kitchen, ta daɗe a kitchen, ta zubawa fridge ido, komai akwai na morewa rayuw a gidan, amma gaba ɗaya ba ta jin daɗinsu, saboda ƙazantacciyar rayuwar da take ciki.
Ta sha ruwa mai sanyi, ta cika cikinta, ta fito falo, sai dai abun da ta tarar ya sanya gabanta mummunan faɗuwa.
Cikin hanzari ya ture Nina daga jikinsa, ya yi tsilli-tsilli da ido, yana kallon ramma.
"Abdul wacece wannan?"
"Amm maid ɗina ce, mai aikina ce".
"Kamar yaya, ina solomon ɗin, shi zaman me yake yi? Me ka ke yi da mace a zaune a gidanka? Abdul kar ka raina mini hankali mana, karuwa ka ajiye Abdul?"
"Kar ki sake ce mini karuwa, ni ba karuwa ba ce, ke ce karuwa amma shi ki tambaye shi yadda aka yi na zo gidan nan?" Ta yi tsaki za ta tafi.
"Abdul ka yi mini magana wace banzar ce wannan?"
Abdul ya miƙe ya ce "ya isa haka, ki je gida za mu yi magana "
"Ban gane ba, ka gaya mini wacece wannan?"
Bayan ramma ya bi da sauri, Nina ta biyo shi, amma yana shiga ɗakin, ya mayar da ƙofa ya rufe da key ta ciki.
Ramma tuni ta kwanta wani abu mai zafi ya tsaya mata a rai.
"Rahma, ki tashi mu yi magana dan Allah, zan yi miki bayani" tayi masa shiru ta ƙi motsawa.
"Dan Allah ki tashi ki ji, zan yi miki bayani"
Ramma ta waiwayo sosai ta kalleshi ta ce "Ba ni zaka yi wa bayani ba, Allah zaka yi wa bayanin abun da kake aikatawa ba tare da tsoronsa ba. Ni baƙincikina, muzanta rayuwata da ka yi ne da wulaƙanta ni.
Ka yi zina da wasu, ko wankan janaba baka yi, ka zo ka kuma afka mini, wannan wace irin rayuwa ce, Abdul yasar ka gama da rayuwata, wallahi ko baka kashe ni, ina son kashe kaina na huta, dan dai kawai ina tunanin makomata ne, amma ka cuceni wallahi" tayi maganar hawaye na ta gangarowa ta gefen idonta.
Hannu ya sa yana share mata hawayen, amma ya kasa ce mata komai.
Ya numfasa ya ce "Kina ji na?"
"Dalla ƙyale ni, ba abun da zan ji, ni ƙyanƙyamika ma nake ji, mazinaci ƙazami mara tsoron Allah"
Duk da yadda maganganunta suka yi masa zafi, amma ya daure ya ce "Dan Allah Rahma ki daina kirana da mazinaci, kalmar nan na yi mini ciwo sosai. Wallahi tun a kanki ban sake zina ba, yanzu ba abun da ki ke tunani ba"
Aikuwa kamar ya tunzura ta, ta tashi zaune ta ce "Ni abun da ka ke yi mini menene? Na faɗa na kuma" ta sauka daga kan gadon tana huci, cikin ɓacin rai.
***
Naja'atu kuwa tana zaune a bakin gado, tana ta haɗa ƙwayoyi a cikin roba, ta na zuba ruwa a ciki, shiru ta yi tana tunanin maganganun da Nabila ta gaya mata, mamakin ƙarfin halin yarinyar take yi, yadda ake shakkarta da shakkar yin gaba da gaba da ita, ita wannan yarinyar zata yi wa cin mutunci haka. Me take nufi da za tayi exposing ɗin ta. Ta daki teburin gabanta ta ce "Wai ma wacece ita?" Ta yi wata ajiyar zuciya ta ɗaga kai, ta shanye ƙwayoyin cikin robar nan da ta narka.
Nabila ce zaune tare da Nasir, tana bashi labarin yadda suka yi da Naja'atu Bunkure, yake ƙara ja mata kunne, a kan ta bi sha'anin matar nan a hankali, kar ta yi mata illa.
Tayi murmushi ta ce "In sha Allah ni zan karya alkadarin matar nan"
Ya ce "To, Allah ya sa"
Ya amsa da "Amin, na ji an ce kin ce mota ki ke so?"
Ta jinjina masa kai ta ce "Abba ya saya mini mota,kai kuma ka din ga zuba mini mai" tayi maganar cikin shagwaɓa. Kasa amsa mata yayi, sai bin ta da kallo da yake yi, yana murmushi.
Ta ce "DSP ya ake ciki ne, da zancen binciken viper?"
Ya numfasa ya ce "Ina ta cigaba da bincike, gashi ana cigaba da matsa mini a kan kama shi, abubuwan ma na rasa yadda zan yi, duk shaidar da na kama sai ta zille, ace in sake shi, na rasa wannan wane irin abu ne. Amma dai an kwatanta mini wani yaro, dealer ne na wiwi, wai shi ɗan mama, idan na kama shi, ba zan bari a san na kama shi ba, sai na dangana da kama Viper in sha Allah" gabanta yayi mummunan faɗuwa ta ce "To wai suwaye suke sakawa a saki shaidun naka?"
Ya ce "Ban sani ba, daga sama kawai ake cewa na sake su".
Ta jinjina kai ta ce "Kuma anya ba su san in da yake ba, raina maka hankali kawai suke yi ba?"
DSP ya ce "To ko ma dai menene, zan ɓoye bincikena, sai na dangana da kama shi, na danƙa musu shi, su san yadda za su yi da shi. Ina nan mun samu bayanan lokutan da yake zuwa an tabattar mana da idan muka kama shi, zamu iya kama Viper "
Kamar an mintsine ta ta miƙe, ta ce "Bari na koma ɗaki, zan yi wani uzuri" har da gudu ta haɗa, ta tafi ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta din ga kiran Viper, amma yaƙi ɗagawa, tayi masa missed calls sun fi goma, amma ko ɗaya ya ƙi ɗagawa, ga yamma ta yi sosai, idan ta fita kan ta dawo magariba zata iya yi.
Ayshercool
08081012143
51
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Kamar Nabila za ta yi hauka, tana kallon kiran Barrister Kabir yana shigowa wayarta, amma ta share, taƙi ɗagawa, ƙarshe ma rejecting kiran na sa ta din ga yi, taƙi ɗagawa babban burinta kawai Viper ya ɗaga wayarta, amma yaƙi ɗagawa.
Kwana tayi cikin zullumi, da addu'a kar Allah ya bawa Nasir nasarar kama Ɗan mama, dan a labarin Viper ba ta ji yadda aka same shi ba, balle ta san ingancin kasancewar sa tare da shi, tare da tabbacin ba zai faɗi in da Viper yake ba, kodayeke ta san ba zasu taɓa janyo wanda zai cutar da su ba.
***
Abdul ne zaune a gaban Indabo, sai zazzaga masa faɗa yake yi, ya haɗe rai yana ta muzurai.
"Ina magana kana shan kunu, Abdul ko ka ƙi, ko ka so dole ka yi aure, idan ba haka ba, babu yadda za ayi a ɗauki takara a baka, na gaya maka dan ba zaka yi mini asarar wahalar da na yi shekaru ina yi ba, dole ka je ka gano yarinyar party chairman ku daidaita, ko baka santa ayi, idan ya so daga baya sai ka auro wadda ka ke so"
Cikin damuwa ya ce "Daddy, ya za ayi ace na auri wadda ba na so, ni tun ban ganta ba, ba na sonta wallahi, a bar ni zan kawo wadda nake so ɗin"
Indabo ya ce "Inaa lokaci kuma ya ƙure maka, arranged marriage ɗin nan, duk cikin manufa ce irin ta siyasa, dan haka dole ka yi haƙuri, ka je ku daidaita" Abdul ya yi shiru bai ce komai ba.
Indabo ya ɗora da cewa "Sannan za'a fara haɗa structures a kowacce mazaɓa, tun yanzu za ku fara campaign kafin ƙaddamar da takararku" Indabo har ya gama maganganun sa, Abdul bai saki fuska ba, yayi ya gama ya tashi ya bar office ɗin.
Yana fita P.A ya shigo, ya ce "Distinguish yaya dai nake jiyo muryarka tun daga waje?"
Indabo yayi tsaki ya ce "Abdul mana, gaba ɗaya yaron nan ba shi da hankali, wai shi ba zai yi aure yanzu ba, so yake yayi mini asarar wannan uwar wahalar da na sha muka kawo wannan matakin"
P.A yayi murmushi ya ce "Rabu da shi, mu cigaba da dukkan shirye-shirye da suka dace, kuma a cigaba da bin malamai, dan Abdul akwai taurin kai, a kan auren nan zai iya fasa takarar amma a cigaba da matsawa".
Imdabo yayi tsaki ya ce "Yaya ake ciki? Ya batun yarinyar nan?"
"Mu na nan muna bibiyarta, sai dai bakin zaren gano in da Viper yake ne aiki, balle ayi masa tarkon da ita. A binciken da nake yi, shi wannan ɗan sandan ya kama liti, kwanansa kusan huɗu a hannunsa, aka ce lallai ya sake shi"
Indabo cikin damuwa ya ce "Waye ya ce a sake shi ɗin?"
P.A ya girgiza kai ya ce "Ban sani ba, haryanzu babu trace na wanda yake taimaka masa, kuma Viper yana nan a cikin garin nan yana yawonsa, sai dai gaskiya ƙarƙashin kulawar wani yake duk abin da yake yi "
"Kaii wai wannan wane irin abu ne? Hankalina kullum a tashe yake, ban san ta ina zai ɓullo mini ya ce zai ɗauki fansa ba, ka san ba zai taɓa barina ba, shi ma wancan banzan da duk laifinsa ne, ya kasa komai ya kasa kamo shi ya kasa gano in da yake, duk shi ya ɓata lamarin, da bai tabattar da Viper ya mutu ba tun a wancan lokacin, ina cikin tashin hankali".
"Ka kwantar da hankalinka distinguish, Viper fa zai zo hannu, ko da me yake yawo, ka yi haƙuri in Allah ya yarda babu abun da zai faru sai alkhairi" yayi ajiyar zuciya ba dan ya gamsu da maganganun P.A ba.
***
Daga wurin Indabo Abdul gidansa ya wuce, ya tarar da Ramma na ta uban bacci, motsinsa a ɗakin ne ya saka ta farka, ya kalleta ya ce "Baccin nan ba ya isarki ne?" Ta ɗaga masa gira alamar eh.
"Ko ki na da ciki ne?"
"Allah ya kiyaye, ya tsari mahaifata da ƙara ɗaukar ƙazantarka"
Ya ce "Hmm, ki bari cika baki, ki bari ayi gwaji tukuna"
Ramma ta ce "Ba abun da za a gwada"
Lambar saif ya kira, ya ɗaga ya ce "Yeah"
"Saif daddy ya ɓallo ruwa fa"
Saif ya ce "Zancen auren dai?"
"Shi fa, wai wata 'yar party chairman, ni tun ban ganta ba, ba na sonta wallahi dan kawai zan yi takara, sai na auri wata wadda ba na so, ya dage ya dage, kamar na gudu wallahi".
"Kai fa ka fiye gaggawa, ka bi su a sannu tukuna, ka je ka ga yarinyar "
Abdul ya ce "Ba ma wannan ba, Nina ta ga yarinyar nan a gidan nan, tana ta yi mini hauka, ga maganar auren nan idan ta ji, ban san haukan da za ta yi ba, ni gaba ɗaya na rasa abun yi ma".
Saif ya ce "Lallai ma Abdul, ba ka mayar musu da yarinya ba, kai baka kasheta ba, ka bar ta to yaya zaka yi da ita?".
"Mu haɗu in anjima a joint kawai"
Saif ya ce "Shikenan, Allah ya kaimu anjiman" yana kashe wayar ramma ta kalleshi ta ce "Bariki babu riba, dama duk wata hanya idan ba ta Allah, ai ba mai ɓullewa ba ce ba your excellency, na ga ku duniyar kawai ku ka saka a gaba, lahira kuma kun bar mana mu talakawa mu nema. Allah ya bamu a can.
Ni dai in an tashi, a taimakawa 'yan garinmu da hanya, a gyara mana babban asibitin garinmu, sai kuma makarantunmu, dan Allah kar a manta da mu"
Yayi murmushi ya ce "Ki na yi mini rashin kunyar za ayi abun da ki ke so?"
"To ba ma so, dama kuɗin haram bana halal ba" bai ji haushi ba, ya kwanta a jikinta, yana kashe mata murya, yana kiran sunanta.
"Rahmaaaa" ture shi tayi a fusace ta ce "Ni ka daina yi mini wannan abun 'yan iskan ba na so"
"Her excellency rahammaaa" yayi maganar kamar mai shirin yin shagwaɓa.
Wani uban takaici ya cika mata zuciya, ta kasa ture shi, sai ma cakulkuli da ya fara yi mata, ta dunƙule hannunta tana kai masa duka, amma ko a jikinsa, dariya ma yake yi, abun nata gwanin ban dariya.
***
Tun da aka idar da sallar asuba, Nabila ba ta koma bacci ba, ta shirya, gari na yin haske, ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan, fuskarta sanye da niƙabi.
A hanya gari ya ƙarasa waye mata, ta tafi gidan su Viper.
Duk da akwai tafiyar ƙafa sosai, daga titi zuwa gidan, amma yanzu idan tayi bulayin, tana iya gano gidan. Kasancewar wurin da nisa, gari yayi haske sosai ta isa gidan.
Ta tarar da su suna ta shirin ɗora karin kumallo.
Walid ya kalleta da mamaki ya ce "Lafiya?"
Ɗan mama ya ce "Mun shiga uku, wannan akwai mayya wallahi, idan ba kama mu aka yi ba, hankalinta ba zai kwanta ba".
Liti ya miƙe a fusace, ya ɗauki wuƙa a kan taga, ya ce "Ke ware dan kazakazanki, ko shi bai kashe ki ba sai na kashe ki ni, jarababbiya kai, uban me ki ke nema a wurinmu? Ke bayan haushinki da nake ji, har da wannan banzan saurayin naki ɗan sanda da ya din ga azabtar da ni, sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 53 Chapter of 121