Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
in ya kira Ni?". [2/2, 9:25 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* ?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tayi dani sabida wannan ciwon da ya same Ni, babu wanda bai sani ba a gidan, sai ya zamana kuma kamar sun soma jin ?yama na, ko bayi na shiga har gargaWi su Inna Asabe suke yi wa su Fatima a kan, "kar su soma su zu?una a inda na zu?una, don zasu iya kwasa, wannan cutan ba abun so bane, itama Madinan Allah ya yaye mata." Ko kayan sawa na babu mai taSa min, daga an yi magana su ce, "kar su kamu da cutan sanyi." Na soma shiga tashin hankali don da gaske mugun ciwo ne a tare da Ni, tunda ga shi na soma zama mujiya a gidan mu, komai a ce ina da cutan sanyi, abu kaWan a soma maganar, Shiyasa lokaci Waya na firgice bani da sana'a sai kuka, Ganin abun yayi yawa sai na saci jiki na je na faWa wa Yaya Haula halin da nake ciki Ita kanta hankalinta ya tashi, amma sai ta soma rarrashina tana faWa min, "ba mugun cuta bane kamar yanda kika Wauka, kawai dai ana saurin kwasa ne a jikin Mutum shiyasa kika ga suna miki haka, kuma ai kina shan maganin ki da sannu za ki warke kar ki damu kowacce Mace tana dashi, na wasu ya fi na wasu ne." Hankalina bai kwanta da maganar nata ba, taya ya zata ce min kowacce Mace tana dashi kuma ake guduna? Sai nace, "Yaya Haula to meyasa Ni kaWai ce nake soshe-soshe ga shi har an soma guduna? Kenan kuma kuna dashi amma ba a gudun ku sai Ni?" "Kinga Madina, baza ki gane irin wannan cutan ba koda nayi miki bayani, Ummanmu ta taSa min bayanin kawai cuta ne da yawanci ?azanta ne ke kawo ta sai kuma cushe-cushe da wasu Matan ke yi na maganin Mata, wasu kuma suna kwasa ne idan wasu suka yi fitsari a wuri suma suka yi a wurin, kin san nan ?auye ne basu fahimci kalan cutan ba shiyasa suke miki haka, amma in kika bibiya duk ?an gidan mu suna yi naki ne kawai ya fito fili, cutan kala-kala ne kowa da kalan nasa, ke naki kalan ta kenan amma in kika ci gaba da shan magani a hankali za ki warke, ko ba ki ga maganin da na kawo miki bane? To ai muma muna shan shi ne da Anti Hadiza, muna ji?a wa muna sha ne tunda muma muna fama dashi, don haka ki dena damuwa kin ji ko?" Kai na gyaWa mata duk da har yanzu ban gamsu ba sabida ban gama gane abun da take nufi ba, amma na ji sanyi a raina kasancewar cutan ba Ni kaWai ce da ita ba, ashe kowa yana dashi, sai dai na wani ya fi na wani ne kamar yanda Yaya Haula ta faWa min, kuma na yarda cewa rashin shan magani da wuri ne ya jawo cutan tayi ?arfi a jikina, tunda tun farko da na san haka ne da na soma jin alamomin ta; da na faWa mata an nema min magani, Shiyasa tun daga ranan na dage da shan magungunan da ake haWa min ba na wasa da su, Idan ya ?are da kaina nake zuwa gidan Jummai mai magani in amso in ji?a in ta sha, A hankali kuma abun ya soma min sau?i, ?ai?ayin da nake fama dashi da ziryan shiga bayi ya rage sosai, kuma Ni kaina na canza iya gwargwado ina Wan yin tsafta, tunda kusan kullum ina yin wanka ba kamar a baya ba; wanda sai in yi sati jikina bai ga ruwa ba, sai lokacin hankalina ya kwanta na ci gaba da gudanar da rayuwata hankali kwance A wannan lokacin ne aka soma shirye-shiryen bikin mu, Tun ana kwana biyu ?an uwa suka soma zuwa, yayyinmu da suke nesa da ?auyen mu duk sun soma hallara, Babban yarinyar Baban Sasa ta soma zuwa. Hajja Jamma, tare da zugan ?a?anta da ta kwaso, yanzu haka ta aurar da Yara uku biyu mata namiji Waya, Ita ce ?a ta farko a wurin Inna Lami, sai Yaya Yunus wanda yake bin ta, amma shi dayake ya daWe bai yi aure ba sabida yawon cirani da ya tafi cikin birni can garin Lagos, ya daWe a can yana yawon gararanba na neman kuWi, daga bisani kuma ya dawo nan Zaria tunda neman kudin ya gagara a can, A nan cikin Zaria ya samu wani uban gida da ya dauke sa aiki yana masa gadin gida, sanadin da yarinyar gidan ta gansa mai suna Sharhabila, tunda Yaya Yunus ya zo gidan ta Waura ido a kansa ta ji tana matu?ar ?aunarsa, bare ta gansa kyakykyawa jinin Fulani fari tass, shiyasa ta soma shige masa tana nuna masa irin ?aunar da take mishi, Shi kuma Yaya Yunus gani yake yi ya tsinci dami a kala haka ya amince mata yana soyayya da ita, sun sha?u sosai duk abun da take so shi yake so, Sharhabila ita kaWai ce wurin Iyayenta kuma suna ?aunarta, koda ta nuna musu tana son Yaya Yunus basu musa mata ba, sai dai mahaifinta ya nuna masa, "dole sai ya tashi tsaye yayi karatu ya nemi aikin kansa sabida ya mallaki ?arsa, don bazai bama mara ilmi da galihu ?arsa ba, in ya shirya zai biya masa kudi ya Waura karatun sa." Sanadin da Yaya Yunus ya koma karatu kenan, dama a lokacin ko primary bai yi ba, karatun allo kawai yayi, shi ne ya koma makaranta da taimakon mahaifin Sharhabila, kuma suka ci gaba da soyayyarsu babu wata matsala, Dalilin da yasa Yaya Yunus ya jima bai yi aure ba kenan, don lokacin har ?aninsa Yaya Nasiru ya ajiye Mata da nasa ?a?an, Yawanci Yaran Baban Sasa duk an aurar da su Maza da Mata, amma shi Yaya Yunus ya bi ra'ayin Mahaifin Sharhabila yana jiran har sai ya ba shi auren ?arsa, Tun abun yana damun su Baban Sasa don lokacin basu Wauki karatu a bakin komai ba, hatta Mazan ba sa karatun boko a zamanin, amma sai ga shi Yaya Yunus ya fita zakka a cikin su, ya je birni yayi zaman sa a can yana karatu, sai ya jima ma kafin su ganshi a ?auyen, lokaci Waya ya sauya musu zuwan ma sai ya Wauki tsawon lokaci, har manta wa suke yi dashi, tun Baban Sasa yana Waukar fushi dashi har suka ha?ura suka tsaya su ga iya gudun ruwan sa, ga shi sun yi masa Mata a ?auyen amma ya buWe musu ido yace, "bazai auri kowa ba sai Sharhabila, kawai suyi ha?uri." Tun a nan suka san cewa Yaya Yunus ya canza Wabi'u ba ya jin maganar su, Haka suka fita harkanshi suka zura mishi ido tunda ya dena zuwa wurin su gaba Waya A lokacin da ya gama secondary school Win sa, itama kuma Sharhabila ta gama karatun ta na NCE, sai lokacin Abbanta ya amince ya turo magabatan sa, Haka Yaya Yunus ya dawo ya sanar da Iyayenmu, Amma sai Baban Sasa yace, "in har shine bazai nema mishi auren yarinyar nan ba, don ba yanda za a yi kamar sa ya auri Mace irin wannan, wacce ta fi shi komai daga ?arshe sai dai ta juya shi, in har bai bi zaSin su ba baza su taSa zuwa su nema mishi auren ta ba." Duk yanda su Baffa suka so su tausasa Baban Sasa amma ya ?e?ashe, yace, "bai yafe ma wanda ya shiga gaba ya nema masa auren yarinyar ba." Shi kuma Yaya Yunus sai ya koma ya sanar da Abban Sharhabila, sabida ganin ?arsa tana son Yaya Yunus shi kuma ya goya masa baya da kansa ya aura mishi ?ar shi, sannan ya ba shi gidan da zasu zauna a nan cikin Zaria, ya kuma nema mishi aiki a ?ar?ashin sa, sannan ya ba shi dama ya ci gaba da karatun sa, Yanzu haka Yaya Yunus ya gama karatun sa na degree, shi kaWai ne ya fita Zakka a danginmu, shi kaWai ne yayi karatu ya zama Wan birni, Domin Ni kaina ada ban taSa tunanin shi Wan uwanmu bane, sai dai kawai kamanni da muke yi dashi wanda kana kallonsa ka san jinin mu ne, An ja lokaci mai tsawo tun kafin a haife mu har muka girma bamu taSa ganin sa ba, Sai rasuwar Babanmu da ya zo gaisuwa tare da Matarsa da ya'yansa biyu dukka Maza da ya haifa, Wannan zuwan ne yasa da yawa ?a?an gidan mu muka san Yaya Yunus, Kuma ya zo da abun mamaki tunda a lokacin yayi kuWi sosai, ga matarsa ?ar gayu da Yaransa sai zuwa kallonsu ake yi Ya sha faWa a lokacin don kusan tsine mishi Baban Sasa ya so yi a wannan zuwan, An yi tashin hankali sosai Wakyar aka shawo kan Baban Sasa ya yafe masa, Sai da Yaya Yunus Win yayi ta ba shi hakuri sannan yayi masa alkwarin, "daga yanzu zai ri?a zuwa akai-akai yana duba su." Don ma ya yarda da maganar sa har siyan fili yayi a cikin anguwan namu, babu nisa da gidan mu da filin nasa, yanzu haka har an gina masa gidan ginin zamani flat, tunda aka yi ginin sau Waya ya zo ya duba ya koma, basu taSa zama a gidan ba amma duk an zuba komai na bu?ata a gidan, Sai wannan bikin namu da za a yi sai ga su sun dira, domin babu wanda yayi tunanin ganin su sai ga su tsalam, Hajja Jamma ta zo da safe, sai ga su Yaya Yunus kuma da yamma, Nan fa gida ya cika da murnan mutanen birni aka rasa inda za a saka su don tsaban farin cikin ganin su Dukkan su a dakin Inna Lami suka sauka mutane sai tururuwan zuwa gaishe su suke yi, Sai da aka natsa da jama'a sannan su Yaya Yunus suka wuce sashin Baban Sasa suka gaishe shi Shi kansa yayi murnan ganin su baki har kunne, sai kallon jikokin nasa yake yi gunun sha'awa, ya rungume su yana shafa kawunan su yana musu tambayoyi? Jima wa kaWan kuma sauran iyayenmu Maza suka dinga shigowa ana gaisa wa, Daga ?arshe Yaya Yunus kaWai ya zauna tare da yaran, Ita kuma Sharhabila ta koma sashin mu Duk da yanda Yaya Yunus ya ba kowa sha'awa a cikin dangi, dashi da ilayansa, amma hakan bai sa su Baban Sasa sun ji suna son Yaransu suyi karatun Boko ba, domin akwai gaba mai tsanani tsakanin su da karatun Boko, har yanzu kansu ya kasa wayewa a kan zuwan karatun zamanin, sun ?i yarda dashi, suna ganin kamar hanya ce ta gurSacewar ?a?an su, misali ga shi a kan Yaya Yunus, karatun ajami shi suka fi dogara dashi, sauyawan Yaya Yunus bai sa zuciyoyinsu ta sauko ba, kuma baza su taSa yarda wani daga cikin Yaransu ya ?ara ?etare maganar su kamar Yaya Yunus ba, daga kanshi babu ?ari, don shi kaWai ne zai fita Zakka a cikin su, sabida ganin sa suke yi ya gagare su. *** Har dare su Yaya Yunus suna gidan mu; tunda basu wuce sabon gidan su ba, duk da an share an gyara musu komai kasancewar yayi ?ura, su Yusuf aka sanya suka je suka gyara suka tsabtace, Sai bayan sallan isha'i sannan suka wuce gidan nasu Washe gari kuma sauran ?an uwa suka ci gaba da zuwa gida sai ?ara bun?asa yake yi, Tun ranan farko da muka ga Matar Yaya Yunus bamu sake ganin ta ba har ranan bikin, domin ba ta zuwa sai dai Yaya Yunus ya zo da Yaran, Sai a ranan bikin ne ta zo ta ci kwalliya sai ficchi take yi da iyayi, dama Matar akwai yanga, ga shi daga gani tana ?yan?yamin mu don ko magana wannan sai ta ga damar yi, duk wannan wula?ancin amma haka zaka ga ?an uwa suna ta shige mata, abun ka da ?an ?auye mutanen karkara basu saba ganin ?ar birni kamar ta ba, tunda ta zo gidan yau ta shige cikin dakin Inna Lami ko fita ta ?i yi, sai faman latsa babban wayanta take yi tana taunan chewing gum, duk wanda ya zo sai dai ya gaishe ta ita kuma ta amsa a gadarance, ga yaranta akwai shegen ?yuya basu yarda da kowa ba, To dama idan mutum yana da kuWi ba a ganin laifin sa, gani suke yi don ita ?ar birni ce rayuwarta ta fita daban da nasu shiyasa halayyarta ma daban ne A wannan lokacin mu kuwa muna can sashin Baba Sama'ila a can muke taronmu mu Amare, Kowa hankalin sa a kwance ban dani, na kasa kwantar da hankalina sabida yau ne ranan da zamu bar gidanmu mu je mu rayu a gidajen mu, shikenan an raba mu da ?an uwanmu muma zamu je mu yi rayuwa a gidajen Mazajen mu, har kuka sai da nayi Yaya Haula ce kaWai take rarrashina, abun ya haWe min biyu sabida rashin ganin Ummanmu, shiyasa hankalina ya kasa kwanciya sai kuka nake yi ina cewa, "ta kira min Umma ta zo." Amma har aka gama taron nan babu Umma ba labarin ta, tun Yaya Haula tana faWa min, "zata zo zata zo." Har na cire rai tunda ga shi har Magriba ta gabato za a tafi damu, Har lokacin ban dena kuka ba haka aka wuce damu sashin Baban Sasa, a nan dukka aka yi mana faWa sannan aka raba waWanda zasu kaimu Wakunan mu Dama Binta da Fa'iza yayyinmu suka aura, Fa'iza ita ta auri Yaya Ahmadi, Ita kuma Binta ta auri Yaya Shamsu, Kuma duk a gidan zasu zauna Sarayin Samarin gidan, dama duk wanda zai yi aure in dai namiji ne a gidan yake yankan fili yayi auren sa tunda gidan babba ne, kowa yana da gadon sa a gidan, yanzu haka ?ofofi uku ne a gidanmu saboda girman gidan, ta asalin babban ?ofan gidan; ta nan ne sashin su Baban Sasa da su Baffa Yaya Haula da Matar Yaya Nasir; da kuma Matar Baffonmu Abdullahi suka kaini gidan Alh. Badamasi, Gidan madaidaici ne mai kyau, ya sha penti an gyara ko'ina kamar ba ?auye ba, Sashin Alh. Badamasi mu haWu a falo ne, ga Wakina ga Wakin Matarsa haka gidan yake, Sai kuma idan an zagaya ta baya a nan surakansa suke Yaransa biyu Maza da suka yi aure, amma ?ofan su daban ne; sai dai suna iya shigowa gidan tunda a haWe yake, Yara uku ya aurar, Mace Waya tana gaban kauyen mu a can tayi aure, Sai sauran huWun Yaran da yake dasu, Matasa ne sun girma domin babu sa'ana a ciki; sai Autar su Mace wacce yanzu bata fi shekaru takwas ba Yau dai ga shi ina ji ina gani su Yaya Haula sun kawo Ni Wakina sun tafi sun bar Ni, ina kuka da majinu amma babu damar bin su, tunda a ?auyen abun kunya ne a ce Amarya ta gudo dakin Mijinta sabida tsoro, idan hakan ta faru ba ?aramin wula?anta da muzanta take yi ba, kuma zai zama tarihi har ya'ya da jikoki sai ana yi da ita ana faWan abun kunyar da tayi. [2/2, 9:26 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ?? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 7 of 55