Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na ci gaba da kasancewa a haka tunda damuwar da ke tattare da Ni ya soma haifar min da babban matsala, babu bu?atar in ci gaba da kasancewa a haka in har ana son rayuwata, dole sai na fitar da damuwa a tattare da Ni, domin idan irin wannan na faruwa da ?ananun Yara kama ta; rayuwar su tana zama in a difficult situation; Wanda hakan na shafan rayuwarsu su tashi a cikin mental issues, ko kuma ciwon damuwa ko ciwon zuciya, daga ?arshe ma su rasa hankalin su, tunda tun kafin ma su san meye rayuwa; wasu matsaloli masu girma sun addabe su, zasu tashi cikin ?unci wanda zai hana su samun damar fuskantar meye rayuwar ita kanta. Tabbas dole ne yayi iya yin sa domin taimakawa yarinyar nan, babu wani doka da ta amince a yi wa yarinya auren dole ko a tauye mata ha??inta. Tunda yayi save na numfashina ya tabbatar da babu wani matsalar kuma, kawai halin tsorata ne da kuma rudin da nake ciki, wanda dole sai ana bu?atar samun hutun ?wa?walwata, dalilin da yasa yayi min allura kenan sannan ya koma bama Umma ha?uri, kasancewar har lokacin kuka take yi, "Ki yi ha?uri Umma, Ni a ganina in har ana so a ceci Madina daga faWa wa ?uncin rayuwa; da kuma ?wato mata ha??inta dole ne sai mun saka hukuma a cikin zancen, tunda ba ta son auren bai kamata a yi mata ba, a wancan ta sha wahala amma tsaban rashin imani yanzu kuma su sake mata wani auren? Wasu irin mutane ne waWannan? Ai koda suna da hakki a kanta but babu wata doka da ta basu damar tauye ta har haka. Don haka ki kwantar da hankalinki babu mai iya amsar ta, ko meye zamu yi don ?wato mata ha??inta, ki zauna a wurin ta har zuwa nan ta farka, Allah zai bata lafiya, idan ta farka sai a yi gaggawar kira na Please?" Cikin hawaye Umman ta soma mishi godiya har sai da ya dakatar da ita, Fita yayi a Wakin sabida a ganinsa ba ya bukatar godiyan su, aikin sa kawai yake yi, tunda Allah ya haWa su dole ne su taimaka musu, Lallai dole ya kira Hajiya Ummee ya sanar mata halin da ake ciki, idan basu taimaka ma yarinyar nan ba za a Sata mata rayuwa na har abada ne, wannan ai zalunci ne, sun cutar da ita da yawa. *** _____Baban Sasa kuwa ba ?aramin Saci ransa yayi ba ganin sun dawo babu Madina, da kuma yanda suka yi da Umma da suka sanar mishi, yace, "shikenan zai nuna mata iyakan ta kuwa, lallai in bata bada Madina ta dawo gida ba wlh sai tayi nadamar sanin su, bata isa ta wula?anta su ba, ba hukuma ba ko waye zata kai ?ara wajen su shi ya san matakin da zai Wauka a kan duk wanda ke da hannu a kan maganar." Baffa da ransa bai dad'i ba da duk abubuwan da ke faruwa, domin ya Wauki alkawarin bazai yarda a sake wula?anta wa Madina rayuwa ba, yanzu kuwa dole ne ya shawo kan Baban Sasa domin sassauta wa a kan lamuran, abun farin cikin ma da kasancewar Madina Yunus take aure, yana ganin wannan dama ce ta same shi domin ganin Rayuwarta ta inganta, tunda Yunus a birni yake da zama dole ne ya shawo kan Baban Sasa a dan?a Madina a can gidan da yake zaune, ba wai zamanta a ?auye ba, Wannan dalilin ne yace wa Baban Sasa, "don Allah idan da hali shi akwai alfarman da yake so ya nema wa Madina, na tabbata idan Asiya ta ji inda ?arta zata zauna baza ta yi jayayya ba, Ni da kaina zan je in fahimtar da ita wanda aka Waura wa Wiyarta, da kuma inda zata zauna, maimakon da ka ce Madina zata zauna a gidan nan nashi da ke ?auye, mai zai hana Yaya ta zauna a can birnin kusa da shi Yunusan zai fi, na tabbata Asiya baza ta ?i ba, sannan maganar nan fa har da hukuma za a sako, ka san halin su babu abun da baza su iya ba, ka bani dama in je birnin in fahimtar da ita, tunda babu wani gata da ya wuce auren Madinan, sannan ma ba a nan zata zauna ba na tabbata in ta fahimce mu komai zai daidaita." "Kana nufin in janye maganar kawo Madina nan ?auye ta zauna kusa da mu? Kar ka manta nayi hakan ne fa domin nima Wana ya dawo kusa dani hankalinsa ya karkato wajen mu." Baffa gyara zamansa yayi yace, "?warai kuwa Yaya, ai tunda aka yi auren nan dole ne Yunusa hankalin sa ya karkato kanmu, ba wai dole sai Madina ta zauna a nan ba, abun da zamu yi kawai don kwantar da hankalin Asiya shine Madinan ta soma zama a can birnin, na tabbata nan gaba da kansa Yunusa zai iya dawowa da ita nan don ya ri?a le?o mu, amma ba wai mu Wauki zafi ba, domin a can akwai waWanda suke taimaka mata kuma ga dukkan alamu manyan mutane ne, ai na san ka ga Matar da suka taho ?auye tare da ita?" Shiru Baban Sasa yayi duk da har lokacin bai saki fuskarsa ba, cike take da fushi da tsantsan Sacin ran da ke cikin ta; wanda alamun bai yarda da maganar Baffa ba har yanzu, don gani yake yi kamar Asiya ta ci galaba a kansu ne, har kamar Asiya zasu zauna sai abin da ta so zasu yi? Bayan ?ar tasu ce ko'ina za a je, Amma da Baffa ya ci gaba da ba shi baki yana sake fahimtar dashi gwara a bi hanyan lafiya a bi komai a sannu, Wanda su kansu su Baba Iro da ke wurin daga ?arshe suma sun goyi bayan maganar Baffa, sun kuma sake sanya baki wajen tausan Baban Sasa, sun ce, "ko ina Madina ta zauna ai dole tana ?ar?ashin Wansu ne, kuma auren yana nan a kanta tunda bata bijire wa umarnin su ba, dama zaman auren shi suka fi so tayi, don haka ko'ina ta je wannan ba damuwar su bane in har tana tare da Yunusan, ba sai dole ta zauna a nan ?auye ba." Sai lokacin hankalin Baban Sasa ya kwanta har ya amince da Baffan ya je birnin ya fahimtar da Umman, idan ma bata yarda ba zai Wauki mataki don dole, Sannan daga nan sai ya ba Yaya Nasiru umanin kiran Yunus a yau ya zo ya same shi, ko me yake yi ya ajiye ya zo ya same shi, Tunda shi bai san ma wainar da ake toya wa ba, bai san da auren da aka yi masa ba yana can hankalin sa kwance, kwatsam! Sai ya ji wannan kiran da dole aka tilasta masa biyo ?auye da yammaci ya zo don jin ba'asi Bayan ya iso a dan?areren Motansa; ?an uwa da abokan arziki suka mamaye shi ana murnan ganin sa, daga ?arshe suka shiga cikin gidan inda ya sauka a sashin iyayensa, Matan gidan sai tururuwan zuwa gaishe shi suke yi kowa da ?ar abun tarban sa, Babu abun da ya ci tunda bai saba cin abun ?auyen ba, ko an mishi tayi bazai iya ci ba, in fact ma ko ruwa bai sha ba haka suka gama gaisawa har kowa ya watse aka ragu a sasan, ya rage daga ?anninsa su Yaya Nasiru su ke zaune da shi ana Wan taSa hiran yaushe gamo Inna Lami kuma na kichen tana mishi girki tunda basu san da zuwan nashi ba, don haka nan da nan aka sanya yara suka siyo Taliyan Yara aka shiga girka mishi, tunda sun ga irin ciman su ne na gayu ta san bazai ?i ci ba, kasancewar ko a kwanakin baya; irin sa tayi ta dafa wa Matarsa da Yaransa don sun ?i cin komai sai shi Yanzu ma da ko ruwa bai sha ba, sai Yaya Shamsu yace, "ko a siyo mishi ruwan leda ne ya sha tunda ya ?i shan ruwan gidan?" Murmushi kawai yayi ya girgiza kansa yana cewa, "bazai sha bane, idan ma zai sha akwai ruwa a cikin motansa zai Wauka ya sha." Tunda suka ji haka sai basu sake mishi tayi ba, Babu jima wa kuma sai ga kiran Baban Sasa yace, "ya zo ya same shi." Hakan ne yasa ya mi?e ya fita yabar su Yaya Ahamdi a nan wurin shi kuma ya wuce sashin Baban Sasa, A lokacin shi kaWai ne a zaune yana jiransa, Sai da ya zauna suka gaisa ya tambaye sa iyalansa? Sannan yace mishi, "ka ci abinci bayan ka zo?" "A'a Baba, ba na bukatar komai tunda ban daWe da cin abinci ba." Kansa ya jinjina yana mai sake tan?washe ?afafunsa, yakai duba ga Yaya Yunusan da ya sauke kai ?asa yana jiran ya ji abun da yasa aka kira sa da wannan yammacin bai shirya wa hakan ba, kiran sunansa da Baban Sasa yayi, shine dalilin Wago kansa yana duban sa shima tare da amsa wa a cikin sanyin murya, don gaba Waya ya soma sarewa da wannan kiran, haka kawai yake jin ba alheri bane kiran nan, ta wani Sangare na zuciyarsa buga wa take yi alamun akwai abun da zai same shi Baban Sasa kuma gyaran murya ya sake yi yana cewa, "akwai hukuncin da muka yanke ne wanda ban nemi ra'ayin ka ba; duba da cewa na isa da kai sabida kai Wana ne na cikina, a kaf cikin gidan nan babu wanda ban isa dashi ba, babu kuma wanda ba na iya yanke hukunci a cikin rayuwarsa kai tsaye batare da sun yi min jayayya ba, domin in nuna iko a kanka shiyasa na yanke wannan hukuncin kuma na kira ka in sanar maka, na san ka san Madina ?ar wurin Babanka Sule wanda ya rasu, tana Waya daga cikin Yaran da aka yi wa aure wancan zuwan da kayi nan ka halarci auren su, to maganar da nake maka yanzu haka auren ta ya mutu tun kwana biyu da aka kaita, na san ba lallai ka sani ba amma yanzu haka na mayar da auren a kanka, shekaran jiyan nan aka Waura maka aure da ita..." Wani irin zabura da Yaya Yunus yayi shine ya dakatar da Baban Sasa daga maganar nasa, wanda ya bi shi da kallo fuska a turSune yana son ya fahimci halin da yake ciki, Shi kuma Yunus tsananin kiWiman da yayi ne yasa shi shiga wani hali wanda nan take zufan tashin hankali ya soma keto mishi, har yanzu kyawawan idanunsa a zare a kan Baban Sasan yana son ya gaskata abun da yake faWa masa, "Ya na ganka a haka kamar baka yi farin ciki da abun da na faWa maka bane? Wannan umarni ne kuma ba na neman shawaran kowa akai, a baya ka saSa mana wanda mun so mu haWa ka aure da Dije ?ar wurin Baffonku Abdullahi; amma ka bijire ka kawo ra'ayin kanka, in har ba wai ka gagare mu bane ina so daga yanzu ka shirya tarban Amaryan da muka yi maka a koyaushe, da zaran mun amso ta a wurin Mahaifiyarta zan sa a kawo ta har can inda kake zaune, don haka ya rage naka ka zauna da ita ko akasin hakan..." Taran numfashin Baban Sasan yayi cikin tsananin tashin hankali da kiWiman da yake ciki; tare da furta, "amma Baba Ni yaushe nace maka ina bukatar wani aure? In fact ma Ni da nake birni taya ya zaka Wauki ?ar ?auye ka ce zan iya rayuwa da ita?" Sai ya soma girgiza kansa da ci gaba da faWin, "impossible Baba! Ni rayuwata ta bambanta da naku wlh bazan iya zama da wata bayan Matata ba, sai dai ku canza wata shawaran..." Tsawa Baban Sasa ya daka mishi wanda har jikinsa rawa yake yi tsaban yanda Sacin rai ya nuna a kan fuskarsa, duk da dama a cikin Sacin ran yake ga shi yanzu Yaya Yunus yana son ?ara masa, take ya nuna sa da yatsa yana cewa, "bazan zauna ina jayayya da kai ba, umarni ne wannan Yunusa, kuma ba a haife ka da har zaka zauna kana bijire wa abun da na gindaya ba, wlh ka ji na rantse maka idan baka yi abun da nace maka ba; to daga yau zan cire ka a kan zuri'ata; zan tsine maka albarka ka bi duniya a kan ?in bin umarni na, shashasha mara hankali mara tunani, har Ni zan yi magana ka zauna kana faWa min ra'ayin kanka? Ni ne Mahaifinka don haka ya zama dole ka zauna da Madina ko kana so ko ba ka so, zan gani idan ban isa da kai bane". _Happy Juma'at Masoyana, enjoy your day, Allah ya bamu alkhairin da ke cikin ta._ [2/2, 9:37 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 14 of 55