Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ni gidansa bayan ya san komai zai iya faruwa? Bare ?ar uwanshi ce akwai aure a tsakaninmu wata rana labarin zai iya sauya wa, musamman yadda ta ganni kyakkyawa kalansa ina samun gyara zan sauya, ita dai kwata-kwata bata yarda ba don haka ta nuna mishi sam a'a Ya san cewa kishin ta ne ya motsa, don haka ya ci gaba da lallaSa ta yana cewa, "ta ba shi Wan wasu lokuta before ya mayar da Ni, amma ban da yanzu, kuma abun da take tunani bazai taSa kasancewa ba, ya rasa wacce zai kula sai Ni ?ar ?auye? Ai ta san ya fi ?arfina." Daga nan fa ya ci gaba da muzanta Ni a gabanta yana faWan duk maganar da ta zo bakin sa don dai ya sake kwantar mata da hankali A gabana ina jin su duk abun da suke faWa, kaina a ?asa ina jin kamar in fashe da kuka, zuciyata ta cika da ?unci da ba?in cikin yanda yake ci min mutunci yana zagina duk a kan Matarsa, har yana cewa, "mai zai yi da sauran Maza? Ta kwantar da hankalinta ko a kafa aka Waura mishi Ni sai ya kwance." Idanuna na lumshe ina mai jin wasu hawaye masu zafin gaske suna zubo min, Ni kuma a haka zan ?are kenan bani da madafa da farin ciki? Ina ji ina gani ana zagina ana ci min mutunci da aibata Ni, amma bani da yanda zan yi, ko giyan wake na sha ai Yaya Yunus ya fi ?arfina; nesa ba kusa ba, wutsiyan ra?umi tayi nesa da ?asa. Daga ?arshe ina jin sanda suka bar wurin gaba Waya amma hakan bai sa na Wago kaina ba, idanuna suna kullen har yanzu na Waura kaina a ?afafuna tamkar babu numfashi a tattare da Ni, rayuwar duniya kawai nake tunani, da kuma yanda zan rayu a cikin wannan gidan. Sai ga Sharhabilan ta fito tana daka min tsawa, Take na Wago kai ina kallonta da rinannun idanuna masu cike da rauni da zallan tausayi Wani kallon sama da ?asa tayi min tana jan dogon tsaki, tana ri?e da hannun Sadam da ke biye da ita, sai ta zauna a kan Kujera ta Waura kafa daya kan Waya tana cewa, "daga yau ba zaman hutu ya kawo ki ba, tunda already kin san abun da yasa aka kawo ki nan, so da sannu zan kafa miki sharuWWana da yakamata ki sansu kuma babu gindaye wa, zan fara horar da ke a kan abubuwan da nake so; don kaf aikin gidan nan ke za ki ri?a yi komai da komai, abu na gaba ba na son ?azanta, sannan kibar ganin Husband Yayanki ne; ba na son in sake ganin koda magana ta sake haWa ku dashi, duk abun da kike son sani Ni za ki faWa ma wa, ko gaisuwa ba na son ya haWa ku, kina jina?" Ta ?are maganar tana mai daka min tsawa, Take kuwa na amsa ta jikina na rawa kamar mazari, Sai ta ja dogon tsaki tana mai yatsina fuska, ta kalli Sadam tace, "Waga ni mu je in nuna mata masaukin ta." Sai ta mi?e rike da hannun Yaron, batare da ta kalle Ni ba tace, "biyo NI." Kasancewar na gane dani take yi, shiyasa na tashi na bi bayanta jiki na rawa, Har mun fara tafiya ta juya tana kafa min ido, sai tace, "uban wa kika bar wa wancan kayan; baza ki Wauko ki taho dashi ba?" Waiga wa nayi na hangi akwatin kayana a wurin, take na juya na bi umarnin ta na Wauko kayan na bi bayanta har lokacin jikina rawa yake yi Wani Waki takaini Wan dai-dai, gado ne kawai a ciki da wurin ajiye kaya, sai bayi wurin kewaya wa, Ta nuna min tace, "nan ne zan ri?a kwana." Sannan tabar Wakin ta tafi ta bar Ni a tsaye, Bata sake bi ta kaina ba har na gaji da tsayuwa; na zauna ina ta tunani tare da kallon dakin da aka bani mai kyau a ido, Har dare yayi basu sake bi ta kaina ba ina nan zaune na rasa madafa tunda ban san me zan yi ba, ga shi ina son shiga bayi sannan ina son yin sallan da suka wuce Ni, amma ban san inda zan je in yi ba, bayin da ke cikin Wakin ban san mene ne ba bare in duba, tunda na zauna ko jirga wa na kasa yi, Har dare ya tsala ban sake jin wani motsi ba, tun ina gyangyaWi ina matse ?afafuna sabida fitsarin da ya matse ni, har dai barci ya sure Ni a haka cikin wani yanayi ina zaune a yadda nake Sai washe gari Sharhabila ta dawo dakin ta tayar da Ni, tana bi na da mugun kallo cike da ?yama tace, "shegiya an samu wurin banza har da hangame baki ana barci, dalla tashi ki shiga wancan ?ofan ki yi wanka ki canza kayan jikinki; ki zo ki same Ni ina jiran ki, saura ki Sata min lokaci ki ga yanda zan yi da ke." Ta ja tsaki ta fice a Wakin cikin tafiyan ?asaita Ni kuma jiki na rawa na mi?e na nufi ?ofan da ta nuna min, ina buWe wa na fahimci bayi ne duk da babu komai a ciki sai famfo da sabulan wanka, sai bokiti, hakan ne yasa da sauri na du?a na saki fitsarin da ya cika min mara fam yana shirin fitowa, ban tsaya Sata lokaci ba tunda ta sanar min tana jira na, kasancewar na san famfo tunda akwai a ?auyen mu, na san ruwa yake fitar wa shiyasa na Wauki bokitin na tara na zuba ruwan, ruwan sanyi ne amma a haka nan nayi wankan tunda bani da yanda zan yi, dole abun da na gani da shi zan yi amfani, Take kuwa wani sanyi ya ratsa min jiki tsaban azaban sanyin ruwan, duk da na saba wanka da ruwan sanyi amma sai da jikina ya soma karkarwa, tunda damuna ne akwai sanyi a gari sosai na ji sanyi na ratsa Ni, Cikin sauri na gama na fita na bude kayana na Wauko wata doguwar riga ?ar kanti sabuwa fil na sanya, farar riga ce mai igiya a baya, saman rigan wuyan V ne an yi masa aiki da ba?in zare da kore, rigan ba ?aramin kyau tayi min ba nan da nan ta sake fito da yarinta ta, ban tsaya wani Sata lokaci ba na nemo hula na saka a kaina, ko bi ta kallon kayan ban yi ba tunda duk sababbi ne wadanda Alh. Badamasi yayi min na aure, ban taSa ganin kayan ba koda aka nuna a gidan mu, Ni kaina a yanzu na tsorata nayi mamakin ganin yawan kayan, amma hankalina ba ya wurin ban tsaya duba wa ba na fice da sauri, Hanyar da na ga ta biyo dani jiya nan na bi, sai gani a falon inda take zaune ita kaWai, Da alamun babu kowa sai ita, Yaya Yunus tare da yaransa ya wuce da su school Tana gani na ta haWe fuska tana jan tsaki, Ni kuma na zube a ?asa ina gaishe ta amma kamar bada ita nake yi ba, sai da ta sha ?amshin ta son ranta sannan ta mi?e ta nufi wurin Dinnig, abinci ta zuba min a wani plate sannan ta kawo min gabana, ta bani umarnin, "in cinye shi yanzu." Daga haka tabar wurin ta shige Wakinta Dama da yunwa na kwana hanjin cikina sai kaWa wa suke yi, take yawuna ya tsinke sabida ganin soyayyen dankalin Hausa cikin plate Win, nan da nan na saka hannu na dinga Wauka ina tusa wa a baki kamar zan haWiye plate din, yanayin cin da nake mishi take na sha?e ya cika min ma?ogwaro ga babu ruwa, Da sauri na mi?e ganin zan mutu na koma Wakin da ta kaini jiya da gudu, a can na shiga bayi na sha ruwa a famfon sannan na samu damar koma wa na ?arisa cinye dankalin har ina lanWe baki, kwata-kwata bai ishe Ni ba amma babu damar ?ara wa, ga shegen daWi da yayi min a baki har kunnuwa na motsa wa suke yi, Na jima a nan zaune kafin ta dawo ta iza ?eyana ta kaini wani waje, wanda a bayaninta na gane kitchen ne Duk abubuwan da yakamata in sani sai da ta zauna tayi min bayanin komai, daga ?arshe ta sanya Ni na taya ta girki ina yin duk abun da ta sanya Ni ina shan zagin ta, don wani lokacin har marina take yi, Ko kafin mu gama aikin sai da nayi kuka duk ta kumbura min fuska da hannunta, Kuma bata bar Ni a haka ba; ta saka Ni a gaba na wanke mata duk abun da muka Sata, Sannan ta saka Ni shara na share falon na goge duk tana nuna min yanda zan yi, tana jan min kunne, "saura in kuskure kar in koya da kyau, wlh sai ta Wumama min jiki, duk kuskure Waya da zan yi mata kamar na rasa abinci a gidan ne." Tabbas ban san cewa matar nan muguwa ba ce sai yau da na tsinci kaina a hannunta, lallai yau na tabbatar da cewan na faWa wata sabuwar rayuwa mai wuyan fice wa, babu tausayi babu imani ga mutanen gidan, sai dai kuma bani da halin bijire musu duk abun da suka sanya Ni dole in yi, Daga ranan sai na zama tamkar Jaka babu kalan wahalan da ba na sha a hannun Sharhabila, ga shi abu kaWan sai duka, A cikin kwana uku cur ta koya min duk abun da yakamata in sani, abinci ne kawai ba ta sakar min dukka amma tana koya min tare muke komai, ina kuskure wa ko ban fahimci wani abun ba sai ta tafka min mari, nan da nan lokaci Waya fuskata ta sauya kamanni har wani tara jini fuskar tayi, abun ka da farar mace tuni fuskar tayi jawur sabida tsaban wahala, Komai na gidan yanzu Ni nake yi, hatta kula da yaransu ya dawo hannuna, Ni nake saka musu kaya na cire musu sannan na wanke, duk in zasu sauya kaya Ni za a kira in canza musu, wanka ma sai yazamana Ni nake musu, Lokaci Waya yaran sai suka saba dani har magana suna min tunda sun ga ina lallaSa su ina musu duk abun da suke so; Ni kuwa gudun kuskure ne. Sai ya zamana ko wani abun suka samo in har na ci ne sai su kawo su bani su ce in ci, tun ina ?in amsa musamman Sadam yayi ta kuka wai, "ya bani abu na ?i amsa." Hakan ne yasa nake amsa ina ci bani da yadda zan yi, amma cike da tsoro nake kar Sharhabila ta gane ina cinye mata abun Yaranta Ai kuwa kamar na san zan sha wahala ne in ta gane, ranan da Sadam ya kawo min ayaba yace, "ga shi Dadyn mu ya siyo ya bamu, kema ki ci wannan." Har na amsa na Sare ina ci, Sai ga Sharhabila ta shigo Wakin Yaran, tunda a nan nake ina gyara musu Wakin, Tana ganina ta daka min tsawa tana cewa, "shegiya muna-fuka dama abun da kike yi kenan, idan na basu abu ki ?wace ki cinye?" Baki na buWe da ninyar yin magana har na fara rantsuwa; amma marin da ta sauke min a kuncina tuni na saka ?ara na kama kumatun ina ihu sabida azaban zafin marin, sauran ayaban da ke bakina dole suka zubo waje tsaban wahalar da ya tunkaro Ni, Hakan bai yi mata ba sai da ta haWa da duka tana zagina tare da jan min kunne ta murWe Sadam kuwa kuka ya saka yana mai ri?e hannunta da cewan, "Mamy ni na bata fa ta ci, Mamy ki sake ta haka nan Ni nace ta ci." Wani kallo ta watsa mishi tace, "kai ka bata don Ubanka an ce ka bata ne?" Sai ta zare mishi ido tace, "idan ka sake Wauko wani abu ka bata wlh sai na saSa maka Sadam, Sace dalla ka bani waje." Yaron sai ya fita yana kuka har da ?ara volume Ita kuma ta sake Ni tana cewa, "saura ki zauna ki Sata lokaci a nan kar ki zo ki ?arisa min sauran aikin ba, ki kuma gyara musu Wakin da kyau ko tsinke ba na son gani, ki fito da kayansu ki wanke musu kar ki soma ki saka a inji, da hannu nake so." Jiki na rawa na amsa ma????      !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta babu damar sakin kukan da ya taho min, Sai da na ga ta fita sannan na fashe da wani marayan kuka har da shashshe?a, ban tsaya Sata lokaci ba na ci gaba da kimtsa musu Wakin zuciyata kamar zata fashe don azaban marin da tayi min, har ?ara taSa wurin nake yi ina mai ci gaba da zubar da hawaye, Sai da na gama sannan na fita zuwa falon, Babu kowa sai Yaya Yunus da ke zaune daga shi sai singlet yana shan juice a cup, hannunsa Waya kuma ri?e da waya, Kaina na sunkuyar a ?asa da ninyar wuce wa, don ban manta gargaWin da Matarsa take yawan min a kansa ba na dena kallonsa, Har na kusa isa kitchen na ji muryansa yana cewa, "Kee! Zo nan". [2/10, 10:43 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ?? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 16 of 55