Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta buga mishi a kafansa a karo na biyu, tana cewa, "dalla tashi Kasa kamar wani mushe, ko dai sake maka wani daren za a yi? Farouk tashi mana, Farouk... Farouk..." Sai da ta kira sunansa kusan sau uku before ya motsa, Tace, "amma Allah yayi maka nauyin barci wlh, ban taSa ganin mutum irin ka ba." Idanu ya buWe yana kallonta, sai kuma ya mayar yana mai kwantar da kansa batare da yace mata komai ba yana sauraron surutun nata, ganin ta cika sa da faWan yawan barcin nasa ne, cikin magagin barcin da bai ishe sa ba yake cewa, "Hajiya kin cika ?orafi wlh, kina ganin fa ba na samun isasshen barci ne sai a wannan time Win, kuma yanzu na kwanta but kina min ?orafi." "To wani yace kar kayi barcin? Ko Ni na hana ka? Mutum kullum agogo baza ka sarara wa kanka ba kana hanyar asibiti koyaushe, ko lokacin kanka baka dashi, a haka zaka yi auren ma baka da lokacin yarinyar mutane, ai dole ka ?i ?aunar aure tunda aiki ka saka a gaba, ga karatu ka hana kanka sukuni." Sai ta ja yatsun ?afafunsa ganin tunda yayi maganar ya sake kifa kansa a pillow kamar ya koma wani barcin, "da Allah tashi ka bani aron dubu biyar inyaso sai ka koma barcin, ka kwana ma a haka Ni bai dame Ni ba, amma sallame Ni in tafi." ?ago kansa yayi yana bin ta da kallo fuskarsa a dame, da alamun ta takura masa ne shiyasa ya kumbura fuskar yana kallonta ya ?i magana "Tashi mana ina sauri ne, nabar Asiya tana jira na." "Mai za ki yi da kuWi kuma Hajiya?" Yayi maganar yana mai ?o?arin tashi zaune da sanyin jiki, wanda barcin ne ya cire masa karsashin sa Zama tayi gefen gadon tana ba shi amsa da faWin, "Asiya zan ba, zata yi wa Madinanta siyayya sabida zata je duba ta, shiyasa nima zan bada nawa gudummawar." Shiru yayi yana kallonta, kamar zai yi magana kuma sai ya mi?e bai ce komai ba, wurin wardrobe Win sa ya nufa tare da buWe wa, sai da ya za?ulo wani farin gajeren wando mai aljihu da zip a jikinsa, sannan ya zuge ya ciro kudi har 10k, ya dawo ya mi?a mata yana cewa, "nima ga nawa nan a haWa a yi mata siyayyar." Baki Hajiya ta washe cike da jin dadi, tare da furta, "ai kuwa ta gode, ka ga yanzu sai in kai mata duk wani abun bukata na Wiya Mace sai ta siya mata, har kayan girki, Allah yasa dai mu ji alheri don wlh ina tausayin yarinyar nan, Allah yasa ta dace da gidan Miji na gari." "Amin." ya furta yana mai bin hanyar toilet batare da ya koma barcin ba, don ya rigada ya ji barcin kuma ya gudu Ita kuma Hajiya Ummee sai ta tashi ta fice ta koma falon, bata tarar da Umma ba don tuni ta wuce kitchen tana wanke-wanke, can ta nufa ta same ta ta mi?a mata kuWin, "ga shi nan har dana Farouk ya bayar a ba ki, sai ki siyan mata duk abun da kika san zata bu?ata." Hannu biyu Umma ta sanya ta amsa cikin tsananin farin ciki tana yi mata godiya, saboda ta san karamcin Hajiya in har bata amsa ba baza ta ?yale ta ba, shiyasa ta amsa cike da murna tana sake mata godiyar kamar zata du?a mata tana mata addu'o'i Hajiya Ummee tace, "Ameen Ameen, ai babu godiya a tsakaninmu Asiya, yi wa kai ne, kuma zaman tare ne dole mu taimaka wa juna bamu san amfanin da zamu yi wa juna a nan gaba ba, duk sanda kika je dai ki gaishe ta da kyau da kyau, Allah ya zaunar da su lafiya Allah yasa mu ji alkhairi." Umma na murmushi ta amsa da Amin tana sake cewa, "insha Allahu zata ji, zan sanar mata." "To Ni bari in koma Waki, don zan yi sallan walha ne da ban yi ba." "To Hajiya, amma mai za a dafa ne?" ?an yatsina fuskar tsufan ta tayi tana cewa, "duk abun da kika dafa Asiya yayi, amma ki yi dai abun da Farouku yake so ne tunda yana gida, da alamu bazai fita da wuri ba sabida yanzu ma haka barci ya tashi." "To Hajiya." Ta amsa mata tana ci gaba da ?arisa wanke tukunyar da yanzu ta zo kansa Ita kuma Hajiya ta fita ta koma Wakinta don yin Sallah.*** Koda Umma ta tashi aikin a gidan, kai tsaye kasuwa ta wuce tayi duk siyayyar da ta san zan iya bu?ata cike da farin ciki; sabida samun kuWin nan da tayi, ta san bani da matsalar kayan saka wa tunda lokacin da su Baffa suka zo tafiya dani sai da suka yi mata bayanin kayan da zan tafi dashi, don haka abubuwan girki ta haWa min duk abun da ta san zan bukata, musamman namu na ?auye wanda ta san na saba da shi, sannan ta siyan min wasu ?an robobi haka da zasu yi min amfani, a takaice dai sai da ta kashe dubu goma cif ta taho da raguwar dubu biyar, a ciki ta yanke zata yi kuWin mota sai ta bani wasu daga ciki in ri?e a hannu zai yi min amfani Kasancewar ta ga ta samu kuWin mota, shiyasa tana koma wa gida ta sanar da Mijinta zuwa jibi zata je duba Ni, kuma a ranan ta kira Yaya Haula tace mata, "ta je ta samu Baffa ta tambaye shi gidan Yaya Yunus a yi mata kwatance." Jin hakan yasa Yaya Haula tace mata, "itama zata je, don Allah ta bari idan ta zo sai su tafi tare, tana son ta je ta ga ?anwarta, itama hankalin ta duk a tashe yake tunda aka tafi dani tana cikin damuwa." Umma tace, "ai babu damuwa, in har kin tambayi Mijin naki ya bar ki, to zuwa jibin sai ki zo da wuri mu wuce taren." Cike da farin ciki Yaya Haula tace, "to Umma Nagode, bari in je yanzu in tambaya Baffan; tunda na san yanzu haka yana gida ya dawo aiki." Daga haka suka yi sallama da nufin in Haula ta tambaya zata yi mata Flash sai ta kira. *** *** *** *** _____Sai da na daidaici sun gama sun tashi a wurin sannan na je na kwashe kayan gaba Waya, ina shiga kitchen ban fara ci ba na ji kiran Sharhabila tana kwaWa min kira, jiki na rawa na isa Falon lokacin tana tsaye a bakin ?ofan dakin ta tana bi na da mugun kallon da ta saba koyaushe, da sauri na isa gefen ta ina du?a wa tare da amsa mata ina cewa, "gani Anti." Wani kallo ta watsa min cikin kakkausar murya take bani umarnin, "in yi maza in shiga in yi wa su Mabashir wanka, saura kuma in daWe in Sata mata lokaci har ita ta shirya ta fito." Da sauri na amsa mata yayinda jikina na rawa na tashi na bar wurin, ba wai tsoro ne kaWai ya sani rawan jiki ba; har da yunwa tunda ko karyawa ban yi ba, ga shi har sha biyun rana tayi, amma bani da ikon yin magana dole abun da ta sanya Ni zan je in yi, Haka kuwa na shiga nayi musu wankan na shirya su bayan ta zo ta fitar min da kayan da zan saka musu, Sai da na gama sannan ta kira Ni muka shiga kitchen, ta nuna min abun da zan girka kafin su dawo gidan, "saura kuma in yi mata kuskure sai na lahira ya fi Ni jin daWi." Ta ja min kunne tana murWe wa wadda har sai da na fitar da ?wallan azaba, Haka ta ture Ni ta fice batare da ta sake bi ta kaina ba, Ni kuma na ci gaba da aikin jiki a mace ko abinci na kasa ci, haka na Waura abincin gudun in yi laifi, yadda tace min haka nayi tunda jallop Win taliya Macaroni ta nuna min, a risho nake girkin kasancewar har yanzu bata taSa bari na; na taSa mata kayan wuta ba, sai dai ita ta kunna min, risho Win ne kawai take bani damar kunna wa in har ba ta wurin, Ni ina kitchen Win ban san sun fita ba duk da na ji kamar ?aran mota, amma ban fita ba sai da na gama girkin tsab, tuni na cinye sauran breakfast Win su tunda yunwa ta dame Ni, ina yi ina ci har na gama girkin sannan na zuba a Kula na kai saman daining, kasancewar na fahimci kamar babu kowa a cikin gidan hakan yasa na Wan saki jikina, duk da a gajiye nake tiSis ga barci da nake jin yana ?o?arin Wauka na, ko sallah ban yi ba na kwanta a tsakar falon sabida jin iska na hura ni, kuma ganin babu kowa shiyasa na ?i zuwa masaukina tunda nan ya fi iska da daWin kwanciya, kun san Wan ?auye bai iya samun wuri ba, kawai na Ware musu kan Kujera nan da nan daddaWan barci ya sure Ni wanda na daWe ban yi irin sa ba, DaWin barcin ne yasa ban san iya lokutan da na Wauka ina sharan shi ba, ashe har Yaya Yunus ya dawo ya shigo Falon ya tarar da Ni baki a wangale a saman Kujeran su ina sharan barci kamar wata gawa. [2/10, 10:45 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 17 of 55