Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kaWan, ta girgiza mishi kanta alamun a'a batare da tayi magana ba, Duk yanda ya so ta shiga motan ta ?iya, Dama ya san za a yi hakan, shiyasa ya fito shi; yana dubanta fuskarsa yalwace da murmushi, sai ya ja numfashi kaWan before yace, "Umma tace za ki yi tafiya zuwa jibi, shiyasa na kira ki muyi magana, sannan kuma ina so na ba ki kuWi ko kuna bu?ata na hidima, insha Allah zan zo ranan in kaiki har can." ?ago kai tayi ta dube shi, sai dai kallon da yake mata ya sanya ta Wauke idon a nan take, dakyar ta buWe bakin murya ciki-ciki tace, "a'a, ba na bu?ata." "Mene ne ba kya bu?atar? Zuwa kaiki Kadunan ko kuma kudin da zan ba ki?" Shiru tayi masa sabida baza ta iya amsa mishi maganar nasa ba, Wannan yasa yace, "don Allah Madina ki dena wahalar dani haka nan, na tuba na bi Allah da manzo kibar komai ya wuce, Ni ina son alakar mu mai kyau ta ?ullu ne ko domin Wanmu Khalifa, ki bani dama na turo iyayana tunda kin gama makarantar nan, babu amfanin zaman mu a haka kinji ?ar ?anwata?" Tunda ya fara zancen sai ta haWe fuska, kallonsa tayi ido cikin ido tace, "Yaya Yunus ni fa ina ganin girmanka da har yanzu na kasa maka magana, nayi maka shiru ne sabida abun da zai fito daga bakina zai ?untata ka, but baka gane hakan ba har yanzu, Ni bazan yi aure ba, ban kuma shirya aure ba, karatu kuma da kake tunanin na gama; yanzu na fara." Sai tayi saurin haWe hannayenta waje Waya rai a Sace tace, "don Allah kar ka sake min maganar aure domin wlh zan faWa maka babu daWi, ba na so nace." Juyawa tayi ta shige cikin gidan da sauri, Yayinda Yaya Yunus ya saki baki da hanci yana kallon bayanta har ya dena ganin ta, wani irin faWuwar gaba ne ya riske shi domin tunda yake bai taSa ganin Madina a haka ba, infact ma duk maganar da zai yi mata bata taSa kula shi ba sai dai yayi ya gama, ko kuma ya ga tana hawaye ko kuma ta tashi tabar wajen, amma yanzu yanda ya ga ranta a Sace da kuma kalaman da take faWa mishi, alamun akwai matsala a ha?i?anin gaskiya maganar nata ke fita kuma babu tsoro a kan hakan, Meyasa Madina zata kasa gane halin da yake ciki? a tsawon shekarun nan yana bibiyanta ne don kawai yana sonta da ?aunarta, to sai yaushe zai mallake ta? Ai yanzu ya ci ace ta yafe mishi komai ya wuce tunda yanzu ta warke babu abun da ke damunta, an Wauki tsawon lokaci yana bibiyanta da kyautata mata, ashe a tunaninshi gaishe shi da take yi tana girmama shi har yanzu; ashe bata saduda ba babu ma maganar aure a ranta har yanzu, Ya zai yi da ransa, hakika ta razana shi da kalaman ta wanda yana jin tamkar wu?a ta daSa mishi, jikinsa yayi sanyi haka ma zuciyarsa tayi wani irin ?unci sabida tunanin kamar yana son rasa ta, mai zai yi mata ta amince ta ba shi wannan damar a karo na biyu? Ta wanne hanyar zai Sullo mata bayan duk wata hanya ya bi bai samu ta sauko ba, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Ya kasa taSuka komai daga wannan lokacin har sai da ya dauki tsawon lokaci yana faman tunani, Daga ?arshe ya fiddo ledojin da yayi siyayyan ya nufi cikin gidan dashi Madina koda ta shiga bata nuna wata alama a fuskarta ba, Shiyasa koda Umma ta tambaye ta ina kayan? Sai tace, "ai ?arya Khalifa yayi ba wani kaya bane, magana zasu yi." Daga haka sai ta shige Waki, Sai ga kuma Yunus da kayan ni?i-ni?i ya shigo, Umma tace, "kuma tace babu kaya ga shi kai ka shigo dashi?" "Eh Umma nace ta shiga ne kawai zan shigo dashi." Wannan ne yasa Umman ta yarda babu wani abu, sannan tayi masa godiya suka sake sallama ya tafi A ranan da Madina zata wuce Kaduna, da safe wurin karfe goma har ta gama shirya wa zata wuce, sabida tayi hakan ne don kar Yaya Yunus ya zo ya iske ta, ta san muddin ya zo sai Umma ta tilasta mata bin shi tunda yace zai kaita, Allah yasa bai sanar da Umman ba, ce mata yayi, "zai zo ya Wauki Khalifa a ranan." Madinan ya faWa ma wa shiyasa tayi saurin shirya wa don ta wuce da wuri kar ya zo ya tarar da ita, Su Hassana suka raka ta har tasha ta samu abun hawa, Yayinda tana tafiya sai ga Yaya Yunus ya zo gidan, Suna kan hanya ta ga kiran Umman ya shigo, haka kawai ta ?i amsawa sabida a ranta ta ji alamun zata ce mata ta jira shi ne ya kaita, duk yanda aka yi Yaya Yunus ya je gidansu, don haka da ta ga tana ta kiran wayan sai ta saka a silent, Dayake duk waya Waya suke using dashi dasu Hassana, Suna tare da ita har sai da motan da ta shiga ta cika sannan suka wuce, Madina bata taSa zuwa Kaduna ita kaWai ba, infact ma duk zuwan da zata yi kaita ake yi lokacin da tayi zaman gidan, za a kaita a dawo da ita shiyasa duk tafiyar yayi mata wani iri tunda bata saba ba, Allah yasa zata iya gane gidan koda ta sauka a tasha sai ta samu napep ya karisa da ita, Bata sha wahalar shiga gidan ba tun a bakin gate masu tsaron gidan sun gane fuskarta, kuma da tayi musu bayani sun saurin tuno ta, shiyasa suka barta ta shiga. [1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* ???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 46 of 55