Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ci gaba da rayuwa, a yanda nake ji gwara in mutu in huta da irin ba?ar azabar da ke ratsa min can cikin jikina. A haka barci ya Wauke Ni ba tare da na sake sanin me ke faruwa ba A yanda nake saukar da numfashi da ?arfi ina shashshe?a hakan ya tabbatarwa da Yaya Haula barci ne ya sure Ni, sai a lokacin ta saki ?a??arfan ajiyan zuciya tana saka hannu ta shafo kaina har zuwa dogon gashi na da yake ba?in?irin ba shi da cika sosai, ko kaWan ba shi da yawa tamkar kan yarinya, sai dai ina da yalwan gashin saje wanda ya saukar min har wajen kumatu na, koda na rufe kaina da Wankwali dole zaka fuskanci cewa ina da yalwan gashi domin ba ya rufuwa; koda hula na sanya kuwa, abun da ke ?arawa ?ar tsukakken fuskata kyau kenan, tabbas bamu da bambanci da Yaya Haula domin kamannin mu Waya ne zarr, itama haka take da sajen nan domin ita har ta fi Ni yawan gashin kai, sai dai kawai bambancin mu Ni na fi ta hasken fata ne sannan kuma ina da lotsatstsen gemu, ?asan gemu na yana lotsawa musamman idan nayi murmushi, dai-dai gwargwado Allah ya bamu kyau tunda duk mun biyo Mahaifinmu ne, kuma haka ?an gidan mu gaba daya suke da kyawu, WaiWaiku ne basu da haske a duk faWin gidan mu, Kakannin mu duk Fulani ne makiyaya, Asali Kakan mu shi ya soma kafa ?auyen nan wanda har ga shi yanzu tayi rassa ta ko ina, don ma wai wasu suna tashi su koma cikin birni ne sabida kidnappers da suka addabe mu a shekarun baya, sai da aka tashi tsaye da addu'o'i sannan aka samu salama, wanda ina ji a wajen iyayen mu an kafe Garin ne shiyasa aka samu sau?i ba sa shigowa, ko sun zo kusa da ?auyen sai dai su kewaye su wuce baza su taSa shiga ba Yaya Haula ta jima a Wakin kafin ta tashi ta fita, ta yiwa Mutanen gidan sallama sannan ta wuce gida, sai a nan ta samu tayi Wan aikace-aikacen ta wanda dama Matar Yayan Mijinta duk tayi mata wasu abubuwan, kasancewar suna zaune lafiya ana mutunci sosai tare, duk da ita wancan Matar har da yaranta guda biyu da ta haifa, kuma ta girmi Yaya Haula sosai domin ba yarinya bace, ko kaWan ba ta ?yashin Yaya Haula tana janta a jiki sosai, kafin Yaya Haula ta saki jiki a gidan Mijinta Rabi'u duk ita ta koya mata wasu abubuwan, ita take sanya ta a hanya shiyasa Yaya Haula bata sha wahala sosai ba, ga shi uwar mijin su Mace ce me kirki duk tana nuna musu ?auna kamar ?a?an cikin ta, kasancewar bata da Yara mata sai su biyun kaWai da ta haifa Maza, shiyasa take kulawa da Matan su tunda su kaWai gare ta, Yaranta suna sonta sosai suna mata duk abun da take so duk da Allah be hore musu ba sosai, shiyasa itama take yin iya ?o?arin ta wajen ganin sun ji daWin zama da ita basu yi kuka da ita ba. To yau da gobe a haka nake ta jinyan jiki na, tun ba na sanin abun da ke faruwa azaba tayi min yawa, har dai yanzu na soma gane wasu abubuwa, duk da ciwo sosai nayi a cikin sati biyu kacal baza kaso sake kallo na ba idan kayi min duba Waya, na rame sosai na fita a cikin hayyaci na, memakon inyi ba?i sai na kwanWe kamar wacce babu jini a jikinta, to hakan ne amma babu wanda zai taimaka min sai dai ayi ta Wura min saiwowi shi ne magani na, Yaya Haula ita ke min komai sai wasu daga cikin ?annin mu da ake sakawa suna min wasu abubuwan idan babu ita, kasancewar yanda ciwon ya ci ya cini shiyasa su Baban Sasa suke tausayi na sosai, hakan yasa suke bani kulawa dai-dai gwargwado duk da ba wani abun suke min ba, amma suna zuwa akai-akai suna duba Ni sannan su suka sa Matansu su ri?a kula da Ni, duk da babu wanda ke min wani abu domin su kansu ba ta Ni suke yi ba, dama-dama Inna Lami tunda ita ce dama mari?iya ta, kafin wani yayi min abu ita zata yi min, sauran yaran duk sun warke amma ban dani, kullum cikin tashin hankali nake da koke-koke shiyasa jiki na a koyaushe yake sake rikicewa, ba Ni da aikin yi sai tunanin Ummata ina zuba idanun ganin ta zo, amma sai ga shi har an yi wata Waya da min kaciya babu ita babu dalilin ta, tun ina saka rai har na Webe tsammanin zuwan ta, tabbas baza ta zo Win ba duk da a koyaushe ?orafi na a kan Yaya Haula, "meyasa Umman mu bata zo ta duba Ni ba?.. don Allah ta kira min ita in ji muryan ta, ko kuma ta je can ta faWa mata halin da nake ciki." Yaya Haula takan ri?e min hannu tayi ta bani ha?uri tana faWin, "Mijin ta bazai barta ta je a nan kusa ba tunda bata jima da zuwa ba, sannan akwai kuWin mota tafiyan bazai yiwu mata a ?asa ba tunda basu dashi, wayanta har yanzu ba'a gyara ba shiyasa baza ta iya kira min ita ba, amma in kwantar da hankalina zata zo." Kullum zancen nata kenan, "zata zo." Amma shiru har yanzu, na san Yaya Haula tana min wayau ne domin in kwantar da hankali na, duk da ina da ?arancin shekaru amma Allah ya zuba min wayau ba kaWan ba, na fahimce ta ?warai kuma na cire rai da zuwan Umman mu, baza ta taSa zuwa ba tunda dama ba zuwan take yi ba sai idan wani abu babba ya faru, itama kanta tana fama da kanta shiyasa ba kasafai take zuwa ba sabida halin rayuwa. Shiyasa tun daga ranan na cire komai a raina na fuskanci yanda Allah zai mayar min da rayuwata a nan gaba, nayi ta jinya na tsawon watanni biyu ban warke ba; wanda har hakan ya soma ba wa wasu haushi kasancewar kullum ina Waki ba na fita, duk wani aikace-aikace da nake yi a gidan sai dai Matan suyi ko su saka yaran su, ga shi shegen ?yuya ne da Yaran Ni kaWai ce ake saka Ni abu a daWin rai, kuma inyi me kyau babu guna-guni bare Sata fuska tunda na saba, sun ji daban da wannan ciwon da nayi, shiyasa kowa ya fara jin haushi na tunda na ?i tashi in taimaka musu kamar yanda na saba, Ni suke tula ma aikin komai Ni ce jakar gidan, tun ban gama warware wa ba tafiya ma da?yar nake yi domin ba na tashi tsaye sosai, a haka aka soma saka Ni aikin sai dai bani da yanda zan yi haka na koma musu Bauta, abubuwan da suke saka Ni wahalhalun yayi min yawa tunda ba daWin jikin nawa nake ji ba, hakan yasa kullum a tafe nake ina ciwo kuma babu me tausaya min, na sake fita hayyaci na duk na tsamure, sai idanu a waje kamar zasu faWo sabida yanda suka zazzago, kasancewar Masha Allah Ina da idanduna, har kuma a lokacin ba na tafiya yanda yakamata, ba na mi?ewa tsaye sosai saboda yanayin sauyin da na samu a tare da Ni, tun daga lokacin na san na sanja sosai, ada ni sai in daWe ban yi ciwo ba amma yanzu tunda al'amarin nan ya faru ba na yin sati ban kwanta jinya ba, ga shi kullum na shiga bayi bayan na gama uzuri na sai inga abu zare-zare yana bi na me kama da jini, ban taSa damuwa da hakan ba tunda ban taSa sanarwa kowa ba, ko Yaya Haula ne, ga shegen ?ai?ayi da yanzu nake fama dashi, kullum bani da aiki sai susa ina kartan jiki na, haka na ci gaba da wannan rayuwan tunda ban taSa sanin matsala bane bare in sanar da wani, har na saba ma yanzu A hankali a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya kamar yanda ta saba, ga shi yanzu har mun yi kusan watanni goma da yin mana kaciya, mun manta ma da an yi mana, sai yanzu aka tashi da zancen auren mu gadan-gadan, haka Baban Sasa ya tara jama'ar gidan domin a sanar mana da hukuncin da suka yanke Jiki na yayi sanyi a lokacin gaba Waya na rasa sukuni na sabida ban san wanda za'a haWa Ni dashi ba, kwata-kwata a raina ba na bu?atar wani aure a rayuwata, Ni da so samu ne a bar Ni in ci gaba da zama a haka, Ni kaina ina mamakin kaina sabida ko ada Ina da samari waWanda suke so na ?an cikin ?auyen, tunda tun muna yara muna sanin soyayya; kasancewar samarin karkara akwai saurin girma, kuma mu ba komai bane don ?aramin Yaro ya fara samartaka, duk da ban taSa kula su ba domin ko sun tsayar dani guduwa nake yi sabida kunya, amma kuma yanayin da nake ji a wancan lokacin ya sha bamban da yanzu, ada ina farin ciki idan naji wani ya nuna yana so na, amma yanzu daga Mazan har soyayyar ba na sha'awa, ba na jin bege a tare da Ni, babu shau?i ko kusa a tattare da Ni Duk iyalan gidan mu har waWanda suka yi aure Matan a nan kusa sun zo, su Yaya Haula duk suna nan tare dasu aka zauna zaman taron A nan Baban Sasa ya soma jawabi kamar yanda suka yanke hukunci, kowanne lokaci su ne masu zaSa ma Yaran gidan Abokan rayuwa Mazan mu da Matan mu, Binta da Fa'iza su ne aka haWa su aure da Yayyunmu na gidan, Ni kuma da su Nafisa gaba Wayan mu ?an anguwa aka haWa mu da su, yawancin su daga masu Mata biyu sai me Mata Waya, sai dai Ni nawa bayan Matar da yake dashi tsoho ne, domin Mutumin abokin Baffa ne ya girmi Babana kenan, shi ya ganni yace yana so shi ne ya sanar da Baffa, shi kuma Baffa ya zo ya faWama Baban Sasa, bae Yi la'akari da cewa Mutumin babban Mutum bane yayi jika dani amma nan take ya amince; wanda su kansu gaba Waya murna suke yi kasancewar Alh. Badamasi yana Waya daga cikin masu arzikin ?auyen, Matar shi Waya kuma ita duk ta haifa mishi yaran shi guda bakwai da ya haifa, har wasu sun yi aure da jikokin sa, sai Ni yanzu da ake shirin haWa Ni dashi Su kansu Matan gidan sun girgiza da jin wanda za'a haWa Ni dashi Win, duk da a cikin mazajen sauran duk babu sa'annin shi, babban Mutum amma shi ne za'a haWa Ni aure dashi, wasu kuma a cikin su ba?in ciki da hassada sai da ya cika musu zuciya sabida gani suke yi nayi goshi zan auri me arzi?i, har suna jin dama ?a?an su ne ba Ni ba Sun shirya auren nan da sati uku masu zuwa, bayan shekara Waya kuma za'a kai ko wacce Wakin auren ta tunda yawanci hakan ake yi, idan aka Waura aure daga baya ake yin shagali, lokacin sauran sun cika shekaru 13 kenan, Ni kuma ina da 12 Daga Ni har Yaya Haula kuwa; hawaye ne kawai yake zirya a kan fuskokin mu, sai dai bamu bari kowa ya fuskanta ba kasancewar yawan da aka yi a wajen, ita tana kukan tausayina ne; nima haka, tare da kukan ba?in cikin wannan rashin gata da za'a yi min, kamar Ni yarinyata a haWa Ni da wanda ya girmi Mahaifina? Ina zan kai wannan tsohon me ruSaSSen baki? Shiyasa Allah-Allah nake yi in fita in saki kukan da yake cin raina, ana sallaman mu kuwa na fice fit nayi bayan gidan inda babu wanda zai iya gani na; babu wanda zai iya ji na, a nan na saki wani kuka mae tsananin ?arfi wanda ke fita mun tun daga can ?asar zuciyata, har wani Wauke numfashi nake yi sabida azaban ma?a?in da nake ji a ma?ogwaro na, wani abu ne ya tsaya min a wurin kuma ya ?i wucewa, sai kokawa nake yi da hannuna a ma?ogwaro na kamar raina zai fita, inda nake kuka sosai har ba na iya ganin abun da ke wajen, ji nake yi kamar in kwanta in mutu sabida ba?in cikin da nake ji a lokacin yana sake ratsa min zuciya, sai dai babu hali, bani da ikon da zan bijirewa zaSin su domin ba kaina farau ba, kuma ba'a taSa yin hakan ba, gidan mu akwai biyayya, ba a ja da maganar Baban Sasa, sannan Mata basu da wani galihu da zasu Waga murya har aji koken su, na tabbata da yanzu za'a san mae nake yiwa kuka bazan sha a gidan nan ba, za'a yi min dukan tsiya ne musamman idan suka ga zan zubar musu da mutunci, idan aka yanke magana Waya ba a yin ta biyu haka tsarin gidan yake, ko ince haka na taso naga ana yi. [1/30, 5:55 PM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 3 of 55