Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shiyasa Allah ya Waura min ?aunar Madina a raina, yanzu ga abun da yake faruwa babu ko Wigon so na a zuciyarta, babu tausayina a zuciyarta, ai ina ganin ko Allah ana mishi laifi ya yafe wa Bawansa bare mu Wan adam, Madina ta kasa gane inda na sa gaba." Cike da tausayinsa Doctor Bilal yace, "ba wai ta kasa gane inda ka sa a gaba bane Yunus, Ni ina ga akwai cutan da yake damunta sabida abubuwan da suka faru a baya, a mahanga ta idan ka duba abubuwan da ke faruwa da ita; tunda tace baza tayi aure ba to ba na tunanin akwai sha'awar hakan a tattare da ita, irin wannan abun yana faruwa da ire-iren ta duba da abun da ya faru da ita a baya, Ni a ganina tana bu?atar Likita na musamman domin ya bincika asalin me ke damunta, domin abu na farko da zaka fuskanta bayan kun yi aure Akwai yiwuwar kayi dana-sani, sabida baza ta taSa baka goyon bayan mu'amalar ku ba, because tun farko babu sha'awa da kuma soyayya a tattare da ita; da dai makamantan su. Hakan na faruwa gaskiya musamman kaciyar nan da ka taSa bani labarin an yi mata." "No, ba na tunanin haka ne, domin ai ba a kanta aka fara ba, sannan yanzu maganar da nake maka akwai wanda ta amince zata aure shi, ko a baya ai soyayya tayi da wani, Ni ne kawai bata so." "Ban fahimta ba?" Nan Yaya Yunus ya sanar dashi abun da ke faruwa, da musabbabin tashin ciwon nata tunda yayi ?o?arin tafiya da ita ?auye ne; domin yakaita wurin iyayensa ko zasu lallaSa ta ta amince ta aure shi, Ko kafin Doctor yayi magana; sai ga Nurse ta shigo tana sanar musu, "yarinyar ta fice a Wakin, bata ganta ba." Da sauri suka tashi suka fita suna neman ta, duk hankalin Yunus a tashe yake ya rasa inda ke masa dad'i, sun duba kan hanya har waje babu Madina har ta tafi, Ko sallama Yunus bai yi wa Doctor Bilal ba ya shiga motansa yabar asibitin. [1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 49 of 55