Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
min, shiyasa ta duba magani ta bani sannan tace, "ai al'ada ne ya zo mata, kuma da alamu ya zo mata da gardama domin ciwon al'ada ba ya denawa har sai an kai mutum Wakin Mijinshi, Allah yasa ma abun ya zo da sau?i an yi auren, amma ga wannan maganin a ri?a ji?a mata tana sha zata rage jin raWaWin ciwon, Allah ya sawwaka." "Amin AMin." Duk suka amsa mutanen sasan Sannan Baffa ya bata kuWin maganin nata bayan ta faWa mishi. Ya dubi Inna Lami yace, "don Allah a kula da ita yanda yakamata, Allah ya bata lafiya, Ni bari in je sai in Yi ma Baban sasa bayanin halin da ake ciki." A cikin mintuna ashirin har ciwon ya lafa min wani wahalallen barci ya Wauke Ni. Lokacin da na tashi gaba Waya jikina ya ji?e da jini, duk kunya ya kama Ni tunda ina jin abun da aka ce ya same Ni, Ni wato nawa bai zo a cikin sirri ba sai da mutanen gida suka sani, ashe wancan ba jinin Al'ada bane, mai sosan yana gaba Nafisa na zaune gefe na tana kallona, tun lokacin da ta ga na motsa hankalinta ya dawo gare Ni, sai ta soma min sannu tare da cewa, "Inna tace idan kin tashi akwai ruwan zafi a coolern ta na kichen ki Wiba kiyi wanka, sannu gaskiya na tausaya miki domin naki ya zo da wahala, mu kuwa kinga duk cikin mu babu mai ciwo sai dai mu ga ya zo, kinga Ni na wata uku fa na taSa yi, sai in yi wata biyu ma ban sake yi ba, shiyasa nake murna wlh don Ni na tsani jinin nan inga yana zuba, sai duk hankalina ya tashi, ke ma yanzu kin shiga sahun mu kin zama babba." Ta ?are maganar kuma tana dariyan sha?iyanci; kasancewar ta da son wasa da raha Ni dai ban ce mata komai ba illa ?o?arin tashi zaune da nayi, sai nayi shiru ina tunanin yanda zan tashi in fita a wannan halin "Ko in sake miki ruwan wankan ne in kai miki?" GyaWa mata kai nayi batare da na kalle ta ba, domin wlh kunyan haWa idona da kowa nake ji Haka ta sake min ta dawo ta faWa min, "ruwan yana bayi in je in yi." Dole na na tashi ba don ina so ba, sai kare jikina nake yi ina harharWe ?afafu na gaza fita Nafisa tana ganin yanda jinin yayi min sai ta zaro ido tare da cewa, "Kai! Haka jinin yayi miki? Kinga yanda ya Sata miki jiki kuwa?" Kamar in nutse a ?asa haka nake ji, har hawaye ne suka soma taruwa a kwarmin idanuna saboda maganar da Nafisa take min Ita kuwa bata lura ba sai ?ara kururuta yawan jinin take yi tana mamakin yawan shi, "wai kuwa kinga yanda ya Sata miki jiki? Kai ji be ma wurin da kika tashi, ko dai ciwo kika ji?" Ta ?are maganar tana kallo na, sai ta ga yadda nake hawaye kashirSan ?iris nake jira in fashe da kuka, nan kuma hankalinta ya tashi ta soma tambayana abun da ke faruwa? ganin na kasa magana jikina sai rawa yake yi sai ta fita da sauri ta je ta sanar da Innarta Sai ga su sun dawo da Inna Lami, itama ganin yanda jinin ya zuba ta tausaya min, ta kalle Ni tace, "to mene ne na kukan ko har yanzu kina jin ciwon ne?" Girgiza mata kaina nayi ina kai dukka hannayena saman fuskata; tare da share ruwan hawayen da ke Wiga min "To wuce ki je kiyi wankan, Allah ya kyauta gaba, ke kuma Nafisa fito da katifan ki wanke mata." "To Inna." Nafisan ta amsa mata tana yin abun da tace Ni kuma tuni na fice daga Wakin na wuce makewayi. Daga bayin ina jin Inna Lami tana sanar da su Inna Asabe halin da nake ciki, sai Allah ya kyauta suke min Inda har Inna Habibah take cewa, "ai sau?in ta ma an yi mata aure za a huta, ko matsalolin ciwon cikin ma zai ragu." Wankan nayi tsab sai na Waura Wankwalin kayan nawa a ?uguna; tunda skirt Wina ya Saci, a haka na fito jikina a buWe illa daga ?uguna zuwa cinyana dana rufe, kuma ban damu ba tunda na saba yin hakan kasancewar ganin bani da komai da zan iya Soyewa, kunyata kawai yanda na fara Al'adan nan kowa ya sani, har ba na son haWa idanu da mutanen sasan Inna Lami ta taimaka min ta nuna min duk yanda zan yi, har ?unzugu ita tayi min da tsumma na saka da wando, gaba Waya a ranan ji na nake yi a wani irin ba?on yanayi, sam na kasa sakin jiki na saboda jin yanda ?asana yake a takure; sakamakon saka tsumma da kuma jinin da nake fitar wa, a haka na wuni sukuku babu wata walwala a tattare da Ni, duk da dama Ni ba Mutum bace mai yawan magana sai idan ina tare da Yaya Haula ko Ummana, da su kaWai nake iya sakin jikina; a wajen mutane kamar farar Kura haka nake; ga miskilancin tsiya Kwana na biyu ina wannan halin, har Yaya Haula ta zo ta gaishe Ni duk da jikina da sau?i amma jefi-jefi ina fama da ciwon ciki A rana na uku ne na samu sau?i jinin ya Wauke gaba Waya, shiyasa nayi wanka kamar yanda aka koya mana a islamiyya A kuma ranan ne sai ga Alh. badamasi ya zo gaishe Ni; kasancewar Baffa ya sanar mishi halin da nake ciki. A falon Baffan ya jira Ni kamar yanda ya saba zuwa Bai jima ba nima na shigo falon ina sanye da riga da zani na atamfa ba?a da kalan yellow a jiki wanda aka yi kwalliya, duk da kayan sun koWe amma sun amshi farar fatana sun yi min kyau, har Waurin Wankwali Fatimah tayi min ga sabon gyale na Nafisa da na saba saka wa duk idan zan je, nayi kyau fuskata da hoda da tozali sai man baki Shi kansa alamu ya nuna ya ji daWin gani na a haka, nan da nan ya washe bakinsa yace, "in matso kusa dashi." Babu musu na isa inda yake amma na kasa zama, sai ya kama hannuna ya zaunar da Ni a saman cinyansa kamar yanda yake min, ya kalle Ni da murmushi bayan ya Wago fuskata yace, "kin yi kyau Matata, yau har da kwalliya kika yi min?" Ban san sanda nayi murmushi ba har ?asan gemu na yana lotsawa, wanda sosai yake ?ara min kyau idan nayi murmushi ko nayi dariya ya fito, sai na sunkuyar da kaina ina wasa da hannuna "Na ji daWin ganin ki a haka, dama Baffanki ne yace min kina fama da rashin lafiya shiyasa na zo duba ki." Sai yayi wani murmushi har da sauti yana ?ara cewa, "Ashe Amaryan tawa ta girma ne?". [2/2, 9:23 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 6 of 55