Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mai zai hana ki yi amfani da damar nan naki wajen kin tusa naki soyayyar a ranshi?" Zaro idanu waje tayi tana kallonta, Sai Khairiyya ta jinjina mata kanta tace, "?warai kuwa, wa yace miki ba ki cika Macen da Yaya Mashkur zai so ki ba? Kar ma ki fara ?as?antar da kanki a kan wani namijin da kike tunanin ya fi ?arfinki a rayuwa." Sai ta gyara zamanta sosai tana ?ara cewa, "namiji ba ya fin ?arfin kowacce Mace a duniya; komin muninta, ki yi tunani da kyau Madina, Yaya Mashkur da ke ya dace ba da wata Wiya Mace ba, kar ki fara kiyi wasa da wannan damar naki, domin ina ganin soyayyarki a cikin idanunsa, kema haka akwai soyayyarsa a tattare da ke." Daburcewa Madinan tayi sabida jin zantukan nata, tayi saurin cewa, "wlh Ni ban taSa Waukansa a haka ba, Ni babu komai a raina..." Katse ta tayi tace, "ai shiyasa nake faWa miki tunda ke ba ki sani ba, kina sonshi shima yana sonki, abun da Nabeela take hango wa ba ?arya bane, amma kar kiyi wasa da damar ki; kin cancanci ki samu kamar Yaya Mashkur don bai fi karfin ki ba, na tabbata wata rana zai sanar miki cewan yana sonki, kar ki taSa hana zuciyarki abun da take so domin kuskure ne a gare, bare kamar Yaya Mashkur yayi miki komai a rayuwa idan kika ?i shi kamar kin kasa mishi abu guda Waya ?wa??wara da za ki saka mishi ne, ki yi tunani a kan maganata Ni ina ba ki shawara ne a matsayin ki na ?anwata wacce ba na fatan ki rasa kamar Yaya Mashkur, domin baza ki taSa samun kamar shi ba, kinji Madina don Allah ki manta komai ki ri?e Yaya a matsayin Masoyinki wanda shi kaWai ne a rayuwarki za ki iya ba shi wannan damar, idan ba ki sani ba yana sonki." Sai ga Madina tana kuka sabida jin waWannan maganganun da bata taSa zato ba, Hankalin Khairiyya ya tashi da sauri ta soma rarrashinta tana cewa, "wai don na faWa miki wannan maganar ne kike kuka Madina? Mene ne na kuka a nan?" Madina ta kasa amsa mata illa ci gaba da kukan da take yi kanta a saman cinyoyinta, duk a rikice take jikinta har ya soma kerma tana tunanin kamar hakan ma bazai yiwu ba, taya ya ma zata amince da wannan maganar bayan ita baza ta ?ara yin aure a rasuwarta ba? Wayan Khairiyya da ta soma riing ita ta zaburar da su duka, Khairiyya ta Wauka tana duba wa sai ta ga still Mashkur ne ya kira, ta dube ta tace, "ga shi nan, Yaya Mashkur ne ya sake kira, kuma muryanki yake son ji, Madina don Allah ki kwantar da hankalinki ba na faWa miki wannan maganar bane don ki tayar da hankali ba, please ga shi ki Wauka." Ta dan?a wayan a hannunta, Da?yar Madina ta shanye sauran hawayen nata tana shashshe?a ta latsa wayan, sannan ta kara a kunne but ta kasa cewa komai, Khairiyya kuma sai ta mi?e tabar Wakin gaba Waya, Jin shiru daga wurin Mashkur sai ya tabbatar da cewan Madina ce, sabida yana jin numfashinta wanda yake jin har nashi bugun zuciyar ya soma sauya wa, don haka cikin sanyin muryasa mai fita a koyaushe ya kira sunanta, Da?yar ta iya amsa wa sabida already halin da take ciki muryanta ta shige, "Madina, wai nayi miki laifi ne da yanzu kike son ?in kula Ni? Ko kuma a yanzu ba ki da lokacina ne gaba Waya duk kin sauya min, kamar ba ke ba? Meke faruwa Please ki faWa min since ba kya Soye min komai, idan wani abu nayi miki zan ba ki ha?uri ina ta tambayar ki amma still har yanzu kin kasa bani amsa?" A wannan lokacin ta kasa yin magana sai tayi shiru tana rufe idanunta wasu hawaye na zuban mata zuciyarta na tsananin bugawa, maganganun Khairiyya na sake dawo mata cikin kunne, wanda yasa gaba Waya ta kasa samun natsuwa ko na minti Waya, Sai da ya sake kiran sunanta sannan ta amsa shi kamar zata yi kuka, Shi kansa a yanzu ya soma fahimtar yanayin muryan nata, sai yayi saurin tambayarta hankalinsa a tashe sabida a tunaninsa akwai abun da ke damunta ne, nan da nan ya rikice kamar yanda ya saba idan ya ji ta a wata matsala, Hannu ta sanya da sauri ta share hawayenta tana ?o?arin saita kanta, da?yar ta furta, "Yaya babu komai, babu abun da ke damuna." "Kin tabbatar? Ban yarda ba Madina, faWa min me ke damunki?" Bakinta ta ri?e sabida kukan da ke son kufce mata "Madina Please ki yi magana mana, ina ji a raina kina cikin damuwa ki faWa min me aka yi miki? Ni ne fa Madina kin san ba na son Sacin ranki, duk abun da ke damunki ki sanar dani Please ko kin fi son na zo ne gobe?" Saurin girgiza kanta tayi tare da cewa, "a'a kar ka zo, ina.. ina..." Sai kuma tayi shiru sabida duk a rikice take bata san wanne irin karya zata yi masa ya gane cewan babu abun da ke damunta ba, Wanda a halin yanzu sosai Mashkur ya shiga damuwa ya tayar da hankalinsa gaba Waya, sabida ya san cewa dole tana cikin damuwa sai; kiran sunanta yake yi yana ro?onta Allah da Annabi ta sanar mishi da abun da ke damunta? Da?yar ta iya ?a?alo ?aryan da zata faWa mishi, cewan, "wani abu ne ya faWa mata a ido da ta je wanka." Cike da tausayi gami da kulawa ya soma rarrashinta yana cewa, "ya fita abun?" Ta Waga mishi kanta kamar yana kallonta, sai tace, "eh Aunty Khairiyya ta cire min." "Ok to, bari in bar ki kar in takura miki ki huta, zan sake kira anjima sai mu ci gaba da maganar namu, Please Madina ki tanadi abun da za ki faWa min dalilin da yasa yanzu kike guduna, sabida na kula da hakan ba tun yanzu ba kamar kina guduna ne." Sai ya Wan ja numfashi kaWan muryansa a yanzu har rawa take yi tsaban damuwar da yake ciki da kuma yanda yake jinta a ransa, cike da sanyin murya sosai a yanzu din yake furta, "don Allah idan wani laifi nayi miki ki sanar min domin in gyara, ba ki san yanda na Wauke ki bane Madina shiyasa, har yanzu akwai abun da na kasa sanar miki sabida ba na son in jagula miki lissafin ki, kullum neman hanyar farin cikin ki nake yi, ko sau Waya a rayuwa ba na son na ganki a cikin damuwa, wlh Madina zan iya miki komai a rayuwa in har don ki kasance cikin walwala da jin dad'i ne, ki sa a ranki Ni mai son ci gabanki ne." Daga haka bai tsaya ya ji mai zata ce ba yayi mata sallama a kan zai kira zuwa anjima, ya kashe wayan, Kukanta da take ri?e wa ta saki mai ?arfi, ta zamar da wayan a hannunta jikinta na kerma kamar an jona ta a lantarki, zuciyarta gaba Waya ta karye sabida zantukan sa, a yanzu tabbas ta soma fahimtar abun da Khairiyya take faWa mata, amma meyasa yake sonta? Wannan tambayar ta ?a?are mata a zuciya wadda duk ta gama jagula mata lissafi, Mashkur ai ya wuce komai a gare ta, mai zai so a jikinta da zai sanya shi farin ciki? Tabbas tana jin wani abu daban a kansa wanda bata ji a kan kowanne namiji ba, amma kuma ita bata shirya aure yanzu ba, hasali ma baza tayi aure ba, ba ta son ta sake shiga wata mummunar ?addaran da zai tuna mata da rayuwarta na baya, amma kuma Mashkur ya wuce komai a wurinta, ta yarda shi mai ?aunarta ne, kuma zai iya yin komai domin ta, amma tana fargaba taya hakan zai kasance? Taya zasu iya kasancewa Mata da miji? Tana ganin girmanshi fiye da tunani, ya wuce ajinta da dukkan tunaninta, amma baza ta gaza yin mishi duk abun da ya nema a gare ta ba, meyasa ya fara? Meyasa ya fara sonta? Mene ne dalili? Daga wannan lokacin sai Khairiyya ta ci gaba da fahimtar da ita muhimmancin Mashkur a wurin ta, idan ta same shi tabbas tayi dace, tun tana ?in amince wa da zantukan ta a kan cewa itama tana sonshi, tunda ita a ganinta babu yadda za a yi ta so wani Wa namiji, but a yanzu ta fara yarda, kuma ta zauna ta sanar mata abun da take ji a game dashi; da kuma shi abun da yake sanar mata, Yayinda Khairiyya take ?ara warware mata duk wasu abubuwa ta kuma nuna mata yadda zata tafiyar dashi yanzu, domin ta nuna mata kar ta sake kallon duk wani abun da Nabeela zata faWa a kan Mashkur, ta share ta ta fita harkanta, Wanda yasa ita Nabeela ta soma fahimtar kamar Khairiyya tana zuga Madina ne, hakan ya jawo musu faWa har maganar ta je wurin Mummy, Sai dai Mummy ta ja musu kunne a kan, "kar su sake irin wannan, muddin ta sake jin su zata faWa ma Daddyn nasu." Daga nan ta shirya su kuma ta yi wa Nabeela nasiha mai ratsa zuciya kan muhimmancin ta na Wiya Mace, "idan Allah yayi nufin Mashkur rabonta ne zata aure shi, idan kuma wani ne zaSin da Allah yayi mata komai zai zo mata da sauki, amma ta dena cusa kanta a kan dole sai namiji ya so ta in har ba shi ya furta mata hakan ba." Daga nan dai basu sake yin faWan ba amma har yanzu Nabeela tana ?ullace da Madina, musamman yanzu da ta ga sun sake jonewa fiye da baya, har kuka take yi ta shiga Waki ta sha kukanta tunda har yanzu bai bata amsar da take son ji a gare sa ba, duk da ta faWa masa son da take mishi, tana ganin meyasa Mashkur zai wula?anta ta haka? Ya zaSi wata a kanta bayan duk yanda suke dashi, tana ganin kamar bai yi mata adalci bane, ta so ta ba zuciyarta hakuri amma ta kasa, baza ta iya ha?ura da Mashkur ba, idan ta ha?ura dashi waye zata aura? Ansar ya fi ?arfinta fiye da tunani, bata ga fuskar ma da zata haWa kanta dashi ba, Mashkur ne mai sau?in hali kuma shi ne ya koya mata sonshi tun tana ?arama, shi ya soma shiga jikinta amma yanzu ya ja da baya, ?arshe har ?aransa takai wajen Hajiya Ummee don dai ta taimaka ta ro?i Mashkur ya so ta, Ita kuma Hajiya Ummee sai ta bata ha?uri a kan cewa, "Mashkur ya daWe da faWa mata Madina yake so, idan har zai iya haWa su su biyu tana goyan bayan hakan, amma a halin yanzu Mashkur Madina yake so." Wannan ne yasa hankalin Nabeela yayi mugun tashi, ta sha kuka sosai kamar ranta zai fita, tana jin har a lokacin bata ha?ura da Mashkur ba, duk yanda za a yi sai ta aure shi baza ta ha?ura ba, don haka ta yanke shawarar sanar da Daddy While Mashkur kuwa a wannan lokacin ya yanke shawarar sanar da Madinan halin da yake ciki, tunda a yanzu ya ga kamar ya soma cin nasara a kanta kamar akwai wani abu a karkashin zuciyarta; wanda yake ganin kamar itama ta kamu da sonshi. [3/5, 9:49 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 39 of 55