Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zama da Wuwawu na A takaice dai sai da na shafe watanni uku curr sannan na soma samun lafiya sosai, nayi jinya matu?a; na sha wahalar rayuwa wanda ban taSa tunanin zan rayu ba, Duk wannan lokacin babu wanda ya sake tako kafansa daga gidan mu sai Baffa da suke zuwa akai-akai shi da Yaya Haula, su kaWai ne suke zuwa duk cikin Iyayenmu, sai su Yaya Shamsu da suka zo sau Waya suma basu sake zuwa ba, Ta hakan ne kaWai suke samun labarina, tunda idan Baffa ya koma gida yana faWa musu halin da nake ciki, Ita kanta Haula sai lokacin ta samu natsuwa, sai lokacin ta kwantar da hankalinta tunda ina samun lafiya, ga shi komai ya soma wuce wa kamar ba a yi ba, ?anwarta tilo Waya Allah ya bata lafiya kamar bata yi ciwo ba, sai fatan samun lafiyarta gaba Waya Ganin jikin da sau?i komai ya soma lafa wa, shiyasa Dr. Mashkur ya ci gaba da zuwa duba Ni, tunda gaskiya irin wahalar da na sha ba ?aramin tausaya min yayi ba, matu?a na shiga ransa da yawa wanda yake ganin bazai iya jure rashin zuwa ganina har ya ?i kula dani ba, Sai dai halin da nake nuna wa har yanzu bai sauya ba, tunda kwata-kwata ba na son tozali da wani namiji sai hankalina ya tashi fiye da tunanin su, Umma ce ta zauna tayi min bayanin komai tana faWa min, "shi ne Likitan da yake kula dani, in dena jin tsoransa shi ba mai cutar wa bane a gare Ni." Yawan rarrashina da take yi da son fahimtar dani waye shi, shine har na soma saba wa da rage jin tsoron sa, amma duk sanda ya shigo sai hankalina ya tashi na kasa kallonsa har sai ya fita, duk abun da zai yi min bazan kula sa ba, kuma bazan kalle sa ba har jikina yayi ta rawa, sai ya fita nake samun natsuwar zuciya, domin wahalar da na sha a rayuwa a wajen Alhaji Badamasi bazan taSa manta shi ba, ya cutar dani cutar da baza ta taSa gushe wa daga zanen zuciyata ba, yayi min tabon da kowanne namiji na gani dole zan ri?a kallonsa da wannan yanayin, domin a wannan lokacin ba na fatan na sake koma wa ?auyen mu, ina ji a jikina na baro sa har abada sai dai akai gawana can, domin bazan taSa iya jurewa ba, a yanzu Ummana na fi bu?ata a wurina, ita kaWai nake son gani a tattare dani, zama kusa da ita ya fi min samun natsuwa, hankalina zai fi kwanciya, Maraichin da na kasance a ciki tsawon lokaci ina ?ulafucin uwa; a wannan lokacin zan samu, domin bazan taSa bari a raba Ni da UmmanA ba, duk inda ta saka ?afa dole sai na bi ta Komai ya soma sauya wa tunda ga shi har ana tunanin bani sallama, tunda na warke garau sai abun da baza a rasa ba, tun aikin da aka yi min na biyu aka samu nasaran da na dena yoyon fitsari, yanzu haka raman da nayi ne kawai ban koma dai-dai ba, tunda har yanzu akwai damuwa a tattare dani, tunda hankalina bazai taSa kwanciya ba in har ina tunanin ?auyen mu da rayuwar da nayi a baya, duk da a yanzu Umma ta tabbatar min da cewan, "bazan taSa koma wa can ba, a wajenta zan zauna tare da ?an uwana su Hassana." Sai dai hankalina har yanzu ba a kwance bane tunda na san waye Baban Sasa, in har bai amince ba na tabbata sai yasa an dauko Ni, hakan ne ke ?ara tayar min da hankali Ana haka sai ga Yaya Haula ta sake dawowa ita kaWai, wannan karon ko Ihsan bata taho da ita ba ta zo duba Ni, kuma kwana zata yi tunda da yammaci ta zo Ai kuwa ba ?aramin murna nayi ba, haka na rungume ta ina kiran sunanta kamar bakina zai tsage don farin ciki, Wanda yanzu basu saba ganin hakan ba a gare Ni, sai dai a yau din ganin farin cikina ya fi musu komai har suna jin zuciyarsu ta sake sanyi ganin na saki jikina ina ta farin ciki da surutu, har ina tambayarta, "meyasa bata taho da Ihsan ba?" Murmushi tayi itama tace min, "ai Ihsan ta girma sai ta zaSi inda take son zuwa, tunda nace mata wajen ki zan zo, sai ta botsare wai baza ta je ba, ?arshe ma guduwa tayi ta tafi wasanta." Sai nace, "yanzu Yaya Haula da gaske ta ?i zuwa ta duba Ni Ko? Shikenan nima zan dena kula ta tunda ba ta so na." "Ki yi hakuri ?ar ?anwata, kin santa da tsoron mota ba ta son ana hawa da ita mota shiyasa ba ta son zuwa, tace min wai kashe ta zata yi da?yar fa muke zuwa ta dinga min kuka in muka biyo hanya zamu hau keke napep." Umma ce tayi ?ar dariya tana cewa, "ina ruwan takwara ta, sai shegen tsoro kamar farar kura." Sai ta mi?e kuma tana haWa wasu daga cikin kayan da suke wurin, tace ma Haula, "ta kula dani bari ta je ta dawo." Yaya Haula tace, "to Umma sai kin dawo." Tana tafiya Ni kuma na kwantar da kaina a jikin Yaya Haulan ina ce mata, "Yaya don Allah ki Waure min wannan kan nawa, duk ya dame Ni sai ?ai?ayi nake ji." Hannu ta sa tana duba kan nawa tare da cewa, "wai kuwa ana wanke kan nan kuwa? Kinga yanda duk ya koma yayi datti da yawa, bari a wanke miki sai in miki kitso ko ?wara huWu ne." Ita da kanta ta shiga bayin ta tara ruwa ta sake sauran ruwan zafin da muke dashi a Flaks, sai tayi min wanka da kanta ta wanke min kan nawa sosai, Skirt din jikina na sako na fito a bayin ina rawan sanyi sai karkaWa jikina nake yi ina rakin, "akwai sanyi a garin, da na sani ban bari an yi min wankan ba." Dayake ita tana bayi bata kula Ni ba itama tana Wauraye jikinta, Ina zama a kan gadon na ?an?ame jikina ina yarfe kaina, Sai ga Dr. Mashkur ya shigo ciki da sallama, Da sauri na Waga kai na kalle sa nan da nan turaren da yasa ya cika Wakin, Da alamun yanzu ya zo sabida yanda ya Wauki wanka sai ?amshi yake yi, yayi kyau cikin ?ananan kaya farare sol da siririn eye glasses da ya sanya, kyakkyawar kamilalliyar fuskarsa ta sake haske da kwarjini, Dayake ina a tsorace ne nan da nan na mi?e da ninyar guduwa cikin bayin, ina zuwa bakin ?ofan sai ga Yaya Haula ta fito itama, nayi saurin ?an?ame ta ina Soye wa a bayanta da sauri, Ita kuma ganin halin da nake ciki har ta tsorata, don bata kula da Mashkur ba sai da yayi magana, hakan ne yasa ta gane dalilin guduwa na wanda shigowar sa ne yasa na firgita haka, Hannuna ta riko tana wuto dani ciki tare da gaishe shi cikin girmamawa Shi kuma sai bai shigo ciki ba ya tsaya a wurin yana kallon mu, fuskarsa yalwace da murmushi ya amsa mata, sai yace, "Haula ko?" Cikin kunya Yaya Haula ta du?ar da kanta tana amsa mishi, don duk in ya ganta sai ya tambayi sunanta tunda yana yawan manta wa, wannan dai shine haWuwar su na huWu kenan amma bai wani ri?e sunan ta ba Hannunsa ya saka a aljihu yana mai sake tambayarta, "ina Ihsan?" "Tana gida na barta." "Good." Ya furta yana Wauke kai a kanta, ya sake kallona wanda ina manne a bayanta na ?i motsa wa, shi dai har a zuciyarsa ba ?aramin burge shi nake yi ba, yana ganin kyawun mu wanda har yanzu ba ?aramin mamakin ?an?antar mu yake yi ba, a ganin sa kamar Yaya Haula wai har da auren ta da ?a ita kanta tayi ?an?anta; bare Ni da yake ganina kamar ya Wauke Ni ya ri?a jefa wa sama, bai san meyasa yake jin ya damu dani ba matu?a, kuma halin da na shiga da abun da ya faru dani tun kallon farko da yayi min ya matu?ar sosa mishi rai, shi dai ya Wauke mu tamkar ?anninsa ne shiyasa yake jan mu a jikinsa, Yana tsaye a wurin ya ?i shigowa har lokacin, ganin shirun yayi yawa mun haWe kai mun ?i cewa komai, sai ya canza shirun da sake tambayarmu Umman namu? Yaya Haula ce wannan karon ta sake ba shi amsa, a cewar ta, "yanzu Umman ta fita ta je ta dawo." Shiru yayi sai kuma yace, "ok, idan ta dawo sai ki sanar da ita ina office." Abun da ya furta kenan ya fita bayan ta amsa mishi Yana fita tamkar an tsamo Ni a ?aya, sai na sake numfashi mai ?arfi wanda yasa Yaya Haula ta juya ta bi Ni da kallo, "Wai lafiyarki Madina? Mene ne?" ?an waro idanuna nayi wadanda suke a waje har yanzu sabida jinyar nan da nayi, sun yi zuru-zuru sun firfito sun ?ara haske sun yi narai-narai dasu na mara sa lafiya, fuskata a kwaSe nace, "Yaya Ni ba na son ganin mutumin nan, tsoro yake bani." "Tsoro kuma????      !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Madina? Likita ne fa bazai cutar da ke ba." "Ni wlh ba na son sa, ba na son ina ganin kowanne namiji, gani nake yi kamar wancan mugun Mutumin ne." Nayi furucin hawaye na fara zubo min nan da nan Saurin kamo hannuna tayi ta dawo dani gabanta, sai ta soma rarrashina cike da tausayina tana cewa, "babu abun da zai kara faruwa da ke ?anwata, wannan likita ne ki dena jin tsoron sa, shi taimakon ki yake yi idan kina jin tsoron mutane ki dena saka shi a ciki, ba ki ji mai Umma tace mana bane? Tace mu ri?a ce mishi Yaya Mashkur, kinga ai bazai cutar da mu ba, idan kina irin wannan tunanin za ki ri?a shiga damuwa mu kuma ki Waga mana hankali, maza Wauko ledan kayan ki in zaSa miki wanda za ki saka tukunna." Da sauri na juya na Wauko batare dana ce komai ba sabida yadda nake jin sanyi na ratsa Ni, don na ?osa na saka kaya, ina Wauko wa na bata sai na koma zame skirt din jikina na koma babu sauran kaya a jikina, na tsaya ina jiran ta har ta ciro wanda zan sa, Wando ta soma bani na saka sannan na Wago zan amshi doguwar rigan A lokacin ne sai ga Mashkur ya sake shigowa cikin Wakin, Har razana nayi sabida ganin sa, sai nayi saurin koma wa gefen Yaya Haula ina Soye fuskata Shi kuma sai ya bi Ni da kallo yana Wan murmusawa, a wannan karon sai yace, "My sister meyasa kike tsorata ne idan kin ganni? I'm your brother; Stop being afraid, I have nothing to say to you." Daga Ni har Yaya Haula bamu fahimci abun da yace ba daga ?arshe, Ni dai tunda na du?ar da kaina ban sake cewa komai ba Shi kuma sai yayi kamar bai damu ba illa bin mu da kallo da yake yi, cikin natsuwarsa tare da nuna kula wa yace, "ki gama saka mata kayan akwai gwajin da za a yi mata yanzu ki kawo ta Office Wina." Da sauri Yaya Haula tace mishi, "to." Tana amsan rigan tare da ?o?arin sanya min Shi kuma sai ya fita batare da ya sake furta wata kalma ba, sosai ya sake ganin ?an?anta na wai kuma a hakan ne aka yi min aure, mamakinsa to wai meyasa ?auye suke yi wa Yaransu aure tun basu balaga ba? Ji be dai wannan yarinyar ?an?anuwa da ita ko cika Mace bata yi ba amma har an yi mata aure? Dariya ce ta suSuce masa sabida tunanin idan na haihu kuma ko da wanne Nonon zan shayar da Yarana oho? Tunda shi dai bai ga komai a ?irjina ba balle a ce zan iya shayar da yaro in na haifa, "kai suma ?auyawa da jaraba suke, Allah ya kyauta." Ya furta a zuciya yana ?arisa shiga cikin Office Win sa, Wayansa a hannu yana latsa wa sabida kiran da yake son yi, Wani number ya latsa wanda ya rubuta "My blood Brother" Zama yayi a saman chair Win sa yana kara wayan a kunne, sai da aka yi peaking da jin saukar muryan da yake bu?atar ji, hakan ne yasa ya gyara zamansa cikin kamalansa da tausassan muryansa yake cewa, "ba ka jin magana Ansar, I told you to stop talking to me before salam, I don't like that, I will stop answering your calls tunda baza ka dena ba." Daga can wata murya mai kama da nasa take furucin cikin Sacin rai, duk da yana maganar ne da sanyin murya but sai da hakan ya nuna a kan voice Win sa, Wanda hakan ne yasa Mashkur sauya akalar tambayar nasa da faWin, "what's wrong with you? Wa ya taSa min kai?" Cikin yanayin maganarsa da Hausa ba ta fita sosai; kuma da yanayin fitan sautin muryan da sauri yake cewa, "wannan shegiyar yarinyar ce ta Sata min rai, but forgot this issues, ina Hajiya na kira wayanta ba ta zuwa?" Guntun tsaki Mashkur ya ja yana cewa, "kai baka da magana sai maganar wata ta Sata maka rai ko? Ansar Why don't you leave this life? Idan aure kake so ka dawo gida mana a yi maka ka huta da wannan banzan rayuwar, ka san su Momy ransu yana Saci ko? They thought that now you have changed your behavior, but not so..." Katse maganar yayi sabida ganin mu mun shigo cikin office Win, sai ya ?ara da faWin, "zan kira ka ina da patients, ka kira numban ta i know network ne babu; ban jima da fitowa gidan ba." Daga haka ya janye wayan a kunnen sa jin ya amsa mishi, sai ya ajiye yana kallonmu yanda ya ga na ma?ale a bayan Yaya Haula ko le?owa ba na yi, Telephone na office Win ya Wauka batare da yayi mana magana ba ya hau daddannawa zai yi kira.*** Duk wani abu da yakamata an yi min a ranan, wanda ya tabbatar da cewan babu wani abu da yayi saura a tattare dani, illa magunguna da aka bani sannan aka rubuta mana sallama, Nayi farin ciki matu?a; dukkanmu ma mun yi farin ciki tunda yau an sallame Ni zamu koma gida Umma tana dawowa muka tattara kayanmu gaba Waya, Mashkur da kansa ya Wauke mu ya mayar da mu gida a daren nan, Tunda na ganni a gida sai hankalina ya sake kwanciya, wanda na tabbatar da cewan bani ba koma wa ?auyen mu A washe gari ma Yaya Haula kamar kar ta tafi haka take ji itama, amma kuma babu yadda zata yi tunda kwana Waya Mijinta ya bata, zuwa yamma ta wuce gida Baffa shi ya kira ta ya tambaya jikin nawa? Tunda wannan karon bai je ba, kuma ya jima bai samu ya je ba kasancewar yanda damina ta shiga sosai suna aikin gona, bai samu ya zo ba, A nan Haula take sanar mishi da sallaman da aka yi min To wannan dalilin ne har su Baban Sasa suka san an sallame Ni, Sai dai shi bai ce komai ba don kamar bazai yi magana ba, kowa ya zura ido ya ga matakin da zai Wauka musamman da yace zai sake min aure Ita kanta Yaya Haula fargaban ta shine Baban Sasa yace sai an dawo dani ?auyen, amma jin shiru bai ce komai ba tunda ta san sun sani sai hankalinta ya soma kwanciya, Ga shi har lokaci ya ja kusan ina kan rufa wata Waya a gida ban ji daga ?auye an zo tafiya dani ba, Shiyasa nima hankalina ya kwanta haka itama Ummana, tunda itama ba ?aramin fargaba bane a ranta, ta san tabbas idan sun yi ninyar Wauka ta dole ne sai sun Wauke Ni, kasancewar sun fi ta iko a kaina, dole ko kotu aka je suna da damar amsa ta, musamman da na kai wannan munzalin tunda ba yarinya bace Ni, Har mun yi tunanin ?ura ta lafa rayuwata ta soma sauya wa na saki raina da tunanin buWe sabuwar rayuwa, ashe ba haka bane, babu wannan jin daWin a rayuwata, Ni ba mai Sa'a bace da har zan iya tsallake wannan ?addaran tawa, ba a haifo ni a cikin jerin waWanda zan yi rayuwa cikin farin ciki ba, Mummunar labarin da ya kusan tarwatsa min rayuwata gaba Waya, wanda ya dawo dani cikin ?uncin da nayi tunanin nayi bankwana dashi har gaban abada Ashe Baban Sasa ya Waura min aure da Wansa Yaya Yunus, wanda kowa yayi mamakin babban al'amarin, duba da wane ne Yaya Yunus a gidan mu, da kuma girman shi; ya wuce a haWa shi aure da ?waila ?ar ?auye irina, Kowa ya kasa magana tsaban mamaki da al'ajabin wannan hukuncin da Baban Sasa ya yanke, yayi mugun yin musu bazata, Wanda kuma ya yanke ne don ?ashin kansa, domin jefo tsuntsu biyu da dutse Waya, yayi hakan ne don ya nuna wa Umma cewan; su ke da iko da Ni fiye da ita a duniyar nan, kuma dole in dawo ?ar?ashin su in zauna, Sannan yayi hakan ne domin ya samu damar dawo da Wansa gare sa, duk da Yaya Yunus a matsayin Wansu ne yake amma basu da iko a kansa, yayi musu rata da nisan da sun kasa tan?wara shi, a koyaushe Baban Sasa yana zama da ba?in cikin rasa Wansa da ya nuna ya fi karfinsu bare yayi musu biyayya, wanda sai su shafe tsawon lokaci basu sanya shi a ido ba, don haka a ganin sa idan ya haWa auren sa dani dole ne ya ri?a ziyartan su akai-akai, sannan ma tunda yana da gidan sa da ya gina a ?auyen, a nan zan zauna ko don dolen sa ya ri?a zuwa duba Ni, wannan hanyar ce kaWai yake ganin zai bi domin Yaya Yunus ya dena nisa da gida, kuma wannan auren umarni ne ga dukkanmu; babu wanda ya isa ya tsere masa, zai yi fito na fito da duk wanda yace zai bijire a kan maganar Allah Sarki! Ashe somun taSi ne a kan ?uncin rayuwar da na taSa fuskanta, ashe ba a fara ba ma, yanzu ne sabon feji na daga cikin ?alubalen rayuwata zata buWe. Wayyo Ni Madina! Meyasa sai Ni rayuwa zata juya wa baya haka?. ***** Abun da ke faruwa sam Alh. Badamasi bai sani ba, don tun tafiyar sa da kusan watanni uku ya aiko aka kwashe masa iyalansa kaf, waWanda suka yi aure kawai ya bari tare da nasu iyalan, don suma yana da tarin gonaki ne a nan shiyasa ya bar musu su kula mishi dashi, tunda suka ga haka suka tabbatar da cewan Mahaifin nasu guduwa yayi a kan abun da ya aikata, mutanen gari ba wanda ya ji labari sai da Iyalansa suka tafi, Yayinda shi kuma bai damu da wata *RAYUWAR MADINA* ba don ya san cewa Bokansa already yayi masa aiki a kanta, ya gama sakankance wa ita da aure har abada, koda tayi auren ma baza a taSa ji?a masa aikin sa ba tunda Already Boka yayi masa aiki a kan haka, don haka bai da wata damuwa, yanzu sai buWi da yake samu har aiki ya soma ci; ya soma ganin albarkan abun. [2/2, 9:36 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ?? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 13 of 55