Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi kuka tace, "Yaya Haula Ni ba na son aure yanzu, ban san me zance mishi ba shiyasa na amince, sabida ya wuce gaban in mishi musu, tamkar Mahaifina haka na Wauke shi, amma wlh Yaya ba na son aure, Ni na fi son zama a haka." "Kullum haka kike cewa Madina, kuma kin san hakan bazai taba yiwuwa ba, rayuwar Mace bata yiwuwa sai da aure, abun da ya faru dake ba shine hujjar da za ki ri?a fadar haka ba, muna miki zaton alkhairi Madina, insha Allah za ki samu dauwamammen farin ciki daga nan har ?arshen rayuwarki, shiyasa idan ma kina jin haka a ranki ki ri?a addu'a ki bar wa Allah zaSi; shi ya isa da komai, bazai taSa bari ki ?ara shan wahala a rayuwarki ba, ki yi ta addu'a don Allah Madina ki ri?a sallan dare kina neman zaSin Allah, ba wai ki ri?a waWannan maganganun ba sam ba na jin dadin su." Hawaye Madinan ta share tana cewa, "Wlh Yaya tsakanina da Allah nake faWa miki ba na son aure, Ni ba na so kuma ba na jin ko nayi auren zan yi farin ciki, Yaya na san cewa daga lokacin na rasa sauran farin cikin da nake rayuwa dashi domin ku; ban ga mene ne dalilin aure ba da har za a matsa min..." Katse ta tayi tace, "shikenan na ji yanzu mubar wannan maganar, amma dai ki dage da addu'a kinji Madina Allah ya zaSa miki abun da ya fi zama alkhairi." "To Yaya Haula, ina yi ina iya bakin ?o?arina, zan ?ara dagewa insha Allah." Sai kuma Haulan ta koma bata labarin Yaran gidansu da za a yi wa kaciya wannan karon, su huWu duk ?a?an yayyinsu, Sai da gaban Madina ya faWi tace, "Yaya Haula don Allah ki dena faWa min irin wannan zancen, wlh na tsani jin kalman kaciyar nan." Sai kuma tahau sheshshe?an kuka "To ya za a yi Madina? Ai dole ne in faWa miki tunda ?an uwanki ne, abun da muka san dole ne kuma muma mun WanWana dole mu taya su jimami, ki sanar da Umma don Wazu na manta ban sanar mata ba." "Yaya Haula wlh duk ranar da nayi ilmi wata rana sai nayi ya?i da wannan zaluncin, bazan taSa bari kowacce Wiya mace ta ci gaba da karo da wannan ?alubalen ba, wlh sai na hana sai na taimaka musu, domin Ni kaWai na san wahalar da na sha wanda har yanzu ina kan sha; don ina jin ?unan abun matu?a, har yanzu jina nake ban dawo dai-dai ba, ba na jin dai-dai yaya Haula sun rigada sun cutar dani, Allah ya isa." Kukan da take yi sosai; sai itama Yaya Haulan ta fara zubar da hawaye, yayinda tace, "to ya zamu yi Madina? Cuta dai an rigada an cuce ki don naki ya zo da matsalar da har yanzu ba a samu wacce ta sha wahala kamar ki ba, Allah ya ba ki ikon cimma burinki Madina, wlh ina goyon bayanki domin a yanzu Ni kaina a tsorace nake musamman in na tuna Ihsan itama ta kawo kai, lokaci kaWan za ki ji ana maganar nata, wlh gaba Waya a tsorace nake." Da sauri Madinan tace, "to ki Wauko ta ki kawo ta nan kawai ta zauna, kin ga ko makaranta sai tayi a nan wurin Umma, don Allah ki tambayi Mijinki ya barta ta zauna a nan." Murmushin takaici Yaya Haula tayi tace, "ke dai kawai a yi sha'ani Madina, amma wlh baza su taSa yarda ba abun ma bamai yiwuwa bane, an rigada an haife mu a can sai hakuri Allah ya kawo maganin matsalar mu, amma ban san ranan da ?auyen mu zasu waye ba, kwanaki ma wasu sun zo gina makarantar boko wlh ?iri-?iri su Baban Sasa suka hana su, sai da suka shiga suka fita suka yi musu koron kare, Allah mun gode maka ko awanne hali muke shine abun godiya; domin bamu san ya rayuwar wasu yake ba Allah abun godiya ne, don Allah ki dena wannan kukan don ba shi da wani amfani a gare ki, mu taya su addu'a Allah yasa a yi lafiya a gama lafiya, bari in kashe wayana ina da aiki Madina, ki gaishe da su Hassana." Dakyar Madinan ta amsa mata sannan suka yi sallama ta kashe, sai dai ta kasa tashi a wajen don zuciyarta ta karye da tausayin ?an uwanta, yanzu shikenan zasu WanWani azabar da ta WanWana? Shikenan daga yanzu an gurSata musu rayuwa? Ta yiwu ma su kamu da ciwo makamanciyar nata da ta azabtu a sanadin haka, Hawaye sosai ta dinga zubar wa ta faWa zuzzurfar tunanin makomarsu da kuma hanyar da zata bi wajen ganin ta taimaki ?auyen su, amma ta san da kamar wuya burinta ya cika, kamar yanda Mashkur ya taSa faWa mata ne insha Allah baza ta kasa ba sai ta nemi ilmin da zai kaita matsayin nan, sai Allah ya cika mata burinta, Sai da Umma ta kira ta sannan ta tashi a wurin ta fita waje, sai dai tayi ?o?arin share fuskarta saboda kar ta gane halin da take ciki, sai ta je mata da maganar da Yaya Haulan tace ta sanar mata za a yi wa wasu kaciya daga cikin ?an gidansu. [1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 48 of 55