Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
idan ba haka ba sai su ce mu muka kashe ta." "Innalillahi wa'inna ilaihi taji'un! Ina zamu saka kanmu?" A cewar Lantana hankalin ta a matu?ar tashe A lokacin sai ga Jummai mai magani ta shigo gidan tana kwaWa sallama Jin muryanta yasa Lantana ta fita da sauri tana cewa, "Jummai don Allah ki zo ki yi ceton rai, yarinyar nan fa ta mutu ina gani domin jini ya tsinke mata, na dawo na tarar da ita ba ta nimfashi ban san mai ya same ta ba." Da jin haka sai Jummai ta nufi Wakin itama da sauri suka shige zuwa wurin Madina; wacce suke tunanin rai yayi halin sa. ***** Alh. Badamasi kai tsaye daga nan wurin Bokansa ya nufa, bayan ya bayyana a gabansa ya zayyane masa cika aikin da yayi a yau Boka ya bushe da dariya yace, "madalla aikin ka ya zo gargara, domin a wannan lokacin zaka ga cikan aikin ka da zaran ka sanya ?afa kabar ?auyen nan,ka tafi duk inda zaka je ko'ina kake son zama arzikin ka na can, babu haufi a Wan ?an?anin lokaci zaka ga cikan burinka, abu biyu ya rage maka ka saki yarinyar saki uku, sannan wannan layan da zan baka; ka kasance da ita duk inda zaka je, babu kai babu talauci, zaka yi mamakin samun Waukakar ka." Ya ?are maganar yana dariya mai ?ara da amsa kuwa Farin ciki kuwa ya cika Alh. Badamasi tsaban dad'i, domin har hankalin sa ya kwanta sabida jin aikin nasa ya zo ?arshe, yanzu sai biyan bu?ata, don haka ya amshi layan kamar yanda Bokan ya mi?a masa, ya sake cewa, "amma maganar da ka faWa min cewa yarinyar babu ita babu aure, yanzu ya zan yi? Wanne taimako zaka bani Boka domin kar yarinyar tayi aure bani da labari?" Idanunsa ya zare a kansa yana kallonsa da jajayen idanunsa masu ban tsoro, cikin amon muryansa yace, "ba auren ta bane matsalar ka, daga zaran da aka kusance ta ?adarin aikin ka zai karye, sai dai a sake sabon aiki, kuma aikin dole da ita za a sake, domin ita ce ?addaran arzikin ka, dole sai ka sake auren ta sannan zaka sake samun wani arzikin. Tana da ?ashin arziki yarinyar; duk wanda ya aure ta sai ya tabbatar da hakan." Jin haka hankalin Alh. Badamasi ya tashi ainun, domin babban aiki ne a gabansa, idan aikin sa ya Saci taya ya zai iya samo ta har ya aure ta? Shiyasa yace ma Bokan, "Boka babu wani hanya sai wannan dole? Bazan iya auren wata ba dole sai ita?" Fuska ya Waure tamau yace, "ita ce ?addaran ka, ko baka ji mai nace maka bane? Dole da ita za a sake aiki, kuskurenka ka bari wani ya kusance ta." Zufa ya sharce daga fuskarsa, hankalin sa ya ?ara tashi sosai yake duban Bokan, sai yace, "to Ranka ya daWe ka taimaka kayi min aikin da babu wanda zai iya kusantan ta har abada, domin cikan burina na har abada, zan baka ko nawa ne ko me kake so a duniyar nan." Dariya ya bushe dashi yana girgiza jikinsa tare da ware hannunsa, sai ya dube sa yace, "an gama da aikin ka, biyan bu?atarka zata biya babu ita babu wani mahalukin da zai kusance ta har abada, koda tayi aure dubu ne, don haka ka je kayi rayuwarka a duk inda kake so ka Wauka bu?atarka ta biya, ka gaggauta zuwa ka cikasa aikin ka yanzu kar lokaci ya ?ure maka." Daga haka Bokan ya sallame sa tare da Sacewa Sat a wurin Don haka kai tsaye Alh. Badamasi jiki na rawa bayan ya koma cikin ?auyen, sai ya samu wuri ya Soye Jakar kayansa sannan ya nufi kansa tsaye gidan su Madina, A ?ofar gida ya tarar da Baba Iro da Nasir suna magana a tsakaninsu, a tsaye ma suke da alamun tsayuwar su kenan, shi Nasir yana ri?e da fatanya zai tafi gona shi ne Baba Iro yake tambayar sa a kan maganar takin da zasu je su siyo a birni, A nan ya ?ariso wurin batare da yayi musu sallama ba fuskarsa babu walwala a turSune Ganinsa ne yasa Baba Iro ya faWaWa fara'an sa yana cewa, "ah ah! Alh. Badamasi kai ne tafe ashe?" Yaya Nasiru gaishe sa yayi cikin girmamawa yana mai gyara fatanyan sa da ke ma?ale a kafaWa Alh. Badamasi ya amsa har yanzu bai saki fuskarsa ba yake cewa, "dama magana ce ta kawo Ni." "To fa, Allah yasa lafiya? To ko zamu zauna ne? Yaya Ali ma na cikin gida bari in sa a kira sa." "A'a ba zancen da ya kawo Ni kenan ba, maganar da ke tafe dani idan ma na faWa muku ya wadatar ai, a kan maganar ita wannan yarinyar ne da aka kaimin ita, to zancen gaskiya bazan iya zama da ita ba sabida ban zaci haka daga gare ta ba, an munafurce Ni an cuce Ni, maganar da nake muku yanzu bazan iya zama da ita ba, da naso in jure in danne in rufa mata asiri mu zauna a haka, amma na ga abun ba mai yiwuwa bane, shiyasa na yanke shawaran sanar muku domin in yanke hukuncina, sai dai kuyi ha?uri tunda kun cuce Ni tun farko baku faWa min ita yarinyar ta san wani a waje ba kafin ku aura min ita, idan da kun faWa min gaskiya zan iya hakura in zauna da ita, amma wannan ba maganar wasa bane tunda har na same ta ba cikakkiyar budurwa ba, a ce kamar yarinyar nan ta san Maza da yawa kafin tayi aure?" Sai ya girgiza kansa yana mai nuna munin abun daga kan fuskarsa Daga Baba Iro har Yaya Nasiru da yayi ninyar juya wa ya bar su suyi zancen nasu, jin abun da yake faWa yasa shi dakata wa yana sauroron su, ashe mummunar labarin nan ne zasu ji wanda yasa gaba Wayansu gabansu yayi mugun faWuwa, tashin hankali ya bayyana a fuskokin su duk kansu sun kaWu sun gaza yin magana koda jin zancen da ya gama fita daga bakin Alh. Badamasi, sai suka yi shiru suna bin sa da kallo cike da mamakin furucin sa, taya hakan zai faru yace an cuce sa Madina bata je masa a cikakkiyar budurwa ba? Wannan wanne irin mummunar sharri ne wanda hankali bazai Wauka ba? "Wai ka san kuwa mai kake faWa Alh. Badamasi?" A cewar Baba Iro da yayi ?arfin halin furta hakan cikin tsananin ruWu da tashin hankalin sa da ya nuna a muryansa "?warai kuwa na sani, ai shiyasa na zo na faWa muku tun kafin abu yayi nisa, kar kuma ku ga laifina Ni bazan iya zama da ita ba, na sake ta saki uku ku je ku Wauki yarinyar ku daga gidana." "Innalillahi ????      !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wa'inna ilaihi taji'un!" Su dukkan su suka furta hakan suna mai zare idanunsu daga kallon Alhjin cikin tashin hankali mara misaltuwa, Ko kafin suyi magana shi tuni ya juya yabar wurin da saurin sa, Babu mai ?arfin tsayar dashi daga cikin su sabida halin da suka shiga, jikinsu har rawa yake yi sai furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un suke yi "Wai kuwa mafarki muke yi Nasiru ko da gaske ne abun da Alhaji ya faWa? Wannan wanne irin mummunar bala'i ne yake tunkaro mu?" Idanun Yaya Nasiru har sun soma kaWa wa sabida tashin hankali, bai tsaya sauraron Baba Iro ba ya juya da sauri yayi cikin gidan hankalin sa a mugun tashe Baba Iro ya bi bayansa yana ci gaba da salatin a fili, don yanayin da yake ciki yasa shi ruWewan da bai san cewa da ?arfi yake salatin ba. [2/2, 9:30 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 10 of 55