Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kasa yin masa musu." Nan fa sai aka hau hayaniya sabida jin zantukan Baban sasa, wanda ya hautsina wurin nan take wasu suka cika da mamakin furucin nasa, wasu kuma sosai sun yarda da maganar nasa tunda ai Wan siyasa ne dole zai iya yiwuwa akwai abun da yayi musu, musamman ma in har labarin abun da ya aikata a baya gaskiya ne, Al?ali ya buga guduma ya bu?aci a yi shiru, sai sannan ne aka soma natsuwa hayaniyar ta lafa Ansar ya ?ara neman alfarma domin jin ta bakin Madina, Don haka aka ba shi dama; shi kuma ya taka har inda take tsaye kanta a sunkuye, ya kirayi sunanta tare da faWin, "ta basu labarin abun da ya faru a ranan da Alhaji ya tafi da ita, da kuma dalilin da yasa ta aikata mishi hakan?" Kasa Wagowa tayi bare ta kalli kowa da ke wajen, sai dai jikinta wani irin rawa yake yi wanda zaka gane cewan a mugun tsorace take, don ma wai Mashkur ya bata ?warin gwiwa a jiya da suka koma wurin ta, sannan shi kuma Ansar ya ja mata kunne sosai ya kuma gargaWe ta a kan, "muddin ya tambaye ta kar tayi shiru ta ba shi amsar tambayar shi, kuma abun da ya tsara mata shi zata faWa dolenta.. if not zata ga mai zai yi mata don bata isa ta kunyata shi ba, already ya baro aikin da yake yi ne ya zo taimaka mata." Madina gwanar tsoro, bare Allah ya dasa mata tsoronsa da shakkarsa, wannan dalilin ne yasa bata kawo musu gardama ko wani cikas ba a yanzu, har ta iya bada labarin komai tiryan-tiryan, har da ?arin gishiri da Maggi da Ansar yace sai ta faWa, Tana yi tana kuka domin ta kasa jurewa ga tsoro ga tashin hankali Smile Ansar yayi lokacin da ya ji ta gama bada labarin daidai yanda yake so, sai ya juya yana duban Al?ali tare da furta, "My judge! Wannan shi ne abun da ya faru a ranan da tayi ?o?arin ?wace kanta, Macen da ta shiga irin mawuyacin halin nan a wancan lokacin, Macen da ta kasa manta u?ubar da ya gana mata a wancan lokacin; yarinyar da bata san komai ba kamar wannan don ta aikata abin da ta aikata, yana nufin tsoro ne da kuma kokarinta na ?watan kanta, ya nemi ya sake amfani da ita wanda yayi mata barazana da nufin kashe ta da wu?a. Sai kuma ga shi Allah ba azzalumin bawansa bane ita tayi nasaran caka mishi, i know wannan ba laifi bane, ?o?arin kare kai ne, zan so katu mai adalci kamar wannan ta yi wa Madina adalci sannan ta ?watan mata ha??inta a wurin mutumin nan, and we want to file a complaint against laifin raped Winta da yayi da kuma auren dole, muna bu?atar a bi mata ha??inta then a raba auren, thank you my judge." Ya risinar da kansa before ya koma ya zauna Kotun sai ta sake rikice wa da hayaniya kamar jira ake yi ya gama bayaninsa, Al?ali ya buga guduma yace, "a yi shiru don Allah." Sai ya dubi lauyan Sangaren gwamnati yace, "ko kana da abun cewa?" Mi?ewa yayi yace, "ya mai Shari'a wannan zantukan da suka yi zai iya zamowa shiri ne da suka yi domin ganin sun samu nasara, domin bazai yiwu a ce babu Alhaji a nan yana kwance a asibiti sannan a yarda da zancen su ba, kowa ya sani abun da ya faru a gaban Matarsa ne da kuma sauran security Win sa, idan har gaskiya ne cewan abun da ya aikata mata meyasa suka sake ba shi aurenta? Taya ya zasu ce hankalin su ya gushe ba a son ransu suka sake aura mishi ita ba; har sai daga baya? Ya mai Shari'a wannan abun duba wa ne, domin bata yanda za a yi su shirya zantukansu babu hujjoji sannan su zo su faWa kuma a amince da su, ina fata kotu zata yi mana adalci ta tsaya ta bincika maganar su sannan ta yanke hukunci. Nagode ya mai Shari'a." Komawa yayi ya zauna yana duban Ansar da suka haWa ido dashi, Sai dai kowannensu kawar da kansa yayi Inda al?ali ya sake duba takardun asibitin da aka ba shi, sannan ya Wago yana duban su yace, "wannan kotu baza ta yarda da zantukan mutanen nan ba har sai idan sun kawo shaidun da ya fi wannan ?arfi, sannan sai idan Alh. Badamasi ya samu lafiya ya zo kotun nan mun ji ta bakin sa, sannan wannan takardun na asibiti muna son mu ga likitan da ya duba ta domin tabbatar da gaskiya." Zumbur Ansar ya mike yana cewa, "Oh judge! give me a chance to introduce the doctor because he is here." Kansa ya jinjina tare da faWin, "an baka dama." Bayan ya faWa sunan Mashkur, sai Maga-takarda ya mi?e ya hau sanarwan, "ana bu?atar ganin Doctor Farouk Umar Farouk a nan." Mashkur mi?e wa yayi ya fito zuwa wurin da ake tsaya wa, Da kansa al?alin yahau masa tambayoyi a bisa jinyar da tayi, Kuma ya ba shi amsar duk abun da ya faru, Aka sake kiran Umma itama ta bada labarin duk abun da ta sani, Wannan dalilin ne yasa Ansar ya bukaci ganin matar Alh. Badamasi, Dayake ta zo wajen shiyasa aka kira ta, a nan ya tsare ta da tambayoyin da dole ta amsa gaskiyar abun da ta sani, tunda kasancewar yanda ya rikita ta; ta yanda dole ne ta fito da gaskiyar abun da ta sani batare da ta san ta faWa ba, har auren da aka yi lokacin suna ?auye da kuma wannan auren, iya abun da ta sani ta faWa, Nan fa mutane suka yi ca ana ta surutu abun ya Waga hankalin mutane, Shi kansa Al?ali ya gamsu da hujjojin nasu, dalilin da yasa ya bu?aci lauyan Alh. Badamasi yayi magana idan yana da abun cewa, Amma sai yace, "bai dashi." Al?ali bayan yayi rubutu sai ya yanke hukuncin, "za a Wage Shari'a nan da sati Uku masu zuwa, har sai idan Alh. Badamasi ya samu sau?in da za a iya kawo shi nan a ji ta bakinsa, sannan kotu ta bada belin Madina Sulaiman Umaru har zuwa ranan da za a sake dawowa zaman karshe." Sai ya buga guduma yana mi?e wa tsaye Wannan hukuncin ba ?aramin faranta ran duk wani Wan uwan Madina yayi ba, farin ciki ya cika zukatan su Umma, haka suke kukan murna duk sun nufo inda Madinan take, duk da an hana su ?arisa wa don a lokacin ?an sanda sun tasa ta waje zasu fitar da ita, Hakan ne yasa su Mashkur suka isa wurin su suna tattaunawa, Wani police da ya fita zuwa wurin motansu, shi ya je Wauko mukullin da za a kwance hand cuff din hannunta, don haka sai da aka fita da ita waje sannan suka kwance ta, Wurin ya cika ma?il da mutane don ?an jarida sun yi ca suna son musu tambayoyi, ga su Baban sasa suma duk sun iso wurin, Ganin jama'a sun yi yawa ne sai Mashkur ya ja hannunta ya saka ta a motansa, Lokacin Ansar na ciki ya zauna a gaba yana duba wayansa, tunda ya Wago ya dube su ya kau da kansa, yana jin sautin kukan Madina na shiga kunnensa, sai dai bai ce komai ba sabida har a ransa yana jin tausayinta, Mashkur sai da ya koma ya sanar da su Baban Sasa, "kawai su hau mota su biyo su zuwa gidan Kakansu, sai su ga Madinan a can, don nan jama'a sun yi yawa sosai." Hakan kuwa suka yi, bayan su Mashkur sun tafi suma motocin su suka bi bayansu suka tafi gidan Uncle Hashim. [3/2, 9:09 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ?? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* ???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 34 of 55