Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
za a Wauke ta a kaita gidan Ansar a matsayin Matarsa, a ganinta baza ta damu ba but sai da ranan ta kusanto sai duk wani tashin hankali ya tabaibaye ta, fargaba da tsoro ya ?ara Warsuwa a ranta, Fahimtar hakan yasa Falak sai mata dariya take yi tana tsokanarta; amma ita ta kasa mata magana sai dai tayi shiru tana kallonsu, in kuma tana zaune ita kaWai tayi ta faman hawaye tana tunanin wanne irin hali zata shiga a nan gaba? Wanda yanayin tsoron da ke zuciyarta ne ya soma famo mata ciwonta; sabida ?irjinta ya fara ciwo ya takura mata dakyar take iya numfashi, dole ta soma kokarin yakice damuwarta gudun samun matsala daga karshe ta sha wahala a banza, kukan ma ta dena yi but duk da haka jikinta babu dad'i ana gobe bikin a kwance ta wuni jikinta ya motsa, sai dai duk hankalin su Umma ya tashi suna ta rarrashinta da lallaSa ta, Daga karshe da ta sha maganinta ma sai aka samu barci ya soma Wibanta, kasancewar akwai hayaniya a gidan ta kasa barcin sosai, Umma tace ma su Hussaina, "su raka ta ma?ota ta kwanta a can tunda jikin nata babu dad'i, tana bu?atar hutu." Karshe dai ma?ota suka tafi tare a can ta kwanta har ta samu tayi barci ishashshe sosai, Bikin dai an yi shi babu wani armashi tunda amarya ba ?oshin lafiya ta cika ba, kowa ya san ciwon da take fama dashi shiyasa ba a takura mata ba, a can ma?ota ma take kwana tare da su Hussaina da Falak da ta tare a wurin ta, Duk da itama ta ci burin bikin amma kasancewar Madina ba lafiya duk sai ta ji babu dad'i, su kaWai suka yi hidimar su; don ranan bikin ma dakyar suka samu Madina tayi wanka sau daya aka shirya ta, shi ne har suka samu suka yi hotuna kala-kala, Bayan nan ta samu ta sha maganinta ta haWa dana barci, bata farka ba sai yammaci da aka tashe ta lokacin za a tafi da ita Tunda a can gidan su Ansar biki gagarumi suka yi ko'ina ya amsa an san da bikin, Ansar ba don yana so ba ya dinga shiga mutane domin ya nuna wa Daddy babu komai a ransa, An shirya party idan an kawo amaryan a cikin gidan, Koda aka tashi Wauko amarya bai bi su ba sabida duk ?an uwa ne cousin Win sa; infact Abokansa na can Riyadh basu san da bikin ba sai WaiWai a yau da suka ga sanarwar, shiyasa da aka soma damunsa kashe wayan yayi Dayake Daddy wajen Wauko Amarya; gudun samun matsala irin wancan, da taka-tsan-tsan aka taho da ita har da Khalifa da yake tare da su yaya Haula, An kwaso danginta da yawa tunda koda aka zo nan dasa biki aka yi, An gabatar da al'ada da komai ranan kawo Amarya, daga ?arshe aka mayar da ita part Winta ta zauna da ?an uwanta, Washe gari aka gabatar da buWan kai inda aka shirya gagarumin party isu-isu Mata kaWai aka zubar da kuWi, lallai dangin Madina sun san sun zo gidan masu shi; domin komai an wadata su dashi sun ci sun sha sun ture, masu guzuri sun yi, ?an ?auye sun ba ido abinci ba kaWan ba, ko'ina ka bi Camera ke haska wa, Ita dai Madina dole ta saki jikinta don babu halin jayayya, duk abin da aka ce mata shi take yi, Domin tunda aka kawo ta su Aunty Hafsah suke kula da ita da mata kwalliya; su shirya ta tsab, Falak na tare da ita duk inda zata jefa ?afa tunda ita ce babban ?awa, itama da suka zo nan Kaduna har ?an uwanta ta gayyata suka zo, wasu daga cikin cousin Win ta sa'annin ta, sai farin ciki suke yi tana taya ?awarta murna da samun gidan manya da arziki A ranan ba a bar ?an ?auye sun tafi ba tunda wani sabon bikin aka yi, sai a washe gari aka mayar dasu Zaria aka sauke su gidan Umma, Aka watse aka bar Madina ita kaWai da Khalifa, don har su Hassana sun dawo, sai Falak da ke tare da ita; daga baya ma ta koma gida ta je ta dawo, Suka zauna a part Win har da Khairiyya da su Nabeela, Zamansu ne yasa Madina ta rage damuwa da tsoro a tattare da ita; tunda sun ja ta da hira ne suna ta hira da wasa da dariya, Shima Khalifa an samu wuri ya haWu da yara sa'annin shi tuni ya bi su wasa, Har dare suna tare sannan aka shirya ta zuwa sashin su Mummy, Itama Falak sai a lokacin tayi mata sallama ta tafi, tace mata, "gobe zata sake dawowa." A can sashin Mummy suka yi sallan magriba da ishi'i, dukkansu iyalan suna nan tunda duk basu tafi ba; ana ta raha suka ci abinci gaba Wayansu a tsakar falon, Sai da Daddy ya shigo sannan ya zo ya zauna shima, ya saka Madinan ta dawo kusa dashi, Khalifa kuma ya Waura shi a jiki yana mishi wasa, Dayake yana jiran Ansar ne saboda ya haWa su tare yayi musu nasiha da kuma dan?a amanarta wajen shi. [1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* ???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 51 of 55