Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shima Khalifa ya Waga kai yana kallonta yace, "Mama good morning." Dukka sai suka yi dariya, While Madina ta amsa mishi tana cewa, "ka tashi lafiya?" Kansa ya gyada mata yana tambayar ina su Hassana? Khairiyya tace mishi, "ai nace maka sun tafi gida, yanzu kai kaWai ne da Mamanka a nan kun dawo nan da zama, Madina bari in je don Hajiya na jira na, yau muma zamu watse shiyasa har mun fara shirye-shirye, na ?wan?wasa wa Uncle Waki ma na sanar mishi ga breakfast din ku can, bari in tafi." "Please amma zaku zo nan ko?" Yanda tayi maganar ne Khairiyya tayi dariya tace, "eh mana, ai ba yanzu zamu tafi ba zamu kai yamma, sai dai ?an Abuja su baza su daWe ba zasu wuce." Sallama ta sake mata sannan ta fice da sauri, While Madina sai ta ja hannun Khalifa suka shiga cikin Wakinta ta rufe kofa, Da gudu ya cire hannunsa daga nata ya haye kan gadon yana duduma, yana mata surutun, "a irin gadon ya kwanta yayi barci jiya." Dariya tayi kawai bata ce mishi komai ba ta nufi bakin wadrob tana duba ciki, Jefi-jefi takan amsa mishi surutun nashi tunda ya cika mata kunne da magana, Kayan da zata saka ta ciro before tace mishi, "ya jira ta bari tayi wanka ta fito, kar ya je ko'ina kuma kar yayi mata Sarna." "To Maama." Ya amsa ta cikin kwaratsi yana murna, Sai ya koma kan gadon ya sake hayewa yana birgima da kiran sunayen su Aunty Hassana Wanka Madina tayi tukunna ta fito, sai ta Wauki kayan da ta ciro ta saka a jikinta, riga da skirt ne na atamfa, dayake atamfar kalan ja da fari ne ba ?aramin haska ta suka yi ba, tayi wani irin kyau tayi fayau da ita sabida duk ta rame manyan idanuwanta sun zurma ciki, sai suka ?ara haske tau, wannan ne yasa koda ta gama zura kayan sai ta nemi kwalli ta saka a idon; domin ta Soye narai-narai Win da suka yi sukai Wanye kamar majinyaciya, duk da a yanzu alhamdulillah ta tashi babu inda ke mata ciwo tunda ta samu barci ishashshe a daren jiya, sai jefi-jefi takan samu buguwan zuciya idan ta tuna inda take da wanda zata yi rayuwa dashi, Iya kwallin ta saka sannan ta Waura Wankwalin kamar ture kaga tsiya, ya amshe ta kuwa yayinda sajenta ya fito ras ya kwanta luff gunun sha'awa, Babu Winkunne a kunnenta bare sar?a; sabida tunda aka kawo ta ta cire su, dama ba ma'abociya saka su bane shiyasa bata nema ba, A haka ta nufi bakin gadon sabida Khalifa ya dame ta yunwa yake ji bai karya ba, Dungure mishi goshi tayi tace, "meyasa a can da ka kwana baka tsaya ka karya ba?" TaSe Wan ?aramin fuskarsa mai kama da nata sak yayi; cikin wulla ?afafu yace, "Ni bazan ci a can ba, tare da ke zan ci." ?wafa tayi tace, "ka jira Ni to ina zuwa, bari in Wibo maka." Sai ta ciro takalmin ta flat shoes ta saka sannan ta fice a Wakin, Kai tsaye Falon ta nufa don bata yi zaton zata ga mutum ba, sabida sai da ta Wan le?a before ta ?arisa, Ashe Ansar yana daga saman dining yana breakfast Win sa; waya a hannunsa yana latsa wa, so shima bai ji motsinta ba sai da ta kusanto wurin dining Win before ya ji ?aran shoes din ta, sai ya Wago kansa ya kalle ta suka haWa ido, Da sauri ta ja burki ta kasa ?arisa wa inda yake, yayinda ta ?walala mishi ido da ya bayyana tsoron da take ciki suna kallon kallo da shi, A tunaninta zata samu tozarci a gare sa, sai dai kallon nan nashi na ?urilla wanda gaba Waya ya hautsina mata ?an hanji yayi mata, Before ya janye idanunsa gefe ya ci gaba da abun da yake yi tamkar bai san da halittar ta ba, Ita kuma ta gagara ?arisa wa sai tayi kokarin juya wa da sauri, Amma sai Khalifa ya fito da gudu ya nufo inda take yana cewa, "Maama kin Wibo min abincin? I'm feeling hungry." Yayi maganar har da buga ciki yana kwaSe fuska, Tuni Ansar ya Wago kansa yana kallon Yaron, Sai dai bai ce komai ba ya sake janye idanun sabida ganin Madinan zata juya inda yake, Bata da yanda zata yi illa tayi shahada ta nufi wurin, sai dai a Wari-Wari take sabida hankalinta ba a kwance yake ba gudun samun matsala a wurin Ansar, While shi Ansar al?awarin da ya yi wa Daddy a daren jiya na cewan bazai yi sanadin da zai musguna mata har ciwon ta ya tashi ba tunda ya san halin da ta shiga, Daddy ya ro?e sa a kan, "ya ri?e ta amana ya kuma ji tsoron Allah, tabbas idan ya same sa da laifin wulakanta mishi ?a; ya kuka da kansa." Maganganun da Daddy yayi masa a daren jiya da kuma al?awarukan da ya Wauka shiyasa sam ya ji bazai iya saSa wa ba, ya san da zaran yayi mata wani abu karshe shi zai kwana a ciki tunda sauran gawa aka kawo mishi, shi yana mamakin ma yanda yarinyar ta dinga ciwuka kala-kala amma har yanzu take raye, abu kaWan zai yi mata sanadin ya dawo kansa, shi dama da manufa ya aure ta, ta zauna a matsayin Matarsa har abada; amma shi babu ruwan shi da ita, kuma bazai dauwama a haka ba dole zai ?ara aure, bari dai ya samu yabar ?asan first; inda zai tafi babu idon su Mummy bare suyi tunanin wani abu da zai mata... Tunanin da yake yi ne ya tsaya cak sabida jin an taSa shi, sai ya Wago kansa yana kallon Yaron wanda a zahiri ya ba shi sha'awa, murmushi yayi masa kaWan, While sai Khalifan shi kuma ya washe ha?ora yana gaishe shi, Ajiye cup Win hannunsa yayi before ya shafa kansa yana rike hannunsa, sai ya soma tambayar sunansa? Yayinda Khalifan yake amsa mishi cikin farin ciki, While Madina tana jin su amma hankalin ta yana kan haWa wa Khalifa tea, duk ta ?osa tabar wajen tamkar a ?aya take, gaba Waya jikinta rawa yake yi sai dai babu mai fahimtar hakan sai ita; hatta gumi ke keto mata ta cikin riganta duk adaburce take, sai take ganin kamar idanun Ansar yana kanta ne, Dakyar ta daure ta haWa mishi tea, sannan ta zuba mishi Chiefs a plate tare da ?wai a ciki, bata yi ma tunanin cikinta ba bare ta dauka har da nata, Sai ta dubi inda suke a fuzge, ganin ba ya kallonta sai tayi maza ta Wauki plate Win tare da cup tea zata juya; kuma cikin sanyin murya ta kira sunan Khalifa batare da tace komai ba tayi gaba, Yaron ya amsa but bai taho ba, Domin Ansar ya ri?e shi yace, "ya zauna shi zai hada mishi sai ya sha a nan." Wannan ne yasa shiru-shiru Madina tana jiran Khalifa ya biyo bayanta amma bata ganshi ba, sai da ta Wan Wauki lokaci before ta koma da sanWa tana le?a wa, a can ta hange su zaune Khalifa yana ta tusa burodi a baki yana kurSan tea, ya zauna a saman kujerar kusa dana Ansar sai faman cilla ?afa yake yi yana kaWa kai, While shi kuma Ansar hankalin sa yana a kan wayansa ne a time Win, Hakan yasa Madina ta juya ta koma batare da tayi tunanin kiran sa ba, zama tayi tana tunani a ranta but fuskarta duk a dame yake, zuciyarta ta kasa natsuwa har yanzu buga wa take yi kamar wacce take gabanshi har yanzu, bata san meyasa take tsoron shi har haka ba, takan rasa me ke damunta muddin ta ganshi domin already zuciyarta ta kamu da tsananin shakkarsa, uwa uba kallon da take mishi tamkar Mashkur Win ta, Sai ga hawaye kuwa a lokacin sakamakon tuna wa da tayi da Mashkur, idanunta ta rufe ta kwanta zuciyarta na mata zafi da suya, ta san idan ta jima a haka dole zata iya ja wa kanta, shiyasa tayi ?o?arin mantar da kanta wannan damuwar but duk da haka babu walwala a tattare da ita, ?o?arin karya wa tayi da abun karin amma dakyar take cusa wa, Sam bata yi tunanin Ansar yabar Falon tare da Khalifa ba, Sai shigowar su Nabeela ne ta san cewa babu su, Daga baya ma sai ga Falak ta zo gidan; tare da wasu daga cikin cousin Win ta, Hakan ne yasa duk suka taru a sashin suna ta hira da dararraku, har da su Aunty Yusra, Daga baya Aunty Hafsah ta soma tarkata ?a?anta suka wuce tunda Mijinta ya zo, Sai Nabeela itama da ta wuce duk da ita Flight zata bi Karfe biyar da rabi su Falak suka wuce, Ita kuma Khairiyya takai dare before Mijinta ya zo ya Wauke ta, Sai ya zamana kowa ya watse a gidan biki ya ?are, Madina tana can part Win su Mummy a can ta zauna, bata ga Khalifa ba sai daga baya da Ansar ya dawo ashe sun fita tare ne, A can part Win suka tarar da ita har wajen sallan ishi'i, sabida a can ma suka karya dukkansu sannan Mummy tace, "Ansar su koma part din su." Hakan yasa suka wuce tare, Khalifa na hannun Ansar sabida yayi barci, maimakon ya sauke shi a Wakinta sai ya wuce dashi kai tsaye dakinsa ya rufo ?ofa, Shiru - shiru Madina zata ga ya zo ya kawo mata Khalifa amma shiru, tana ta zagaye tana jiran motsin sa, but a zahiri tana mamakin ganin soyayyyar Wanta a wurin shi, bata zaci hakan ba, a wnanan lokacin har ta gaji dai ta kwanta cike da tunanuka kala-kala barci ya Wauke ta Sai a washe gari sannan Khalifan ya dawo wurin ta, sai tayi mishi wanka ta shirya shi, tana gama wa ya koma wajen Ansar tunda shi yace mishi, "ya je a yi mishi wanka ya dawo." Lokacin ?an aiki sun zo sun gyara part din an ajiye musu breakfast, Wakunan su ne kawai basu shiga ba, amma ko'ina sun gyara sai ?amshi yake yi, Itama Madina koda tayi wanka ta shirya ta kasa fita tunda tana jin motsinsu, sai can wani lokaci sannan ta saka Hijab ta fice tunda ta dena jin motsinsu, yau ma ta san sun fita tare ne, don haka ta wuce sashin su Mummy sabida baza ta iya zama ita kaWai ba, Sai ya zamana a can Madina take wuni wanda ta samu sau?in zamanta a gidan babu takura; damuwarta ya soma gushe wa haka walwalanta ya Wan dawo, domin ko kusa bata yi tunanin zaman nasu a haka ba, a zahiri ta fi farin ciki da rashin ganin Ansar tunda babu abun da ke shiga tsakanin su, ko gaisuwa tunda take bata taSa mishi ba, bata ganinshi sai idan sun dawo bayan magriba shi da Khalifa, domin ya samu abokin yawo ko'ina tare yake zuwa dashi, yana son yaron tunda yana da shiga rai, ita kuma Madina da zaran safe yayi ta gama shirya wa sai ta wuce can part Win, a can take karya wa, Komai masu aiki suke yi bata Waukan ko tsinke, Wakinta ne kawai take gyara wa, Wakin Ansar bata taSa le?a wa ba ko masu aiki ba sa shiga, A haka har ta Wauki sati biyu a gidan, tuni Khalifa ya fara zuwa school, while itama bayan sati biyun sannan ta fara zuwa, A can suka haWu da Falak tunda ita tayi sati tana zuwa, sai murnan ganin juna kuma ya biyo baya, sun ji dadin haWuwar su Falak sai tsokanarta take yi sabida sauyawan da tayi, a zahiri gaskiya Madina ta canza sabida ta ?ara haske sai she?i take yi; kuma ta Wan murmure tunda hutun ya amshe ta; yanzu babu wani fargaba a tattare da ita shiyasa ta Wan samu natsuwa Tun daga ranan kuma komai ya ci gaba da tafiya a haka, babu ruwanta da Ansar koda zasu ci karo a sashin su sai dai ta sadda kai ta wuce shima ya wuce, Khalifa shine Abokin Hiranshi in dai yana gida bai da aiki, ko shima Khalifan yana gida, to Madina baza ta sake ganin Khalifa ba ko barci a can wurin Ansar yake yi, shiyasa yaron ya sha?u da Ansar sosai; wanda a yanzu Baba yake kiransa, kuma Ansar yana jin dadin hakan shiyasa bai hana shi ba, Sai dai gefe Waya shi Madina mamaki take ba shi sabida ya zura mata ido ne ya ga iya gudun ruwanta, bata san cewa rashin gaishe shi da take yi yana masa zafi ba, tara ta yake yi sabida ya Wauki mataki a kanta, a ganinsa raini ne su kwana part daya har su haWu amma baza ta iya gaishe shi ba, kamar ita ce babba dashi, ko kuma so take yi ta jira ya gaishe ta ta amsa Dayake yau weekend ne haka ta sako hijab har ?asa ta zo wuce wa zata tafi wurin su Hajiya, sai ta tarar dasu a falo shi da Khalifa, fitowar ta sun haWa ido da Ansar amma sai ta Wauke kanta zata wuce, yayinda ya bi ta da kallo da wannan shegen kallon nasa na ?urilla, sai da ya bari takai bakin ?ofan fita before yace, "kee zo nan, gidan uwar wa za ki je bada iznina ba?" Saukar maganar a kunnenta wanda ta tabbatar da wanda yayi; sai da kanta ya Wan juya ?irjinta ya bada daram na sautin tsoron da ya tsirga mata. [1/27, 5:18 PM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 52 of 55