Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a gidanmu ba Waya ba; ba biyu ba, irin ciwon da suke yi da wahalar da suke sha, duk da su ba zubar musu ake yi ba Sarewa yake yi, don haka tsoron wahalar da zan sha yasa na ji sam bazan taSa yarda ba, wai yau Ni ce da cikin haihuwa; zuciyata ta kasa yarda da hakan ji nake yi kamar mafarki wai ina da ciki, ?an?ame cikin nayi ina mai runtse idanuna sosai tare da jin zullumin abun da zai faru a gaba, ashe shiyasa na ga cikin nawa ya kumbura ashe dalili kenan? Koda na ganmu a gida har ajiyar zuciya na sauke ina jin sanyi a raina, Tunda na ganmu a gida na sadakar ya ha?ura kenan, Sai dai kalamansa da a yanzu yake faWa min, "in na shiga in haWa kan kayana zai mayar dani ?auye." Wani irin sara wa gabana yayi, domin ba ?aramin tashin hankali ne ya riske Ni ba tunda ya furta zancen ?auye, amma babu fuskar magana don tuni yabar motan ya wuce cikin gida, Dole nima na fita na nufi ciki don in yi abun da yace A lokacin da Yaya Yunus ya sanar da Sharhabila, "yau zai mayar dani ?auye." DaWi ta dinga ji, don dama har zata sauke kwandon bala'i sabida ganin mun jima bamu dawo ba, amma tunda ta ji haka sai farin cikin ta ya bayyana, tace, "ai gwara haka, don na gaji wlh da ganin ta, ai zaman nata yayi haka gwara a mayar da ita ?auye can ta ?arata. Allah ya raka taki gona, Ni da kaina zan nemo wacce zata maye gurbinta, kuma Ni ba na bu?atar budurwa don hankalina bazai taSa kwanciya da su ba, babban mace zan samo." Yaya Yunus dai bai kula ta ba, tuni ya tafi Wakinsa zai shirya, hakan yasa itama ta bi bayansa tana masa magana Ni kuwa ina can Waki na kasa kwantar da hankalina, ban san sanda kuka ya kufce min ba don wlh ba na son koma wa wancan ?auyen, gwara ya mayar dani wajen Ummana amma bazan iya komawa can ?auye ba, A haka na haWa kayana ina matse hawaye na fito muka tafi, Dayake babu su Mubashir tunda satin Hutu ne suna can an kaisu gidan su Sharhabila, Ina ji ina gani muka bar gidan a raina ina jin farin cikin yau wahalar da nake fuskanta a gidan ya ?are min, sai dai kuma ban san mai zan tarar a can ?auye ba, da nan da can duk babu gwara a gare Ni, shiyasa baki na Sari nayi ?o?arin sanar mishi da cewan, "don Allah yakaiNi wurin Ummana ba ?auye ba." Amma sam Yaya Yunus bai kula Ni ba sai ma wani banzan kallo da ya sauke min, a haka ya durfafi ?auye ina ji ina gani ya mayar dani can, A lokacin da ya isa Mutanen gidan sun yi mamakin ganin mu da wannan yammacin, lokaci Waya maganar dawowan mu ta bazu ga ?an uwa nan da nan mutane suka cika gidan ana cewa, "a zo a ga Madina." Tunda tun jinyar da nayi aka Wauke Ni yau kimanin shekara Waya da rabi da barina ?auye, Shiyasa na zamar musu wata iriya na sauka daga Madinan da suka sani, domin a yanda suka ganni yau ba ?aramin bazata na basu ba, irin girman da nayi musu a fuska da kuma jikin da nayi kowa in ya kalle Ni ri?e baki yake yi, Ni kuwa kunya ya hana Ni sakin jiki sabida yadda na ga suna bina da ido suna faWin yanda na girma, Inna Asabe har da cewa, "lallai kam! Birni ya amshe ki Madina, ?ar tselen ?a; ji be yadda fa ta haSake nan da nan tayi mama har da ajiye wasu kumatu, yo Ni gani fa nake yi kamar ciki ne da ita." "Abun da zan faWa kenan kika riga ni Asabe, wlh ciki ne da yarinyar nan kun ga yadda ta sauya." A cewar Inna Habiba tana ri?e baki, Dayake duk a lokacin muna cikin sasansu yara sun tabaibaye Ni sun hana Ni zama sai murna suke yi, Shi ne suka tasa Ni gaba suna ta maganganun da na kasa Wago kaina sabida kunya A lokacin sai ga Yaya Haula wacce yara suka je suka kira ta don ta zo ta ganni, da farin ciki ta iso gidan goye da ?ar jaririyarta wacce ta haifa aka sanya mata Abeeda, da gudunta ta ture Yaran tana kiran suna na, Koda muka haWa ido ai sai muka rungume juna cike da murna, Ni farin cikin ganinta sai na saki kuka nan take ina ?ara matse ta cike da tsananin kewarta da nayi tsawon lokuta, Ita kuma farin ciki ya hana ta magana sabida ganin yadda na sauya bakin ta ya ?i rufuwa, Sai da Inna Lami tayi magana tace, "mu zo mu zauna mun tsaya a tsaye kamar an coge mu." Sannan ne muka zo muka zauna a kan ?aton tabarman da aka shimfiWa a tsakar sashin, Sasan sai ?ara cika yake yi da mutane; hatta su Nafisa da suke gidan mazajen su sai da suka taho don ganina tunda an basu rahoto, kowacce ta bazamo gyale ta shigo don ganina ana murnan zuwan nawa Shi kuwa Yaya Yunus can sashin Baban Sasa ya wuce tunda a lokacin mutanen gidan duk suna nan, su Baffa duk sun dawo daga gonakin su; suma suna jin labarin zuwanmu kowa ya fito daga sasasn shi, sai suka taru a falon Baban sasa ana gaisa wa, Baffonmu Abdullahi yace, "to ai sai ka kira mana itama Madinan mu gaisa da ita a nan, tashi maza ka kira mana ita." Baban Sasa da ke murmushi yace, "?warai je ka kira mana ita ta zo mu ganta." Ya ?are maganar da fara'a don ba ?aramin jin daWin wannan ziyaran yayi ba, duk da dai an jima da auren amma ya ji daWi matu?a da zuwan nasu, alamu wata rana da sannu Wan nasa zai ri?a ziyarar su akai-akai tunda bai taSa yin makamanciyar irin wannan zuwan ba, yakan shafe fiye da shekaru uku kamar an yi masa baki bai zo ya duba su ba sai dai waya, yau kuwa ga shi albarkan wannan auren shekara Waya da watanni biyu da auren har sun soma kawo musu ziyara, ai abun farin ciki ne wannan, Suna nan zaune sai ga Yaya Yunus Win ya dawo ina biye dashi a baya, Da sauri na du?a har ?asa na soma gaishe su cikin girmamawa cike da kunyar da ke tattare da Ni Suka amsa min a tare cike da farin ciki wanda ban taSa zaton hakan ba, domin a fargaban abun da zai biyo baya nake kasancewar abun da ya faru baya, amma sai na ga ba haka ba; domin kowannen su ya ja Ni a jiki sai tarin farin ciki da yake a fuskokinsu musamman in ka kalli na Baffa da na Baban sasa, sai tambayoyi suke min cike da jin daWi suna tambayana yadda nake da kuma irin zaman da nake yi a can? Dole na bude baki na amsa musu cike da kunya ina ?ara du?ar da kaina Baban Sasa da ke murmushi har lokacin yace, "ai haka ake so, Allah ya ?ara zaunar da ku lafiya gaba Wayan ku, yayi muku albarka, hakika na ji dadin ganin ku a wannan yanayin ba kaWan ba, dama burina kenan kuma ga shi Allah ya cika min, Allah ya albarkaci auren nan naku wata rana in ga zuri'a a tsakaninku..." Shi sam Yaya Yunus ya dena jiyo zancen Baban Sasan sam, domin tunanin da ke ransa da irin abun da yake shirin aikatawa ya dama masa lissafin sa, amma ba shi da zaSi ne dole hakan zai yi domin a yakice masa yarinyar daga jikinsa salin-alin, idan ba haka ba a yanda ya ga irin tarin farin cikin da iyayensa suke yi ya san baza su taSa raba auren nan ba, Shiyasa yayi shaha??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da ya soma bayyana ainihin abun da ya kawo sa gidan, yayinda ya sauya murya da yanayinsa domin su yarda da abun da zai ambata musu Babu zato babu tsammani kalaman nasa suka soma ratsa kunnuwan su, wanda gaba Waya nan take annurin fuskokinsu ya Wauke gaba Waya, rikici da tashin hankali ya soma bayyana a kan fuskarsu, Da sauri Baffa ya dakatar dashi da faWin, "kar ka raina mana hankali mana Yunusa, ya za ka ce tayi ciki kuma cikin ba naka bane; to na waye?" Cikin tarin damuwa yace, "wlh Baffa cikin nan ba nawa bane, nima ban san ya aka yi Madina ta je tayi cikin nan a waje ba, kwatsam rana Waya muka tabbatar wanda Likita ne ya gwada ta da kansa." Tsawa Baban Sasa ya daka mishi yana cewa, "kai ba ma son iskanci kaji ko? Taya ya zaka ce cikin ba naka bane bayan da hannunmu muka kaita gidan ka a matsayin Matarka; idan tayi ciki tana Matar aure ai dole kai ne uban cikin, idan ba kai bane uban waye?" "Shine ai Baba nake son in Fahimtar da ku, Ni ban taSa sanin ta a Mace ba wlh, hasalima Ni ina tausaya mata ne a matsayin yarinya ?arama shiyasa kawai nayi ?o?arin ta zauna a wurina Ni da Matata muka Wauke ta tamkar ?armu, amma ashe tana fita tana bin Maza bamu sani ba, kawai sai ga ciki a jikinta Ni kuma na tabbatar ba nawa bane, cikin jikinta ba nawa bane Baba wlh zan iya rantse wa, don Ni gaskiya bazan iya zama da ita ba shiyasa na dawo da ita ku tuhume ta ga ta nan, kuma na sake ta saki biyu na ha?ura da auren ta". [2/24, 12:05 AM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ?? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 24 of 55