Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su da kuma farin cikin gidansa, tun yana Soye halin da yake ciki sai ga shi Matarsa ta soma fuskantar komai, wanda ya ja musu tsiya da faWace-faWace kala-kala, har kuma ya fito fili ya bayyana mata matsayin Madina a wurin sa a can baya da bata sani ba, wanda sanadin hakan yasa tayi yaji tabar gidan ta koma gidan ubanta, kuma ta kwashe Yaran ta tafi dasu, sannan kuma takai ?aranshi wajen mahaifinta, Wanda shi ya goya mata baya ne sabida ita kenan ?arsa da ya haifa, duk abun da take so shi yake so, yana ganin tamkar cin amana ne Yunus yayi mata tunda har ya iya aure batare da ya faWa mata ba, sannan kuma har da sakamakon Wa, don haka ya kira shi yayi masa zaga-zaga kuma ya ?wace duk wani abu da ya san ya ba shi, hatta da gidan da suke zaune, Ko kusa a lokacin basu san cewa Yaya Yunus ya siya sabon gidansa ba tunda har wannan lokacin ya ?i komawa bare ya sanar da Sharhabila, shiyasa koda mahaifinta ya ?wace komai kuma ya kore shi a wurin aiki abun bai taSa shi ba, tunda dama yana sana'ar sa ya kafu da kanshi, ko kusa bai ji haushi ba sai dai da gayya ya saki Sharhabilan tunda shima yana ganin ai yana da hanyar da zai rama, Ya kuma sake ta ya koma sabon gidansa, wanda ya Wauki alwashin sai ya samu hanyar da zai dawo da Madina cikin rayuwarsa, komai zai iya yi domin ta a yanzu, idan ta kama koda dur?usa mata zai yi ya kuma ?as?antar da kansa a wajen su domin su yafe mishi kuskuren da yayi, don ya Wauki Wammaran komawa gidan Umma domin ya sake basu ha?uri A ranan ya je ya ga gidan a kulle kamar wancan lokacin da ya zauna jiransu, yanzu ma yana nan jingine da motansa yana ta duban hanya; sai ya ga sun fito daga gidan su Mashkur, ita Madinan tana ri?e da coolern abincin su, Umma kuma ta goya Khalifa a bayanta, basu ankare dashi ba sai da suka taho gab dashi sannan ne suka ganshi, Da sauri Madina tayi baya kamar zata kifa ta Soye a bayan Umma gabanta na wani irin buga wa, Hakan ne yasa Umma ta kamo hannunta suka yi maza suka nufi bakin gidansu, Umma ta saka mukulli zata buWe Hakan ne ya samu damar ?arisa wa inda suke cikin sanyin murya yace, "don Allah Umma ku saurare Ni wlh ban zo da nufin cutarwa a gare ku ba, ina son in gyara kuskurena ne kamar yanda nayi a baya, yanzu haka na sanar da dangi cewan Yaron da Madina ta haifa Wana ne, don Allah ku taimaka ku yafe min mu gyara abun da ya faru baya, na yarda zan mayar da Madina Wakinta zan kula da ita." Tuni Umma ta buWe ?ofan ta shigar da Madina ciki, itama ta shige tana shirin rufe ?ofan, Amma sai yayi saurin saka hannu ya ri?e ?ofan yana ?ara ro?anta cikin tsantsan nadamar abubuwan da yayi, Umma sam ta kasa sauraren shi domin a yanda take ganin ba?in shi da tsanar da take mishi; sam ta kasa ba shi wata damar da zasu yi magana, sai ma cewa da tayi, "ai ka makaro wlh har abada Madina ta fi ?arfin ta koma gidanka, ka cire ma wannan tunanin a ranka." Ta ja ?ofan da ?arfi ta datse, Ya kasa jirgawa a wurin yana tsaye kamar gunki, kuma ya ci gaba da buga musu ?ofan yana kiran sunan Madina, Ya jima a wurin yana buga ?ofan, sai da ya ga baza a buWe mishi ba sannan ya juya zuwa bakin motansa ya ci gaba da tsayuwa a wurin Har su Hussaina suka dawo makaranta suka tarar dashi, suna ta kallonshi duk da basu sanshi ba, Shima Win ya zuba musu ido yana kallonsu bai dai ce komai ba har suka nufi ba?in ?ofan gidan, Buga ?ofan suka soma yi amma ba a buWe musu ba, tunda a tunanin Umma har yanzu Yunusan ne a wajen bai tafi ba, shiyasa tayi banza dashi ta ci gaba da aikin ta, Madina na zaune a cikin daki ta gama shan kukanta tayi shirun dole tana cin abinci Sai can da Umman ta tuna da cewan lokacin tasowan su makaranta yayi shiyasa ta nufi ?ofan tana cewa, "wane ne?" Da sauri suka amsa mata da faWin, "Umma mu ne." Jin muryansu yasa ta buWe ?ofan suka shige, ta mayar da ?ofan ta rufe duk da ta ga Yaya Yunus a wurin, tana jin dole ne ta Wauki mataki mummuna a kansa don baza ta bar shi ya ri?a mata sintiri a gida yana tsorata mata yarinya ba, Don haka Baba na dawowa ta sanar mishi halin da ake ciki, don a lokacin tuni ya gaji da zaman wurin ya shiga motansa ya tafi, shiyasa koda Baba ya dawo bai gansa ba, Baba Yace, "ki ?yale shi kawai idan ya gaji da sintirin zai dena zuwa, ai sai an kula shi sannan zai samu damar yin abun da ya kawo shi." Umma tace, "Ni kuma zuwan nasa ne ba na so ko kaWan, kana tunanin bazai aikata wani abun ba? Kullum muna fita yana tsorata min ?ata duk idan ta ganshi sai ta firgice, da haka zai iya Wauke yaronsa ya kama gabansa, abun da ya yi wa Madina wlh sam ko fuskarsa ba na son gani, ya je can ya ji da tsiyansa, amma idan ya ci gaba da takura mana da Mashkur zan haWa shi ko don yayi mana maganin sa." Hakan kuwa ta faru domin tun ranan sai Yaya Yunus ya zo ?ofar gidan dai-dai lokacin da suke dawowa, tunda shima ya fahimci daga gidan da suke fitowa, Umma baza ta iya ganin yana firgita mata ?a ba tunda Madinan ta kasa kwantar da hankalinta; a guje take ?arisa wa gida duk idan tayi karo dashi, kuma idan suka koma gidan ta dinga kuka kenan tana ce ma Umman, "ba ta son ganin shi zai cutar da ita ne." Wannan ne yasa Umma ta sanar da Mashkur don tayi ?o?arin Soye wa bai san da zancen ba, kuma ta hana Madina faWa masa duk da a kwanakin bai zo gidan ba ma, dayake ba ya fita da wuri da safe in sun je suna haWuwa dashi su gaisa, idan ya tafi kuma sai dare, Hakan ne yasa Umma ta sanar mishi yau da safe da suka je gidan, Dama a lokacin yana ta tambayar Madinan ne abun da ya same ta? Duk da ya ganta cikin damuwa a kwanakin nan kuma ya tambaye ta amma ta ?i sanar mishi, yau kuma ya ganta kamar idanunta sun kumbura kamar ta kwana tana kuka, Shi ne Umman take sanar musu da abun da ke faruwa har Hajiya, tunda a jiya ma da daddare ya zo Baba ya buWe gidan bai san cewa shi ne ba, Sai da Umma tayi masa zaga-zaga tace, "wlh yanzu zata Wauki mataki a kansa tunda bazai dena zuwa musu gida ba." Hajiya Ummee tace, "yanzu shi Wan uwan nata ne yake ta muku sintiri a gida a nufin yana son mayar da ita?" "Wlh kuwa Hajiya, abun ba?in cikin ma kullum sai ya zo, Ni damuwata halin da Madina take shiga tunda ta kasa cire sa a ranta ta dena wannan koke-koken, nima sam ba na son yana ganinta tunda bamu san me zai yi mata ba duk kashedin da nayi masa ya ?i dena zuwa, tsorona kar yace zai Wauki Khalifa shiyasa ma na sanar muku ko akwai matakin da za a Wauka, tunda bazai yiwu ya ci gaba da mana sintiri a gida ba, da ina da hali ma wlh bazai sake ganinta ba ko ya zo." "To ai kuwa wannan abun dole ne a Wauki mataki, amma bari Farouk yayi magana mu ji hukuncin da zai yanke ko hukumar ne ma a haWa shi da su, haka kawai ana zaune ?alau ya zo da wani shirmen shi." Mashkur kuwa kasa yin magana yayi sabida halin da ya tsinci kansa, kasancewar sa mai sanyin hali shiyasa baza ka taSa fahimtar ya zuciyarsa ta shiga da jin wannan zancen ba, amma hankalin sa yayi matu?ar tashi ransa ya Saci sosai, sai dai yayi ?o?arin Soyewa gudun gane halin da yake ciki, shiyasa da ya bude baki yace, "Ni ina ga idan har ya dena ganin Madinan hakan zai fi bazai ci gaba da takura muku ba." Hajiya tace, "to ina za a kaita ga mahaifiyarta a nan? Kana ganin akwai inda za a kaita ne?" Kansa ya jinjina yana duban Umma tare da cewa, "Umma idan har kin amince sai a Wauki Madina a kaita gidanmu can Kaduna ta zauna a can, na san hakan ma zai taimaka mata wajen sakin jikinta ta manta da duk abubuwan da suka faru da ita, idan tayi nesa zata fi samun kwanciyar hankali, inyaso sai tayi karatun ta can kinga bazai sake ganinta ba bare ma ya san inda take, babu wani zancen hukuma shi da kansa zai hakura da nemanta." Da sauri Hajiya tace, "yauwa shawara mai kyau kuwa, domin can ne kawai ya fi dacewa ta zauna tunda Zulaihat bata da wata matsala zata rike ta kamar ?arta, idan har kin amince Asiya sai ku yanke shawara da Mijin naki a tura ta can ta zauna tayi karatun ta a can, kinga abun da Mashkur yace ai." Cike da sanyin murya Umma tace, "amma anya Hajiya hakan zai yiwu? Baza mu takura a dauke ta a kaimusu ita ba? Ai Wawainiyar sai yayi yawa." "Kinga Asiya nace miki babu matsala in dai ?ata ce zata rike ta, suka ri?e na wasu ma bare wacce mu muka kai musu, ai yanda Mijinta yake da taimako ko gidan kika je za ki ga a cike yake da jama'a masu cin arziki, wlh in dai kin amince babu wata matsala Asiya a kaita can Win kawai; itama zata samu sauyin rayuwa." Umma ta yarda da shawaran nasu tunda har a ranta tayi tunanin da tana da inda zata kai Madina baza ta barta a nan ba, amma tunda ta samu hanyar da zata kaita kamar taimakonta aka yi, ta san waWannan Mutanen masu kirki ne da sanin yakamata, ta san cewa Madina zata ji daWin zama a can fiye da tunanin ta. Don haka tayi amanna da hakan har a ranta kuma ta ji dad'i sosai, sai dai kuma bata san yanda ita Madinan zata Wauki zancen ba ko zata amince? Tunda matsalar dama ita ce, Ga Madinan a zaune tana sauraron komai kanta a saman gwiwowinta ta ?i Wagowa ma bare tayi ?wa??waran motsi, Lallai kam in dai Madina ta amince to itama ta amince bata da matsala, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi. [3/4, 8:55 PM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ?? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 37 of 55