Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
har wani lokacin ma Falak faWa take mata, Amma da?yar Madina ta iya cire kunya ta sanar mata tana kuka; saboda idan ta ci gaba da barin abin a zuciyarta mutuwa zata yi, tana son ta fitar da shi ko don ta samu salama, Falak ta tausaya mata matu?a don bata taSa tunanin wannan abun ke azabtar da ita ba, ita kanta sai tayi mamakin wai dama akwai ire-iren su Madina masu rashin jindaWin wannan abun? To ko dai akwai laifin Mijin ne ko kuma ita Madinan da har ake samun wannan matsalar? But duba da yanda ta sanar mata, "duk sanda suka kasance tare sai jini ya fita a jikinta ga azaba da take ji." Cikin tausaya mata tace mata, "ai bai kamata ta zauna batare da ta nemi magani ba, su maza baza su tausaya mata ta wannan fannin ba, irin haka ma sai ta saka a yi mata kishiya tana zaune lafiyarta." Haushin maganar yasa Madina ta banka mata harara tare da cewa, "to ina ruwana da kishiyar da zai yi min? Cewa nayi ina sonshi? Wlh da zai sake ni a yau ya auro Mata huWu da na fi kowa murna." Falak sai ta ?yal?yale da dariya sabida ganin yanda Madinan ta harzu?o tayi maganar, sai tace, "Allah ya ba ki hakuri, amma duk da haka ai Mata da Miji sai Allah Madina, ba ga shi kuna tare ba har yanzu tsawon wata huWu? Kema kin san Ansar kyakykyawar saurayi ne wanda kowacce Mace zata yi fatan ta samu kamar..." Katse ta Madina tayi cike da takaici tana cewa, "ba na son wulakanci, ba na faWa miki don ki yi min wannan sharhin bane, na faWa miki ne domin samun sau?i a cikin zuciyata kuma don kin matsa min." Dafa ta Falak tayi tace, "I'm so sorry ?awata, but duk da haka matsalar ki dole ne ki je ki ga likita, ta yiwu ma infection ne tunda an ce ba abun da ba ya saka wa." Shiru Madina tayi sabida itama ta yarda maybe shi ne, amma ai tayi magani kala-kala a baya ko haka yake da naci? Sai ta dubi Falak cike da damuwa tace, "kin san babu irin maganin da ban yi ba a kan cutan nan, but ya ci ace na rabu dashi, kawai dai ni ban yi sa'a bane, duk Mazan da suke kasancewa dani suna azabtar dani ne a kan hakan, ni ban san me ake ji ba a wannan tarayyan, ba na son wannan abun Falak, ji nake yi tamkar zan kashe kaina idan na tuna dole zan rayu da irin wannan abun ne, shiyasa tun farko na tsani in sake aure Falak, amma su Umma sun kasa gane wa, ni kuma haka rayuwata zata kasance cikin u?uba Falak? Wlh na gaji kowa na tsane shi a duniyar nan ban san mene ne amfanina ba, Allah ka Wauki raina ko na huta." Yanda take wani irin kuka mai fitar hayyaci lokaci guda, sai da Falak ta rufe mata baki ita kanta kukan tausaya mata take yi "Don Allah ki dena kukan nan haka Madina, ki yi hakuri ki yi hakuri, wlh ko a Film ban taSa haWuwa da wata wacce ta sha wahala kamar ki ba, ki yi hakuri dan Allah domin ki cinye wannan jarabawar, kar ki butulce wa Allah, ki yi hakuri insha Allah akwai maganin damuwarki a duniya, wata rana za ki ji dadi ?awata." Cikin kuka tace, "sai yaushe Falak? Sai yaushe wannan ranan zata zo? Kullum haka kuke cewa. Umma tana faWa min hakan a koyaushe, itama Yaya Haula tana faWa min, sannan kema ga shi kina maimaita min; kuma hakan ta ?i faruwa, wannan ranan ta ?i zuwa har yanzu, kullum ni da sabuwar ?addaran da take zuwa min, babu hutu a rayuwata? Ko dai na yi wa Allah laifi ne yake hukunta Ni da..." Rufe mata baki Falak tayi, sai ta rungume ta suna kukan a tare sun kasa tsagaita wa, Allah yasa a wurin da suka zauna babu mutane kusa dasu, amma jefi-jefi sukan wuce, Wannan yasa Falak ta Wago kanta tana faman rarrashinta tare da furta, "ki yi shiru haka nan don Allah kar mutane su zo su ganmu a haka, ki yi hakuri, ki bari yau idan na koma gida zan sanar da Ammeena halin da kike ciki, na tabbata zata taimaka miki tunda itama Likita ne a kan Mata, idan ma akwai cutar da ke damunki zata bincika, zuwa gobe sai mu je asibitin mu same ta, kinji ki yi shiru haka nan don Allah." Da?yar ta iya rarrashinta amma hawaye sun kasa tsayuwa a idanunta, sai suka yi shiru dukka a wurin duk surutun Falak ta kasa ?ara kowacce kalma, Daga karshe sun kasa koma wa class bare su ?arisa lectures Win su, sai ta raka Madina shago ta siya ruwa ta sha maganinta sabida yadda take ta ?wannafi tana numfashi sama-sama alamun ciwon zuciyarta ya motsa, jikinta har ya Wauki zafi, Karshe Falak ita ta mayar da ita gida tunda ita tana da Mota, bata jira a kira Direban Madina ba. Dayake Ansar tun jiya yayi tafiya zuwa Baushi kan wani Shari'a, kuma bazai dawo ba sai jibi, kwana uku zai yi, Madina ta fi kowa murna, don a daren jiya har barci mai daWi tayi har da munshari, Shiyasa yau ma da ta koma gida sakamakon yanayin da take ciki sai ta kwanta a sashinta tayi barcinta ishashshe, da ta farka kuma sai ta ji dad'i babu abun da ke mata ciwo, Kasancewar magriba tayi sai ta tsaya yin Sallah before ta wuce sashin su Hajiya, Khalifa ma na tare da ita, Waya daga cikin ?ar aiki ta rako shi zuwa part Win tunda ya ji shiru bata zo ba, Sai hayaniya yake mata da guje-guje shi kaWai, wannan ne yasa ta haWa shi da wayanta tace, "ya buga Game." Ita kuma ta shiga wanka ta Wauro alwala a lokacin, Tana fitowa ya shigo Wakin a guje da wayan a hannu yana ihun kiran sunanta, Ta amsa shi tana cewa, "wai mene ne haka Khalifa? Lafiya?" "Mama, Baba ne yake kira a wayanki, shine yace in kawo miki." Da mamaki take bin wayan da kallo, sai dai bata ce komai ba ta mi?a hannu domin ya bata wayan, duba wayan tayi ta ga number ne kaWai, sam bata yi tunanin Ansar bane duk da baba yake ce mishi, but sai ta kara wayan a kunne tana jiran jin muryan waye, Babu zato ta ji saukar muryansa yana kiran sunanta, da sauri ta Wago wayan tana sake duban numban, mamaki kwance a kan face Win ta, but bata tsaya dogon tunani ba tayi saurin kashe wayan, tana shirin kashe wayan gaba Waya sai kiran ya sake shigowa, sai tayi reject tana kashe wa gaba Waya fuskarta a turSune har da jan dogon tsaki Khalifa da ke kallonta yace, "Mama ba ki Wauki wayan ba, Baba ne yace in kawo miki ku gaisa." Wani kallo ta watsa mishi sai ka ce shi ne Ansar Win, ta harare shi da faWin, "oya shiga bayi ka Waura alwala muyi sallah an kira, ban son kuma ka dame ni da surutu." Bai yi mata musu ba ya wuce cikin toilet Win yana Wauro alwala, Ko kafin ya fito ta nemi riga ta saka; sai ta zura hijab sannan suka gabatar da sallan A daren ranan kwata-kwata Madina bata sake kunna wayanta ba, duk da a zuciyarta tana cike da mamakin yanda aka yi Ansar ya samu numbanta, ta san bazai wuce su Hajiya ya tambaya ba, amma sam baza ta iya amsa wayansa ba, da ya san yanda take ji a kansa da bai shishshige mata ba, ko uban me zai gaya mata oho? Ita kanta abun ma mamaki yake bata a yanda ya sauya mata cikin ?an?anin lokaci haka, duk wulakancin da yayi mata a baya da irin zagin da yake mata a matsayin ta na ?ar ?auye, wacce aka haife ta a ?auye, sai yanzu ta tabbatar da maza basu da kunya ko kaWan, duk abubuwan da yayi mata yanzu ya manta sabida son zuciya irin nasa, idan ta tuna hakan har hawaye take yi sabida takaici da kuma rasa hanyar da zata yi ta rama, baza ta taSa yafe mishi ba domin baza ta taSa ?aunarsa ba, already ya rigada ya yi wa kansa ba?in fenti na har abada, kowa ma ta tsane shi in dai namiji ne, mutum Waya ne take mishi uzuri, koda ya dawo duniya ya yi mata abun da suka yi mata baza ta taSa tsanar shi ba, shi ne na daban a gare ta, ya nuna mata tausayi da soyayya wanda bata taSa ganin irin sa ba, a kansa ne kawai ta san shaukin so har takan iya dariya ba?in cikinta su gushe baki Waya, amma ya tafi kamar yanda ta san farin cikin ta bazai taSa dawowa ba, ta yi wa kanta al?awari zata ci gaba da rayuwa da Ansar a matsayin Mijinta ba don tana sonshi ba, sai don kar ta ?ara faWawa hannun wani namijin da bata san wanne hali zata shiga ba, Shi yanzu ya sauya ta ga canji mai yawa a tattare dashi, amma baza ta taSa ?aunarsa ba har abada, domin har yanzu tana ganin kamar yaudara ne, mutumin da ya ?i ka a baya idan ya dawo yace yana sonka ku zauna lafiya, tana ga kamar akwai wata manufa a tattare dashi, duk da har yanzu bai taSa furta mata yana sonta ba, amma duk wani soyYyya da kula wa yana bata, wanda ita kanta kunyar kasancewar su tare take ji don ta kasa saba wa da maganganun da yake mata, but da ta fahimci haka shi rayuwarsa yake ya furta duk abun da ke zuciyarsa, haka nan take hakuri tunda bata da yadda zata yi.**** Washe gari bayan sun je school, daga can suka wuce asibitin su Falak, wato Family hospital Win su, tunda Falak tayi magana da Ammeenta, tace mata, "su zo su same ta da ?arfe 11." After sun je school sun yi lecture Waya sannan suka wuce a motan Falak, Lallai Madina ta ga abun mamaki sabida girman asibitin da suka je; ga kyau ga girma gunun sha'awa, Ashe ganinsa a fili ya fi labarin da Falak take bata, Lallai ta yarda cewa babban Family ne dasu duk da bata taSa zuwa gidansu ba, Amma yanda Falak Win ta gabatar da ita da yawan mutanen da ke cikin hospital Win; ta yarda cewa ?ar dangi ne, tunda duk yawancin su daga tace mata Yayyinta ne sai wadanda suke matsayin Iyayenta, ga su duk suna kama masha Allah kyawawa dasu, ga aji da gayu uwa uba kuWi da ya zauna musu, Sai da Falak ta gama nunnuna mata yawancin Familyn ta da suke duty a ranan; sannan kai tsaye suka wuce office Win Ammeen su, Lokacin da suka isa ba?in ?ofan sai ta nuna mata wani office da ke kusa da na Ammeen tace mata, "na Daddynsu ne but ba ya zama sosai a kasar ma, sai jefi-jefi yake zuwa irin two months or three." Duk da a yanzu an sauya tsaruka da yawa; ga gine-gine da aka ?ara, amma kowanne likita da sunansa a bakin ?ofan da zaka shiga, na Daddynta da Madina ta duba an rubuta, "Dr. Uthman Noor Al'amin." Na Ammeenta kuma an saka sunanta, "Dr. ?ahira Al'amin Al'amin." Sai sauran jerin offices da ke wurin birjik kowa da sunansa Koda suka shiga ciki office ne mai girman gaske wanda haWuwar sa ya wuce kwatance, infact ma a lokacin Madina bata tsaya kallon office din ba sakamakon haWuwar su da Ammee da ke zaune tayi musu iso; face Win ta Wauke da murmushi wanda ya ?ara wa kyakykyawar fuskarta kyau da kwarjini, Duk da Madina tana jin labarinta a wajen Falak but ganinta sai ya zame mata abun sha'awa, Matar ta matu?ar burge ta sosai, fara ce sosai duk da ba wata mai jiki bane, Kamilalliyar Mace mai kwarjini da cika ido, ba abun da ya fi jan hankalin Madina ga kallon Matar sai idanunta sabida sun kasance sky green masu daukan hankali, musamman da ta sanya eyeglasses ya ?ara ?awata idanun, Ko kusa ma Falak bata yi kama da Matar ba sai dai jini da kuma kasancewarta Uwa a gare ta Sai da Falak ta janyo ta sannan suka je suka zauna, Madinan tayi saurin yin ?asa da kanta tana gaishe ta, Ammee wacce ke duban Madinan ta amsa ta cikin sakin fuska, tana cewa, "Auta, Wauko muku drinks mana." Sai ta kira sunan Madinan tana cewa, "ita tayi fushi ma da ita saboda duk wannan tsawon lokacin bata taSa zuwa ta gaishe ta ba, babu wanda bai san labarinta a Familyn su ba sabida Falak tana sanar musu." Madina kasa magana tayi sabida kwarjinin Matar sai murmushi take yi, While Falak tana kare ta da faWin, "Oh Ammeena, ai tace zata zo har yanzu bamu samu time bane, but ba ga shi yanzu ta zo ba?" Murmushi Ammee tayi tana cewa, "ke dai kawai ki ce kare ta za ki yi. Ki saki jikinki Madina nima tamkar uwa nake a wurin ki, But yanzu ina da patient da zan duba zan je in dawo, sai muyi magana. Auta ki kula da ita kinji ko?" "Ok Ammee, sai kin dawo." Daga nan tashi tayi ta fice ta bar su a office Win, Sai Falak ta ja hannunta suka koma wurin kujerun huta wa tana shirya mata drinks kala-kala a gabanta tare da ce mata, "sai ta shanye su dukka, since Ammee tace ta kawo mata." Madina kuwa dariya kawai take yi abun ta sabida ta san halin Falak, wani lokacin takan taSa halayyar su na ?an Auta. [2/5, 9:21 PM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 54 of 55