Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Hassana ce ta sa?a mata; tunda ta iya don har yi wa mutane take yi suna biyanta, Sanya ?afafunta tayi a wajen; wanda yayi dai-dai da Wago kan Mashkur suka haWa idanu, da sauri ta janye idanunta a kansa, wanda sai yanzu ne ta ji ta daban sabida fitowar ta babu hijabin, duk da shiganta babu illa amma kwata-kwata ba ta yawo babu hijab, yanzu ta rigada ta saba bata jin daWin hakan, shiyasa nan da nan ta soma ?an?ame jiki kamar wata za'a ?wace ta, sai yazamana ta kasa sakin jikin nata a haka ta zauna gefen Umma, Umma tace, "ina Khalifan kuma? Ga Mashkur nan shi yake neman ki." Cikin sanyin murya ta amsa mata da faWin, "yana wurin Hussaina." Sannan ta gaishe shi batare da ta sake kallonsa ba While shi kuwa ya kawar da idanunsa ne kawai don akwai Umma a wurin, amma yanda yake jin wani abu na fizgarsa zuwa kallon kyakkyawar fuskarta, musamman yanzu da bata da hijab sai ya ji duk wani karsashi nasa ya soma saccewa, wani irin ?aunarta da son kallonta yana ?ara tasirantan sa, ba ?aramin jarumta yayi wajen amsa ta cikin wani yanayin da shi kaWai ya san halin da yake ciki, don koda ya fahimci Umma hankalinta ba ya wurin sai ya Wago da idanunsa ya zuba mata yana kallonta cike da burgewa da tsantsan ?aunar da yake mata, Kamar kuwa ta san yana kallonta sai itama ta Wago manyan idanunta tayi masa wani fizgaggen kallo, wanda take nan ta mayar da kanta ?asa don bata taSa tunanin zasu haWa ido ba, gabanta ne yayi wani irin buga wa sabida halin da take ciki na rashin hijab, nan da nan sai ta ji yanayin ya soma sire mata don har ga Allah tana jin idanunsa a kanta, wanda nan take sauran natsuwan nata ya ?arisa tafiya, Tana ganin Hussaina ta kawo yaron; tunda Umma tayi kiran ta, sai ita kuma tayi wuf ta shige Waki har tana cin tuntuSe, Umma tace, "ki yi a hankali mana kamar ba kya gani? Nakan rasa irin ki ne Madina." Mashkur kuwa murmushi yayi yana ri?e da Khalifa gam a hannunsa, sai duban fuskarsa yake yi kamar zai cinye sa, Umma ta dube sa tace, "ban san meyasa Mashkur kake mayar da gidan nan namu tamkar ba?onka ba, idan an yi maka tayin ruwa ka sha ba ka sha; na rasa yaushe ne zaka fara cin abin gidan nan? don Allah ko ruwa ne ka sha kar ka tafi haka nan, kana mana Wawainiya amma kai baka son amsan abun hannun mu." Da sauri ya furta, "Umma wlh ba haka bane, amma bari in sha ruwan tunda kin matsa, but Ni ina yin komai ne domin Allah." "Duk da haka dai idan ka sha zamu ji dad'i, tunda yaba kyauta tukuici, bari in Wibo maka." Mi?e wa tayi ta shiga Wakin nata ta Wibo masa ruwan randa, sannan ta kawo masa, Tana tambayarsa Hajiyan? Duk da basu daWe da dawowa ba amma sai da ta sake tambayar sa, Ya amsa mata bayan ya Wauki ruwan ya kurSa kaWan, Da haka suka Wan taSa hira kaWan yace mata, "zai tafi." Umma ta amshi Khalifan shi kuma ya mi?e zai wuce, tana ta masa godiya a kan Wawainiyar da yake musu, sai addu'a take mishi tana mishi fatan gama wa da duniya lafiya, Ya amsa cike da farin ciki a ransa sannan ya ?ara mata sallama ya fice, duk da a ransa ya so ?ara ganin Madina; amma ya san baza ta taSa fitowa ba ko kaWan, Yana fatan Allah ya nuna masa ranan da zai mallake ta domin ya nuna mata farin cikin da ta rasa, ji yake yi tamkar Allah ya cika masa burinsa idan ya rufe ido ya buWe, A jikin motansa ya jingina yana mai lumshe idanunsa tare da sha?o iskar yammacin, fuskarsa yalwace da murmushi mai kyau da nuna annashuwan da yake ciki, a hankali ya furta, "ina matu?ar ?aunar ki Madina, ya Allah ka nuna min Lokacin da zan mallaki wannan baiwa taka." Sai ya buWe idanunsa yana kallon kofar gidan nasu, sassanyan ajiyan zuciya ya sauke tare da sake furta, "har a raina ina jin kamar cewan Ni ne zan zame miki canjin ?addaranki, wanda na san cewa aurenki shi ne cikan burin nan nawa, ina sonki Madina! Ina matu?ar sonki!." Shiru yayi daga haka bai sake cewa komai ba kuma ya kasa shiga gidan, yana nan a tsaye a wurin yana ta faman sa?e-sa?e, har sai da wayansa tayi ring sannan ya dawo cikin hayyacinsa, ya ciro wayan daga aljihu ya duba, sunan wani abokin aikinsa ne Likita, don haka sai yayi answering call Win yana nufan cikin motan ya zauna, Horn yayi bayan ya kunna motan, Sai da mai gadi ya buWe masa sannan ya kutsa motan ciki ya je yayi packing, har lokacin wayan yake yi bai gama ba, don haka sai da ya gama sannan ya fito ya rufe motan ya sake koma wa wajen tunda lokacin sallan magriba tayi, shiyasa ya fita zuwa masallacin.*** Tun daga ranan sai ya zamana Mashkur yana zuwa gidan Umman duk idan ya dawo aiki ya ga sun koma gida, musamman zai je suyi hira da Umma sannan daga bisani ya nemi ganin Madinan, Duk da Wari-Warin da take yi dashi amma haka nan take zama gabanshi tana sauraron duk zantukan da yake mata, tunda ?warin gwiwa yake bata a kan case Win ta, yana tausanta tare da ?arfafa mata gwiwa, Ada ya so ya Soye abun da ke cikin ransa, sai ya ga ai wannan ce damar da zai bayyana mata abun da yake burin yin mata ko don ta sake sakin jiki dashi sosai, tunda yanzu ba kamar da bane, ada ta fi sakin jiki dashi fiye da yanzu, domin gani yayi kamar an sake sanja ta wani lokacin yakan kasa gane mene ne a cikin ranta, ba ta son mishi magana duk abin da zai faWa sai dai tayi shiru kanta a ?asa baza ta kalle shi ba, sannan a takure zata zauna har su rabu, ko walwala ba ya gani nata, duk da irin Wawainiya da kuma hidimomin da yake mata, Shi kansa bai taSa tunanin idan ya faWa mata maganar komawarta makaranta zata buWe baki tayi masa godiya ba, sai ya ga saSanin hakan ne, domin tunda ya faWa mata sai ta Wago idanuwanta masu cike da danshin hawaye, da alamun hawaye take zubarwa, sai da ta Wago kanta ya ankare, Da sauri ya furta, "Subhanallah Madina! Kuka kuma? Mene ne hakan?" Muryanta na rawa tace, "Nagode sosai Yaya Mashkur, Ni ban san da wanne kalman zan maka godiya ba, a kullum idan na buWe baki da ninyar gode maka sai in ga kalmomin bakina basu kai in furta maka su ba, Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, kaima Allah yayi maka abun da kayi min domin Allah ne zai biya ka." Sai tayi shiru sabida kukan da ya ciyo ?arfin ta, Yayinda shi kuma murmushi ya saki mai yalwa sabida farin cikin jin kalaman ta, ashe tana da hankali har hakan? Sai yayi saurin furta, "bakomi Madina duk da wane kalma kika yi min amfani dashi zan iya gane abun da ke cikin ranki, ina yin miki hakan ne domin Allah ba don komai ba, domin Allah ya bani damar taimaka miki kuma bazan bar ki cikin wata matsala ba in dai ina a raye, don haka ki sanya a ranki Ni Mashkur zan iya sadaukar da dukkan abin da na mallaka in har zan sanya ki farin ciki, ke ?anwata ce wacce nake jinta can cikin jikina, bazan taSa bari wani abu ya cutar da ke ba, sai dai ke kin kasa bani wannan damar har yanzu kin kasa yarda dani." Kuka ta fashe dashi tana dubanshi tare da girgiza mishi kanta, "a'a wlh na yarda da kai har cikin zuciyata, ban taSa yarda da wani mahaluki ba irin yardan da nayi maka, na san da cewa kai mutumin kirki ne mai zuciyar imani, Allah na Wauke ka a matsayin Yayana kuma ina fatan wata rana in saka maka da dukkan abubuwan da kake min, Nagode Allah ya saka da alkhairi." "To ki dena kukan haka kar Umma ta fito tayi tunanin wani abun nake miki, na gane kuma Nagode na ji dadin kalaman ki, hakan ma ya ishe Ni Madina, Allah ya bamu Sa'a a kan wannan Shari'an, in har aka raba auren nan komai ya ?are duk abun da kike bukata na game da karatunki; Ni zan Wauki nauyin ki, ke ko ba karatu ba komai da kike bukata ki faWa min Madina, Ni dai fatana ki Wauke Ni a matsayin Yayanki mai share miki hawaye kinji ko?" Da sauri ta jinjina mishi kanta tana mai share hawayenta da gefen hijabinta, Murmushi yayi mai ?ara mishi kyau tare da kallon fuskarta yace, "yauwa ?ar ?anwata, amma da sharaWi abun da nake bukata a game da ke." ?ago kanta tayi ta dube sa, Wannan murmushin da ke fuskarsa har yanzu bai Sace ba, irin kallon da yake mata shiyasa ta ji kamar ta nutse a wurin, da sauri ta mayar da kanta ?asa gabanta na ci gaba da faWuwa "Abu Waya nake bukata a gare ki shine ki yi min alkawarin za ki manta da komai daga cikin abun da ya shafi rayuwarki, ina son murmushi, farin ciki; walwala da annashuwa ya dawo kan kyakkyawar fuskar ?anwata, domin nayi alkawarin cewa sai na dawo da dukkan farin cikin da kika rasa Madina, don Allah ki yi min wannan alkawarin idan har kin yarda Ni Yayanki ne kuma kin amince dani?" Shiru tayi ta kasa cewa komai, sai faman wasa take yi da yatsun hannunta, Sai ya ja numfashi yace, "Wago kai ki kalle Ni Madina, ki natsu ki dube Ni ki dena jin kunyata Please, ina son ki Wauke Ni kamar abokin rayuwarki." Sam bata fahimci kalman sa na ?arshe ba, amma tayi ?o?arin Wago kansa ta kalle sa sau Waya sannan ta kawar da kanta, Yace, "yauwa, ki yi min alkawari da bakinki za ki sauya daga yanzu, Madinan da dana yanzu zasu bambanta, za ki manta da duk wani Sacin rai da kika samu a baya, kinga idan kina son yin karatu dole sai kin cire damuwa a ranki kin manta komai before ki samu damar yin karatu har ki fahimta, kin gane ko?" Kanta ta jinjina, sai kuma cike da sanyin murya still kanta a ?asa batare da ta Wago ba tace, "na gane Yaya Mashkur, nayi maka alkawari Insha Allahu zan yi abun da kake so, zan yi duk abun da ka ce." Ta ?are maganar kuma tana zubar da hawaye "Madina, kukan ne ban son ganin kina yi, ko kina son mu Sata ne tun yanzu?" Saurin girgiza mishi kanta tayi, tana kai hannunta wajen share hawayen, Sai yace, "to yi murmushi in gani, wanda zai tabbatar min da cewan ?anwata tana jin maganata." Zancen nasa ne kuwa ya bata dariya, wanda yasa ta murmusawa har jerin ha?oranta kaWan suka bayyana a fili, Shi kansa ya gani duk da face Win ta yana gefe, Sai ya ji wani tarin farin ciki ya kama sa, saurin lumshe idanunsa yayi ya buWe a nan take yana furta, "that's good my dear sister, na ji daWin hakan da kika yi, ki kasance cikin farin ciki domin ya fi komai saka ki kyau, bazan so ganin ki cikin damuwa ba. Ni zan tafi yanzu, kuma zan dawo gobe sai mu ?ara yin hira kamar na yau, Insha Allahu zan yi ?o?arin faranta miki a koyaushe bazan taSa barin ki kina cikin damuwa ba, nace miki duk abun da kike bu?ata ki tambaye Ni kai tsaye kinji ko?" "To." Ta amsa mishi tana Waga mishi kanta, yayinda take jin ta cikin kunyansa sosai yana ?ara mamaye ta, Har a cikin ranta tana jin wani irin farin ciki da sauyin yanayin da baza ta iya fasalta yanda take ji ba, amma ta yarda Mashkur shi ne komai nata a yanzu, ta yarda zata yi mishi biyayya tayi duk abun da yace mata in har hakan zai sanya shi farin ciki, shi mutum ne wanda bata san yadda zata misalta shi ba, duk da akwai fargaba a tattare da ita amma tayi ?o?arin cire wa a kansa tare da kokarin nuna masa matsayin da yake dashi a wurin ta, Wanda ya sa tun daga ranan ta soma sauya wa daga irin ?uncin rayuwar da take ciki, kuma ta dena ?untata kanta duk don Mashkur tunda a kullum ranan duniya sai ya zo gidan tunda ya samu dama, Umma kuma bata taSa cewa don me ba bare tayi tunanin wani abu, sabida ita kanta ta Wauki Mashkur tamkar Wanta, ta san cewa ba don shi ba da tuni ta rasa ?arta, don haka a yadda ta Wauke shi sam bata taSa kawo tunanin ko yana son Madina bane, sabida a ganinta ya fi ?arfin Madina nesa ba kusa ba, kawai dai yana taimaka mata ne sabida Allah yayi sa mai zuciyar tausayi da kuma son taimakon, kuma ta yarda cewan Allah ne ya haWa jininsu daga shi har Hajiya Ummee, ba don su ba basu san ya zasu yi ba, tana fatan Allah ya kawo ranan da zata saka wa waWannan bayin Allan A yanda Mashkur yake ba wa Madina kulawa tuni ta ?ara aminta dashi fiye da yanda tayi a baya, don a halin yanzu duk abun da ke cikin ranta sam ba ta iya Soye mishi, ya zame mata tamkar mai share mata hawaye ne, tana ganin shi kamar shi ne maganin damuwarta, duk abun da ya bu?ata tana mishi in har don tayi masa biyayya ne, ta saki jikinta dashi fiye da tunanin mutane, wani irin sha?uwa ne ya shiga a tsakanin su; Wanda kafin sati ukun nan ba ?aramin taimaka mata yayi ba wajen kwantar mata da hankali, fargabanta kaWan ne a yanzu da kuma tunanin makomarta a Shari'an nan, tana fatan a ce ta samu ?ancin da zata cika burin da take dashi, ko don yanda Mashkur ya sake ?arfafa mata gwiwa a kan karatun ta; ya kuma nuna mata karatun da zata yi zai iya sa ta taimaka wa jama'ar ?auyen su kan matsalolin da suke fuskanta na auren dole da kuma kaciyar da ake musu, wannan yasa wani daWi da farin ciki ya shiga zuciyarta har tana jin a ranta tabbas zata iya, kenan akwai ranan da zata iya samun damar taimaka wa wasu kar su shiga irin wahalar da ta shiga? Lokaci Waya wani irin ?warin gwiwa da tunanin dagewa????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  domin ta cika wannan burin da ke ranta, yanzu bata da burin da ya wuce ta soma zuwa makaranta har ta samu wannan damar, ta Wauki alkawarin sai ta taimaka wa ?an ?auyen su itama ta kawo musu canji, ta yarda da maganar Mashkur itama zata iya taimaka wa ?an ?auyen su, wannan tunanin shine kawai a ranta yanzu don bata tunanin har abada zata sake aure, ta manta da wannan tunanin ma Ana gobe zaman Shari'an Ansar ya dawo ?asan, sai dai daga can Abujan ya sauka gidan Kakansu Uncle Hashim, Shiyasa Mashkur shima tun a ranan suka wuce da Madina zuwa Abujan, har su Hajiya Ummee da Umman, A can gidan Uncle Hashim suka kwana gaba Waya zuwa washe garin da za a yi zaman Shari'a. [3/4, 8:52 PM] Oum?ahira: =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? ? ? *RAYUWAR MADINA* =ا? =؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎?=؎? _Writing Story:_ *NAFISAT ISMA'IL* ? ? ? ? ?? _(UMMUDAHIRA)_ *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>???* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 36 of 55