Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fito wa daga masallaci don haka sai kawai yanufi part din shi, domin dai yasan yarasa karatun yau, dakin shi yanufa yahau kwamfuta yafara gudanar da aikinsa ba tare daya kalli inda *Jana* take ba, kasan cewar tunda yashiga take bin shi tana bashi hakuri wanda zaya iyacewa shine karona farko datayi masa laifi yanuna bacin rai shine tabashi hakuri, ganin zata dame shi yasa yace yaji tafita tabashi guri zayayi aiki ne sannan tafita tsaki yayi mtww tareda cigaba da aikin shi. ****๐ŸŽ๐ŸŽ***** Yau Monday kuma ayau nesu *Deeya* zasu fara rubuta NECO don haka koda sukayi sallah basu koma bacci ba, kodama basu saba da hakan ba Bayan su yi karatun alqur'ani sai sukayi wanka suka shirya Cikin uniform suka fito basu tsaya karin kumallo ba kasan cewar sun tashi da azumin litini, don haka saidai kawai suka sallami Hajiya da Abba ida sukai masu fatan alkhairi, Sannan suka fita part dinsu lnna suka shiga nan ma fatan alkhairi su kai masu, sannan suka fito suka shiga part din *Habeeb*. direct dakin *Habeeb* suka shiga dake nan kasa yana tsaye gaban madubi sanye yake da wata dakakkiyar shadda sky blue, kamshi turaran shi duk yacika dakin, yana kokarin saka hulla yaji sallamar su amsa wa yayi ba tareda yajuya ya kalle suba, cikin sanyi murya sukace Hamman *Habeeb* ina kwana?.. yace kun tashi lafiya, cike da mamaki sukace lafiya lau domin bai taba yimasu haka ba, hakan ne yasa sucewa Hamman *Habeeb* yau zamu fara jarabawa, yace to madallah sai amaida hankali cike da zumud'in sukace to *Deeya* Ce yar daukan magana tace to Hamman *Habeeb* ai ba kayi mana addu'a ba, dasauri yajuyo ya kalle ta, itakuma tayi saurin ta dukar dakai kasa tana wasa da hannun ta yayinda kirjinta yake bugawa, fuska hade yace to aisai ku zauna KO a tsaye za'ayi addu'a?... zama sukayi shima yazauna sanna yafara kwararo masu addu'a sun amsawa, bayan sun shafa yace to Allah yabada sa'a sukace ameen sannan suka fita. *****๐ŸŽ๐ŸŽ**** Kwance tashi asarar me rai gashi har lokacin zabe yazo anyi kuma Cikin nasara *Habeeb* yalashe zabe, kuma ayau ne Jumma'a aka rantsar dashi anbashi office dinshi da gidan dazai zauna yanzu haka ranan Monday zaya fara aiki, dawowar su kenan daga abuja don haka, yau gidan Alh Hashim soro cike yakeda yan'uwa da abokan arziki masu ta ya su murna, "Aban garen su *Deeya* kuma tuni sun gama jarabawar su dukka daga neco har weac yanzu haka ma gobe asabar zasu yi send4t walima, shiyasa sun kasa zama sai shirye-shirye suke don haka duk fuskar wanda ka kalla agidan dauke take da fari ciki, musamman *Deeya* da *Feeya* bakinsu kamar gonar audiga don farin ciki, Hajiya tasa anyi masu gyaran jiki kamar wasu amare ga fulawa da akai masu ahannu da kafa kai yan biyun Hajiya sunyi matukar kyau kamar kasa ce suka gudu. ****** Washegari Tunda misalin karfe 7:30am su *Deeya* suka isa Makaransu kasan cewar sune manyan dalibai kuma shugabanni koda karfe 10:00am tayi alfurqan ta cika tabatse da mutane, dakuma manyan baki acikin har da gwamna da sanata wato *Habeeb* Hashim soro, su Adda Mamu da Adda Rahma sunzo dukkasu tareda yaran su, Cikin nutsuwa ake gudanar da program me ban sha'awa da burgewa, musamman yadda dalibai keta zuba larabci da turanci gwanin sha'awa, sannu ahankali har aka gama liyafar. yayinda shugabar dalibai wato *Haleematus-sadeeya yusuf* da mate makiyarta *Safeeya Hashim* sune dalibai mafi hazaka akowani fanni shiyasa duk suka washe rabin kyaututtukan, wanda hakan ba karamin burge mutane sukayi ba, Shi yasa ake ta daukar hoto dasu su Adda Mamu suna son suyi hoto dasu amma mutane sun hanna, *Habeeb* ma har zaya tafi sai *Harees* yace ya tsaya su dauki hoto dasu *Deeya*, shiyasa yatsaya saidai kuma sunfi minti talatin suna jiransu amma basuzo ba hakan ne yasa gaba daya ran *Habeeb* yabaci. Cikin bacin ran *Habeeb* yace da *Harees* kaga mlm kana bata mun lokaci fa, ahankali yace kayi haku bari nakira su fuska ba annuri yanufi gurinsu da'alama shima ran nashi ya baci, *Harees* yana isa gurinsu wani kyakkyawa saurayi shima yana'isa dan kimani shekara ashirin da biyu, sanye yake da t-shirt fara da wando baki Cikin yanayi na gayu yace yamma ta don Allah inason muyi hoto, har da *Feeya* za tace to sai tafasa sakamakon wani irin kalla da *Harees* ya watsa mata, dasauri ta daukar dakai kasa yayinda gaban take faduwa fuska daure yace mujen kuko?..Cikin sanyi murya su kace to tareda bin shi abaya, saidai kuma jiki su yai sanyi da ganin yanayin shi wanda hakan bai masu dadi ba domin basu taba ganin shi haka ba, yayinda wannan saurayin yake binsu yana cewa pls babys ku tsaya muyi hoto mana, ko sauraren shi basu yi ba domin bacin ran dasu kagani a fuskar *Harees* duk ya daga masu hankali musamman *Feeya* suna karasawa gurin su Adda Mamu, shi kuma saurayi yana kai hannun shi yariko academy gown din dake jiki *Deeya.* Aikam Cikin tsanani bacin ran *Habeeb* ya sharara mashi wani irin mahaukacin marin dayasa shi kusan faduwa, dasauri abokan shi sukarike shi kasan cewar suna biye dashi abaya Cikin tsanani bacin ran saurayin yadago tareda cewa?... *_Barkan mu da Jumma'a MASOYANA_* Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [7/2, 11:46 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 2โƒฃ3โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ Baki yasaki tareda zaro ido cike da tsoro saka makon ganin *Habeeb* kasan cewar shi din sanan ne, ga kuma wani irin azababben kwarjini da *Habeeb* din yaimasa wanda hakan ne yasashi kasayin magana, Cike da bacin ran *Habeeb* yanuna shi da d'an yatsa tareda cewa Kai! tabbas Kaci darajar "mahaifin ka, amma badan haka ba dayau sai na KO" ya maka tarbiyya domin naga alama bakada ita, Cikin tsoro saurayin yace Sorry sir, Da karfi *Habeeb* yace rufe mun _stupid mouth_ dinka agurin nan, kona sake watsa maka wani marin ni tsaranka ne Ina magana kana magana, dasauri yarufe๐Ÿคญ tareda girgiza Kai, yace "to nabaka bashi wannan idan kasake kuskure sake aikata haka KO?.. Na rantse sai nayi maka mummunan hukunci dasai kayi mamaki, Kai! hattara wlhy ba kasan kowane *Habeeb* bako?... Shikama dan saurayin nan duk ya tsorata da ganin yanayin *Habeeb* din, Cikin tsawa yace bace mun agurin nan stupid boy kawa, Cikin sauri yamatsa shida abokan sa. yayinda *Habeeb* ya watsama su *Deeya* wani irin firgetattace kallo dayasa ji kinsu yasake yadaukar rawa saboda tabar tsoro, tsawa yadoka masu Wanda yasa suka Kara tsoro ta, yace Ku kuma zaku wuce mutafi kosai na tattakaku agurin nan?.. Da sauri suka nufi inda motacin su yake yayinda *Hafeez* daketa wata masu harara tun dazu, yace aidama tattakasu kayi tunda su wawayen yarane ba tareda *Habeeb* yace komai ba, yabi bayansu rai bace yayinda *Harees* da *Hafeez* suma suka bisu, suma su Adda Mamu suka dafa masu baya, Saidai sukam zuciyoyin su cike da mamaki fadan da *Habeeb* yayi duk dacewa "eh sunsan lallai saurayin bai kyauta ba, to amma kuma fadan da *Habeeb* din yayi yayiwa inji cewar su fa๐Ÿ˜€. haka dai suka nufi gurin motocin guda biyar ne ajere guda Adda mamu suka shiga da iyalanta, itama Adda Rahma haka guda kuma *Hafeez* ne da *Harees* da *Deeya* da *Feeya,* biyu kuma ta uban gayyace *Habeeb* yashiga daya escort din shi suka shiga daya, alokacin guda suka bar harabar makaranta dagu. Shikam dan saurayin nan suna gefe shida abokansa suna kallon su harsu ka bar harabar school din, sannan ya sauke ajiyar zuciya dai-dai lokacin da naga me girma gwamna ya'isa gurin shi kafatar shi yadafa, tareda cewa Mustee my boy duk abinda yafaru nagani saidai banji dadin hakan ba, naso nakaraso naba hon BB soro hakuri amma nakasa saboda tsabar kunyar abunda ka aikata, Wanda wannan din alama ce kanuna ta rashin tarbiyya kuma kasan inayi maka ita dai-dai gwargwado, to amma meyasa zakayi mun haka acikin mutane shi baka ganin hakan zaya iya zubar mun da mutunci a idon mutane?... hawaye naga sun zubo akan kyakkyawar fuskarshi yace Dad kuskure ne amma bazan sake aikata haka ba kaji?...murmushi Dad yayi tareda cewa nayi my boy to kashare hawaye mana, yace to Dad nashare amma gaskiya inason yarinyar nan, baki Dad yabude cike da mamaki yace wacce acikin su?..yace *"Sadeeya* inason ta sosai pls Dad kayi wani abu kaji?.. dariya yayi tareda cewa kar kadamu my boy zanyi so mutafi gida yace yauwa Dad na inason ka, yace nima haka my boy, Sannan suma suka nufi indan motacin su suke suka shiga suka tafi. Nasan me karatu zaya so yasa wanene Mustee?...wato Mustafa shine cikakken sunan shi, shine d'a na biyu ga me girma gwamna mustee ya kasan ce nutsatsen yaro yanada biyayya sosai Sannan baya da irin rigima nan ta yaran masu kudi, shiyasa Dad shi yake matukar sonshi sosai bayan yagama secondary dinshi sai Dad shi yakai Cairo university ya kuma gama yau kwanan shi biyar kenan da dawowa, shine alfuqan ta gayyaci Dad shi shikuma yarakoshi wannan kenan, gashi kuma yaga *Deeya* yana so to bari mu gani ko yasa mu?...๐Ÿค” ******* Da gudu su *Deeya* suka shiga falo inda suka iske Hajiya zaune, itada lnna da Hajiyar su *Harees* dasu Goggo Lanti suna fira kasan cewar sunzo,Cikin shagwaba Suka fada jikinta suna cewa Hajiyarmu kinga "Hamman *Habeeb* KO" yace" wai mutaho gida kuma fa bamu ko gama daukar hoto da sauran kawayan muba, shine shikuma Hamman *Hafeez* har dace mana wawaye, dai-dai lokacin da su Adda Mamu suka shiga har *Hafeez* din yace ance maku wawaye. dasauri Hajiya ya tace a ah karka sake ce musu wawaye, yace to Hajiyarmu naji amma dai yau yaranki sun buga mana shirme tace me sukayi kuma?..nan yafada mata abunda yafaru, tace "a ah haba hali dubuna ya haka kuma.. *Feeya* tace Hajiyarmu dama famuna son ne mu gama dauka da kawayan Mu Sannan mu zamu sauka dasu, Hajiya tace kena tambaya?..baki ta turo tareda cewa ai hakane ko sweet *Deeya*?.. tace "eh mana. Adda Rahma tace mudai yaukun bamu haushi wlhy, Adda Mamu tace hmm! kedai bari kamar na doke su don haushi wlhy, ainaji dadi da Hamman" *Habeeb* ya kwashe "saurayin nan damari kai! amma dai gaskiya yamaru sosai, dariya suka kwashi dashi dukkan su, Da sauri Hajiya tace mari kuma?.. *Hafeez* yace "eh maruwan kyau kuwa. Hajiya tace ashsha meyayi aka mare shi kuma?.. nan su ka fada mata abunda yayi, tace ayya aida ba mare shi zaiyi ba da sai yai mashi fada kawai, Adda Mamu tace aikam yayi fada sosai kamar zaya rufe sa da duka fa, nihar abun yabani mamaki Hajiya tace hmm! ai yanzu Hamman ku yarikice dafada dan abu kadan sai yakama fada, Adda Rahma tace tab! yau kam yayi fad'a sosai ni tunda nake ban ma taba ganin fad'a shi haka ba, Hajiya tace hmm! Allah dai ya kyauta yanzukam Hmm ku yazama mafad'aci, yanzu d'a gidan wanene ya mara?.. *Hafeez* yace "Mustee ne fa d'an gidan gwamna tace Allah sarki har ya ban tausayi, *Deeya* tace tab Hajiyarmu aini Hamman *"Habeeb* yayimun dai-dai-da yazuba mashi mari, da yanzu yataba ni da wannan jagulallain hannun na shi, *Feeya* tace kai! sweet *Deeya* ๐Ÿ˜‚ amma dai ke muguwa ce yanzu wannan kyakkawan "yaron ne zakice yana da jagulallain hannu, tace "eh mana haka kawai ya tabani yajaza mun masifa ko kin manta abunda Hajiyarmu tafada mana ne?.. tace "eh fa kuma haka ne. Add Rahma tace kunga kutashi muje _garden_ muyi hoto, muzo mutafi gida kunsa gobe akwai family mitin kunga idan muka koma gida dawuri gobe ajidadin barinmu mudawo kome kikace maman Walid?..tace kwarai kuwa kinga sai mu bar masu yaran su KO?..hakane nan dai suka dunguma zuwa garden din Da kenan cikin gidan. Bayan su gama daukar hoto Sannan suka tafi gida inda suka bar su Walid dasu Salima, kasan cewar su *Deeya* zasuyi wata walimar karfe 4:00pm wacce dagasu sai kawayan sune kawai. Shikam *Habeeb* direct part din shi yanufa yayinda zuciyar sa take wani irin bugawa, koda yashiga bai iske *Jana* ba sai me aiki don haka tambayar tayai Ina *Jana*?.tace ita wlhy batasan inda taje ba tadai ce mata zataje tadawo, jiyayi ran sa yasake baci kasan cewar su Adda mamu sunce ta shirya su tafe guri walima tace bazata samu zuwa ba amma kuma gashi tafita yawo, tsaki yayi tareda shigewa daki. Wanka yashiga bayan yafito daure da alwala kasan cewar ankira sallah azahar, don haka kodaya shirya sai ya nufi masallaci. ******* Da misalin karfe 4:00pm *Deeya* Da *Feeya* nagani sunfito cikin wani hadadden gown din shidda pink color, anyi masu dinkin stone work tundaga sama har kasa yayi kyau sosai, yayinda suma sukai kyau acikin kayan, ababban falo suka shirya walima takuma yi kyau sosai sai misali 5:30pm Sannan suka gama inda suka sallami kowace kawa da kyaututtuka mai yawa. ******** "A hankali kuma Cikin nutsuwa suke tafiya suna fira *Deeya* da *Feeya* kenan sun dawone daga raka wata kawarsu, acikin fitar ta sune naji *Feeya* tana cewa sweet *Deeya* nifa duk abunda nakeyi karfi haline kawai, amma zuciyata ta kasa samun nutsuwa, musamman idan na tuna bacin ran da nagani afuskar Hamman *Harees* sainaji gabana yafadi, *Deeya* tace gaskiya sweet *Feeya* bamu kyau taba kuma fa ran shi yaci sosai kila shiyasa har yanzu bai shigo ba, tace hmm! inafa muka kyauta aina san fushi "yayi shi yasa duk na matsu naje naduba _give_ din daya bani kinsan yace" akwai letter acikin, *Deeya* tace kuma yace" idan kika karanta ki bashi amsa ba tace "eh kinga daga nan ma saina bashi hakuri ko?.. tace "eh mana tace to yanzu sai mu shiga part din lnna kinsa can su "Salima suka kai mana _gives_ dinmu, tace "eh haka ne to mu shiga can din haka suka cigaba da tafiya suna suna fira. yayinda wata bakar mota ke binsu abaya sai horn takeyi masu amma ko juyawa ba suyi ba balle me motar yasa ran zasu tsaya, sukan tafiyarsu kawai suke abunsu suna firar su da'alama ma basu san su ake yiwa horn ba, ahaka har suka shege gida. dai-dai lokacin da me motar ya'isa bakin get din gidan yayi horn megadi yabude masa kofa yashiga ba tareda bincike ba, guri yasamu yai fakin Sannan yafito kyakkyawa ne saurayi wankan tarwada, Dai-dai kuma wannan lokacin ne *Habeeb* yafito daga part din shi kasan cewar ance a nayi masa sallama. gaisawa *Habeeb* yake da mutumin amma kuma hankali shi yana kansu *Deeya* dasuka nufi part din lnna, "a ran shi yake fadi to su kuma yaran nan daga ina suke?... shi kuma wannan saurayin dake tsaye fa gurin wayazo?.. mutumi ne yakatse *Habeeb* daga zancen zucin dayake, dacewa ranka yadad'e gashi inji me girma "gwamna yace" a kawo maka, dasauri *Habeeb* yajuya ya kalli mutumin dayake mika masa envelope, fuska amutse yace mene wannan din?..yace ranka ya dad'e bansani ba yadai ce" yana jiran amsar ka, shuru yayi na dan wani lokaci Sannan yakar 'ba tareda cewa "OK nagode Sannan sukayi sallama da mutumin yanufi motar shi yashiga yatafi. yayinda *Habeeb* yanufi part din shi sai kuma yafasa shiga, yajuyo yanufi gurin da wannan saurayin yake tsaye Wanda zasuyi shekarun daya da *Hafeez*, saurayin yana ganin *Habeeb* yanufa shi yai saurin isa suka hade cikin girma mawa yarusu na yana gaida *Habeeb* amsawa yayi fuska ba annuri yace gurin wa kazo?.., kai tsaye yace gurin yan matan nan nazo da suka shiga part din can yakareshe fadi tareda nuna indasu *Deeya* suka shiga, cikin tsananin mamaki *Habeeb* yace?... *_Afuwan๐Ÿ™ MASOYANA jiya nace zanyi posting amma Allah binufa ba, Sannan kuma gaskiya โ˜น kun rage hannun guri comments so kukara hannu idan ba haka ba kuma, nima fa๐Ÿคท๐Ÿปโ€โ™€ zan rage hannu gurin rubutu โœ๐Ÿฝkun san dama typing is not easy ๐Ÿ˜”._* Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [7/2, 11:47 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 2โƒฃ4โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ Gurin "yan'matan can fa kace" kazo?..cikin washe baki yace "eh ranka yadad'e gurun su nazo, fuska *Habeeb* ya daure tareda cewa wanene yabaka izinin zuwa gurin su?.. yace ah! yallabai ba wanda yabani izini, yace "OK wato kai kaba kanka izinin kenan?.. Cikin dan jin kunya domin har yana dukar da kai tareda sosa keya, yace "eh ranka yadade nine naba kaina saboda acikin su" naga wacce tayi mun shine n..., yakasa karasawa saka makon wani uban tsawa da *Habeeb* yadoka masa cikin bacin rai, yace wato shine ka tsayar dasu akan titi har ka dauko su" acikin motar ka ko?..cikin tsoro yace "a ah yallabai bani nadauko su" ba nadai biyo su" ne kawai, yace saboda kana stupid ko?..shin kaga sunyi kama da irin yan' matan da ake tsayarwa atiti ne?.. dasauri yace a ah yallabai, yace "OK wato kune irin samarin nan dasuke bata tarbiyyar yan mata ko?..Cikin tsoro yace wlhy yallabai bani daga cikin su" tsaki *Habeeb* yayi tareda cewa to shiga motar ka katafi, cikin sanyi murya yace yallabai inason guda daga cikin su" cikin ya tsawa yace wai bakaji abunda nace bane?.. cikn sanyi murya yace naji yallabai, yace to oya ja motar ka tafi kuma kar na sake ganin kafarka anan gidan domin bazaka samu ko guda acikin su" ba saboda ariga anyi masu" miji, cikin sanyi murya yace to jiki bakwari yanufi motar shi yashiga saida *Habeeb* yaga fitarshi daga harabar gidan Sannan yanufi part din lnna. su *Deeya* kam suna shiga dakinsu suka nufa bayan sun cire hijab sai suka zaune tsakiyar kyaututtukan dasuka samu, sai turesu sukeyi suna neman kyautar da *Harees* yabata kasan cewar shine farko don haka duk sai sauran suka danne shi, can taza kuloshi tareda cewa yeeeee! nagani, dai lokacin da suka jiyo muryar *Habeeb* yana kiran su aida sauri tasaki dan kwalin suka fito falo bashiri, Tsaye suka iske shi rai bace hakan ne yasa su kajin gaba su yafadi har zasuyi magana, sai suka fasa saboda wani uban tsawa daya doka masu wanda yasa su kankame juna saboda tsabar firgita, Sai kuma yabisu da wani mugun kallon dayasa su saurin sakin juna kirjin su kam sai bugawa, yake yayinda *Deeya* ta yamutsa fuske tareda yarfe hannu wa cike da faduwar gaba cikin yanayin tana shagwaba tace kai Hmm *Habeeb* to yanzu kuma me muka yayi?.. dasuri yace Oh! tambaya tama kikeyi ko?..baki ta turo ba tareda tace komai ba, fuska daure yace "OK to shi wannan saurayin; dakuka gayyato dan gidan uban wane?.. ido suka zaro๐Ÿ˜ณ tareda cewa saurayi kuma...yace "eh ko zanyi maku karya ne?... dasuri suka ce "a ah amma dai mu bamu gayyato kowani saurayin ba, tsaki yayi tareda cewa bari kuji nagaya maku duk wacce ta kuskura ta gayyato saurayi cikin gidan nan wlhy sai nayi mummunan saba mata Sannan yajuna yafita. Ajiyar zuciya sukayi a lokaci guda *Feeya* tace kai! amma dai ko wane wannan gabi" shi gaskiya kuma ya cuce mu, *Deeya* tace hmm! kedai bari mugun gabi makuwa hamago kawai, ke kinji yadda zuciya ta ke wani irin mahaukacin beating(bugawa) kuwa, tsaki *Feeya* tayi tace bashi ai sai Allah yasaka mana *Deeya* tace wlhy kuwa, ke muje muduba kyaututtukan mun kinji tace to. lnna ce tafito daga daki kasan cewar duk tanajin abunda yafaru tun shigar *Habeeb* din, kallon su tayi rai adan bace tace ba Allah yasaka maku zakuyi ba, kula zakuyi da kanku idan ba haka ba kuma ku tabka babban kuskure a rayuwar ku musamman ma ke *KYAUTA*, dasuri tace lnna me kuma mukayi?.. hararan ta tayi tareda cewa yanzu ku saboda Allah yau-yau dagama karatun ku har kunfara gayyato samari; dasuri suka ce wlhy lnna mufa bamu gaiyyaci kowani saurayi ba, tace Oho! kudai ku kasani ai kunji dai abunda Hamman ku yafadi sannan tashige daki abunta, Baki *Deeya* ta turo tareda kama hannun *Feeya* tace zamuje muduba kyaututtukan mun. ****** Ahankali suke walwale ripped din da akayima dan karamin kwalin dawa taleda me kalkali, bayan sun wlwale sai *Feeya* tabude kwalin wani irin kamshine yadaki hancin su a lokaci guda sukace Woww! hannun tasa taciro wasu flowers ja da yelo masu asalin kamshi, hancinta kai flowers shakar kamshi tayi tareda lumshe ido tace my sweet *Deeya* this flowers is so Nice tace very nicely ma kuwa, Sannan taciro wasu greeting cards nan suka fara karanta wa, duk nata yata murnan gama karatun ne tareda fatan alkhairi, bayan sun gama karanta wa sai tace thanks my special Hamman sannan ta sake ciro wata farar takarda da aka kulle da janzare, Ahankali ta kwance kullin wani lafiyayye rubutune ya baiyyana wanda akayi shida biro me ruwan zaiba (wato ruwan gwal), yayinda wani irin sanyayye kamshi ke fita daga cikin rubutun gyara zama sukayi zasu fara karantawa cikin harshen turanci ne, (saini kuma nace bari na fassara maku) ๐Ÿ˜œ ahankali suka fara kamar haka.. _*Zuwa ga me Darajata*_ _*Amenci Allah ya tabbata ga ZUCIYAR datake MULKINZUCIYAR Harees Al-mustafa Abban Safeena MIJIN Safeeya Insha'allah, me Darajata kisani dacewa ZUCIYATA tadad'e da kamuwa da SONKI" wanda nasan zakiyi MAMAKIN jin haka ko?.... to karkiyi mamaki domin shi UBANGIJI babu yadda baya tsara lamarin sa, da don haka kisani ZUCIYATA na matukar KAUNARKI inafata kema zaki SONI?...koda kwatan yadda nake SOKI ne, Ki huta me Darajataaaa! inajiran AMSAR KI Bissalam daga me KAUNAR KI Harees Al-mustafa me fatan ki zama mallakin sa yazama mallakin ki.*_ Suna gama karantawa suka saki wani irin ihun murna tareda kankame juna suna dariya, dasauri lnna ce tale kosu tana cewa ku kuma lafiya kukeyi ma mutane ihu haka, dariya sukayi tareda cewa lafiya lau lnna muna duba kyaututtukan damu kasa mune, tace shine kukeyi ma mutane wannan ihun?.. Dariya sukayi tareda kashewa juna ido, tsaki lnna tayi tace Allah ya shirya ku sannan tajuya tashige daki. Dasauri *Deeya* tace ni dama nasan Hmm *"Harees* SON KI yake, kema aina san kina SON SHI ko?.. *Feeya* tace hmm sosai ma, tace yauwa to dauko biro da takarda kibashi amsa, tace to tareda mikewa tadauko acikin jakar makarantar ta tace sweet *Deeya* idan na rubuta beyi dai-dai baki fada mu kinji?.., tace to sannan tara rubutawa kamar haka. _Zuga yayana na musamman_ Amincin Allah yatabba taga my Husband to be (mijina Insha'allah), sai ta kalli *Deeya* tace yayi ko nasake?..tace yayi ki cigaba, tace "OK tareda cigaba da rubutawa inda tarubuta mashi ta amince sannan kuma taba shi hakuri nabunda yafaru a school sannan ta nade taba *Deeya* tareda cewa idan yashigo ki bashi tace to, sannan suka cigaba dasu sauran kyaututtukan. ****** *Habeeb* kam yana fita direct part dinshi yanufa *Jana* na zaune afalon kasa wanda tuni tamayar shi gurin zaman ta, tun bayan dawowar ta daga yawon tazubar dinta take aikin danna waya, Dakin shi yanufa ba tareda ya kalli inda take ba yana shiga ya wurga envelope din saman gado, sannan yahau kwanfuta ya cigaba da aikin sa wanda dama shi yake yi akai mashi sallama yafita, bai sauka daga kan kwanfutar ba saida akakira sallar magrib sannan yatashi, yashiga toilet ya dauro alwala yafito zaya nufi masallaci. Still *Jana* tana nan zaune harara ya watsa mata tareda cewa kitashi kije kiyi sallah ko yanzu nan nachanja ma wayar nan kamanni, tasan zaya iya domin waya ta uku kenan daya fasa mata tana siyan wata, don haka dasauri tamike tanufi sama tsaki yayi tareda fita abun shi. ****** Su *Deeya* kam suna gama wa suka fita suka

Chapter 9 of 42