Afalo ajiye basket din sannan yanufi bedroom dasauri ya karasa bakin bed din murmushi yayi ganin har tayi bacci, gyara mata kwanciya yayi tareda fadin kiyi bacci kin lafiya me dadi tareda mafarkin Hmm dinki, inason ki *Leemah* ta irin son da baki bazaya iya fada ba, inama ki fatan tashi cikin amincin Allah *Leemah* ta sannan yai mata kiss agoshi da baki sannan yafita yanufi part din *Harees*.
*****
*Jana* kam kuka take sosai kamar ranta zaya fita hankalin ta yai mummunan tashi, domin dai ko kad'an batayi zaton cewar *Habeeb* yagansu ita da Ado lokacin da suke aikata fasikancin su ba,
Cikin kuka tace nashiga uku na tayaya zanbar wannan daular?..
*Jana* kam duk tabirkice sai surutu take saki kamar mahaukaciya sabon kamu, can tamike zumbur kamar zararriya tafita part din su Hajiyarmu ta nufa.
Bako sallama *Jana* tafada falon tamkar mahaukaciya, tazube gaban Abba da Hajiyarmu dasuke zaune suna fira, cikin tsanani kuka tace Abba Hajiyarmu kunga banyima *"BB* na komai ba yasakeni cike da tashin hankali Abba yace subhalallahi! Saki kuma?...
Kai ta gyada alamar "eh cike da bacin rai yace haka kawai "yasakeki ba tareda kinyi masa mummunan laifi ba?. tace "eh yace to yanzu shi Na ALLAH yana ina?... tace "yana part na baro shi, Waya Abba ya daga yafara kiran layin shi amma akashe hakan ne yasake bata wa Abban rai sosai,
Itakam Hajiyarmu ba tace komai ba amma aran tafadi take yau takai shibango kenan, rai bace Abba yakalli Hajiya yace ki kira mun Laraba tace to tareda tashi tanufi sama,
Can sai ga su tareda Laraba Abba yace jeki ki kira mun Na Allah yazo yanzu nan inason ganin shi, tace to tareda fita.
*Habeeb* kam rai bace yashiga part dinsu *Harees* afalo ya iskesu zaune *Harees* yanayin abinci shima bai dade dawowa daga office ba, gani *Habeeb* din ne rai bace yasashi tashi daga cin abinci cike da mamakin ganin sa yace ah kaine yau?..yafadi tareda kama hannun *Habeeb* suka nufi dakin sa.
Zaunar *Harees* yayi sannan yadauko ruwa me sanyi yabashi yasha sannan, yadafa kafad'arsa tareda cewa Dan'uwa meke FARUWA?..wata iska me zafi *Habeeb* sannan yafada wa *Harees* abinda yafaru tsanani sa da *Jana*, in daya karasa she dacewa kasan Allah Dan'uwa yau sai naji ni sakayau kamar ansauke mun wani katon dutse daya dan ne mun kirjina,
*Harees* yace dama haka jakaji musamman da yakasan ce *Janar* ba macen kwarai bace, to Allah ya kiyaye ya kuma shiryar da'ita.
Yanzu Ina "yaran?..tsaki *Habeeb* yayi yace yara kam su nan kasa ita Lili tuni na damka wa "Hajiyarmu, shidai Junior ne dama yake gurin "ta shekaran jiya kuma damu kai waya da *"Leemah* ta take fadamun wai dasu "Walid sukazo gaida su Hajiyar mu sai suka bisu gidan su" har da Lilin shine Mamu tace abar su, su kwana biyu.
*Harees* yace to shikenan Allah yarayasu yace ameen, sannan suka fito saida yakai shi har bakin get sannan yakoma shi kuma yanufi gida.
Zaya shiga part dinsa kenan saiga Laraba tafito daga part din, cikin girmama wa tace yallabai "Alh yana kiran ka yace OK tareda nufar part din, DA sallama yashiga falon Hajiyarmu Ce ta amsa,
Abba kam wani irin kallo ya watsama sa ba tareda yabari *Habeeb* ya zauna ba rai bace yace, Na ALLAH lafiya zaka saki matarka ba tareda tayi maka laifin komai ba, cike da mamaki yajuya ya kalli *Jana* wacce ke tafaman gunshaki kuka kamar ance uwarta da uban ta sun mutu, zama yayi ba tareda yace komai ba saidai ransa abace yake, cikin dan tsawa Abba yace dakaifa nake?..
Rai bace yace ita tace ba tayi mun laifi ba na sake ta?.. Abba yace "eh ba haka kikace?..ciki kuka tace "eh, Kai *Habeeb* ya girgiza yace ashe zaki iyakin fadin laifin daki kai mun?..
Sannan ya kalli Abba yace tunda har takasa fadin laifi datayi mun, to nima nayi mata wannan alfarman bazan fada ba saidai Abba kasani mummunan laifi *Jana* ta yi mun shiyasa na sake ta, Abba yace to kayi hakuri kamai da matarka dakinta,
Yace Abba ai babu sauran zama tsakanin mu, da sauri Abba yace saki nawa kai mata kai tsaye *Habeeb* yace Uku Cike DA tashi hankali yace...
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenart๐น
[7/13, 4:24 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
6โฃ4โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Subhalallahi! Na ALLAH ba kada hankali ne da zakaiwa matar ka saki uku alokaci daya?... sakin da Ubangijin mu yahane mu, shine zakayi, Na ALLAH yau me yasamu kwakwalwar ka shin ka manta na gargard'eka da aikata irin wannan sakin ba tareda wani mummunan laifi ba?...,
Da sauri yace Abba kagafar ce ni; tabbas nasan ka gargad'eni da irin wannan sakin, saidai wlhy laifin da *Jana* tayi mu banajin zan iya cigaba da zama da'ita shiyasa nasake ta domin laifine me matukar muni. Abba yace Na ALLAH duk laifi da Murjanatu tayi maka be kamata kayi mata irin wannan sakin ba har uku alokaci daya, Da sauri yace Abba ba'a lokaci daya nayi mata ba,
Dama nayi mata saki biyu saina barta tayi iddarta kamar yadda addini ce, sannan nace mata duk ranan da tasake taka bakin get ba tareda izini naba, to zan yanke sauran igiyar dake tsakanin mu shine yau Ina shigowa *Jana* tana dawowa daga yawonta wanda tafita ba tareda ta nemi izinina ba ko dayake aidama tasaba yin haka,
To amma tunda nace karta fita shin Abba meka mata tayi?..cikin sanyi jiki Abba yace saita tsaya inda ka'ajiyeta, yace to batayi hakan ba gaka aishikenan yanzu babu wani sauran zama tsakanin mu tunda tafita kaga saki yacika uku kenan ko?...Abba yace haka ne lallai Murjanatu baki kyauta ba, kinga yanzu aure yabaci koda yake Ina zuwa.
Wayarsa yadaga yakira layin Baffa inda yace yazo yanason ganin sa aikam, batareda bata lokaci ba saiga Baffa ya shigo da slm bayan sun gaisa sai ya zauna, sai Abba yafada masa abinda yafaru da sauri Baffa yace subhalallahi! meyai zafi haka *Habeebullah?..*
nan yafada masa kamar yadda yafawa Abba, Baffa yace assha Murjanatu baki kyau taba, Abba yakalli Baffa tareda cewa to lallai dai kam yah sheikh aure yakare kenan KO?...
Murmushi Baffa yayi yace Alh aikaima kasan hakan Abba yace nasani inadai son suma su sake sanin hakan daga bakin Shehin malami ne, Murmushi Baffa yasake yi tareda cewa almajiri dai Alh, to maganar gaske kuma a addini babu sauran aure tsakanin su hakan kuma baiyi dadi ba, Abba yace to yaza'ayi Allah ya kaddara saidai akiyayi gaba
Allah kuma yakiyaye Hajiya tace to ameen nan dai Baffa yayi tayima *Jana* nasiha ganin yadda take ta kuka kamar ranta zaya fita, wanda yasan tana kukan rabuwa ne da *Habeeb* din yace kiyi hakuri Murjanatu inason ki dauki wannan din a matsayin kaddaran ki, kije ki nutsu ki gama iddarki idan harki kayi yadda addinin mu yace' Insha'allah Allah yaza zaba maki miji kwatankwaci *Habeebullah,*
Cikin kuka tace to tunda Lili tana gurin Hajiya abata "Junior ta tafi dashi, har *Habeeb* zayayi magana sai Baffa ya hanashi ta hanyar daga masa hannu, yace Murjanatu kiyi haku kinsa kyanda gidan ubansa don haka kibar Muhammad agidansu, keda kiyi masu adda'a Allah yashira su a tafarkin lslama kinji ko?..kaita gyada, hakan nan dai *Jana* tafito,
tanufi part dinsu ta hada kayanta tasaka cikin motar ta tanufi gidan su, badan ranta yaso barin gidan *Habeeb*
ba.
Bayan fitarta sai Abban yace da *Habeeb* yason duk abinda ya mallakawa *"Jana* karya karba komai, sannan karya dai nayi ma iyayen ta alkhairin daya saba kodan albarkacin zuri'ar dake tsakanin su, yace Abba aibazan karbi komai ba alkhari kuma Insha'allah bazan fasaba, yara daine datake tunanin abata bazan bata ba.
Abban yace to shikenan yara kam dama baza'a bata ba, Allah yai maka yakuma shirya su sukace ameen sannan *Habeeb* yafito ransa wasai yanufi part din sa, yayinda yakeji wani irin dadi yana ratsashi musamman da Abba bai dauki lamarin dazafi ba.
****
Direct bedroom dinsa yanufa yana shiga ya'iske *Deeya* tana gyara kwanciya tareda Jan bargo tana sake tarufe jikinta, murmushi yayi tareda kallon agogon dake manne da bangon dakin wanda yanuna karfe hudu saura, ahankali yakara sa bakin gadon ya tsaya kuri yaimata da ido yana kallon baby fice dinta tareda cute pink mouth dinta, Wani irin sonta yakeji na musamman yana ratsa jini da jijiyoyin jikinsa.
Mamaki ne yaka masa ganin ga ac kunne amma sai gumi take, Hannun yasa yanajan bargon zuwa kasa yayinda ita kuma take jasan zuwa sama, murmushi yake ganin yadda take jasosai kamar zatayi kuka alamar dai adaina jan bargon, dariya yayi tareda fadin am sorry *Leemah* lokacin sallah yayi _so wake up my sweet Dear_ tareda sake Jan bargon da d'ankarfi,
itama taja dakarfi cike magagin bacci me had'e da tsoro tace pls my sweet *Feeya* ki bari naboye kinga tabiyoni zata caka mun wuka ko?... Ido yazo tareda fadin _what?.._ *Leemah* ta wanene yake kokarin caka maki wuka?...dasauri yahauwa kan gadon ya dagota yana fadin *Leemah* ta, dai-dai lokacin data saki wani irin razanannen kara tareda bude ido,
Dasaurin ta rungume shi yayinda jikinta yadauki karrrrrrrrrma! bakinta narawa tafara karanto Addu'a, yayinda jikinta yake fitarda wani irin gumi sai kace babu a c adakin sai kuma tasaki kuka tareda sake kwakume shi still jikinta naci gabada karrrrrrama.
Shikam *Habeeb* wani irin bugawa kirjinsa yakeyi gawani azababben tsoro dayaji yadarsu masa jin abinda *Deeya* take fadi acikin bacci ceke tsoro yake tambayar kansa wane yake son caka mata wuka?...
kirjinsa ne yasake bugawa dakarfi hakan ne yasake sa shi rungume ta ajikinsa tamkar zaya mayar ita cikin jikinsa, yana fitarda Wani irin numfashi me cike da fargaba, dakyar yasamu bakinsa yabud'e yafara karan tama ta addu'ar ne mantsari daga mummunan mafarki domin ya tambar dashi *Leemarsa* tayi.
Ahankali yacigaba da yimata addu'ar tareda hura mata iska akunne yana kuma shafa bayanta, har tayi shuru sai kuma sannu ahankali nutsun take ratsa sassan jikinsu.
Ahankali ya dagota kanta yahade bakin su tsawon wani lokaci sannan yacire bakinsa daga nata, cikin sarkakkiyar murya yace *Leemah* ta cikin shsheka tace na'am, yace wanene ki kai mafarki dashi zaya caka maki wuka?..tace "Aunty *Jana* ce pls Hmm na, ni dai don Allah kamai da "Aunty *Jana* daya daga cikin gidajenka kaga sainayi ta mafarki da'ita" tana bina da wuka zata caka mu,
KO yanzu ma ita Ce ta biyoni da wuka zata caka mun saika riketa", nidai inajin tsoro kar wata rana ba kowa tayi mun illa kaga haka ranan daka tafi.... Nan tafada masa abinda yafaru har da marin bata boye masaba,
Ajiyar zuciya yayi tareda sake rungumeta yace kwantar da hankalin ki *Leemah* ta, *"Jana* bata isatayi maki abinda Allah bai makiba yanzu haka tsakanin muda *Jana* saidai zumunci, koshima albarkacin yaranta in badan haka ba ko zumunci bazamuyi da'itaba domin itadin bata cikin tsarin mutanan da zamu yi zumunci dasu.
Dasauri tadago ta kalle sa cikin rashin fahimta tace Hmm na banga ne ba?..murmushi yayi tareda gyara mata kashin kanta da yabar baje, sanna yace *Leemah* ta basaki *Jana* yau, ido tazaro cike da tsoro tace me tayi maka?... yace komai ma nan yafada mata abinda yafaru, saidai bai fada mata maganar kamata dayayi da Ado ba.
A gaskiya ba taji dadin rabuwar su ba kodan su Lili to saidai kuma haka Allah yatsara Allah yaraya su,
yace tashi muje muyi sallah sai mu ci abinci kai tadafa tareda cewa kashhh!, am so sorry Hmm na yaufa banda fa komai ba, amma bari nayi alla sai nadafa maka simply food b4 nayi maka special dinner KO?..
takareshe fadi tana murmushi tareda shafa lallusan sajensa, cike da kaunar ta yace yes my Honey amma karki damu dawanda zan ci yanzu already Hajiyarmu tabayar ankawo mun, namanta ma dazu nafada maki da nashiga tace wai yau tun safe da kika shigaku ka gaisa bata sake ganinki ba, takira wayar ki baije ba kuma taji lokacin dakika dawo, amma kuma baki shigo ba ko lafiya?..
Da har zata turo Laraba tadubo ki sai gani. tace Humm! ai tunda nayita kiran layukan ka baije ba sa haushi yasa na kashe wayata Sannan tsabar kewar ka, yasa dana dawo banshiga part din kowa ba na nufo dakin ka ko naji sauki,
Murmushi yayi cike da kaunar ta yace humm! *Leemah* ta nima tsabar kewar ki ce tasana baro abj tamkar mahaukaci, saida nazo kika tashayar dani daddad'ar zumarki sannan naji sauki.
murmushi tayi cike dajin kunya take kokarin tashi dasauri ya mai da'ita jikinsa tareda yimata rad'a akunne, dariya tayi tareda dan dukan sa kad'an akirjinsa tace Kai! Hmm na again?..
Shima dariya yayi tareda daukar ta yana fadi "eh KO" bazaki bani ba?.. tace zan baka mana Hmm na aini din ta kace KO?.. cike da shaukin kaunar ta yace yes nikad'ai ma kuwa baby na shi yasa nake Kara SONKI tace nima haka, toilet suka shiga saida yajirata tasakeyin wanka saboda gumin datayi, sannan suka dauro alwala suka fito shi yanufi masallaci ita kuma tayi anan dakin sa.
bayan ta'idar sai ta'isa gaban mirror tayi kwalliya sannan tasa wata roba gown ja wacce ta kamata sama da kasa gaba daya shape dinta yafito sosai, bayan takama gashin kanta tadaure dawani jan ribbon sai ta daura wani bakin bandana me ratsin ja tagefe,
Sannan tafeshe jikinta da turaruka masu kamshi gaskiya tayi kyau sosai, sannan ta nufi falo dai-dai lokacin da *Habeeb* ya shigo.
Dasauri ya'isa gareta cike da farin ciki ya sureta yafara zagaye falon da'ita, suna dariya sannan ya zauna
tareda zaunar da'ita akan cinyar sa kallon ta yake cike da so da kauna, yace kai! *Leemah* ta zaki kasheni da gayunki fa fari tayi masa wanda yasake rikitasa,
Sannan tace Hmm na nayi kyau?..yace kin gani ko *Leemah* ta shiyasa nace zaki kasheni da gayunki, dariya tayi tareda fada wa kirjinta cikin salon shagwabar ta, tad'an dukesa akafadar sa tace kai! Hmm na idan nakashe ka to na rayudawa?.. rungumeta yayi yana dariya yace *Leemah* ta kinyi kyau sosai gayunki yana tsumani har naji kamar zan shide don farin ciki,
Pls ki cigaba dayi mun inason shi
kinji?.tace Insha'allah I will do it just only for my Hmm ta kareshe fadi tana shafa lallusan sajensa, idon sa lumshe yace thanks so much my honey *Leemah*,
tace don't thanks me aikina ne nafaranta maka, tashi muje ma kaci abinci yace to tareda mikewa da'ita rungume ajikinsa suka nufi gurin abinci, bayan sun zauna sannan tafara bubbude kulolin.
********
Aban garen *Jana* kam tana tuki tana kuka har ta'isa gida, da ihu tashiga cikin gidan wanda yasa mahaifiyar ta Dije "KO nace Hajiya Dije tunda tuni *Habeeb* yakai su makka,
Tafito daga daki dasauri ganin *Jana* ce yasa taji faduwar gaba, domin rabon da taganta har ta manta rana kasan cewar bata zuwa gidan,
_nikam nace shashasha kawai aigashi yanzu kin zo dole,_
Dasauri tace keee! lafiya?.. zaki shigo mana gida da ihu, cikin kuka tace Dije *"BB* yasake ni saki uku wani uban zaman dirshan Deja tayi a bakin kofa tareda fadin shikenan, Dai-dai lokacin da Baban ta yafito d'aki zaya tafi masallaci,
Wani irin mugun kallo yawatsa wa *Janar* kasan cewar duk yaji abinda suke fadi, gadan-gadan yanufe ta ransa bace wanda hakan yasa taji mugun faduwar gaba, domin tunda take bata taba ganin shi haka ba dasauri taja baya cike da tsoro, wani irin tsawa yadoka mata cikin azababben bacin rai yace....
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE*_ (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenart๐นc[11/9, 9:38 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
6โฃ0โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
*Leemah* ta wai me yafaru ne?..Cikin kuka tace to bakai bane kayi tunanin Zan aikata ZINA da aure akai na ba,
Dakarfi yace no! *Leemah* ta banyi tunanin haka daga gareki ba yafadi yana kokari janta zuwa jikinsa.
Da sauri ta matsa cike dajin haushi tace karka tabani kaji ko?.. ido yazaro cike da tsoro yace wa _what?.._ *Leemah* ta Karna tab'a kifa kikace?.. tace "eh kuma aikayi tunani tunda har kace karna aikata wannan abin da mukayi kai da wani d'a namiji, wanda ni sai yanzu ma na tuna ansha fada mana a islamiyya cewa wannan abun mata da mijine kad'ai Allah ya halasta suyi shi, idan ba mata da mijiba to duk wayanda zasuyi shi to zina ce haka ne ko?..
Da sauri yace "eh *Leemah* ta.
Ta cigaba da cewa sannan kace wasu "matan auren sunayin zina da auren su", ko?.. Da sauri yace wlhy *Leemah* ta sosai wasu "matan auren suke aikata zina da auren su,
Wani kuka ne yasake kwace mata me cike da tsan-tsan bacin rai, tace shine kayi tunani nima Ina daya daga cikin su ko?...Hmm na shin ka matan illolin da ke tattare da zina ne?... tareda azabobin da Allah yata nadarwa masu aikata zini?...da sauri yace "a ah ban manta ba, tace shine kake alakan tani da ita?..
yace "a ah *Leemah* ta wlhy ban alakantaki da'ita ba, tace kayi don haka baruwa na dakai, ta kareshe fadi tareda kokarin sauka daga gadon yayinda hawaye ke bin kumatun ta sosai.
Cike da tashin hankali yajata jikinsa ya rungume ta tareda cewa "a ah, *Leemah* ta karkice haka nan wlhy ban fadi hakan da wata manufa ba to tayaya maza'ayi na alakanta *Leemah* ta, da wannan mugun abun ZINA fa... haba *Leemah* ta..
Cikin kuka tareda kokarin kwace kanta daga karesa tace kace!" kace!! kace!!! kuma kasan Allah yace" _Latakrabul zina kada ku kusanci zina,_ shiyasa natsani ZINA arayuwata kullun nake rokon Allah yatsari da aikata ta, nake kuma rokon Allah yashirya masu aikata ta, Dasauri yace wlhy *Leemah* ta nima matsani ZINA arayuwata tร ce amma shine yau da kanka kร ke alakantani da'ita KO?...ta kareshe fadi cike da matsanancin kuka.
gaba daya fa *Deeya* tabirkicewa *Habeeb,* sosai take kuka tareda son kwace kanta daga gareshi amma ina takasa hakan saboda yariketa sosai, yayinda hankali shi idan yakai miliyan to duk sun tashi musamman kukan ta dayake taba masa zuciya,
Cike da tashin hankali yace to Don Allah *Leemah* ta kidaina kukan nan haka wlhy yana taba zuciyata sosai, bata saurare shiba itadai burinta kawai ya kyaleta tafita daga dakin domin wani irin haushin sa takeji.
"Ganin taki sauraren shine yasashi had'de bakin su guri daya, sosai take kokarin kwace kanta amma takasa domin sosai yake shan bakinta, yayinda hannun shi daya yake rikeda ita gam dayan kuma yake shafa bayanta alamar lallashi, tun *Deeya* tana kucekucen kwace kanta harta gaji tabari karshema saita fara mayar masada martani,
Wanda hakan ne yabashi damar sakin asirtatcen ajiyar zuciya, tareda sake janta jikinsa ya rungume ta sosai yayinda yacigaba da shan bakinta cikin wani irin yanayi me cike da zallar kaunar ta, tsawon wani lokaci suka dauka itace fara tacire bakinta daga nashi tana sauke ajiyar zuciya tareda turo bakin.
Numfashi yasauke akasalce sannan yace *Leemah* ta don girman Allah kiyi hakuri, wlhy ban fadi hakan danufin b'ata maki RAI ba, sai don tsawatarwa akan wani abuda yafaru wanda idan na tunashi sai naji Wani irin mugun bakinci tareda Wani irin tsoro wanda har nakanji zuciya ta nacewa idan kayi wasa wannan abun zaya iya FARUWA dakai.
Dasauri tace sai kuma akace akaina hakan zaya faru KO?...Da sauri yace no *Leemah* ta Insha'allah hakan baya taba faruwa akan kiba, nan dai yayita lallashin ta hartayi shuru daga karshe ma yaga tana kokarin yin bacci Don haka yace *Leemah* ta muje muyi wanka sai mu zo mu kwanta ko?..
Kai ta gyada masa cak! yadauke ta suka nufi toilet a ranshi yana fadi wai! *Leemah* ta rigima kai irin wannan rikici haka hmmm! kร dร รllah ya maimaita.
_Ni kam nace kai kaji Hmm *Habeeb* din nanfa๐ *Deeya* aikinyi mun dai-dai dakika rikice masa, kinga hakan zaya sake tabbatar masa dacewa aike ba irin *"Jana* bace KO readers.?._
Bayan kwana biyu
*Deeya* taji sauki sosai duk inda takejin yanai mata ciwo yadaina,
Da misalin karfe 11:30pm *Habeeb* ne zaune akaramin falon sa yana aiki akan computer, saidai da alama yagama don naga yana kokarin kulle computer ta,
Sanye yake da wata rigar bacci me bud'and'an gaba, Don har ana hango lallausan suman dake kwance luffff afaffad'an kirjinsa rigar iya guiwa take.
*Deeya* Ce naga tashigo dakin bakinta dauke da slm sanye take da kayan bacci farare irin masu tasushin nan, riga me guntu hannun da wando iya guiwa kanta saye dawata hula me gara, gurin *Habeeb* tanufa kwanta wa tayi a bayan sa tareda tura hannun ta duka biyu acikin kirjin sa ahankali tafara wasa da lallausan suman dake kwance lufff, kirjinsa sannan ta dora kanta akafad'arsa,
Ahankali tafara goga fuskarta asajen sa, cikin cool voice din me dadi wacce ke cike da bacci tace Hmm na sannu da aiki.
Cikin sarkakk'iyar murya yace yauwa *Leemah* ta aina gama dai-dai lokacin da yakarasa kulle computer, yatashi tareda juyota gaban sa yace *Leemah* ta bakiyi bacci ba?... tace "eh yace why?.. baki ta turo tareda cewa to bakai bane kasa bamun da kwanciya anan takareshe fadi tareda d'an dukan sa akirji.
Murmushi yayi me Cike da shaukin kaunar ta yace to am sorry *Leemah* ta, zomuje ki kwanta a nan din dama kuma aikirjin naki ne, dai-dai lokacin da yadagata yana fadin yauwa mujema kiji wani labari me dad'i.
Tsaki yar gado yazaunar da'ita shi kuma yana tsaye sai yace kinaji KO?..Kai ta gyada alamar "eh, yace" wata beautiful Lady ce mijinta zanyi Making Love da'ita, idon tazaro tareda cewa Kai! Hmm na taya akayi to kai kasani?..,
yace hmmm kedai tsaya kiji, dama already shi Mijin yayanta harma tana kiransa Hmm dinta kamar yadda kike kirana, lokacin da zaya fara making Love da'ita kinsan me tace"?.. tace a ah.
Kan gadon yahau yakwanta kansa yana kan filo sannan yace kina kallona?..kaita gyada masa alamar "eh aranta kuma tana fadin toshi Hmm na taya akai yasan abinda yafaru tsakanin mata da miji?..,
ido taga ya lumshe tareda fara jujjuya Kansa akan filon, sai kuma taji yafara fadin wayyo "Inna ta wayyo "Baffa na wayyo Hajiyar mu pls my sweet *Feeya* kuzo kiceceni Hmm *Habeeb* zaya kashe ni, sannan yabud'e idon yana mata dariya me Cike da zolaya.
itakam baki da hanci ta bud'e tana kallon sa cike da mamaki wato da'ita yako?..,aikam dasauri tahaye ruwan cikin sa tareda daukar filo tana dukan shi Cike da shagwaba tace Hmm na Dani kake fa...cikin dariya yace "eh dake nake koba haka kikace ba?. yakareshe fadi tareda kashe mata ido daya.
Baki ta turo sannan tace to aida gaske ne kakusa kashe ni, murmushi tayi tareda rike hannun ta yakarb'e filon datake dukansa dashi yaijifa dashi sannan yace, *Leemah* ta idan na kasheki to narayu dawa?.. tace ah! ga "Aunty *Jana* nan, had'e fuska yayi.
Aaikam dasauri ta waske da fadin Lah! aikai manaji abunda ka fadi ranan cike da zumud'in sonji abinda yafad'a aranan, yace mata me nafad'a *Leemah* ta gaya mun kinji"?..cikin da zolaya tace cewa kayi wayyo *Leemah* ta wayyo my Honey inason ki u are so sweet *Leemah* ta pls don't left me kinji?.. if u left me l will die l will die *Leemah* ta Kuma kanata maimaita wa.
Dariya yake sosai sannan yajawo ta ya rungume sai kuma ya mirginata takoma kasa shi kuma yana saman ta mean yai mata runfa, cike da shaukin kaunar ta yace Allah da gaske ne *Leemah* ta idan kika bar ni mutuwa zanyi domin kaunarki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 42