Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wai ya munafurce ta ya aurar da yar'sa ba tareda saninta ba, sai yace mata ai lokacin daya samu diyar bata sani ba don haka "KO aurar da'ita bai zama dole tasani ba, aiko tace Ina wuta tasa kashi saboda tsabar masifa shidai yace "Oho yarsace kuma ya aurar da'ita ga wanda yakeso. Tunda misalin karfe hudu na asuba lnna Rakiya tadinga bugawa su Yusufa kofa su tashi, koda yabude kofa tana tsaye tana girgiza jiki cikin sanyi murya yace Inna lafiya?..harara ta zuba masa tareda cewa "toh ubana aisai kafito katafi kiyo KO?..da sauri yace haba Inna "KO sallafa ba ayiba tace "eh ainasani, zaya sakeyin magana tace shin zaka fito kosai nacimaka mutunci hakan yafito badan ranshi nasoba, yakora shanu zuwa kiwo, ita kuma lndo tace tafito tayi aikin gida. Dagari ya waye mlm Babuga ya kawoma lndo kayanta tareda masu jera mata, inda lnna Rakiya take ta zuba ruwan masifa da bala'i sudai masu Jere basu tanka ba domin kowa tsoron ta yake bayan sungama sannan suka tafi. Sannu ahankali lnna Rakiya tamaida Yusufa da lndo bayinta, shi wahalar kiyo ita kuma wahalar aikin gida da kuma tallar nono tun karfe hudu take tadasu barci su tatsi nonon shanu da lndo kezuwa talla, bayan sun gama shi yatafi kiyo ga shanun suna da yawa sosai wanda ya kamata ace akwai wani dake tayashi, ga kuma tumaki suma da yawa amma hakanan yake korasu zuwa kiyo. Sannan ita kuma tayi aikin gida bayan tagama sai ta tafi talla, gashi bata basu wani abincin kirki duk sun rame sunyi baki su KO" dan kyan'nan da amarya da ango keyi su basu yi ba, yayinda ita kuma lnna Larai tazo taimasu rashin mutunci ta tafi. ******** A haka rayuwa tamika shekaru sunja don alokacin shekaran su biyar dayin aure, kuma alokacin tuni mlm Babuga yadade da rasuwa saka makon rashin lafiya dayayi Na tsawon shekara biyu, shiyasa suka sake shiga cikin kunci tunda dama shike taimaka masu dayan wasu abubuwa, kuma har wannan lokacin lndo ko batan wata bata tabayi ba domin lnna Rakiya tasha tace masu suda haihuwa saidai sugani anayi amma badaisu suyi ba, gori da habaici kuwa kusan kullum yimasu take musamman idan jikokinta sunzo wato ya'yansu Lanti, ba dama lndo tayi masu magana idan sunyi marna saita lnna Rakiya hautada masifa da ba'ai. Da abin bai damu lndo ba amma gani lokaci yaja bata haihu ba, sai abin yafara damunta ita kuma tafara damun Yusufa, Saidai yace mata kiyi hakuri lndo kibar damuwa da'abunda lnna Rakiya take fadin akan mu, tabbas nasan inda lnna Rakiya ke bada haihuwa toh saidai muyi hakuri domin nasan bazata taba bamu ba, "toh sai kuma akayi sa'a ba'ita ke bayarwa ba Allah ke bayarwa don haka kisa aranki muma wata rana Allah yaza bamu kinji?..sai tace "toh. haka rayuwa ta tafi ranan wata laraba cikin dare misalin karfe uku sai yusufa yatashi yayi sallah kamar yadda malamin sa yakoyar dashi, bayan ya'idar sai ya zauna yana kuka wanda sautin kukansa ne yatada lndo daga barci cikin sanyi murya ta tambaye shi lafiya yake kuka?.. yace mata yatuna iyayansa ne saitace "toh kayi masu addu'a mana yace nayi masu" sannan ina kuka ne akan irin wahalar da Inna take baki, nikam nariga nasaba amma kefa?..tace nima yanzu nasa ba yace hakane saidai nikuma hakuri na yagaza akan wahalar datake baki, don haka kitashi kihada mana kayan mu mubar kauyan gudun fulani, wadda tazamo mahaifarmu saidai kuma yau zamu barta kuma bari na har'abada domin banajin zamu dawo kauyan nan, tace "toh yanzu Ina zamuje?.. yace kar kidamu Allah yasani kedai tashi kihada mana kayan mu, tace "toh tareda tashi ta hada kayan ta kullesu adan kwalinta, dama ba komai dakin sai katifar su kasan cewar lnna Larai da Inna Rakiya duk sun kwashe kayan, don haka kayan sawarsu kawai suka dauka suka fita abinsu ba tareda lnna Rakiya tasani ba. Sai kusan asuba suka isa cikin garin Bauchi lokacin anata kiraye-kirayen sallah, wata anguwa mai kyau suka fada akofar wani gida mai kyan gaske suka tsugun'na suna huta gajiyar tafiyar dasuka yi domin ba karamin tafiya sukayi ba, basu dade da tsugun'nawa ba sai gawani kyakkyawan mutun managarci yafito daga wannan gidan tareda wani d'an kyakkyawan saurayi, bakowa bane wannan mutumin face. Alh Hashim soro bayan shi kuma *Habeeb* ne alokacin duk baifi shekara goma sha biyu zuwa sha uku ba, da'alama masallaci zasuje. har zasu wuce su domin shi Alh Hashim soro Sam ba kula da mutane agurin ba, *Habeeb* ne yagansu yace Abba kaga wasu mutane anan, da sauri Abba yajuya aikam sai yaga mutane rakube jikin bango. ahankali ya karasa kusada su yace bayin lafiya daga Ina kuke da'asubar fari haka?..Yusufa ne cikin gur'batacciyar hausarshi domin bawai ya'iyata sosai bane, yace Alh mu baki ne daga kauyen gudum fulani muke fito, yace Allah sarki sannun ku da hanya, yace yauwa Alh sannu yace "toh meke tafeda Ku?..yace Alh Labarin mu yanada tsawo, Abba yace Allah sarki zanso naji labarin ku "toh amma yanzu lokacin sallah ya gabato, don haka kazo muje muyi sallah idan mundawo sai mushiga gida matarka tayi sallah kai kuma saika bani Labarin ku KO?.. Yakarashe fadi fuskarta daukeda murmushi, shima yusufa murmushi yai tareda cewa "toh Alh mungode, sai Yusufa ya kalli lndo cikin harshen fullanci yace mata tafa zauna karta Kara matsawa ko'ina, tace "toh amma tanajin tsoro Yusufa zayai magana sai Abba yai sauri cikin harshen fullanci yace karki damu babu abinda zaya same ki insha'allahu, cikin matsanancin mamaki Yusufa yace.... Muje zuwa A _*KYAUTAR ALLAH CE*_(Labarin Sadeeya) Tareda Alkalamin โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนLufhat๐ŸŒน [7/2, 11:27 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 7โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* _*ASSALAMU'ALAIKUM YAN'UWANA KUMA MASOYANA, DAFATAN KUNA CIKIN KOSHIN LAFIYA TAREDA IYALANKU ALLAH YASA HAKA AMEEN, MASOYA ALHAMDULILLAHI ANYIMUN OPERATION LAFIYA ANCIRE MUN CIWON DAKE DAMUNA, YANZU HAKA NASAMU SAUKI SOSAI WANDA HAR ALLAH YABANI IKON MIKA GODIYA TA AGAREKU AKAN IRIN ADDU'O'IN, DA KUKAITA KWARARA MUN, GASKIYA MASOYA SUNA DA MATUKAR DADI๐Ÿ’ƒ๐Ÿฟ KAI! NI AMEENA UMAR FARUQ NAGA RUWAN MASOYA, KIRA AWAYA NE, TEXT NE ZUWA ASIBITI NE ZUWA GIDA NE KAI! BABU WANDA BANGANI BA, DON HAKA NAGODE KWARAI DA KULA WARKU AGARENI ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI YABAR KAUNA DA ZUMUNCI MAI DOREWA, YAKUMA KARA MANA LAFIYA DA IMANI AMEEN.๐Ÿ‘YAH ALLAH๐Ÿ‘ INASAKE ROKONKA KA KARA BANI LAFIYA TARE DA DUKKAN WAYAN DABASU DA' LAFIYA WAYAN DA KUMA SUKE DA LAFIYAR ALLAH KA KARAMASU LAFIYA MAI INGANCI ALFARMAN ANNABIN RAHMA AMEEN YAH RABBI.*_๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘ ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirrahim*!_ Yace Alh ko kaima dai fulfulde ne?..murmushi Abba yayi tareda cewa tabbas nima bafullace ne gaba da baya, daga kauyan soro nazo neman ilimi sa kuma Allah ya kaddara mun nayi zama na acikin birni, saidai ina zuwa soro. cike da farin ciki Yusufa yace Allah nagode maka daka hadani da d'an'uwana bafullace. murmushi Abba yayi tareda cewa ya sunan mlm din?..yace sunana Yusufa matata lndo Abba yace Allah sarki toh mlm Yusufa muje muyi sallah idan mun dawo saika bani Labarin ka" nima saina baka labairna KO?..yace toh Alh sannan suka nufi masallaci. _Assalamu'alaikum_ Abba yai sallama acikin kayatattace falon nasu, yayinda Hajiya Rabi'atu ta amsa da _wa'alaikassamu_ dai-dai lokacin da tamike, Ahankali take ninke abun sallah bayan ta kuma kyawawan yan' mata ne guda biyu yayinda yar karamar ke ninke abun sallah wacce shekarunta bai wuce shida ba, bakowa bace illa "Adda Rahma wacce ayanzu haka tana zaune a Tambari estate da mijinta babban soja da yaranta hudu mata biyu maza biyu Walida da Salma sai Salim da Walid, sai kuma babbar yar shekara takwas bakowa bace ita illa Maryam wato Adda mamu yanzu haka itama tana zaune a G R A da mijinta wanda yake babban alkali ne, da yaranta biyar maza biyu Hassan DA Hussain sai mata uku Husna Hafiza da Adawiyya sai tsohon ciki datake daukeda shi. Hajiya tace kun dawo?.. Abba yace eh" muntashi lafiya tace lafiya lau *Habeeb* ma yace mun tashi lafiya tace lafiya lau, mamu ta matsa kusa da Abba tsugun na tareda cewa antashi Abba, kanta yadafa tareda cewa lafiya lau uwata. sannan tace *Hamman Habeeb* antashi lafiya?.. yace lafiya itama Rahma ta tsugun Na ta gaida Abba da *Habeeb* bayan ya amsa sai yace ku dauko Qur'ani muje afada mana karatu kafin lokacin makaranta yayi sukace toh" tareda nufar hanyar daki. Zama Abba yayi adaya daga cikin kushin din falon yana cewa a ah *Na ALLAH* Ina kuma mutanan nan suka tsaya?..(kasan cewar Haka yake kiran *Habeeb* din) cikin ladabi *Habeeb* yace Abba ai can waje suka tsaya, yace Allah sarki toh" jekace sushigo mana yace toh" tareda fita. Dai-dai lokacin da Hajiya ta zauna kusa da Abba tana cewa Alh munyi baki ne?..yace "eh nan yafara fada mata abunda yafaru dasuka fita zuwa sallah. *Habeeb* yana gaba suYusufa suna biye dashi abaya, cikin sakin fuska Abba yace a ah mlm Yusufa shine kuma kuka tsaya awaje, baku shigoba?.. Yusufa yace Alh ai malamina yasha fadamun cewa bamu kyau mutun yashiga guri ba tareda anyi masa izini ba, Murmushi Abba yayi tareda cewa mlm Yusufa kenan wannan haka yake, toh" yanzu nabaku izini kushigo ga kuma gurin nan Ku zauna. Zama sukayi yayida Yusufa yake cewa toh" Alh mun gode sannan yace Hajiya wayan nan sune bakin, tace Allah sarki sannun Ku dazuwa sukace yauwa, sannan Abba yace sunan shi mlm Yusufa matar shi kuma lndo da sauri Yusufa yace Alh kanata kirana mlm alhalin kuma nidin Almajirine yafadi cikida ladabi da biyayya, murmushi Abba yayi yace Hajiya kikai ta tayi sallah, tace toh" tareda tashi tana cewa mushiga ciki sai kiyi sallar lndo tace toh" tareda tashi tabi bayan ta. Dai-dai lokacin da su Mamu suka fito hannunu wansu dauke da al'qur'ani *Habeeb* yakarbi nashi sannan suka fita zuwa gurin daukar karatu. Ahankali Abba yamaida kallon sa ga Yusufa Wanda kansa kekasa, sannan yace mlm Yusufa inasan kabani Labarin ka cikin nutsuwa Yusufa yace toh" tareda fadawa Abba komai tun dagakan mutuwar "iyayensa har kawowa Auren sa da "lndo da irin kuntatawar da "Inna Rakiya takeyi masu saida yafada masa. Aciyar zuciya Abba sauke yayinda zuciyar shi tacika da tausayinsu Yusufa, _kasan cewar shi mutun mai matukar tausayi_ don haka sai yaji tsanar "Inna Rakiya ya darsu aransa. cikin bacin rai yace tabbas "Inna Rakiya ta zalinceka ta kuma gwada rashin imani akanka da matarka. kamar yadda kafada mun labarin ka nima bari nabaka Labarin Na, nan dai Abba yafada masa koshi wane inda yakarashe fadi dacewa yanzu haka nid'an majalisa ne kuma nadauki alkawairn zan karewa mutane mutuncin su, haka zalika nasha alwashin duk wanda aka tauye masa hakkin sa insha'allah saina kwato masa abunsa don haka dole "lnna Rakiya ta fusakanci mummunan hukunci akan abunda ta aikai- agareka. Dasauri Yusufa yace a ah Alh akyaleta nikam tuni nayafe mata abunda taimun cikin matsanancin mamaki Abba yace.. _*Washhhh! ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€don Allah kuyi hakuri da wannan wlhy Ina cikin typing din duk sai naji nagaji๐Ÿ˜”, lah๐Ÿ˜€ kilan dan Na kwana biyu banyi bane shiyasa, koda yake dama ai typing dinma is not easy walla am๐Ÿ˜ amma dai karku damu next page zanyi kokari nayi maku read moreeeeeeeeee.๐Ÿ˜€*_ Muje zuwa A _*KYAUTAR ALLAH CE*_(Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนLufhat๐ŸŒน [7/2, 11:27 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 8โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirrahim*_ Kace me?..yace nayafe mata Kai Abba yajinjina sannan yace toh" shi kuma hakkin kafa?..yace Alh wannan kam ban yafe mata ba, domin kuwa Annabinmu ma yace kabi hakkinka saidai idan ba'a baka ba toh" kabar mutun da Allah, Abba kam jiyayi zuciyarsa tacika da kaunar Yusufa haryana fadi aransa tabbas wannan da'alama zayayi rukon amana, cikin sanyi murya Abba yace wanna haka yake. Yusufa yace toh" don haka kaga inada da damar da zanbi hakkina saidai kuma Alh bazan iyaba, da sauri Abba yace saboda me?.. yace bayaga ubangijina bawani dan Adam din danake tsoro aduniya irin lnna Rakiya Alh Ina matukar tsoronta don haka nibazan iya tunkaranta akan tabani hakkina ba, Cikin tsanani tausayin sa Abba yace indan wannan ne karka damu ni Zan karbar maka hakkin ka insha'allahu, yace toh" Alh nagode sosai, saidai don Allah Alh karkace nakoma kauyan nan dan nikam yanzu banajin zan'iya komawa gudun fulani domin naji kauyan yafita araina. Murmushi Abba yayi yace mlm Yusufa kenan bazance ka koma gudun fulani yanzu ba, saidai kuma kasani dole zakaje wata rana domin bukatar zuwan naka zayazo, yace toh" shikenan Alh nagode sannan kuma don Allah ina naiman wani taimako agurin ka, Abba yace mlm Yusufa kafadi bukatar ka indai baifi karfina ba toh" insha'allahu zanyi maka, yace Alh dama sonake kataimaka mun da gurin zama nadan wani lokaci sannan kuma kanema mun dan wani aikin dazan rike iyalina dashi. Abba yace kar kadamu zan taimaka maka Insha'allah yace toh" nagode kwarai Allah yasaka da alkhairi, Abba yace bakomai idan dawata bukatar kafada nikuma zan biya maka ita muddun baifi karfina ba, Yusufa yace "eh toh" akwai saura saidai kuma kar nadora maka nauyi dayawa, dariya Abba yayi yace Mlm Yusufa kenan babu komai, nidai burina nataimaki wanda baya dashi fatana kuma wanda nataimaka shima wata rana yataimaki wani, don haka fadamun menene yaisaura?.. yace "eh toh" dama damuka gama sallah sainaga yawancin mutane sun kewaye liman din kowane da al'qur'ani mai girma harda wasu littafan addini zasu dauki karatu sai abun yaburgeni toh" shine nakeso nima narika zuwa daukar karatun domin burina arayuwa nasamu ilimin Addini mai zurfi. Abba kam ajiyar zuciya yayi domin kuwa gaba daya zuciyar shi tagama yadda da Yusufa mutumin kirkine, don haka yace kar kadamu Insha'allahu zakasamu abunda kakeso. yace toh" nagode sosai, dai-dai lokacin da su Hajiya suka fito itada lndo, Abba yace tayi sallah nan?..Hajiya tace eh yace yauwa toh" akira Kulu takaisu shashin baki suyi wanka su huta idan angama karin kumallo sai akai masu, inafata dai shahin agyare yake?..tace "eh Alh aikasan bamu rabuwa da mutanan arziki don haka koda yaushe cikin gyarashi ake, yace yauwa ai hakan yanada kyau, kai mlm Yusufa tashi muje gurin mlm Liman nafada masa zakaringa zuwa daukan karatu, yace toh" Alh aini yauma zanfara dauka dama da Qu'rani na nake tafe kaganshi nan ma, yafadi yana nunawa Alh qur'ani dake cikin jakar datake rataye akafadarsa yayinda fuskarshi ke dauke da matsanancin farinciki, Murmushi Abba yayi tareda mikewa yana cewa a ah mlm Yusufa bayau zakafara daukar karatun ba, sai Allah yakaimu gobe domin yau sonake Ku huta sosai kaji KO?..yace toh" Alh yadda kace haka za'ayi dai-dai lokacin da suka fita. _*GUDUM FULANI*_ Inna Rakiya kam dama tasaba bata tashi daga barci sai Rana tafito kwal sannan tafito ta bubbuga sallah, cikin masifa ta turo kofar dama haka takeyi tsaye tayi tana mika ba tareda salati ba yayinda hamma yabiyo baya cak! ta tsaya baki hankade sakamakon ganin gida kaca-kaca gakuma shanu d'add'aure, wani uban ashar tayi tareda cewa su wayan nan yan'iska yau me suke nufi?..cike da masifa tanufi dakinsu Yusufa, tana cewa kai isuhu. _domin ita bata kiransa Yusufa_ Dakarfi take bugamasu kofa tana cewa dan'ubanshi yau ba zayakai shanu kiwo ba ne ita kuma Indo bazata fito tayi aikin gida bane?..sanna yau bazataje tallar nonon bane?.. shuru ba amsa don haka dakarfi tasa kafa tabanki kofar aikam sauran kad'an tafadi ๐Ÿ˜‚yayinda kafarta daya tana waje daya kuma tana cikin dakin, dasauri tadafa bakin kofar dakin Wanda yake wayam bakowa sai Yar tabarmar dasuke kwana. _tunda dama tuni sun siyar da kayan dakin sunci abinci_ Cikin matsanancin tsoro tazaro!๐Ÿ˜ณtareda kunduma uban zagi sai kuma tafito cikin masifa take fadin su wayan yan'iskan Ina suka tafi?..ba'amsa dayake ita din masifaffiyace don haka saitafara masifa tareda zage-zage aikam nan da nan aka ciki gidan ana tambayar ta meya faru?.. nan take tafadi bataga su" Yusufa ne, cikin takaici mutanan suka fara fita suna gun-guni fadi su "Yusufa kam aiba kananan yara bane daza ta daga hankalin ta don bata gansu ba duk inda sukaje aizasu dawo, duk mutanan suka fita suka barta tana masifa sai wata makociyarta me suna Kulu ta tsaya. _wacce ita kam sam bata tsoron lnna Rakiya,sabani yawanci mutanan dake masifar tsoron ta_ Tsaki tayi tareda cewa don baki ga su" yusufa shine duk saiki tayarwa da mutane hankali, cikin masifa tace ya bazan tada hankali ba tare da "sufa muka kwanta amma yanzu kuma gari yawaye bangansu ba, hararanta Kulu tayi tareda cewa "eh kuma fa hakane dole kitayar da hankali saboda kina tsoron idan "suka kufce maki bazaki sake samun bayi kamarsu" ba KO?...,hararanta lnna Rakiya tayi tareda cewa ban gane ba?..baki Kulu ta tabe tareda cewa ai zakigane toh" bari nafada maki abunda baki sani ba," Yusufa da "Indo sun gudu saboda sungaji da azabtar dasu" daki keyi bakar azzaluma kawai kinsamu marayun Allah sai azabtar dasu" kikeyi, ke bakiko tsoron haduwarki Da Ubangiji, don haka kisani "Yusufa da "lndo bazasu taba dawowa gareki ba, indai dasunan "su cigaba dayi maki bautane toh" har abada bazaki sake ganinsu" ba saboda haka saiki nemi wasu bayin tafadi tareda juyawa zata wuce abunta. Cikin masifa lnna Rakiya tajawo rigar kulu tana cewa aidama tunda naga kina yimun katsalanda acikin al'amurana, dama nasan Wata Rana sai haka tafaru don haka bazaki fita gidan nan ba sai kin fadamun gidan uban dakika turasu" domin na tabbatar keki kasa suka gudu, itakam Kulu kamar dama tanajira Inna Rakiya aikam cikin masifa tajuwo tace tace "eh ninasa suka gudu don haka sainaji kamshi mutuwa sannan Zan fada maki inda suke kinji KO?.. kafin kace me tuni dambe yakaure tsakaninsu aikam tuni Kulu ta turmushe lnna Rakiya tana ta jubga saikace Allah ya'aikota, Kai! da'alama lnna Rakiyan madai batada karfi๐Ÿ˜œ domin kuwa sai ihu take zubawa๐Ÿ˜ฉ tana fadi ataimake ta zata kulu zata kashe ta, saidai kuma ina babu Wanda yaleko balle yataima keta, yayinda itakam Kulu sai kirbarta take kamar tasamu fura๐Ÿ˜‚ saida taimata shegen duka wanda ko iya tashi batayi sannan tafita daga gidan. _Nikam nace alhaki marayun Allah ne_ *********** A bangaren su Yusufa kuma shashin da'aka kaisu maikyau kuma akwai komai ciki, bayan sunyi wanka sai sukasa sabon kayan da'aka basu sunyi fesss abunsu gwanin sha'awa, sannan aka kawo masu karin kumallo sukayi bayan sungama sai suka fara firarsu Abba da Hajiya, suna mefadin kirkirnsu tareda jin-jina karamci irin nasu har bacci yadauka su me nauyi, Wanda rabon dasuyi irin sa harsun mata rana Allah sarki bayin Allah, har sun bani tausayi ๐Ÿ˜” kuhuta kunji marayun Allah. _*Bayan kwana biyu*_ Sai Abba yakira Yusufa yasanar dashi cewa ya yanke shawaran zaya hadashi da wani amintatcen yaronsa me suna Al-mustafa suringa kulamasa da gidan gonansa, _kasan cewar yanada wani tabkeken gidan gona da ake masa noman Rani da DA muna domin yatallafawa al'umma,idan ancire amfanin gonan sai yaraba kashi biyu daya yana raba masu kyauta daya kuma yana siyarwa cikin sauki domin shidin mutun ne mai matukar tausayi Al'umma._ Yusufa yayi na'am da aikin da Abba yace zaya ringayi shida Al-mustafa, don haka cikin lokaci kan-kani suka cigaba da aikin kulada gidan gonar yadda yaka mata, ahaka kuma Yusufa yake daukar karatu kamar yadda ya bukata. Akwana atashi bawuya agurin Allah su Yusufa watansu Uku agidan Alh Hashim, sunyi kyau abinsu kamar basu ba don haka basuda wata matsalar komai daga abinci har suturar sawa, Indo kuma tana shiga shashin Hajiya Rabi'atu ta tayata aiki, yayinda Yusufa yake cigaba da aikinsa tareda karatun al'qur'ani dama wasu littafai addi'ni duk yayi nisa acikin karatun su, domin shi mutun ne me matukar hazaka. kuma acikin watannin uku nan Abba yagane Yusufa mutumin karkine kuma shi me amana ne, shiyasa yajashi jikinsa sosai don haka sha kuwa mai karfi hade da kauna da yarda tashiga tsakanin Abba da Yusufa harda iyalinsa ma inda su *Habeeb* suke kiran Yusufa Baffa lndo kuma lnna tun Abban su yace Yusufa dan yan'uwansa ne. Ranan Wata Jumma'a da milasalin 4: 30 Pm Abba da Yusufa da Al-mustafa suna zaune aharabar gidan kan babbar dadduma, kallo daya zakai masu ka fahimci akwai aminci me karfi atsakaninsu wanda bazaka taba cewa mai gida ne da yaran shi ba, saidai kace wayan nan aminan juna ne tun bayan dasuka sufito sallar la'asar suke ta fira abunsu gwanin sha'awa, _kasan cewar ranan Jumma'a basa zuwa gona_ Abba yace mlm Yusufa nagama shirya komai gobe in Allah yakaimu zamuje gudun fulani, cikin girmamawa yace toh" Alh Allah yakai mana rai lafiya Abba da Al-mjstafa sukace ameen, yayinda Abba yace ai harda su Hajiya da Al-mustafa zamu tafi yace toh" shikenan Alh yadda kace haka za'ayi nan dai suka cigaba da fira har lokacin magrib yayi suka tashi suka nufi masallaci. Washegari koda 10:00Am tayi sun gama shirinsu tsaf mato biyu suka cika daya Hajiya Rabi'atu Indo *Hamman Habeeb* Adda Mamu Adda Rahma sai direba, daya motar kuma Abba Yusufa Al-mustafa dan'sanda sai direba suka nufi. _*Gudum fulani*_ Kwance take saman katifa nishitake da kyar kallo daya zakayi mata kafahimci tana matukar jin jiki, bakowa bace illa Inna Rakiya wacce ciwon shanyewar barin jiki yaima dirar mikiya acikin watanni uku kacal tazama bata'iya yima kanta komai sai anyi mata kashi da fitsari duk a kwance takeyi, gefenta Lanti Ce keyi mata fiffita da mafici yayinda take tazuba mata ruwan sannu, duk tasan cewa lnna Rakiya ba amsawa zatayi ba tunda batayin magana, amma haka Lanti keta jera mata sannu. Wata yarinyace Yar kimani shekara goma sha biyu me suna mairo, mairo diyar makotan lnna Rakiya ce mairo suna matukar shiri daYusufa, yayinda take matukar jin haushi lnna Rakiya akan abunda takewa Hamman Yusufan ta da Adda lndo, don hakane ma take kiranta masifaffiya, tafito gidansu kenan saitaga Yusufa yafito daga mota, don haka da murnarta tanufi cikin gidansu Yusufan da gudu tashiga dakin lnna Rakiya tana cewa lnna masifaffiya, Ga Hamman Yusufa can yazo acikin mator yan birni harda yan'sanda sunzo sutafi dake birni suyita baki wahala, kuma suki baki abinci kamar yadda kike yiwa Hamman Yusufa da Adda lndo, dama kin kusa mutuwa shikenan idan kika mutu sai ajefaki ashara sai tsutsotsi su cinye naman jikinki kinga shikenan kowa yahuta da masifarki takarashe fadi tareda yimata๐Ÿ˜›dai-dai lokacin da Lanti tajefa mata mafici tana cewa toh" shegiya me mugun fata bakin ki yasari danyan kashi, saidai ina bata same taba domin tuni mairo tafalla da gudu, yayinda lnna Rakiya ta daga kai dakarfi cikin matsanancin tashin hankali da karka tattacce bakinta dake tafaman zubar da miyau tace..... _*Washhhhhh! ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€nagaji saidai kuma yaseen naji zaki๐Ÿ˜€tunda nacika alkawari so*_ Muje zuwa A _*KYAUTAR ALLAH CE* (Labarin Sadeeya)_ Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนLufhat๐ŸŒน [7/2, 11:27 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 9โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *Ga SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* *_WANNAN_* page nakike ke kadai nabawa *_KYAUTAR shi my Aunty JIDDA BALA_* kiyi yadda kikeso dashi kisani inayinki irin babu din nan fa๐Ÿ˜€. ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ E....e.....eeeeeh......nahhh....isuhun yake?????.. dasauri Lanti ta matsa kusa da ita sosai fuskarta dauke da fara'a tace Alhamdulillahi yau lnna tayi magana sannu lnna yajiki..? Bata amsa sannun ba saidai cikin gurbatacciyar murya tace nace ina isuhun" yake...? Lanti tace lnna ki kyale waccan yar banza yarinyar me kama da kazar mayu, karya take ba Yusufa bane, cikin masifa tace ba karya "take ba naji'ajikina cewa "shine don

Chapter 3 of 42