Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciya tareda fita dasauri. ****** *Deeya* Da tafita kai tsaye part din *Feeya* tanufa kwance ta'iske *Feeyar* hannun ta rikeda hand out tana karanta wa, _kasan cewa ranan Monday zasu fara jarabawa shiyasa itama *Deeya* ta dauko Nata don tayi karatun,_ Ahankali *Feeya* ta tashi daga kwance kasan cewar cikin ta yafara girma, murmushi tayi tareda ajiye hand out din tana kokarin daura dankwali, *Deeya* ta ajiye jakarta akan table tareda yaye gyalen kanta fuskarta dauke da murmushi. Tace sannun da hutawa me ciki hararanta *Feeya* tayi tareda fadin bana son iskanci fa, ba me ciki ba walla me Kai! Cike da zolaya *Deeya* tace to me kai yakike ya my unborn baby?..tace kedai ki kasani tace kefa?.. tace bansani ba Allah my sweet *Deeya* kin cika shegen tsoka, dariya *Deeya* tayi tareda zaunawa tafadin aike kinsan tsokana ajinina yake, itama dariyar tayi tareda fadin aikam nafi kowa sanin hakan. *Deeya* tace hmm ke kinsan abunda yafaru yanzu kuwa?..tace "a ah saikin fada nan *Deeya* fada mata abunda yafaru tsakanin ta da "Aunty *Jana*, dariya sukai sosai saida sukai me isarsu sannan suka tsaya. *Feeya* tace kinyi mun dai-dai my sweet *Deeya* aigara da kika yimata haka, kinsan ita batasan darajar iyayenta ba shiyasa Kai! amma fa kinyi na miji kokari dakika mari wannan shad'ikar tace hmm ai kedai bari ni kaina saida nayi mamaki kain....karar wayar tane yakatseta dasauri taciro daga jakarta *Habeeb* ne yakirata video call ganin hakan ne yasata fadi Oh! my sweet Hmm I love u l miss u so muchhhh!, ta kareshe fadi dayin dariya. Shima dariyar yayi me cike da sonta da kaunar ta sannan yace miss u two my honey *Leemah,* and Love u more than Love me Dear, cike da farin ciki tace nagode Habibina to yakake ya hanyar?... yace to gani nan dai hanya kuma gamunan a kanta tace Allah yatsare yace ameen kina Ina ne?... tace gurin my sweet *Feeya* yace Oh! my *Leemah* shine kikafito?.. me makon kiboye mun kanki um?..cike da shagwaba tace to sowee my Hmm Allah daka tafi gidan babu dadi shiyasa nazo nan kaga tun ba'aje ko'ina ba nafara kewarka KO?..., pls nidai ka dawo dawuri kaji?.. murmushi yayi me kayatarwa tareda shafa suman kanshi yace, hmm Allah *Leemah* ta nima tun bamu fita bauchi ba kewarki tafara kamani sosai, tace kagani ko tozaka dawo dawurin?.. cike da shaukin KAUNAR ta yace karki damu *Leemah* ta zan dawo very soon kinji?.. tace to nan suka taba fira sannan sukai sallama, bayan yaimata gargadin ta maida hankali tayi karatu sosai tunda taga jarabawa zasuyi, tace to tareda zuba masa addu'ar tsari. Daga nan kuma suka cigaba da fira itada *Feeya* can kuma sai ko wacce tafara karatu saida misalin karfe 4:30pm sannan tako gida part dinsu tashiga bata dad'e ba tafito tashiga part din Hajiya nan kam sai bayan isha'i sannan tafito ta nufi part dinsu dasauri tashige daki ta kulle. _Nikam nace Kai!๐Ÿ˜‚ *Leemar* *Habeeb* tun yanzu shiga bacci ko dai kina tsoron kar *Jana* ta suburbud'a kine?_ ๐Ÿ˜œ. *_Bayan kwana hudu_* ***** Tun ranan da *Deeya* tamari *Jana* basu sake hadu wa ba domin kuwa tuni suka kulla wasan yar buya, duk yadda *Jana* ta so su hadu *Deeya* Don tayi mata illa kamar yadda take qudirtawa azuciyarta, Allah bai nufa ba domin *Deeya* tana rigata tashi sannan ta riga ta kwanciya. Idan sukaje school suka dawo sai su yada zango gidan *Feeya* idanta ta so kuma sai tashiga part dinsu lnna ko tashiga part din Hajiya, sai bayan sallar isha'i sannan ta nufi part dinsu idan kuma tashiga bata iske *Jana,* Don haka sai tashige daki abinta, Waya kuma tsakanin ta da *Habeeb* kullu yisuke suna zuba soyayya abinsu wacce take Kara masu shak'uwa da kaunar juna. ***** Yau alhamis tunda ta tashi takejin aranta yau duk yadda zatayi sai taje gurin Shafa da Adonta, saida ta tabbatar *Deeya* tafita zuwa school ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ja, tayafa gyale ja sannan ta dauki wata yar karamar jar jakar sarka da yankune sai tadauki pos da key motar ta data dade ba tashiga ba sannan tafito, tanufi ma'jiyar motocin motar duk tayi kura amma haka tashiga kafin takai bakin get saita fara kuka wanda kana ganin shi zaka ga ne na karya ne, tana isa get din ta tsaya tareda sauke glassa sannan kara sautin kukan sosai. Dasauri baba megadin yafito yana gani tana kuka yace subhalallahi! Hajiya lafiya?..., cike da kukan kissa tace wlhy yanzu aka kirani aka fadamun ankai "Mamana asibiti batada lafiya, yace assha Allah yabata lafiya yafadi tareda bude mata get tafita saida ta hau kan titi sannan tasaki dariya tace bazan megadi sannan takarwa motar gudu. _Nikam nace ai ita ce banza๐Ÿ˜ lamba daya ko masu karatu_?.. *Jana* bata tsaya ko'ina ba sai gidan Shafa saidai kuma tayi rashin sa'a "Shafar bata nan don haka saita nufi gidan Ado, tana isa ana kokarin fitowa dashi zuwa asibiti kasan cewar kafatar tashi ta rure sai wari take tana fidda ruwa cikin tashin hankali tafito take tambaya abokansa suke fada mata take tace su sashi cikin motar ta suka nufi asibiti, suna isa aka fara bashi taimakon gaggawa domin sai ihu yake nan Dr yagano kafar tarub'e, don haka dole sai anyanke ta hankalin *Jana* yatashi sosai yayinda ado yaketa faman ihu shikada ayanke masa kafa, Dr yace dole sai anyanke kafar zaya samu lafiya kuma kudin aikin dubu dari,. *Jana* tace to yanzu batada kudi saidai tana abin kudi zataje tasiyar takawo ayanke masa kafar, Don yasa mu lafiya Dr yace to sannan tatafi. Dubu sittin aka siyi sarka ta kawoma Dr kudin yace gaski bazai iyayin aikin nan dubu sittin ba, tace zataje gida ta ciko kudin yace to saita kawo cikon zatayi aikin sannan ta nufi gida, tabar ado sai ihu yake yana fadin wlhy sai yadauki fansa. *Jana* tana tuki amma zuciyar ta cike take da tunanin ta inda zata samo cikon kudin daza aima ado aikin, akan hanyar ta takomawa gida ne ta tsaya bakin titi tasiya lemo da ayaba sannan tanufi gida. Tana shiga harabar gidan motocin *Habeeb* suna shigowa, bayanta kashe motar sai tafito dai-dai lokacin da Saminu yafito dasauri daga mota yabude ma *Habeeb* yafito, kafarsa sanye takeda farin takalmi jikinsa kuma wani tsaddan yadi Navy blue me sharashara don har anagani farar vest dinsa, hannun sa rikeda wayoyinsa saidai kanshi babu hulla Don haka suman sai sheki take yayi matukar kyau. Yayinda gaba daya kamshi turarensa yacika harabar gidan, wanda yasa *Jana* juyowa dasauri aikam sukayi ido hudu *Habeeb* cike da tsananin firgici Da tsoro tasaki ledar lemon suka watse takasa, tadora hannun wa akai๐Ÿ™†๐Ÿป cike da tashin hankali tabude baki zata ce.... *_Notice, daga wannan page din nadai na tura wa groups din da ake karantawa amma ba asharhi akai, wato comments wanda kunsan cewa shike karawa marubuci kwarin guiwar cigaba da rubutun sa nagode SO._*, Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [7/8, 9:26 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 6โƒฃ2โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Kasa cewa komai tayi saka makon wani irin mugun kallo da yawatsa mata me cike da tsantsar tsana da kyama, Baice mata komai ba yanufi part din su *Deeya* ran shi amatukar bace. Kirjin ta tadafe dake matukar bugawa sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tareda tsugunnawa tana cintar lemon da ayaba, zuciyarta cike da tunani me yadawo da *BB* yau?.. Shikam *Habeeb* dama yazone don yaga *Leemarsa* kasan cewar kullum da kewarta yake kwana da'ita yake tashi, duk dacewa kullum dare da rana suna waya tareda yin video call amma duk hakan be isheshi ba, kamar yauma tashi yayi yanajin matukar son ganin ta azahiri tareda son jinta ajikinsa, shiyasa ya yanke shawar zuwa ba tareda yafada mataba saboda yason yai mata surprise. Da sallama yashiga falon gaba daya suka amsa Baffa da lnna dasuke zaune suna fira har da *Hafeez,* saidai shikam badashi ake firar ba asalima bawa cikinsa hakkisa yake wato yana da'amun ne, Cike da mamakin ganinsa Baffa yace "a ah *Habeebu* ne yau?..cikin girmamawa yace "eh Baffa tareda zama kusada *Hafeez*, Baffa yace to Allah dai yasa lafiya?.. yace lafiya lau Baffa akwai wani aiki Da zanyi ne shiyasa nazo tun yau, yace to to Allah ya taimaka yace ameen sannan suka gaisa yagaida lnna ta amsa tareda yimaya hanya yace lafiya lau, *Hafeez* ya tsaya da cin abincin ya gaidai *Habeeb* ya amsa yana d'an hararan shi, sai kuma yace Baffa kuyiwa yaron nan aure yadaina cinyewa lnna abinci ta haka nan, Da sauri *Hafeez* yazaro ido๐Ÿ˜ณtareda sakin baki yana kallon *Habeeb* wanda yahade fuska tareda cewa yadai?.. ko baka isa auren bane, dasauri ya gyada kai. Aikam me lnna da Baffa zasuyi ba dariya ba, *Habeeb* yace Oh! amma ka isa cinyema mutane abinci su KO?.... Kai yadukar tareda dan turo baki, lnna tace to nidai kar adamar mun yaro na bai isa aure ba tukun, murmushi *Habeeb* yayi yana fadin Baffa kaji lnna ko wai wannan kawon yaron ne bai isa aure ba?... murmushin manya Baffa yayi yace kyalesu *Habeebu* aini tuni na samar masa mata lokacin dazan bayyana nasa kawai nakejiran Allah yabani ikon, yace yauwa Baffa yayi dai-dai Allah yabada iko suka Ce ameen, sannan ya tashi yana cewa zan shiga part din su Hajiyarmu, sukace to sannan yafita yanufi part din Hajiyarmu. *Jana* kam bayan ta tsince lemon da ayaban ta part tanufa afalon kasa ta zauna tafara cin ayaba hankalin ta kwance, saboda taga *Habeeb* bai ce mata komai ba Don haka ne bata wani tada hankalin ta ba Don yaganta, asalima remote ta dauka tareda cewa nasan wannan shegiyar aljanar bata dawo ba, Mtsww kai!, Allah yasama idan zata dawo tayi hatsari tamutu nahuta da jaraba, sannan ta kishingid'a tareda kunna kallon tafara yi ta cigaba da cin ayaba tana jifa da bawon, awani gefen kuma tana tunani ta yadda zata samu cikon kudin aikin ado. ******* A ban garen *Deeya* kuwa tuni tadawo daga school kasan cewar yau paper daya sukayi, Don haka tana gamawa tafito suka tanufo gida yau bata tsaya shiga part kowa ba direct part dinsu tanufa, Dakin *Habeeb* tashiga domin yau wani irin kewar sa itama takeji gashi tunda sukai waya dazata tafi school basu sakeyiba, takira wayar shi tafi akirga amma baije ba shiyasa duk taji ba dadi, Don haka tana shiga tanufi cikin bedroom din sa, tsaf dakin yake agyar kamshin turaren shi sai tashi yake, ahankali takarasa baki gado rigar banshi tadauka tareda kaiwa hancin ta tashaki kamshi daddad'an turaran shi me kasheji ido ta lumshe tareda sauke ajiyar zuciya tace l really miss u Hmm na pls came back soon because I want, hanan tai tafaman surutai masu cike da tsakanin kewar sa. Can sai ta ajiye riga tareda jakarta da gyale ta cire kayan jikinta ta daura towel dinsa tanufi toilet tayo wanta tafito, bayan tashafe jikinta da mai da turaruka masu kamshi sannan tabude wardrof tadauko wasu shegu riga da wando masu kyau tasa, Wandon swaga ne black da ratsin milk yanada duwatsu ajiki ita kuma rigar milk colon ce tanada igiya agaba arubuta I miss u ajikin rigar da small letter, sai takama igiyar ta kulle wanda hakan ne yabawa albarkatu kirjinta rabi damar fitowa, gaskiya tayi kyau sosai sai tasa wata bakar hula me kyau bayan tasake feshe jikinta da turare sannan tagyara gurin, tareda daukar key dakinta tafito falo. Bazato suka hada ido da juna kowani saida gaban sa yafadi, musamman *Jana,* domin batayi zaton *Deeya* na cikin gidan ba itama *Deeya* batayi zaton cewar *Janar* na cikin gidan ba, kitchen *Deeya* tanufa gaban ta na faduwa, Tsaye tayi a kicthe din ahankali ta furta wai dama ita wannan mama katuwar tana cikin gidan ne?..baki ta tabe tareda d'age ka fada tace to kotana ciki ni Ina ruwana "da'ita, can kuma sai tace to wai me nashigoyi kitchen ne?.. mtsww tayi tsaki tareda fitowa ba tareda ta kalli gurin da *Jana* take bata nufi sama danufin zuwa dakinta. Da sauri da sauri take hawa step din kamar yadda tasa ba, yayinda jikinta yake Wani irin shaking na daukar hankalin duk wani lafiyayyan Da namiji, tahau step na daya tahau na biyu ta hau na uku zata hau na hudu kenan sai wani mugun santsi yakwashe, saka makon bawon ayaban da *Jana* jefa mata, aikam tuni tayo baya zata fadi hakan ne yasa tasaki wani irin Kara me karfi tareda fadin wayyo Allah Hmm na zan fadi. Dai-dai lokacin *Habeeb* yashigo cikin azababben zafin nama yai sufa yatare ta wanda har saida guiwoyin sa suka bugi steps na biyu sannan suka zube gaba daya kasa, sai ya kasan ce shi yana kasa ita kuma tana saman jikinsa tabayan ta dasauri tajuya ta rukunkume shi, ajiyar zuciya suka sauke alokaci daya, sai kuma tasaki wani irin kuka me cike da tsantsanr tsoro had'e shagwaba, ido yarintse saboda yadda yaji kukan ta yadaki zuciyarsa hannun shi duk biyu yasa ya rungumeta sosai yayinda yaji kirjinsa yawani irin mugun bugawa, ahankali yafara Shafa bayanta cikin tsanani fargaba yace it's Ok my *Leemah* l'm here with u noting will happen to u by the great of God, cikin kukan shagwaba tace Hmm na da baka zo ba Da yanzu nafad'o yace hakan bazaya taba faruwaba Insha'allah kinji *Leemah* ta?...Kai ta gyada alamar to. Ahankali yamike da'ita ajikinsa tareda kallon gurin da bawon ayaban yake, wanda yakeda tabbacin shine yasa *Leemarsa* takusan fadowa ba don Allah yakawo sa ba da shikenan tafado da babu, abinda zaya hana batayi mummunan rauni ba. jiyayi ransa yai bala'in baci domin tuni fahimci cewar *Jana* ce ta haddasa faruwar hakan, Wani irin mugun kallo ya watsama *Janar* wacce tayi mutuwar tsaye domin batayi zaton shigowar sa adai-dai wannan lokacin ba, aikam take kirjinta yabuga yayinda jikinta yadauki rawa domin tahango wani mugun bacin rai akwayar idonsa, Cak! yadauki *Deeya* wacce tasake ruk'unk'ume shi tana sauke ajiyar zuciya, wani mugun kallon yasake watsama *Jana* me dauke da zan dawo gareki, sannan yanufi dakin shi rungume *Deeya*. Hannun tadora akai tareda fadin nashiga uku shikenan yau nabani, jifa tayi da remote din hannunta dasauri tanufi sama buguzu-buguzu hankalin atashe take hau step din tahau dai-dai in da bawon ayaban yake, itama ta taka aikam take tasaki wani uban ihu tareda fadin wayyo nashiga uku mutuwa karki zo yanzu, _nikam nace tab! *Jana* ai saida in lokaci baiyi ba_ Duka guiwoyin ta biyu suka bigi steps din dasauri tarike karfen benen, yayinda taji wani irin zafi yaratsa kwakwalwarta, dararrafe ta isa daki tana fadin wayyo washhh kafata. *_Kaikayi koma kan mashekiya inji ado gwanjan MATA_* ๐Ÿ˜‚. *Habeeb* kam bai dire *Deeya* ko'ina ba sai kan faffad'an gadon sa, tareda yimata runfa ahankali yasa harshen sa yana lashe sauran hawayen dayake fuskarta, Saida yalashe hawayan tas sannan tabude idon ahankali ta zubasu akanshi shidin ma ita yake kallo, cike da shaukin kaunar ta sun dauki mintuna suna kallon juna can sai ta turo baki tareda kauda kai gefe, dasauri yajuyo da kanta tareda fadin Oh! no *Leemah* ta don't angry with me, cike da shagwaba tace to bakai bane damukai waya dasafe baka fadamun yau zaka zo ba, gashi ban dafamaka komai ba sannan inata neman layin ka ban samu ba kuma yau Ina taji kewar ka sosai. Murmushi yayi me cike da kaunar ta da sha'awarta, fuskar takama yahade danasa ahankali yake goga hancisa anata cike da kasala yace, am so sorry *Leemah* ta nima kewar nice tada me ni shiyasa nayanke shawar nazo ba tareda nafada maki ba saboda nayi surprised naki, so are u happy to see me?.. tace yes I am very happy, yace nima haka *Leemah* ta kirjinta yatsurawa ido wanda ke tayi masa welcome, hannu yasa yaja igiyar gaban rigar aikam take kullin yasance dago kai yayi ya kalle ta tareda cewa kai! *Leemah* ta amma fa kwalli yar nan tayi mun kyau sosai, yakamata ma nabada tukuici KO?.. yakareshe fadi tareda kashe mata ido daya yana kokarin tura hannun sa ciki rigar. Murmushi tayi tareda tura hannuta cikin suman kansa, sannan tayi fari da ido wanda yasake tsuma masa sha'awar ta, cikin cool voice dinta tace "eh dasauri yace to me kike so fadamun zan baki kinji *Leemah* ta?.. tace Hmm na komai yabani inason, amma dai yanzu ka fara bani sweet tongue dinka na sha saboda nayi kewar sa dayawa dasauri yace really?.. tace yeap, Wani irin kayataccen murmushi sannan yace to take it my honey *Leemah* yafadi tareda mika mata harsa aikam dasauri ta cafke tafara tsota, nikam inaganin haka na arina kare๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€don my Habity ta hanani ganin kwaf lol. Saidai suka samu nutsuwa sannan suka kasararama Kansu, sannan suka shiga toilet sukayi wanka sannan suka fito, *Habeeb* yanufi wedrof yadauko wata farar jallabiya yasa, *Deeya* kam da towel din jikinta tahaye gado murmushi yayi tareda nifar gurin ta yace ya'akayi ne *Leemah* ta?.. Cike da shagwaba tace Hmm na nagaji kuma bacci nakeji, kumatun ta yashafa yace sorry *Leemah* ta nine natara maki gajiya ko?.. Dasauri ta rufe ido cike da jin kunyar abinda yafadi, dariya yayi sannan yaja bargo yarufe mata rabinjiki yace kiyi bacci ki zanje nadawo kinji?..tace to sannan yafita. Dakin *Jana* yanufa dakarfi yabanki kofar zumbur tamike cike da tsoro ta kalle sa, yayinda ya watsama ta mugun kallo rai bace yace... Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [7/10, 9:32 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 6โƒฃ3โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ _Today is final So_ maza-maza ki tattara naki yanaki kibar mun gida na dama nasakeki tu...wani uban tsalle tayi ta'isa gaban shi tareda tasakin ihu cikin azababben tashin hankali tace *BB* na kasakeni fakace?..... Matsawa yayi baya cike da bacin rai yace "eh au dake tunanin ki yana baki cewa bazan iya sakin ki ba ne KO" me?.....tab! lallai tunanin ki yafada maki robish, to bari kiji ni *Habeebullah Hasheem Sorro* nasakeki saki biyu tun ranan da Allah yanuna manku kuna aikana *ZINA* agidan nan dake da kwartonk...... Wani irin kara tasaki cikin tsananin tashin hankali tace nashiga uku na lalace kaganmu fa kace?...,wani uban naushe yakai ma bakin ta sannan yashiga sharara mata lafiyayyun marurru ka afuskar ta, wacce tuni tahade da jini da majina tofa๐Ÿ˜ณ da dama kunsa yana cike da ita, Cikin bacin rai yace yar iska kina nufin ka zafi zanyi maki kenan ko?....kai ta gyada cike da tashin hankali, wani marin yashara mata rai bace yace u are very stupid *Jana* ribarme zan samu idan nayi maki kazafi?...idan harma zanyin kaza sai narasa wacce zanyi ma kazafin sai mata ta?...kuma kazafin mana ZINA?.... lallai *Jana* kin cuceni domin nidaki kaganin natsani ZINA arayuwata, bana fatan aikata ta balle har nayiwa mutun kazafin ya'aita ta, amma wai sai gashi matata ta sunna nagani da idona tana aikawa har cikin gida na har kan gado na, Kai! *Jana* to wai ma dame narageki ne arayuwa?... ci da sha?...KO sutura?...eyeee yafadi da karfi tareda shake mata wuya cikin bacin rai yace tambayar ki nake?.... Cike da tsanani wahala take sonyin magana amma takasa saboda mugun shaka yai mata, murmushi yayi me cike da tsantsar bakin ciki sannan yasake mata wuya tareda hankadata baya tayi taga-taga kamar zata fadi sai kuma tadafe bango, tafara tari saida tayi sosai sannan ta tsaya duk yana tsaye yana kallon ta. Rai bace yace acikin abinda na lissafa mena rageki dashi?.. dasauri tace babu kodaya, da sauri ya'isa gurinta yasake shakar wuyanta cikin tsawa yace ainasan ban rageki da kodaya ba, kuma baki isa kice narageki da *SEX* ba domin kinsa koni wanene awannan fagen, ko kina nufin kice narageki tanan gurin ne?...Kai! ta girgiza alamar a ah yace ainasan ban rageki anan ba tunda harda kudi nake biyanki idan zanyi, wanda ban tabasanin cewa idan miji zaya sadu da matar sa saiya biya ta kudi ba sai akanki, kuma kinsani nasani cewa a, addinin mu ba'ayin haka amma haka nake biyan ki kudin sannan nasadu dake saboda gudun karnaje Ina aikana zina, shiyasa nake biyan kudin domin tuni nafahimci kedin muguwar mayyar kudi Ce shiyasa nake bakisu gudun Karkema kije kina aikana ZINA, Ashe bansani ba kedin tantiriyar mazinaciyace fasika tunda har zaki iya aikata zina da aure akanki tabbas *Jana* kedin maciya amanace, nisai aranma nagane cewa dama can ke mazinaciyace tunda lokacin da na aureki duk daban taba sanin ya mace ba saike hakan be hanini gane cewa ke ba cikakkiyar budurwa ba ce, Wanda dakika fahimci nagane cewa ke ba cikakkiyar budurwa bace sai ki kai mun karya cewa ai fyad'e aikai maki KO?..., hummm Kai! *Jana* kinci amanata ta dalilinki nasamu ciwon ulcer da ciwon sanyi badan Allah yaganar dani dawuri ba, da bansan irin cututtukan dazaki kwaso kiyaba mun ba, Lallai *Jana* kin cuceni cuta mafi muni arayuwa kinci ha'ince kwarai da gaske azaman mu, saidai nadauki hakan amatsayin kaddara dakuma rabon zuri'ar dake tsakanin mu wanda Allah ya kaddara samuwarsu ta tsotsonki, don haka kije nabarki da Allah. Cikin tashin hankali tace don Allah kayi hakuri karka sakeni, dasauri yace saki na nawa kuma?... kina nufin duk wannan abinda daki kaimun shine kike tunani bazan iya sakin ki ba?.. tab! kinyi kuskure *Jana* aituni dama nayi maki saki biyu tu ranan dana ganku, dama nabarki ne kiyi idda adakin ki kamar yadda addinin mu yace, bawai don na mai dake ba "a ah saidon na d'and'ana maki kwatankwacin bakin cikin dakika d'and'ana mu, to Alhamdulillahi kin d'and'ana, Sannan kuma dama kinsan nafad'a maki duk ranan dakika sake taka bakin get, zan datse sauran igiyar dake tsakanin mu ko?...ya kareshe fadi a tsawa ce, Dasauri tace "eh yace yauwa to kinga yau shikenan babu sauran wata alaka ta aure tsakanin mu, tunda ba bakin get ba yau har waje kika fita ba tareda izinina ba, don haka saiki tashi kibarmun gidana, Tun baki nakasamu rayuwata ba saboda *"Leemah* ta itace rayuwata kisani, Ina *"SONTA* fiye da yadda nake son kaina, saboda kin fahimci haka shine kike son ki "illatamun ita KO?... saboda kedin bakar mutuwa ce KO?.., Domin dai wannan abinda ki kai mata yau badan Allah yakiyaye ya kawoni ba, datayi mummunan rauni tab! narantse *Jana* da yau sai na kashe ki; wlhy murusss zan kashe ki, kinga alabashi nima sai akashe ni don haka, Ki tashi kitafi gidanku kine can kikarata da kazamar rayuwar dakika zabarwa kanki, idan kinga dama kin nutsu sai ki karasa iddarki, idan kuma baki natsuba saikije kiyi ta sha shan ciki babu abinda yada meni, yana Kai nan yasa Kai zaya fita. *Jana* kuka tasaki sosai cikin tashin hankali tace don Allah *BB* na kayi mun rai tafadi tana kokarin rike masa Riga, wani azababben tsawa yadoka mata rai abace yace idan kikai kuskuran tabani da wannan kazamin hannun naki, narantse sai nayi maki dukan mutuwa fiye da wanda naiwa tsinannan kwartonki, Wanda har da renamun wayo kukasoyi ko?...ga kato kirikiri nagani amma wai kikace mu kawarkice saboda kin rai nawa kanki dawayo kice ni kika rai nawa, shashasha kawai kidahumar banza dawofi, nikam ai tuni nayi dana sanin saninki a rayuwata wlhy Sannan yafice ransa abace. Zaya fita kesai saiga me aikin Hajiyarmu da basket dauke da kulolin abinci, Cikin girmama wa tace gashi inji "Hajiya Karba yayi tareda fadin Oh! aina manta "Hajiyarmu tace zata aikomun da abinci, kice nagode sannan ki fada mata na'iske *"Leemah* ta tadawo saidai tana bacci ne, tace to tareda dajuyawa shikuma yakoma dakin shi,

Chapter 27 of 42