tadauko mai hunnun shima tareda hula tasa iyakarta rigar guiwa sannan tafeshe jikinta da turare sannan tabude drower, tadauko wani littafin hadith takoma gefen gado ta zauna tana dubawa.
Shikam *Habeeb* saida yaga Hajiya ta haye sama Sannan yayi ajiyar zuciya tareda lumshe ido ahankali ya furta da gaske fa nake Hajiyarmu, gaba daya mata basa burgeni amma fa banda mutun daya, yafadi yana sakin kyakkyawan murmushisa mai karamasa kyau da kwarjini, still idonsa rufe yake, yayinda yacigaba da cewa.. "itakam tana matukar burgeni komai tayi yana bani sha'awa saboda Ina *SONTA"* irin *SON* da bayan ke Hajiyarmu babu wata y'a mace dayake yiwashi,
Ina *SONTA* ina kuma matukar *KAUNARTA* sosai irin wanda nikaina bansan adadinsa ba, saidai Inada tabbaci dashi aka halicci *RUHINA* wanda duk fitar numfashi na yana fita ne tareda matsanancin *"SONTA* yayinda duk lokacin da naganta sai *ZUCIYATA* tabuga saboda tsananin *SONT*....
Shuru yayi saka makon fadawa dayaji anyi ajikinsa tareda cewa Daddy Oyoyo, ahankali yabude idanusa dasu kafara ja yazuba akan wata yar farar flower girl wadda batafi shekara biyu ba, kamarsu daya da shi harda kwayar idanun, tana sanye da pink din riga da wando da d'an karamin farin hijab, murmushi yayi tareda rungumeta yace oyoyo my lili Mama kundawo?..
kai ta gyada alamar "eh tareda dagowa daga jikinsa ta fincike d'an hijab din, tamika masa yakarba fuskarta cike da farin ciki, baki ta turo tareda cewa Daddy inajin inwa.
Ido yazaro dai-dai lokacin da wani kyakkyawan saurayi ya shigo shima kamarsu daya da *Habeeb* dan kimanin shekara ashirin da biyu, hannunsa rikeda wani dan yaro wanda shekarunsa basufi uku zuwa hudu ba, saidai shi kalar fatarsa daban, dasauri wannan yaron ya'isa gurin *Habeeb* yana cewa Daddy oyoyo, kanshi yashafa tareda cewa oyoyo Junio yakake?..yace lafiya qalau yace good.
cikin girmamawa saurayin yace *Hamman Habeeb* sannu da dawowa, yace yauwa kuma sannu ku da dawowa, sai kuma ya kalli lili Mama daketa turo baki murmushi yayi tareda cewa amma Uncle Hafiz ya'akai aka barmun lili Mamata da inwa?..
murmushi Hafiz yayi tareda cewa koda mugaje mun'iske "Adda Mamu tuwan shinkafa tayi da miyar kuka, shine takici, dasauri yace no no ai my lili Mama batacin miyar kuka "KO kamanta ne?.. yace a ah ai andafa mata lndomi bataci ba,
yace ayya aida yanwan yara suna cin Indomin amma banda my lili Mama I don't know why, Hafiz yace kuma aka siyo mata take away saita chakulashi tace wai babu dadi, dariya *Habeeb* yayi yace Allah sarki ai d'iyar irin Daddy tane bako wani abinci take ciba KO?..Kai ta gyada alamar "eh yace yauwa my lili "toh zauna kici wannan nima yanzu nagamaci yana fadine tareda mika mata sauran dambun daya rage a filat,
Zama tayi tareda fara cin dambun sai shima Junior yace Daddy nima zanci, dasauri Hafiz yace haba junior kabarta taci mana kaga ita bata cikomai ba sai bobo datake tasha, bata fuska junior din yayi sai Hafiz yace kyaleta zan siya maka sweet kaji yarona ai zaka shako?.. dariya yayi tareda cewa "eh yace yauwa my boy, yace Uncle kuma baza'aba lili Mama bako?.. yace "eh bazamu bata ba.
tsayawa tayi da cin abincin tana hararan Junior tareda cewa ainima Daddy zaya ciya mun ko Daddy?.. Kai ya gyada mata alamar "eh sannan ta cigaba da cin abincin yayinda Hafiz yace *Hamman Habeeb* "Hajiyarmu tadawo?..
yace "eh tana sama amman kayi sauri kafito muje masallaci domin ankusan kiran magrib, yace "toh tareda mikewa yanufi sama da sassarfa.
Da sallama Hafiz yashiga dakin Hajiya tana zaune gefen gado tazuba uban tagumi, har ya zauna kusa da ita amma bata saniba ahankali yacire mata tagumin tareda cewa, Hajiyarmu lafiya inatayin sallama amma baki amsa ba,
kuma naga kinyi tagumi kuma kin sha fada mana cewa babu kyau yin tagumi, amma kuma yauna gakinyi lafiya meya faru?..ajiyar zuciya tayi tareda cewa kundawo?
Yace "eh tace ya Addar taku da yaranta suna lafiya?..
yace lafiya lau suke tana gaida Ku "toh muna amsawa inasu "lili din?..yace suna can many falo gurin Daddy su, tace "toh yayi kyau. yace Hajiyarmu meyasa meki?. tace ba komai ka tashi kaje Kai sallah yace toh tareda tashi har yafara tafiya sai kuma yajuya yace Hajiyarmu cikin kosawa da mahanar tace...
_Nasan dai *Zuciyar* me_ _karatu_
_tacika da_ _tambayoyi_ _kamar haka_ _๐wanene_ _*Habeeb..?*_
_wacece_ _*Sadeeya..?*_ _wacece *Jana..?*_
_sannan shin_ _wace mace ne_ _me sa'ar data_ _siye *Zuciyar..?*_ _*Habeeb* "toh_
_meson jin amsar_ _yabiyoni_ ๐๐ปโโ
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE* (Labarin Sadeeya)_
Tareda
Alkalamin
โ๐ฝ
๐นLufhat๐น
[7/2, 11:18 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
3โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*ga SADEEYA SADEEQ KD UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
Ko yanzu madai Kalmar kenan daya zan sake fada maka wato *HAKURI,* kaci gabada yin hakuri da duk wani abinda *"Jana* takeyi maka Insha'allah zata dainai wata rana ma "KO ance tayi ba zatayi ba.
"Ajiyar zuciya yayi tareda cewa "toh nikam yana iya tunda kin daurawa *ZUCIYATA* *HAKURI,* murmushi tayi tace a ah banice na daura maka ba Allah shine ya daura maka,
don haka karkayi kuskuren sakinsa domin zuwa gaba zai maka amfani.
yace "toh shikenan naji na dauka *HAKURI* saidai kuma wlhy *CIKINA* bazaya taba daukar *HAKURI* ba, asalima shi baisan wata kalma wai ita *HAKURI* ba domin nan wani irin yinwa nakeji dan haka idan kun rage abinci kubani, idan baso ake nawulle nafadi ba a gurin nan ba.
murmushi tayi cikin zolaya tace babba dakai saika fadi saboda yinwa?.. yace hmm! Hajiyarmu ai ita yinwa baruwanta da babba baruwanta da karami, tace "toh bari na tambayi "Hali dubu na, idan sauran abincin namu yarage takawo maka, saidai yaka mata kafara shan ruwan zafi kafin kafaracin wani abun don dai yanzu nasan cikinka ya kulle,
Yace hmm! shiyasa nace maki *"Jana* sotake kawai ta kasheni, kinsa Allah Hajiyarmu saboda tsabar yinwar dana keji har wani amai-amai naji yana taso mun,
Murmushi tayi ba tareda tace masa komai ba saidai kawai ta tashi tanufi saman bene.
๐๐๐น๐๐
Ciki nutsuwa *Sadeeya* ta cire riga yayinda farar singlet da wando lages fari ya baiyana, cikin sanyi murya tace my sweet *feeya* nifa zafi nakeji wlhy, murmushi tayi tace kinada lafiya ne shiyasa kikejin zafi nikam da banida ita ai sanyi nakeji sosai wlhy.
Cikin tausayin yar'uwar nata tace Sorry my sweet *feeya* Bari nabaki maganin ki kisha kinji?..dai-dai lokacin da ta'isa gaban wani kyakkyawan Mirror mai daukeda hadaddun kayan kwalliya dasu turaruka da manshafawa masu asalin kyau da tsada, magunguna tadauka cikin wata farar leda sannan tanufi wani dan karamin fridge, tabude tadauko ruwa tareda cup sannan takoma gefen gadon ta zauna, tareda cewa tashi kisha kinji my sweet *feeya*?...
Fuska ta yamutsa tace gaskiya my sweet *Deeya* ni bazan shaba, ido tazaro tace saboda me?..baki ta turo tareda cewa nidai nagaji dashan maganin nan, cikin sanyi murya tace yi hakuri kisha kinga fa sun kusan karewa kuma insha'allahu kina gamasha zakiji sauki tace a ah gaskiya bazan shaba.
tace "OK shikenan bari naje na fadawa "Malam zalumun kin kishan magungunan ki, dasauri tashi tareda cewa "toh kawo zansha. dariya *Sadeeya* tayi sannan tace aha! yarinyar idan baki shaba yanzu yazo idan kuma yazo kinsan sauran, tafadi tareda kashe mata ido๐.
itama *Safeeya* idon ta kashe mata tareda cewa Oho! wato "yazo yimun zalun KO?..murmushi tayi tareda ballo mata maganin tamika mata, saida takarba sannan tace aibazai maki komai ba tunda bakida lafiya.
Saida tasha sannan tace toh aikema bazayayi maki komai ba tunda "Hajiyarmu tace ya daina dukanmu, tunda yanzu mun zama big girls KO?.. tafadi tana murmushi itama murmushin tayi tareda cewa Yeap!,
Saida ta bata dukka magungunan tasha sannan ta tashi tamai da shi inda tadauko, tace my sweet *Feeya* Bari nashiga nawatsa ruwa tace "OK saikin fito, har zata shiga toilet din sai taji Hajiya tana kiranta,
Da sauri tanufi bakin kofa tabude tsaye taga Hajiyar tace Hajiyarmu naji kin kirani KO?..Hajiya tace "eh, *Safeeya* tashi magani nata?. tace "eh tasha, tace "toh yayi kyau. dama nace "KO akwai sauran abinci?.. tace "eh Hajiyarmu akwai tace yauwa "toh kije kizoba kikaiwa *"Hamman* dinku yana can falon kasa yanaji ranki, amma ki hada masa da ruwan coffee kinji?..
Hannu tadora๐โโ akai cike da shagwaba tace wayyo! Hajiyarmu shikenan *"Hamman Habeeb* zaya dukeni, murmushi Hajiya tayi tareda cewa cire hannun nan akai ainayi masa magana don haka bazaya dokeki ba kinji KO?...sauke hannun tayi tareda rungume Hajiyar tana dariya tace yauwa Hajiyarmu inasonki sosai-sosai, tace nima haka Hali dubu na kiyi sauri kije kikai masa tace "toh.
Sannan Hajiya tanufi dakinta itaku takoma daki tadauki dogon hijab har kasa mai hannu tasa zata fita, sai *Safeeya* ta tuntsire da dariya tareda cewa hahaha wata yarinya zata suburbud'u agurin *"Hamman Habeeb*
dariya itama *Sadeeya* tayi sannan tace tab aiba sawa wlhy sata rahira azo duniya asiyar, kinsan Allah duk zaluntarmu dayai tayi "toh saina Rama manashi tace a ah fa my sweet *Deeya* bakijin tsoro?. tace tab kinsa Allah aikoda kirjina yana fadowa kasa ina dauka ina mayarwa saboda tsoron shi "toh sai na rama mana, ai tunda Hajiyarmu takama mun kan maciji, yarinya ai dole ne nayi wasa da bindi tafadi tana girgiza body tareda cewa "ko yanzu saina tsokane shi, dasauri *Safeeya* tace again?.. tace Yeap ai tunda matarsa ta zama Laziness bazata zage taringa yi masa abinci yanaci ba, saidai idan munyi yazo yacinye mana yana wani mazurai da wannan idanun shi masu ba mutun tsoro.
Dariya *Safeeya* tayi har da buga katifa saikace bamara lafiya ba, tace Kai! my sweet *Deeya* ba kifada kyau, sai kuma tace kinsan Allah niban taba ganin wawuyar mata irin "Aunty *Jana* ba.
tsaki *Sadeeya* tayi tareda cewa kyale banza irinsune mijinsu keyo masu kishiya ta kwace miji sunan nan suna wawanci banza, tace wlhy kuwa kai! aini sonake *"Hamman Habeeb* yakara aure, tace wlhy kuwa sai muga karshen lalaci, tace tab! gashi "KO Aunty *Jana* batason kishiya ba, *Sadeeya* tace idan kuma Allah yace sai yakara aure ita bata isa tahana ba wlhy, *Safeeya* tace haka nefa ke! Bari naje tafita da sauri.
Kichin tanufi saida ta hada masa coffee mai zafi sannan tab'ude wani d'an madaidaicin kula mai kyau, dambun shinkafa ne dayaji kayan lambu an yanka anta kana-kana acikin, kamshin sai tashi yake.
Baki ta tabe tareda cewa kamar nasani dazu nadiba na'ajiye, aiduk cinsa wannan ya'ishesa sai tarufe, sannan tadauki tire tadora tareda filat da spoon da kuma coffee sannan tadauka tafito.
Saifaman dan ne dan ne yake awaya yaji shigar falon amma ko dagakai beyi ya kalleta ba, baki ta tabe sannan ta, ajiye abincin kasa sannan tajawo table gabansa sai tadora abincin, har zata juya ta tafi.
Ba ba tareda ya kalleta ba yace ke! kina nufin ni zanyi saving din kaina?..duk da bugawar da kirjin tayake hakan bai hana ta turo baki ba, sannan ta duka tabude abinci tadauki filat da spoon tabara saving dinsa, yayinda kamshi hadadd'en turaran arabiyan oud dinta wanda yahadu da kamshi sanyayyan turaran humran yabugi hancinsa,
Saidai da'alama ba hancinsa kadai ya bugaba harda kwakwalwar sa, don haka da sauri yace, ke!.barshi banaso.
"Ajiyewa tayi yajuya saida ta taka step din sannan tajuyo aikam karaf suka hada ido, kirjinta yasake bugawa amma saida ta murguda ๐ masa baki tareda cewa gaskiya yaka mata mutun yariga saka matarsa tanayi masa girki, don baiyuyuwa sai munyi girkinmu sannan mutun yazo ya zauna yacinye takarashe fadi tareda turo baki.
ido yazaro๐ณ cikeda mamaki yace Ke! nidin abokin wasanki ne?..cike da tsoro ta girgiza kai tareda fallawa da gudu, kai ya girgiza tareda jan tsaki mtwww! yace Kai! wannan yarinya idan nabiye mata saita rainani, kai! kaga mun yarinya sai dan banzan tsokana ga shegen tsoron tsiya kamar farar kura, da'anyi mata magana kuma saita wani falla da gudu saikace barewa, ya karashe fadi tareda sakin kyakkyawa murmushi sa.
Sannan yadauka coffee yafara sha, saida yagama sha sannan yayi saving din kansa, yafara cin abinci cikin nutsuwa har yana lumshe ido da'alama dambun yaimasa sweet ne lol.
Hajiya kam koda tashiga daki kasa zama tayi saifaman safa da marwa take, ga dukkan alama halin da d'anta keci ne yake da munta har ta zauna sai kuma ta tashi tafito.
Koda ta'isa falon har yagama cin abincin, zama tayi tareda cewa har kagama cin kenan?.. yace "eh tace dama wata shawara nazo maka da'ita, yace "toh Hajiyarmu inajinki wacce irin shawara Ce?.. tace dama nace ne meze hana bayan angama election wato zabe, saika karayin wani aure dasauri yace...
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE*_(Labarin Sadeeya)
Tareda
Alkalamin
โ๐ฝ
๐นLufhat ce๐น
[7/2, 11:26 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
5โฃ
WRITTEN
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
Hafiz wai menene haka ne bana ce " katafi Kai sallah ba?..yace yi hakuri Hajiyarmu yanzu zantafi, dama zan tambaye kine yaushe "Abba yace zaya dawo?..tace munyi waya dashi dazu yace sai gobe zasu dawo, yace "toh Allah yadawo dasu" lafiya tace ameen, sannan yafita yayinda ita kuma tamike tanufi toilet don tayi alwala tazo ta gabatar da sallah.
Daddy na koci inji cewar lili Mama tana tashi murmushi *Habeeb* yayi tareda cewa my lili Mama kenan, d'azu anajin inwa yanzu kuma an koci "toh Alhamdulillahi, saida kuma banji kinfadi abin nan ba...wanda Aunty *"Sadeeya* tace" kiringa fadi idan kin gama cin abinci...yafadi tareda alamar yimata tuni, dasauri tace kai! Daddy Aunty *Deeya* fa ake cewa, murmushi yayi ganin yadda ta turo maki alamar bataji dadi ba tunda baice *Deeya* ba,
yace "toh nace Aunty *"Deeya* shikenan KO?.. dariya tayi tareda gyada kai alamar "eh yace yauwa "toh say it, cikin rashin cikakkiyar hausarta tace *_Al'andulilahi-lazee-at'amani-haza-warazakani-himin-ghayri-hawlin-minnee-wala-kuwwah_,* yace yauwa my good girl, dai-dai lokacin da Hafiz yake saukowa, *Habeeb* yace Hafiz Ka kwashi kayan nan ka kai ciki kazo mutafi masallaci.
yace "toh tareda dauka yanufi sama, can sai gashi yadawo yace nakai yace "OK mutafi, dasauri lili tace Daddy nima zanje gurin Aunty *"Deeya* da Aunty *Feeya* nayi callah yace "toh kije, Kai kuma Junior mutafi masallaci yace "toh, suka tafi ita kuma ta haye sama tana ihun kiran Aunty *Deeya* Aunty *Feeya*.
*Habeebullah Hashim Soro* wannan da Abokansa ke kiransa da ( *BB SMART* ) D'ane ga Alh Hashim soro, asalinsa bafullacen kauyan soro ne karatu yakawosa cikin garin Bauchi
Bayan yagama makaratu sai yafada harkar siyasa.
Inda yazama shahararran dan siyaya ne wanda yai suna sosai acikin ta kuma ya kasan ce mutun ne mai matukar tausayin talakawa, gashi da kyauta don haka mutane suke matukar son shi domin yanayi masu yadda suke so, shiyasa ma duk kujerar daya nema sai yasamu don haka yarike matsayi iri-iri da ban, da ban harda governor yayi matarsa daya me suna Haj Rabi'atu amma ita yar nan cikin garin Bauchi ne.
Haj Rabi'atu takasa ce mace kyakkyawa me kyan hali wanda halinta yazama iri daya da mijinta, domin kuwa macece mai matukar hakuri tanada kirki sosai, bata kyamar talaka, sannan abin duniya bai rufe mata ido ba, ya'ya'nsu biyar maza biyu mata uku *Habeeb* shine babba wanda ya kasan ce mutun mai hakuri yanada kyauta sosai, halinsa sak irin na iyayansa,
Saidai yanada matukar zurfin ciki wanda duk yanda kaso kagane cikinsa Sam bazaka gane ba, amma duk da haka wani lokaci mahaifiyarsa tana gane cikinsa, sai me binsa Maryam wacce taci sunan mahaifiyar Abban su amma suna kiranta Adda mamu itama halinta irin na mahaifanta, sai Rahma sai Hafiz sannan auta *Safeeya*.
***********
_*Shekaru masu yawa dasuka wuce*_
A wani kauye mesuna *GUDUM FULANI* ayin wani attajirin bafulance mesuna Alh Isyaku yanada shanu sosai yanada mata biyu uwargida wadda suke kiranta lnna Rakiya tanada ya'ya' uku duk mata, Lanti da Harira da Mari sai amarya lnna Halima tanada d'a namiji daya mai suna yusufa wanda Lanti ce kawai ta girmi yusufa don awance lokaci anyi mata aure amma da Harira da Mari duk yusufa ya girmesu amma dayake matane alokacin suma ansa ranan aurensu dukkansu kasan cewar girmansu daya,
Inna Rakiya ta kasan ce masifaffiyar mata yayinda lnna Halima ta kasan ce mace mai hakuri, lnna Rakiya tana bala'in jin haushin lnna Halima da d'anta yusufa musamman dataga Alh isyaku yana matukar son yusufa, shiyasa take jin kamar ta kashe shi, tabi malamai da bokaye don ta raba Inna Halima da Alh isyaku amma takasa.
Don haka kullum gidan Alh isyaku cikin fada da tashin hankali yake, wanda kuma lnna Rakiya ce mai tada fadar duk dacewa ita Inna Halima bata biye mata amma kullum cikin masifa take, wanda abin yana matukar damun Alh isyaku saidai kuma ba yadda ya'iya da'ita domin itadin irin matan nan ne dasuke zama jaraba ga miji Kai! harda al'uma wanda bamai iyayin maganin su saidai Allah,
Haka dai akayi rayuwa agidan Alh isyaku da dadi ba dadi Kwatsam Wata ranan juma'a sai akawayi gari lnna Halima ta mutu, mutuwar data girgiza mutane musaman mijinta da d'anta domin lafiya lau aka kwanta, da'ita saidai kawai aka bude daki aka iske rai yayi alinsa, haka akayi jana'izarta akaita gidan ta na gaskiya. saidai kuma wani abin al'ajabi shine ranan da lnna Halima tayi kwana uku da rasuwa,
"toh aranan ne kuma Alh isyaku shima yarasu Allahu Akbar Allah mai ikon,
Aranan kam yusufu kamar zayayi hauka saboda tsabar tashin hankalin daya shiga Na rashin iyayansa alokacin daya, saidai kuma babu yadda ya'iya da abinda Allah ya kaddara masa sai hakuri, haka shima Alh isyaku aka kaisa gidan sa na gaskiya. Saidai kuma tun bayan mutuwar Alh isyaku da Inna Halima yusufa yake fuskar matsala agurin Inna Rakiya sannu ahankali tamai dashi tamkar bawa, duk wani aiki shita kesawa, harda aikin da ya kamata su Harira suyi amma saita nasashi yayi dayayi magana sai tace aure zasuyi kuma idan suka tafi shi zaya cigaba dayi don haka dole sa yayi, kiyo kuma dama shikeyinsa.
Bayan anyi auren su Harira sai aiki yakaru sosai saida kuma ahaka yake samun lokaci yana zuwa makaranta allo, ba tareda Inna Rakiya tasani ba ahaka har yasauke al'qur'ani, aranan dataji tayi masifa sosai tace wai ya munafurce ta tunda har yasauke al'qur'ani ba tareda tasani ba shidai baice komai ba, domin shi bama'aboci magana bane.
hakan yasata takarajin tsanarsa a zuciyarta domin tarasa yadda zatayi dashi duk hanyar datasan zatabi don taga bayansa tabi, amma abunya agagara don haka ta karaninka masa azabar wahalar aiki fiyeda Wanda yakeyi, ahaka rayuwa tamika duk sa'anninsa sunyi aure amma ban dashi duk yarinyar dayaje neman auren ta, sai taje gidansu yarinyar tace karsu kuskura suba shege yar'su domin shidin shege ne da cikinsa Halima tashiga gidan Alh Isyaku, abun mamaki shine babu Wanda ya karya ta wannan sharri da Inna Rakiya tayiwa Yusufa.
Haka Yusufa yacigaba da rayuwa cikin wahala yayinda yadaina Neman auren gaba daya, mlm Babuga wani bafullace ne yanada ya' maisuna lndo kyakkyawa ce mahaifiyarta tarasu "toh matar daya aura mai suna Larai saitana bata wahala shi kuma yarasa yadda zayayi da'ita domin itama halinta irin na lnna Rakiya ne, Wata rana yusufa yadawo kiyo saiya hadu da mlm Babuga sai yatsugun'na ya gaidashi cikin farin ciki ya amsa tareda cewa yusufa dama inason ganin ka,
Yusufa yace "toh Baffa gani Allah daiyasa lafiya? yace lafiya lau yusufa, nidai nayaba da hankalinka da kuma nutsuwar ka, don haka nayanke shawara daura maka auren ya'ta lndo, Yusufa yai shuru.
Mlm Babuga yace Yusufa naji kayi shuru kodai baka sonta ne?..dasauri yusufa yace wlhy Baffa Ina son ta saidai banida halin yin aure kuma kasan anceni din shegene, taya zaka aurawa yar'ka wanda bayada uba?.dasauri mlm Babuga yace kul! nasake jin kakira kanka shegene, waye bai sanan cewa Alh isyaku ne mahaifika bane?..saidai kawai a kifada saboda masifa Rakiya,
Don haka nidai nariga nabaka Indo kuma bana bukatar "KO sisinka dama dai sadaki shine aure ko?..yusufa yace "eh, yace "toh nizan baka gobe in Allah yakaimu kazo kofar gidan mai gari za'a daura auranka da "Indo kuma kar ka kuskura kafadawa Rakiya kabarta kawai saidai taganka da matar ka kaji ko?..,yace "toh Baffa nagode aranan yusufa kamar zayayi kuka saboda farin ciki don haka yaita zubawa mlm Babuga godiya.
Washegari juma'a aka daura auren Yusufa da Indo ba tareda anyi shela ba kuma Larai da Rakiya basu saniba, domin maigari yahana a fada masu, bayan angama daurin auren sai mlm Babuga yace da Yusufa yaje yagyara daki anjima yazo yadauki matar, yace Baffa ai dama dakin bawani gyara daza'ai masa yace "toh madallah anjima saikazo kadauki matarka kayanda zatayi aiki kuma zan kawo mata suda kaina, yace "toh Baffa nagode Allah yasa kasa alkhairi yace babu komai tashi katafi.
Bayan sallah isha'i Yusufa yaje yadauki matarsa lndo suka nufo gida, lnna Rakiya tana zaune atsakiyar gida tana cin abincin, suka shiga da sallama bata amsaba yusufa badamu ba domin yasan itadin bama'abuciya amsa sallama bace, don haka sai kawai suka nufi dakin shi cikin matsanancin mamaki tace kai! Yusufa,
Tsaya yayi tareda cewa na'ama Inna, tace "eh lallai abinda ake fada da gaske ne domin kuwa yau gashi har gidana za'ayi nagani, "toh wlhy baka'isaba kayi kad'a, gani inda zancenta yadosa yasa dasauri yace lnna Rakiya wlhy bana neman mata, cikin masifa tace Kai kaniyarka ga karuwa kashigo mun da'ita cikin gidana amma kace mun kai baka neman, mata..
yace lnna wlhy ba karuwa bace, duk da cikin duhu ne hakan bai hanata zagba masa harara ba tareda cewa, "Oho wato ita wannan din uwar kace "Halima tafifo daga kabari tabiyo kako?..cikin sanyi murya yace lnna Rakiya lndo ce yar'gurin Baffa Babuga dazu aka daura mana aure, cikin matsanancin bala'i da tashin hankali tamike tanufi gurinsa hartana kokarin faduwa tace..
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE*_(Labarin Sadeeya)
Tareda Alkalamin
โ๐ฝ
๐นLufhat ce๐น
[7/2, 11:26 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
6โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*ga SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
_*Wannan nan page gaba dayan sa nakine my sister Shafa'at, kiyi yadda kikeso dashi nagode sosai da kulawarki agareni inayinki irin over din nan fa*_๐
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
Kace me?..yace an daura mana aure dazu, cikin masifa tace kan uban can nizaka munafurta shine kayi aure ba tareda sani naba wato shanu na kadauka ka siyar kayi aure KO?.. "toh wlhy baka isaba sai kabiyani shanu na kuma bazaka zauna agidan nan ba...dasauri yace wlhy Inna ban daukar maki shanu ba KO daya ba, tace "toh ubanwa yabaka kudi kayi aure?.. yace wlhy Baffa Babuga yabani auren lndo ba tareda kosisi naba, tace "toh yayi kyau kutashi kufita mun agida.
Da sauri ya tsugun'na tareda cewa don Allah Inna kiyi hakuri, kirufa mun asiri kibarni Na zauna da matata kinsan cewa banida gidan daya wuce wannan, shewa tayi tareda cewa Allah sarki ai yanzu kam kanada gidan dayafi wannan, don haka kadauki matar taka kutafi can gidan ubanta daya baka aurenta Ku zauna agidansa amma banan ba, rokon ta yake akan tabarsa yazauna amma takiya, sai mafa man yimasa masifa take.
Aikam nan da nan gida yacika da mutane, ana tambayar meya faru Yusufa yafadi, nan akaita bata hakuri akan tabarshi ya zauna da matarsa amma tace Sam saidai yakoma can gurin "mlm Babuga kamar yadda yabasa mata "toh yabasa gurin zama, amma banan gidan taba.
Wasa-wasa saida aka Kai ruwa rana da lnna Rakiya sannan tabari suka shiga dakin, koshi saida maigari yazo yace idan bata kyalesu ba sai yafitar da ita daga garin sannan tabarsu.
Acan kuma gidan mlm Babuga Inna Larai tasashi gaba da masifa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 42