haka tashi ki kiramani shi na nemi gafararsa" tunkafin na mutu domin wannan ciwo bazaya barni ba,
Cikin sanyi murya Lanti tace toh" lnna amma kibar fadin haka ai cuta ba mutuwa bace, tace kayya kedai tashi kidubo shi kar yatafi ban roki gafarar shi ba, jiki asanyaye tamike tareda cewa toh" Inna, tana fita tsakar gida saitaji sallama don haka sai ta tsaya.
Da sallama Yusufa yashiga gidan lndon nabiye dashi yayinda su Alh ke biye dasu a baya, Lantin kam mamaki ne yakamata naganin da gaske ashe Yusufan din ne abunda batayi zato ba,
Don haka dasauri takoma daki tana cewa lnna ashe mairo da gaske take ga Yusufa nan yadawo, kokarin tashi lnna Rakiyan takeyi tana cewa ina yake isuhu..? dasauri Lanti ta matsa gurinta tareda dagata tasa mata filo a bayanta yadda zataji dadin jingina tana cewa gashi nan waje bari nace sushigo,
Shi kam Yusufa tsaye yayi cak! yana kallon garken shunu wayanda basufi guda goma ba, juyawa yayi fuskarshi dauke da matsanancin mamaki ya kalli lndo wacce itama fuskarta daukeda mamaki take kallon shi, harzayayi magana sai ga Lanti tafito fuskarta daukeda farinciki tana cewa sannun ku dazuwa Yusufa ku karaso mana bari na dauko shinfida, dasauri yace toh" Adda Lanti Alh ku karaso, sukace toh" tareda karasa shiga daga ciki dai-dai lokacin da Lanti tadauko babbar tabarma,
_Lanti kam tayi haka ne domin dakin babu abunda yakeyi sai tashin wari da tsami, wanda bakowa ne zaya iya shiga dakin ba_
tashin fida masu, tana tayi masu sannu dazuwa bayan sun zazzauna sai takawo masu ruwa suka sha sannan tazauna suka gaisa
Bayan sun gama gaisawa, sai Yusufa ya gabarar da Alh da iyalain, sannan yace Adda Lanti lnna Rakiya banganta ba sannan kuma meya faru naga duk shanu sun kare...? Kuka Lanti tafashe dashi tareda cewa Yusufa maganar shanu labari ne me tsawo,
Sannan lnna kuma tana cikin daki batada lafiya tsawon wata uku kema bata iyafita ko'ina don haka kashiga kaga yadda Allah yamaida ita, wanda kuma nasan alhakin Kane ya kamata harma damu gaba daya,
Jiki asanyaye Yusufa yamike tareda cewa Alh kushigo bamusu suka shiga dakin saidai kuma tuni suka fara toshe hanci saboda wari, da sauri *Habeeb* yajuya yafita daga daki hannun sa toshe da hancinsa yayinda yan'uwansa suka rufa masa baya, domin shi mutun ne da yatsani wari arayuwar sa, suna fita tsakar gidan *Habeeb* yasaki ajiyar zuciya, dariya Rahma tayi harara yawatsa mata aikam tuni ta tohe bakinta domin tasan shi baya son raini,
Suma su Abba Bayan sun gaida lnna sai suka fito don da alama bazasu jure shakar wannan warin ba.
Shi kam Yusufa ya tsorata dagani yadda lnna Rakiya takoma cikin watanni uku kacal dayayi bayanan, tarame tayi baki idan bakayi mata farin sani ba bazaka taba ganeta ba domin kamanita yasake sai takoma Kamar mutun ba, dasauri Yusufa yace Adda Lanti meyasa mu lnna Rakiya haka..? cikin kuka tafara bashi Labarin kamar haka.
Ina zaune sai ga mairo diyar Hajjo tazo da gudu tana cewa Adda Lanti kizo ga Innnar su Jauro can tana bugun Innar ku Dasauri Na tamike na sauki gyale, na nufi gida koda na'isa gidan na'iske lnna kwance atsakar gida sai nishi nakeyi dasauri na daga ta tareda kamata muka shiga daki, sai nake tambayar ta me yahadata da Kulu nan tafada mun, raina abace Na tashi zanje gidan Kulu naimata tijara amma sai lnna tahanani saidai tace nadora mata ruwa zatayi wanka,
haka nafada mata ruwa Ina masifa da Kulu tareda zaginku kaida lndo har najuyema mata ruwa taje tayi wanka, tafito ban daina masifa ba dama nadora karin kumallo bayan nagama hada Karin kumallo ina cikin zuba mata saiga Harira da Mari, nan dai muka hadu muna ta zaginku saida muka gama sannan ko wacce tanufi gida,
***********
Bayan kwana biyu sai lnna ta taramu take cewa toh" yanzu wanene zaya ringa zuwa kiwon shanu...? shuru mukayi domin bamusan waza yaringa zuwa ba, can sai nace mezaya hana aba Babuga mijina tunda yanzu babu abunda yakeyi inyaso sai aringa biyanshi, sukace toh" shikenan lnna tasa aka kirashi tayi masa magana yace toh" shikenan.
Washegari Babuga yakora shanu zuwa kiwo
wanda saida lnna ta kirgasu tsaf kuma agaban shi sannan yatafi, koda Babuga yadawo lnna ta kirga shanu saitaga babu guda biyar koda ta tambaye shi" sai yace shi besan inda suke ba, takaraci masifarta ba tareda yasake ce mata komai ba washegari Babuga yasake zuwa Inna tasake bashi shanu yatafi kiwo, Kai natakaita maka idan yau Babuga yaje kiwo sai yabatar da shanu biyar KO" fiyeda haka gobe ma haka,
Kai haka nan dai yaci gaba da daukar shanu yana zuwa kiwo yana kuma batar dasu wani abun mamaki kuma tun fadan da lnna taimasa bata sake cemasa komai, abun kamar asiri mu dinma babu wacce tace masa komai saidai zuciyoyin mu cike yake da tambayr inda yake kai shanu, ahaka dai har shanu suka rage guda arba'in ranan dayaje kiwo nakarshe sai yadawo da shanu guda ashiri lnna kam tana ganin shanu sun rage yan'kadan tayan ke jiki tafadi,
Haka muka dauke ta zuwa asibin birni
Bayan Likita ya duba ta sai yace mana barin jikinta
yasamu matsala ma'ana yadaina aiki,
munyi kuka sosai da mukaji haka amma sai Likita yace mu kwantar da hankali mu zataji sauki inda har zamu ringa siya mata magunguna, mukace zamu siya mata shanu biyu muka dauka muka siyar muka siyama lnna magani, wani abun mamaki kuma shine me makon muga sauki a ah sai sannu ahankali ciwon lnna hake karuwa, kuma tana shan magunguna wanda kuma shanu muke dauka muna siyarwa muna sai mata magani, har shanu suka rage guda goma kuma babu wani sauki,
"Kwanan mu hamsi acikin asibiti aka sallame mu tunda babu wani cigaba likitoci sunata mamakin ciwon lnna da yakijin magani haka
muka dawo gida muka cigaba dajinyar ta, Bayan nadawo ne kasan cewar nice yanake jinyarta Mari da Harira kuma suke zuwa su wuni, sai nakeji jin wai ashe Babuga acaca yaitasa shanun mu anacin yewa
aikam nace sai yabiya mu, yace" bazaya biya ba kuma yasake ni saki uku haka nadawo gida ina kuka na fadawa lnna itama kukan tafarayi ba tareda tace komai ba, kasan cewar bata son yin magana tunda kotayi baji ake sosai ba.
Washegari tunda safe saiga Harira tashigo da kuka wai Sale yasake ta Saki uku batayi masa komai ba, kuka muka saki dukkan mu harda lnna saida mukayi mai isarmu sannan mukayi shuru nace oh! Allah meyake faruwa damu haka, dakyar lnna tace tabbas alhakin kane yakama mu don haka tanaso mu kula maka da shanun dasuka rage idan kadawo mubaka, sannan muroke ka kayafe mata abunda taimaka domin tanagani wannan ciwon bazaya bar taba haka muka cigaba da jinyar lnna nida Harira Wanda har yanzu gatanan kamar kullum,
kuma tun ranan da tafadi mukula maka da sauran shanu bata sake magana ba sai yau da mairo tace gaka can kazo, don Allah Yusufa kayafe mana abunda mukai maka itama lnna kayafe mata domin tabbas alhakin Kane yaketa binmu.
Zufa Yusufa ya share tareda cewa Adda Lanti nayafe maku
Cikin murya me dauke da tsantsar nadama lnna Rakiya tace isuhu maso kusadani na nemin gafarar ka,
ahankali yamatsa tareda cewa sannu lnna, tace yauwa isuhu don Allah kayafe mun kaji kona samun saukin wannan ciwon, yace bakomai lnna Allah yabaki lafiya nima kiyafe mun, tace a ah isuhu nibakai mun komai ba nagode kaji Allah yaimaka albarka Ina lndo..?
yace gata nan tace kiyafe mun kinji..? tace lnna nayafe maki Allah yabaki lafiya tace ameen nagode Allah yaimaku albarka, sai kuma tafara wani irin tari me karfi dasauri Lanti tadauko ruwan magani akwano tabata tasha tareda cewa sannu lnna Kai kawai ta gyada sai kuma wani yasake zuwa sosai take tarin can kuma sai tabari sai tafara fisge-fisge, yayinda Lanti take fadi sannu lnna can sai idanun ta suka kakkafe sai jikinta yasaki, cikin matsanancin tashin hankali Lanti tace....
_*Kuyi hakuri da rashin ganin posting dina dawauri wani uzuri ne ya tsayar Dani*_
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE*_(Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นLufhat ce๐น
[7/2, 11:27 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
๐
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem!*_
Inna tareda girgiza ta saidai ina da alama rai yayi halinsa๐ fahimtar hakan ne yasa Lanti sakin wani irin kuka ๐ญtareda cewa don Allah lnna karki mutu kibar mu kinsan bamu dakowa saike, dai-dai lokacin da Harira tashiga dakin cikin tashin hankali tace shikenan tamu ta same mu sai kuma tafashe da kuka.
Cikin matsanancin tausayi Yusufa ya girgiza kai tareda cewa _innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un!_ dai-dai lokacin da wasu hawaye suka gangaro masa a fuska sakamakon tunawa da mutuwar iyayansa wanda yaji tamkar lokacin ne abun yafaru, dasauri yashare hawayan tareda sa hannun yashafe fuskar lnna Rakiya,
Cikin sanyi murya yace Adda Lanti ba kuka yakamata kuyi ba addu'a zakuyi mata cikin kuka tace shikenan bamu dakowa, yace Allah shine kowan mu sannan yafita don yasanar da su Alh wanda yake da tabbacin sunji abunda yafaru kodan kukan dasu Lanti sukeyi.
Cikin kankani lokaci ashirya lnna Rakiya aka kaita akabaro daga ita sai halinta, sai da misalin 5:00pm sannan su Abba suka tafi sukabar su Yusufa inda Abban yabashi kudi masu yawa saboda yasan zasu bukaci wani abun, sannan ya tabbar mashi da cewa sai bayan kwana biyu zasu dawo sutafi tare, yana nufin sai ranan addu'ar bakwai kenan Yusufa yayi masa godiya sannan suka tafi, kamar yadda Abba yace hakan KO" akayi.
*********
Ranan asabar wanda yakama kwanan lnna Rakiya bakwai da rasuwa, tunda misalin 8:00Am su Abba suka isa gudum fulani don ayi addu'a dasu yayinda su Adda Lanti sukayi masu tarba mai kyau, bayan anyi Addu'a sai Abba ya umarci direban shi daya bude but yakwashi kayan dasu kazo dashi yashiga dasu cikin gida, wato buhun masara ne da gero da dawa da kuma shinkafa.
Yusufa kam harda kuka yayin don farin ciki abunda Abba yaimashi, cikin dan bacin rai Abba yace a ah mlm Yusufa nifa banason haka don nayi maka d'an wannan abun shine kake kuka..? yace yi hakuri Alh farin ciki ne yasani kuka amma tunda bakaso insha'allahu bazan sake ba, Abba yace yauwa aini banason naga hawayan kane kawai idan nayi maka abu kaji dadi toh" kayimun Addu'a sai nima naji dadi, kuma ma aiba wani Abu bane don nayiwa dan'uwana alkhari KO...?
Yafadi hakan ne tareda rike hannu Yusufa yayinda fuskar shi dauke da fara'a shima Yusufa cikin fara'a yace hakane, Alh nagode sosai ubangiji yasaka maka da alkhairi ya albarkaci zuri'ar ka addu'a kuma tun ranan da Allah ya hadamu dakai nakeyi maka ita", saidai zan ninka addu'a ta agareka insha'allahu Zan cigaba da yi maka addu'a daganan har karshen numfashi na domin alkhairi ka agareni mai girma ne,
Cikin farin ciki Abba yace nagode sosai Allah yabar mu tare duka suka amsa da ameen fuskokinsu cike da farin ciki tareda kaunar juna, saida sukayi sallah la'asar sannan suka Kama hanyar komawa cikin garin Bauchi Bayan Abba yabasu Lanti kudi meyawa, yayinda shi kuma Yusufa yayima su alkawain cewa insha'allahu zayaringa kawo masu ziyara lokaci-lokaci, sukace toh" tareda cewa ya tafida shanun shi sai yace masu a ah sudai cigaba da kula masa suka ce toh" sannan suka tafi.
**********
Sannu ahankali komai yake tafiya yadda ya kamata, yayinda kauna da aminci tareda yarda me karfi yake sake shiga tsakanin Abba Yusufa harma da Al-mustafa, kamar yadda Yusufa yace zaya riga zuwa yana gani su Adda Lanti toh" haka yakasan ce,
Wanda Abba ya tsara zuwan duk bayan sati biyu ranan Jumma'a idan sun dawo sallah sai suje gidansu a Al-mustafa su gaida iyayansa kasan cewar shi nan cikin Bauchi iyayansa suke kuma tareda dasu yake zaune da matarsa daya Hadiza da yaransu biyu mace da namijin wanda yake tsaran *Habeeb* ne mesuna *Hareesu* mace kuma Zakiyya.
Ranan asabar kuma sai su shirya dukansu su tafi gudun fulani kuma da shatara na arziki suke zuwa, ranan Lahadi kuma sai su shiryasu tafi Soroh garinsu Abba kasan cewar maifan Abba suna nan darai mahaifima shine sarki fulanin Soroh, kuma Abba yayi-yayi dashi sudawo cikin garin Bauchi da zama amma sun kiya, shiyasa ya kyale su saidai koda yaushe yana kaimu ziyara tareda abu arziki me yawa, haka dai suka cigaba rayuwa abun gwanin sha'awa.
*_Bayan shekara goma_*
***************
Abubuwa da dama sun faru damasu dadi da akasin hakan, bayan mukamin da majalisa da Abba ya yarike ya kuma yi senate alokacin kuma shekaran shi daya da hawan kujerar gwamna, Mamu tana gama ss3 akayi mata aure kasan cewar tsarin Abba kenan y'a mace baza taci gaba da karatu agidan saba saidai gidan mijinta idan ya yarda, don haka itama Rahma tana gama ss3 akai mata aure shikam *Habeeb* cigaba yayi da karatun sa tunda shi namiji ne, Hajiya Rabi'atu kuma tasake haihuwa tafaifi namiji wato *Hafiz* alokacin ma shekaran shi shidda tundaga shi kuma bata sake haihuwa ba.
Alh Al-mustafa wanda yaran suke Kira da Baffa Al-mustafa, shima matarsa ta sake haihu yara biyu duk maza sanna shima yabi tsarin Abba, Zakiyya tana gama ss3 yai mata aure,
Baffa Yusufa kuma Wanda yaza'a kirashi da Alh mlm Yusufa ๐ tunda yayi kudi dai-dai gwargwadon yaje makka shida lnna lndo, wai Hajiya Aisha๐ kuma yakai Adda Lanti da Harira wacce daga baya tadawo gurin shi da zama har tasamu miji tayi aure tanada yara biyu mace da namiji,
_saidai ita kam Mari tarigamu gidan gaskiya gurin haihuwa tarasu_๐ญ,
Sannan kuma burin shi yacika yasamu ilimin Addini sosai yazama shahararran malamin Addini wanda akeji dashi a garin Bauchi,
kuma shine limanin Wata BABBAN masallaci da Abba ya gina alokacin kuma shine babban _ _special adviser_ na gwamna, wato shiyake ba Abba shawara me tsafta, tsawon shukarun nan babu abunda Baffa Yusufa yanema yarasa arayuwarsa sai haihuwa๐ita kam Allah bai bashi haihuwa ba tun yanasa rai har yafitar.
Kwatsam Rana Wata laraba sai Inna Aisha ta tashi da zazzabi mezafi Baffa yafadawa Abba shikuma Abban yasa aka Kira masa likinta, koda likitan yaduba ta baya yan gwaje gwaje tareda tambayoyi yagane tana dauke da ciki har Na tsawon Wata biyu, wai zokaga farin ciki agurin wayan nan bayin Allah, yayinda Abba da Baffa Al-mustafa sunkai matukar murna domin dama suma rashin haihuwar sa yana damunsu sosai shiyasa ma Abba yabashi *Hafeez*.
wani abun mamaki kuma shine itama Hajiya Rabi'atu sai ga ciki Wanda za'a iyacewa lokaci daya suka same shi ba tareda sun sani ba, don haka farin ciki yakaru domin itama da har tafidda rai da sake haihuwa, haka nan suka cigaba da rainon cikinsu cikin farin har' Allah yasauke su lafiya,
Ranan Jumma'a lnna ce tafara haihu da safe misalin karfe goma, yayinda ita kuma Hajiya ta haihu da yamma kuma duka mata suka haifa kwawa dasu kamar y'aya'n larabawa musamman ma Y'ar gurin lnna, murna kam ba'a magana musamman agurin Inna da Baffa Yusufa wanda shi kam saidai yayi lafiya Na godiya ga Allah da yabashi wannan kyakkyawa *KYAUTAR*.
Koda suka haihu *Habeeb* yana makaranta tun 8:00am daya tafi bai dawo ba sai 5:30pm sannan yadawo, yana shiga shashin su ya'iske Hajiya zaune rikeda jaririya dasauri yakara sa gurinta yana cewa Hajiya kin haihune..? tace "eh tareda mika masa jaririyar fuskarsa cike da farin ciki ya karbe ta tareda cewa sannu, tace yauwa yana kallon kyakkawar jaririyar yace Hajiya munyi Kama da'ita ko..?
murmushi tayi tare da cewa haka Abbanku yace, kaje ka gaida lnnan Ku itama ta haihu tunda karfe goma na safe, dasuri yace itama mace tahaifa..? tace "eh jiyayi gabansa yafadi sosai wanda yarasa dalilin dayasa yaji hakan, tace kawota kaje ka gaida "ita bayan takarbi jaririyar sannan yanufi shashin su Baffan,
Da sallama yashiga lnna ta amsa fuskarta dauke da fara'a tace mlm *Habeebu* yan makaranta nadawo..? yace "eh lnna sannu tace yauwa ya karatu.. yace lafiya qalau, Hajiya tace kema kin haihu murmushi tayi tare da mika masa jaririyar tashiga daki, shi kam *Habeeb* yana karan ban jaririyar yaji wani abu _garrrrrrr! kamar shocking_ tun daga tsakiyar kanshi har zuwa babbar yatsar kafarsa, yayinda yaji kirjinsa sai bugawa yake da sauri da sauri,
tsurawa jaririyar ido yayi tsawon wani lokaci domin shikam tunda yake bai taba gani jaririya me matukar kyau irin wannan ba, lnnan ce tafito da'alama wanka zatayi dasauri yace lnna gata Allah ya yara karban jaririyar tayi ba tareda tace komai ba, dasauri *Habeeb* yafita shashin suya nufa zama yayi nesa kadan da Hajiya yana sauke numfashi kallon shi tayi tareda cewa ka gaida "ita..? yace "eh Hajiya saidai jaririyar nan da lnna tahaifa ba *MUTUM* bace cikin matsanancin tsoro Hajiya tace....?
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE* (Labarin Sdeeya)_
Tareda
โ๐ฝ
๐นLufhat๐น
[7/2, 11:27 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ2โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem!*_
Ba nace kar kusake shigo mun dakiba....? cikin tsoro ta gyad'a kai alamar "eh, harara ya watsa mata tareda cewa wato saboda bakin jin magana shine kika shigo KO"...? ciki kuka tace Hamman *Hafeez* ne yabiyoni zaya doke ni, shine yaki shigo mun daki don kin rai nani harda wani rikeni saboda baki da kunya KO...?๐ก
Cikin kuka shagwaba tace yi hakuri, yace dalla rufemun baki aikam tuni tayi shuru tareda tsura masa oil eyes dinta, masu matukar kyau da tsuma zuciyar me kallon su rankwashinta yayi akai tareda cewa daina kallona da wannan idonun naki mekama dana aljanu,
Dasauri tadukar dakai yayinda hawaye keta siyaya akasa, cikin tsawa yace meyasa kika bata masa littafi...? cikin kuka tace shine yake cemun _*KYAUTAR 'BERA*_ harara ya watsa mata tareda jan tsaki mtww yace ance kyautar bera din sai me to...? kuma idan kika sake bata masa littafi sai na zaneki,
aikam tuni tasake sakin kukan shagwaba, cikin tsawa yace dalla fita kiba mutane guri, kuma idan nasake ganin kafarki a dakin nan har hannun ki yayi kuskuren sake tabani sai na karya maki kafa da hannu, da gudu tafita tana kuka.
*Harees* da tunda suka fara yake tafaman dariya yasauko daga saman gado da sauri yabi bayanta yana kiranta, amma takin tsayawa sai tafita take tana kuka tareda bubbuga kafa, irin na shagwabab'bu yara dasauri ya riko hannuta yace haba *Sadeeya an baba* Queen of beauty tsaya mana, _kasan cewar haka yake kiranta_
tsayawa tayi saida kuma tana cigaba da kukan, yace Hamman *Habeeb* ne ko...? kai ta gyada yace yi hakuri kyaleshi kinji ai daga yau bazaya sake saki kuka ba, tunda gobe zamu tafi U.K kuma sai mun dade kafin mudawo, cike da yarinta tace Hamman *Harees* kar kudawo kaji...?
yace toh" amma hardani fa kenan...? tace a ah kai kadawo shi ka barshi can yazauna tunda shi dukan mu yakeyi, yace toh" shikenan, share hawayan kinji tace toh" tareda sharewa yace yauwa hali dubun Hajiya *KYAUTAR* lnna da Baffa koba ita bace..? dariya tayi tareda cewa nice, shima dariya yayi yace ni nasani amma yau ina Sofee..? tace tana part dinsu yace toh" sannan ta tanufi part din su tana tsalle kamar da'ita tayi kuka ba.
Shikam *Habeeb* fadawa yayi saman gadon tareda sauke nauyayyan ajiyar zuciya, ahankali yafurta yah ilahee! Kai! gaskiya wannan yarinyar kam aljanace,
dai-dai lokacin da *Harees* ya shaga daki ya amsa dacewa Queen of beauty ba aljana bace mutunce tamkar Kai, tsaki *Habeeb* ja mtww! tareda cewa idan ba aljana bace yaza'ace duk lokacin da naganta sainaji faduwar gaba idan kuma nataba ta sai naji wani irin abu yana yawo ajikina,
dariya *Harees* yayi tareda cewa toh" amma dai Kai kadai kakejin hakan KO....? saboda nidai banajin komai kaga yanzu nan ma Dana tsaya kusa da'ita har hannun tana rike banji komai ba da,
tsaki *Habeeb* yasake yi tareda cewa kagani ko" aljanace mayyar yarinyan kawai nitakeso takama, shiyasa take tayi mun siddabaru iri-iri saidai kuma nidin Nafi karfinta,
gobe ma barin garin zanyi kaga sai taje kuma tayima wani, siddabarun nata amma bani *Habeebullah* ba.
shikam *Harees* dariya yake harda rike ciki saboda jin abunda *Habeeb* din yake fadi, cikin dariya yace toh" ai da aljani da maye ko'ina kaje cikin duniya sai sunbika,
harara *Habeeb* ya Watsa masa yace au hakane..?.yace tabbas yace toh" shikenan duk aljanin da mayen da ya'isa ya biyo ni U.K idan banyi kasa-kasa dashi acan ba,
yace dalla nidai ka taso mutafi nagaji da maganar wannan aljanar yarinyar, yafadi tareda nufar kofa zaya fita yayinda *Harees* yabi bayanshi yana cewa hhhh! Yaro zakasha mamaki domin tabbas sai sun bika har U.K.
Washegari Jumma'a jirginsu *Habeeb* yatashi zuwa U.K.
*********
Akwana atashi ba wuya agurin Allah kwana kin sun tafi har zuwa shekaru, tun dasu *Habeeb* suka tafi basuzo hutu KO" sau daya ba, saidai waya kawai sukeyi da mutanan gida,
Haka zalika komai yafaru agida sai anfada masu har da minister da shugaban kasa yana Abba saida aka fada masu, tunda alokacin ya sauka daga kujere governor Wanda mutane Sam basu so ya sauka ba saboda adalcinsa agaresu,
A haka dai tafiya ta tafi har su *Habeeb* suka gama karatunsu, suka dawo cike da nasaran abinda sukaje nema,
sun zama cikakkun samari kwawa masu cike da kwarjini, sun iskesu su *Sadeeya* sunyi girma sosai inda suka koma *Deeya* da *Feeya* saboda yawan kallon India films Da sukeyi, anan ne sukaji sunan sai sukace wai ai sunan sune a kayan ke don haka suma deeya da feeya zasu ringa kiran junansu,
sun Fara zama yan mata tunda lokacin suna jss1 har sun mafara kirgen dangi,๐ mamaki sosai *Harees* yayi da ganin yadda suka girma, saifaman washe baki yake yana fadin gaskiya kannaina kunyi sauri girma me Hajiyarmu da lnna suke baku kunaci haka ne...?
dariya sukayi ba tareda sun ce komai ba, shima *Habeeb* mamaki yayi amma dai bece komai ba saidai kawai yatabe baki, ganin saifaman wani rawar kai sukeyi ko" don sunga yan wannan kushashin dasuka fara fito masu ne Oho!๐kuji *Habeeb* fa.
**********
Bayan Wata daya da dawowar su sukafara aiki akamfani da Abba ya gina, cikin kwanciyar hankali suke gudanar da aikinsu, ranan wata alhamis sunfito cikin shirinsu nazuwa gurin aiki kamar yadda suka saba,
Cikin nutsuwa suke tafiya suna fira abunsu gwani sha'awa, har suka isa gurin ajiye motoci sai *Habeeb* yami kawa *Harees* key motar da zasu shiga, harara shi yayi tareda cewa wato kana nufin yauma nizanyi driving dimu..?Kai *Habeeb* ya gyada alamar "eh *Harees* yace toh" bazan yiba,
cikin sanyi murya yace haba nawa yi hakuri mana, *Harees* yace naki wayon *Habeeb* yace banajin dadi ne shiyasa kasan Allah ko" office dinma dole zanjeshi saboda takardun jiya daka kawo mun banga ma cika suba,
yace kuma saika cikasu ba murmushi yayi tareda cewa dolema, yanzu dai karbi kaja mutafi karban key yayi tareda cewa toh" wai meke damun kane...?
Maimakon yayi magana sai yasaki wata kara tareda rike ciki, saikuma yafadi kasa dasauri *Harees* yanufeshi saidai koda ya dagashi baya numfashi, cikin matsanancin tashin hankali yace...?
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ1โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 42