Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
akan gallery yake, Wuce wannan hoton yayi yaje wani inda take kan doki nan ma dariya take tana rike da linzamin dokin, murmushi yayi yanajin son ta da kaunar ta suna sake ratsa sassan jikinsa, shima wuce shi yayi sannu hankali yaketa wuce hotunan wasu tareda shi suka dauka wasu kuma ita kadai. Cak! ya tsaya akan wani hoto datayi mugun kyau dariya yayi saka makon tunowa da lokacin daza yadauke ta, Cikin yanayin tana shagwaba tace sweet Hmm na zan kwaso shoki saika dauke yi, aikam tana kwasowa yana dauke ta tana dariyar nan nata me matukar burgewa da kara mata kyau da kwarjini. Ahankali yajingina bayan sa da kujerar tareda lumshe ido yana sakin lallausan murmushi, ahankali yake juyi akan kujera ya naji wani irin tsananin kaunar ta tareda matsanancin sha'awar ta suna bin jinin sa, wanda har yanajin kamar yayi tsuntun yanzu yaje gareta, idonsa yasake rintsewa saka makon tunowa da yana yinda suka kasance jiya kafin yataho wani irin yarrrrrrrr! tsikar jikinsa tayi hakan yasa yafurzar da wata iska me zafi ta bakin sa, Tabbas yasan shi mutun ne me matukar sha'awa saidai tun lokacin da ciki ya bayyana ajikin *Leemarsa* sha'awar sa takaru, a koda yaushe so yake yajishi a tareda ita domin jiyayi kamar anakara mata ni'ima gashi dai jiya suka rabu amma yanzu wani irin matsanancin feeling dinta yakeji tareda son kasan cewa da'ita, ahankali yafurta l need u my honey *Leemah* tareda bude idon sa dasuka rikide daga fari zuwa ja, wayarsa yadauka dake kan table din yajona da laptop sannan yayi calling din layin *Deeya*. *_Bauchi_* ****** Tun 12: 00pm *Deeya* tadawo daga school kasan cewar yau ita kadai taje school din ba tareda *Feeya* ba, kasan cewar cikin taya tsufa haihuwa ko yau ko gobe don har ma yawuci lokacin haihuwar sa, amma haka take zuwa school saidai kuma yau ayi sa'a batada lecture sai ita *Deeyar* kea lecture kuma daya sukayi, shiyasa suna fitowa ta taho gida. Part hajiya tashiga saidai bata nan don haka tafito tashiga part din lnna, saidai ko zama batayi ba lnna tace ta tafi part dinta don haka fito cike dakin haushi abinda lnna take mata, gashi yau tunda ta tashi take jin wani irin yanayi ahaka ta nufi part din ta kamar zatayi kuka, tana shiga yafada toilet tayi wanka tasa wata green riga me hannun shimi iyakar rigar cinyata tafeshe jikinta da turare sannan tadauki laptop dinta tahau kan katafaran gadonta wayar ta jona da laptop assment tayi da kyar domin wani iri take jinta, Bayan tagama sai ta tsurama screen di laptop din ido tana kallon hoton su itada *Habeeb* dasuka dauka akan doki suna dariya sunyi kyau sosai, wani irin son ganin sa take azahiri gefe ta tura laptop din sannan ta kwanta sai juyi take tarasa abinda kemata dadi. Tana haka ne sai kiran *Habeeb* yashigo wayar ta kasan cewar karar datasa masa ta musamman ce, yasata tashi zumbur tareda fadin sweet Hmm na sannan tadaga atare suka sauke ajiyar zuciya, kuri sukayi wa juna da ido cike da kaunar juna kasan cewar video call ne ahankali yakebin tada kallo har zuwa kirjinta da yayi kamar zaya faso rigar ta, ido yarintse ya naji wani irin yanayi sai kuma yabude tareda cewa my honey *Leemah* yakike?.. ahankali tace lafiya lau sweet Hmm na kaifa?.. sai kuma ta fashe da kuka wanda yasashi mikewa zumbur arikice yace meya faru *Leemah* ta wanene ya taba mun ke?..., pls yishuru kukan ki yana taba mun zuciya so kiyi shuru ki fadamu me yafaru?.. Cikin kukan daya ki tsaya wa tace sweet Hmm na l don't know what's happen to me, cike da tsoro yace my honey *Leemah* bakiji wani guri ajikinki yana maki ciwo ba?.. ina nufin kamar cikin ki ko kanki kodai wani guri ajikin ki umuh! fadamu meki kejine?... Cikin kuka tace sweet Hmm na inaji wani irin abu yanayi mun yawo acikin jikina inajin kamar zan mutu pls Hmm na kazo, cikin tsananin tashin hankali yace no my honey *Leemah* ai idan kika mutu nima mutuwa zanyi bakisan yanda nake jinki a zuciya taba ne, Cikin kuka tace nima haka sweet Hmm na pls to ka zo kaji?..dasauri yace to my honey *Leemah* kiyi shuru ki daina kukan gani nan zuwa Insha'allah kibani 30 minute bari naje nahau flight kinji?..tace to sai kaza Allah yatsare mun kai, yace ameen kema haka ki kula mun da kanki kinji ko?.. tace to sannan ya kashe wayar yadauki abin dayake bukata sannan yafita dasauri daga office din. **** *Jana* CE keta faman sauri tana waige waige da'alama tayi abinda tasa bane wato satar fita, dasauri tashige lungun titin ta tari adaida tahau tareda fadi masa inda zaya kai ta wato anguwan su Ado, suna isa tafito dasauri tabiya shi kudin sa tashige gidan. Zaune ta iske shi yayi sha ya yabugu zama tayi kusada shi zatayi magana yafisgota dakarfi yahade bakin su, yafara aika mata da banzan sakonni take tafara mayar masa da martani cikin lokaci kankani suka fada duniyar asararru, saida suka dauki tsawon wani lokaci sannan suka sararawa kansu. Ba tareda ya kalle taba yace inajinki fadi abinda zaki fada,tace *"BB* fa yasake ni; saki uku tsaki yayi tareda cewa ai dama dole ne sai yasake ki, kuma ba saki uku ba idan anayin saki dubu to shi zatayi maki, yanzu ina "yaran suke?..tace yakwace su" dasauri yace har da Junior?.. tace "eh cikin tsawa yace kut! kan uba dan uban "sa to ai Junior ba d'a sa" bane d'a bane, Cike da tsoron ganin yanayin sa tace... *_Barka da Jumma'a yan'uwana_* Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [11/9, 10:08 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 6โƒฃ8โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Haba adona ai nasan "Junior d'an kane bana shiba, to amma tunda yakarbe shi ya zanyi umuh?...wani matsiyacin kallo ya watsa mata me dauke da mamakin jin abinda tace" wai ya zatayi?...cike da bacin rai yace ya zakiyi fa ki kace?...tace to adona ya zanyin mana tunda yariga ya karbe shi, yace to bari kiji nafa maki yanda zakiyi shine ki karbo mun yarona, Cike Da tsoro tace nakarbo shifa kace?...haba adona tayazan karbo "shi tunda ba wanda yasan cewa ba dansa" bane, cikin had'e rai yace "eh idan ba wanda yasani ke aikin sani nima nasani dan haka dole ne ki karbo mun "d'ana dan wlhy bazan taba bar masa gudan jinina ba eheee, Dan baiyyu yuwa ya gama na ka sani sannan yaraba ni "d'ana Don idan bakisani ba yau nasanar dake, shine "mutumin dayasa narasa kafata daya ehee kuma wlhy sai nadau fansa, ido tazaro cike da tsoro tace "eh adona bangane ba me kake nufi ne?... yace "eh nan yafada mata duk abinda yafaru, sannan ya cigaba da masifar sai takarbo masa dansa. *Jana* kam hankalin ta yatashi musamman dataji labarin nan, gashi taga da gaske ado yake wanda idan har ya matsa to asirinta zaya tonu wanda sam itakam bazata taba son haka ba, don haka sai ta kwantar da murya tafara lallashin sa dafadin. Haba adona ka kwantar da hankalin ai "Junior danka ne don haka kamar yadawo gurin ka amma dole sai munbi ahankali, kasan me?... fuska had'e yace inajinki fadi tace kaga nagama idda dama nazo ne nafada maka...... Nan dai *Jana* tafada masa kudirin ta nasan suyi auren kisan wuta, sannan tace kaga idan nakoma sai muyi masa asirin dazaya mallaka mun komai nasa, kagama saina shi yamaida sunan "Junior adukan kadarorin sa kasan Allah adona wlhy *"BB* yanada kudi sosai sunada kamfanin har biyu bayan tulin kadarori dayake dashi, Yana kuma business sosai sannan sunayi tareda wannan shegen *Harees* din kuma wlhy mugun kudi suke samu, najima ance yabude gurin saida motoci irin sababbin yayi masu shegen tsada, shiya nake son nakoma don musamu mu kwashi dukiyar daga nan sai musan yanda zamuyi dashi Inafata ai kaga ne to amma Kaiya kagani?...don wlhy idan bamu mallaki dukiyar naba *"BB* yacuce mu. Shuru ado yayi yana zararin maganar ta aransa yake fadin tabbas haka yaka mata yayi, wanda ta hakan ne zaya mani damar daukar fansa akan abinda shegen yai masa, ajiyar zuciya yayi tareda cewa to naji amma sai nayi shawara tace to shikenan adona amma kamar yaushe kenan?...kaga yanzu Baba ya mugun samun ido baya barina fita saidai idan yafita sai nasato hanya nafito. fuska had'e yace idan naga zan iya nafada maki idan kuma bazan iyaba to shikenan saikije kinemi wani, dasauri tace haba adona zaka iya mana yace humm! to kibani lokaci zanyi tunane sannan yanzu banida kudi kuma banida wayar dazan kiraki, Dasauri taciro wayar ta Nokia acikin jaka tabashi _kasan cewar Barau yasake siya mata wata_, sannan tabashi dubu biyar tace akwai sabon sim card acikin sai kasa kati nasa maka sabon layina kayi mun flashing sainaga lambar, inagani ma kamar akwai sauran kudi aciki haka akayi bayan yayi mata flashing din sai tayi seving sannan suka sake aikata fasikanci su sannan ta tashi ta tafi akan sai sunyi waya to Allah ya shirya. *_Abuja_* ******** *Habeeb* kam yana fita daga office escorts din suka nufi shi Dasauri, Saminu yace barka da fitowa yallabai zamu fita ne?..dasauri *Habeeb* yace "eh tareda mika masa jakar laptop dinsa yace Sir Ina zamu?..yace airport zaka kaini zamuje Bauchi ne yanzu my honey *"Leemah* batada lafiya, dasuri yace subhalallahi! yallabai Allah dai yasa dasauki?... Yace Ina fatan haka zamuje dai mu gani yace to Allah yabata" lafiya, yace ameen Insha'allah gobe zamu dawo Saminu yace to Allah yakai mu lafiya, yace dai-dai lokacin da yabude masa mota yashiga suma suka shiga sai airport, ba tareda bata lokaci ba jirginsu yatashi zuwa Bauchi shida Saminu da sauran escorts din sai direbobi ne suka juya gida. *_Bauchi_* ***** *Deeya* kam suna gama waya da *Habeeb* ta tashi duk da batajin dadin jikin ta haka bai hanata shiga kitchen ba, don ta sama wa *Habeeb* abinda zayaci tunda dama yace mata yau bazaya dauki azumi ba saboda yanajin ulcer sa nason tashi, gashi dama ko banza tasanshi da mugun tsandar abincin waje kilama tun karin safe ke cikinsa. Bat areda bata lokaci ba tayi masa simple girki me kayatarwa irin wanda tasan yanaso, saidai dakyar tagama saboda jikinta kwata-kwata batajin dadin sa. Bayan tagama sai tashiga tayi wanka tayi simply make up sai tafeshe jikinta da turaruka masu kamshi sannan tasa wata riga yellow, me shegen kyau itama me hannu shimi ce kamar wanda tacire, saidai ita wannan takawo mata guiwarta sannan tanada zif ta gaba tun daga sama har kasa sa banin wacan datacire iya cinya sannan batada zif, saboda yanzu ire-iren kayan data kesawa kenan idan tana gida saboda tafi jin fadin su. Bayan ta gama shiryawa sannan tafito falon kasa ta kishingid'a akan kushin me zaman mutun uku tareda daukar remote, ta kunnan kallo tashar zee world takamo tayi sa'a sun sawani India film me kyau tafara kallo tayi tana kallon wayar ta. Su *Habeeb* na sauka sai ya Saminu yakira direba tareda escorts din dake Kai su *Deeya* school, aikam cikin lokacin kankani sai gasu sun isa airport din motoci uku dasauri Saminu ya budema *Habeeb* yashiga suma suka shiga sannan suka ja suka tafi gida. Suna isa *Habeeb* yafito dasauri ba tareda yajira Saminu yabude masa kofaba cikin takun kasaita yanufi part dinsa, yana shiga yafara fidin my honey *Leemah* where u?...Dasauri tamike jikinta har yana karrrrrrma tsabar son taji ta ajikinsa, kuri sukaiwa juna da ido kowa ne yana jin tsanani kaunar dan'uwan sa tareda sonjin sa ajikin sa ahankali yaware mata hannu alamar tazo gareshi. Aikam cikin sassarfa ta'isa tafa dafaffad'an kirjinsa wani iri yar ajiyar zuciya suka sauke me karfi, sai kuma *Deeya* tasaki kuka dasauri yace no no my honey don't crying l'm here with u zo muje ki fadamun meke damu ki, sannan meyasa ya baki kira "dan'uwa yaduba munke ba umuh?.. ya kareshe fadi tareda daukar ta cak! yanufi bedroom dinsa ciki kuka tace komai yacewhy dai lokacin da suka isa cikin bedroom. Kan gadon yakwantar da'ita yayi mata runfa sannan yace haba my honey *Leemah* soki ke wani abin yasa meki ko?.. kai ta girgiza yace to fadamu ina keyi maki ciwo?...tace Hmm na niban saniba, cike da dan tsoro yace yah elahee! to ko baby baya motsine?... yafadi tareda shafa cikin ta daya dan taso kadan, kasan cewar duk cikin yashige cikin kirjinta da hips.. tace Hmm na yanayi ko dazu yanata yi, Yace To kuma bana ce ki daina zama a part din nan ke kadai soboda irin haka umuh?.. amma bakiji ba ko?.. Kindai jin magana ta ko?..my Honey *Leemah* why?.. cikin kukan tace sweet Hmm na sorry bazan sake zama ni kadai ba kaga da nadawo school sai nashiga part din "Hajiyarmu sun tafi anguwa har dasu Lili mama, to shine fa nashiga part din "lnnan mu nafada mata banajin dadin jikina amma sai tace" waina tafi part dina bata ko tsaya nafada mata ba ta kareshe fadi tareda turo baki still hawaye na gangarowa afuskar ta. Ran sa a had'e yasa hannu yashare mata hawaye tareda cewa Sorry kinji stop crying bari nakira "Dan'uwa yadubaki kinji?..Dasauri tace a ah ka bari "yadawo ido yazaro tareda cewa what?..kina nufin har sai "yadawo daga aikin sannan zaya duba ki?..baijira amsar taba yace niban sa meyasa kike son wasa da lafiyar kiba yafadi yana kokarin ciro wayar sa dake aljihu, Dasauri ta rike masa hannu tareda cewa pls kafin kakira shi" fara bani dumin jikinka tukun, cike da mamaki yace you??? tace yeah it's me u *Leemah* ta kareshe fadi tareda yimasa fari sai kuma ta kashe masa ido daya, aikam take yarikice yayinda yaji tsikar jikinsa tayi yarrrrr har zayayi magana tayi saurin had'e bakin su, ido ya lumshe yana jin wutar kaunar ta tana sake roruwa azuciyar sa ahankali yasa hannun sa zaya zuge zif din gaban rigar. *_Nikam ganin hakan yasa nafe ce da gudu arai na kuma ina fadin kai! ashe Deeya ta zama expert a wannna fagen._*๐Ÿ˜œ Saida suka samu nutsuwa tukun na sannan *Habeeb* ya rungume ta tsam akirjinsa yana jin tsananin kaunar ta, ahankali yasa hannu yana gyara mata lallausan kashin kanta daya barbaje, sannan yatallabo fuskar ta idon ta lumshe tana sakin murmushi shima murmushin yayi tareda yimata kiss agoshi da lips yace thanks my honey, saidai gaskiya kinyi mun wayo daga cewa nabaki dumin jikina shikenan kuma duk sai ku tsotse mun ruwan jiki na dake da baby ki ko?... hmm to nidai inajin yinwa don haka sai a bani abinci naci dasauri ta bude ido tareda dukan sa kadan akirji, cike da zola yace auchhhh! ni *Habeebullahi* zakuma afasamun kirji ne?.., dariya tayi sai kuma taturo baki cike da shagwaba tace kai! sweet Hmm na to aikai ne ka tsotse mun ruwan jikina, dariya yayi cike da nishadi yace yes my honey nine na tsotse maki ruwan jiki bakece kika tsotse mun ba, nagode sosai da farin cikin da kike shayar dani Allah yashayar dake ruwan alkausar tace ameen tareda sweet Hmm na murmushi yayi yace ameen, yanzu tashi muje muyi wanka sai kiraka ni part din lnna naci abinci sannan naji meyasa idan kinje part dinsu take koran munke, tace yauwa sweet Hmm na ka tambaye ta" abinci kuma gashi can na girka maka, kai yadafe tareda cewa Oh! my honey wai meyasa kike son wahalar mun da kanki ne?..ashe ba nace ki daina yin girki ba umuh?..tace to kayi hakuri zan daina amma dai nafison ka ci abinci na, Murmushi yayi me cikeda farin ciki yace godia nake yar albarka nikaina idan ba abincin ki danasu lnna naci ba sam banajin dadi, sannan yadauke tasuka shiga toilet. Bayan sunyi wanka sai suka dauro alwala suka fito kasan cewar azahar har tawuce, sai suka shirya cikin jallabiyya shiyasa fari ita tasa baki bayan sun gaba barin turaruka ajikinsu sannan sukayi sallah, Bayan sun idar sai suka nufi dinnig table tazuba masa abinci yafara ci, sosai *Habeeb* yake cin abinci yana zubama *Deeya* tasani tareda yaba mata iya girki itakam tana ta dariya, saidai ita ko kadan bata iyaci ba domin tunda ta samu ciki wani lokacin idan tayi girki bata iya ci kamar yanzu yinwa takeji amma kuma sam bata jin cin abincin, Asalima jita ke kamar zatayi amai yayinda takeji jikin ba dadi, kula da hakan ne yasashi saurin gama ci abinci yatashi tareda daga ta yaman nata dajiki sa, saidai wani irin zafi yaji ajikin ta yayi sosai hakan ne yasashi saurin dago kanta dake kafadar sa ya kalleta, saidai me gani yayi idon ta yana wani irin juyawa bakin yana kekokarin ba cewa hakan yasa shi zaro ido cike da tsoro yace... *_Slm don Allah kuyi hakuri darashin ganin posting dina kwana biyu akan lokaci, hakan yafaru ne saboda bukin sister na da mukeyi, da fatan zaku sata acikin addu'ar ku?.. nagode barkan mu da Jumma'a dafata munyi lafiya Allah yakarbi ibadun mu ameen._*๐Ÿ‘๐Ÿฝ Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [11/9, 10:08 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 6โƒฃ9โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Meya faru my honey *Leemah*?.. dai-dai lokacin da ta tafi luuuuu! zata zube kasa domin tuni numfashin ta yadauke, aikam cikin zafin nama ya tallabo ta tareda fadin yah! elahee!, cikin matukar gigita yakoma ya zauna a gujerar daya tashi tareda zaunar da'ita akan ciyar sa yana girgiza ta, saidai bata motsa ba hakan ne yasashi fadin no my honey *Leemah* open u eyes kinji?.. Sai kuma yayi sauri yadauki sauran ruwan da yasha yarage, yayyafa mata afuska aikam take tasaki ajiyar zuciya wanda kusan a tare suka sauke, ahankali tabude ido ta kalle shi shidin ma ita yake kallon Cike da tausayi tareda tsantsar damuwa yace sannu kinji?.. Kai ta gyada masa alamar yauwa, sannan yace my honey *Leemah* nace kibar nakira "Dan'uwa ya dubamun ke kince "a ah shin kinason wani abin yasamar muke ne?... Cikin shagwaba tace "a ah sweet Hmm na nidai yinwa nakeji muje part din "lnnan mu naci abinci kaji?...yace to zaki iya tafiya ko na dauke ki?..tace zan iya yace to oya tashi muje sai kici abinci sannan nakira "shi ya dubaki KO?..tace to Hmm na amma don Allah idan "yazo kace karyai mun allura kaji?.. bana son injection ko kadan, ta kareshe fadi kamar zatayi kuka. Murmushi yayi dai-dai lokacin da yatashi tareda dagata yagyara mata gyalen datayi rolling akanta sannan yadauki wayar yasa aljihun sa, sannan ya rungume ta akafadar yana fadin don't worry, bazayai maki ba tunda bakiso saidai idan yabaki magani zakiyi hakuri kisha kinji?...kai ta gyada tareda yamutsa fuska domin dai shidin ma bason shi take ba. Ahankali suke tafiya har sun kusa isa bakin kofar fita sai suka tsaya, yace l hope kin karashe shan wayan can magungunan na ki?..gaban ta ne yafadi wanda yasata saurin sun kuyar da kai kasa domin dai tasan bata shaba, hakan ne yasashi yajuyawa ya kalli wata leda dake ajiye saman table "a can gefen, yace ina zuwa gurin ledar yanufa yadauko yadawo gurin ta, Sannan yabude ledar magani naga yaciuro yana dubawa sai kuma naga yadago kai da sauri ya kalli *Deeya* wacce na hango tsabar tsoro a idon ta, sosai *Habeeb* yake kallon magani tareda watsama *Deeya* wani irin kallo me cike da tuhuma wanda yasake tsora ta. Ahankali yace my honey *Leemah* tunda na tafi ba kinsha maganin ki ba ne?..., cike da tsoran gani yanayin sa tace um umm! da..ma.. yace *Leemah* ba kinsha maganin ba dai ke nan ko?...to why ummuh?... kamar zatayi kuka tace um umm! Hmm na dama zan sha idan naci abinci kaji?... Magani ya mayar cikin ledar tareda rintse ido da alama baiji dadin rashin shan maganin ba, ahankali kuma yabude idon tuni har sunyi ja aikam take taji gaban ta yasake faduwa domin rabon data ganshi haka har ta manta rana, ba tareda yace mata komai ba yakama hannun ta suka fita falon hannun shi daya rike da ledar magani. Kallon shi tayi inda ta hango bacin rai kakara afuskar shi, kamar zatayi kuka domin idan akwai abinda ta tsana to bai wuce bacin ranshi ba, kamar yanda tasan shima babu abinda ya tsaya arayuwar sa irin bacin ranta tareda jin kukan ta, to amma itakam yazatayi ne?...kwata-kwata batason magani tareda allura. Ahankali haka, cikin sanyi murya tace pls sweet Hmm na kayi hakuri idan naci abinci zansha kuma daga yau bazan sake kinsha ba kaji ?... bai ce mata komai ba suka shiga falon bakin sa dauke da sallama, Baffa da *Hafeez* su amsa kasan cewar suke cikin falon zaune suna fira, cike da mamaki Baffa yace "a ah *Habeebullah* Kai ne kuma yau?... Murmushi yayi yace "eh Baffa ni ne tareda zama ya zaunar da *Deeya* kusada shi wacce gaba da hankalin ta yatashi saboda ganin yanda *Habeeb* din ya kyaleta, cikin girmama wa yagaida Baffan ya amsa itama tagaida shi *Hafeez* ma yagaida shi ya amsa, sannan Baffa ya tambayi *Habeeb* lafiya yazo yau?... yace *Leemarsa* ce batada lafiya shiyasa yazo, Baffa ya kalli *Deeya* wacce sai kallon *Habeeb* take kamar zatayi kuka, yake yace "a ah ikon Allah to amma mu bamu saniba, dai-dai lokacin da lnna tafito. Baffa yace to Da sauki ko?..yace "eh lnna tace ah! *Habeebu,* jiya akatafi yau kuma sai gaka Allah dai yasa lafiya?... yace *Leemah* ce bata da lafiya tace to tareda kallon *Deeya* wacce kadan takejira ta fashe da kuka, sannan tace shiyasa kazo?... yace "eh tace to Allah yasa wake yace ameen, amma lnna meya sa idan *Leemah* tazo nan part din saiki koreta?.... murmushi tayi sai kuma ta tabe baki tace au karata aka kai maka?... yace "a ah lnna ba karanki takawo ba kawai dai tace idan tashigo sai kice ta tafi part din ta, tace saboda bazan iya wannan bakuncin na taba mutun dayazo sai yafara cewa shi abu kasa zayaci, idan kuma anyi yace bazaya ciba shi sai abu kaza yakeson yaci, to idan ita Hajiya ta'iya dauka toni dai ba zan iya daukar wannan aiki. Baki *Deeya* ta turo cike da shagwaba still kamar zatayi kuka, yayinda shi kuma yayi murmushi yace to lnna ai hakuri za'ayi kinsan me ciki saida lallabawa, kinga yanzu ma munzo ne idan kinada abinci ki taimaka kidan bamu *Leemah* yinwa takeji kin sa idan tayi abinci bata iya ci, tace haka fa! abinci kam akwai shi saida tuwon shinkafa ne miyar kuka idan zayaci to sai nazubo Mata. ba tareda ya kalli *Deeya* ba yace zakici?.. muryar ta narawa tace "eh yace to lnna zataci nan lnna taje takawo mata, loma uku tayi ta ture tareda cewa ta koshi tana kallon *Habeeb* wanda har yanzu bai kalle ta ba, yace nasan baki ko shiba so kikaraci ganin yanda yai mata yasa tasaki kuka wanda dama kiri takejira ido yarintse domin jin kukan ta yayi kamar saukar guduma atsakiya yarkan sa, Baffa da lnna da *Hafeez* kam baki da hanci suka saki cike da mamaki suna kallon su, dama shi Baffa tunda suka shigo ya fahimci akwai wani abi tsakanin su. Ba tareda ya kalle taba yace meya faru kuma *Leemah* ta?... cikin kuka tace Hmm na idan na cigaba da ci amai zanyi kuma inajin yinwa sosai, dasauri yace to barshi haka nan

Chapter 32 of 42