Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sauri yace _Wha_?.. tareda zuba masu wani irin azababben kallo me cikeda bacin rain abunda suka aikata ga *Leemarsa* aikam tuni sukai tsuru-tsuru kamar marasa gaskiya ashe su๐Ÿ˜, yayinda jiki su yadauki rawa musamman jikin Na'omi sai rawa yake kasan cewar tana bayan *Jana* ta boye, Lili tace "eh Daddy ada Junior kuma ai Aunty *"Deeya* na bata chon fela ko?..kai! ya gyada alamar "eh, Cike da tashin hankali yamaida duban sa ga *Deeya* wacce har yanzu bata mota ba, yace Don Allah *Leemah* ki bude idon ki kinji gani tareda ke bazan bari komai ya same ski ba kinji?.. saida kashhhh! *Leemah* kam ko gezau batayi ba. hakan ne ya sake firgita *Habeeb,* dan haka cikin tashin hankali da tsanani firgita yadauke ta cak! kamar yar tsana yasab'a akafada da sauri yafita waje yayinda Lili tabi bayan shi tana kuka da sauri yajuya yajawo kofar falon da karfi ya kulle. _To๐Ÿ˜ณfa *Habeeb* me kuma zakayi???_ Drive shi nagani shi yataso da sauri yana cewa subhalallahi! yallabai bata da lafiya ne?...tareda dazuwa Da sauri ya bude mota, dasauri *Habeeb* yasata ciki tareda shiga ya zauna ya rungumeta; dasuri Drive ya rufe kofa, Lili tasaki kuka tareda cewa Daddy janje Aunty *Deeya* cikin sauri yace da Drive sata gaba mutafe yace "OK tareda bude gaba yasata ya rufe sannan ya zagaya yashiga yatayar yafita da gudu, kasan cewar tuni megadi yabude masu get yayinda bodyguard din sa suka rufa masa baya, dama tunda suka ga yafito hannun shi dauke da *Deeya* sun san ba lafiya shiyasa suka shiga mota sukai ready basu tsaya ko'ina ba sai wani hadadd'en private hospital Wanda aka tanada domin su da iyalai su. Cikin sauri Drive yabude ma *Habeeb* mota yafito da'ita, Cikin gaggawa nurse su kazo da gadan daukar maralafiya aka dorata emergency room aka nufada ita. Likitoci sunkai guda boyar akan tasu nafama dan ganin numfashi ta; yadawo sukai kusan awa uku suna abu daya duk hankalin su yatashi, dakyar dai suka samu numfashi Nata yadawo koshi saida ta makon oxygen, sannan babban likitan yasa akafito da'ita akanufi wani special room da'ita sannan shima babban likitan ne yafito yana sharan gumi. Shikam *Habeeb* tunda aka shiga da *Deeya* emergency room din yakeda faman safa da marwa, shida Lili wacce da tagaji da safa da marwa sai ta zauna tafara gyan-gyadi, daukan ta yayi ya rungume akafad'a yaci gaba da da safa da marwa Cike da tashin hankali yana Cikin haka ne babban Likita yafito yace Da *Habeeb* yabiyo shi bamusu yabi bayan dasuri suka nufi office din likitan. Bayan sun zauna sai likitan ya kalli *Habeeb* Wanda shima shi yake kallo, yace yallabai munyi nasara numfashi ta yadawo da taimakon Allah yana tafiya dai-dai amma fa saida akasa mata oxygen, dasauri yace oxygen Dr?..yace "eh yallabai saboda taga wani abunda yai mummunan firgitata wanda shine ya haifar mata da dauke war numfashi sosai, Wanda kadan yarage tashiga common, saidai Allah yatsare ba tashiga ba amma dai abinciken mu mungano damuwa tayi mata yawa Wanda idan ba'ayi kokari rabata dashi ba to komai na iya faruwa da'ita; dan yanzu haka ma kad'an yarage ciwon zuciya yaka mata; da sauri cike da tsanani mamaki *Habeeb* yace _What?_ Dr ciwon zuciya kuma _for how_?.. Dr tace "eh to yallabai kai zan tambaya domin akarancin shekarun ta bai kamata ace ciwon zuciya yakamata ba, cike da tashin hankali yace Dr I hope dai be kamatan ba KO?.. yace "eh amma dai yana barazanar kamata, ajiyar zuciya *Habeeb* aran shikuma mamaki yake wai ciwon zuciya kesan kama *Leemarsa* to wai agari yaya hakan tafaru?.. Dr yace yallabai ya kamata akula da'ita sosai domin dai tana bukatar kulawa wanda hakan ne zaya kareta da kamuwa da ciwon zuciya, Cikin sanyi murya *Habeeb* yace nagode sosai Dr kuma insha'allahu za'a kiyaye, yanzu Zan iya ganin "ta?.. yace "eh amma sai zuwa anjima lokacin an cire mata oxygen din, wanda muna saran farfado warta insha'allahu. yace OK" ba damuwa zan iyazuwa gida nakai Dota na na dawo?.. yace "eh karka damu akwai nurse da suke tsoron marasa lafiya yace OK" tareda tashi yasabaLili akafad'a suka fito tareda likitan yanuna ma *Habeeb* dakin da'akakai *Deeyar* room 5 ne ta window dakin *Habeeb* yaleka tana kwance sanye da abi numfashi, tsura mata ido yayi yana kallon ta wani irin azababben SONTA ke yana bin jininshi gawani irin tausayin ta daya Kama shine, gawani masifaffen rama datayi masa shimamaki mayake tareda tambayar kanshi waida yaushe *Leemarsa* takoma haka dubu cikinta kamar bata cin komai koda yake dama Cikin nata haka yake ashafe kotaci abinci kamar bataci ba saidai wannan lokaci yafi shafewa sosai, ajiyar zuciya yayi tareda cewa Allah yabaki lafiya *Leemah* sannan yakalli wasu bodyguards dinsa guda biyu kirnsu yaida hannu aikam cikin sauri suka karasa gurin shi cema suyayi su tsaya abakin kofar nan zayaje gida yakai lili yadawo dasauri sukace Ok" Sir Sannan ya nufi mota direba yabud'e mashi ya shiga suka ka nufi gida. ****** ***** Su *Jana* Kam bayan fitar *Habeeb* suka sauko falon kasa bayan Na'omi tadauko kwalin ta kwashe beraye sannan suke tafaman safa da marwa, kasa kallo daya zakai masu ka fahimci dukkan sun atsora ce suke, musamman Na'omi da jikinta sai rawa yake dasauri tanufi kofa zata fita sa tajita arufe, Cikin tashi hankali takalli *Jana* tareda cewa pls Aunty ki bud'e mun kofa nafita kafin Sir *Habeeb* yadawo ya kashe ni nikuma banason namutu pls, harara *Jana* ta watsama ta tareda yin tsaki mtww! tace dayake ni na rufe ai dole kice na bud'e maki, kuma yadda baki son ki mutu nima banason ta, don haka dole ki tsaya duk abunda zayi yai mata tare dake, tunda ke kika kawo berayen. Ni bakin ciki ma daya da sihirin danai mashi ya karye tunda dama mlm dare yace" dazaran yataba ta shikenan daga lokacin sihiri zaya karye gashi yataba ta, harma dauka ta yayi mtww! tasake yin tsaki tareda cewa nidai kin cuceni wlhy. Dai-dai lokacin da sukaji motsin bud'e kofa dasauriJunior yaboye bayan kushin jikinsa nata rawa dama shi yana matukar tsoron *Habeeb*. "Akam *Habeeb* ne yashiga kafadar shi dauke da da Lili juyawa yayi yarufe kofar Sannan yanufi dakin shi, ya kwantar da ita kan gado, yafito yana kokarin zare belt din jikinshi rai bace yanufi Na'omi wace tun shigowar shita zube kasa tana murza hannu alamar neman afuwa, saidai bai tsaya sauraren taba yashig labta mata belt, "Ai kam tuni tasaki ihu tare da fadin _Sorry Sir_, Cikin bacin rai yace" _u don't know who she to me ba_?..Cikin azaba tace _Sorry Sir l know she is u wife_, Cikin tsawa yace Oh! kinsani matata ce shine kike kokari kashe mun ita; bakisan cewa itace rayuwa taba?.. shegiya uban wa yafada maki tana tsoron bera?.. Cikin tsanani azaba tace Aunty domin tuni yafara fasa mata jiki da belt din yace OK" is good tareda cigaba da labtanta. *Jana* kam jikinta sai rawa yake domin tunda take dashi bata tana ganin baci ranshi irin yauwa ba,don haka dasuri zata gudu ciki zafin nama yafisgo ta yajefa kan kushin tareda watsa mata wani irin mugun kallo me dauke da gargad'e kika kuskura ki kabar gurin nan sai nayi mummunan saba maki, aikam tuni ta nutsu saidai jikinta sai rawa yake cigaba yayida dukan Na'omi. Saida yayi mata lilis domin tuni yafarfasa mata jiki sannan ya kyaleta dama ga jikin yasha bilichin, cikin tsawa yace _get out of my house_, kuma daga yau nakoreki daga aikin don haka idan nasake ganin ki agidan nan saina sa an daure ki, _stupid woman_ kawai dakyar take Jan jiki zata fita cikin tsawa yace dan ubanki zoki dauki kwalin kazantar ki, dasauri tajuyo tazo ta dauka tafita dakyar da karfi yarufe kofar rai bace yanufi gurin. *Jana* wacee tuni tafara rokon shi yayi hakuri bai tsaya sauraran taba yashiga zuba mata mari tako'ina hagu da dama, yana fadin dan iskanci kinsan cewa bata son bera shine kika sama ta don kiyi mata illa ko?.. hakuri take bashi amma ina ran yan maza yabaci saida yahada mata jini da majina tukun sannan ya kyale ta; domin tuni bakin ta da hanci sun fashe jini kawai ke fita, Cikin tsawa yace ina Junior?.. dasauri tanuna mashi inda Junior yake wanda tuni yasaki fitsari saboda tsabar tsoro. Zuwa *Habeeb* yayi ya kamoshi tareda zaro wayar redio yashiga tsaula ma shi yana fadin dan uban ka harda kai ko?.. sai ihu yake yana fadin sorry Daddy nadai, na saida *Habeeb* yazane shi tas sanna ya kyale shi yanufi daki zuciyar shi tana kuna. Toilet yashiga yasa karma kashi ruwa yadauki lokaci sannan yayi wanka yafito, yana cikin shiryawa lili ta tashi daga bacci tace Daddy ina Aunty *Deeya* ta tashi aga baccin?..yace a ah Dai-dai lokacin daya karasa shiryawa, tace to Daddy wane jaya dafa mana abinci?.. cike da mamaki yace my lili dama Aunty *"Deeya* ce take dafama ku abinci?.. tace "eh shuru yayi, tace Daddy janje "Aunty *Deeya* tabani abinci inajin inwa yace to muje nayi maki wanka sai muje nakai kiko?..tace "eh bayan yaimata wanka ya shirya ta sannan suka fita saida suka biya wani gidan saida abinci suka siya sannan suka nufi asibiti.... *_Assalamu'alaikum, MASOYANA kuyi hakuri da wannan, koshima saboda nariga nafara typing ne shiyasa na karasa shi dakyar, saboda kanin Baba na yarasu yau din nan๐Ÿ˜ญ don haka ina Neman addu'ar ku don ALLAH._*๐Ÿ‘ Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* _(Labarin Sadeeya)_ Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [7/2, 11:49 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 3โƒฃ6โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _Not edits_ "A asibiti bayan tafiyar *Habeeb* bada wani dad'ewa ba sai numfashi *Deeya* yafara fita da sauri da sauri alamar nata numfashi yadawo, don haka dasauri nurse din dake kula da'ita tayi sauri taje takira Dr yazo ya cire mata oxygen din Sannan ya duba ta yaga babu wata matsala a koda yaushe zata iya farfadowa normal, sai dan zafi da jikinta yayi shidin ma bawani abun damuwa bane dazaran ta farfado tasha magani komai zayayi dai-dai Sannan Dr yafita, bayan yafada ma nurse din cewa idan takarfa tazo takira shi tace yesss Sir. Ba'afi minti talatin da cire mata oxygen din ba tafar ka, bakinta dauke da salati tana kokarin tashi sai nurse din dake tsaran ta tayi saurin taimaka mata ta tashi ta zauna tareda samata filo ta bayan ta, tadan tajingina yadda zataji dadin zaman, Cikin turanci nurse tace mata sannu, ahankali ta amsa dacewa yauwa tareda kurama nurse ido tana mata kallon rashin sani, Can kuma saita kauda kanta daga barin kallon nurse din Wanda ganin nurse din ya tabbatar mata da cewa a asibiti take, shuru tayi tana tunani to meya kawota asibiti?...can sai ta tuna don haka ne yasa tayi sauri rintse ido yayinda taji tsikar jikinta yana tashi tareda wani irin karrrma, "Ahankali ta furta bismillahi'layadurruma'isme'shai'unfil'ardi'walafissama'iwahuwassami'ul'aleen, la'ilaha'illa'antassubahanaka'innikuntuminazzalimin, Sai kuma ta fashe da kuka dasuri nurse tace sannun sis jikin ne?.. kai ta gyada mata alamar "eh dasauri tace to bari nakira "Dr dama yace" idan kin farka nakira shi, dasauri *Deeya* tace "a ah basai kin Kira shi ba dama dai bana danjin karfin jikina ne amma nasan zuwa ajinjima insha'allahu zanji sauki, Nurse din tace ai haka ne dama sai ahankali KO" kina bukatar wani abun ne?.. *Deeya* tace no saida don Allah idan kinada kudi acikin wayar ki kibani zanyi magana, nurse din tace "OK tareda mika mata wayar *Deeya* takarba tareda cewa nagode sannan nurse tafita tabata guri don taji dadin sakewa tayi maganar, sannan tafara daddana number *Feeya.* *_Bauchi_* ******* Kamar koda yaushe *Feeya* Ce kwance sama kafar *Harees* wanda dawowar shi kenan daga office, ya'iske ta kwance hannun ta rikeda wayar ta tana kiran layin *Deeya* saidai amsar kenan guda daya kullum wato switch off, Shine ya'iske ta tana kuka saboda bata samu layin *Deeya* ba dama haka takeyi idan takira baje basai tafara kuka, to sai shikuma yaita aikin lallashi Cikin kwantar da hankali yace it's OK" my precious inajin ajikina "Queen of beauty sun kusan dawowa kinji?..kaita gyada dai-dai lokacin da wayar ta take ringing. kurama wayar ido tayi ganin new number yasa bata dauka ba har wayar ta tsinke, aka sake kira, har zata kashe sai yace "a ah me Darajata baki san ko wane ba don haka kar ki kashe, baki ta turo tareda dacewa to ni bansan me number "ba, yace to dauka kiji kowane" tace to tareda yin pick muryar dataji ne yasata tashi zumbu, dasauri *Harees* yariketa tareda cewa take easy my precious, ajiyar zuciya tayi sai kuma tasaki kuka, tareda cewa kai my sweet *Deeya* kullum sai nata kira layin ki amma switch off kinsan nayi miss dinki sosai fa daga can itama kukan take tareda cewa nasani my sweet *Feeya,* nima l really miss u magana suke amma kuma suna kuka ganin hakan ne yasa *Harees* karban wayar tareda sake rungume *Feeya* ajikin shi, yana Shafa bayanta tareda fadin it's "Ok, wayar yakai kunnan sa yana jin sautin kukan *Deeya* Wanda kanaji zakasan cike yake da tarin damuwa, hakan ne yasa sam baiji dadin jin kukan nata ba har saida yaji zuciyarsa tadan sosu, Cikin kwantar da murya yace it's "Ok Queen of beauty fadamun menene ya faru idan ankira layinki dana "Dan'uwa ba'a samu, sannan kuba kukira kowa "a family ba kuma tunda kuka tafi baku zo ba gashi har yau kimatin wata uku har dawa su kwana ki shin meke faruwa ne?.. Cikin shashshe kar kuka tace nidai wayata ce tabata amma shi Hmm *"Habeeb* bansan meya samu wayar shiba, yace to yanzu ina *"Habeeb* din yake?.. tace nima bansan inda yake ba, dasauri yace ke! kina Ina ne yanzu?..cikin kara sautin kukan ta tace ina asibiti ne dasauri yace _what?.._ asibiti fa kika ce" meyasa meki?.. tace "eh pls Hmm *Harees* kazo ka dauke ni ka kaini gida gurin "lnna da "Baffa da "Hajiyar mu, don ni bazan sake koma wa gidan Hmm *"Habeeb* tunda dama baya sona gashi kuma yanzu ma yace bayason ganina don haka nima banason shi banason ganin shi, na tsane shi! na tsane shi!! na tsane shi!!! ta karashe fadi cike da tsanani kuka. *Harees* kam jikinsa sai rawa yake saboda tsabar tashin hankali, yace Queen of beauty kiyi shuru ki fadamun wai meke faru wane?.. Cikin kuka tafama shi duk abunda yafaru tun daga ranan da *Habeeb* yace" baya son yasake ganin ta afalo, da abubuwan da *"Jana* takeyi mata har dana yau datasa mata beraye wanda shine yai sanadin zuwa ta asibiti duk saida tafada *Harees,* Wanda tun kafin ta karashe fadi ya fahimci shiga tsakanin su akayi wanda koyayi rantsuwa bazaya taba kaffara ba *Jana* ce tayi wannan aikin. Ciki kwantar da murya yace to kiyi hakuri kiyi shuru ki daina kukan kinji?.. tace to zaka zoka dauke ni?..shuru yayi, jin baice komai bane yasata sake fashewa da kuka tareda cewa Hmm *Harees* idan bakazo ka dauke niba, Allah zan fito natare motar da duk nasamu nace yakai ni Bauchi dasauri yace no Queen of beauty kar kiyi haka nan kinga bakisan guri ba kinji ko?.. tace to kazo ka dauke ni; yace to ki kwantar da hankalin ki zanzo yaudin nan yanzu ma zanje na hau jirgi kinji ko?.. Cike da farin ciki tace to, yace ya sunan asibiti?.. dai-dai lokacin daga can yaji *Deeya* tana tambayar nurse din sunan asibitin, tafada mata saita fada ma *Harees* sannan sukai sallama ta. Duk dacewa *Feeya* taji wasu maganganu dasuka guda na tsakanin *Deeya* Da *Harees,* hakan bai hanata yimasa kallo me dauke da neman Karin baya niba, murmushi yayi tareda Shafo fuskarta yace kwantar da hankalin ki yau sweet *"Deeya* dinki zata zo gida, Cike da murna ta rungume shi tace yauwa Hmm *Harees* thanks yace zanje na dauko ta saboda tana Cikin damuwa, muje ki tayani nashirya ba musu tabishi zuwa dakin shi Cikin kanka ni lokaci ya shirya yafito yace mata karki fadama kowa inda naje kinji ko?...tace to sannan yafita direba yakai shi filin jirgi, Cikin sa'a mutu daya ya rage yahau sai ABJ small London๐Ÿ˜€. *_Abuja_* ******** *Deeya* kam jin cewa *Harees* zaya zo ya dauke ta yasa taji wani matsananci farin ciki ya ziyarci zuciyar ta wanda rabon dataji irin sa har ta manta rana, don haka fuskar ta dauke da fara'a ta mika wa nurse wayar ta tareda cewa ta gode. Tun bayan dasuka baro gidan cin abinci suka kama hanyar asibiti Lili keta faman zubama *Habeeb* surutu, wanda jinta kawai yake amma kwata-kwata baya fahimtar abunda take fada domin gaba daya hankalin shi yagurin *Deeya,* tunanin shi meke damun ta har yake kokarin haifar mata da ciwon zuciya to wai mada yaushe hakan yafaru ne?... Ido ya lumshe sakamakon tunawa da abunda *Jana* tayi mata jiyayi ransa yanai masa zafi, ahankali yafurta kiyi hakuri *Leemah* ta sai inaji ajikina kamarni ne sanadin damuwar ki Wanda bansan tayaya hakan ta faruba, amma I promise to u my *Leemah* insha'allahu bazan sake bari wani damuwa yashige kiba har yayi kokarin haifar maki da ciwon zuciya saboda Ina *SONKI* dayawa *Leemah* ta, Lili dake ta kallon shi tace Dad ai nima inachon Aunty *Deeya* chocai ahankali yabude idon shi da har sun fara chanja kala daga fari zuwa ja, murmushi yayi tareda cewa really?.. itama murmushi tayi tareda daga babbar yatsan ta tace yesss! hannun yakama tareda cewa hmm to aina fiki *SONTA,* tace no Daddy nafika chonta yace um-umh nafiki chonta, tace "a ah Daddy tareda bubbuga kafa zatayi kuka dariya yayi tareda rungume ta yace to naji kinfini chonta shikenan ko?... Kaita gyada alamar "eh Dai-dai lokacin dasuka shiga asibitin ana kiran sallah azahar direct dakin da *Deeya* take suka nufa. Koda suka shiga dakin nurse suka iske tana gyaran gado, dasauri *Habeeb* ya ajiye ledojin dake hannun shi tareda tambayar nurse ina matar shi take?.. tace tashiga toilet yin alwala ajiyar zuciya yayi tareda cewa ok" shi maza yaje yayi sallah, yace Lili kijira Aunty *"Deeya* tafito toilet kinji ko tace to sannan yafita zuwa masallaci dake cikin asibitin don yaga batar da sallar azahar, ita kuma nurse din ta cigaba gyaran gadon bayan tagama gyara sai ta shinfida mata abun sallar da takawo ma da hijab sannan takoma saman kujera ta zauna. *Deeya* na fitowa daga toilet lili taje da gudu ta rungumeta cike da murnan ganita tace Aunty *Deeya* na kin tashi daga baccin?.. Murmushi tayi tareda Shafa kan Lili tace "eh Lili Daddy natashi, dariya tayi tace yeeee chikenan gobe zakiyi mana blakfache da omo work KO?.. dariya sukayi itada nurse jin kwama tsalan hausar Lili, sannan *Deeya* tace "eh zanyi maku yanzu ki shiga toilet ki yo alwala kizo muyi sallah tace to tareda shiyasa toilet din. Bayan sun idar da sallar sai *Deeya* ta tashi ta koma kan gado ta kishin gid'a tareda lumshe ido tana tasbihi ahankali. Bayan *Habeeb* ya'idar da sallah sai yafito daga masallaci wayar sa yaciro daga aljanu nabobin *Harees* yashiga daddan nawa, mamaki ne Yakama shi ganin sunan Dan'uwa bai bayyana akan wayar ba kamar yadda yai saving, tambayar kanshi yake to ya'akayi haka?..dai-dai lokacin da no tashiga tafara ringing Wanda yaji karan kamar ta bayan shi yake fitowa don haka dasauri yajuya, aikam yakarba da *Harees* tsaye rikeda waya yana doka murmushi Dasauri *Habeeb* ya'isa gurin shi fuska cike da fara'a suka rungume juna yace dan'uwa saukar yaushe?.. yace yanzu nan na'iso shine nace bari nayi salla tukun kaga yanzu ma nagama alwala sainaji kiran ka yashigo, yace OK" bari naji raka kafito yace to tareda shiga masallaci. da Kallo daya zakai masu ka gane cewa su din cikakkun aminai ne, hannun su sarke Da juna cikin nutsuwa suke taku me cike da kwarjini *Harees* yace Dan'uwa kayi wuyar gani, wani lallausan murmushi *Habeeb* yayi tareda cewa kai aiko nayi wuyar gani bazan taba yiwa Da'uwa na wuyar gani ba, yace Hmm gashi kuwa kai mashi wuyar gani bama shi kadai ba harda iyayan mu, dasauri yace banga ne harda iyayan mu ba?... *Harees* yace hmm aini dan'uwa ka bani mamaki! wai ace rabonka da gida yau wata uku harda wasu kwanaki, zaro ido *Habeeb* yayi cike da mamaki yace nidin?... *Harees* yace "eh Dai-dai lokacin da suka shiga dakin. gaban *Deeya* yafadi jin muryar *Habeeb* Wanda gaba daya kanshi yadaure dajin abunda *Harees* yafada, nurse Ce tayi masu sannu suka amsa yayinda lili taje da gudu ta rungume *Harees* tana fadin oyoyo Daddy, daukan ta yayi yana dariya dai-dai lokacin da nurse din zata fita Dasauri *Deeya* tace sis ga hijab dinki tace lah ba komai kisa tace to nagode sannan tafita, *Habeeb* ne yanufi *Deeya* fuskar shi dauke da fara'a yana cewa *Leemah* ta yร ji?โ€ฆba tareda ta kalle shiba cikin cool voice dinta tace da sauki, tareda dabi ta gefenshi ta wuce zuwa guri *Harees* tace hmm *Harees* muje dasauri *Habeeb* yace inaza ku?.. *Harees* yace Bauchi Cikin tsanani mamaki yace... Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [7/2, 11:49 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 3โƒฃ7โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* *_Wannan page din nabaku ne KYAUTA ๐ŸŽdomin kaunar ku da KYAUTAR ALLAH CE_,* *_Sis Aesha ~K N T~ mean kontagora and Sis Khadija_ ~_SARKI_~* *_don haka kuyi yadda kuke so dashi nagode sosai da kulawar Ku, kusani inayin Ku irin sosai sosai din nan Love yours my Lovely SISTER'S._*๐ŸŒน๐Ÿ˜ ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _Not edits_ _What?.._ Bauchi fa naji kace" *Harees* yace "eh haka nace" Dai-dai lokacin da yake sauke Lili, yace insha'allahu yau Zan maida Queen of beauty gida, daure fuska *Habeeb* yace kamar ya bangane yau zaka maida *Leemah* ta gida ba to _for what reason_?.. Shima *Harees* din daure fuska yayi tareda cewa saboda bazaka iya riketa ba, cike da bacin ran *Habeeb* yace "a ah Dan'uwa wai yau meye haka kake yimun ne?...yanzu fa kagama cewa wai rabona da gida yau kimanin _three months,_ sannan kuma kace zaka maida *Leemah* ta gida saboda bazan iya riketa ba, shin Kai kowani yace" maka bazan iya rike *Leemah* ta ba bazakai mutsu ba?... Cikin daure fuska *Harees* yace mutsun me zanyi?..ainine ma mutum nafarko da zaya fara fada kamar yanzu Dana fada maka, sannan dakake cewa nace watan ka uku bakage gida ba to ba haka bane?..ko yaushe raban ka da agidan umh KO" kana nufin karya zanyi maka eye?..., Queen of beauty kuma Zan tafi da'ita gida ne tunda baka son ta baka ra'ayin ta, so gara amaida 'ita gaban iyayanta tun kafin "matarka ta illata ta tunda tariga tamaida ita yar aikin, kuma tasayi sarai cewa Queen of beauty tafi karfin tazama yar'aikin ta wlhy kum... Da karfi *Habeeb* yace _enough!! enough!!_ enough!!!, haba Dan'uwa wannan wasu irin maganganu ne haka kake fadamun Wanda gaba daya nakasa fahimtar su, yace... Nan danan *Harees* yafada masa komai tundaga ranan daya kirashi yake tambayar sa *Deeya* yace masa shi baigane taba har, cewa da yayi baya son yasake ganin ta afalon sa da kuma abubuwan da *Jana* take tayi mata, harda nayau wanda ba dan Allah yakawo shiba da kila saidai a iske gawar *Deeya* din tunda *"Janan* tasani sarai cewa *Deeya* bata son bera , don haka duk sai Da *Harees* yafada masa kamar yadda ita *Deeya* tafada masa, inda ya kareshe dacewa I hope yanzu ka fahimta ko?.. saidai ni wlhy Dan'uwa kabani mamaki banyi zaton haka daga kare kaba sam. *Habeeb* kam jiyayi kamar zaya fadi saboda tsabar firgici dajin abinda *Harees* yace don haka Dasauri yafada bango, yayinda wani irin zufa yashiga tsatsifo masa ta ko'ina, jin maganar yake tamkar

Chapter 15 of 42