Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
almara KO" ta tsuniya wai shine ne dakan shi yace baya son ganin *Leemarsa* tambas zuciyar sa batayi masa adalci ba, tunda har zata iya cewa batason gani abunda yafi kauna arayuwar sa fiye da kanshi. "Ahankali ya kalli *Deeya* wanda itama shi take kallo saidai gabanta yanata faduwa lallausan murmushi yasa karma ta, take yaji tausayin ta yakama shi yayida yakeji wani iri tsananin *SONTA* yanabin jini da jijjiyoyin sa, aranshi yace Oh! Allah sarki *Leemah* ta _no wonder_ Dr yace" ciwon zuciya yakusa Kama ki, saidai Insha'allah bai taba kamaki ba, ahankali yanufi gurinta dasauri ta boye bayan *Harees* cak! yatsaya. Cikin sanyi murya yace kiyi hakuri *Leemah* ta nasan ban kyau taba saidai wlhy duk bansan yadda akai haka ta faruba, amma nayi maki alkawari hakan bazaya sake faruwa ba, kaima Dan'uwa kayi hakuri hakan bazaya sake faruwa ba Insha'allah wlhy ni kaina jina nake tamkar bani ba sai inajina kamar wani sabon mutu, yafadi tareda rike hannun *Harees*. Wanda shikan shi tausayi *Habeeb* din yabashi domin yasan tabbas makirci mace ne yaka mashi, Cikin sanyin murya yace ba komai Dan'uwa yawuce Queen of beauty kiyi hakuri kinji ki koma ki zauna dakin ki, wani irin tsalle *Deeya* tayi tareda koma wa gefe, Sai kuma tasaki kuka me cike da shagwaba domin kuwa harda bubbuga kafa tareda yarfe hannu, tana cewa ita sam bazata koma gidan Hmm *Habeeb* tunda yace baya SONTA, itama bata son shi kuma bata yin auren don haka yasake ta ta koma Bauchi gurin lnna da Baffa da Hajiya da kuma sweet *Feeya*, *Habeeb* kam jin kalaman dasuke fitowa daga bakin *Deeya* ne yasashi yai mutuwar tsaye, domin baiyi zaton jin haka daga gareta ba gaban shine yafadi yayinda yaji wani irin tsoro yadarsu acikin zuciyar shi, dasauri *Harees* ya isa gurinta cikin lallashi yace kiyi hakuri Queen of beauty kibar kukan haka kinga bakida lafiya kuma ma aiyace hakan bazaya sake faruwa ba kinji?.. tace to nidai bazan koma gidan sa ba Bauchi zaka kaini, yace to shikenan amma dai yanzu idan mu je Bauchi a part din shi Zaki zauna ko?...kara sautin kukan tayi tareda cewa nifa bazan je part din shiba, part din Hajiyarmu zani eheee! ta kareshe fadi tareda murgud'a ma *Habeeb* baki Wanda ya zama tamkar butun-butumi, tsabar tashin hankali yasashi yakasa cewa komai ga kukan ta dayake ji har cikin ZUCIYAR sa, *Deeya* kam gaba daya ta birki ce masu ita dai kawai sukai ta Bauchi, suna Cikin haka Dr yazo dubata ganin hawaye afuskar ta yasa shi fara fada wai meyasa za'asata kuka alhali ansan batada lafiya, *Harees* yace kuka take zata gida murmushi Dr yayi yace to zona dubaki saina sallame ki tunda kinji sauki kai! amma sai kin bar kukan, dasauri ta share hawaye cike da shagwaba tace tona bari, yace to zona duba ki bamusu taje yaduba ta babu wata matsala saidai tana matukar son hutu sosai sannan ya rubuta mata magunguna suka fito. *Harees* yace Dan'uwa kayi hakuri kabari mutafi, Cikin sanyi murya *Habeeb* yace Dan'uwa saidai mutafi tare yace to shikenan gida suka nufa dan ajiye lili sannan adauki kayan *Deeya* domin tace ita bazata shiga gidan ba, *Habeeb* kam koda yashiga gida kota kan *Jana* bai biba yadauki kayan *Deeya* tareda abunda zaya bukata yafita direba sa yakai su airport suka shiga jirgi sai Bauchi. *_Bauchi_* ******* Suna isa *Harees* yakira direba yaje yadauke su zuwa gida yayinda *Habeeb* yake tajin faduwar gaba, kogama parking direba baiyiba *Deeya* tabude mota tafito da gudu tanufi part din Hajiya *Habeeb* kam bin bayanta yayi da kallo yayinda yaji kirjinsa yatsanan ta bugawa, jiki a sanyaye suka fito suka nufi part din. Tana shiga tafada jikin Hajiya tareda sakin kuka kasan cewar Hajiyar suna falon kasa suna fita itada Abba, Cikin tashin hankali tadago ta tareda cewa lafiya hali dubu na ba amsa sai kuka, tace subhalallahi! me yafaru ne inashi Hamman naku?.. nan ma ba amsa sai kukan dai take, tace Oh! ikon Allah kodai baki da lafiya ne?..kaita gyada alamar "eh, Abba yace Bayan rashin lafiya akwai abunda ke damu ta, Hajiya tace nima abunda nafara tunani akai kenan, ahankali tace hali dubuna me yafaru?..Cikin kuka tace Hajiyarmu ni bazan sake zuwa Abuja ba, Dai-dai lokacin da suka shiga falon zama sukayi Abba ne yayima *Habeeb* wani irin kallo wanda yasake firgita shi, Sannan yace tsawon watanni uku dakayi baka zo gida ba sam bai bata mun rai ba, saiyau kachal dana ganka naji wani irin bacin rai wanda na dade banji irin sa ba, kasan dalili?..Kai *Habeeb* ya girgiza cike da tsoro murmushi Abba yayi me dauke da bacin rai yace saboda jin kukan *Halimatus-sadeeya* danayi wanda duk wani me hankali idan yanutsu yasaurari kukan zaya fahimci meyinsa yana tattareda damuwa, Karin bacin raina ma bansan tsawon wani lokacin ta dauka tana wannan kukan ba, shin Na ALLAH haka mu kayi dakai???.. *Habeeb* kam gaba daya ya tsorata dajin kalaman Abba hakan ne yasashi yakasa cewa komai dakyar ya'iya yafurta A..b..bahhh, dasauri yadaga masa hannu tareda kallon *Harees,* yace *Hareesu* akira metting yanzun nan cikin ladabi yace to Abba tareda tashi yafita, Abba ma tashi yayi yanufi dakin sa Hajiya ma tashi tayi ta kama *Deeya* suka nufi sama akabar *Habeeb* yanzu cikin tashi hankali. Wanka Hajiya tasa *Deeya* tayi sannan tasa taci abinci dakyar sanna suka sauko falon kasa lokacin har yan'uwa sun fara taruwa, Cikin lokaci kankani kowa ya'iso har alokacin *Habeeb* yana zaune inda yake tamkar andasa shi, falon yayi tsit kowa yana zaune amazauni shi Baffa ne yabude tareda addu'a kamar yadda akasa ba, sannan Abba yai gyaran murya yace shin Alh Al-mustafa idan mutun yagaji da abu ya yakeyi dashi?. Baffa Al-mustafa yace rabuwa yake dashi, Abba yace haka ne to *Hafeez* kawo mun takarda da biyo yace to tareda tashi yaje yadauko yakawo masa karba Abba yayi tareda mika wa, *Habeeb* wanda duk ac falon bai hana shiyin gumi ba Abba yace karbi kansa yana kasa bai karba ba, Cikin tsawa yace karbi nace hannun shi na rawa yakarba Abba yace yauwa to sonake ka rubutama *Sadeeya* saki uku yanzun nan, Cikin azababben tashin hankali *Habeeb* yace.. *_Kutttt ๐Ÿ˜ณran Abba yabaci ku zo muje bashi hakuri nidai nayi gaba๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€ sai kun zo_* *_yawan comments yawan typing_*๐Ÿ˜‰ Muje zuwa A *KYAUTAR ALLAH CE* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [7/2, 11:49 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 3โƒฃ8โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ "Abba Kai mun rai wlhy KO saki daya bazan iyayima *Leemah* ta ba balle har saki uku, don Allah kayi hakuri nasan nayi kuskure saidai wlhy ba acikin sani na aikata hakan ba, Pls Dan'uwa kayima Abba bayani bakai kafada mun cewa rabon danazo gida yau wata uku ba KO?.., dasuri *Harees* yace "eh Abba tabbas nina fada masa wanda ni kaina saida nayi masa fada akan hakan, sai yanu namun shi sam baisan ya'akai hakan tafaru dashi ba, Dasauri *Habeeb* yace wlhy Dan'uwa bansan nakai tsawon wannan lokaci banzo gida ba, kuma duk wani abunda *"Jana* ta aikata ga *Leemah* ta wlhy ban saniba saida tafada ma Dan'uwa, Don Allah Abba kayi hakuri ka janye maganar sakin nan wlhy bazan iyaba, *Harees* yace don Allah Abba kayi hakuri Ina ganin duk abubuwan dasuka faru baya Cikin hankalin shi, Cikin tsawa Abba yace Ina hankalin na shi yaje eye?...shuru *Harees* yayi yayinda *Habeeb* yasake riki cewa, hannun Abban yamika mashi tareda cewa rubuta kabani akwai wanda zan aura ma kuma inada tabbaci zaya rike mun ita da kyau, Wani irin tsananin tsoro ne yasake kama shi yayinda zufa keta faman tsasufo masa, bugun kirjinshi kam har yawuce misali jiyake har antar cikin sa tana kadawa saboda tsabar tashin hankali, wanda shi tunda yake bai taba shiga tashin hankali irin wannan ba, cikin tashin hankali yace kayi hakuri Abba Ina son *Leemah* ta sosai bazan iya sakin taba, ya kareshe fadi tareda hada hannuwa guri guda alamar roko. Biro da takarda kam tuni yasake su kasa bayan ya chukui-kuiye takardan, Baffa Al-mustafa ne yace Alh ayi masa hakuri, Abban baice komai saidai yaima takardan dake dunkule akasa kuri da ido Cikin hade fuska yace takardan Dana baka kenan kaima haka, koda yake na baka mutun maka wulakan ta to balla takarda kwalin banza. Dasauri *Habeeb* yadauki takardan jikinsa yana rawa yake budewa tareda cewa kayi hakuri Abba, *Leemah* tafi karfin walakanci aguri na shiyasa ma bazan iya sakin taba Abba yace to shikenan tunda bazaka iya sakin taba, dama ai lokacin da aka daura auren baka saniba, don haka yanzu ma bazakasan lokacin da za'a rabashi ba don haka Alh Yusufa rufe mana taro da Addu'a. Cikin gigita yace don Allah kayimun rai karka raba auren mu da *Leemah* yin hakan zaisa nashiga wani hali yafadi yana kokarin rike kafar Abban, aikam tuni yadaka masa lafiyayyan tsawan wanda yasa shi saurin fasa abunda yai niyya, yayinda jikinsa keta faman rawa Cikin hade fuska Abba yace mlm Yusufa ayi mana Addu'a Mu tashi. Cikin sanyi jiki Baffa yace to wanda tunda akafara maganar bai ce komai ba hankalin shina kan *Deeya,* wacce yaga tareme sosai tausayi ta gaba daya ya cika shi saidai kuma ganin halin da *Habeeb* yashiga cikin lokaci kankani duk saiya shafe tausayin *Deeya* din, domin ya hango zallar kaunar TILON yarsa akwayar idon *Habeeb* din, Kai har dama RUHIN sa da gangar jikin sa gaba daya domin abunda yakefi da gaske yake har Cikin ZUCIYAR sa, zaka fahimci hakan ne ta yanayin dayake cikin, Ajiyar zuciya Baffa yayi me karfi wanda tasa duk aka kalle shi Sannan yadaga hannu yafara add u' yadauki lokaci yana kwarara addu'a, wanda da'alama yadad'e baiyi irin ta agurin meeting din ba, Bayan yagama sai Abba tashi yanufi dakin sa sannan kowa yatashi yana fita jiki a sanyaye alamar hukuncin da Abban yace zaya zartar baiyi ma kowa dadi ba. Dasauri *Habeeb* ya mata kusada Baffa wanda yake zaune bai sa alamar ta shiba, hannu sa yarike me rikeda tasbi Cikeda tashin hankali yace Baffa don Allah kace Abba yayi kuyi hakuri karya taba aurena da *Leemah* wlhy Ina SONTA da duk kan ZUCIYATA, _*Allah sarki โ˜บHabeeb harka tuno mun da SEERAJ din SAJEEDAH na cikin ZUCIYATA CE.*_ Murmushin karfin hali Baffa yayi cike da tausayi shi yadora hannun sa daya kan *Habeeb* din yace ka kwantar da hankalin ka *Habeebu,* Insha'allah ba wanda zaya raba kada matarka nasan ran "Alh ne yabaci akan abunda yafaru, dasauri yace Baffa ka yarda dani wlhy basan ya'akai hakan ta faru dani ba, yace nasani *Habeebu* kuma na yadda da kai don haka karka damu *KYAUTA* zata koma dakin ka kajiko?.. kaiya gyada dasauri tareda cewa to Baffa nagode, sanna Baffan yatashi yafita *ZUCIYAR* sa cike da tausayi halin da *Habeeb* din yake cikin, sanyin jiki *Habeeb* yatashi yafita dakyar yake taka kasa domin jiyake har wani jiri (hajijiya juwa) na daukar kasa, gurin fita kamar zaya fadi dasauri *Harees* yarike shi kasan cewa yana tsaye bakin kofa yana jiran fitowar *Habeeb* din, Cikin kwantar da murya yace take easy dan'uwa ahankali yadago dakai ya kura ma shi *Harees* jajayen idon sa, Cikin kwantar da murya yace ka kwantar da hankalin ka dan'uwa in Allah ya yarda "Abba bazaya taba raba auren kada "Queen of beauty ba, Cikin wata irin murya me cike da fargaba yace Dan'uwa tsoro nakeji kar Abba yara banida farin ciki na wlhy *"Leemah* ita ce farin ciki na. Yace inaji ajikina "Abba baza yai haka ba muyi addu'a insha'allahu komai zayai normal, saida yaraka shi har part dinsa Sannan yafito shima yanufi gida ba tareda ya tsaya jiran *Feeya* ba, wanda yakeda tabbacin koya tsaya bazaya gane mata ba tunda sweet *Deeya* dinta tazo. "Aikam suna can sunkule acikin dakin Hajiya suna fitar yaushe gamo, yayinda hankalin *Deeya* yake kwance abunta tunda taji "Abba yace" zaya raba auren ta da *Habeeb* sai tasaki jikinta tana tayima *Feeya* fira, wacce rabin hankalin ta yana ga dan'uwan ta da'ake kokarin raba shida sahibar ta Wanda itakam bazata taba son hakan yakasa ce ba. ****** Zaune suke afalon sama Hajiya Adda mamu da Adda Rahama, Adda mamu ce tace Hajiya niko sai naga hukunci da Abba yake shirin yankewa kamar baiyiba Hajiya tace "eh dayake ku kunfisa sani abunda ya dace da wanda bai dace bako ?..tace "a ah Hajiya ba haka bane saidai inagani kamar yin hakan zaya sake ba *"Jana* damar yin abunda ta ga dama, Adda Rahama tace wlhy kuwa tunda ko yanzu ita ce tashiga tsakanin su" har dama mu yan'uwan sa, tunda babu yadda za'ayi ace Hmm *Habeeb* yana cikin hankalin shi yakai har tsawon wannan lokacin baizo yaga iyayan saba tareda mu yan'uwan sa koba haka ba?.. maman Walid, Adda Mamu tace sosai ma ai a yadda Hmm *Habeeb* ke son *Deeya* nasan idan bashiga tsakani ba ba yadda za'ayi yayi mata haka. Hajiya tace hmm aini yadda Abban Ku zayayi shine dai-dai, ido suka hada domin sun fahimci cewa "Abba da Hajiya bakin su daya don haka Adda Mamu tace to Allah yazaba abunda yafi zama alkhairi suka ce ameen, Adda Rahma tace to nizan tafi gida itama Adda mamu tace ainima gidan zan tafi Hajiya tace ana kokarin kiran sallah magrib zaku tafi, aidakun tsaya kuyi sallah tukun suka ce to bayan sunyi sallah sannan ko wacce tashiga motar ta tanufi gidan ta. Dakyar *Habeeb* ya'iya shiga toilet yai wanka sannan yadauro alwala yafito jiyayi kamar zazzabi ne yake son ka mashi, ga wata irin yinwa dayake ji haka nan dai yasa brown din jallabiya, sannan yafita yanufi masallaci don ya gabatar da sallar magrib, saida akai isha'i sannan suka fito shi da *Harees* yace muje part dina muci abinci, Kai kawai *Habeeb* ya'iya gyada wa sannan suka nufi gidansu *Harees* din. Kusan alokaci daya suma suka fito daga masallaci Baffa Al-mustafa Abba da Baffa tsayawa sukai, Baffa yace Alh kayi hakuri kajenye hukuncin da kake kokarin yankema *Habeebu,* wanda nafa maka tun lokacin danai istihara akan dalilin rashin zuwan su gida nagane cewa ba laifinsa bane, an hadashi da bakin aljanine wanda yasashi yamanta da kowa nashi kuma, Wannan yana daya daga cikin kaidin mace ne wanda babu wani da namijin daya'isa yakauce masa saidai wanda Allah ya tsare, daga kai dinsu shiyasa dakace abi suna ce maka "a ah mubisu dai addu'a domin ita ce ta dace dasu, kuma kaga cikin yardan Allah komai yazoda sauki tunda yanzu baya tareda wannan bakin aljani. Murmushi Abba yayi yace Alh Yusufa nasani sarai ba laifin sa bane tunda nasan babu yarda za'ayi ace "Na Allah yana da rai da lafiya yaki neman inda muke sannan yaki kula da *Sadeeya* wanda nasani yana *SONTA* sosai, nayi masa haka ne saboda kar gaba ya aikata laifi maka mancin haka kasan yaran wani lokaci idan ba'ana tsawa ta masu ba sai su ringa aikata ba dai-dai ba, shiya na tauna tsakuwa don kasa taji tsoro, yakareshe fadi fuskar shi dauke da murmushi. suma murmushi sukai Baffa Al-mustafa yace tabbas yaran saida haka nan, to yanzu dai ayi hakuri abashi "matar "shi,Abba yace za'a bashi amma sai taji sauki tunda batada lafiya, murmushi Baffa yayi zuciya sa cike da farin ciki yace to Allah yabata" lafiya, su kace ameen sannan sukai sallama kowa yanufi part dinsa. Saida *Harees* yashiga part din Hajiyar su yahado ma *Habeeb* coffee yasha sannan ya'iyacin abin, bayan sun gama sai suke dan taba fita wanda Rabin firar duk *Harees* ne yake yin ta yau kam tun misalin 9:00pm yabaro part din *Harees* yanufi part din Hajiya. Zaune ya'iske Hajiya ita kadai afalon kasa kasan cewa su *Deeya* sun fita zuwa part din lnna don ta gaida su daga can kuma taraka *Feeya* zuwa gida suna fita kenan shikuma *Habeeb* yana shiga, Cikin sanyi jiki ya zauna kasa tareda gaida ita amsawa tayi ba tareda ta kalle shiba, sai kuma shuru ya biyo baya, can dai cikin sanyi murya yace don Allah Hajiya ki ce "Abba yai hakuri dasauri tace ni Rabi'atu zan ce masa" yai hakuri?.. a ah ni ba zance yai hakuri ba kaidai kawai kayi abunda yace", yace bazan iyaba Hajiyarmu, tace to shikenan ai shi zaya iya yin abunda yace", tafadi tareda tashi tanufi sama. Bin bayanta yai da kallo *ZUCIYAR* shi cike da tsoron abunda ka'iya yafaru nan gaba, ahankali yafurta wai me zanyi maki ne *"Jana* na huce takaicin abunda kikai mun ne eye?..idan na sake ki Abba zayai mummunan fushi dani domin yace" karna kuskura nayi saki ba tareda laifin da yasa bama Ubangiji ba, kuma idan nace zan doke ki *"Jana* nakasa ki kawai zanyi, amma nasan abunda zanyi maki domin ni wannan abunda ki kai mun babba ne agurina, Wanda kamata yai ace "ke akasa nasaki bawai atilastani nasaki wacce zuciya takeso gangar jiki na ke *MURADI* ba, sannan yata shiya zauna akan kushin din tareda jigina bayan shi ya dauki kafa daya yadora akan daya sai kuma ya lumshe ido, Sannan yana cigaba dacewa Hmm wai ni *Habeeb* ake so na saki *"Leemah* ta, tab lallai akwai aiki shine har dawani kiran meeting aini wlhy idan duk mutan duniyar nan za'a tara saidai atara su amma bazan taba sakin *Leemata* ba, jiyayi ance nikuma sai ka sake ni tunda baka sona, dasauri yabude ido cike da tsoro yace... *_Jumma'atul Mubarak!!!!!_* Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [7/2, 11:49 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 3โƒฃ9โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Kai! *Leemah* ta meyasa kike fadin haka ne?..wai ke bakisan Allah yana fushi da matar datake tilas ma mijinta ya sake ta ba ummh?...ya karashe fadi tareda tashi yanufi gurin datake tsaye, Sanye take da wata blue abaya me duwatsu farare wacce ta matse ta sama wanda hakan ne yaba albakatun kirjin ta fitowa sosai, sai kuma tabude takasa duk dacewa tare me sosai hakan bai hana abayar yimata matukar kyau ba, especially da tayi rolling da gyalen abayar wanda yakara fitowa da zagayayyiyar kyakkyawar fuskarta me dauke da dogon hancin, inda lumsassun idanun ta suka kara kyau saka makon yar ramar datayi. Wani irin kyau tayi masa yayinda yaga jikinta yai sanyi da' alama jin abunda yafada ne yasata jin haka, don haka cikin Kwantar da murya yace *Leemah* ta don Allah kidai nafidin haka babu kyau kinji? kuma inason kibani dama zan nuna maki ni *Habeebullahi* ina matukar sonki kinji?.. *Leemah* ta, yakara shi fadi tareda mika hannu zaya kama hannun ta. matsawa tayi kadan tareda turo dan'karamin bakinta Sannan tace to nidai gaskiya ban yarda ba kuma banyin auren don haka kawai karabu dani eheee!. "Ahankali yace to *Leemah* ta gashi nikuma inayi shiyasa ma bazan iya rabuwa dake ba yanzu yakenan za'ayi?..ya kareshe fadi tareda tsura mata kyakkyawan idan shi masu bata tsoro, kafa tafara bugawa cike da sangarta aikam tuni jikinta yafara _shaking_ wanda yasa *Habeeb* din rufe ido domin wani irin abune yaji yana bin ajikinsa, Wanda ya tabbatar tsananin *SONTA* ne tareda matsananci _feeling_ dinta dake Adda bar shi, ahankali yabude idon tareda tsura mata su Murmushi yayi ganin abunda takeyi wanda kana gani zakasan kuriciya na matukar damun ta da kuma shagwaba, Yarfe hannu wa take tareda cigaba da buga kafa cin yanayin tana wauta tace nidai gaskiya Hmm *Habeeb* tunda ba dole ka kyaleni kajiko?..yace *Leemah* ta aina fada maki bazan iyaba, tace to shikenan ni kuma banyi! banyi!! banyi!!! eheee! tafadi tareda murgud'a mashi baki sannan ta haye upstairs din da gudu. Murmushi yayi tareda bin bayanta da kallo yace Kai! kaga mun yarinya sai dan'karan rigima, wai batayin auren hmm *"Leemah* ta kenan aitunda igiyoyin hannun na suke ai tuni kin gama yin aure domin dai bazan taba yin abunda akeso ba wlhy yafadi tareda nufar hanyar fita. _*Abuja*_ ******** *Jana* kam tun bayan shigar *Habeeb* dakinsa da sauri ta tashi tadauki Junior wanda baya ko iya tashi saboda dukan da *Habeeb* yaimasa, sama suka haye dakinta suka shiga direct toilet suka shiga wanka tayi masa sai faman kuka yake yana fadin Aunty *Jana* "Daddy mugune ko?.. bata saurare shiba domin gaba daya hankalin ta atashe yake saboda asirin daya karya Cikin lokaci kankani Wanda ita Sam bataso haka ba, shiyasa kwata-kwata bataji zafin dukan dayai ma Junior tareda marurru kan dayai mata ba kamar yadda taji zafin karyewar asirin, Bayan ta gama wa Junior wanka sai itama tayi ko data fito ta'ise shi yai barci wanda kana gani zakasan barcin wahala yake. Dasauri ta dauki wayarta dake kan gado afili tafurta Oh! Allah yasoni dazu na'ajiye wayata anan, da yanzu tana dakin shi kilama idan naje dauka yakara mun wasu marurrukan, layin Shafa tafara nema bayan tagani saita kira cikin sa'a tasa me ta bude karan wayar tayi, don haka anaji daga can Shafa ta dauka tareda cewa ke! ta *BB* bada kanki asare kije gida ki ce yafadi mutanan small London kuna shanawa fa, *Jana* tace hmm Shafancy kenan ai yau nafada maki duk wani shanawa babu shi, dasauri Shafa tace kamar ya bangane ba?... nan tafada mata duk abunda yafaru wani uban ashar Shafa tayo tareda cewa amma dai ke banza ce wlhy shine kika Bari har "suka hada?..tace wlhy Shafancy banyi tsannanin zaya dawo dawuri ba, tunda bai saba dawowa a wannan lokacin ba, yanzu yaza'ai kenan?.. tace gaskiya ban saniba sai dole mun koma gurin mlm "Dare, kuma kinsan shiba'ai masa sako saidai kaje da kanka tace haka ne yanzu kuma kozamu dawo gida sai anyima yara hutun makaranta, gashi ban sannan lokacin da zasu yi hutun ba, don Allah Shafancy idan akwai wani gurin daki kasani kifara zuwa mun kafin nadawo kinji?.. tace to Zan duba saidai bayani kudi, *Jana* tace ba damuwa kibayar idan nazo saina baki tace to shikenan sannan ta kashe wayar, saiga Lili tashiga dakin da gudu tana cewa Aunty *Jana* buyeni "Daddy jaya kai Aunty *Deeya* allula bana cho yaje dani, _kasan cewar haka *Habeeb* din yace" mata saboda tace zata bisu itakuma ba tason allura._ Dasauri *Jana* tace to zo nan kiboye tafadi tareda nuno mata kuryar gado, dasauri Lilin taje ta boye, yayinda ita kuma ta tashi ta nufi bakin kofar ta tura tareda labewa tana kallon lokacin da *Habeeb* yashiga dakin *Deeya* yadauko akwataiya sannan ya kulle dakin murmushi tayi me daukeda tsantsar farin ciki tace shegiya Allah yasa mata tafi kenan. *_Bauchi bayan kwana biyu_* ******* *Deeya* kam ta murmure abinta tayi kyau sosai tamkar ba'ita ce tashiga damuwa ba kwankin baya dasuka wuce, "Aban garen *Habeeb* kam ba'a cewa komai Cikin kwana ki biyu nan idan kagan shi, sai yabaka tausayi damuwa tayi masa yawa domin gaba daya yakasa shawo kan Abba da Hajiya, har dauwar tafiyar wato *Deeya* gawani irin *SONTA* dake sake ruruwa *ZUCIYAR* shi ga kuma gurin aikin shi sai faman kiran sa ake don hakane ma komai yasake da gule masa. Washegari yakama laraba da misalin kar 10:00am *Habeeb* yafito sanye cikin wani brown din yadi Wanda kallo daya zakai masa kagane me tsadan gaske ne, duk dacewa yarame hakan be hana yadin yimai matukar kyau sosai ba, yayinda kamshin turare ke faman tashi ajikinsa saidai fuskar shi babu walwala, fitowa yayi yanufi part din Baffa. Da sallama yashiga falon Baffa ne ya amsa kasan cewar suna zaune shi da lnna su nafira, Cike da fara Baffa yace a ah *Habeebu* ne?.. Cikin sanyi jiki ya amsa tareda zama kusada Baffan, bayan ya gaida su sai yayi shuru tareda dukar dakai kasa yayinda lnna ta tashi tanufi daki, Baffa kam ido yatsurwa *Habeeb* din inda ya fahimci akwai abinda

Chapter 16 of 42