nika kwanta na gyara maka wannan ruwan daka fisge saboda tsabar fitinar ka data motsa,
Hararan ya watsa masa cikin bacin rai yace mlm bazan kwanta din ba amsa zaka bani, batamun lokaci zaka tsaya yiba saboda inada abinyi kaji ko?..yace hum aikam ni banda abin yi sai kai, to ai kafi kowa sani abinda na karanta.
Dr *Harees* kuma da ake kirana aiba wai bane tabbas nidin cikakken likita ne wanda kaine sheda, tunda agaban ka nakarbi takardan shedar zama Dr ko?...
tsaki yayi cike da masifa yace to lallai kakoma ka karo karatu domin dai baka iya komai ba, kasani *Leemah* ta bata mutu ba don haka zanje na dauke ta nakaita wani asibitin inda kwararrun likitoci suke suduba mun ita, yakareshe fadi tareda ture hannun *Harees,*
Dasauri yarike shi tareda fadin aikam fa ban iya komai ba musamman idan numfashi mutun yatafi, to duk duniya babu kwararran likitan dazaya dawo da numfashin nan idan ba Allah yabashi ikon hakan ba, lallai kam *Leemarka* bata mutu ba dogon suma tayi ta kuma farfado da yardan Allah.
Wani mahaukacin ajiyar zuciya ya sauke dasauri yace Allah nagode maka yanzu tana ina?..yace gata can yafadi tareda nuna mashi inda ta kwance saidai tana bukatar hutu, kamar yanda kaima kana bukatar hutun so kwanta na gyara maka ruwan.
Cikin sanyi murya kamar ba shine ya gama masifa yanzu ba, yace pls dan'uwa I want to see her kaji?.
cike da tausayi shi yace muje kaganta,
Da taimakon *Harees* din suka isa wurin bed din dama sufa jiri sai kwalar *Habeeb* yake sosai, kuri yai mata da ido yana kallon kyakkyawa fuskar ta yanaji sonta da kaunar ta suna sake shiga jinin da jijiya da bargon shi, ahankali yakama lallausan hannun ta dayai matukar dumi yarike yace don Allah *Leemah* ta karki tafi kibarni kini?..
zaya sake magana ahankali *Harees* yace idan ka matsa zata farka ba'akan ka'ida ba, kuma hakan zaya iya haifar mata da matsala wanda nasan bazaka so hakan bako?..kai ya gyada alamar "eh yace yauwa to barta tahuta kaina muje ka huta idan kuka tashi sai kafada mata abinda zaka fada mata kaji?..cikin sanyi murya yace to.
Har zasu wuce bed din twice Cikin zolaya *Harees* yace dan'uwa wai me kake nufi ne?.. da bazaka ga twice baby boys dina ba, koda yake nagane haushin su kakeji saboda ta sanadiyar zuwan sune kake kokarin rasa *Leemarka* ko?..yakareshe fadi tareda daga net din da'aka zagaye su dashi,
yace ga *KYAUTAR* da Allah yabamu wanda kai ko sau daya baka kalle su ba, saboda kanajin haushi zasu rabaka da *Leemarka* KO?...
shin idan da hakan ta kasan ce laifin sune ko?...
Dasauri ya kalli *Harees* din sai kuma yamai da kallon shin kan kyawawan twice
dinsa da suke matukar kama dashi, tamkar yayi kaki sai barcinsu suke abinsu gwani sha'awa saidai basu dawani girma,
tsawon lokaci yana kallon su
yanajin son su da kaunar su yana ratsa shi, saidai so da kaunar dayake yi wa maman su yaninka nasu sau babu adadi,
Ahankali yasaki lallausan murmushi wanda rabon da *Harees* yaga yayi irin sa har ya manta rana, sannan ahankali yace...
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นmeenat Lufhat๐น
[11/9, 10:17 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
8โฃ2โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
A ah dan'uwa banajin haushin su" ko kadan, sannan kuma koda Allah ya kaddari hakan aiba laifin su bane,
asalima nine me laifin da kaunar maman su tarufe mun ido har na manta dasu.
yace uhum dan'uwa kenan ai basu kadai ka manta ba, kowa da komai ma ka manta, kaidai *"Leemarka* kawai, shin dan'uwa wani irin so kake yima Queen of beauty ne haka?... pls ka fadamun domin yau nasha mamakin ka yanda duk ka birkice, yes I know u love her so much saidai banyi tsammanin kaunar da kake yi mata yazarta wanda nasani ba.
Yace dan'uwa indai akan kaunar *Leemah* ta ne zakaga fiye da abinda kagani, ni kaina bansan irin kaunar danake mata ba saidai nasan abu guda, wato so da kaunarta ajinina yake wanda ya dade dayiwa ZUCIYATA illah,
dasauri yace illah kuma?..murmushi yayi me kayatarwa yace "eh ba illah me cutarwa ba, cike da mamaki yace au dama akwai illar da bata cutarwa?..cikin sanyi murya yace au Kai baka sani ba?..yace a ah nikam ban sani ba, yace to bari kaji illah mara cutarwa,
kaga dai ina daya daga cikin mutane masu matsananciyar sha'awa wanda kai kasan haka ai?...kai ya gyada alamar "eh, yace yauwa sai kuma ya lumshe ido tareda yin shuru na dan lokacin sai yabude idon sannan yace dan'uwa kasan me?..."a ah sai kafada,
yace yauwa kaga dai *Leemah* ta tasiye zuciya ta da abubuwa masu matukar yawa, nafarko tun ranan da muka kasan ce abu daya ni; da *Leemah* ta ban taba nemanta ta kiyarda ba, dan'uwa idan zan nemi *Leemah* sau goma ashimfida ta, zata zo kuma bazata taba nuna mun gajiyawar taba, wanda akarancin shekarun ta bukata ta tayi mata yawa amma haka take kokarin biyamun ba tareda gazawa ba,
wanda na tabbatar idan watace bazata iya hakan ba, bayan haka duk abinda nakeso tanayi mun batason bacin rai akoda yaushe burinta shine ta faranta mun, idan nace banason abu to tabarshi kenan kasan tunda tasamu ciki bata iyacin abincin data dafa da kanta?...
amma haka zata tashi tadafa mun wanda wani lokacin da kyar take gamawa, kuma duk don ta kyautata mun Wani lokaci idan nace *Leemah* ta kibari banason fakina wahalarda kanki akaina, sai tace" indai zanyi farin ciki to shikenan kuma duk lokacin da zance mana nabaro abuja zanzo bauchi,
to zan iske ta girkamun abinci kala-kala masu kyau kai itadai burinta akoda yaushe ta kyautata mun, hum kai dan'uwa abubuwan da *Leemah* ta takemun suna da yawa wanda idan nace zan fada maka su to zamu kwana bangama fada makasu ba,
don haka wannan shine illar da kaunar ta yaimun wanda ba cutarwa,
Shin Dan'uwa don Allah meyi maka irin wannan kyautatawar arayuwa kaga kana nema rasashi yaza kaji?..
yace gaskiya dole mutum taji ba dadi ya birkice kai yama shiga wani hali ba tareda yasan yayi hakan ba, yace yauwa kaima zaka fada
Shiyasa bana fatan ta mutu tabarni, domin idan har hakan zata kasan ce to akwai matsala saboda wlhy Zan shiga wani irin mawuyacin hali karshe na bita domin rayuwa babu ita wlhy zaiyi wuya agareni.
Cike da tausayi yadafa kafadar shi yace haka ne dan'uwa nagani kodaga bacewar ta, saidai kasani, babu matsala ga abinda Allah ya rubuta zaya samu bawa, Kai musulmine ka yadda da Allah da manzon shi ka kuma yadda da kaddara me kyau KO Mara kyau don haka sai kayi imana da duk abinda yasamu bawa to haka Allah yaso,
cikin sanyi murya yace haka ne nagode da tunatarwa.
Yauwa to yanzu yima twice dina Addu'a ahankali ya duka ya dauke su yai masu Addu'a daya bayan daya, sannan sukaje yamai da mashi ruwan tareda yimashi alluran bacci bayan yagama sannan yace to sleep better *Habee-Leemat* murmushi yayi cike da jindadi ya lumshe ido sannan yace Ok" thanks and take care of her before I wake, yace karka damu I will do it insha'allahu nan take wani barci me nauyi yadauke shi, Kai ya girgiza yace Kai! irin wannan kauna haka to Allah yabar ka da *Leemarka* har karshen rayuwar ku ameen ya allah sannan yafita.
*_Nima nace ameen kuma readers kuce ameen_*โบ
Cikin kankani lokaci yan'uwa suka cika asibitin har da Abba da Baffa al-mustafa, amma banda baffa da lnna sukam sunce tunda yan'uwa sunje tosu basai sunje ba,
Saidai *Harees* yace adinga shiga daya bayan daya ana ganin su, saboda kar hayaniyar mutane yatashi gashi kuma suna bukatar hutu,
Haka akayi saidai *Feeya* da Hajiyarmu kam dasuka shiga su kaga yanda *Deeya* takoma gakuma halin datake ciki, aisai suka fara kuka har jikinsu na rawa saida aka fitar dasu daga dakin,
kasan cewar tare suka shiga,
sosai yan'uwa suka tausawa halin da suke ciki musamman *Deeya* don haka suke ta zuba masu addu'a allah yabasu lafiya, twice kam kamar za'acinye su don so da kauna musamman *Feeya* da Hajiyarmu kasan cewar sukam dama komai nasu akan *Deeya* yafina kowa,
akam cikin kankanin lokaci aka shirya twice cikin wasu kayan sanyi kalar ja da ratsin yalo masu kyau, Bayan kowa yaga su yai masu addu'a tareda fatan allah yaraya su akan sunna ya albarkaci rayuwar su, sannan akai mai dasu aka kwantar saboda *Harees* yace kar acika jagulasu tunda sudin bakwaini ne, kuma duk abinda ake suna ta barci abinsu da'alama yaran bamasu rigima bane.
Suna nan zaune har bayan isha'i basu farka ba, hakan ne
yasa hankalin yan'uwa yafara tashi, musamman Hajiyarmu da *Feeya* saida *Harees* yace karsu damu koda sun kai gobe basu farka ba, babu komai duk cikin samun sauki ne don haka hankalin su ya kwanta.
Shiyasa suka tafi gida sai gobe zasuzo inda aka bar Hajiyarmu da goggo Lanti zasu zauna da'ita tareda kula da twice, shikam *Harees* dama nan zaya kwana dole don haka *Feeya* da *Harees* su basu tafi gida dawuri ba sai 11:00pm sannan.
********
*_Washegari_*
*********
Da misalin 10:30am *Habeeb* yafarka *Harees* ya taimaka mashi yatashi ya zauna idon shi na kan bed din *Deeya* Dasauri yace dan'uwa har yanzu *Leemah* ta bata farka ba?..yace "eh amma fa babu matsala zata iya farkawa koda wani lokaci, ajiyar zuciya yayi Ok",
yace yanzu ina ke yi maka ciwo?..fuska ya yamutsa yace kai na saidai ba sosai ba sannan banajin karfin jikina, yace sorry yanzu tashi muje kai wanka ko kaji karfin jikin sannan kazo karanka sallolin da'ake binka sannan na auna BP naka, yace Ok saida yaje yaga *Deeya* yadade tsaye akanta yana kallonta yanajin kaunar ta nasake 'karuwa acikin ran shi,
ahankali yashafa kanta yaimata addu'a bayan yagama sai yaimata kiss agoshi, sannan yaje yashiga toilet yai wanka tareda dauro alwala yafito sanye da jallabiya brown wacce *Hafeez* yakawo mashi, balaifi yadanji karfin jikinshi bayan ya'idar sallah sannan *Harees* ya auna jininshi balaifi ya sauka ba kamar da ba,
bayan yayi dan rubutu a file sannan ya kalli *Habeeb* yace tashi muje gurinsu Hajiyarmu yace sun zo ne?.yace "eh ainan suka kwana cike da mamaki yace suna ina?..yace suna nan adakin dayake kusa da wannan har su Mamu duk sunzo kaga idan kun gaisai sai kakarya sannan kasha magunguna Dasauri yace to *Leemah* ta fa waza yatsare ta?..
yace Allah wanda dama shike tsare da'ita, goshi yadafa yace to ainasani ina nufin wanda zaya tsaya adakin kafi mudawo koda tafarka, yace Oh! kamar nurse kake nufi ko?..yace "eh karka damu akwai nurse da nayi wa magana,
yace Ok har zasu fita saiga wata nurse tashigo gaida su tayi *Harees* ne ya amsa tareda fadin yauwa, sis Balki kafin nadawo idan ruwan yakare kisa mata wani pls kiyi yanda nace tace to idan kuma kinga da matsala ki kirani ina wannan daki dake kusada wannan, tace ok sir sannan suka fita.
Da sallama suka shiga dukkan suka amsa mamaki ne yakama *Habeeb* gani yan'uwa cike da dakin kasan cewar duk sunzo, aikam ba karamin dadi yaji ba daya gansu tsugunna wa yayi yagaida su goggo Lanti suka amsa tareda tambayar shi yajiki?.yace da sauki,
sannan yamike ya zauna akan kujera, yayinda yan'uwa suke ta gaida shi yana amsa wa *Feeya* tace Hmm *Habeeb* na hada maka coffe?. kai ya gyada mata domin wata irin yinwa yakeji, bayan ta hada tabashi yana cikin sha sai *Harees* yadauki remote din t-v tareda fadin bari muga labarai.
yana kunnawa ana fadin a yau ne aka samu Labarin jiya yan sanda sunyi nasaran kama barayin da suka sace matar *Senate Habeeb,* yanzu haka suna hannun yan'sanda, yayinda ita kuma matar Senate take kwance a gadon asibiti ba lafiya bayan ta haifi tagwaye duk maza, to muna ta ya Senate murna ganin matar shi tareda samun karuwa sannan muna taya shi addu'ar allah yaba matar shi lafiya tareda dukan al'umma da basuda lafiya,
wayan da kuma suke da'ita allah yakara masu lafiya ameen, duka dakin aka amsa da ameen yayinda *Habeeb* yayi tsaki tareda fadin kai allah dai yasa wake wato shi dan siyasa duk abinda zagayi arayuwar shi sai kowa yasani?...Hajiya tace to meye dan kowa yasani?..
yace hum wato shi baya da sirri kenan KO?.. tace to ba gashi yanzu anyi maka addu'a ba, ita kuma dama addu'a wani lokaci sai kayi Allah bai karba amma idan wani yayi maka sai kaga an karba, yace haka ne Hajiyarmu amma nasan bazaki gane ba yanzu kinga maganar nan zuwa anjima zakiga yan jarida sunzo sun cika mutane da tambayoyin iskanci yakareshe dayin tsaki,
Sannan ya mikawa *Feeya* cup din tareda sauran coffee, karba tayi tareda fadin azubo abinci?..cike da hassala yace bana bukata dasauri *Harees* yace "ah! dakata mlm aiba ita takar zomon ba, Hajiya tace ko ratayama ba'a bata ba *Harees* yace kaji gaskiya kam daga mun taimaka maka sai kafarayi mana ihu,
shikam shuru yayi tareda lumshe ido ya jingina kaida bango, aranshi ya najin haushin duk abinda zaya yi ko yasame shi sai anyada shi agari. dakarfi aka banko kofar dakin hakan ne yasa duka dakin suka kalli kofar harda *Habeeb* da tuni yabude ido dasauri, nurse Balki ce jikinta na rawa cikin tashin hankali tace...
*_Slm readers don Allah ku cigaba da hakuri dajin shuru, insha'allahu mun kusa kai karshen Labarin nagode._*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeeenat Lufhat๐น
[11/9, 10:18 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
8โฃ3โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
Sir tafarka saidai tana jijjiga sosai nayi kokarin tsayar da'ita amma nakas....aibata karasa ba *Habeeb* yai wani irin mahaukacin mikewa zumbur kamar wanda aka tsirawa allura bazato aikam kafin kace me har yabar dakin,
dasauri *Harees* yabi baya shi nurse Balki ma tabisu yayinda duk yan'uwa suka tashi tsaye, cike da tashin hankali suna me Addu'a samun sauki ga *Deeya*.
Cikin tashin hankali suka shiga dakin dasauri *Habeeb* ya karasa gurin ta yarike hannun ta, yayinda *Harees* yafara bata taimaka cikin gaggawa, sannu ahankali tadaina jijjagan sannan numfashin ta yafara tafiya dai-dai yanda yake hakan ne yasashi cire mata oxygen din,
ahankali take kokarin bude idon ta hakan ne yasa *Habeeb* kara damke hannun ta cikin nashi, muryar shi na rawar yace pls open u eyes *Leemah* ta kinji?..ahankali ta bude idon sai kuma ta lumshe idon yayinda hawaye ke gangarowa tagefen idonta, can sai bakinta yafara motsi,
Dasauri yakai kunnan shi saitin bakin ta tareda fadin sannu sannu *Leemah* ta meki keson uhum?..jiyayi tana salati can kuma saita furta Hmm na, dasauri yace gani nan kusada ke, still idon ta rufe take kiran hmm ta tana kuma jujjuya Kai shikuma sai fadin yake gashi kusada ita saidai ga dukkan alama banajin shi, can kuma saita furta Hmm ta dakarfi tareda zabura zata tashi
dasauri ya rungumeta tareda fadin *Leemah* ta gani nan tareda ke kinji?.. ajiyar zuciya tadauke dakarfi tareda rungume shi sosai jikinta sai kerrrma yake sai kuma tasaki kuka, cikin rawar murya tace Hmm na mutafi gida mutafi gida mutumin can mugune yanata bani wahala kuma yace zaya kasheni, pls Hmm na ka dauke ni mutafi ida inajin tsoron shi, I don't want to see him again kaji?..
ajiyar zuciya ya sauke tareda shafa bayan ta Cikin sigar lallai shi yace it's Ok it's ok my *Leemah* stop cry l'm here with you no body can hut u again kinji?.,ahankali tadago kai ta kalleshi tareda shafa sajen shi still hawaye na gangarowa kan fuskar ta yatsa yasa yana share mata, cikin sanyi murya tace u are my sweet Hmm ko?...
yace yes I'm u sweet Hmm u are my honey *Leemah* right?... yakareshe fadi tareda sakin lallausan murmushi, itama murmushi tayi tace yes.
Sai kuma ta kwabe fuska tareda dafa goshin shi tace Hmm na bakada lafiya KO?...yace *Leemah* ta yaza'ayi nayi lafiya bayan baki tareda ni umuh?..
Ke bakinsa rashinki agareni babban matsalane arayuwata ba?...kuma aikema aibaki da lafiya so nima aidole nayi rashin lafiya tunda abokiyar rayuwata batada lafiya, so yanzu fadamun ina ke yi maki ciwo?...
ahankali tace kai na sannan inajin yinwa sosai tafadi tana yamutsa fuske tareda shafa cikin ta jitayi wayam bakamar yanda yakeba, hakan ne yasata kallon *Habeeb* dasauri wanda shidin ma ita yake kallon fuskar shi daukeda annuri, fuska takwabe tace wayyo Hmm na shikenan yacire ma my sweet *Feeya* baby ta, dama yace" zaya fasa ciki na yaga abinda ke ciki, ta kareshe fadi hawaye nasake zubowa,
dasauri yace "a ah *Leemah* ta ki daina wannan kukan banaso, tace to to Hmm na nadai na amma ai yacire unborn baby ko?..tunda banga shiba yace "a ah shidin aibai isa yacire ajiyar da Allah yayi acikin *Leemah* ta ba, tace to Ina Cikin?..
dariya yayi tareda Shafa cikin ta yace ga cikin nan abinci ki kuma Allah yanufa kin haifi twice lafiya, baki tabude tareda zaro ido cike da mamaki tace Hmm na twice nahaifa kuma a seven month?..
cike da farin ciki yace yes *Leemah* ta suna nan duka maza kuma lafiyar su lau nagode *Leemah* ta Allah yai maki albarka ciki sanyi murya tace Hmm na don't thank to me thanks to almighty Allah, yace yes I thanks to him since kuma zan cigaba da gode masa har karshen rayuwata yakareshe fadi yana kokarin had'e bakin su.
Dasauri *Harees* yai gyaran murya wanda dama tuni suka zama yan kallo shi da nurse Balki, ahankali *Habeeb* yadago kai ya kalli shi tareda fadin Oh! Dr *Harees* ashe har yanzu kana nan kenan?..
harara ya wata mashi yace "a ah ban ma zoba tukun kaji dan rai ni hankali kawai, kawani manta wa da mutane agurin sai zuba soyayya kake kai adole ga Mr Love ko?.dariya yayi yace sorry aikasan soyayyar ta ajinina yake, shiyasa idan ina tareda ita kaina ma manta wa nake dashi,
yace wato balle wani ko?..yace yauwa ashe dai kaga ne, yace tun yaushe nagane baban soyayya to ai sai kayi mata ahankali tunda kagadai bata da lafiya, ke kuma sauran kibiye masa ya cika ki da surutu har kanki yakara yin ciwon, tunda shi na kula idan yana tareda ke bakinshi zuba yake kamar anbude fanfo tsabar surutu.
Dariya sukayi har da *Deeya* cike dajin kunyar *Harees* taboye fuskar ta akafar *Habeeb,* *Harees* yace to yallabai dan gyara na dubata ko?.. murmushi *Habeeb* yayi tareda gyarwa nan ya auna BP ta inda yaga yasauka sosai yai rubutu a file sannan ya tambaye ta yanzu inake mata ciwo?..tace kai amma ba sosai ba yace sorry zaya daina idan kin shi magani, Kai ta gyada tareda kallon *Habeeb* Wanda shidin ma ita yake kallo fuska dauke da annuri yace ya'akai ne honey ta?.. Cike da shagwaba tace hmm na Inajin yinwa kuma inason ganin my sweet *Feeya* da Hajiya ta dakowa dakowa nayi kewar su sosai, yace Oh! sorry yanzu
zaki ci abinci kuma zakiga su sweet *Feeya* suna nan sunzo suma sunyi kewarki sosai, sannan ya kalli *Harees* yace pls kace su shigo su ganta *Sofee* ta hado mata tea me kauri da abinci, Oh! da brush kaji?..
Cikin irin girmama wannan da yaro keyma boss dinshi yace angama ranka yadade, Mrs senator hamman safiyya angon Halimatus-sadiya
Baban "safina da "Affan namijin duniya na Dr *Hareesu,* au na manta inji ance sai yaje yakaro karatu sannan zaya cika Dr to yanzu za'a taimaka mashi ne yakaro karatun KO?.
yakareshe fadi tareda dan rusunawa,
Cike da farin ciki *Habeeb* yake dariya sosai irin wanda yadade beyi ba, cikin Wani irin nishadi da yakeji yace godiya nake na baka KYAUTAR mota kaji hamman Halimatu-sadiya, angon sofee baban Rabi'atul adawiyya baban twice, likintan *Habeebullah* bakada bukatar zuwa karo karatu domin u are the best Dr in word,
ido *Harees* yazaro tareda fadin really?..dariya *Habeeb* yayi yace yesss!
yace kai amma naji dadi na kuma gode don haka bari nayi sauri na cika aikin Oga yakareshe fadi tareda nufar han yar fita dasauri yana dariya, su ma dariyar suke yayinda nurse Balki tabi bayanshi tana dariyar zuciyar ta cike da sha'awar su.
Cikin lokaci kankani yan'uwa suka cika dakin suna gaida ita tana amsa wa cikeda farin ciki, *Feeya* Da Hajiya kam kamar zasu cinye ta don kauna,
bayan tayi brush tasha tea sannan aka zuba mata lafiyayyan tuwan farar shinkafa, da miyar kuka dataji kayan cikin rago ta man shanu kamshi sai tashi yake tare suka ci da *Habeeb,* suna ta zuba santi aikam sai dariya ake masu kwanan su biyu asibiti *Harees* ya sallame su ganin sunji sauki sosai saima soyayya, suke zubawa abinsu batareda sun damu da mutanen dake gurin ba.
Koda suka koma gida abokan arziki nata zuwa gaida su, lnna da Baffa kam dakyar suka shiga ganin *Deeya* saboda tsabar kawai ci irin nasu, aikam *Deeyar* sai fushi take ta naturo baki saida Baffa yai lallashi tukun tareda fada mata Kala mai masu dadi aikam sai dariya take tana zuba mashi shagwaba yayinda lnna keta hararan ta, tareda fadin wai tagirma amma batasan ta girma ba.
Naran suna twice
sukaci sunan Abba da Baffa sai *Feeya* tace aringa kiran su *Haneef* da *Haleem,* mejego tayi kyau har tagaji itada *Feeya* suna tasa kaya iri daya gwani sha'awa,
shima angon jego yayi kyau sosai suma kaya iri daya suke sawa shida *Harees* kai anyi shagali sosai ranan *Habeeb* yayi *KYAUTA* har bai san adadi ba haka shima *Harees*.
********
Bayan sati daya dayin suna Wanda yayi dai-dai da sati biyu kenan da haihuwar *Deeya,* acikin sati biyu nan idan kaga *Deeya* sai kayi mamaki tayi kyau abin ta haka ma *Haneef* da *Haleem* sunyi shar abinsu gwanin sha'awa kamar ba yan wata bakwai ba, kasan cewar suna samun kulawa sosai a gurin Hajiya sai kuma akayi sa'a nonon *Deeyar* yana da kyau.
Ayaune *Habeeb* ya samu zuwa police station saidai be iske D.p.o ba don haka yasa aka fito mashi dasu ado, wayan da gaba daya sun fita hayyacin su saboda dukan da suke sha kullun,
*Habeeb* ya kallesu daya bayan daya sannan ya tsayar da kallon shi kan ado fuska had'e yace wanene yabaka izinin shiga rayuwata?.
dakyar yace ba kowa, yace good kashi ga rayuwata akaro nafarko nayi maka gargadi amma bakaji ba saboda kaidin jakine, saika sake shigowa rayuwata akaro na biyu ko?.
to inason ka bude kunne ka saurare ni dakyau zayi maka gargadi na karshe wato kar kayi kuskuren sake shiga rayuwata akaro na uku, idan kayi haka to ka shafawa kanka lafiya idan kuma ba kayi ba humm, Ina nufin idan ka sake shiga rayuwata akaro na uku to kasani zanyi maka abinda har ka mutu bazaka manta dani arayuwar kaba,
don haka abinda yafi maka sauki shine kawai kasa aran kabaka taba sanin wani mutun wai shi *Habeeb*
ba, Cikin tsawa yace kaji ko?.. dasauri yace to domin wani irin mugun kwarjini *Habeeb* yaima shi, yace yauwa bad man ka kyauwa maka ka,
sannan yamike dasauri cike da kasaita ya kalli police din dake tsaye, yace kuna iya sakin su domin banida bukatar su, yace to yallabai amma sai D.p.o yadawo yace ok tareda fita dasauri police din yanayin mashi a sauka lafiya.
koda da *Habeeb* ya'isa gida direct part din Hajiya yanufa da sallama yashiga babban falon saidai bai iske kowa ba don haka yanufi falon sama, *Deeya* ce zaune ita kadai ta zuba ta gumi tana sanye da riga da sike na wata koriyar atamfa me ratsi yalo tayi mata kyau fuskar ba kwalliya,
saidai hakan be hana kyanta fitowa ba, saidai kallon daya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 42