take sakeyi mata huduba data rike mijinta da kyau tayi masa biyayya, ta kula da duk abunda yake so takuma kiyaye wanda bayaso, domin "shi me hakuri ne saidai idan aka kureshi to fa sai ahankali do haka ta kula da hakan, sanna ta kula da cikin "shi domin shidin acici ne baya wasa da cikin sa dariya *Deeya* tayi tareda cewa kai Hajiyar mu "Hmm din nawa ne acici?..
tace "eh aikin san haka don haka sai ki kula sosai, sai shinfid'ar sa shima ki kula dashi da kyau, tace to Hajiyar mu ai zan din ga gyara masa kamar yadda nake gyara maki naki ko?..murmushi tayi domin ta fahimci *Deeya* bata gane inda tado saba, "eh kawai tace domin tasa nan gaba kad'an zata gane sannan ta cigaba da fada mata abubuwa masu mahimmanci da zata kula dasu agidan auren ta, bayan tagama sai ta tashi taje ta dauko mata wani hadadden tsumi acikin cup ta bata, fuska taya mutsa tareda karban cup din a zaton ta magani ne me d'aci
dariya Hajiya tayi tareda cewa sanye ki bani cup, ahankali ta kafa cup din a baki tareda rintse ido sannan tafara sha, dadin dataji ne yasata waro ido tareda sake bude d'an mitsitsin bakin ta, ta nasha sosai wanda saida ta shanye tas sannan ta cire cup din tana lasan baki tareda lumshe ido,
Tace umh dadi idan akwai akara mun, dariya Hajiya tayi tace yana nan dayawa nata nade shi domin ke do haka duk lokacin daki ka tashi kizo ki sha, tace yauwa Hajiya ta nagode daga nan suka cigaba da fira.
Can saiga kiran *Feeya* ta wayar Hajiya murmushi Hajiyar tayi tareda cewa *Deeya* dauki wayar nan Auta ce nasan dake take san magana, dasauri tadauka tareda cewa Oh! my sweet *Feeya* am so sorry kinji waya ta akashe KO?.. tace wlhy to ya'akayi ne?.. tace dai-dai daga nan suka fara fira, wanda sun dauki tsawan lokaci suna yi saida Hajiya tayi masu magana sannan suka kashe wayoyi,
bayan tafada mata Hmm *Habeeb* yace" ta kun na waya zaya kiran ta,
Key Hajiya tabata tareda cewa ga makullin dakin ki nan don haka tashi kitafi Allah yatashe mu lafiya, tace to tareda kar batayi mata saida safe sannan tafita.
part dinsu ta nufa alokacin 11:30pm dai-dai na dare, DA sallama tashiga falon dai-dai lokacin su Baffa suka mike zasu shiga bacci, ganin ta yasa suka tsaya cikin mamaki Baffa yace *KYAUTAR ALLAH* daga ina kika fito haka?.. tace part din "Hajiyarmu, yace me ki kazoyi nan din?..ido tazaro cike da tsoron jin abunda Baffa yace" sai kuma tayi shuru tana kallon shi, domin wani irin kwarjini Baffa yai mata wanda yasa takasa cewa komai ahankali tadukar dakai tana wasa daya tsunta.
Saida yasake tambayar ta sannan ta dago kai tareda turo baki tace ayya Baffana nazo ganin kune fa, yace dayake mudin bakine agurin ki ko?.. cikin kwantar da murya yace haba *KYAUTA* yanzu fa karfe 11 :30pm amma sai yawo kike ba tareda kin zauna dakin kiba to idan "mijinki yazo bai'iske kiba fa?, cikin sanyi murya tace to ai Hmm *Habeeb* din ba yana nan,
Dasauri lnna tace tunda bayana nan sai akace kiyi ta yawon bi shiya-shiya KO?.. tace to ai yace" idan yadawo zaya kirani, lnna tace to kije dakin ki ki zauna ya'iske ki acan ba sai yadawo yana kiran kiba har zatayi magana, Baffa yace jeki dakin ki *KYAUTA* Allah yatashi mu lafiya karki sake fitowa a irin wannan lokacin kinji ko?..
ahankali tace to saida safen ku lnna tace Allah yatashi mu lafiya
kuma karki sake shigo mana shiya ba tareda izinin "mijinki ba kinjiko?...tace to tareda fita.
Ahankali take tafiya tamkar kazar da kwai yafashe wa aciki, tunani take aranta yanzu shikenan ta daina kwana part dinsu Dana Hajiyarmu, sai ana Hmm *Habeeb* hawaye ne suka zubo mata.
Karar wayar ta ne yakatse mata tunanin datake tareda tsaya wa, ahankali ta bude jaka taciro wayar
Hmm dina ne ya bayyana akan wayar, cikin kuka tadaga tace Hmm dina kadawo ne?..gaban shine yafadi jin tana kuka don haka da saurin yace *Leemah* ta kuka kike mesa meki wane ya taba mun ke?... Duk alokaci daya yajero mata wayan nan tambayoye yin tareda kokarin shi
gowa harabar gidan,
Tafiya ta farayi ahankali still wayar tana kunna cikin kuka zata fara yi masa ba yani, dasauri yace gani nan zuwa *Leemah* ta juyoma kiganni;
Ahankali ta juyo tundaga ne sayake sakar mata kyakkyawa murmushi, cikin takun kasaita yanufe ta tareda bud'e hannu wan shi alamar taje gareshi aikam cikin sassarfa tafad'a faffad'an kirjinshi tareda sakin kuka me cike da shagwab'a.
Ajiyar zuciya yayi tareda yarintse ido domin jin kukan ta yayi har cikin ranshi.
Ahankali yace Oh! my Lovely *Leemah* me yafaru wanene yasa mun ke kuka
yi shuru ki fadamun kinji?..cike da shagwaba tace to ba "Baffana da lnnata bace daga nashiga ganin su "KO zama banyi ba shine suka koroni, murmushi yayi sai kuma yace Kai!Kai!!Kai!! yanzu Baffa da Inna ne suka koroki?..tace "eh,
yace to saboda me?.tace wai dare yayi na tafi dakina, yace ayya *Leemah* ta to kiyi hakuri kibari da safe sai kije kinga su ko?.. yafadi tareda da go kanta daga kirjin shi, yana me share mata hawaye tareda kallon kwayar idon ta yana jin SONTA yana bin jinin shi, baki ta turo tareda cewa to ai "lnna tace" karna sake shiga part dinsu" ba tareda izini ka ba,
yace karki damu *Leemah* ta indai nine tona lamunce maki duk lokacin daki
ka tashi ki shiga duk part din daki keso ko'i na nan ko bana nan kinji ko?.. Cike da farin ciki tace to har da part dinsu my sweet *"Feeya?..* yace "eh amma ban yadda kiringa zuwa da dare ba,
Cike da murna tace yauwa hmm Dina nagode yace to muje mu kwanta yafadi tareda daga ta sama yanufi part dinsu, dariya ta kyalkyace dashi tareda kwakume shi cike da shagwaba tace wayyo Hmm Dina zan fadi dariya shima yayi tareda cewa ba zaki fadi *Leemah* ta
Dai-dai lokacin da suka shiga falon.
Dasauri
*Jana* dake zaune tamike ta tari gaban su, sanye take da wata yar figigiyar riga bacci iya guiwa kanta yarbatsai-yarbatsai, kallon ta *Habeeb* yayi
sama da kasa yayinda *Deeya* mata ke bintada kallo fuska daure yace lafiya kika tare mana hanya?.. tace dama ku nakejira da tun dazu, cike da mamakin ta yace...
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenat๐น
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
5โฃ4โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
Kamar ya mu kike jira tace "eh kuna kejira, yace to gamu saiki fadi abunda za muyi maki dakike zaman jiranmu tun dazu kinji ko?..tace "eh saboda gaskiya niban yadda sai kayi kwana bakwai adakin ta ba sannan kaje dakina, yace to sai me don baki yadda ba?..tayi shuru cikin tsawa yasake cewa nace to sai me don baki yadda ba eyeee?... Dasauri ta dan matsa baya kadan tareda cewa atoba sai abar shi akwana biyu-biyu ba, inba dai so ake aci amana taba yaza'ai ace sai ka kwana bakwai adakin ta sannan kazo dakina gaskiya bazan yadda ba ehee, Cikin bacin rai yace to kar Allah yasaki yadda kinji KO?..waima angaya maki Ina neman yaddar kine?..to bari kiji nagaya maki koki yadda ko karki yadda babu abunda ya dameni kinji ko?..domin ke baki isa kiyi jayayya da fadin Allah ba haka kuma baki isaki haramta mun abunda Allah ya halasta mun ba kinji KO?
Yar rainin hankali kawai me yasa acan gaban su" Abba bakice baki yadda ba sai nan saboda kin raina niko?..to kisani ni *Habeeb* nafi karfin raini agurin ki wlhy kuma baza'a barshi akwana biyu-biyun ba sai nayi kwana bakwan yar bakin ciki inyaso duk abunda zakiyi sai kiyi kuma na rantse da sarkin daya busamun numfashi idan ki kasake kirana da maciyi amana zakisha mamaki, zaki bani guri na wuce KO sai nayi ball dake agurin nan eyeee?..
ya kareshe fadi da karfi.
Aikam da sauri ta masa gefe yanufi dakin shi rungume da *Deeya* wacce tasake kwa'k'ume shi saboda tsoron tsawar da ya bugawa *Jana,* ltakam *Jana* bin bayan su tayi da kallo zuciyarta Cike da mamakin abubuwan da *Habeeb* yake mata tareda tambayar kanta wai shin meyasa *BB* tan yake mata haka ne?..to kodon yaga yayi sabon aure ne?..Oho! mashi kwaf tayi tareda hawa sama tana fadin aiza kagama kwana bakwan ne zakazo kasa meni.
*Habeeb* kam bai dire *Deeya* ko'ina ba sai bedroom dinsa akan katafaran gadon shi tareda yimata runfa, dariya yake mata sosai ganin yadda ta k'wak'ume shi kamar wacce akace za'akama, gaba daya hannu wanta ta zagaye bayan shi dasu yayinda ta tura fuskar ta afaffad'an kirjin shi sai sauke ajiyar zuciya take tareda shakar dadd'adan kamshin turanan shi, ahankali yazare hijab din ta.
Cike da shaukin kaunar ta yace Kai! *Leemah* ta kin cika tsoro dayawa yanzu d'an wannan tsawar danayi ma *"Jana* shiya baki tsoro?..Cike da shagwaba tace Hmm dina ni banason tsawa tsoro take bani, ahankali yake goga sajen sa afuskarta yanajin wani irin sonta da sha'awarta suna bin sassan jikin shi, cikin cool voice yace am so sorry *Leemah* ta zan kiyaye yinta a gaban ki tunda bakiso kinji?.. idon ta lumshe tace to.
"Ahankali ya cigaba da goga mata sajen shi afuskar ta yayinda yasa hannun daya yazame ribbon dinta tareda cusa hannun shin cikin lallausan suman kanta yana, ya mustawa yanajin wani irin ma tsanancin feeling dinta har gangar jikinshi yana bukatar ya kusance ta" saidai kuma aranshi yanajin bazaya iya kusantar *Leemarsa* ba alhalin yana dauke da wannan ciwon wanda dazaran ya kusance to itama zata dauka ne shikuma ba zayaso haka ba.
Sannu ahankali yahad'e bakin su yafara tsotsa, wanda yake ganin haka ne kadai zaya rage mashi abunda yakeji game da'ita, saida yadauki tsawon wani lokacin sannan yacire bakin shi daga nata yana sauke numfashi da sauri da sauri. ahankali, tace Hmm Dina inajin bacci cikin wata rikitacciyar murya yace to *Leemah* ta, bari nayi wanka sai narakaki dakin ki ki kwanta amma kema zakiyi wankan KO?...tace "eh yace to bari nashiga nafito sai kema kishiga ko?..tace to,
Ahankali yatashi tareda dagata yana gyara mata sumanta datuni ya wargaza shi saida yasa ribbon din yadaure mata sannan yashiga toilet. Be dade ba yafito daure da towel yace tashiga itama bata dade ba tafito daureda towel, tsaye ta'iske shi jikin mirror yana saye da rigar bacci irin me igiyar nan ta gefe, yana kum din kanshi sai kamshi yake zubawa murmushi yasakar mata ta mirror, itama murmushi tayi Cike da kunya tareda dukar dakai kasa, ajiye kum din yayi tareda juyawa yanufe ta yana fadin *Leemah* ta kinfito? ahankali tace "eh, yace OK" to muje narakaki ki kasa kayan baccin sai ki kwanta yafadi tareda daukar hijab din ta, tace to tareda daukar jakarta suka nufi dakin ta.
*Habeeb* ne ya ciro mata wasu riga da wando iya guiwa cike da kunya takesa kayan baccin, kasan cewar *Habeeb* yana zaune gefen gado yana kallon ta tunda har zata shiga toilet yace saidai ta tsaya tasa agaban shi dole ta tsaya ba dan ta so ba , Ahankali yamike yanufi gurin ta jawota ya rungume tareda cewa *Leemah* ta kinyi kyau sosai to ki kwanta saida safe kinji, tace to saidai ya kwantar da'ita tareda yimata addu'a sannan yarufa mata bargo yai kiss dinta agoshi sannan yamike zaya tafi,
Dasauri tarike masa hannu tace Hmm dina yanzu ni kada'ai zan kwana a daki?...yace"eh *Leemah* ta to ai bakomai, cike da shagwaba tace Aa Hmm Dina gaskiya nidai tsoro nakeji, dasauri yakoma ya zauna tareda cewa to *Leemah* ta ko zamuje dakina mu kwanta?.. ido tazaro tace kai! Hmm dina tareda kai zamu kwanta kenan fa?..
yace "eh mana to meye nifa mijinki ne ke kuma matata, shuru tayi batare da tace komai ba, yace to tashi muje mu kwanta can dakina kinji *Leemah* ta ahankali tace to amma kar kabari "Hajiyarmu tasani idan tasan tare muka kwana fada zatayi Mu kaji?.., dariya ce taku sa kwace masa amma sai ya dan ne yace kai! *Leemah* ta ai bazan bari tasani ba, tace to har da "Baffa da "lnna suma kar su sani kaji Hmm dina?..ta kareshe fadi tareda langab'ar dakai murmshi yayi tareda dagata ya rungume ahankali yace karki damu *Leemah* ta babu wanda zaya sani kinji?, tace to sannan suka fito yarufe kofar suka koma dakin shi suka haye faffad'en bed dinshi bayan yaimasu addu'a sannan ya rungume ta tsam ajikinsa tareda jan bargo ya rufe su, to asuba tagari *Habee-Leemat.*
****
Ado kam koda su Saminu suka fito dashi saida suka wuce unguwan ni biyar tsakanin fadaman madan sannan suka jefar dashi gefen wani bola suka tafi abun su, misalin karfe daya na dare wasu gayu su hudu sun dawo shar holiyar su suna tafiya suna wakokin su, na mashaya zasu wuce ta gefen bolar sai suka ji nishi kamar mutun dasauri daya daga cikin su yace kai! gayu baku jinishin mutun tagurin nan ba?..daya yace yaji dukkan su sukace sunji, nan daya ya kunna touch wayar sa suka haska aikam suka ga ado, duk daya sha duka ligis hakan bai hana daya daga cikin su yaga ne ado ba domin kuwa dasauri yace kai! wannan ai Oga adonjana ne _haka suke kiran shi_ suka rufu akanshi kokarin sance shi suke saidai duk sun kasa kasan cewar babu wani me sauran karfi acikin su, sai daya daga cikin su ne yaciro wuka acikin aljihun sa ya yake sauri wani irin ajiyar zuciya ya sauke na tsantsar wahala,
tambayar shi suke wanene yayi masa haka?.. amma tsabar azabar dayakeji yasashi kasa magana don haka sai suka dauke shi suka nufi gida dashi, inda biyu suka kama kafafu biyu kuma suka kama hannuwa suna tafiya suna faduwa kasan cewar duk abuge suke ahaka har suka isa gidan sa, suka jefar dashi suka b'ingire da bacci abinsu shikam ado be iyayin bacci ba domin yadda yaga rana haka yaga dare.
*_Bayan sati daya_*
******
A cikin sati dayan nan kuwa wani irin shakuwa ne yashiga tsakanin *Habeeb* da *Leemarsa* duk da cewa babu wani abunda yashiga tsanani su tafan ni auratayya, saidai hakan be hanasu jin kamar su cinye junan su ba dan so da kauna kasan cewar komai tare sukeyi bacce ne cin abinci ne, shiga kichin kai! har da wanka saida *Habeeb* yasan yadda suka koma yi tare tun tana jin kunya har ta daina, school kuma dama tuni yake bin ta suna zuwa tare idan angama lectures su koma gida ko su tafi fadaman madan House su shakata abunsun gwanin sha'awa.
Aban garen *Jana* kuwa ta shiga wani irin ya nayi narashin kasan cewa da d'a namiji, saboda duk wata hanya da zatabi don ta kasan ce da adonta *Habeeb* yabi ya toshe domin tun washegari da aka kawo mata sabuwar waya tasa sim da memorin ta me dauke da finafinan banza,
layi ado tafar kira beje ba sai takira na Shafa shima be jeba saita ajiye wayar anan falon kasa tanufi sama, kafinta dawo sai *Habeeb* ya shigo yana ganin waya yadauka yashiga gallery yafara duba wa abunda ya gani ne yasashi saurin rintse ido, daidai lokacin data dawo su idota zaro ganin wayar ta ahannun shin shikam wani irin mugun Kallo ya watsa mata, tareda cewa ashe mugayen halin dakike aikata wa aboye suna dayawa to daga yau bazaki sake gani wannan wayar ba kuma kika sake kika ga yawa "Abba cewa na kwace wayar ki wlhy sainanu na masa abinda kikeyi aika tawa da wayar.
Sannan kuma nagaya masa abunda kike yi aboye wanda ke atunanin ki bansan kina aika tawa ba ko?..sannan yashige daki abinshi yayinda ta zauna ragwaf cike data shin hankali.
Bayan *Deeya* tagama kwanaki bakwai sai *Jana* takarbi girki, aran nan tasa me aiki tagi girki saidai ko kallonin da abinci yake *Habeeb* be yiba, asalima *Deeya* yace ta dafa masa wani abinci yaci.
koda dare yayi *Jana* taje dakinsa sai yace mata shi baya da lafiya don haka babu wani abunda zaya iya yimata tafanni auratayya shiyasa tashi gawani irin yanayi domin kuwa bazata iya rayuwa ba tareda d'anamiji ba gashi tunda ga ranan dayace mata baya da lafiya duk ranan girkin ta haka yace mata shiyasa tafara tunanin menan mafita domin daita na bukatar taji namiji a tareda ita wannan kenan.
****
Da misalin karfe 9:40pm na ranan Juma'a *Habeeb* da *Leemarsa* na gani sun fito cikin wata dakakkiyar farar shadda wacce tasha aikin wuta, shiyasa riga da wando iya guiwa anyi mata aiki da zare brown yayi kyau sosai, kanshi ba hula ita kuma *Deeya* riga da siket tasa itama da brown din zare akai mata aiki tasa gyale brown takalmi da jaka suma brown kai! gaskiya *Leemah* ta tayi kyau sosai, sai kamshi suke zubawa sun fito tsaf cikin shirin fita kasan cewar yau su *Deeya* zasu fara test shi kuma yaune *Habeeb* yagama shan magungunan shi don haka yake so yaje *Harees* yasake duba lafiyar.
Cikin nutsuwa suke tafiya suna fira gwanin sha'awa hannun su sarke da juna, part din Hajiyarmu suka shiga bayan sun gaida su sannan suka fito suka shiga part dinsu lnna suka gaida su sannan suka fito suka tafi.Bayan sun sauke *Deeya* aschool har *Habeeb* zaya tafi sai tayi saurin rike masa hannun riga da sauri yajuyo ya kalle ta cikeda shagwaba ta rungume shi tare dacewa pls Hmm din na kadawo dasauri kaji kaga yau my sweet *"Feeya* ba zata zo ba, kuma test din bazamu dade ba zamu fito kuma ni banason zama ni kadai kaji?.. murmushi yayi tareda sake rungumeta tsama jikin sa sannan yace karki damu *Leemah* ta dana gama abunda naje yi zan dawo very soon kedai ki rubuta test da kyau kinji?.. tace to kiss yaimata agoshi sannan ya tafi asibiti.
Koda *Habeeb* ya'isa asibiti ya iske *Harees* da mutane marasa lafiya sosai don haka saida yajira shi ya sallame su tukun, sannan *Harees* yad'ibi jinin *Habeeb* da fitsarin sa yafara gwadawa cikin kan kanin lokaci yagama komai inda yafitar da result, sannan ya zauna tareda kallon *Habeeb* Wanda shidin ma kallon shi yake, cikin sanyi jiki *Harees* din yace...
*_Pls kuyi hakuri da typing errors_*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenat๐น
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
5โฃ5โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
*_Innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un kullimafsin'za'ikatulmaut!!!!_*
_*Wannan page din sadaukarwa ne ga my best friend๐ฉโโคโ๐ฉ Maryam Muhammad miss Mamman gas*_, _*don girma Allah Ina rokon๐๐ฝ duk Wanda ya karanta page din na yaimata Addu'a domin Allah yaimata rasuwa yau kwana bakwai kenan*_๐ญ _*tabar yara biyar, ya Ubangi Ina rokon ka*_ ๐๐ฝ _*don tsarkin mulkin ka don darajar fiyayyan halitta Allah kajikan maryam, kasata huta karaya abunda*_ _*tabari*_ _*ya Allah kasata aljannar firdausi*_
_*ma dauwamiya tareda kulluhin musulman*_ _*dasuka rigamu gidan gaskiya, ya Allah idan tamu tazo kasa mucika da imani kabamu ikon tashi dashi ameeeen*_๐๐ฝ _*yarabbi, I miss u l really miss u so muchhhh my besty Maryammm.*_ ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem!*_
_NOT EDITS_
_Congrats_ Dan'uwa yafadi yana murmushin shakiyanci tareda mikawa *Habeeb* hannun, shima hannun ya mika masa yana me sauke ajiyar zuciya, tareda cewa _thanks_ Dan'uwa amma fa kabani tsoro wlhy yadda naga jikinka very cool sai nayi zato ko har yanzu akwai sauran ciwon ne a tareda ni.
Dariya *Harees* yasaki me cike da farin ciki naganin *Habeeb* yarabu da wannan mugun ciwo, sannan yace a ah Dan'uwa babu sauran ciwon komai atareda kai kawai nadai yi haka ne don na zolaye ka, murmushi *Habeeb* yayi tareda cewa aiyayi maka kyau nima zan rama Ai, yace am so sorry Dan'uwa aibamu haka KO?..dariya *Habeeb* yayi tareda cewa "eh zakace haka aibayan kagama latsani I hope dai yanzu komai normal KO?..
*Harees* yace Insha'allah babu komai sai aje aci angonci lafiya, yafadi tareda mika masa hannun suka tafa suna dariya *Habeeb* yace Hmm kaida bari aini badan lokacin sallah juma'a yakusa ba da yanzu zan zanje nafara cin angonci na, amma bari mudawo masallaci kagani.
Ido *Harees* yazaro tareda cewa kai! Dan'uwa tun yanzu saika ce abun gudu, yace Dan'uwa kenan sai kace baka sannan matsalata ba?..kuma ainayi kokari yaufa _four week's_ kenan rabona da mace, duk dai inadan zage zafi kad'a ta wani gurin *Harees* yace gaskiya ne Dan'uwa kayi kokari koni da bani da matsala iri taka gaskiya bazan iya _four weeks_ ba tareda "mace ba, saidai inda wani babban lalura kamar irin taka din nan.
*Habeeb* yace to kagani yanzu dai bari na tafi *"Leemah* ta nacan tana jirana, yafadi tareda mikewa shima *Harees* din mikewa yayi tareda cewa, to nima ganinan zuwa sai mutafi masallacin gaba daya ko?.. *Habeeb* yace Ok" sai kazo har zaya tafi sai *Harees* yace to yau ko zaka samu zuwa Soron da gudun Fulani?..
Dasauri yace wah! tabdi ai wlhy ba zanje Soro da gudun Fulani yau ba saidai kuyi ta tafiya, amma nikam yau angoncina zan tsaya na ci wlhy. dariya ce ta kwace wa *Harees* sosai harda rike ciki sai dayayi me isarsa tukun sannan ya tsaya, *Habeeb* din na kallon shi.
Sannan yace Kai Dan'uwa har dasu shan wlhy yace "eh domin dai kasan tsawa shekarun dana dauka inason *"Leemah* ta, wanda sannu ahankali yarikide yakoma zallar kaunar ta me yawa Wanda ahalin yanzu babu inda ba kaunar ta acikin jinina, sannan kasani aduk inda so da kauna suke tsakanin mace da namiji to dole ne sai ansa mu sha'awa,agurin ko?..
yace haka ne.yace to wlhy Dan'uwa sha'awar *"Leemah* ta yakai makura a tareda ni, Kai! kamar ma karka tabbatar mun dacewa na warke sainaji wani irin matsanancin feeling dinta" yasake kamani sosai, wanda har inajin wani irin abu yana yawa acikin jikina, kai! Dan'uwa bari dai nata kai tamaka wlhy inaji idan har yauban kasance da *"Leemah* ta ba, to komai yana iya faruwa.
Ajiyar zuciya *Harees* yayi tareda murmushi sannan ya bubbuga kafadar *Habeeb* din, sannan yace karka damu Dan'uwa babu abunda zaya faru sai alkhairi kaidai kawai kabida "ita ahankali kasan yarinya ce" ba zata iya daukar bukatar ka alokacin guda ba, sai sannun a hankali zata iya dakai,
yace kar kaji komai kasan "itadin *RUHI* nace so bazanyi _Hot_ dinta ba, saidai kuma idan har zatayi mun *GARDAMA* to zan ajiye *TAUSAYIN* ta kad'an agefe nasa marwa kaina nutsawa idan yaso daga baya nayi lallashi kagane ai, ya kareshe fadi yana sakin wani shu'umin murmushi tareda daukar wayoyin sa dake kan table yace da *Harees* sai ka zo.
Dasauri yace jirani mutafi tare tunda 1:30pm tayi, Dakarfi *Habeeb* yace _what?_ dai-dai lokacin da ya'isa bakin kofar fita tareda duba kyakkyawan agogon dake daure ahannun shi yace Oh! _shatttt!,_ yanzu har 1:30pm tayi aikam nasan *"Leemah* ta na can tafito tana jirana tunda tace 11:30pm zata gama test,
*Harees* yace to bari nazo muje mu dauko ta idan muka ajiye ta gida sai mutafi masallaci, yafadi tareda kwasar wasu takardu da kuma jakar lapton da wayoyinsa, sannan suka fita suka nufi school din don dauko *Deeyar.*
*******
Koda suka isa school din sun iske *Deeya* tacika b'am da fushi kiris take jira ta fashe kuka saboda, haushin dadewa datayi tanajiran *Habeeb* bezo dawuri ya dauketa ba,don haka tana bango shi zuwa ta jiya baya, murmushi yayi cikin ta kun kasaita ya'isa gurinta ya rungumeta ta baya, tareda fadin Oh! my *Leemah* am sorry kinji?.cikin kukan shagwaba tace ni ba ruwana dakai, tunda kamanta dani agurin nan tun dazu fa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 42