*Deeya* akan cinyar sa.
*_Nikam danake gefe ina dauko maku rahoto, ido nazaro cike da mamaki Habeeb tofa su BB kenan wato dai ita Leemah nan ba'a hadata dakowa ba lol._*
*Deeya* kam sarkin sanjiki kwantar da kanta tayi akan faffaden kirjinsa tana sauke ajiyar zuciyan kukan datayi, bayan shugaban makaran ta yakoma ya zauna sai yamika wa *Habeeb* hannu fuska murtuk ya mika masa nasa hannun suka gaisa, cikin girmamawa mutumin yace yallabai meke tafe dakai?...
Cikin bacin rai *Habeeb* yace wannan matata ce sannan yanuna *Feeya* dake tsaye yace wannan kuma kanwata Ce matar "dan'uwana ce, yau suka Fara zuwa school din nan shine wani _stupid guy_ yace" wai yanason matata kuma anfada masa matar aure Ce, shine yace wai ai irin ta yakeso Kai kaji fa?..dasauri yace subhalallahi! wanene shi?.. kallon escort din dasuka shi office din shiyayi, yace yaje yakira su,
Ai kam Dasauri escort din yafita zuwa kiran su kasan cewar dazasu shiga sai *Habeeb* yace su tsaya awajen office din.
Can sai gasu sun shigo dasauri *Habeeb* yace gashi nan don haka inason ajamasa kunne hawainiyar sa takiyayi ramata, KO" kallon matata yasakeyi zaya fuskaci mummunan hukunci daga kareni eheee.
Shikam shugaban makarantar sai Kallon _guy_ din yake wanda yaci duka sai numfashi yake fitarwa Da kyar, cikin harshen turanci yace da _guy_ din wani department yake?.. shuru bai amsa ba sai nishin wahala yake, Cikin tsawa yace badakai nake magana ba?.. cikin tsananin galabaita yace yallabai niban san abinda kake nufiba,
Cike da mamaki yake kallon shi cikin hausa yace bakajin turanci ne?..Kai _guy_ din yadaga, alamar "eh bai iya ba mamaki ne yasake kamashi don haka sai yace nace ne awani shahi kake karatu?.. yace yallabai niba dan makaranta bane, Dasauri yace _what_?.. cikin mamaki *Habeeb* yadoka masa tsawa tareda cewa to uban me kazoyi ciki makarantar?..
yace yallabai akwai samarin dasuke shigowa saboda wasu mata auren dasuke daukar su haya don subiya masu bukatar "su tahanyar kwanciya da su, sai subashi kudi to nima Ina daya daga cikin samarin.
Dasauri *Habeeb* da shugaban makarantar sukace a'uzubillahi!.
*_Wa'eyazubillahi! wannan wace irin masiface" ZINA da AURE ya elahi, wai meke damun wasu mata auren ne?...haba YAR'UWA duk bukatar ki da mijinki yake biya maki bai isheki ba?..har saikin sake BIYAN KUDIN KI don abiya maki wata bukatar, wacce take tattareda MASIFA da BALA'I, ya Allah kai mana tsari da aikata ZINA musamman ma da aure, wayan da kuma sukeyi Allah kashiryasu Ameen_*.
Cikin bacin rai *Habeeb* yace ya ilahee matar aure da ZINA?... _shame,_ shugaban school din yace kadai bari yallabai babban abin kunya ma kuwa, *Habeeb* yace yakamata ku dauki tsatsauran mataki akan irin wayan mutanan, yace kwarai kuwa kuma yau din nan zamu fara dauka *Habeeb* yace lallaikam,
yace don haka kayi hakuri kuma Insha'allah hakan bazaya sake faduwa ba, domin zamu dauki mataki akan su sosai kiyi hakuri kinji madan yafadi yana kallon *Deeya* dai-dai lokacin da *Habeeb* yatashi yana me rungume ta aka fadarsa, ahankali tace bakomai sannan sukai mai sallama suka fita.
Suna tafiya *Habeeb* ya nafada dacewa ai saida nace nahada kuda escort kikace "a ah saboda bakinjin magana ta ko?..to aiga irin tanan, cikin sanyi murya tace to kayi hakuri fuska had'e yace bazan yi ba, tace pls yace nakiya dai-dai lokacin da suka karasa gurin motocin su, tace pls now yace no cike da shagwaba tafara bubbuga kafa tana fadin nisai kayi hakuri,
shi dariya mata bashi yayinda yake jin *SONTA* yana fisgar shi jawota yayi ya rungume ba tareda shakkar komai ba, yace kai *Leemah* ta idan kina irin wannan abin zakisa na rigayin _hug_ dinki a gaban kowa fa, tace to bakai bane nace kayi hakuri kace ba zakayi ba, yace to zanyi amma da sharadin zan bar maku escort hudu tukun,
Dasauri tace kai Hmm *Habeeb* har hudu?..yace "eh idan kuma baki yadda ba to bazan hakura ba, baki ta tabe tareda kallon manya-manya escort din dake can gefe tsaye fuska murtuk, tace to na yadda amma dai ba motar mu zasu shiga bako?.. yace "aah waccan zasu shiga tace to shikenan yace yauwa *Leema* ta yafadi tareda yimata kiss agoshi, sannan yakira mutun hudu yace su kula dasu *Deeya* sannan ya sallame su yatafi.
*****
Saida karfe 4:30pm sannan su *Deeya* suka dawo gida har zata shiga part dinsu, sai Baffa yace mata ai lnna bata nan taje gidan goggon ta Lanti don haka sai tanufi part din Hajiya, wanka tashiga.
Tana fitowa gada toilet shikuma *Habeeb* yana shiga dakin, lallausan murmushi suka sakar ma juna yace student kun dawo?. tace "eh yace to ya studies din?..tace alhamdulillahi yace to masha'allah sai amaida hankali sannan duk wanda ku kaga zayai maku iskanci kuhada shida escort din nan suci ubansa ni nace,
Cike da farin ciki tace to Hmm *Habeeb* Allah na tsani irin mutanan nan, yace konima wlhy ai wawaye ne kazamai kawai, inban da kazanta meke cikin zina?.. ke! *Leemah* ta _we close this stupid chapter_ kinji?..tace gaskiya kam babu ko dadi firar, yace inafa.
Yauwa *Leemah* ta ina tason na tambaye ki amma dazaran mun hadu sai shaukin *SONKI* yasa na manta, yakara she fadi tareda kashi mata ido daya dariya tayi tareda cewa me zaka tambaye ni?..yace wayar ki fa?.. bakita turo tace tun yaushe ta bace a, abuja yace Oh! *Leemah* ta shine baki fadamun ba?..rai adan bace tace to aiba ka bani damar hakan ba, tafadi tana kokarin isa gurin dressing mirror.
Hannun ta yariko ahankali ta juyo suka hada ido wani irin kallo yake mata me cike da tsantsar *SONTA* DA sha'awarta, cikin sanyi murya yace sorry *Leemah* ta shirya muje na siya maki wata ke! ko guda nawa kike so zan siya maki kinji?.. dasauri tace really?.. yace yeap my *Leemah,* wani irin tsallan murna tayi tareda rungume shi aikam tuni yaimata masauki afaffadan kirjinshi
suna dariya sai kuma yafara yimata chakulkuli,
hakan yasa dariyar ta yakaru tana ta zillewa shikuma yana cigaba dayi mata chakulkulin, sunata dariya har suka fada kan bed sai kuma yafara sumbatar ta tako'ina cikin shaukin sonta, ahankali wasan ya chanja salo cikin wani irin yanayi yake aika mata da zafafan sakonni, Wanda yasa gaba daya kwakwalwar ta takasa dauka hakan ne yasa jikinsu yadauki rawa _especially_ ma ita aikam tuni tasaki kuka me cikeda tsoro da kuma rashin sabo,
ahankali yabar abunda yakeyi tareda da gokai cikin wata rikitacciyar murya yace menene *Leemah* ta?..murya tana rawa tace ni banason wannan abunda kakeyi mun, murmushi yayi yace to nabari kiyi shuru kibar kukan yafadi tareda koma wa gefe yana sauke numfashi,
Dasauri taja bedsheet ta rufe jikinta kasan cewar tuni yara batada towel din jikinta, cikin mutuwar jiki yamike yace ki shirya nima zan jena shirya kinji?...
kaita gyada sannan yafita baki ta turo tareda jawo towel ta daura sannan tashi tafara shiryawa.
****
Wani hadadden shop complex sukaje aikam suna shiga kallo ya koma kan su kasan cewar sunyi shiri kusan iri daya, *Deeya* tana sanye da wata roba gown blue ta dan Kama jikinta kadan sai tayi rolling Da bakin gyale tasa bakin glass tayi kyau sosai, shikuma *Habeeb* yana sanye da bakin wando da blue T-shirt sai yasa bakin glass, shima yayi kyau sosai, wata hadaddiya kuma tsadaddiyar waya ya siya mata saikuma ya siya masu laptops itada *Feeya* tareda wasu siyayya sannan suka dawo gida.
*_Bayan sati biyu_*
*******
Tuni *Habeeb* yakoma gurin aikin sa ya cigaba da gudanar da aikinsa, yayinda su *Deeya* ma suka cigaba dazuwa school din su cikin kwanciyar hankali Da escorts dinsu, agefe daya kuma Adda Mamu da Adda Rahma suna ta gyara ta harda Hajiya ma ba'a bar ta abaya ba gurin gyara hali dubun ta, shiwa waya kusan kullun sunayi itada *Habeeb* sosai suke soyawa ta waya especially ta video call Wanda tana gama kwalliya saita nuna masa sannan ta tafi school.
"Abangaren *Jana* kam tana ta holewar tada Ado yanzu ta dai zuwa gurinsa, saidai shine yake zuwa gurinta da irin shigar da yake ta bakaken kaya.
"Ayau Jumma'a kuma yaune akesa ran zuwan *Habeeb* kasan cewar bai samu zuwa satin da yawuce ba saboda ayyuka da sukai masa waya, kuma yau ne *Deeya* zata koma dakinta anyi mata gyara sosai tayi kyau har tagaji.
Misalin karfe 2:30pm *Habeeb*
ya'iso Bauchi yaso yafara shiga part din Hajiya, to amma hakan bai samu ba saboda mutane da ya'iske suna jiranshi, don haka sai daya sallama su tukun sannan yashiga suka gaisa da Hajiya sannan yake tambayar ta
*Deeya* tace ta part dinsu,tashi yayi yafita kamar zaya shiga part dinsu *Deeyar* sai kuma yafasa saka makon wani irin nauyin su Baffan dayaji yakama sa murmushi yayi tareda nufar part dinsa.
Yana shiga falon yaji wani irin faduwar gaba, ahankali yake takawa zuwa sama direct dakin *Jana* yanufa da ya hango sa abude, tun kafin yakara sa yafara jiyo wani irin sautin nishi me dauke da wasu surutai, ahankali yakara sa bakin kofar abinda idonsa yaganar masa ne yasashi juyawa dasauri, cikin wani irin azababben tsoro me dauke da tsanani tashin hankali yace...
*_Yeeeee๐๐ป readers anzo gurin fa so ku bani buhuhunan comments, idan ba haka ba kuma nafasa eheeeee๐._*
*_Barkanmu da Jumma'a_*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenart๐น
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
4โฃ8โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
"A'uzubillahi! yah ilahee yau me zan gani agida na haka ni *Habeebullahi?..* wani irin rawa jikinsa yake har wayar dake hannushi takusa faduwa saboda tsantsan tashin hankali saka makon abinda idon sa ya gani, wato *Jana* da Ado tsirara akan gado suna aikana fasikancin su tsabar shakin masifa yasa sun manta basu rufe kofa ba,
Dagani ma sun da deyin nisa dabarin duniyar mutane suntafi duniyar kazamai marasa tsoron Allah sai nishi suke, tareda surutan banza wanda kanaji zaka fahimci basa cikin hayyacin su saboda tsabar masifa da bala'i dasuka sa kansu ciki.
*_Wa'eyazubillahiayya matan auren da kuke aikata ZINA da aure kunyi makan Ku adalci tareda mazajan Ku kuwa???..., nasan tabbas idan har ba'asa SON ZUCIYA ba to amsar itace A A lallai yar'uwa bakiyi makanki adalci ba,sanna bakiywa MIJIN Kl adalci ba, sannan kisani kece maciya AMANA ta farko A DUNIYA, domin cin Amana DA YAWA kinga yar'uwa da farko kinci AMANAR ALLAH mahaliccin ki, kinci Amanar AURE sunnar Annabi (S W A), kinci Amanar MUSULUNCI kinci Amanar IYAYANKI domin ba'irin TARBIYAR dasu baki bake nan and than kinci Amanar MIJIN KI Uban yayanki, kin gurb'ata masa zuri'a kin hada mas tsaftatattu da kazantattu, sannan suma yayanki kinci Amanar su domin kinbar masu abun fade da gori ga al'umma, kuma kisani duk dakin kasance UWA agaresu daga ranan dasuka san ke "mazinaciyace tofa daga ranan zasu" tsaneki har masuji dama bakeki ka HAIFE suba, don haka yake yar'uwa Ina me baki shawara dakiyi gaggawar daina ZINA domin itadin MASIFA CE BALA'I CE_* *_Hmm yar'uwa ZINA babbar BALA'I Ce wacce take TARWATSA Al'umma wlhy yar'uwa inda kinsan BALA'IN DA ZINA take dauke dashi na rantse da SARKIN daya busamun NUMFASHI dabaki aikata ZINA ba Allah ka tsaremu daga aikata ZINA masu aikata wa kuma ka shirya su ALFARMAN BIJAHI SAYYADIL WARA ameen._*
Ido yarintse cikin wata irin rikitacciyar murya yafurta yah ilahee kasa mafarki nake yi, Ina kuma rokon ka dakata Dani daga wannan mummunan mafarki, sai kuma yayi shuru nadan wani lokacin da'alama yanajiran ubangiji yafarkar dashi daga _bad dream_ din ne, saidai kuma me?..
sound din dayaji yana cigaba da moving shine ya tabbatar masa bafa mafarki yake ba is really, don haka ne yasake rintse idon shi domin baya fatan yasake ganin wannan mummunan kazanta, ahankali yafara tafiya zaya sauko.
Murya Lili mama Ce tadoki dodon kunnan shi hakan ne yasashi saurin bude idon shi dasuka rikid'e suka koma jajir tsabar tashin hankali daya shiga, hangota yayi sanye da riga ja me hannun shimi tanada hoton Tom and Jerry da wando baki iya kwauri kanta sanye da hula baka irin me tuntu taga ba tayi kyau sosai kamar furen fulawa, Cike da farin ciki take tako upstairs din tareda fadin Dady oyoyo bayan ta kuma Junior ne biye da ita,
gaban shine yafadi gani cewa zasu haune kuma idan har suka hauwo to tabbas zasuga abinda yagani, Wanda shi kuma baya fatan suga wannan kazantar musamman ma Lili data kacen me dan karan wayo da surutu, don haka da sauri yai wani irin mahaukacin juyawa idon shi rufe yakai hannu yajawo kofar ya rufe dai-dai lokacin da suka karasa hawowa.
Dasauri ta rungume shi cike da farin ciki tace Dady kadawo?..cikin wani irin murya yace nadawo Lilin Dady yafadi tareda shafa kanta Junior yace Dady sannu da dawowa, shima kan shiya shafa tareda daga mai kai alamar "eh Lili tace Dady Ina Aunty *"Jana* tafadi tana kokarin isa bakin kofa,
Dasauri *Habeeb* yariketa tareda cewa ayya Aunty *"Jana* kanta yana ciwo ta sha magani ta kwanta, fuska tabata alamar tausayawa ga maman ta ahankali tace Dady anyi mata alluna ne?..yace "eh mujen ku falon kasa Mu zauna KO?..suka ce "eh dom haka yasaka su gaba suka sauka kasa.
Suna zama lili tahaye kan cinyar sa tana wasa tareda daba shi labarin abinda Aunty *"Deeya* tayi mata, wai ita Ce takira meyin lalle fulawa tayi mata a hannu da kafa sannan ku tayi mata kicho kalli Dady tacire hulan aikam saiga yan kanana kitso masu kyau sun sha kalolin beat, mikewa yayi zumbur tareda zaunar da Lilin kan kushi sannan yashafa kan nata ba tareda ya kalla ba kamar yadda ta bukata saidai yace nice, domin gaba daya hankalin sa yana sama, aran shi kuma addu'a yake Allah yasa karsu fito su Lili sugan su,
can sai tace Dady me kacuyo mana kacuyo mana ice cream da sweet da chocolate? shuru bai amsa ba sai safa da marwa yake yana kallon saman benen, yayinda kallo daya Zakai masa ka fahimci yana cikin matsanancin tashin hankali duk sanyi ac falon hakan bai hana matsanacin gumi tsatsufo masa ta ko'ina ajikin saba, musamman ta wuyan rigan shaddar dayasa sky blue duk tajike da gumi yayinda yaketa share na goshin sa da hand kerchief, sai magana suke amma bayajin su da'alama yana tunanin yadda zaiyi ne kar su Lili suga su *Jana* da kuma irin hukunci daza yayima *Janar* da kwarton tane.
"Junior ne yai magana da dan karfi yace Dady kasiyo mana sweet?..Dasauri yace "eyeee Junior meka ce?..yace Dady kasiyo mana sweet ne?..yace Oh! Sorry Junior na manta amma ga kudi kuje uncle *"Hafeez* ya siyo maku yafadi tareda sa hannu aljihun rigarsa yaciro kudin da baisan ko nawa bane ya mika masu, ganin yawan kudin ne yasa Lili zaro ido tareda bude baki Cike da tsoro tace ah! Dady juka wannan kuchin dayawa fa,
Dasauri ya kalla tareda cewa Oh! Sorry Lili ban gani bane hannun shi yana rawa yakirga dubu biyar yabasu, yace to gashi kuje ya siya maku kunji?.. sukace to tareda karba sannan suka fita da gudu suna murna,
Ajiyar zuciya yayi tareda cewa thank God than yah ilahee kanuna mun yadda zanyi da wayan nan bayi naka dasuka zalunce ni, wayar sa ya daga yakira wani layin jinayi yace saminu inason kasa mo mun igiya me kauri sosai, sai kuma yayi shuru can sai yace "eh zamu fita to shikenan sannan ya kashe wayar.
Zama yayi tareda tura hannu wan shi duka biyu acikin lallausan suman kamshi yana ya mutsawa, yayinda yakejin wani irin bakin cikin aran shi me tsanani dago kai yayi tareda furzar da iska taba kin shi, sannan yajin gina bayan shida kushin tareda dora kafarsa daya kan daya yana girgiza wa. tsawon wani lokaci yana zaune ahankali ya kalli agigon dake daure a hannun shi karfe 3:30pm yanuna masa, dai-dai lokacin da yajiyo dariya tareda taku alamar za'a sauko kasa hakan ne yasa ya tsurama benen ido,
mamaki ne ya kamashi ganin *Jana* sanye dawata rigar bacci iya kwauri, shikuma kwarton nata sanye da bakaken kaya tunda ga sama har kasa harda nikaf, idan kaganshi sai karantse da Allah mace ce ahankali yafurta no wonder hakan yayi kyau l like u style, firasu ke suna dariya amma ganin *Habeeb* yasa sunyi shuru yayinda suka sha jinin jikinsu, musamman ma *Jana* domin gabanta yafadi dagani shi saidai da yake ita din yar duniya Ce saita basar gudun karya ganota, _nikam nace aikin makaro_ .
fuska dauke da fara'a ta karasa gurin shi tareda cewa lah! *BB* na ashe kadawo ban saniba?.. wani irin kallo yake mata Me cike da tsantsar tsanar ta da kyama aran shi yace taya za'ayi kisan nadawo tunda kina can kinyi nisa agurin aikata cin amana, azzaluma macuciya fasika nibankin ciki na ma bansan tsawon lokacin daku ka dauka kuna cin amana ta ba, Kai! yah ilahee kasa batasa mun cuta ba Allah ya'isa *Jana* tsakani na dake.
Ganin irin kallon daya kema tane yasata saurin cewa sannu da dawowa yace uhum! tareda kallon Ado, tace wannan kawatace sunanta malama zabba'u yace Oh! sannun fa mlm zabba'u yakike?..shuru ba amsa sai yace "ah! kurma ce mlm zabba'un?..
dasauri tace "a ah bata dai magana da mazane yace Oh! Allah sarki aikota kyauta makanta, yafadi yana tashi yace nizafita idan badamuwa tazo mu rage mata hanya wace unguwa take??, Dasauri tace Lah! ba damuwa akobi take, yace OK" tazo muje tanan zamubi dama sannan yanufi hanyar fita,
Dasauri *Jana* ta isa gurin ado tana cewa to mlm zabba'u kuje sai a sauke ki sai anjima nagode tana fadi tareda leken *Habeeb,* wanda tuni yafita aran shi yana fadin zakuci uban ku dagake har kwarton naki, tace kai dakaga kunyi tafita kadan sai kayi muryar mata kace su sauke ka zaka karasa, yace to amma kuma gaban shi yana faduwa sannan yafita.
*Habeeb* yana fita escorts din shi suka tasoda sauri sai kuma suka tsaya cak, sai Saminu ne ya'isa gurin shi kasan cewar duk cikin escorts din shine babba, kuma *Habeeb* ya yadda dashi don haka a duk lokacin daya sukaga *Habeeb* yafito shine kefara isagare shi tukun sannan suma su iso ko yanzu shine yafara isa sanna su,
Cikin girmama Saminun yace Sir za'afita din kenan?.. dasauri yace "eh, sai yabude masa bayan motar yashiga ya zauna dama tuni direba yashiga ya zauna, sai *Habeeb* yace Saminu" acikin wacce mota akasa igiyar?..yace Sir cikin hillos din can yace OK" to inason "wancan mutun yashiga ciki, "Joy da "Samuel su shiga su sa shi tsakiya karsu bari yayi ko da kwakkwaran motsi,
Cikin
mamaki saminu yace Sir macece aiba namiji ba, wani irin murmushin takaici *Habeeb* yayi tareda cewa Saminu ba mace bace "namiji ne, cike da tsoro yace _what "him dressing like a woman_ amma dai bashi da hankali ko?..
yace "eh shiya sa zanko ya masa hankali so ku kaima shi _fadaman mada farm house,_ kusaya tube kubarshi daga shi sai boxes idan yanada shi idan
kuma baya dashi to sai ku bar shi da dogon wandon sa, sannan ku daure mun shi sosai ta yadda ko motsi bazai iyaba, akwai inda zani yanzu so idan nagama abunda naje yi zan iske ku kaji ko?.. yace ok Sir angama.
Dasauri ya'isa gurin ado dake tsaye kasan cewar da yafito yaga suna magana sai yakoma gefe ya tsaya cike da zullumin, Saminu yace madam shiga mota ba mutsu ado yashiga saida kuma gaban shi nata faduwa, sannan Joy da Samuel suka shiga sukayi kamar yadda *Habeeb* yace",
Sai Saminu yashiga yaja suka fita motar *Habeeb* tana gaba ta escorts dinsa nabiye sai tasu Saminu, suna fita motar su Saminu tanufi unguwar fadaman mada su kuma su *Habeeb* suka mike, basu tsaya ko'ina ba sai asibiti direct office din *Harees* yashiga.
Zaune ya'iske shi yana aiki akan computer, ahankali yadago kai ya kalli *Habeeb* yasa kar masa murmushi tareda cewa mutanan abj kenan saukar yaushe?. ba tareda yace komai baya zauna, sannan ya tsurama *Harees* ido cikin wata iri murya yace nazone kaimun gwajin *HIV* zumbur *Harees* yamike tareda cewa _what?._ *HIV* fa kace Dan'uwa meye hadin kada *HIV* kodai kafara neman matane acan abujan?..
Zumbur *Habeeb* yamike rai bace yace zakai mun gwajin ko bazakai ba naje wani asibitin?.. cikin sanyi muryar yace zanyi, yace OK" fara yace to zauna mana.
Cikin kankani lokaci yad'ibi jinin sa yafara gwada wa, kasan cewar yanada komai na aikin acikin office, don haka ba tareda bata lokaci ba yagama komai yafitar da result duk *Habeeb* yana zaune yana kallon shi,
zama yayi jiki ba kwari tareda tsurama *Habeeb* din ido, shidin ma kallon *Harees* din yake saidai kuma zuciya sa tana wani irin matsanancin bugawa, cikin sanyi muryar *Harees* yace...
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenart๐น
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
4โฃ9โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
_"Result_ yanuna baka dauke da *HIV* wani irin mahaukacin ajiyar zuciya *Habeeb* yayi, *Harees* yace Dan'uwa akwai yar matsala fa cikin wata irin rikitacciyar muryar yace mene ne matsalar?.., yace idan ba damuwa zanyi maka wasu yan tambayoyi?..cikin tsinkewar zuciya yace go ahead...
yace Ok" kanajin mararka tanayin ciwo?.. yace "eh kwanan nan nafara jin haka sannan idan zanyi fitsari sai naga wani farin abu kadan yana fitowa wani lokacin ma ko ba zanyi fitsari ba idan na tsugun na sai naga yafito, sannan inajin kaikayi, yace zayakai kamar tsawon wani lokacin da kafara jin haka?..
yace week din Dana koma ne, danaso nakiraka awaya nai maka bayayi sai kuma nafasa nace bari idan nazo sai nayi maka magana. sauke ajiyar zuciya *Harees* yayi tareda cewa maganar gaskiya ciwon sanyi ne, yafara kama ka saidai baiyi nisa sosai ba dazaran kasha maganin zaka rabuda shi, saidai kuma maganar gaskiya Dan'uwa kabani mamaki kwarai kuwa banyi zaton haka daga gareka ba wlhy, haba dan Allah kaida keda mata har biyu meye nazuwa neman mata umh?..
cikin bacin rai *Habeeb* yace aka fada maka Neman mata nake?.. yace aibasai anfada mun ba ga abunan nagani, kuma neman matan ma irin wanda bayada tsari ka keyi wato kanemi wannan kane wacce ko?..to bari kaji infada maka _Sex anyhow_ shike kawo cututtuka iri-irin don haka gara kayi gaggawar bari haba Dan'uwa *ZIN...*
Wani mahaukacin tsawa *Habeeb* yadoka tareda mikewa zumbur, yacakumi kwalar rigar *Harees* ya daga shi tareda girgiza shi cikin tsananin bacin rai yace *Harees* nikake alakan tawa da wannan kazantar?..., NI *Habeeb* kake tunanin Ina aikata *ZINA?..*
azatona kowani kaji yace Ina aikata *ZINA* zakayi musu domin kasan kowane *Habeeb* kasan abun da Zan iya aikata wa kuma kasan abunda bazan iya aikata waba, amma yau dabakin ka kake cewa ni *Habeeb* Ina aikata *ZINA* why! why!! why!! Dan'uwa ya kareshe fadi tareda girgiza shi dakarfi sai kuma yatura shi yafada kan kujeran sannan yafita daga office din ranshi amatukar bace.
Kai *Harees* yadafe jiyayi ranshi badadi ahankali yace _am so sorry_ "Dan'uwa tabbas kamar yadda kace" haka ne, ni nasan kokai wane kuma zan iya bada shedarka ada saidai kuma banda yanzu, domin ban sani ba KO" ka canja hali ta yadda bazan iya shedar ka ayanzu ba, mummunan dana ganka da wannan ciwo Wanda akasarin masu shi *MAZINA TANA NE* kedashi shiyasa nayi mamaki,
ya'akai kasa meshi domin nasan kaidai ba mazinaci bane asalima ZINA ita Ce abunda kafin tsana arayuwar ka to amma ya'akai kahadu da wannan ciwon????..ajiyar zuciya yayi tareda cigaba da'aikin shi.
********
*Habeeb* kam koda suka fita daga asibitin direct unguwar fadaman mada farm suka nufa, wani katafaren gidan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 42