Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gona ne yake dashi acan anayi masa noma tareda kiwon dabbobi musamman ma dawakai irin na polo din nan, kasan cewar yana kiwon su sosai masu polo suna siya agurin shi. Kamar yadda *Habeeb* yace" haka su Saminu sukai, yadauri kyai sukai ma ado irin daurin huhun goron din na sai rokon suyake sukyaleshi amma ko kallo bai ishe suba, hakan ne yasa yayi yinkuri guduwa amma Ina ba gurin bayan sin daure shi sai suka jefashi wani doki da aka zagaye shida katako saidai badoki aciki. Motar *Habeeb* tana tsaya wa Saminu yajeda sauri yabude masa kofa, Cikin girmama yace barka da isowa Sir anyi yadda kace gashi can adakin can yace OK" good nan da nan ma'aikan gurin suka fara kawo gaisuwa gurin *Habeeb,* bayan yagama amsa gaisuwar sannan yanufi dakin da Ado yake adaure, Dasauri Saminu yadauko irin kujeran roba nan ya kaima *Habeeb* ya, zauna tareda dora kafa daya kan daya saminu kam Dasauri yafita dak. Yayinda *Habeeb* yazuba ma ado kyawawan tsuman mun idanun shi masu matukar kwarji wayan da cikin lokaci kankani suka kad'a sukayi jajir, tsabar bacin rai wani irin kallo yake ma adon me cike da tsantsar tsana da kyama, aikam take tsoro yasake kama ado domin yaukam yasan sai buzun shi, kallon *Habeeb* din yake cike da wani irin danasani abunda yayi gawani irin mugun kwarjini da yai masa, Cikin had'e fuska *Habeeb* yace yadai?..KO" asance kane muyi dambe domin naga kanayi mun wani irin kallo ne kamar kana iya dambe daniko?.. Cikin wahalalliyar murya ado yace "a ah yallabai bazan iyaba, yace ah! zaka iya. Saminu zoka sance shi muyi dambe yafadi yana tattare hannun rigar shi, cikin tsanani wahala yace yallabai wlhy bazan iya dambe da kai ba don Allah kayi hakuri, tsaki mtww! *Habeeb* yayi tareda cewa banza stupid kai dakiki ne jahili kawai anfada maka nizan iya dambe dakai ne?..tirrrrrr Allah yakiyaye ni *Habeebullahi* na hada jiki dakai ne dasu nan dambe kana kazami mazinaci faciki kawai, Saminu bani bulala ta dawakai yau zan koya maka hankali akan abunda ku aikata mun, wanda KO" gobe wani yace kashiga har cikin gidan mutun kai *ZINA* da matar shi bazakai ba, koda yake baka da laifi, "itada ta gayyace ka har cikin gidana kuka aikata *ZINA* tafi ka laifi don haka yau zakaga ne kuren ka, Saminu wai Ina bulala. Dasauri Saminu yakawo masa wata katuwar murtukekiyar bulalar da saida naji tsoro da nagan ta, batareda bata lokaci ba *Habeeb* yashiga zabgama ado bulala aikam tuni yashiga zunduma ihu yana neman me ceton shi, saidai kuma ina babu wanda yakawo masa dauki, Sosai *Habeeb* yake jibgar ado idan yaga alamar ya suma sai ya watsa masa wani kazantatcen ruwan doki, sai yafarfado duk yafarfasa masa jiki gaba daya kamannin adosun sauya. Saminu kam gaba daya ya tsorata daganin yanayin ubangidan sa, musamman dayaga yana shirin kisan kai don haka dasauri yadaga waya yakira layin *Harees* yafada masa abunda kefa ruwa, Dasauri *Harees* yace ok ga yana zuwa, sannan yakara *Hafeez* yafada masa shima yace gashi nan zuwa. Cikin lokaci kankani sai gasu sun iso kusan atare suka fito mota dai-dai lokacin da *Habeeb* yafito daga dakin, yanufi wani hadadden apartment dake nan cikin gidan gonar, sai da yagaji don kanshi da jibgar adon yafar shi, wani kyakkyawa falo yashiga tareda fadawa kan wata lallausan kushin. Dunkulewa yayi tareda Kama kanshi domin wani irin sa rawa yakemai tamkar zaya tarwatse, gawani irin bakin ciki da yakeji wanda tunda yake baitaba jin irin sa arayuwar shiba, ahankali yake dukan kirjinsa da hannun shi daya dayan kuma yana murza wuyan shi domin wani irin Abuda yaji yana taso mashi daga kirjin sa yazo kahon zuciyar shi ya tsaya shi bai fito bashi kuma bai koma ba, dakyar ya'iya furta yah ilahee!. Sai kuma yafashe da wani irin kuka me cike da tsananin bakin ciki da bacin wanda kanajin shi kuma zaka fahimci, meyin shi yadade baiyi kuka arayuwar shi ba sosai *Habeeb* yake kuka tamkar karamin yaro. Dasauri su *Harees* suka shiga falo ido suka zaro cike da mamaki ganin yadda *Habeeb* yake kuka, *Hafeez* kam saida yakusa faduwa saboda tsabar tsoro don haka dasauri yarike labule domin tunda yake baitava ganin Hmm dinsu yana kuka ba, *Harees* kam dasuri ya'isa gurin *Habeeb* hannun shi yarike tareda fadin shin Dan'uwa wai me yafaru ne, wanene wanca "guy din me kuma yaimaka dakai ma irin wannan dukan haka eyeee?.. Cikin tsananin kuka *Habeeb* yadamke hannun shi cikin na *Harees* sannan yace Dan'uwa dazu ka fahimceni ta baibai, har kana zaton ciwon da kaganni dashi Neman mata nake ko?..cikin sanyi murya *Harees* yace kayi hakuri, yace nayi saidai kasani samun ciwon akai domin ban taba Neman matan banza ba balle nasa meshi, asalima aikasan abunda na tsana arayuwata ko?.. yace nasani ka tsanini *ZINI* sosai, yace to wannan "guy din mazinaci ne Kama shi nayi yana aikata *ZINA* kasan ai'na?..kai *Harees* ya girgiza alamar "a ah wani guntun murmushi *Habeeb* yayi tareda share hawaye sannan yace agida na adaki na tareda matata *Jana,* dakarfi *Harees* yace _What_?.. yace "eh shiyasa nai "masa wannan hukunci wanda tare yaka mata nai masu da *Jana* ammasaobanyihakanba kasan dalili?yacea ah,yace saboda idan nayi mata irin humunci da nayi mashi mutu wa zatayi, nikuma banason ta mutu ba kasan dalili?..cikin wani irin yanayi *Harees* yace a ah, yace saboda Abu biyu na farko saboda ya'yanta wanda nasan komin daran dadewa za'afada masu ni nakashe mahaifiyar su, bazasu ji dadi ba nikuma bazanso haka ba dik dacewa kona kasheta ba'a komai tunda dama'ai hukunci wacce tayi *ZINA* da aure shine kisa KO?.., yace "eh yace to bazan kashe taba saidai kuma daga yau babu sauran aure tsakanin mu, na saketa amma bazan bata takarda yanzu ba har sai tayi idda kamar yadda addini yace, kafin wannan lokacin kuma na tabbatar itama d'and'ani irin bakin Cikin data kun samun don haka , wannan shine hukuncin ta" agare ni saidai kuma banason kowa yasa wannan maganar ya kareshe fadi tareda tashi zaya nufi daki. Sannan yajuyo yace Dan'uwa pls l want to see my *"Leemah* now kaji?.. kai ya gyada masa, sannan yanufi dakin, yana hada hanya yayinda *Harees* din yabishi da kallo har yashi yashige dakin zuciyar sa cike da tausayi shi na irin cin amanar da *"Jana* tayi masa, ajiyar zuciya yayi tareda maida kallon shi ga *Hafeez* dake tsaye rakube cikin sanyi muryar yace... *_Barka mu da Jumma'a_* Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 5โƒฃ0โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ "Young brotherrrrr! kaji mummunan aikin da *Jana* ta aikata KO?... Kai! *ZINA* fa abunda Dan'uwa yatsana arayuwar shi shine yau matarsa ta aika acikin gidan sa, cikin wata, rikitacciyar murya *Hafeez* yace Naji Hmm *Harees,* ni abun ma tsoro yabani ace kina "matar aure amma kikawo wani namiji cikin gidan mijinki har Ku aikata *ZINA* kai! amma dai "Aunty *Jana* takai babbar maciyiya amana, *Harees* yace hmm Kai! dai bari lamba one makuwa acikin masucin amana abu kamar acikin film, *Hafeez* yace hmm Hmm ai iren iren abubuwan dake faruwa kenan aduniya shine yau yafaru agidan Mu" yace haka nefa Kai! Allah yai mana maganin masifa da bala'i, yace ameen yakuma yimana tsari da *ZINA* da kuma masu aikata ta, yace ameen ya Allah, gaskiya banyi zaton haka daga *"Jana* ba, lallai tacika babbar maciya amana tunda har ta iya aikata *ZINA* da aure akan ta?..,gaskiya ta zalinci mijinta sosai domin yauna naga bacin ran daban taba gani a fice din shiba tunda nake, gaskiya sai Allah ya'isar "masa don haka bashi ta zalinta ba, kanta ta" zalinta wawuya kawai, zakuma taga saka makon abinda ta aikata insha'allahu, kuma hukuncin daya yanke akanta shine dai-dai, don haka Kaje ka dauko masa "Queen of beauty yana bukatar ta akusa dashi, domin "itace kadai zata iya lallashin sa amma mukan bazamu 'iya ba kaji KO?... "Ahankali yafurta to tareda juyawa yafita zuciyar shi cike da tausayin Dan'uwan shi tawani gefe kuma tsanar *"Jana* ce fal aran shi, tsaki yayi tareda cewa banzar "mata kawai dama ni kwata-kwata batayi mun sannan yashiga mota yatar yafita aguje daga gidan gonar ran shi amatukar bace. "A ban garen *Deeya* kam dama tun lokacin da sukai Waya da *Habeeb* yace nata gashi nan zuwa, tace me zata dafa masa?.. yace" tayi masa Jellof din cus-cus me dad'i tace angama Hamman dina. Batare da bata lokaci ba ta hada masa jellof din cus-cus wanda yaji kayan lambu saita, yayyanka koda kanana-kanana aciki cikin yan mintina kad'an ta kammala komai harda drink din zobo tahada masa, wanda yasha kayan yaji kamshi sai tashi yakeb bayan tagama, sai tashiga toilet tayi wanka tafito. tana cikin shafa mai saiga *Feeya* tashiga dakin Murmushi sukayi wa juna, Zama tayi tareda cewa a ah! gaye kai kaga amarya agidan "Hon *BB* Smart gaskiya Sweetie na kina jinba kyau fa ke kingan ki kuwa sai wani walkiya kike kina shainin like a Diamond in the sky yakareshe fadi tareda yin dariya, itama *Deeya* dariya tayi tareda cewa Kai! my sweet *Feeya* kina fasamun kai dayawa fa, sai naringa jina kamar wata sarauniya abirni... Dasauri *Feeya* tace ai sarauniyar ce ta birin *ZUCIYAR* yaya na, hakane?.. *Deeya* tace kwarai kuwa tace yauwa tawan kashe min nan tafadi tana mika mata hannu itama tamiko mata suka tafa tareda yin dariya, sannan *Feeya* tace barina dauko maki kayan dazaki sama yayana wedrof tanufa tadauko mata wata hadaddar gown din material, ash color me stones ajikin. bayan tagama kwalliyar sannan tasa rigar gaskiya tayi matukar yimata kyau rigar kasan cewar dinkin yafitar mata da sharp dinta sosai, kanta babu kitso domin kotayi sai ya warware saboda tsabar santsi shiyasa ma bata wahalar da kanta gurin yi, saidai kawai tanan nad'e abinta ko yanzu ma haka tayi, sannan tadauki farin gyale tayi rolling, sai tafeshe jikinta da turaruka kusan kala biyar *Feeya* nata kallon ta tana yaba kwalliyar ta bayan ta gama sai ta zauna suka fara fira, har zata kira layin shi sai suka jiyo kar jiniyar motar *Habeeb* din ajiyar zuciya *Deeya* tayi sai kuma sukayi Murmushi sai kuma *Deeya* ta bata rai, Dasauri *Feeya* tace me yafaru?.. tace naji wani irine araina da bani zaya fara zuwa yaga niba, tace fara ganin nata baya da wani alfanu tunda ba komai zaya samu ba, idan kuma har zaya samune to saidai ko takaici, baki *Deeya* ta tabe tareda cewa Allah yasawa ke tace to ameen sai suka cigaba da fira. can kuma sai sukaji karar fitar sa ido *Deeya* tazaro tareda cewa ina kuma zashi?..tace kilan wani gurin zashi, tace to shine bazaya zo yaga kwalliyar danai masa ba sannan yatafi, tace karki damu zayazo yagani ya kuma yaba har ma yabada tukuici tafadi tareda kashe mata ido murmushi kawai tayi ba tareda tace komai ba, can saita kira layin shi tana ringi bai daga ba data sake kira saita ji a kashe, hakan ne yasa taji haushi tayi jifada wayar akan gado tareda warware rolling din kanta tajefar sannan ta kwantar da kanta saman kafar *Feeya,* sai kuma tasaki kuka me cike da shagwaba tace wato maka she wayar yayi ko?..ai yayi kyau ni ba ruwa na ma "dashi. cikin kwantar da murya *Feeya* tace kiyi hakuri kiyi masa uzuri maybe wani muhimmin abune yafitar dashi, Dasauri tace ashe har akwai abinda yafini mahimmanci agurin sa?..tace a ah banyi tsammanin haka ba indai azuciyar sa ne, ko kema ai kinsan kedin tada bance agurinsa ko?... Dai-dai lokacin da wayar *Deeya* tayi kara da sauri ta tashi tadauka azatonta *Habeeb* ne sai taga *Hafeez* baki ta turo tareda dagawa, yana jin muryar ta yasan akwai magana don haka yace ya'akayine amaryar big bros naji muryar tana shaking wanene yataba mana ke?..cike da shagwaba tace to bashi bane yace" nayi masa jellof din cus-cus nagama kuma fa har da kwalliya nai masa amma baizo yaci cus-cus din ba balle yaga kwalliyar kuma nakira wayar shi sai ya kashe. Murmushi yayi me dauke da farin ciki wa Dan'uwan sa daya samu mata kamar *Deeya* yasa zata kula dashi sosai, cike da zolaya yace to kwantar da hankalin ki inafata dai baki cinye cus-cus din ba?..tace "a ah yace yauwa to kwalliyar fa?.. baki ta turo tareda cewa na bata ta, yace kashhhh..to amma yi sauri kigyara ta saiki dauko abinci kizo nakai ki gurinshi dama shine yace" nazo na tafi dake gurin sa,Dasauri tace da gaske yana ina?.. yace yesss *KYAUTAR* bera sai kin zo zan fada miki in dayake, tace kai Hmm *Hafeez* banaso, yace to nadai nayi sauri ki zo mutafi tace to sannan ya kashe wayar. *Feeya* tace yauwa to ki gyara kwalliyar ni kuma bari naje na shirya maki abinci a basket tace to, Nan da nan ta gyara tafita falon dai-dai lokacin da *Feeya* tafito kichin dauke da basket din abinci, Innan dake zaune a falon tace sai ina kuma haka? *Feeya* tace zata kaima "Hmm *Habeeb* abinci ne, lnna tace to adawo lafiya aida naji shigowar sa sai kuma naji yafita sukace "eh tareda fita. sai da *Feeya* taga tafiyar su *Deeya* sannan ta koma part din lnna. *Habeeb* kam yana shiga daki yaciro wayoyin sa daga aljihu tareda wallet ya watsa su kan gado, sannan yafada toilet da kayan jikin shi yasakar wa kanshi shawa yadauki tsawon wani lokaci sannan yayi wanka tareda dauro alwala yafito daure da tawul akugunsa da wani karami yana goge kai, *Harees* ya'iske yaciro masa jallabiyya baka me guntun hannu, cikin kwantar da murya *Harees* yace dan'uwa ka kwantar da hankalika ka dauki wannan abunda yafaru amatsayin kaddara, kashirya nace *"Hafeez* yadauko "queen of beauty bari naje nasiyo maka magunguna, kafi su'iso Kai kawai ya gyada masa sannan yafita shikuma yasa riga yanufi falo don yayi sallah la'asar. Bayan ya idar da sallah sai yakoma kan kushiya kwanta tareda lumshe ido yana jin wani irin mugun sarawa da kamshi ke yi gawani zafi da jikinsa yayi, alamar zazzabi yakama shi sosai sai juya kanshi yake ahannun kushi, Sallamar dayaji ne cikin zazzakar murya tareda sanyayyan kamshin turaranta suka sashi bude ido tareda zubasu akanta, dai-dai lokacin data ajiye basket din tanufi gurin shi gaban tane yafadi saka makon gani idon shi da sukai jajir cikeda tashin hankali tace.... *_Kuyi hakuri da wannan sai Allah yakaimu bayan sallah, ina rokon addu'ar Ku alfarman wannan wata me alkhairi Allah yabiya mana bukatun mu ameen, yasamu fara azumin nan lafiya ya kuma bamu ikon gama wa lafiya ameen._*, Muje zuwa A _*KYAUTAR ALLAH CE*_ (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 5โƒฃ1โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ "Wayyo! Hmm *Habeeb* din na meyasa mi idanuwan ka sukai yayi jajir?..murmushi yayi me cike da sonta tareda mika mata hannun shi "alamar taje gareshi aikam dasauri ta karasa gurin shi, ta saka hannun ta cikin nashi tareda zama agefen shi. Cike da kulawa takai hannun ta daya kan goshin sa zafi taji sosai hakan ne, yasata zaro ido cike da tsoro! tace Hmm *Habeeb* din na naji kan ka yayi zafi sosai har da jikin kama yayi zafi baka da lafiya ne?..ta kareshe fadi tareda sauko da hannun ta kan lallausan sajen fuskar shi, murmushi yayi cikin sanyi murya yace banda lafiya *Leemah* ta amma kin san me?..kai ta girgiza alamar "a ah yace *Leemah* ta dana ganki sainaji na naji sauki sosai yafadi yana murza lallausan hannun shi ta akan sajen fuskar shi, Cike da tausayi tace sorry Hmm *Habeeb* din na kuma kanajin yinwa KO?..tafadi tana shafa cikin sa, murmushi yayi me cike da wani irin *SONTA* Wanda koda yaushe jiyake yana karuwa acikin zuciyar sa, ahankali yadora hannun shi kan nata sannan yace *Leemah* ta inajin yinwa sosai am...dasauri ta katse shi dacewa dama aina san tun karin safe shike cikin ka, shine kuma kana dawowa kasake fita me makon katsaya ka huta kaci abinci dakace nayi maka, harda da kwalliya nayi maka amma kaki tsayawa kaga kwalliyar balle kuma kaci abinci dana girma maka, da kuma nakira ka sai maka kashe wayar, gashi yanzu kana tajin yinwa kilama ita Ce tasakar makada zazzabi Allah Hmm *Habeeb* yau am angry with u sosai tafadi tana turo baki sannan tajuya masa baya tareda rufe ido. Dasauri yatashi daga kwance yajawota jikin shi sosai tareda tallabo fuskarta da dukka hannuwan shi biyu, yace "a ah *Leemah* ta am so sorry kinji karkiyi fushi da Hmm din ki kinji? wlhy bansa lokacin da nayi reject din call din ki ba amma Insha'allah bazan sake kin daukar kiran kiba kinji *Leemah* ta?... pls open u eye's ki kalle ni mana. "Ahankali tabude idon tareda zubasu aka shi kurin sukai majuna kowanin su yanajin son dan'uwan sa yana ratsa sassan jikinsa, musamman ma *Habeeb* dayake jinson *Leemah* mahadine na rayuwar shi, itakam duk sai taji yabata tausayi gawani irin rama dataga yayi, hannun ta tasa itama ta tallabi fuskar shi kamar yadda yai mata cikin sanyi muryar tace na hakura amma pls kadai na zamada yinwa kaga kanada ulser kuma kasan itaba tason yinwa gashi yau daka wuni da yinwa duk Karame kafada sosai, murmushi yayi yanajin sonta yana sake fisgar shi, acikin ranshi yace *Leemah* ta ba yinwa ce tasani ramewa ba tsabar tashin hankali da masifar dana gani yau sune su kasani ramewa, wanda bana fatan sake ganinsu arayuwata koda ko acikin bacci ne yah Allah kaimin tsari dasake ganin wannan mummunan kazantar ameen. Jin yayi shuru yasata shafa lallausan hannunta akan lallausan sajanshi wanda yake kwance lufff Cikin sanyi muryar tace, Hmm *Habeeb* din naka daina zama da yinwa kaji?..Dasauri yace nadai na *Leemah* ta nadai na kinji?.. kaita gyada masa sai kuma ta kura masa ido aranta tanajin akwai wani abunda keda munshi aikam bazato yaji taje homasa tambaya da cewa Hmm *Habeeb* din na meke damu ka?.. Dasauri ya kalle tada idanun shi dasuka sake rikid'ewa, har suna wani ruwa-ruwa saboda tsabar bakin cikin da abunda *Jana* tayi masa wanda dazaran yatuna saiji wani irin bacin rai da bakin ciki mara musaltuwa, shikam Allah yasa yatsani *ZINA* amma wai matar shi ta sunna yakama tana aikata *ZINA* dawani har cikin dakin shi to waima tun tsawon wani lokaci suke aikata wannan kazantar ne?.. wata zuciya ce tace masa tunkafin ka aureta" ko kamata cewa duk da baka taba sanin wata 'ya mace ba sai ita amma hakan bai hanaka gane cewa ita" din ba'a budurwa kasa me taba, jiyayi kirjinsa yaiwani irin luguden faduwa da sauri yakauda kai gefe a ranshi yace *Leemah* ta *"Jana* Ce taci amana ta, ta ha'inceni kuma ta zalunceni saidai Allah ya'isa ban yafe mata ba, hannuta sa tajuyo da fuskar shi yayinda yai saurin maida hawayen dake shirin zubowa. Murmushi yasa kar mata tareda cewa kinyi kyau sosai *Leemah* ta, tace thanks Hmm *Habeeb* Dina nace meke damunka?.. yace yinwa nakeji *Leemah* ta, Dasauri tamike tareda cewa bari nadauko maka abinci, dasauri yace a a *Leemah* ta tareda mai da ita kan cinyar sa ya zaunar ya rungumeta sosai akirjin shi tareda dora kanshi aka fad'ar ta, yana shakar daddad'an kamshin turaren ta wanda tuni yasakar masa kasala. ahankali yasa dukka hannun shi ya tallabo fuskar ta yahad'e danasa ahankali yake goga mata sajenshi afuskar ta, cikin wani irin yanayi yace *Leemah* ta nifa yinwar ki nakeji bata abinci ba, Dasauri tabude idon ta da suke lumshe, zaro sutayi cike da dan tsoro tace kai! Hmm *Habeeb* dama anajin yinwar mutun ne?.. murmushi yayi tareda "eh mana auke baki saniba?.. tace "eh to me zan baka?..yace kawo kun nan ki naga ya maki. kunnan tamika masa yai mata rad'a Wanda banji abunda yace mata ba saidai, nagata zaro ido tareda tureshi ta tashi tana dariya tace la! la!! la!!! Kai! KO?.. yace "eh tareda tashi shima yana dariya, tace tau nidai ban tabaji ba yace tau yau kinji so pls *Leemah* ta kibani Allah yinwar sa nakeji kinji?..yafadi yana kokarin riketa yana dariya, tsalle tayi taboye bayan kushi tana dariya tace umh nakiya yace pls *Leemah* ta tsaya kiji mana, tace a ah nidai kaci abinci yace zanci amma kin fara bani wannan tukun na. tace tau zan baka amma sai kafara cin abinci, Dasauri yace da gaske zaki bani?.. tace "eh yace pls promise me *Leemah* ta?.. tace Allah Zan baka yace yauwa *Leemah* ta tauki dauko mun abinci amma saikin fara hada mun coffee tukun nan yafadi tareda zama tace to. Bayan taje kichin tahado masa coffee takawo masa yasha, sai ta zuba masa abinci tami kama sa saida yakar ba ya ajiye sannan yarike hannun ta tareda cewa yauwa wanaka ma umuh?..yafadi yana kashe mata ido tareda jawota jikinsa, cike da shagwaba tace ayya Hamman Dina nace zan baka, yace Hmm tau d'an bani sweet mouth dinki nasha Allah nayi kewar sa sosai har zatayi magana ya had'e bakin su, yana tsotsa saida yasha bakin sosai sannan yacire bakinsa daga nata tareda, da sauke numfashi yace oya muci abinci bamusu suka fara ci. yanaci yana bata tareda zuba mata santi ita kuma sai dariya take masa, ahaka har suka gama sannan takwashi kayan takai kichi ta dawo falon ta zauna kusada shi, yace bani alkawari na tashi tayi dasauri zata gudu cikin zafi nama yajawo ta tafada jikinsa dariya ce takwace masu gaba daya, yace hmm! wato da wayo zakiyi mun ko?..yafadi tareda yimata cakulkuli dariya take tana cewa a ah ba wayo zayin maka ba. Cikin dariya ya kwantar da'ita akan kushin din tareda yi mata runfa yace tau oya bani, dariya take sosai jin yadda yake mata cakulkuli har tana tura hannun wanta Cikin lallausan suman kanshi ba tareda ta saniba, cike da zolaya tace Kai! Hmm *Habeeb* dina nifa bansan ta inda zif din rigar yake ba, jin hakan yasashi lumshe ido cike da shaukin kaunar ta wanda yasashi mantawa Da bakin cikin da *"Jana* takunsa mashi, ahankali yasaki lallausan murmushi tareda cewa karki damu *Leemah* ta ni nasan ta inda zif din yake, barima kigani yanzu na nemo shi yafadi yana kokarin tura fuskar shi tsaki yar kirjinta yayinda hannun shi ke laluben ta inda zif din yake, _nikam Ina ganin haka na falla da gudu na bar falon domin ido na ba zasu iya ganin abunda *Habeeb* yake shirin yiba lol_. ***** "Aban garen *Jana* kam idan hankalin ta yai dubu to ya tashi kasan cewar tunda *Habeeb* yafita da ado sai hankalin ta yakasa kwanciya, don haka saita kira layin ado don taji inda yake wayar tayi kara saidai kuma bai dauka ba data sake kira sai taji akashe, Saita kira layin *Habeeb* shima sai taji aka she hakan ne yai mugun daga mata hankali, tafara safa da marwa, tana cigaba dakiran layukan su amma duk ba wanda tasamu, don haka saita kira Shafa tafada mata abunda yafaru takara dacewa do Allah taje ta duba mata ko "ado yakoma gida, Shafa kam masifa tafara yimata tareda cewa amma dai ke banza ce wlhy to yanzu idan yaga ne cewa ba mace bane namiji ne fa ya zakiyi?.., gaban ta ne yafadi ta dafe kirji tareda cewa ai koda nashiga uku ni *Jana*, cike da haushi ta Shafa tace aiko idan bakiyi da gaske ba zaki shiga

Chapter 21 of 42