haifeta agidan talauci ba, sannan kuma tayi aure agidan talauci ba shi kuma Ado baya sana'ar fari bare Na baki, sai zaman kashe wando da shaye-shaye wannan kenan.
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ5โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Da gudu *Jana* tashiga gida tana ihun fadin yau tasamu irin mijin datake son ta aura, zama tayi tsakar gida saman kujera yar tsugun ne, jikinta narawa tafara kirga kudin da bata taba rike irinsu ba tunda take,
dubu hamsin da biyar takirga, wani ihun tasa tareda cewa tayi miji wlhy gobe kasuwa zata tayo siyayya dama kayantaa duk sun tsufa, sannan ta kalli mahaifiyarta dake tsugunne abakin murhu tana faman kokarin hura wuta da toton masara,
tace Dije _haka suke kiranta_ kingani ko"...? dama nace maku nidin yar gidan arzikice, cikin sanyi murya tace murjanatu waya baki kudi masu yawa haka...? dariya tayi tace mijina, dasauri Dije tace ayya murjanatu bazaki daina bin samarin banza ba wato ma acikin su harda da miji kika ajiye ko...?
wani irin kallo tayiwa uwar tareda cewa kefa Dije haka kike toh" mijin da zan aura nake nufi fa, nan dai tafada mata abunda yafaru tsakanin ta dasu *"Habeeb*,
Ajiyar zuciya Dije tayi tace da dai yafi maki da wannan shashancin dakike tafaman yi, agari Allah ya tabbatar da alkhairi tace ameen toh" Saiki fara fadawa Baba tun yanzu nasamu miji don haka zanyi aure nabar wannan gidan da babu komai cikinsa sai zallar talauci, takarashe fadi tareda tashi tana yatsina fuska tashiga dakinta Kai Dije ta girgiza tareda cewa Allah ya shirya ki.
Can saiga *Jana* tafito sanye dariga da zani nawata kodaddiyar n atanfa tareda yafa wani tsohon gyale hannun ta rike da jaka, Dije ta kalleta tareda cewa ina kuma zakije yanzu da yamma..? ba tareda ta kalli inda Dijan take ba tace gidan su Shafa zani _shafa kawar tace_ sannan tafita abunta, Kai Dije ta girgiza tareda cewa Allah ya kyauta.
Da *Jana* tafita bata tsaya ko'ina ba sai dakin Ado saurayin ta, yana zaune bakin kofar dakinsa sai faman busa taba yake yana ganin ta yamike tareda Kama hannun ta suka shiga daki,
Ba tareda bata lokaci ba suka shiga aikata bad'alarsu saida sukayi mai isarsu
Sannan suka sararawa kansu, sai *Jana* taciro kudi dubu goma taba Ado jikinsa narawa yakar ba yana cewa *Jana* Waya baki kudi..? tace mijin dazan aura fuska ya daure tareda cewa yanzu da gaske bazaki aure niba saboda banida kudi..?
Cikin sanyi murya tace kayi hakuri Ado gaskiya niba zan'iya rayuwa acikin talauci ba, yace toh" yanzu kina nufi idan kinyi aure mun rabu kenan..? tace "a ah zansan yadda zanyi muna haduwa yace toh" shikenan kinsan nariga nalasa zumarki tace nima haka, sannan tafito ta tafi gidansu Shafa tafada mata tareda cewa gobe zata rakata kasuwa tayi siyayya daga nan suje gidan Aunty Binta tace toh"
sannan takoma gida.
*******
Kamar yadda *Harees* yace zasuje gidan lnna Hafsatu gurin Safeena sunje,
Safeena takasan ce doguwa kyakkyawa yar siriri, yace saidai tanada _sharp_ me kyau itadin ba fara bace saidai kuma ba za'a kiranta baka ba irin _chocolate, color_ din nace alokacin shekarunta goma sha bakwa alokacin satin ta biyu dagama secondary.
Ba tareda bata lokaci ba *Harees* yafada mata abunda ketafe dasu ta, amince tareda nuna farin cikinta.
*Bayan kwana biyu*
**********
Acikin kwana biyu *Habeeb* da *Jana* sun dan shaku ba laifi sun kuma fahimci juna, domin *Jana* ta'iya jan hankalin namiji da kalamai tareda kwarkwasa, don haka tuni tasamu dan wani matsayi agurin *Habeeb* kodon kasan cewar su talakawa, duk da bawani mugun jinta yake aransa ba, saidai kawai yana jin tausayin ta, kuma yaji aranshi yana son ya aure ta kodon yanayin dayake ciki,don haka yanemi tabashi dama yaturo magaba tanshi.
ba tareda bata lokaci ta amince mashi yaturo gidansu don a tsayar da magana, mahaifin *Jana* yakarbrsu Baffa hannu bibbiyu cikin mutunci musamman ma dasuka fadi cewa *Habeeb* dan Alh Hashim soro ne tsohon gwamnan su me adalci, su Baffa sunji dadi yadda yai masu, kuma batareda bata lokaci ba yace yaba *Habeeb Jana* *KYAUTA* bayan sadaki baya bukatar komai,
Don haka sadaki kawai su Baffa suka bayar akasa biki tareda na *Harees,* Wata daya wanda zayayi dai-dai da lokacin angama gini sabon gidajen da Abba yasa aginina masu a New G R A,
*******
Akwana atashi bawuya agurin Allah saura sati daya buki alokaci tuni angama ginin gidajen harsun koma inda aka gina part uku biyu _upstairs_ Na Abba da *Habeeb,* daya kuma na Baffa shi yace bayason gidan sama, sai nasu Baffa Al-mustafa wanda yake ta can bayan nasu *Habeeb* suma tsari gini iri daya ne Dana su Abba,
wato Baffa Al-mustafa da *Harees* sunan _upstairs_ ne su kuma Kakanni *Harees* irin ginin su Baffa akai masu domin suma basu son gidan sama.
Su *Jana* anata shirye-shiryan buki itada Shafa, *Habeeb* ya cikasu da kudi sosai ranan Wata Jumma'a, *Habeeb* yaje gurinta dama tace sai yazo yakai ta ta gaida Hajiya, saidai ita badon tagaida Hajiyar zataba saidon taga gidan da'akace duk New g r a babu kamar shi agurin kyau da tsaruwa,
Koda suka isa direct part Hajiya suka shiga, *Safeeya* da *Sadeeya* suna zaune afalo sunsa Hajiya tsakiya sai faman shagwaba sukeyi mata, suna sanye da riga da wando na fakistan yai masu kyau sosai, sallamar *Habeeb* ne yasa sukayi shuru, Hajiya ta amsa tareda cewa yauwa aiga Hamman kunan,
Don Allah Kara bani da rigimammun yaran nan, waisu sai dole nasa Musa direba yakai su gidan "Addansu Mamu nace subari sai gobe tunda yau Murjanatu zatazo sannan yanzu karfe 5:00 yamma tayi waisu a ah saidai sunje, fuska daure yace toh" ance baza kuje yau din ba kuma duk yarinyar data sake damunta sai na 'bata mata rai tunda ku baku da hankali,
bayan yagama fadin haka sai yakalli *Jana* yace zaya shiga gidansu *Harees* idan sun gaisa da Hajiya da "Inna su *Sadeeya* su kawota tagaida Hajiyar su *Harees* tace toh" , sannan yafita bayan sun fito part su Inna sannan suka nufi gidansu *Harees.*
Suna gaba tana biye dasu abaya saifaman kuskus suke suna kallon *Jana* suna dariya kasa-kasa, KO" meke basu dariya oho!, ita kuma *Jana* data kalli *Sadeeya* sai taji gabanta yafadi domin kyan *Sadeeya* ya firgita ta sosai, sannan tarasa meyasa idan suka hada ido saitaji wani irin tsoro tareda faduwar gaba,
Tsayawa sukayi suka sata tsakiya sai kuma suka kalleta sannan suka hada baki sukace, tab amma dai gaskiya Aunty *Jana* ke banza Ce, kirasa wanda zaki aura sai Hamman *"Habeeb* , ido tazaro ๐ณcikeda tsoro tace meyake dashi.?
Sukace tab! ke baki San cewa shi" mugu bane rankwashimu fa yake harda da duka kema idan kiga aureshi haka zaya dingayi maki, KO" *Feeya* tace "eh mana inji cewar *Sadeeya,* ajiyar zuciya tayi murmushi duk da cewa tasan acikin maganar su akwa zallar kuruciya hakan bai hana tajin zafin banza da suka ce mata ba,
Sai tace aini bazai duke ni ba tunda ni matarsa ce Ku kuma kannan shine zaya iya dukan ku idan kunyi masa laifi, ido suka hada tareda tabe baki, *Sadeeya* tace toh" aishiko ba'ai masa laifi ba sai yadinga yima mutane mugunta yana zare masu idanun nan nashi masu ba mutun tsoro ko...?
*Feeya* tace "eh mana bayan ya duke ka koya rankwashe ka sai kuma yace" wai kayi ma shi shuru๐คซ tafadi tareda nunawa dai-dai lokacin da suka isa kofar gidan suka kwankwasa kofar megadi yabude masu suka shiga, basu Dade ba su kafito suka koma gida.
*Habeeb* ne ya Kallin *Jana* yace naga tunda muka baro gida baki ce komai ba sannan naga ranki kamar yabaci lafiya..?
Yatsina fuska tayi sannan tace gaskiya "kannan ka sunbata mun rai sosai musamman ma wadda tafi kyau din nan, dasauri yace me "sukayi maki, nan tafada ma shi abunda su *"Sadeeya* suka cema ta,
Rai bace yace tayi hakuri zatayi maganin su tace toh" sannan yasauke ta tashiga gida azaure ta tsaya tana lekensa, yana rebas tace yan'iskan yara Allah yasa idan yakoma yaimasu dukan tsiya harma dai wannan meshegen kyau kamar aljana sanna taja tsaki tashiga gida shima ya nufi gida.
Part din Hajiya yashiga bai same su nan ba, don haka dasauri yafito yanufi part din su lnna, nan ya'iskeku suna tazuba ma lnna shagwaba suna ganin shi suka sha jinin kin su" yace sannu lnna tace yauwa sannu *Habeebu* an kai murjanatu gida ko..? yace "eh tace to" madallah Allah yakaimu lokaci lafiya, cikeda jin kunya yace ameen.
Sannan ya kalli su *Sadeeya* yace kuzo nan bamusu sukabi bayan shi har zuwa part din shi, saidai gaba daya atsorace suke musamman ma *Sadeeya,* zama yayi saman kushin tareda dora kafa daya saman daya, sannan ya watsa masu wani irin firgitattace kallo da yasa suka zube kasa ba tareda sun shirya ba,
Cikin tsawa yace idan har matar dazan aure an kiranta" banza toh" ni kuma me za'akira ni...? Cikin subutar baki *Sadeeya* tace mugu, sai kuma tarufe baki ๐คญ cikeda matsanancin tsoro dasauri *Safeeya* tace ke! Ko..? *Deeya* sai kuma tarufe baki cike da tsoro, dasauri *Habeeb* yamike cikin matsanancin mamaki yace...?
*_SLM MASOYANA kuyi hakuri dajinkirin danayi banyi maku posting akan lokaci ba, kwana biyu ina wasu ayyuka ne shiyasa_*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ6โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Wato ni kuma mugu za'akira ni ko..? dasauri tace a ah Hamman *Habeeb* za'akira ka, yace "a ah mugu dai za'akira ni, don haka yanzu zanyi maku muguntar tawa kunga sai kuji dadin kirana mugu da tushe, dai-dai lokacin daya fisgo wayar radio ajikin station,
*Safeeya* yafara tsulawa kasan cewar ita ke kusa dashi aikam tuni tasaki ihu tana fadin yayi hakuri, amma Ina bai saurareta ba sai tsulamata wayar radio kawai yake,
itakam *Sadeeya* tun kafin akai kanta take ta kasharban kuka tana tsalle tareda yarfa hannuwa, tana fadi don Allah Hamman *Habeeb* kayi hakuri basan sake cemaka muguba, saida yayi ma *Safeeya* goma sannan ya kyale ta aikam da gudu tafita dakin tana kuka,
Sannan yanufi *Sadeeya* wacce ke tafaman zagaye gushin tana kuka, har zata gudu yai surin rikota yadaga wayar radio zaya tsulamata kenan tayi sauri shigewa cikin jikinsa, ta cukuikuikuyeshi aikam tuni yaji yarrrrr! ajikinsa yayinda kirjinsa yabuga, idon yarintse ahankali yafurta yah ilahee! Cikin kasalalliyar murya yace sakeni, Ina itakam batama jishiba domin ihu kawai take tana fadin don Allah Hamman *Habeeb* kayi hakuri karka dukeni nadai na,
Cikin tsawa yace naceki sakeni dasuri tasakeshi jikinta sai rawa yake aikam tuni yafara tsulamata wayar radio, sai ihu take tareda bashi hakuri sau biyar yayi mata zayayi na shidda taruga da gudu sai part dinsu *Safeeya,* Hajiya tana falo tana kallo tafada jikinta tana kuka, cikin matsanancin tashin hankali Hajiyar ta dagota tana salati tareda tambayan ta wane ya doke ta...?
Cikin matsanancin kuka tace Hamman *"Habeeb* ne, dai-dai lokacin da lnna tashiga rikeda hannun *Safeeya* kasan cewar can part din tanufi, gaba dayansu sai kuka suke cikin gigita saboda zafin dasukeji yana ratsa jikinsu,
kasan cewar tunda suke ba'a taba yimasu irin wannan dukan ba, don haka duk sai suka gigice suka cika falon da kuka musamman *Sadeeya*, da bata hada jikinta da komai ba,
Cikin mamaki Hajiya tace me kukayi masa"..? Inna Ce tafada mata abunda *Safeeya* tace *Sadeeya* tace ma *Habeeb* din, Hajiya tace "eh lallai sunyi laifi toh" amma aibaika mata yai mata irin wannan dukan ba dubi jikinta fa,
_abuga fara duk gurin yayi jajir_
lnna tace Hajiya *KYAUTA* dai tayi laifi kuma ita kadai ya kamata yaima duka tunda banajin magana, amma bawai yahada harda *Safeeya* ba dubi jikinta fa da'alama yafi dukan ta sosai, Hajiya tace aishine kyau namarar kunya kenan Wanda bayajin magana,
lnna tace ga marajin magana nan kusada ke marar kunyar yarinya me shegen daukar maganar tsiya, ta karashe fadi tana hararan *Sadeeya* dake tafaman kuka tana turo baki,
tace ai zakiyi me tunshe ne idan nasa *Habeebu* yasake dukan ki dakyau, dasuri Hajiya tace a ah Hajiya Aisha karki farashi wlhy duk wannan dukan bai'isaba saikin sake sashi yakara mata wani toh" bazan yadda ba,
lnna batace komai ba saidai taja hannun *Safeeya* suka fita tana cewa muje kiyi wanka kinji, suna fita Hajiya tace ma *Sadeeya* yi hakuri tashi muje kiyi wanka kinji hali dubu na, kyale shi aizaya shigo yasame ni, amma ke kuma karki sake yi masa rashin kunya daga shi har matar shi kinji KO"..? tace toh".
Tunkafin *Sadeeya* tagama wanka tafara rawar sanyi alamar zazzabi yakamata, bayan Hajiya ta taimaka mata tashirya sannan suka fito falo Hajiya ta daga wayar line land ta Kira *"Harees* tace yazo da alluran zazzabi yaima *Sadeeya*, aikam tanajin ance allura tafara fadin Hajiyarmu niba nasan allura, tace kinyi hakuri ayimaki sai zazzabin ya sauka, dai-dai lokacin da *Harees* yashiga hannun shi rikeda wata yar karmar box,
Bayan sun gaisa sai yake tambayar Hajiya meya samu *Sadeeya..?* nan tafada ma shi abunda yafaru, sannan yai mata allura dakyar ta tsaya domin batason allura sannan yafita part din lnna ya nufa, inda ya'iske itama *Safeeya* zazzabin yarufeta sosai itama alluran yai mata sannan yafita yanufi part din *Habeeb* yana fada akan irin wannan dukan da *Habeeb* yai masu.
********
*Habeeb* kam *Sadeeya* na guduwa yasaki wayar radio kasa tareda fadawa saman kushin domin kafafun shi sun kasa rike shi, sai kuma numfashin shi yafara fita dasauri-dasauri, yayinda yaji kanshi yasara sai kuma sanyi yafara ratsa sassan jikinsa don haka dasauri ya dunkule cikin kushin din yana fitar da numfashi dasauri-dasauri.
Yana cikin wanan halin ne *Harees* yashiga dakin yana masifa ganin halinda *Habeeb* din yake ciki yasashi yai shuru tareda karasawa gurinsa dasauri yana cewa lafiya...?
Dakyar *Habeeb* yabude 'idanunsa da sukai jajir sannan yace inajin zazzabi ne yake son Kama ni, hararan shi๐ *Harees* yayi tareda cewa Allah yasama zazzabi ne ya kamaka kaga kaima sai kaji abunda su" "Sofee sukaji mugu kawai,
Cikin mamaki *Habeeb* yace kaima mugun zaka kirani..? yace "eh ankiraka mugun toh" idan ba mugu ba wanene zayayi irin wannan aikin,
ka kama "yara kawai sai duka ka ke kamar ka samu jakai, tsaki *Habeeb* yayi tareda rufe idon yace shine harka kecewa Allah yasa zazzabi yakama ni...? yace "eh nace din,
Toh" aishi ciwo daka ganshi yasan dakin kowa kuma an duke su din sai me..? *Harees* yace saiga shi nan Allah yasa ka masu, tsaki yasake yi tareda cewa kai! "yaran nan ma sun rainani wlhy, yace renin me sukai maka..? hararan shi yayi tareda cewa idan basun renani ba yaza'ayi sukira matar da zan aura banza, sannan nikuma sukirani mugu sai kuma ace karna hukunta su...?
Ina ai ba zaiyyuba don haka KO" gobe sukai mun rashin kunya saina hukuntasu marasa kunya yara kawai ko'anfada masu ni din tsaran sune,
*Harees* yace ai sun sannan kai ba tsaransu bane, sannan kuma aiba wai nace karka hukuntasu" bane, hukuncin da kayi masu"ne yayi yawa
tsaki yayi tareda cewa muddun suka sake yi mun rashin kunya sainayi masu" hukuncin dayafi wannan.
Yace saboda kana bakin mugu ko mlm nidai gyara nayi maka allura, yace bana so yace ai kuma baka isaba box din yabude yaciro allura yadai-daici gurin da'ake alluran yacira tareda kallon *Habeeb* din da idonshi ke rufe kamar ba'a ajikinsa ake tsira alluran har *Harees* yagama mashi alluran, amma KO" motsi *Habeeb* beyi ba, baki *Harees* yatabe tareda cewa toh" sarkin jarumai ai saika mulmula, idan kuma baka mulmula ba ni baruwana kafarka ce zatarike shikenan sai kazama gurgu *"Jana* tace" tafasa itakam bazata auri gurgu ba,
yafadi tareda daukar dan akwanin yafita dasauri yana yimasa dariya,
yayinda *Habeeb* yai sauri yasa hannu yana mulmula gurin๐tareda cewa toh" bakin mugu bakinka yasari danyan kashi๐.
*Bayan kwana biyu*
********
Su *Sadeeya* sunji sauki daga zazzabin dukan da *Habeeb* yai masu, saida Abba da Hajiya sukai masa fada akan yasan irin dukan dazaya ringa yi masu idan sunyi masa laifi, bayan suma anyi masu fada wanda tun daga ranan suke bala'i tsoron shi musamman *Sadeeya,* dako ido suka hada sai taji gaba ta yafadi.
*********
Ranan Jumma'a akasa amare da angwaye lallai dagari yawaye asabar aka daura aure, bayan "angama shagalin buki amare suka tare adakin mazajen su, inda *Harees* yasami Safeena cikakkiyar budurwa sabani yadda *Habeeb* sami *Jana* duk dacewa baita ba nasani wata 'ya mace basai ita hakan behana shigane cewa itadin ba cikakkiyar budurwa bace,
Domin kuwa *Harees* yafada masa duk yadda cikakkiyar budurwa take, shi kuma duk bai ga hakan agurin *Jana* ba Wanda yayi mamaki hakan yayinda ranshi yabaci sosai, data fahimci cewa yagane bata kawo masa budurcin taba sai tafara yi masa kukan karya tana fadi yayi hakuri itama bada son ran ta haka yafaru ba wlhy fyade akai mata,
jikinsa yai sanyi don haka sai ya lallashe ta tareda cemata ba komai, saidai kuma yarasa meyasa zuciyarshi bata yadda da cewa "eh fyade akai mata ba, hakan nan dai yai hakuri aka cigaba da harka.
*Bayan sati uku*
*******
Wanda cikin sati uku nan *Jana* ta fahimci *Habeeb* mutun ne mabukaci sosai, don haka sai tafara kokarin hana masa kanta
Ranan wata Jumma'a bayan sun dawo masallaci sai *Habeeb* yashiga part din shi a matukar bukace ko" daya nemi *Jana* sai tace Ina ita sam ba zatayi yace haba *Jana* saboda me zaki ce haka..?
tace saboda ita gaskiya ta gaji haka kawai sai yaita faman gurzanta kullun kamar kayan wanki, yace toh" aike matata ce dole idan bukatata ta taso nazo gurinki, tace toh" itadai tagaji ba zatayi ba yace haba *Jana* don Allah kiyi hakuri wlhy amatukar bukace nake,
tace itafa gaskiya ba zatayi ba don haka ya kyale ta kawai Cikin tsanani bukata yace don Allah *Jana* kiyi hakuri ki taimaka mun wlhy jinake idan banyi ba mutuwa zanyi, tace toh" taji zata taimaka mashi amma da shiradi dasuri yace menene sharadin..? kauda Kai tayi daga barin kallon shi domin wani irin mugun kwarjini yai mata sannan tace saika biya kudi Cikin tsanani mamaki yace...?
*_Jumma'atul-mubarak MASOYANA._*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ7โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
*Jana* kinji abinda kika fada kuwa..? ba tareda ta kalle shiba tace "eh ai kunnuwa na sune suka faraji sannan bakina yafada,
Cikin tashin hankali yace yah ilahee *Jana* kina a matsayin matata ta sunna don zanyi tarayya dake saina biyaki kudi...? tace tabbas sai kabiya kudi domin wlhy bazan sake yadda ka cigaba da gurzana a banza ba, kusan sau uku fa kakeyi kullum don haka kawo kudi, tafadi tareda mika masa hannun still bata kalleshi ba,
Cike da mamaki *Habeeb* yabi hannun ta da kallo, tace idan bazaka biya ba zan tashi da sauri kuma cikin tsanani bukata yace toh" naji nawa zan biya...?
tace kawo dubu ashirin dasauri yaciro wallet acikin aljihun riganshi, yabude yazaro kudi akalla zasukai dubu hamsin,
jikinsa sai rawa yake tsabar abunda yakeji har yafara kirgawa sai yaga kirgawar zata bata masa lokaci, don haka sai yamika mata kudin duka tareda cewa gashi,
dasuri takarba tana washe baki tace yauwa *BB* na ko kaifa kasan tun ran da nafara ganinka nagane kai dan arzikine irin albarka, tafadi tana kokarn kirga kudin da sauri yace kibar idan mungama saiki kirga kudin tace toh" Bismillah.
_Nikam nace ita kuma yar maciyata jikan fakirai ba๐, dafatan dai maikaratu bai mantaba har yanzu Cikin *TUNA BAYA* muke ba.....?_
*******
Sannu ahakali *Habeeb* yafahimci *Jana* rikakkiyar kazamace domin hatta da pants da brezias bata wankewa, Wanda baisan hakan ba sai ranan dayaga meyi masu wanki da guga yashan yasu atsakar gida, duk sai kunya yakama shi saboda duk Wanda yazo wucewa sai yagani,
Rai bace yanufi part dinshi dasuri ta taso zata rungumeta shi yadakatar da'ita da hannun, domin alokacin tuni yafara *_DANA SANIN AUREN TA_* musamman daya gane itadin Maison abun duniya ne, gata kuma muguwar marowaciya domin yakula batason yana yima mutane alkhairi,
inda yanuna mata itaba ta'isa tahana shi yin alkhairi ba, gashi tuni yagane itadin dankwalace kan nan nata bakomai ciki domin yasha yimata magana da turanci bataji balle ta'iya mayar masa sai kace bata taba shiga ajiba, hakama fanni karatun addinima komai bata iyaba,
Cin bacin rai yace kar tasake saka pants da brezia Cikin kayan wanki,
Sai tace toh" idan batasa su Cikin kayan wanki anwanke ba toh" yaza tayi dasu...?
yace ta
wanke dakanta mana, tace a ah itakam gaskiya bazata iya wankewa ba haka kawai zata wahalar da kanta bayan Allah ya hutar da'ita,
Cikin bacin rai yace toh" muddun tasake sakasu Cikin kayan wanki sai ya bata mata rai, ganin yadda yayi mugun hada rai yasa tace toh" bazata sake sawa ba, don haka tundaga ranan bata sake sakawa ba saidai ta wanke abunta.
Sannan *Jana* bata'iya girkiba ko kadan tun bayan da Hajiya tadaina kai masu abinci, sai tafara girka nata saida KO" kalluwa abinci baiyi balle yaciyu, don haka sai *Habeeb* yafara shiga part din Hajiya yanaci, dayaga zata fahimci wani abu sai yadaina zuwa yakoma shiga part din lnna, itama dayaga zata fahimci wani abu sai yadaina shiga,
yakoma zuwa gidan *Harees* wanda shida matarshi Safeena zaman su lafiya lau, gashi ta'iya abinci ga tsabta bashi dawata matsala sabani *Habeeb* dayake da'ita dumu-dumu,
kuma bayason kowa yasani don haka sai yadaina zuwa part din kowa, yakama zuwa gidan siyar da abinci yanaci sai kuma *Jana* tafara nuna kin yan'uwanshi, musamman *Safeena* da *Sadeeya*,
Su kam jitake kamar tashafe su adoron kasa shiya sama basu cika shiga part din sosai ba, kuma tasan da cewa *Habeeb* din baya sakarwa su *Sadeeyar* fuska amma haka take nuna tsanarsu" afili, domin tafahimci sunada matukar matsayi azuciyar shi shiyasa takejin mugun haushin su.
shikam tuni yaja mata burki inda yanuna mata cewa shifa yan'uwansa bai hadasu dakowa ba, don haka dole ta nutsu take dan jansu ajiki, sudama bawai sun damu da'ita bane kamar yadda suka damu da Safeena.
Kuma tundaga ranan da *Jana* tace sai yabata kudi zaya kusan ceta, toh" shikenan duk lokaci da *Habeeb* zaya kusance ta sai yabata kudi, idan kuma bai bata ba bazata taba bashi kanta ba,
tun abun yana damun *Habeeb* har yadaina damun shi, saidai kuma batada wani sauran daraja agurin shi,
Shidai yana zaune da'itane don biyar bukatarsa shiyasa ya cigaba da biyanta kudi, yana kusantar ta domin shikam idan akwai abunda yatsana arayuwar sa toh" bai wuce *ZINA.*
Sannan kuma idan takarbi kudin sai tayi duk yadda zatayi tafita dasunan zuwa Unguwa sai tayi, saidai kuma tana fita sai tanufi Unguwar su Ado taje tabashi kanta yayi yadda yakeso, sannan kuma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 42