Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yake tafe dashi, saidai ya fahimci yanajin kunya fadine wanda kuma ya tabbatar bazai wuce maganar *"KYAUTA* ba, Don haka cikin hikima Baffa yake janshi dafira har *Habeeb* din yafadi masa abinda ketafe dashi, inda ya karashe fadi dacewa Baffa gashi inason zan koma gurin aiki tunda anata ki rana a waya saidai inajin tsoron kar bayan natafi "Abba yaraba aurena da *Leemah* ta, kamar yadda yafada. Murmushi yayi tareda cewa *Habeebu* kenan ai nafada maka babu wanda zaya raba auren Ku don haka katafi gurin aikin ka, saidai inason kasake riko da ibada ka dogara ga Allah kuma rike addu'a sosai ga wasuma zan baka yace to Baffa nagode, nan dai yafada mashi addu'o'i masu yawa sannan yatashi zaya fita yanata godiya inda Baffa yaketa maimaita masa ya rike Addu'a tareda yawan anbato Allah domin yanason harshen dayake yawan anbato nashi. Part din Hajiya yanufa gaban sana faduwa bakin sa daukeda addu'a yashiga falon saidai be'iske kowa ba, don haka sai yashiga dakin Abba zaune ya'iske shi adan karamin falon sa zama *Habeeb* din yayi kusada Abban tareda sake gaida shi amsawa yayi fuska sake Wanda yasa *Habeeb* yaji wani irin sanyi zuciyar shi domin raban dayaga fara'ar Abban tun ranan dasu kazo, aranshi yake fadin Allah yasa Abba ya hakura yajenye maganar sakin ameen. Abba yace ya'akayi ne Na ALLAH?.. kalar tausayi *Habeeb* yayi tareda cewa Abba dama yau nake son koma wa gurin aiki shine nazo nasake baka hakuri, don Allah kayi hakuri wlhy bazan taba iya sakin *Leemah* ta ba, sannan don Allah Abba ko bayan natafi kar karaba auren kamar yadda kace wlhy Abba ina *SONTA* sosai. Murmushi Abba yayi tareda dora hannun shi saman lallausan suman kan *Habeeb* din, sannan yace *Habeebullah* da *Haleematus "Sadeeya* hadin Allah ne wanda babu wani mahalukin daya isa ya rabashi ba, kamar nidin nan ban'isa na rabaka da "itaba domin itadin "takace ALLAH yabaka *KYAUTA* tun fil'azal, shin wakake gani zaya rabaka da abinda Allah yabaka?..babu shi Na ALLAH don haka ka kwantar da hankalin ka kaje kayi aikin ka idanka dawa wani zafi sai katafi da matarka, sai ka kula sosai banaso wani abu makamancin wannan yasake faruwa kaji ko..? Cikin wani irin farinciki mara musaltuwa yace to Abba nagode sosai, kuma insha'allahu hakanan bazaya sake faruwa ba Abba yace to shikenan Allah yasa haka, yace ameen, to tashi kaje ka sallami hajiyarku tana nan sama yace to tareda tashi yanufi saman, *ZUCIYAR* shi fari tas kamar wanda akaima bishara da aljanna. Zaune ya'iske Hajiya yayinda *Deeya* ke kwance akan kafafunta, fira suke abun su gwanin sha'awa zama yayi tareda kallon su jiyayi kaunar su tana bin dukkan ilahirin jinkinsa, cikin sanyi murya ya gaida Hajiya domin yaga tahade fuska wanda hakan ne yasa yaji jikinsa yai sanyi, dai-dai lokacin da *Deeya* ta tashi fuska daure ba'alamar fara'a, Sanye takeda wata jar tamfa me ratsin yalo dinki riga da siket ne wanda yadan kamata kadan, saidai hips dinta yafito sosai wanda yasa gaba daya *Habeeb* ya shagala da kallon ta domin wan irin kyau tayi masa marar musaltuwa, itakam ba tareda takalli inda *Habeeb* din yake ba tace ina kwana, Dasauri yace lafiya lau *Leemah* ta kin tashi lafiya?.. bata amsa ba saidai tace hajiyarmu zanje na kwanta, tace to hali dubu na atashi lafiya tace Allah yasa tareda shigewa dakin Hajiyar. Hajiya ta kalli *Habeeb* tareda cewa inason naje umara, cikin girmama wa yace to Hajiya yaushe ki keson tafiyar?.. tace wani sati tunda akwai komai akasa tare kuma zamu tafi da "hali dubuna, dasauri yace Hajiya maganar komawar tafa ?..gashi "Abba yace" idan nazo wani sati na tafi da'ita". tace "eh zata koma tunda yace" takoma amma sai mun dawo umara ko shima da sharadi cike da tsoro yace... Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน[7/2, 11:49 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 4โƒฃ0โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Hajiyar mu wani irin sharadi kuma?..tace da farko karka kuskura kasake aikata laifi maka manci haka domin bazan dauki hakan ba, kasani sarar ban hada hali dubu na dakowa ba, cikin farin ciki yace nasani Hajiyar mu kuma insha'allahu hakan bazaya sake faruwa ba, Tace to sannan idan mun dawo bazata koma abuja ba saidai "ta zauna anan Bauchi, don bai yuwa kasake mayar da ita can "matar ka taci gaba da cuta "mata bazan sake yadda da hakan bako kad'an kuma kagaya mata karta sake samata beraye tunda tasani sarar bataso, sannan kuma kafin mudawo ka samo masu admissions "itada *"Safeeya* tunda Jam dinsu yafito kuma yayi kyau don haka inason su cigaba da karatu, idan ka amince to idan kuma baka amince bato maganar rubuto takarda t.... Dasauri ya katse ta dacewa haba Hajiyar mu indai wannan nan ne sharadi na amince, Allah yadawo daku lafiya tace ameen yace to amma Hajiyar Mu ita *"Sofee* "mijinta ya amince taci gabada karatu ne?...tace munyi maganar "dashi kuma ya amince, dasauri yace ah! to ai shikenan, insha'allahu kafin kudawo angama komai saidai kawai su fara zuwa school din KO?... ya kareshe fadi fuskar shi dauke da fara'a, tace to shikenan yayi kyau tafadi tareda tashi tana cewa bari na iske "Abban naku akwai maganar da zamuyi dashi yace to, yana ganin tanufi falon kasa yai sauri yatashi yanufi dakin ta. Yana shiga yarufe kofar fuskar shi dauke da fara'a tsaye yayi yana me karama *Deeya* kallo kwance take akan faffadan gadon Hajiya ahankali yake sand'ar tafiya zuwa gurin ta, _Nikam nace Kai *BB* meye nayin sand'a kuma?.. ๐Ÿ˜‚kaida matar ka ko dai kana tsoron rigimar *Leemar* taka ne?????_๐Ÿคฃ. Tsaye yayi agaban gadon yana kare mata kallo kwanceta ke rigingine ma'ana tana kallon sili, tayi filo da dukka hannun wanta biyu hakan ne yaba shafaffen cikinta damar sake shafewa wanda yake kullun ashefe kamar wacce bata cin abinci, yayinda dukiyar fulanin ta sukai kamar xasu fasa rigarta, barci takeyi saidai da alama beyi nisa sosai ba zaka fahimci hakanan ne ta yadda takeyi tana juya kanta ahankali. *Habeeb* kam ahankali ya hau gadon zama yayi agefen ta tareda sa hannun sa dukka biyu ya tallabe fuskaskar sa yana kallon ta, zuciyar shi cike da zallar kaunar ta wanda besan iyakarsa ba, "Ahankali yakai hannun sa kan shafaffen cikin ta yana shafawa sannu ahankali har yakai saman dukiyar fulanin ta, aikam take yarikice yayinda natsuwar sa take kokarin kufce masa. *Deeya* kam cikin barcin ta da beyi nisa bataji kamshin daddan turaren sa, dasauri ta bude ido dai-dai lokacin dayake kokari tura hannu shi Cikin rigar ta,๐Ÿ˜‚ Ido tazaro cike da tsoro ta bige hannun shi tareda mikewa zumbur zata sauka daga kan gado, dasauri yajawota tafado masa ta bayanta yayinda yasa dukkan hannu wansa biyu yaima ta kyakkyawan runguma afaffad'en kirjin sa tareda sauke ajiyar zuciya me karfi. Cikin rawar murya yace Kai! *Leemah ta* nazo ne famu yi sallama shine zaki gudu ummh?... Bata bashi amsa ba saidai jikin ta dake ta faman rawa yayinda tafara mutsu-mutsu kwatar kanta, amma takasa cike da shagwaba tace nika kyaleni kaji KO?...idon sa lumshe yana murmushi tareda shakar daddad'en kamshin turaren ta yace um-umhhh! *Leemah ta* kibarni mana naji kamshin jikin nan naki me dadi, ummh! yafadi yana tura kanshi ta bayan wuyan ta wanda lallausan suma ke kwance luf-luf. *Deeya* kam takasa kwance kanta kamar yadda taso saida kuma takasa hakan, murmushi naga tayi wanda bansan meta tunaba saida naga tadago ta kalli santalelen hannun sa me kwance da lallausan suma luf-luf, bakin ta naga takai. _Dasauri nace Kai!๐Ÿ˜ณ *Leemah* me zakiyi_?.. Lafiyayyan cizo tayi masa wanda yasashi sakin ta bashiri tareda fadin auchhhhh!, dasauri ta sauka saman gadon tana yimasa gwalo, dariya yayi tareda yarfe hannun yace Kai! *Leemah ta* cizo nafa kikayi, tace "eh din anciza ba nace ka kyaleni ba kakiya shiyasa ni kuma na cije ka eheee! ta kareshe fadi tareda murguda masa baki sannan ta bude kofa tafita da gudu. Murmushi yayi tareda girgiza Kai! yace *Leemah ta* kenan, sannan yasauko yafito bai ganta ba bai kuma iske kowa afalon kasa ba, don haka sai kawai yanufi part din sa ba tareda bata lokaci ba yadauki abinda yake bukata yafito, direba yabude masa mota yashiga saida suka biya asibiti gurin *Harees* sukai maganar da zasuyi sannan driver yakaisa airport yahau jirgi sai Abuja. *_Abuja_* ******** Koda *Habeeb* ya'isa *Jana* tanayi masa sannun bai amsa ba asalima ko kallon ta baiyi ba, Lili yadauka yana me sumbatar ta agoshi tace Daddy na where is my Aunty *"Deeya?..* murmushi yayi tareda sa hannun yaja hancinta yace tana gurin me allura ido tazaro sai kuma ta tab'e baki tace Daddy yoche jata dawo?..yace very soon tareda sauke ta yana cewa lilin Daddy bari naje nayi wanka kinji?.. tace to yanufi daki ba tareda yabi ta kan *Jana* ba. **** Sannu ahankali rayuwa tamike yanzu kam duk sati sai *Habeeb* yaje Bauchi kasan cewar tuni sun *Deeya* sun dad'e da tsufa asaudiya, yayinda *Habeeb* yafita har kar *Jana* kwata-kwata baya shiga sha'aninta harda Junior gaisu warsu kawai yake amsawa, yayinda yamai da hankalin ga aikin sa tareda ruko Da ibadar sa dakuma kama addu'o'i sosai, wanda yake ganin sakaci da'ita neyasa komai yafaru abaya, Wanda yanzun kam baya fatan hakan yasake *FARUWA* nan gaba yayida kullum safiya jiyake kamar ana Kara masa so da kaunar *Leemah* acikin zuciyar shi tareda wani irin azababben sha'awarta wanda yakeji kamar zai masa illa don haka nema yake yawan yi azumi, domin yana rage kaifin sha'awar Dan adam saidai kuma da yasha ruwa sai yaji yana bukatar mace a tareda shi, saidai kuma yayi alkawari bazaije ga *Jana* ba har saita horu abisa laifin datai masa. "Aikam tana horuwa domin ita awannan fagen batada hakuri don haka batada aiki sai kallon fina-finan banza awayarta, wanda aganin ta suneke rage mata sha'awar ta, *Habeeb* kam baima san ta nayi ba tunda idan yaje aiki yadawo baya kulata abokirar firar sa lili maman shi, "Wanda hakan yana matukar damun *Jana* don hakane ma duk abubuwa suka jagule mata gara shinjin wani gamsasshen bayani daga gurin Shafa, agame da aikin datasa ayimata shiyasa damuwa yai mata yawa duk tarame ga rashin cin isasshen abinci me kyau tunda yanzu bame aiki, ita kuma bata iyaba shiyasa ko tayi bata iyaci, ranan nanma datayi Lili taci saita furzar tareda sakin kuka tace ke! Aunty *Jana* tullun bati iya abunci ba kuma bajan kalacin abuncin kiba tunda babu dadi aikam ranan lili taci duka gurinta. Da *Habeeb* yadawo Lili tafada masa ranshi bace ya'iske *Jana* yaimata fada kaca-kaca, ya kuma ce karta sake dukan lilin tunda aiba karya tayi mata ba aibata iya abincin ba, Shikenan tunda ga ranan Lili tadai cin abinci saidai *Habeeb* yayo masu take away suci idan sun rage sannan su *Jana* suci wanda itasam ba'isar ta yake ba, lol alhakin my sweet *Deeya* ne. *_Bauchi_* ******* "Ayau alhamis kuma yau ne su *Deeya* zasu dawo daga ummara da sukaje, Da misali karfe 11:30pm jirgi su yasauka *Harees* ne da *Hafeez* da kuma *Feeya* sukaje dauko su, da d'an gudu *Feeya* taje suka rungume juna itada *Deeya* suna murnan ganin junan su, Cikin dan tsawa *Harees* yace stop it my precious. Baki ta turo tareda cewa to ai my sweet *Deeya* nace tadawo ba dole nayi murnan ganin ta ba, yace to ai nasani amma aisai kiyi ahankali tunda kinsan bake kadai bace, *Hafeez* kam harara ya watsama su tareda cewa waiku bakusan kullum girma kuke ba amma sai kuyi tayi abu irin na kananan yara mtww yai tsaki tareda cewa ai sai ku wuce mutafi ko, baki suka turo batare da sun ce komai ba, Hajiya kam tana gefe tsaye sai Murmushi take. Kasan cewar babbar mota sukaje da'ita dan haka gaba dayansu ta dauke su Hajiyata can sit din baya, su *Deeya* kuma suna sit din tsakiya yayida *Hafeez* ke tuki *Harees* kuma yana gefen shi, "Ahankali *Deeya* da *Feeya* suke fira inda *Feeya* keta yaba kyanda *Deeya* takara, tace ai kema kinyi kyau unborn yakara maki kyau sosai murmushi *Feeya* tayi tareda cewa albishirin ki?.. *Deeya* tace goro fari kalkal, tace angama komai ranan Monday zamu fara zuwa school inda zaki karanta Law dinki nikuma zan karanta medicine Dina, cike da farin ciki *Deeya* tace da gaske?.. tace Allah Da mana bari sai kun dawo nafada maki, tace kai! amma naji dadi shikenan burinmu zaya cika tace insha'allahu, kuma Hmm *Habeeb* ya siya mana mota ke daya ni daya taki fara tawa baka yace muringa zuwa school, baki *Deeya* ta tab'e tareda cewa mungode, sannan *Feeya* ta cigaba da cewa shi kuma Hmm *Harees* yabude mana account tareda sama na kudi dubu dari biyu da hamci hamci, yace" muyi hidimar school dariya tayi tareda cewa Kai! amma mungode sosai. Cikin kwantar da murya *Feeya* tace my sweet *Deeya* yanzu dai komai yawuce zaki koma dakin kiko?.. Dasauri *Deeya* tace wa?.. ni tab! tafadi tareda pointing din kanta, tareda cewa aini babu inda zan koma cike da mamaki *Feeya* tace... Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 4โƒฃ1โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Saboda me bazaki koma ba?..tace saboda ban manta da'abun da akai mun ba, tace haba sweet *Deeya* ki manta mana. Dasauri tace bafa zan manta sweet *Feeya,* ke bakisan irin wahalar dana shaba ne shiyasa, tace to kiyi hakuri kiyafe masa" kinga fa ba'a cikin hayyacin "sa yayi maki haka ba, tace hmm to nayafe masa" saida bazan koma ba don idan nakoma bansan irin bakar wahalan da matar sa zata sake bani ba. *Feeya* tace ai insha'allahu hakan ma bazaya sake faruwa ba, tace hmm my sweet *Feeya* kenan kedai kawai muyi hakuri da juna yabani takarda na shiyafi alkhairi, tace aganin ki hakan shine mafi alkhar agare ki?.. tace "eh, *Feeya* kam jitayi ranta yadan sosu har tana fadi aranta wato hakan yana nufi *Deeya* batason Hmm *Habeeb* kenan KO?.. Cikin d'an bacin rai tace OK" shikenan dama can bakison shi don haka kike so yasake ki, amma inda kina son shi ai da duk abinda yaimai kin zaki hakura, itama Cike da bacin rai tace "eh aishima baya sona Da sauri tace karya ne kinsani sarar "yana *SONKI*, tace ah! sosai ma kuwa shiyasa ma yace" yatsaneni baya son ganina saboda ganina akusa dashi yanasa ransa yana baci, wanda hakan ne yaba matar shi damar mayar Dani baiwa yar'aiki wannan kam duk cikin so ne KO?.. tace duk abinda zakice kice saidai ki sani ke baki isa ki goge kaddarar kiba balle ki goge tawani KO?.. tace to dama aibabu wani dan "adam din dayake Da matsayin yin hakan. tace to Alhamdulillahi tunda kinsan da hakan kuma Hmm *Habeeb* zaya sake ki kamar yadda kike bukata, kinga saiki jeki auri wanda kikeso wanda kike ganin yafi maki "Hmm *Habeeb* din. har zata bata amsa sai Hmm *Hafeez* yadaka masu tsawa, kasan cewar duk abinda suke ba wanda ya tanka masu sai yanzu, cikin fada yaxe wai meye haka kukeyi ne?..Dai-dai lokacin da yake shiga harabar gidan, Hmm *Harees* yace ah! ka kyale su mana badai yau mun gansu arana ba, tsaki yayi tareda cewa shirman mu yara kawai. Dai-dai lokacin da yai parking tareda kashe motar Cikin bacin rai *Feeya* tafito tanufi part din su, yayinda itama *Deeya* tafito ranta bace tanufi part dinsu. Hajiya kam tunda suke abinsu batace masu komai ba har suka isa gida, batace kala ba asalima dasuka fito daga motar binsu tayida kallo, Karo na farko kenan dataga fada su murmushi tayi tareda fitowa tanufi part dinta tana cewa ai wannan fadan naku babu inda za yaje tunda nasan daya baya iyayi saida daya, *Harees* dake biye da'ita jaye da akwatan shi da *Hafeez* yace Hajiyar Mu maganar ki haka take. Zaune suke suna fira Baffa da lnna sai ganin *Deeya* sukai tashiga da sallama, cike da farin cikin Baffa ya amsa tareda cewa a ah" barka da zuwa *KYAUTAR ALLAH* Mu, wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar *Deeya* saka makon gani iyayenta don haka tuni ta manta da bacin ran da tashiga dashi. Dasauri ta'isa gurin su fuskarta dauke da fara'a tace yauwa Baffa na tafadi tana zama tsakanin su, tareda kama hannun lnna sannan tadora kanta akafadar Baffa sai kuma tasauke ajiyar zuciya, sannan tace lnna ta da Baffa na nayi kewar ku sosai murmushi sukayi a lokaci guda, Baffa yace Allah sarki *KYAUTAR* Mu, muma munyi kewarki sosai dafatan kun dawo lafiya ya ibada?..tace Alhamdulillahi Baffa na munsa me kula lafiya?.. yace lafiya lau, lnna tace ita "Hajiyar ta ku tana can part dinta ko?.. tace "eh, tace to bari naje na gaida ita" tafadi tana tashi, Da sauri *Deeya* tadago tareda sake rike hannun lnna sosai tace kai! lnna ta ki tsaya mana nasake ganin ki, hararan ta lnna tayi tace to kin dawo ko zaki fara yiwa mutane shirme ba?.. Murmushi Baffa yayi tareda cewa nima bari na tashi muje tare, dasauri tace ayya Baffan akai ma?..yace "eh ai yanzu zamu dawo tace to bari naje nayi wanka kafin ku dawo yace to sannan suka fita ita kuma tashiga dakin su. Bayan tayi wanka tafito lokacin su lnna sun dawo shiryawa tayi cikin Riga da wando na fakista pink color, tayi rolling da gyale kayan saita feshe jikinta da dadd'an turaruka masu asalin kamshi tayi kyau sosai sannan tafito falo, Zama tayi tsaki yar su suka fara fira wanda sun dauki tsawon a lokaci sannan, ta tashi tanufi part din Hajiya tana shigata tambaye Hajiya ina sweet *Feeya* dinta, murmushi tayi tareda cewa ta tafi part dinsu akwati guda *Deeya* tadauka cikin akwan da suka zo dashi, tafita tanufi part dinsu *Feeya.* Koda tashiga kwance ta'iske *Feeya* kan cinyar *Harees* akwatin ta'ajiye gaban ta tareda cewa ga tsare ba nan, cikin hade fuska tace malama dauki abinki banaso itama fuska a hada tace aiba naki bane na unborn child, Dasauri ta tashi tana fadin kai! kai!! kai;!!! yanzu kina nufin duk wannan kayan ba nawa ciki?.. tace "eh, tace tab aiko baki isaba tace to maidani saudiya mana, tace ai Zaki koma ne yanzu kuma tsaki *Deeya* tayi tareda cewa Malama ki tashi muje sama akwai maganar dana keso muyi, tace bazan tashi ba dariyar da *Harees* yake kunshe wace tafito saida yayi sosai domin salon fadan nasu dariya ya bashi, sosai Sannan yatashi yana cewa nikam kunga tafiya ta zama *Deeya* tayi tace kawo kun nan ki kinji, Kunnan ta mika mata rad'a tayi mata dariya naga sunyi tareda tafawa *Feeya* tace au haka ne??. tace "eh tace to shikenan daga nan kuma sai suka fara kamar basu ba. *_Abuja_* ******** *Jana* kam da wahala ya' isheta dole tanemi sulhu da *Habeeb* wanda shima yaso sulhun saboda yana a matukar bukace, saidai benuna mata ba har saida tanema dakanta sannan ya hakura amma saidai yaimata gargadin karta sake sama *"Leemarsa* beraye tunda dai bata so, Sannan yace mata koda sun koma Bauchi karta sake sata aiki tunda ba yar aiki bace kamar yadda take takama ita matar sace, to itama *"Leemah* matarsa ce so ta kula tace to sannan yace tashirya gobe zasu tafi bauchi harda yara tunda anyi masu hutu school cike da farin ciki tace to, aranta tanajin dadi zata iske adonta. Aranan kuma itada *Habeeb* suka dinke koda yaneme ta bata tsaya bata lokaci ba tabashi hadin kai, ba tareda ta bukaci kudi ba kamar yadda tasa ba. ***** Washegari Jumma'a ana'idar da sallah *Habeeb* yakwashi iyalinsa suka taho Bauchi, kasan cewar amota sukayi tafiyar shiyasa duk yajiya yaji saboda yadad'e beyi tafiya a mota ba. bayan yai wanka saita shirya cikin kana nan ka riga T-shirt fari da wando navy blue yafeshe jikinsa da turaruka masu, kamshi yinwa yake ki sosai saida zuciyar shi cike takeda son ganin *Leemarsa* don haka koda yafito part din Hajiya yanufa a tunanin sa *Deeyar* tana can, zaune ya'iske ita gaida tayayi tareda yima barka da dawowa, shuru yayi yanason ya tambayi *Leemah* amma kuma yana jin nauyi, ahankali yace Hajiya *"Leemah* fa?.. ba tace tana part dinsu yace to tareda tashi yace zan shiga part din Dan'uwa tace to tareda tashi tanufi sama sannan shima yafita. Har yanufi hanyar fita zuwa part din *Harees* kamar yadda yace sai kuma yajuyo tareda fadin no I want to see my *"Leemah* first, yafadi tareda yin murmushi sannan yanufi part din sun *Deeya* Cak! ya tsaya a bakin kofar saka makon abinda kunnan sa yajiyo masa, wanda yasashi jin mugun faduwar gaba, kunnu wan shine suka cigaba da jiyo masa kalmar da yatsani jinta wato *SAKIN* sakin mana *Leemarsa.* Muryar *Deeya* CE ke cewa Baffa da lnna ita dai su sa Hmm *Habeeb* yasake ta tunda baya *SONTA,* Dasauri yafada falon ba tareda sallama ba, gabanta ne yafadi saka makon gani *Habeeb* din bazato balle tsanmani shikam tsura mata kyawawan idon sa yayi masu firgita ta, wanda kana kallon su zaka hango zallar kaunar ta acikin su cikin wata iri yar murya yace *Leemah* me ki kace?.. bata bashi amsa ba saidai kawai ta bita gefen sa tafita, dasauri yabita yana kiranta amma bata amsa ba balle yasa ran zata juyo har suka shiga part din Hajiya tana kokarin hawa upstairs din, ya fisgota cikin bacin rai yace *Leemah* wai meye haka me kike nufi dani ne?.. daure fuska tayi cike da faduwar gaba hade da wani irin tsoro tace mlm me nake nufi dakai" kodai me kake nufi dani, aure ne nace banayi tunda ba dole to ka sak....wani lafiyayyan *MARI* *Habeeb* yashara mata wanda yasa takasa karasa wa, dasauri tasa hannun ta dafe kumatun ta yayinda hawaye suka fara anbaliya akan kyakkyawa fuskarta, ido yarintse tareda tura hannun wan shi cikin lallausan suman kamshi sai kuma yabude aikam tuni sun kad'a sunyi jajir, wanda ganin hakan yasa gabanta yai mummunan faduwa yayinda wani irin tsoro yadarsu acikin zuciyar ta, tuni taga yarikid'e yakoma mata asalin Hmm *Habeeb* din da tasani na can baya wanda tarada masa mlm zalumun, Cikin bacin rai yanuna ta da yatsa tareda cewa Keeeee! ni ki kefa dama wannan maganar?.. don kinga *ZUCIYATA* ta mutu akan *SONKI* shine zakiringa gayamun maganar da duk ki kaga dama?.. To bari kijida ga yau bazan sake binki ba kuma bazan sake kiba don haka sai kiyi duk abunda zakiyi kinji ko?..sannan yajuya zaya fita zuciyarsa tana wani irin kuna, saida me yana kaiwa bakin kofa sai wani irin dubu yana mamaye maganin sa, wanda hakan ne yasashi yayi baya luuuuu! sai kuma yafadi kasa jikake ribbbbb!, Cikin wani irin firgita *Deeya* tanufi gurin shi ta zube akasa tareda kama hannun shi cikin tashin hankali tace wayyo Allah na Hmm *Habeeb* meyasa me ka?.. murmushin karfin hali yayi tareda sake damke hannun sa cikin nata, kasan cewar baya ganin ta saidai muryar ta kawai daya keji cikin wata wahalalliyar murya yace *Leemah ta* mutun zanyi *SONKI* zaiyi ajalina, Cikin tsanani tashin da bata taba shiga irinsa tunda take, tace no Hmm *Habeeb* karka mutu wlhy ina *SONKA* ka na yadda zan koma kaji?..murmushi yayi har zaya sakeyin magana sai yakasa, saboda numfashi sa daya tsaya cak! wanda yasashi sakin hannun ta, wani irin Kara tasaki tareda fadawa jikin sa sumammiya, Dai-dai lokacin da Hajiya take sauko wa kasan cewar taji hayaniya abinda ta gani ne yasata jin mugun faduwar gaba, cikin tsananin tashin hankali tace... *_Gaskiya comments dinku yayi Low so kukara ko nima typing dina yai Low yaseeeee_*๐Ÿ˜‰ Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [7/4, 12:23 PM] My

Chapter 17 of 42