yace to Lilin Daddy Junior yace Daddy sorry yace yauwa, nan dai yan'uwa sukai ta gaida shi daya bayan daya yana amsawa.
*Jana* kam gaba daya hankalin ta yana kansu *Deeya* itada *Habeeb,* sai kallon su take me cikeda tsana jitake kamar taje ta shak'e *Deeya* don bakin cikin ganin ta zaune kusada *Habeeb.*
*_Bayan kwana biyu_*
******
"Ayau lahadi kuma ayaune *Harees* ya sallami *Habeeb* daga asibiti kasan cewar tuni yaji sauki sosai tamkar bashi ba har da yar ki ba yayi, acikin kwana biyu nan kuma wani irin shakuwa ce sosai tashiga tsanani sa *Deeya* da,
yayinda itakuma *Jana* aduk lokacin data shirya tafito daga gida dasaunan zuwa asibiti gaida *Habeeb* saita fara zuwa gurin *Ado tukun sun gama bad'alar su tukun sannan tanufi asibitin.
*_Allah kashirya matan auren dasuke aikata ZINA da AUREN SU ameen._*
Gaba daya familiy sun hadu a babban falon part din Abba kasan cewar yaune ranan dasu ke family meeting, bayan Baffa yabude taro da addu'a kamar yadda aka saba sai Abba yafara magana indaya yanke hukunci cewa nan da sati biyu *Deeya* zata koma dakinta lokacin *Habeeb* yasake samun sauki sosai, kowa yayi fari ciki dajin haka musamman *Habeeb* da yaji kamar yajawo sati biyun kusa bayan an gama sai aka tambayi kowa idan yanada magana yayi wayan da suke dashi sunyi sannan akayi addu'a kowa yatashi yafita.
*Habeeb* da *Harees* ne tsaye a harabar gidan inda *Harees* yake cewa da *Habeeb* Dan'uwa amma dai ba gobe zaka koma bako?..yace "a ah saidai jibi insha'allahu, yace to Allah yakaimu yace ameen nan dai suka da'n tattauna akan al'amuran yauda kullum sanna kowa yanufi part dinsa.
*Washegari Yakama Monday*
*******
Kuma ayaune su *Deeya* zasu fara zuwa school da misalin karfe 9:00AM, *Deeya* CE tafito cikin shirin tana zuwa school din sanye take da riga da siket na wani tsadadden less blue yanada zanan flowers fari, dinki rigar have gown ne yadan kamata ta sama siket din kuma me tsaga ta baya ne saidai kuma ba ko wane zaya game akwai tsaga ta bayan ba, ya kuma fito mata da sherp dinta sosai.
Sannan tasa wani tsadaddan passion din sarka da dan kun'ne da zobe da awarwaro masu asalin kyau duk farare saidai suna da ratsin blue, bayan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi sannan ta kashe daurin dankwali saita dauko gyale fari me flowers blue, tayafa sai tasa takalmi sannan ta rataya jaka fari gaskiya tayi kyau sosai, mirror ta kalla sai tayi dariya domin ta san tahadu matuka Cikin cool voice dinta tace wannan kwalliyar ta Hmm *Habeeb* dina ce.
Sannan tafito zaune ta iske Baffa da lnna (kasan cewa nan part dinta kwana), cikin ladabi tareda tsantsar kaunar iyayan nata ta zauna tsaki yar su kamar yadda tasa ba, cike da shagwaba tace lnna ta Baffa na, na fito zan tafi kuyi mun addu'a murmushi sukayi "a lokaci daya sannan Baffa yace to *KYAUTARMU* Bismillah! daga hannu.
Nan ta daga hannu yai ta kwarara addu'a suna amsawa da ameen itada lnna har yagama sannan yace to Allah yabada sa'a amai da hankali akan abunda a kajeyi, tace to Baffa na lnna tace to lallai dai kam kar aje aita shiriri ta ba, Baffa yace sannan kuma mutun yakula sosai akwai aure akan shi aure kuma ba'abin wasa bane, don kar mutun yaje yai wasa dashi cikin sanyi jiki tace to sannan tashi suka ce mata a dawo lafiya tace Allah yasa tareda fita.
Ta fitowa suna haduwa da *Hafeez* kallon ta yayi tareda cewa, "A ah amarya agidan Hon *BB Smart* anfito kenan?.. tace "eh kuma uwargida ba, dariya yayi yace kai! *Deeyar-Feeya* duk ke kad'ai?.. tace "eh idan naso kaina dayawa ba, zan'iya fadar haka tunda saida akafara daura nawa auren sannan aka daura "nata amma kuma bazan fadi haka ba, don haka nabar "mata sarautar "uwargidan na dauki ta amaryar, murmushi *Hafeez* yayi yace haka ne kin kyauta, tareda nufar part din su lnna yana cewa to adawo lafiya ayi karatu sosai, tace to tareda nufar part din Hajiya.
Bayan ta gaida Hajiya da Abba sunyi mata fatan alkhairi sannan tafito, tashiga part din *Habeeb* da sallamar ta tashiga falon *Jana* tana zaune afalon amma bata amsa ba, hakan bai damu *Deeya* ba domin ta sannan itadin ba ma'abuciya amsa sallama bace, don haka sai tace Aunty *Jana* ina kwana?..ko kallon *Deeya* ba tayiba balle ta amsa gaisuwar, hakan nan ne yasa *Deeya* tabe baki,
tareda bin hanyar dakin *"Habeeb* cikin nutsuwa take taku hankali kwance babu abinda yadame ta, saime cikin wani irin tsawa *Jana* tace karki kuskura kishigar mun dakin miji, cike da mamaki *Deeya* tajuyo ta kalle ta sannan tace...
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenat๐น
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
4โฃ5โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
Kamar ya kar in shiga maki dakin miji?.. cike da isa tace kamar yadda ki kaji nafada, murmushi *Deeya* tayi tareda cewa "Aunty *Jana* kenan haka kam kika fada, saidai kuma yakama ta bakin naki yasaba da fadin mijin Mu,
dasauri *Jana* tace to bazan ce mijin mu din ba kinji ko?? mijina zan ce, domin dai kowa yasan an daura mana aure dashi don haka ko "shidin mijina ne nikad'ai bada wata banza can ba wacc.....
Da sauri *Deeya* ta katseta da cewa niba banza bace, kamar yadda aka daura maki aure dashi" to nima haka aka daura mun aure "dashi, don haka kinga yanzu shidin Mijin mace biyu kafin zuwa gaba yakara biyu kinga shi kenan mun zama mu hudu, kamar yadda Allah yafada namiji daya Mijin mace hudu na eheee! ta karashe fadi tareda nuna yatsunta guda hudu har da murguda mata baki,
Cikin macifa *Jana* tace karya kike wlhy babu macen data isa tasake tashigo wa gidan nan, ko kema idan naga dama bazaki zauna acikin saba wlhy, domin *"BB* mijina ne nikad'ai keda shi.
dasauri *Deeya* tace wlhy ke baki isa ki hanani shigowa gidan nan ba tunda ba gidan ki bane, tace karya ne gidana ne tunda gidan "mijina ne, *Deeya* tace sanma kar nima gidana ne tunda gidan mijina ne so ke baki isaki hanani shaga ba wlhy ta kareshe fadi tareda juyawa zata shiga dakin *Habeeb* din.
Dasauri *Jana* tajawo hannun ta tareda cewa bakifa isaba yarinya, ina zaune kishigo mun gida kice zaki shigar mun har turakar miji, cike da bacin rai tareda tsiwa *Deeya* tace dallah malama sakarmun hannu kinji ko, kuma wlhy sai nashiga tace bakuma zaki shiga ba aikam nan rikici tabarke tsakanin su.
*Habeeb* yana ciki yana aikin sa a computer kasan cewar tunda yadawo sallar abuba yai karatun alqu'an me girma saida misalin karfe 8:00 am sannan yatashi, yahau computer yarafa gudanar Da wasu ayyuka,
Yana cikin aikin ne sai yaji cikin sa yana kuuuuuuu! alamar yinwa tsake yayi mtwww!, tareda tashi yaje ya had'owa kansa coffee, wanda yasan bazai masa maganin yinwar dayake jiba, amma yanada tabbacin zaya rage masa kugin da cikin sake _before_ gari yawaye yasa masa abu me nauyi,
"Ahankali yake aiki gefi-gefi yana daukar coffee yakurb'a don haka baisan wainar da ake toyawa abbban falon ba.
Sama-sama yakejiyo hayaniya sannu ahankali hayaniyar takeyi yawa, hakan yasa shi mikewa tareda jan tsaki mtww! alamar hayaniyar tada meshi, sanye yake da jallabiya _ash color_ me garen hannu cikin nutsuwa yake taku yanufo falon.
Mamaki ne yaka masa gani *Jana* rike da gyalen *Deeya,* cikin had'e fuska yace da *Jana* lafiya kika rike mata gyale?... dasauri suka juyo gaba dayan su, domin basuji takun saba saida saukar maganar sukaji,
Cikin masifa tace haka kai kawai tashigo zata shiga dakinka ba tareda tace kun komai ba, cike da mamaki *Deeya* tace kai! Aunty *Jana* kiji tsoron Allah saida fanayi mata sallama sannan na gaida ita amma duk bata amsa ba saida taga zan shiga dakin ka wai bazan shiga ba ni kuma nace sai nashiga, shine tarike mun gyale pls kace tasa kar mu gyale gaskiya banason haka.
Cikin had'e fuska yace sakar mata gyale ta, tace ah! bafazan sake taba ta shigar mun har turakar miji wannan ma ai raini ne da rashin kunya, cikin tsawa yace nace ki sakar mata gyalen ko?..
dasauri tasaki gyalen tareda kallon shi cike da tsoro, cikin bacin rai yace yadda kike takama ke" matata ce itama matata ce, kinga bakida _right_ din dazaki hanata shiga dakina kamar yadda itama bata da damatar hanaki shiga, so banason fitina kinji ko?.. har zatayi magana ya daga mata hannu alamar baya son jikomai, *Deeya* kam tuni tashige dakin.
Yayinda *Habeeb* yabi bayan ta dasauri *Jana* tace indai akaci amanata banyafe ba, juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallon ranshi "A bace yace amanar ki din me zanci *Jana*?...tace to me zaku shiga kuyi adaki yanzu eyeee?..yace idan muka shiga daki ni dake me mukeyi?...
tace shiyasa nace idan akaci amanata ban yafeba eheee! idan gaskiya ne abari har tadawo cikin gidan araba kwana mana sannan tafara shiga dakin, yace *Leemah* fa matata ce KO" nayi wani abuda ita ba haram bane kuma ni *Habeeb* bazan taba cin amanar ki ba, sannan yashige dakin yabarta nan tsaye zuciyarta kamar zata fitowa je don bakin ciki da tsabar kishi.
Tsaye *Habeeb* ya'is *Deeya* zuciyar ta cike da jin haushi rike mata gyale da *Jana* tayi, musamman ma dataga har yafara _squeeze,_ hakan ne yasa take tafaman tsaki tareda kokari warwareshi,
hannun ta
*Habeeb* Yakama suka shiga bedroom dinsa tareda rufe kofar, bakin gado ya zauna sannan ya zaunar da'ita akan cinyar sa, cikin sanyi murya yace ya'akayi ne *Leemah* ta?..
baki ta turo cike da jin haushi had'e da yanayin tana shagwaba tace gaskiya Hmm *Habeeb* ni banason abunda "Aunty *Jana* take mun tun dazu fa nashigo na fad'a maka zantafi school shine tarike mun gyale kallifa haryayi _squeeze_ wai ita bazan shigar mata dakin mijiba, to ainima matar kace ko?...ta kareshe maganar cike da kuruciya.
Murmushi yayi yana Shafa bayan ta da hannu sa daya, dayan kuma yana shafa kyakkyawa fuskarta wani irin *SONTA* yake ratsa shi, tunani yake aransa shi bai masan iya adadin yawan sonda yake mata ba, cikin cool voice dinta Ta sake cewa Hmm *Habeeb* nima ai matar kace ko?..
Cikin
murmushi yace purely wife ma kuwa, tace a to amma "ita sai tayi ta cewa" ita kadai ce matarka.
Yace kyaleta *Leemah* ta ke ce mace mafi soyuwa acikin zuciyata, inason ki sosai irin wanda bansan iyakarsa ba, cikin sanyin jiki tace Hmm *Habeeb* nima fa inason ka irin sosai sosai din nan fa ta kareshe fadi tareda sakin lallausan murmushi, shima murmushi yayi yace to nagode sosai *Leemah* ta yanzu me kika kawo mun?..
tace gaisuwa in kuma nuna maka kwalliya ta sannan kayi mun addu'a yau zan fara zuwa school, tafadi tana me rufe fuska cike da jin kunya, wata irin dariya yasaki me cike da zallar farin ciki tareda cewa Wowww! duk ni kadai *Leemah* ta?..tace "eh yace kai amma naji dadi na kuma gode, to yanzu mu gaisa "Ahankali tace Ina kwana?..
dasauri yace no! no!! no!!! *Leemah* ta bana son wannan gaisuwar, ido tazaro cike da dan tsoro tace saboda me?.. yace saboda irin wannan nakeso yafadi tareda tallabe fuskarta ya had'e bakin su guri daya, hakan neyasa tayi saurin rufe ido.
Kusan ten minutes *Habeeb* yadauka yana kiss *Deeya* sannan yacire bakin sa daga nata, yana sauke numfashi fuskar sa daukeda an nashu wa cikin kasalalliyar murya yace _pls open u eyes kinji_ *Leemah* ta?.. _and show me u_ kwalliyar mana nagani yafadi yana dariya,
itama dariyar tayi tareda bude idon ahankali cike da kunya ta sauka daga kan cinyar sa tareda yaye gyalen data yafa, ahankali yamike yanayi mata wani irin kallo me cike da so da kauna, wani irin kyau yaga tayi masa musamman kirjinta har yana fadi aran sa yanzu fa haka zataje school din nan maza suyita kallon ta ko?..
aikam take yaji wani irin azababben kishi yaturnike shi wanda yasa take annurin fuskarsa ya chanja daga fara'a zuwa bacin rai, wanda yasa gaban ta faduwa amma haka ta turo baki cike da shagwaba tace Hmm *Habeeb* banyi kyau ba ko?.. Cike da mamaki yace...
*_Barka mu da Jumma'a_*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenat๐น
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
4โฃ6โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
Injiwa yace" haka?.. tace to aibanji kace komai ba ne, dasauri yana karasa gurinta tareda yajowo ta ya rungumeta, ajikinsa sosai har yana sauke ajiyar zuciya,
Cikin wata rikitatciyar murya yace *Leemah* ta kinyi *KYAU!* kinyi *KYAU!!* kinyi *KYAU!!!* sosai irin wanda baki bazaya iya fadin a dadin sa ba, kuma dama aike din me *KYAUCE* ko bakyi kwalliya ba, kawai dai naji wani irin kishin kine ya turnikeni ganin zakije school maza suyi ta kallon ki, don haka nema na yanke shawar kawai afasa karatun nan.
Dasauri tadago Kai ta kalle shi sai kuma ta kwabe fuska kamar zatayi kuka, cike da shagwaba tace "ah! Hmm *Habeeb* pls don't say that?.. kuma fa kasan _I want to be a Lawyer_, murmushi yayi tareda da shafa kyakkyawar fuskarta me cike da kwarjini da haiba yace l already know my *Leemah* kar kidamu u want to be a lawyer insha'allah kinji KO?.. *Leemah* ta.
Lallausan murmushi tayi tareda cewa thank you yace yauwa saidai gaskiya banason ki kula kowa kawai kiyi abinda yakai ki kinji KO?..,tace to aiba zan kula kowa ba sai my sweet *"Feeya* KO?..yace "eh haka nake so *Leemah* ta meye acikin handbag din, yafadi yana dariya tareda kokarin bude jakar.
"Abinda yagani ne yasa shi yin murmushi tareda cewa hmmm! *Leemah* ta kenan shazuma me sarkin shan zak'i yanzu duk wannan tarkace zak'in Ina zaki zuba su?...dariya tayi tareda cewa ciki na mana, yace Kai! *Leemah* ta yanzu duk zaki shanye wannan kayan zak'in?..tace "eh yace ayya *Leemah* ta basuyi yawa ba kallar sufa _chocolates, sweets, lollipop, bubble gum, and biscuits,_
Cike da shagwaba tace Hmm *Habeeb* baiyi yawa bafa, yace to shikenan amma dai ariga sha ahankali wannan five k fa waya baki?..tace "Baffa yabani had'e fuska yayi tareda cewa meyasa kika tambaye shi?..dasauri tace Lah! banfa tambaye shi ba" dakan shi yabani, yace to karki tambaye shi duk abunda kike so come and ask me zanbaki kinji *Leemah* ta?.. tace to.
Gurin drawer yanufa yabude yadauko bandir din yan dubu-dubu an rubuta fifty thousand ajikin, yar takardan dake nan nad'e da kudin, jakar ta yabude zayasa gani abunda aka rubuta ajikin kudin ne yasata zaro ido cike da tsoro tace Kai! Hmm *Habeeb* me zanyi da fifty K?..murmushi yayi tareda karasa saka kudin cikin jakar, sannan yace ki kashe *Leemah* ki siya duk abunda kike son kinji?..
fuska ta kwabe tareda cewa Hmm *Habeeb* sunyi yawa fa, yace basuyi yawa ba *Leemah* ta yafadi yana me rungumeta tabaya tareda Dora kanshi akan fadarta yana shakar daddaden kamshin turare ta sannan yacigaba da cewa kinga saiki siya hand out da hand books and _ice cream_ dan ban gashi acikin jakar ba ya kareshe fadi tareda yimata kiss akumatu.
Cikin shagwaba tace to amma dai sunyi yawa, irin yadda tayi maganar shima yayi dacewa basuyi yawa ba *Leemah* ta, dariya tayi tace to shikenan nagod....dasauri yaka tseta dacewa shhhhhhh! tareda dora yatsar shi akan labbenta, yace banaso Ina key motar ki koba da ita zaki school din ba?..
dasauri ta rufe ido cike da jin kunya tace Lah! Hmm *Habeeb* yi hakuri na manta naga mota nagod..., kallon dayai matane yasa tayi shuru tana dariya yace _U say it again_ KO?.. Cikin sanyi murya tace to soweey amma dai thanks, tafadi tana dariya tareda kanne masa ido daya shima dariyar yayi yace _for what?..._
tace for komai ma, dariyar yasake yi tareda sa hannu yaja hancin ta yace *Leemah* ta kenan to yanzu Ina key yake?.. tace yana hannun my sweet *"Feeya* yanzu zan kar ba, saidai muntsara bada ita zamu fita yauba data my sweet *Feeya* zamu tafi, sai gobe zamu tafi data wa, yace Ok" twice din Hajiya muje to naraka ki kar kiyi late karfe nawa ne zaku shiga lecture?..ya fadi yana kallon agogon dakin daya nuna 9:35am,
suna tafiya tana cewa karfe 10:30am amma su sweet *"Feeya* sai 10:00am zasu shiga yace Ok" dai-dai lokacin dasuka isa falon.
*Jana* tana ganin sun tamike zumbur tamkar wata kwancen hauka yayida take bin *Deeya* dawani irin mugun kallo jitake kamar taje ta shaketa ta mutu, ba tareda sun kalle taba suka nufi hanyar fita, da karfi *Jana* tace tunda ku kaci amanata banya feba eheee! tabe baki *Habeeb* yayi ba tareda yace komai ba suka fita abinsu.
escorts dinsa suna ganin shi suka ta so suka kawo gaisu hannun yadaga masu, part dinsu *Harees* suka nufa yana cewa *Leemah* ta kodai na hadaku Da escort ne?.. ahankali tajiyo ta kalli escort din dasuke tsaye tamkar gunki suna sanye da black din suit da bakin glass, ita wani lokaci ma tsoro suke vata mutane haka ko dariya basayi baki ta tabe tareda cewa "a ah bama so yace to shikenan.
Suna shiga su kuma su *Feeya* suna fitowa daga part din Hajiyar su *Harees*, da'alama sun shiga gaida su ne.
Dariya *Harees* Da *Habeeb* sukayi alokaci daya ganin kayan da ke jiki *Deeya* shi ke jikin *Feeya,* cikin wasa *Harees* yace au! abun yar anko ne ah! dan'uwa tomu ma muje musa kaya iri daya, murmushi *Habeeb* yayi tareda muka mashi hannun suka gaida *Feeya* ta gaida shi, ita kuma *Deeya* ta gaida *Harees* daga nan suka nufi gurin ajiye motoci.
*Harees* ne yafito da motar bayan yafito yace oya my precious Bismillah!, bayan tashiga ta zauna sai *Habeeb* yabude ma *Deeya* tashiga sannan suka rufe masu kofofin a lokaci daya, *Habeeb* yace Da *Feeya* banda tukin ganganci cikin girmama wa tace to sannan ta tayar suka fita yayinda suke daga wa juna hannu har suka fice daga harabar gidan *Harees* yako part dinsa sannan *Habeeb* shima yafito yanufi part dinsa.
*_Nasan me karatu zaya ce da yaushe su Deeya suka iya mota?..to kun san su da rigima musamman Deeya don haka tuni suka ko ya agurin Hmm Hafeez._*
*_A school_*
*******
Misalin 12:00pm
*Deeya* tafito lecture jikin wata bishiyar mangoro taje ta zauna tana jiran fito war su *Feeya,* wani book take duba wa, bata dade da zama basu *Feeya* suka fito *Deeya* tanufo kasan cewar sunyi dacewa duk wanda yariga fitowa to ga gurin da zaya iske shi Dan'uwa shi, zama *Feeya* tayi kusada ita tareda mika mata wayar ta amsa tayi sai kuma suka cema juna ya lecture?..dariya sukayi sannan kowa yace alhamdulillahi,
game *Deeya* tafara bugawa awayar can kuma sai tace tashi muje mu samu abunda zamuci, don banason baby na ya wahala tafadi tana kai hannunta kan dan cikin *Feeya* da yafara fitowa kadan, murmushi tayi tace to maman baby tashi muje tace ok".
har zasu tashi sai sukaji ance hi _guys_ ahankali su ga daga kai suka kalle shi, wani dan siririn saurayi ne wanda kallo daya zakai ma saka fahimci dan ganyene, *Feeya* tace mlm lafiya?.. yace "eh itane taka wani inason nayi magana da wannan baby ne yafadi yana nuna *Deeya,* dasauri *Feeya* tace to kayi hakuri matar aure Ce ita, yace good ai irin ta nakeso domin sunfi dadi Harka.
Dasauri *Deeya* tace a'uzubillahi!
yayinda taji wani kololon bakin ciki yatokare mata kahon zuci, aikam take hawaye suka fara ambaliya a fuskarta yace ayya baby wallah sonki nake, cikin kuka tace Allah ya'isa tsakanina dakai tunda anfada maka ni matar aure ce kace ai irina ka keso, to ban yafe ma ba mugu kawai kuma sai na fadama Hmm *"Habeeb* mijina takareshe fadi tareda kokari neman layin *Habeeb* din dake cikin wayar *Feeya*.
Saurayi yace Oh! baby ki tsaya mu fahimci juna zan biya maki bukatar ki baby ko baki bani kocici ba kinji?..ko kallon shi *Deeya* batayi bata ta cigaba da kiran layin Cikin sa'a yashiga, *Habeeb* dake zaune ababban falo ya naga nawa da wasu mutane dasu kazo gaishi, sai kawai yaga kiran *Feeya* wanda saida yaji faduwar gaba yace Sofee saida yatsan ke sannan ya kira,
Muryar *Deeya* yaji tana kuka hakan ne yasa shi mikewa Zumbur, tareda cewa *Leemah* ta me yafaru meyasa meki waya taba mun ke?..duk alokaci daya yajero mata wayan nan tambayoyin, cikin kuka tace Hmm *Habeeb* kaga wannan mutumin daga ganina wai shi yana sona ance masa ni matar aure ce, yace"wai ai irina yake so dakarfi yace _what?? am coming right now_ yafadi tareda kashe wayar,
Nan ya sallami mutanen wanda tare suka fita escorts dinsa suna ganin shi suka tashi mota uku suka cika, cikin abinda baifi
30 minutes ba sukai sa school din.
Kiranta yayi ya tambaye ta Ina suke tafada masa saiga su dasauri ta'isa gurin *Habeeb* tana nuna mashi saurayin dake tsaye sanye da wata ko daddiyar riga saida tasha guga da'alama guy din me tsafta ne, sai wani wargajejen wandon shi dayayi as level, gawata hular sa hana sallah daya mayar da gaba baya,
*Habeeb* kam kallon saurayin yayi wanda bai fi ya dauke shi da hannu daya yafed'ar ba, tsaki yayi aikam take yaji wani irin tsanar shi yadarsu azuciyar shi tareda wani azababban kishi, Cikin kuka *Deeya* tace Hmm *Habeeb* shine nan, yace Ok" sannan ya kalli escorts din sa Cikin bacin rai yace...
*_Kuyi hakuri da wannan wlhy waya tace ke dan bani matsala shiyasa typing din yake yin kadan._*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
( Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenart๐น
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
4โฃ7โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
"Me kuka tsaya jira?.. cikin rashin fahimta daya daga cikin su yace _"Sir what are we going to do?.._ Cikin tsawa yace beat him, aikam tuni suka rufe shi da duka wanda yasa hankali mutane yayo kan su yayinda yafara ihun nai man taimako, saida kuma babu wanda yakawo masa dauki,
*Deeya* kam tana rungume agefen kafadar sa still kukan take ahankali me cike da bacin rai abunda saurayin nan yai mata, Wanda itakan aganin ta yai mugun cutar ta sosai.
Saida *Habeeb* ya tabbatar _guy_ din nan yadaku sannan yace su kyale shi, Sannan yace da mutun guda ya dauko shi aikam dasauri daya daga cikin su yadauki _guy_ din yasaba aka fada, Cikin bacin rai yace oya _follow me yace "Ok "Sir_ Cike da isa da takama yake taku Wanda hakan yasake bayyanar da kwarjinin sa da haibar sa, hannun *Deeya* na cikin nashi *Feeya* kuma tana biye da shi yayinda su kuma escorts din suke biye dasu.
Basu tsaya ko'ina ba sai office din shugaban makarantar, tunda babu inda *Habeeb* bai sani ba acikin school din ba, Cikin sa'a kuwa suka iske shi zaune yana rubuce-rubuce, yana ganin *Habeeb* ya mike zumbur Cike da girmama wa, duk dacewa mutumin ya girmi *Habeeb* din amma hakan bai hana shi bashi girma a matsayin shi na senetor ba, Cikin girmama wa yace ah! yallabai ne?.. sannu da zuwa yafadi yana nuna masa kujera, Bismillah! yallabai zauna mana ga kujere nan,
fuska murtuk *Habeeb* zauna tareda dora
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 42