Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shigowar sa adai-dai wannan lokacin ba, aikam take kirjinta yabuga yayinda jikinta yadauki rawa domin tahango wani mugun bacin rai akwayar idonsa, Cak! yadauki *Deeya* wacce tasake ruk'unk'ume shi tana sauke ajiyar zuciya, wani mugun kallon yasake watsama *Jana* me dauke da zan dawo gareki, sannan yanufi dakin shi rungume *Deeya*. Hannun tadora akai tareda fadin nashiga uku shikenan yau nabani, jifa tayi da remote din hannunta dasauri tanufi sama buguzu-buguzu hankalin atashe take hau step din tahau dai-dai in da bawon ayaban yake, itama ta taka aikam take tasaki wani uban ihu tareda fadin wayyo nashiga uku mutuwa karki zo yanzu, _nikam nace tab! *Jana* ai saida in lokaci baiyi ba_ Duka guiwoyin ta biyu suka bigi steps din dasauri tarike karfen benen, yayinda taji wani irin zafi yaratsa kwakwalwarta, dararrafe ta isa daki tana fadin wayyo washhh kafata. *_Kaikayi koma kan mashekiya inji ado gwanjan MATA_* ๐Ÿ˜‚. *Habeeb* kam bai dire *Deeya* ko'ina ba sai kan faffad'an gadon sa, tareda yimata runfa ahankali yasa harshen sa yana lashe sauran hawayen dayake fuskarta, Saida yalashe hawayan tas sannan tabude idon ahankali ta zubasu akanshi shidin ma ita yake kallo, cike da shaukin kaunar ta sun dauki mintuna suna kallon juna can sai ta turo baki tareda kauda kai gefe, dasauri yajuyo da kanta tareda fadin Oh! no *Leemah* ta don't angry with me, cike da shagwaba tace to bakai bane damukai waya dasafe baka fadamun yau zaka zo ba, gashi ban dafamaka komai ba sannan inata neman layin ka ban samu ba kuma yau Ina taji kewar ka sosai. Murmushi yayi me cike da kaunar ta da sha'awarta, fuskar takama yahade danasa ahankali yake goga hancisa anata cike da kasala yace, am so sorry *Leemah* ta nima kewar nice tada me ni shiyasa nayanke shawar nazo ba tareda nafada maki ba saboda nayi surprised naki, so are u happy to see me?.. tace yes I am very happy, yace nima haka *Leemah* ta kirjinta yatsurawa ido wanda ke tayi masa welcome, hannu yasa yaja igiyar gaban rigar aikam take kullin yasance dago kai yayi ya kalle ta tareda cewa kai! *Leemah* ta amma fa kwalli yar nan tayi mun kyau sosai, yakamata ma nabada tukuici KO?.. yakareshe fadi tareda kashe mata ido daya yana kokarin tura hannun sa ciki rigar. Murmushi tayi tareda tura hannuta cikin suman kansa, sannan tayi fari da ido wanda yasake tsuma masa sha'awar ta, cikin cool voice dinta tace "eh dasauri yace to me kike so fadamun zan baki kinji *Leemah* ta?.. tace Hmm na komai yabani inason, amma dai yanzu ka fara bani sweet tongue dinka na sha saboda nayi kewar sa dayawa dasauri yace really?.. tace yeap, Wani irin kayataccen murmushi sannan yace to take it my honey *Leemah* yafadi tareda mika mata harsa aikam dasauri ta cafke tafara tsota, nikam inaganin haka na arina kare๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€don my Habity ta hanani ganin kwaf lol. Saidai suka samu nutsuwa sannan suka kasararama Kansu, sannan suka shiga toilet sukayi wanka sannan suka fito, *Habeeb* yanufi wedrof yadauko wata farar jallabiya yasa, *Deeya* kam da towel din jikinta tahaye gado murmushi yayi tareda nifar gurin ta yace ya'akayi ne *Leemah* ta?.. Cike da shagwaba tace Hmm na nagaji kuma bacci nakeji, kumatun ta yashafa yace sorry *Leemah* ta nine natara maki gajiya ko?.. Dasauri ta rufe ido cike da jin kunyar abinda yafadi, dariya yayi sannan yaja bargo yarufe mata rabinjiki yace kiyi bacci ki zanje nadawo kinji?..tace to sannan yafita. Dakin *Jana* yanufa dakarfi yabanki kofar zumbur tamike cike da tsoro ta kalle sa, yayinda ya watsama ta mugun kallo rai bace yace... Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [11/9, 10:07 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 6โƒฃ3โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ _Today is final So_ maza-maza ki tattara naki yanaki kibar mun gida na dama nasakeki tu...wani uban tsalle tayi ta'isa gaban shi tareda tasakin ihu cikin azababben tashin hankali tace *BB* na kasakeni fakace?..... Matsawa yayi baya cike da bacin rai yace "eh au dake tunanin ki yana baki cewa bazan iya sakin ki ba ne KO" me?.....tab! lallai tunanin ki yafada maki robish, to bari kiji ni *Habeebullah Hasheem Sorro* nasakeki saki biyu tun ranan da Allah yanuna manku kuna aikana *ZINA* agidan nan dake da kwartonk...... Wani irin kara tasaki cikin tsananin tashin hankali tace nashiga uku na lalace kaganmu fa kace?...,wani uban naushe yakai ma bakin ta sannan yashiga sharara mata lafiyayyun marurru ka afuskar ta, wacce tuni tahade da jini da majina tofa๐Ÿ˜ณ da dama kunsa yana cike da ita, Cikin bacin rai yace yar iska kina nufin ka zafi zanyi maki kenan ko?....kai ta gyada cike da tashin hankali, wani marin yashara mata rai bace yace u are very stupid *Jana* ribarme zan samu idan nayi maki kazafi?...idan harma zanyin kaza sai narasa wacce zanyi ma kazafin sai mata ta?...kuma kazafin mana ZINA?.... lallai *Jana* kin cuceni domin nidaki kaganin natsani ZINA arayuwata, bana fatan aikata ta balle har nayiwa mutun kazafin ya'aita ta, amma wai sai gashi matata ta sunna nagani da idona tana aikawa har cikin gida na har kan gado na, Kai! *Jana* to wai ma dame narageki ne arayuwa?... ci da sha?...KO sutura?...eyeee yafadi da karfi tareda shake mata wuya cikin bacin rai yace tambayar ki nake?.... Cike da tsanani wahala take sonyin magana amma takasa saboda mugun shaka yai mata, murmushi yayi me cike da tsantsar bakin ciki sannan yasake mata wuya tareda hankadata baya tayi taga-taga kamar zata fadi sai kuma tadafe bango, tafara tari saida tayi sosai sannan ta tsaya duk yana tsaye yana kallon ta. Rai bace yace acikin abinda na lissafa mena rageki dashi?.. dasauri tace babu kodaya, da sauri ya'isa gurinta yasake shakar wuyanta cikin tsawa yace ainasan ban rageki da kodaya ba, kuma baki isa kice narageki da *SEX* ba domin kinsa koni wanene awannan fagen, ko kina nufin kice narageki tanan gurin ne?...Kai! ta girgiza alamar a ah yace ainasan ban rageki anan ba tunda harda kudi nake biyanki idan zanyi, wanda ban tabasanin cewa idan miji zaya sadu da matar sa saiya biya ta kudi ba sai akanki, kuma kinsani nasani cewa a, addinin mu ba'ayin haka amma haka nake biyan ki kudin sannan nasadu dake saboda gudun karnaje Ina aikana zina, shiyasa nake biyan kudin domin tuni nafahimci kedin muguwar mayyar kudi Ce shiyasa nake bakisu gudun Karkema kije kina aikana ZINA, Ashe bansani ba kedin tantiriyar mazinaciyace fasika tunda har zaki iya aikata zina da aure akanki tabbas *Jana* kedin maciya amanace, nisai aranma nagane cewa dama can ke mazinaciyace tunda lokacin da na aureki duk daban taba sanin ya mace ba saike hakan be hanini gane cewa ke ba cikakkiyar budurwa ba ce, Wanda dakika fahimci nagane cewa ke ba cikakkiyar budurwa bace sai ki kai mun karya cewa ai fyad'e aikai maki KO?..., hummm Kai! *Jana* kinci amanata ta dalilinki nasamu ciwon ulcer da ciwon sanyi badan Allah yaganar dani dawuri ba, da bansan irin cututtukan dazaki kwaso kiyaba mun ba, Lallai *Jana* kin cuceni cuta mafi muni arayuwa kinci ha'ince kwarai da gaske azaman mu, saidai nadauki hakan amatsayin kaddara dakuma rabon zuri'ar dake tsakanin mu wanda Allah ya kaddara samuwarsu ta tsotsonki, don haka kije nabarki da Allah. Cikin tashin hankali tace don Allah kayi hakuri karka sakeni, dasauri yace saki na nawa kuma?... kina nufin duk wannan abinda daki kaimun shine kike tunani bazan iya sakin ki ba?.. tab! kinyi kuskure *Jana* aituni dama nayi maki saki biyu tu ranan dana ganku, dama nabarki ne kiyi idda adakin ki kamar yadda addinin mu yace, bawai don na mai dake ba "a ah saidon na d'and'ana maki kwatankwacin bakin cikin dakika d'and'ana mu, to Alhamdulillahi kin d'and'ana, Sannan kuma dama kinsan nafad'a maki duk ranan dakika sake taka bakin get, zan datse sauran igiyar dake tsakanin mu ko?...ya kareshe fadi a tsawa ce, Dasauri tace "eh yace yauwa to kinga yau shikenan babu sauran wata alaka ta aure tsakanin mu, tunda ba bakin get ba yau har waje kika fita ba tareda izinina ba, don haka saiki tashi kibarmun gidana, Tun baki nakasamu rayuwata ba saboda *"Leemah* ta itace rayuwata kisani, Ina *"SONTA* fiye da yadda nake son kaina, saboda kin fahimci haka shine kike son ki "illatamun ita KO?... saboda kedin bakar mutuwa ce KO?.., Domin dai wannan abinda ki kai mata yau badan Allah yakiyaye ya kawoni ba, datayi mummunan rauni tab! narantse *Jana* da yau sai na kashe ki; wlhy murusss zan kashe ki, kinga alabashi nima sai akashe ni don haka, Ki tashi kitafi gidanku kine can kikarata da kazamar rayuwar dakika zabarwa kanki, idan kinga dama kin nutsu sai ki karasa iddarki, idan kuma baki natsuba saikije kiyi ta sha shan ciki babu abinda yada meni, yana Kai nan yasa Kai zaya fita. *Jana* kuka tasaki sosai cikin tashin hankali tace don Allah *BB* na kayi mun rai tafadi tana kokarin rike masa Riga, wani azababben tsawa yadoka mata rai abace yace idan kikai kuskuran tabani da wannan kazamin hannun naki, narantse sai nayi maki dukan mutuwa fiye da wanda naiwa tsinannan kwartonki, Wanda har da renamun wayo kukasoyi ko?...ga kato kirikiri nagani amma wai kikace mu kawarkice saboda kin rai nawa kanki dawayo kice ni kika rai nawa, shashasha kawai kidahumar banza dawofi, nikam ai tuni nayi dana sanin saninki a rayuwata wlhy Sannan yafice ransa abace. Zaya fita kesai saiga me aikin Hajiyarmu da basket dauke da kulolin abinci, Cikin girmama wa tace gashi inji "Hajiya Karba yayi tareda fadin Oh! aina manta "Hajiyarmu tace zata aikomun da abinci, kice nagode sannan ki fada mata na'iske *"Leemah* ta tadawo saidai tana bacci ne, tace to tareda dajuyawa shikuma yakoma dakin shi, Afalo ajiye basket din sannan yanufi bedroom dasauri ya karasa bakin bed din murmushi yayi ganin har tayi bacci, gyara mata kwanciya yayi tareda fadin kiyi bacci kin lafiya me dadi tareda mafarkin Hmm dinki, inason ki *Leemah* ta irin son da baki bazaya iya fada ba, inama ki fatan tashi cikin amincin Allah *Leemah* ta sannan yai mata kiss agoshi da baki sannan yafita yanufi part din *Harees*. ***** *Jana* kam kuka take sosai kamar ranta zaya fita hankalin ta yai mummunan tashi, domin dai ko kad'an batayi zaton cewar *Habeeb* yagansu ita da Ado lokacin da suke aikata fasikancin su ba, Cikin kuka tace nashiga uku na tayaya zanbar wannan daular?.. *Jana* kam duk tabirkice sai surutu take saki kamar mahaukaciya sabon kamu, can tamike zumbur kamar zararriya tafita part din su Hajiyarmu ta nufa. Bako sallama *Jana* tafada falon tamkar mahaukaciya, tazube gaban Abba da Hajiyarmu dasuke zaune suna fira, cikin tsanani kuka tace Abba Hajiyarmu kunga banyima *"BB* na komai ba yasakeni cike da tashin hankali Abba yace subhalallahi! Saki kuma?... Kai ta gyada alamar "eh cike da bacin rai yace haka kawai "yasakeki ba tareda kinyi masa mummunan laifi ba?. tace "eh yace to yanzu shi Na ALLAH yana ina?... tace "yana part na baro shi, Waya Abba ya daga yafara kiran layin shi amma akashe hakan ne yasake bata wa Abban rai sosai, Itakam Hajiyarmu ba tace komai ba amma aran tafadi take yau takai shibango kenan, rai bace Abba yakalli Hajiya yace ki kira mun Laraba tace to tareda tashi tanufi sama, Can sai ga su tareda Laraba Abba yace jeki ki kira mun Na Allah yazo yanzu nan inason ganin shi, tace to tareda fita. *Habeeb* kam rai bace yashiga part dinsu *Harees* afalo ya iskesu zaune *Harees* yanayin abinci shima bai dade dawowa daga office ba, gani *Habeeb* din ne rai bace yasashi tashi daga cin abinci cike da mamakin ganin sa yace ah kaine yau?..yafadi tareda kama hannun *Habeeb* suka nufi dakin sa. Zaunar *Harees* yayi sannan yadauko ruwa me sanyi yabashi yasha sannan, yadafa kafad'arsa tareda cewa Dan'uwa meke FARUWA?..wata iska me zafi *Habeeb* sannan yafada wa *Harees* abinda yafaru tsanani sa da *Jana*, in daya karasa she dacewa kasan Allah Dan'uwa yau sai naji ni sakayau kamar ansauke mun wani katon dutse daya dan ne mun kirjina, *Harees* yace dama haka jakaji musamman da yakasan ce *Janar* ba macen kwarai bace, to Allah ya kiyaye ya kuma shiryar da'ita. Yanzu Ina "yaran?..tsaki *Habeeb* yayi yace yara kam su nan kasa ita Lili tuni na damka wa "Hajiyarmu, shidai Junior ne dama yake gurin "ta shekaran jiya kuma damu kai waya da *"Leemah* ta take fadamun wai dasu "Walid sukazo gaida su Hajiyar mu sai suka bisu gidan su" har da Lilin shine Mamu tace abar su, su kwana biyu. *Harees* yace to shikenan Allah yarayasu yace ameen, sannan suka fito saida yakai shi har bakin get sannan yakoma shi kuma yanufi gida. Zaya shiga part dinsa kenan saiga Laraba tafito daga part din, cikin girmama wa tace yallabai "Alh yana kiran ka yace OK tareda nufar part din, DA sallama yashiga falon Hajiyarmu Ce ta amsa, Abba kam wani irin kallo ya watsama sa ba tareda yabari *Habeeb* ya zauna ba rai bace yace, Na ALLAH lafiya zaka saki matarka ba tareda tayi maka laifin komai ba, cike da mamaki yajuya ya kalli *Jana* wacce ke tafaman gunshaki kuka kamar ance uwarta da uban ta sun mutu, zama yayi ba tareda yace komai ba saidai ransa abace yake, cikin dan tsawa Abba yace dakaifa nake?.. Rai bace yace ita tace ba tayi mun laifi ba na sake ta?.. Abba yace "eh ba haka kikace?..ciki kuka tace "eh, Kai *Habeeb* ya girgiza yace ashe zaki iyakin fadin laifin daki kai mun?.. Sannan ya kalli Abba yace tunda har takasa fadin laifi datayi mun, to nima nayi mata wannan alfarman bazan fada ba saidai Abba kasani mummunan laifi *Jana* ta yi mun shiyasa na sake ta, Abba yace to kayi hakuri kamai da matarka dakinta, Yace Abba ai babu sauran zama tsakanin mu, da sauri Abba yace saki nawa kai mata kai tsaye *Habeeb* yace Uku Cike DA tashi hankali yace... Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [11/9, 10:07 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 6โƒฃ4โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ Subhalallahi! Na ALLAH ba kada hankali ne da zakaiwa matar ka saki uku alokaci daya?... sakin da Ubangijin mu yahane mu, shine zakayi, Na ALLAH yau me yasamu kwakwalwar ka shin ka manta na gargard'eka da aikata irin wannan sakin ba tareda wani mummunan laifi ba?..., Da sauri yace Abba kagafar ce ni; tabbas nasan ka gargad'eni da irin wannan sakin, saidai wlhy laifin da *Jana* tayi mu banajin zan iya cigaba da zama da'ita shiyasa nasake ta domin laifine me matukar muni. Abba yace Na ALLAH duk laifi da Murjanatu tayi maka be kamata kayi mata irin wannan sakin ba har uku alokaci daya, Da sauri yace Abba ba'a lokaci daya nayi mata ba, Dama nayi mata saki biyu saina barta tayi iddarta kamar yadda addini ce, sannan nace mata duk ranan da tasake taka bakin get ba tareda izini naba, to zan yanke sauran igiyar dake tsakanin mu shine yau Ina shigowa *Jana* tana dawowa daga yawonta wanda tafita ba tareda ta nemi izinina ba ko dayake aidama tasaba yin haka, To amma tunda nace karta fita shin Abba meka mata tayi?..cikin sanyi jiki Abba yace saita tsaya inda ka'ajiyeta, yace to batayi hakan ba gaka aishikenan yanzu babu wani sauran zama tsakanin mu tunda tafita kaga saki yacika uku kenan ko?...Abba yace haka ne lallai Murjanatu baki kyauta ba, kinga yanzu aure yabaci koda yake Ina zuwa. Wayarsa yadaga yakira layin Baffa inda yace yazo yanason ganin sa aikam, batareda bata lokaci ba saiga Baffa ya shigo da slm bayan sun gaisa sai ya zauna, sai Abba yafada masa abinda yafaru da sauri Baffa yace subhalallahi! meyai zafi haka *Habeebullah?..* nan yafada masa kamar yadda yafawa Abba, Baffa yace assha Murjanatu baki kyau taba, Abba yakalli Baffa tareda cewa to lallai dai kam yah sheikh aure yakare kenan KO?... Murmushi Baffa yayi yace Alh aikaima kasan hakan Abba yace nasani inadai son suma su sake sanin hakan daga bakin Shehin malami ne, Murmushi Baffa yasake yi tareda cewa almajiri dai Alh, to maganar gaske kuma a addini babu sauran aure tsakanin su hakan kuma baiyi dadi ba, Abba yace to yaza'ayi Allah ya kaddara saidai akiyayi gaba Allah kuma yakiyaye Hajiya tace to ameen nan dai Baffa yayi tayima *Jana* nasiha ganin yadda take ta kuka kamar ranta zaya fita, wanda yasan tana kukan rabuwa ne da *Habeeb* din yace kiyi hakuri Murjanatu inason ki dauki wannan din a matsayin kaddaran ki, kije ki nutsu ki gama iddarki idan harki kayi yadda addinin mu yace' Insha'allah Allah yaza zaba maki miji kwatankwaci *Habeebullah,* Cikin kuka tace to tunda Lili tana gurin Hajiya abata "Junior ta tafi dashi, har *Habeeb* zayayi magana sai Baffa ya hanashi ta hanyar daga masa hannu, yace Murjanatu kiyi haku kinsa kyanda gidan ubansa don haka kibar Muhammad agidansu, keda kiyi masu adda'a Allah yashira su a tafarkin lslama kinji ko?..kaita gyada, hakan nan dai *Jana* tafito, tanufi part dinsu ta hada kayanta tasaka cikin motar ta tanufi gidan su, badan ranta yaso barin gidan *Habeeb* ba. Bayan fitarta sai Abban yace da *Habeeb* yason duk abinda ya mallakawa *"Jana* karya karba komai, sannan karya dai nayi ma iyayen ta alkhairin daya saba kodan albarkacin zuri'ar dake tsakanin su, yace Abba aibazan karbi komai ba alkhari kuma Insha'allah bazan fasaba, yara daine datake tunanin abata bazan bata ba. Abban yace to shikenan yara kam dama baza'a bata ba, Allah yai maka yakuma shirya su sukace ameen sannan *Habeeb* yafito ransa wasai yanufi part din sa, yayinda yakeji wani irin dadi yana ratsashi musamman da Abba bai dauki lamarin dazafi ba. **** Direct bedroom dinsa yanufa yana shiga ya'iske *Deeya* tana gyara kwanciya tareda Jan bargo tana sake tarufe jikinta, murmushi yayi tareda kallon agogon dake manne da bangon dakin wanda yanuna karfe hudu saura, ahankali yakara sa bakin gadon ya tsaya kuri yaimata da ido yana kallon baby fice dinta tareda cute pink mouth dinta, Wani irin sonta yakeji na musamman yana ratsa jini da jijiyoyin jikinsa. Mamaki ne yaka masa ganin ga ac kunne amma sai gumi take, Hannun yasa yanajan bargon zuwa kasa yayinda ita kuma take jasan zuwa sama, murmushi yake ganin yadda take jasosai kamar zatayi kuka alamar dai adaina jan bargon, dariya yayi tareda fadin am sorry *Leemah* lokacin sallah yayi _so wake up my sweet Dear_ tareda sake Jan bargon da d'ankarfi, itama taja dakarfi cike magagin bacci me had'e da tsoro tace pls my sweet *Feeya* ki bari naboye kinga tabiyoni zata caka mun wuka ko?... Ido yazo tareda fadin _what?.._ *Leemah* ta wanene yake kokarin caka maki wuka?...dasauri yahauwa kan gadon ya dagota yana fadin *Leemah* ta, dai-dai lokacin data saki wani irin razanannen kara tareda bude ido, Dasaurin ta rungume shi yayinda jikinta yadauki karrrrrrrrrma! bakinta narawa tafara karanto Addu'a, yayinda jikinta yake fitarda wani irin gumi sai kace babu a c adakin sai kuma tasaki kuka tareda sake kwakume shi still jikinta naci gabada karrrrrrama. Shikam *Habeeb* wani irin bugawa kirjinsa yakeyi gawani azababben tsoro dayaji yadarsu masa jin abinda *Deeya* take fadi acikin bacci ceke tsoro yake tambayar kansa wane yake son caka mata wuka?... kirjinsa ne yasake bugawa dakarfi hakan ne yasake sa shi rungume ta ajikinsa tamkar zaya mayar ita cikin jikinsa, yana fitarda Wani irin numfashi me cike da fargaba, dakyar yasamu bakinsa yabud'e yafara karan tama ta addu'ar ne mantsari daga mummunan mafarki domin ya tambar dashi *Leemarsa* tayi. Ahankali yacigaba da yimata addu'ar tareda hura mata iska akunne yana kuma shafa bayanta, har tayi shuru sai kuma sannu ahankali nutsun take ratsa sassan jikinsu. Ahankali ya dagota kanta yahade bakin su tsawon wani lokaci sannan yacire bakinsa daga nata, cikin sarkakkiyar murya yace *Leemah* ta cikin shsheka tace na'am, yace wanene ki kai mafarki dashi zaya caka maki wuka?..tace "Aunty *Jana* ce pls Hmm na, ni dai don Allah kamai da "Aunty *Jana* daya daga cikin gidajenka kaga sainayi ta mafarki da'ita" tana bina da wuka zata caka mu, KO yanzu ma ita Ce ta biyoni da wuka zata caka mun saika riketa", nidai inajin tsoro kar wata rana ba kowa tayi mun illa kaga haka ranan daka tafi.... Nan tafada masa abinda yafaru har da marin bata boye masaba, Ajiyar zuciya yayi tareda sake rungumeta yace kwantar da hankalin ki *Leemah* ta, *"Jana* bata isatayi maki abinda Allah bai makiba yanzu haka tsakanin muda *Jana* saidai zumunci, koshima albarkacin yaranta in badan haka ba ko zumunci bazamuyi da'itaba domin itadin bata cikin tsarin mutanan da zamu yi zumunci dasu. Dasauri tadago ta kalle sa cikin rashin fahimta tace Hmm na banga ne ba?..murmushi yayi tareda gyara mata kashin kanta da yabar baje, sanna yace *Leemah* ta basaki *Jana* yau, ido tazaro cike da tsoro tace me tayi maka?... yace komai ma nan yafada mata abinda yafaru, saidai bai fada mata maganar kamata dayayi da Ado ba. A gaskiya ba taji dadin rabuwar su ba kodan su Lili to saidai kuma haka Allah yatsara Allah yaraya su, yace tashi muje muyi sallah sai mu ci abinci kai tadafa tareda cewa kashhh!, am so sorry Hmm na yaufa banda fa komai ba, amma bari nayi alla sai nadafa maka simply food b4 nayi maka special dinner KO?.. takareshe fadi tana murmushi tareda shafa lallusan sajensa, cike da kaunar ta yace yes my Honey amma karki damu dawanda zan ci yanzu already Hajiyarmu tabayar ankawo mun, namanta ma dazu nafada maki da nashiga tace wai yau tun safe da kika shigaku ka gaisa bata sake ganinki ba, takira wayar ki baije ba kuma taji lokacin dakika dawo, amma kuma baki shigo ba ko lafiya?.. Da har zata turo Laraba tadubo ki sai gani. tace Humm! ai tunda nayita kiran layukan ka baije ba sa haushi yasa na kashe wayata Sannan tsabar kewar ka, yasa dana dawo banshiga part din kowa ba na nufo dakin ka ko naji sauki, Murmushi yayi cike da kaunar ta yace humm! *Leemah* ta nima tsabar kewar ki ce tasana baro abj tamkar mahaukaci, saida nazo kika tashayar dani daddad'ar zumarki sannan naji sauki. murmushi tayi cike dajin kunya take kokarin tashi dasauri ya mai da'ita jikinsa tareda yimata rad'a akunne, dariya tayi tareda dan dukan sa kad'an akirjinsa tace Kai! Hmm na again?.. Shima dariya yayi tareda daukar ta yana fadi "eh KO" bazaki bani ba?.. tace zan baka mana Hmm na aini din ta kace KO?.. cike da shaukin kaunar ta yace yes nikad'ai ma kuwa baby na shi yasa nake Kara SONKI tace nima haka, toilet suka shiga saida yajirata tasakeyin wanka saboda gumin datayi, sannan suka dauro alwala suka fito shi yanufi masallaci ita kuma tayi anan dakin sa. bayan ta'idar sai ta'isa gaban mirror tayi kwalliya sannan tasa wata roba gown ja wacce ta kamata sama da kasa gaba daya shape dinta yafito sosai, bayan takama gashin kanta tadaure dawani jan ribbon sai ta daura wani bakin bandana me ratsin ja tagefe, Sannan tafeshe jikinta da turaruka masu kamshi gaskiya tayi kyau sosai, sannan ta nufi falo dai-dai lokacin da *Habeeb* ya shigo. Dasauri ya'isa gareta cike da farin ciki ya sureta yafara zagaye falon da'ita, suna dariya sannan ya zauna tareda zaunar da'ita akan cinyar sa kallon ta yake cike da so da kauna, yace kai! *Leemah* ta zaki kasheni da gayunki fa fari

Chapter 30 of 42