Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dubu bama uku ba tunda kedin nagane shashasha ce wawuya me kwakwalwarki kifi, taya za'ai kiyi haka eye?.. Cike da tashin hankali *Jana* tace nayi kuskure shiyasa nakeso kije ki duba mun ko sun sauke "shi ya'isa gida,tace to ke bazaki jeda kanki ba saini?..tace kiyi hakuri kin san duk ranan da *"BB* na yadawo bana fita, tace to bari zanje naduba, tace to nagode sanna ta kashe wayar. Koda Shafa taje unguwar su Ado ta tambaye shi sai akace mata tun safe "daya fita bai dawowa ba, don haka ne takira *Jana* tafada mata to shi take ta faman safa da marwa a tsaki yar falo. *_Agidan gonan fadaman mada_* ******** *Harees* ne keta sallama akofar falon saidai babu wanda ya amsa, shiyasa yakutsa kai cikin falon, turus ya tsaya sai kuma yasaki murmushi ganin yadda *Habeeb* ya Kwakume *Deeya* a kirjinsa sai kace wani yace" zaya kwance masa ita, bacci suke abinsu me cike da nutsuwa da kwanciyar hankalin wanda ya kwashe su tun bayan dasuka gama yan wasan nisu, Kai Harees ya girgiza tareda karasawa gurin wani table me dauke da takardu, takarda yadauka da biro yafara rubuta kamar haka. _Hmm Dan'uwa kenan irin wannan hot hug haka sai kace ance" za'a kwance maka Queen of beauty?..to kadai yimata ahankali kasan yarinya ce, ga magunguna nan siyo maka kayi amfani dasu Insha'allah nan da sati biyu zaka rabuda duk wani sanyi dake tareda kai, har da maganin zazzabi aciki saidai nasan bazaya yi amfani ba domin ganin danai maka yanzu, ya tabbatar min Queen of beauty takawar da zazzabin tareda duk wata damuwa dake ZUCIYAR ka, a sha bacci love lafiya, ni natafi gida sai kunzo ina maku fatan tashi cikin amincin Allah._ Bayan yagama rubutawa sai yasaka masa cikin ledar maganin sannan yafita yatafi gida, *Hafeez* kam dama shi tunda ya ajiye *Deeya* yatafi gida. Kiran sallah magrib shine ya ta dasu daga bacci *Habeeb* ne yafara tashi, murmushi yayi ganin yadda suka kwakume juna, har yana fadi a ranshi kamar ance za"araba mu, sai kuma yai dariya tareda girgiza kai yace no body can separated us *Leemah* ta we are together forever Insha'allah. ahankali yake shafa bayan ta cikin rad'a yake kiran sunanta, cikin yanayin bacci ta amsa, tareda tura hannu ta cikin suman kamshi tana ya mutsawa ido ya lumshe alamar yana jin da din hakan datake masa, cike da kasala yace *Leemah* ta tashi muyi wanka sai muyi sallah magrib sannan mutafi gida ko?..ahankali tamike tana salati, cike da so yace muje muyi wanka tare ido tazaro tareda cewa tare kuma?.. yace "eh mana to meye?..ni mijinki ne ke mata ta ce sanna kuma aida kai dakaya duk mallakin wuya ne, so tashi muje tace a ah nidai bazan iyaba, murmushi yayi tareda tashi yana cewa wata rana zaki iyane *Leemah* ta, sannan ya shafi fuskar ta yace bari na fito kaita gyada masa alamar to. Bayan yayi wanka yadauro alwala yafito sai itama yace tashiga koda tafito ta'iske ya shirya cikin kananan kaya Riga T-shirt brown an rubuta *H* & *H* ajikin rigar tabaya da wando black *Deeya* ma irin kayan yaciro mata itama rigarta an rubuta *H*& *H* tareda hijab brown me hannu, cike da mamaki tace Hmm *Habeeb* kayan wanene nan?.. yace na *Leemah* ta ne na tanade su dayawa domin ita, so idan har basuyi mata ba taduba cikin wedrof tasa wanda take so ta'iske ni falo muyi sallah, yakareshe fadi tareda tsura mata kyawawan idon sa masu rikitata kauda kai tayi daga barin kallon sa tareda sakin murmushi tayi me cike da farin ciki sannan, tace kai Hmm *Habeeb* dina sunyi fa kuma thanks, cikin wani irin harara me dauke da So yace thanks for what?.. tace for komai ma, yace kika ce KO?..tace "eh din yace hmm yarinyar nan ranan dana kamaki zakiyi baya ni dalla-dalla, tace "eh naji din tafadi tareda yi masa gwalo dariya yayi tareda fita yana cewa zaki sani ne ai. Saida sukai sallar isha'i sannan suka tashi tana cikin nad'e abun sallah ya rungume ta tabaya tareda cewa *Leemah* ta kodai mu kwana nan ne da safe sai mutafi gaida?..tace umh umh nidai mutafi gida, yace to dauko mun wayoyina da wallet akan bed sai kizo mutafi ko?. tace to tareda nufa daki. Shikuma yanufi table din dayaga leda akai kodaya duba sai yaga magani da takarda, saida yaduba magungunan sannan ya karanta takardan murmushi yayi tareda cewa "Dan'uwa kenan to naji nagode, dai-dai lokacin da *Deeya* ta dawo dauke da tarkacen. Karba yayi yasa wallet din aljihu wayoyin kuma da ledar magani yarikesu a hannun hagu, sannan yarike hannun ta dana dama yayinda ita kuma tadauki jakarta tarataya wanda tun shigarta falon ta'ajiye ta agurin sannan tadauki basket, yace oya mutafi har zasu fita., saiga Saminu dasauri yashiga falon *Habeeb* yace Saminu lafiya?.. yace Sir "mutumin nan fa yana cikin mawuyacin halin rayuwa ko mutuwa cikin tsananin bacin rai *Habeeb* yace... *_Dafatan munyi sallah lafiya Allah yakarbi ibadar mu ya, kuma maimaita mana ameen_*๐Ÿ‘๐Ÿฝ Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 5โƒฃ2โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* *_WANNAN PAGE GORON SALLAH NE GA DUKKAN MUSULMAN DUNIYA, INA ROKON ALLAH YAKARBI IBADAR MU YAKUMA YA MAIMAI TA MANA AMEEN๐Ÿ‘๐Ÿฝ._* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pesn writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ To Ina ruwana "ya mutu ko ya rayu babu abinda ya dameni kaji KO?..wai ma kana nufin kace mun har yanzu wannan stupid "man din yana cikin gidan nan?..Da sauri yace "yes Sir, cikin bacin rai yace saboda me?.. cike da girmama wa yace Sir tunda ka gama dukan "shi baka Ce" komai ba shiy... Cikin tsawa *Habeeb* yace _shut up u mouth_ Saminu, yace sorry Si...dakarfi yace nace karufe mun bakin ka agurin nan kanaji ko?.. banason shirmen banza kana nufin sai nace" kufitar dashi sannan zaku fitar dashi?..to daku kabar shi me zaiyi mun eye?.. cikin girmama wa yace Sorry Sir., Cikin bacin rai yace dalla kuje kufitar mun dashi daga gida kujefar dashi can idan mazaya mutune to ya mutu acan, amma ba'a gidana ba kaji ko?..yace OK" Sir tareda juyawa yafita da sauri. Ido *Deeya* tazaro cike da tsoro jin ance aje ajefar da mutun dama tunda suka Fara maganar gaban ke faduwa, Rai bace *Habeeb* yaja hannun ta suka fita dai-dai lokacin da su Samuel suka fito da Ado jini sai tsiyaya yake ta ko'ina ajikin sha, Yana nan akulle kamar kayan wanki yayi bala'in dakuwa saika kalle shi da kyau ma zaka gane yana numfashi tsabar galabaita dayayi, haka suka jefashi abayan hillos. *Deeya* kam ganin yadda aka fito Ado baya ko numfashi yasa taji gaban ta yatsana ta bugawa, gawani irin tsoro daya sake kamata, har aranta tana cewa ya salam wannan mutumin aiya mutu, Kai! yanzu Hmm *Habeeb* ne yai masa duka haka?..wata zuciya tace "eh mana bakiji abinda yaron sa yace" ba?.. jitayi kirjin ta yabuga dakarfi aikam aranta tace shikenan yakashe shi" dasauri ta kalli *Habeeb* Wanda kallo daya zakai masa ka fahimci ransa amatukar bace yake, ganin haka ne yasata saurin dukar dakai yayinda taji wani irin tsoron shi yadarsu aranta, domin gaba daya yarikide yakoma asalin Hmm *Habeeb* din datasani, wanda baya daukar raini KO kadan. Direct gurin motoci suka nufa, Dasauri Saminu yaje zaya bude ma *Deeya* mota cikin tsawa *Habeeb* yace nasaka ne?.., dasauri yamatsa gefe tareda cewa no Sir batare da nuna wata damuwa ba KO bacin rai ba domin dai yasan ba halin megidan su bane yiwa mutun tsawa, *Habeeb* ne yabude mata mota tashiga bayan ya karbi basket din yamika ma Saminu yakarba yasa acikin boot, sannan shima *Habeeb* yashiga Saminu yarufe kofar direba yaja suka fita yayinda motar escorts din sa tarufa masu baya, Dasauri Saminu yaje shima yashiga tasu motar suka fita. *Habeeb* yana kunna wayoyin shi Kiran *Harees* yana shiga dauka yayi tareda bude karan, yace ya'akayi ne Dan'uwa?.. yace lafiya lau inafata kuntashi lafiya daga baccin Love din?.. wani irin murmushi yayi me kunshe da farin ciki da bakin ciki, sannan yace "eh gamu nan zuwa gida ina son kasake yimun bayanin yadda zanyi using magunguna, yace "OK tau sai kunzo sannan yakashe wayar, wasu kiran ne suke ta shigowa wayar yana amsawa sai gakiran *Jana* yashigo wani irin kololon bakin ciki ne ya tokare masa kohon zuci, aikam take yaja wani irin matsiyacin tsaki mtwwww! tareda cewa bastard women kawai, ido *Deeya* tazaro Cike da tsoron jin abunda *Habeeb* yafada ga *"Jana* domin taga sunan ta afuskar wayar, Kiran kam sai sake shigowa yake amma yaki dagawa ranshi abala'in bace yake sosai, sai tsaki yake tareda yin rejected call din nata, duk abunda yake *Deeya* tana kallon sa, dayaga ma alamar zata dameshi kawai sai ya kashe wayar yajefata set din baya tareda ledar maganin cike da bakin ciki yadafe kanshi, dai-dai lokacin da suka shiga gida. *Deeya* kam taso tashiga part dinsu amma hakan bai samu ba domin bataga fuska ba, hannun ta cikin na *Habeeb* suka nufi part din shi gaban ta sai faduwa yake, koda suka shiga falon *Jana* suka isake tsaye hannun ta rige da waya wani irin kallon mamaki take masu, *Habeeb* kam ko kallon inda take baiyi ba fuskan nan nashi ahade yanufi dakin shi, Dasauri *Jana* tabi bayan su cike da masifa tace kan uba wato ni ina nan ina zaman jiranka kai kuma kuna can kuna cin amanata kaida wannan yar'iskar yarinyar, shiyasa nake ta kiran wayar ka kaki dagawa saboda kana tsoron karta shafeka KO?.. tab! lallai to bari kaji idan har Kai kana jin tsoron ta, to ni banajin tsoron ta kuma wlhy bazan yadda da wannan cin amanar daza ku ringayi mun ba ehee kuma mlm ka tsaya ka fadamun inda ka Kai matar mut... takasa karasawa saka makon juyowa da *Habeeb* cikin zafin nama ya zabga mata lafiyayyan mari tareda tura ta jikin bango sannan yasa hannun shi daya yashake mata wuya ta, cikin matsanancin bacin rai yace yauwa saikin fadamun me kalmar cin amana take nufi?.. _kunsan me hakuri be iya fushi ba_ Yace idan kuma har baki fadamun ba to zanyi maki mummunan illah arayuwar ki koma na kasheki kowa yahuta da kazamin halinki na boye dakike aikata wa, duk da banyi nufin aikata kisa agareki ba to yau zanyi idan har baki fadamun ba, dakarfi yasake shake wuyanta tareda ihun cewa nace ki fadamun meye Kalmar cin amana take nufi eyeee?.. Aikam tuni idanun ta suka firfito waje, tareda juyewa yayinda bakin ke kokarin bacewa. *Deeya* kam tsoron ta yasake yawa sosai wanda yasa kafafunta suke kokarin kasa riketa, hakan ne yasata dafa bango dasauri domin tuni jakar dake hannun ta yakai kasa, yayinda take jin kirjinta kamar zaya tarwatse tsabar masifar bugawa dayake, mata saboda tsabar tashin hankalin data gani har numfashi ta yanason barin jikinta, dasauri tafara kokawar maidashi gurin zaman shi, saida kuma ina takasa hakan saka makon ganin bakin idon *Jana* yabace b'at, tsabar tsoron ganin hakan ne yasata sulalewa kasa sumammiya, wanda yasa *Habeeb* juyowa dasauri yasaki wuyan *Jana,* ta zube kasa ragwaf kamar guzumar saniya, yanufi gurin *Deeya* cike da tashin hankali yadago ta yana kiran sunanta, bata amsa ba don haka yadauke ta cak yanufi dakin shi da'ita. Kan kushin yakwantar da'ita tareda cire mata hijab sannan yanufi fridge dasauri yabude yadauko goran ruwa, yabude ya yayyafa mata afuska, dakarfi tasaki ajiyar zuciya tareda bude ido ahankali dasauri ya'ajiye gorar tareda d'aga ta ya rungume akirjinshi tareda sakin ajiyar zuciya yace *Leemah* ta are you "OK?.. kuka tasaki tareda tureshi daga jikinta tana cewa ni ka kyaleni ba ruwana dakai tunda kashe mutane kakeyi, ta kareshe fadi tareda kokarin mikewa. Dasauri ya mai da'ita ya kwantar tareda yimata runfa yace pls *Leemah* ta listened to me, cikin kuka tace nidai ka kyaleni bazan saurare kaba ganin taki tsayawa ta saurare shin yasashi rufe bakinta da nashi, dole tayi shuru... tana sauke ajiyar zuciya, saida ya tabbatar ta nutsu sannan yacire bakin shi daga nata. Cikin wata irin murya yace pls *Leemah* ta ki saurare ni kinji?..baijira amsar taba ya cigaba dacewa *Leemah* ta idan wani yazo yafada maki ina kashin mutane bazakiyi mashi musu ba?.. baki ta turo tareda cewa to ba gashi nan kayima wancan "mutumin duka harya mutu ba, sannan yanzu kuma kashake Aunty *"Jana* kace saika kasheta, ahankali yace *Leemah* ta wannan mutumin bai mutu ba saidai ya daku iyakar dakuwa wanda hakan hukunci ne, nayi ma saboda mummunan laifin daya aikata a gareni; Shiyasa nima nayi masa mummanan hukunci wanda ko gobe akace" yaima wani irin laifin bazaiyi ba, to balle har yayi tunanin sake aikata shi a gareni, "ita kuma bakiji abunda take ce" mun ba ni sa'anta ne da zata dinta fadamun maganar dataga dama?..bayan haka sai taringa kirana maciyi amana to cin amanar menayi mata umh?..nine ya kamata na kirata maciyiya amana amma banyi hakan ba sai ita ne zata kirani da hakan, saboda taji dadi na kyaleta ban hukunta ta akan laifi datayi mun bako?.. Cikin sanyi murya tace to basai kayi hakuri ba tunda kasan halin "ta amma kace zaka kashe ta to idan "mala'iku suka amsa fa ta mutu shikenan sai ace Hmm *Habeeb* dina yayi kisan kai, gaskiya nidai kar kasake cewa zakayi kisan kai domin babu kyau mutun nafadin haka kaji Hmm Dina?.. murmushi yayi me cike da SONTA, sannan yace to *Leemah* ta nadai na kinji tace to zan tafi part din "Hajiyar mu na kwanta, cike da mamaki yace part din Hajiyar mu kuma *Leemah* ta?..tace "eh acan yau zan kwana, yace a ah *Leemah* ta ai daga yau kin daina kwana apart din "Hajiyar mu dana "Inna saidai anan part din, shin waikin manta Abba yace" yauzaki tare?..ahankali tace a ah yace yauwa to tashi muje na rakaki dakin ki tunda angyara ko anan dakin zaki kwana?.. dasauri tace a ah, murmushi yayi tareda cewa to tashi muju, tace to amma dai zanje naga Hajiyarmu yace "OK muje nima zan shiga part dinsu lnna na gaida su, ya kareshe fadi tareda daga ta saida yasa mata hijab sannan suka fito falon, basu iske *Jana* ba so hakan bai damu *Habeeb* ba asalima jakar *Deeya* yadauka tareda Kama hannun ta suka fita. ***** *Jana* kam tunda *Habeeb* yasakar mata wuya take faman tarin wahala domin tuni tajiyo kamshi mutuwa, dakyar ta iya tashi ta dauki wayar ta data tashi aiki domin kuwa tuni tayi ratsa-ratsa saka makon faduwa datayi akan tiles, sannan tanufi dakinta zuciyar ta cike dawani irin fargaba tareda wani irin azababben tsoro saboda jin kalaman *Habeeb,* zama tayi a gefen gado. ahankali tace me *"BB* yake nufi da kazamin halina danake aika tawa aboye?..jitayi gaban ta yafadi dasauri tadafe kirji tareda cewa nashiga uku, badai *BB* yaga ne abunda nake yiba?..dasauri tace a ah bai gane ba can kuma tace a ah kai! yaga gane haka dai tayi ta gardama da zuciyar ta, daga karshe dai ta yadda dacewa bai gane ba, Sai kuma tafara juya wayar ta wacce bata da sauran amfani, yayinda take tunani inda *Habeeb* yakai Ado, Cikin sanyi jiki tace ga wayar talala ce dana Kira Shafa nafada mata, Oh! ni Murjanatu ko a wani hali ado na yake?.. _Nikam nace nasani tazo nafada mata KO masu karatu lol._ Su *Deeya* zasu shiga part Hajiya kenan saiga *Hafeez* yafito, Cikin girmama wa ya gaida *Habeeb* tareda cewa dama Abba yace" nakira ku har da Aunty *"Jana* baki *Habeeb* yatabe tareda cewa jeka ka kiranta, yace to sannan suka shiga falo din da sallam, Zaune suke afalon suka d'ai suna fira Abba da Hajiya, lokaci daya suka amsa sallama, zama *Habeeb* yayi kusada Abba yayinda *Deeya* ta zauna kusada Hajiya gaida su sukai a lokaci daya suka amsa, Hajiya tace hali dubu na ya'akai?.. tace lafiya lau tareda shigewa jikinta, dai-dai lokacin da *Jana* ta shigo falon bayanta gaida su sannan ta zauna, gyaran murya Abba yayi tareda yin salati, Sannan yace nakira kune don nayi maku d'an takaitatcen nasiha akan zaman takewar aure, da farko inason kusani aure bautan Ubangiji ne wanda yake tattareda hakuri acikin sa don haka duk abinda zakuyi salingo hakuri musamman ma kai na Allah kaga nauyi yasake hawa kanka, nan dai Abba yai tayi masu nasiha bayan yagama sai yace idan akwai me magana yayi, Dasauri *Jana* tace tana da magana Abba yace tayi, saida ta gyara zama tareda karkace daurin dan kwalinta sannan tace tana so araba kwana tun yau saboda bazata yadda da wannan cin amanan ba, tunda yanzun nan daga tayi magana akan cin amanar ta dayayi shine yashake mata wuya kamar zaya kashe ta, wanda ta dalilin haka ne har wayar ta tafadi talala ce don haka sai ya biyata wayar ta ehee takareshe fadi cike da rashin kunya. Kamar ba'a gaban surukanta take ba, cike da tsananin tashin hankali Abba yace... *_Hmm Jana kenan ke kam ai anriga anbaki red card so baki ba kwana turakar miji ko reads lol_*. Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 5โƒฃ3โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Subhalallahi! Na ALLAH kaida kanka ka aikata haka ga matar ka me tayi maka haka dazafi?..da har zaka sheke mata wuya kisan kai dazaka yi?..to waima da yaushe kafara zama marar hakuri eye?... *Habeeb* kam baice konai ba sai wani irin kallon tsana dayake watsama *Jana* wacce tayi mirsisi kamar ba'ita tayi maganar ba, cikin bacin rai Abba yace Na ALLAH dakai fa nake magana, Cike da takaici yace Abba maciyi amana take Ce mun fa, Abba yace kaci amanar tane shiyasa take ce" maka haka yace Abba na rantse da mahaliccina banci amanar taba, idan kuma har tana ganin ni *Habeebu* naci amanar tane, to na yadda Allah yasaka mata idan kuma ita Ce taci amanata Allah yasaka mun ya kareshe fadi cike da tsantsar bacin rai. Jikin Abba yai sanyi dajin kalaman *Habeeb,* aran shi kuma fadi yake yarinyar nan tafara kai Na ALLAH bango, kallon *Jana* yayi tareda cewa Murjanatu kinji abunda mijinki yace" KO?..tace "eh ya to inason kiyi hakuri da duk abunda yafaru, Kai kuma Na ALLAH kar kasake aikata hakan kaji ko?.. Kai kawai *Habeeb* ya gyada, Abba yace yauwa sannan ke kuma inason ki yadda da duk abunda yafadi, dama ai duk wanda yaci amanar dan'uwan sa sai Allah ya saka masa kinsan da haka ko?..tace "eh yace yauwa maganar kwana kuma dakika ce araba, dama aiko A addini idan namiji yakara aure sai yayi kwana uku adakin amaryar idan bazawara ce idan kuma budurwa ce sai yayi kwana bakwai adakinta sannan araba kwana bibbiyu hakane akeyi, ko Hajiya?..tace "eh dasauri *Habeeb* yace Abba aini banyi kwana ba kwanda akeyi ba, Abba yace wai hakane Murjanatu?..tace "eh yace to kinga daga yau zaya fara kwana dakinta saiyayi sati daya, sannan kuraba kwana biyu-biyu zaku ringayin girki idan kinyi kwana biyu itama tayi kwana biyu shikenan ko?.. tace "eh yace sai maganar Wayar ki gobe insha'allahu *"Hafeez* zaya kawo maki sabuwa kinji KO?..tace to yace yauwa. Kai kuma Na ALLAH nasan ka da hakuri don haka inason karayin hakuri ka kuma yi adalci a tsakanin matan ka kaji ko?...to kawai yace, Abba yace yauwa Hajiya KO kinada abunda zakice dasu?...tace ah! nikam ai saidai nace Allah yabasu zaman lafiya da hakuri da juna kai kuma sai karayin hakuri sosai fa, Abba yace to ameen Insha'allah zayayi, tashi ka dauki matan ka kutafi Allah yatashe mu lafiya Hajiya tace Ameen. Dasauri *Habeeb* yace su tafi kawai nizan fitane Abba yace to *Sadeeya* tashi kutafi har zatace to sai, *Habeeb* yayi mata wani irin kallo wanda yasata saurin cewa Abba niba yanzu zan tafi ba, murmushi yayi tareda cewa to shikenan Murjanatu kije zasu iske ki kinji?.. ba tareda ta Ce komai ba ta tashi fukusun-fukusun tafita, Bayan fitatar ta Hajiya da *Deeya* suka tashi suka hau sama yayinda suka bar Abba yana sake yiwa *Habeeb* fada bayan yagama yi masa fadan sannan yatashi yafita. Part din su Inna yanufa da sallama yashiga falon suna zazzaune suna fira harda *Hafeez* fuska dauke da fara'a Baffa ya amsa tareda cewa a ah *Habeebu* ne?..yace "eh Baffa ni ne mun same ku lafiya?.. yafadi yana zama lnna tace lafiya lau, cikin girmama wa ya gaida su suka amsa tareda tambayar shi ya aiki?..yace lafiya lau, nan ma saida Baffa yai masa nasiha, bai dade ba yafita. Saida ya tsaya yadauki wayoyin sa da ledar maganin da yabari a mota sannan yanufi part din *Harees.* A falon kasa ya'iske su *Feeya* kwance akan cinyar *Harees* sallamar *Habeeb* din ce yasata tashi cike da kunya, ta gaida shi bayan ya amsa sai tace Hmm *Habeeb* Awani part my sweet *"Deeya* take?..yace tana part din Hajiyarmu, mikewa tayi tareda cewa yauwa to bari naje dasauri suka hada baki sukace ina zaki?..ahankali tace gurin my sweet *"Deeya,* hararan ta *Habeeb* yayi tareda cewa baki da hankali ne kina dauke da baby shine zaki fita yanzu da daren nan?.. *Harees* mikewa yayi tareda cewa yi hakuri me Darajata ki taimake ni kibari saida safe, koki kirata a waya ma kawai sai kuyi magana kinji?..tace to ai nakira wayar "ta akashe, *Habeeb* yace kira layin "Hajiyar mu ta hadaki da "ita kice nace" tabude wayar ta idan nata so zan kiranta, tace to tareda daukar wayar ta dake kan table tanufi sama. Zama sukayi lokaci daya *Harees* yana cewa dan'uwa ya'akayi ne?.. *Habeeb* yace dai-dai, yace to ya zazzabi?..ko dayake "Queen of beauty ta kori zazzabin ko?..ya kareshe fadi yana dariya, murmushi *Habeeb* yayi me kayatar wa tareda cewa hmm aikam in fada maka koran kyau *"Leemah* ta tayi wa zazzabi nan, shiyasa nima nazo kayi mun bayanin yadda zanyi amfani da magungunan don nakori wannan ciwon da aka lakamani da wuri ko nasamu damar cin amarcina, Kai! dan'uwa *"Jana* ta zalunce ni dayawa fa ko kasan hutun one month na dauko don nazo naci amarcina da kyau, amma sai wannan azzalumar "ta lakamun ciwo wanda zaya hanani cin amarcina kamar yadda nayi buri. Kafadar shi *Harees* yafada yace kayi hakuri dan'uwa, *"Jana* Kanta a ta zalunta ba kai ba amarci kuma zakaci yadda ka keso kaidai kayi amfani da magungunan nan insha'allahu bazaka wuce two week ba karabu da ciwon kaji?..Kai *Habeeb* ya gyada masa, sannan yayi mashi bayanin yadda zayai amfani da magungunan, bayan yagama fada masa. Sai *Habeeb* yace kai Dan'uwa kasan abunda *"Jana* tace" a gaban "Abba kuwa?. yace a ah,yace hmm wai shiya kiramu yayi yai mana fada kawai sai tace.. nan dai yafada masa abunda yafaru, Murmushi yayi tareda cewa su *"Jana* manya yanzu itafa atunanin ta bakasan abunda ta'aikata ba ko?.. yace "eh dayake itadin sha sha sha ce bashi yasa har take maganar raba kwana, batasan dazuta mugun kaini bango bane shiyasa nashaki wuyan ta inba dan haka ba ai ko yatsarta bana fatan sake taba wa, balle har na sake had'a jiki da'ita wancan da Allah ya kaddare ni nayi ya'isa. *Harees* yace hakane to Allah ya kyauta to kai yanzu idan kwanan yaza gayo "kanta yaza kayi?..tsaki yayi mtww yace sai nace bana ra'ayin yi idan kuma za'a saniyi dole ne to saina gani, dariya *Harees* yayi tareda cewa dan'uwa baka da kyaufa amma dai zaka horata, yace batta kawai ai saina gasa "mata gyada ahannu kafin iddarta yacika nan dai suka cigaba da tattaunawa. Cikin daki Hajiya da *Deeya* suka kule inda

Chapter 22 of 42