Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ma had'in rayuwata ne, Sannan kuma ked'in aita dabance *Leemah*, domin kina dauke da wata irin ni'ima me dad'i dasauri tace kai Hmm na sai kace nid'i wata sweet ce ko honey, yace ai kinfi sweet da zuma. Pls *Leemah* ta taimaka mun manayi abin nan dayasa naketa zuba maki subad'i, ido tazaro cike da tsoro tace wayyo Hmm na abin nan fa akwai zafi sosai, yace l promise u yau bazaki jizafi ba har zata sakeyin magana ya had'e bakin su. _Nikam ganin haka yasa nafece ๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€domin bazan iya ganin abun nan ba lol_. *_Bayan sati biyu_* ***** Duk yadda *Jana* taso fita Don ta aikata mugun nufin ta, abin yagagara domin duk *Habeeb* yabi yatoshe hanyar hatta da bakin get yace" idan tasake zuwa ba tareda izinin shiba abakin auren ta, ita kuma idan akwai abunda ta tsana arayuwata to be wuce rabuwa da *Habeeb* ba. _Nikam nace rabuwa ta nawa kuma KO readas_? Don haka dole ta hakura gashi dai babu rashin ci babu rashin sha, amma tayi wani irin mugun ramewa tayi dubu tamkar ba *Jana* ba kasan cewar abubuwan sunyi mata yawa musamman rashin samun abun nan๐Ÿ˜ da batayi. Kasan cewar tuni ta fahimci *Habeeb* da *Deeya* sunayin abin, hakan ne yasata sake shiga wani irin ya nayi, domin bataga fuska ba balle tace itama aimata abin asalima yanzu wani irin mugun tsoron sa take ji data gashi sai taji gaban yafadi gawani azababben kwarjini dayake mata wanda kotasoyi masa magana akan abubuwan dayake ta wayanda suke mugun kona mata rai sai takasa, gashi itaba ma'abociya ibada ba balle tayi kokarin kai kukanta ga Allah ba don yaimata maganin matsalarta saidai ma tasake tura kanta ga halaka, wato ta cigaba da biyama kanta bukata kamar yadda tasa ba. Aban garen *Habeeb* da *Deeya* kam cikin sati biyun nan kuwa sun murji amarcin su son ransu, wanda ta dalilin hakan ne shak'uwa me karfi yasake shiga tsakanin su, idan kaga su sunyi kyau sunyi kiba musamman *Habeeb* da ya kasan ce yanzu bashi da wata matsala, daga b'angaren cikin sa har shimfid'ar sa, yana samun yadda yake so agurin *Leemarsa* wanda hakan ne yasata sake samun wani irin matsayi me girma a ZUCIYAR sa. **** Yau lahadi kuma yaune *Habeeb* zaya koma gurin aiki, kamar kullum idan suka tashi sai sun shiga part by part sun gaida iyayan su, KO yanzu masun shiga sun gaida su tareda sallamar su akan zaya koma gurin aiki. Ahankali suke tafiya tamkar marasa lafiya makale suke dajuna kamar zasu shiga jikin juna *Habeeb* da *Deeya* kenan, sanye yake dawani blue suit me a sakin kyau da tsada wanda yasake fito masa Da kyausa da kwarjinsa. Ita kuma tana sanye dawani blue material wanda tayi masa dinkin riga da siket, dinkin yad'an kama jikinta kad'an don haka yai mata kyau sosai saita kashe daurin zahra buhari sosai tayi kyau fuskarta sai wani annuri yake fitarwa, hannun ta rikeda _briefcase_ dinsa sunyi kyau sosai saidai kallo daya zakai masu ka fahimci sam basusan rabuwa dajuna. Saida suka isa dai-dai bakin kofar fita babban falo sannan suka tsaya, jantayayi ya rungume tsam akirjinsa yana jin SONTA da kaunar suna ratsa jini da bargon sa, yayinda yakeji kamar karya tafi yabar ta cikin sanyi murya *Habeeb* yace *Leemah* ta l will miss u so muรงhhh!, ahankali tace me twooo Hmm na pls come back soon kaji?..yace l will Insha'allah *Leemah* ta kiyi mun addu'a kinji, ahankali tace Allah yakareka dakare warsa yabaka abinda kaje nema na alkhairi, ya kuma dawo mana dakai lafiya yace ameen *Leemah* ta nagode Allah yaimaki albarka pls ki kulamun dakaki kinji?., Tace to ni maka kula mun da kan ka sosai pls karka kula kowace "mace idanka kula wata" Allah babu ruwa na dakai takareshe fadi tareda turo pink mouth dinta, dariya yayi cike da shaukin kaunarta yakama bakin ya tsotsa sosai sannan, yace karki damu *Leemah* ta ai babu macen datake da matsayin da zan kulata, yace oya we started our sing sake kwantarda kanta tayi akirjinsa yayinda hannun ta daya yake shafa lallausan sajensa, shikam sai lumshe ido yake domin yana matukar son haka ahankali tafara fadin. _Zan rayu dakai zan mutu dakai abadan Dani dakai zamu zauna, idan nace ni; ina nufin kai" idan nace kai Ina nufin ni;_ Ahankali shima yace _zan rayu dake! zan mutu dake! abadan dani; dake! zamu zauna idan nace ni; ina nufin ke! idan nace ke! ina nufin ni_; Dariya sukayi gaba daya sannan suka daga wa juna babbar yatsa, tareda fadin yessss! sannan yakarbi jakar yana fadi byeee *Leemah* ta itama tace byeee Hmm na sannan yanufi gurin mota, Dasauri Saminu yazo yakarbi jakar tareda bud'e masa kofar motar yashiga tareda sa jakar sannan ya rufe, sannan yaje yashiga tasu motar suka fita daga harabar gidan da gudu abuja tayi Kira, to mu kam sai muce asauka lafiya *Habee-Leemat*. Jiki bakwari *Deeya* tajuya zuwa cikin gida kamar zatayi kuka zuciyar ta cike dakewar Hmm dinta, takai tsakiyar falo kawai sai taga *Jana* k'idis agabanta Wanda hakan ba karami tsora ta da razanata yayiba, gawani irin muguwar fad'uwa da gaban ta yayi dasauri tafara karan to addu'ar neman tsari, sannan ta kalli *Jana* wacce ke tsaye rik'e da k'ugu sai cika take tana ba tsewa, tareda watsama *Deeya* harara. Tsaki *Deeya* tayi tareda watsa mata wani mugun kallo domin yanzu wani irin haushin ta takeji wanda tarasa dalilin dayasa takejin haka, _nikam nace kishine๐Ÿ˜_ cikin had'e fuska *Deeya* tace... *_Tau fa ๐Ÿ˜ณsaida Habeeb yatafi ๐Ÿค”to ko wata wainar kuma za'atoya tsakanin Deeya da Jana Oho!_* Muje zuwa A _*KYAUTAR ALLAH CE*_ (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [11/9, 10:06 PM] My Ameena: ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐŠ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 6โƒฃ1โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Lafiya zaki tare mun hanya?..cikin masifa *Jana* tace antare maki hanyar dan ubanki, ido *Deeya* tazaro cike da mamaki jin yadda *Jana* ta k'unduma mata zagi, cikin bala'in dayake cinta tace dan ubanki natare hanyar kiyi abinda zaki shegiya aljana tunda aka likawa "mijina ke shikenan narasa gane kansa saboda asirin da shegen uban.... takasa karasawa saboda kyakkyawan marin da *Deeya* tazuba mata, Wanda ya gigita yasata rike kumatu cike da kwantena kwantena na mamaki take kallon *Deeya*. Cikin tsananin bacin rai *Deeyar* ta nunata da yatsa tareda fadin duk abinda zaki fad'a kifad'a akaina zan iya dauka, amman banda "iyayena domin "sud'in mutane ne masu matukar kima da daraja agurin, Don haka bazan taba yadda wani mahaluki yaci musu mutunci inaji da gani banyi magana ba, wlhy bazan yadda ba KO kad'an kinji. Cikin masifa *Jana* tace kutumar uba ni kika Mara?..cikin bacin rai *Deeya* tace "eh domin kigane iyayena ba abokanan wasan ki bane, inafatan kin fahimta ai?. Cikin masifa *Jana* tace kan uba tunda kika mareni yau sai nayi maki dukan tsiya agidan nan, Gaban *Deeya* ne yafad'di jin zancen duka, amma sai bata nunaba asalima tsaki tayi tareda kokarin bita gefen ta zata wuci still kirjinta yana dukan uku, cikin wani irin mahaukacin masifa *Jana* ta finciko *Deeya* tareda cewa dun ubanki dawo ke har kin iyasa ki mareni, sannan ki wuce tab!.yariyan baki isaba wlhy ai yau sai na lahiri yafikin jin dadi agidan nan. Wani irin razanannen tsawa *Deeya* ta dokawa *Jana* tareda fadin dalla gafara mlm sakar mun riga ki naji ko?.., aikam dasauri *Jana* tasaki rigar cike da razana jikinta har yana kerrrrrrrma! lokaci daya kuma sai tsoron *Deeya* yad'arsu mata gawani irin mugun kwarjini datayi mata, *Deeya* kam ita tayi tsawar amma saida tsawar tabata mugun tsoro wanda tayi mamaki har tana fadi aranta wai itace ta doka wannan tsawar haka?.., ranta amatukar bace yayinda kirjinta yake cigaba da matsanancin bugawa, ta kalli *Jana* tareda nuna kanta da yatsa tace kinga nayi maki kama da wacce zaki taba fatar jikinta?.. Shuru *Jana* tayi takasa cewa komai domin gaba daya *Deeya* tayi mata kwarjini gawani mugun tsoron ta da yakamata, tsaki *Deeyar* tayi tareda fadin mlm kije kinemi wacce zakiyiwa dukan tsiya amma bani ba domin tab'ani dai-dai yakeda samun matsala arayuwarki, tana kaiwa nan tawuce sama zuwa dakinta hankalita kwance abinta. Yayinda tabar *Jana* tsaye sake da baki da hanci, zama tayi akan kushin jabar tareda tura hannu ta acikin wannan uban attachment din da batasa lokacin cire shi ba, abu sai tashin tsami yake mtsww kai Allah dai yarabu da kazaman mata ameen. Wani irin iska me zafi tafesar daga bakin ta tana hura hanci rainta amatukar bace tace kan uba ai wlhy tunda kikayi kuskure marina yarinya sai naci ubanki agidan nan, KO bayau ba dama *BB* kike takama dashi to yawuce Don haka kwanan nan zakigane kuren ki tadan dad'e tana sakawa da warware wa, can saita tashi ta nufi sama buguzun-buguzun. *Deeya* kam tana shiga daki tayi sauri ta kulle kofa taje ta zauna agefen gado tareda dafa kirjinta tana sauke numfashi kamar wacce tayi tseren gudu, sannan tad'aga hannun ta tana kallon kyakkyawa tafin hannun ta me dauke da zanen fulawa ja, cike da tsoro tace kai! yau nice namari "Aunty *Jana* har da yimata tsawa Kai!...amman nimafa naji tsoron tsawar nan. Can kuma sai ta kyalkyace da dariya saka makon tunowa da reaction din da *Jana* tashiga lokacin da tayi mata tsawa, cikin dariya tace Kai! Ashe nima dai *BOSS* Ce, can kuma sai tamike zumbur tareda cewa Kai! wlhy bari nazo na bar gidan nan kar tayi mun duka kamar yadda ta fada tunda taga Hmm na baya nan, kafi azo aceceni naji jiki. tana fadin haka ne tareda daukar gyalen ta yafa sannan tadauki wayar ta dake kan gado da jakarta da kuma hand out sannan tabude kofar ahankali, gaban ta yana d'an faduwa kadan tafita tareda kulle kofar ta sauka kasa atunananin ta zataga *Janar* saidai kuma bata ganta ba, Don haka tasaki ajiyar zuciya tareda fita dasauri. ****** *Deeya* Da tafita kai tsaye part din *Feeya* tanufa kwance ta'iske *Feeyar* hannun ta rikeda hand out tana karanta wa, _kasan cewa ranan Monday zasu fara jarabawa shiyasa itama *Deeya* ta dauko Nata don tayi karatun,_ Ahankali *Feeya* ta tashi daga kwance kasan cewar cikin ta yafara girma, murmushi tayi tareda ajiye hand out din tana kokarin daura dankwali, *Deeya* ta ajiye jakarta akan table tareda yaye gyalen kanta fuskarta dauke da murmushi. Tace sannun da hutawa me ciki hararanta *Feeya* tayi tareda fadin bana son iskanci fa, ba me ciki ba walla me Kai! Cike da zolaya *Deeya* tace to me kai yakike ya my unborn baby?..tace kedai ki kasani tace kefa?.. tace bansani ba Allah my sweet *Deeya* kin cika shegen tsoka, dariya *Deeya* tayi tareda zaunawa tafadin aike kinsan tsokana ajinina yake, itama dariyar tayi tareda fadin aikam nafi kowa sanin hakan. *Deeya* tace hmm ke kinsan abunda yafaru yanzu kuwa?..tace "a ah saikin fada nan *Deeya* fada mata abunda yafaru tsakanin ta da "Aunty *Jana*, dariya sukai sosai saida sukai me isarsu sannan suka tsaya. *Feeya* tace kinyi mun dai-dai my sweet *Deeya* aigara da kika yimata haka, kinsan ita batasan darajar iyayenta ba shiyasa Kai! amma fa kinyi na miji kokari dakika mari wannan shad'ikar tace hmm ai kedai bari ni kaina saida nayi mamaki kain....karar wayar tane yakatseta dasauri taciro daga jakarta *Habeeb* ne yakirata video call ganin hakan ne yasata fadi Oh! my sweet Hmm I love u l miss u so muchhhh!, ta kareshe fadi dayin dariya. Shima dariyar yayi me cike da sonta da kaunar ta sannan yace miss u two my honey *Leemah,* and Love u more than Love me Dear, cike da farin ciki tace nagode Habibina to yakake ya hanyar?... yace to gani nan dai hanya kuma gamunan a kanta tace Allah yatsare yace ameen kina Ina ne?... tace gurin my sweet *Feeya* yace Oh! my *Leemah* shine kikafito?.. me makon kiboye mun kanki um?..cike da shagwaba tace to sowee my Hmm Allah daka tafi gidan babu dadi shiyasa nazo nan kaga tun ba'aje ko'ina ba nafara kewarka KO?..., pls nidai ka dawo dawuri kaji?.. murmushi yayi me kayatarwa tareda shafa suman kanshi yace, hmm Allah *Leemah* ta nima tun bamu fita bauchi ba kewarki tafara kamani sosai, tace kagani ko tozaka dawo dawurin?.. cike da shaukin KAUNAR ta yace karki damu *Leemah* ta zan dawo very soon kinji?.. tace to nan suka taba fira sannan sukai sallama, bayan yaimata gargadin ta maida hankali tayi karatu sosai tunda taga jarabawa zasuyi, tace to tareda zuba masa addu'ar tsari. Daga nan kuma suka cigaba da fira itada *Feeya* can kuma sai ko wacce tafara karatu saida misalin karfe 4:30pm sannan tako gida part dinsu tashiga bata dad'e ba tafito tashiga part din Hajiya nan kam sai bayan isha'i sannan tafito ta nufi part dinsu dasauri tashige daki ta kulle. _Nikam nace Kai!๐Ÿ˜‚ *Leemar* *Habeeb* tun yanzu shiga bacci ko dai kina tsoron kar *Jana* ta suburbud'a kine?_ ๐Ÿ˜œ. *_Bayan kwana hudu_* ***** Tun ranan da *Deeya* tamari *Jana* basu sake hadu wa ba domin kuwa tuni suka kulla wasan yar buya, duk yadda *Jana* ta so su hadu *Deeya* Don tayi mata illa kamar yadda take qudirtawa azuciyarta, Allah bai nufa ba domin *Deeya* tana rigata tashi sannan ta riga ta kwanciya. Idan sukaje school suka dawo sai su yada zango gidan *Feeya* idanta ta so kuma sai tashiga part dinsu lnna ko tashiga part din Hajiya, sai bayan sallar isha'i sannan ta nufi part dinsu idan kuma tashiga bata iske *Jana,* Don haka sai tashige daki abinta, Waya kuma tsakanin ta da *Habeeb* kullu yisuke suna zuba soyayya abinsu wacce take Kara masu shak'uwa da kaunar juna. ***** Yau alhamis tunda ta tashi takejin aranta yau duk yadda zatayi sai taje gurin Shafa da Adonta, saida ta tabbatar *Deeya* tafita zuwa school ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ja, tayafa gyale ja sannan ta dauki wata yar karamar jar jakar sarka da yankune sai tadauki pos da key motar ta data dade ba tashiga ba sannan tafito, tanufi ma'jiyar motocin motar duk tayi kura amma haka tashiga kafin takai bakin get saita fara kuka wanda kana ganin shi zaka ga ne na karya ne, tana isa get din ta tsaya tareda sauke glassa sannan kara sautin kukan sosai. Dasauri baba megadin yafito yana gani tana kuka yace subhalallahi! Hajiya lafiya?..., cike da kukan kissa tace wlhy yanzu aka kirani aka fadamun ankai "Mamana asibiti batada lafiya, yace assha Allah yabata lafiya yafadi tareda bude mata get tafita saida ta hau kan titi sannan tasaki dariya tace bazan megadi sannan takarwa motar gudu. _Nikam nace ai ita ce banza๐Ÿ˜ lamba daya ko masu karatu_?.. *Jana* bata tsaya ko'ina ba sai gidan Shafa saidai kuma tayi rashin sa'a "Shafar bata nan don haka saita nufi gidan Ado, tana isa ana kokarin fitowa dashi zuwa asibiti kasan cewar kafatar tashi ta rure sai wari take tana fidda ruwa cikin tashin hankali tafito take tambaya abokansa suke fada mata take tace su sashi cikin motar ta suka nufi asibiti, suna isa aka fara bashi taimakon gaggawa domin sai ihu yake nan Dr yagano kafar tarub'e, don haka dole sai anyanke ta hankalin *Jana* yatashi sosai yayinda ado yaketa faman ihu shikada ayanke masa kafa, Dr yace dole sai anyanke kafar zaya samu lafiya kuma kudin aikin dubu dari,. *Jana* tace to yanzu batada kudi saidai tana abin kudi zataje tasiyar takawo ayanke masa kafar, Don yasa mu lafiya Dr yace to sannan tatafi. Dubu sittin aka siyi sarka ta kawoma Dr kudin yace gaski bazai iyayin aikin nan dubu sittin ba, tace zataje gida ta ciko kudin yace to saita kawo cikon zatayi aikin sannan ta nufi gida, tabar ado sai ihu yake yana fadin wlhy sai yadauki fansa. *Jana* tana tuki amma zuciyar ta cike take da tunanin ta inda zata samo cikon kudin daza aima ado aikin, akan hanyar ta takomawa gida ne ta tsaya bakin titi tasiya lemo da ayaba sannan tanufi gida. Tana shiga harabar gidan motocin *Habeeb* suna shigowa, bayanta kashe motar sai tafito dai-dai lokacin da Saminu yafito dasauri daga mota yabude ma *Habeeb* yafito, kafarsa sanye takeda farin takalmi jikinsa kuma wani tsaddan yadi Navy blue me sharashara don har anagani farar vest dinsa, hannun sa rikeda wayoyinsa saidai kanshi babu hulla Don haka suman sai sheki take yayi matukar kyau. Yayinda gaba daya kamshi turarensa yacika harabar gidan, wanda yasa *Jana* juyowa dasauri aikam sukayi ido hudu *Habeeb* cike da tsananin firgici Da tsoro tasaki ledar lemon suka watse takasa, tadora hannun wa akai๐Ÿ™†๐Ÿป cike da tashin hankali tabude baki zata ce.... *_Notice, daga wannan page din nadai na tura wa groups din da ake karantawa amma ba asharhi akai, wato comments wanda kunsan cewa shike karawa marubuci kwarin guiwar cigaba da rubutun sa nagode SO._*, Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [11/9, 10:07 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 6โƒฃ2โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Kasa cewa komai tayi saka makon wani irin mugun kallo da yawatsa mata me cike da tsantsar tsana da kyama, Baice mata komai ba yanufi part din su *Deeya* ran shi amatukar bace. Kirjin ta tadafe dake matukar bugawa sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tareda tsugunnawa tana cintar lemon da ayaba, zuciyarta cike da tunani me yadawo da *BB* yau?.. Shikam *Habeeb* dama yazone don yaga *Leemarsa* kasan cewar kullum da kewarta yake kwana da'ita yake tashi, duk dacewa kullum dare da rana suna waya tareda yin video call amma duk hakan be isheshi ba, kamar yauma tashi yayi yanajin matukar son ganin ta azahiri tareda son jinta ajikinsa, shiyasa ya yanke shawar zuwa ba tareda yafada mataba saboda yason yai mata surprise. Da sallama yashiga falon gaba daya suka amsa Baffa da lnna dasuke zaune suna fira har da *Hafeez,* saidai shikam badashi ake firar ba asalima bawa cikinsa hakkisa yake wato yana da'amun ne, Cike da mamakin ganinsa Baffa yace "a ah *Habeebu* ne yau?..cikin girmamawa yace "eh Baffa tareda zama kusada *Hafeez*, Baffa yace to Allah dai yasa lafiya?.. yace lafiya lau Baffa akwai wani aiki Da zanyi ne shiyasa nazo tun yau, yace to to Allah ya taimaka yace ameen sannan suka gaisa yagaida lnna ta amsa tareda yimaya hanya yace lafiya lau, *Hafeez* ya tsaya da cin abincin ya gaidai *Habeeb* ya amsa yana d'an hararan shi, sai kuma yace Baffa kuyiwa yaron nan aure yadaina cinyewa lnna abinci ta haka nan, Da sauri *Hafeez* yazaro ido๐Ÿ˜ณtareda sakin baki yana kallon *Habeeb* wanda yahade fuska tareda cewa yadai?.. ko baka isa auren bane, dasauri ya gyada kai. Aikam me lnna da Baffa zasuyi ba dariya ba, *Habeeb* yace Oh! amma ka isa cinyema mutane abinci su KO?.... Kai yadukar tareda dan turo baki, lnna tace to nidai kar adamar mun yaro na bai isa aure ba tukun, murmushi *Habeeb* yayi yana fadin Baffa kaji lnna ko wai wannan kawon yaron ne bai isa aure ba?... murmushin manya Baffa yayi yace kyalesu *Habeebu* aini tuni na samar masa mata lokacin dazan bayyana nasa kawai nakejiran Allah yabani ikon, yace yauwa Baffa yayi dai-dai Allah yabada iko suka Ce ameen, sannan ya tashi yana cewa zan shiga part din su Hajiyarmu, sukace to sannan yafita yanufi part din Hajiyarmu. *Jana* kam bayan ta tsince lemon da ayaban ta part tanufa afalon kasa ta zauna tafara cin ayaba hankalin ta kwance, saboda taga *Habeeb* bai ce mata komai ba Don haka ne bata wani tada hankalin ta ba Don yaganta, asalima remote ta dauka tareda cewa nasan wannan shegiyar aljanar bata dawo ba, Mtsww kai!, Allah yasama idan zata dawo tayi hatsari tamutu nahuta da jaraba, sannan ta kishingid'a tareda kunna kallon tafara yi ta cigaba da cin ayaba tana jifa da bawon, awani gefen kuma tana tunani ta yadda zata samu cikon kudin aikin ado. ******* A ban garen *Deeya* kuwa tuni tadawo daga school kasan cewar yau paper daya sukayi, Don haka tana gamawa tafito suka tanufo gida yau bata tsaya shiga part kowa ba direct part dinsu tanufa, Dakin *Habeeb* tashiga domin yau wani irin kewar sa itama takeji gashi tunda sukai waya dazata tafi school basu sakeyiba, takira wayar shi tafi akirga amma baije ba shiyasa duk taji ba dadi, Don haka tana shiga tanufi cikin bedroom din sa, tsaf dakin yake agyar kamshin turaren shi sai tashi yake, ahankali takarasa baki gado rigar banshi tadauka tareda kaiwa hancin ta tashaki kamshi daddad'an turaran shi me kasheji ido ta lumshe tareda sauke ajiyar zuciya tace l really miss u Hmm na pls came back soon because I want, hanan tai tafaman surutai masu cike da tsakanin kewar sa. Can sai ta ajiye riga tareda jakarta da gyale ta cire kayan jikinta ta daura towel dinsa tanufi toilet tayo wanta tafito, bayan tashafe jikinta da mai da turaruka masu kamshi sannan tabude wardrof tadauko wasu shegu riga da wando masu kyau tasa, Wandon swaga ne black da ratsin milk yanada duwatsu ajiki ita kuma rigar milk colon ce tanada igiya agaba arubuta I miss u ajikin rigar da small letter, sai takama igiyar ta kulle wanda hakan ne yabawa albarkatu kirjinta rabi damar fitowa, gaskiya tayi kyau sosai sai tasa wata bakar hula me kyau bayan tasake feshe jikinta da turare sannan tagyara gurin, tareda daukar key dakinta tafito falo. Bazato suka hada ido da juna kowani saida gaban sa yafadi, musamman *Jana,* domin batayi zaton *Deeya* na cikin gidan ba itama *Deeya* batayi zaton cewar *Janar* na cikin gidan ba, kitchen *Deeya* tanufa gaban ta na faduwa, Tsaye tayi a kicthe din ahankali ta furta wai dama ita wannan mama katuwar tana cikin gidan ne?..baki ta tabe tareda d'age ka fada tace to kotana ciki ni Ina ruwana "da'ita, can kuma sai tace to wai me nashigoyi kitchen ne?.. mtsww tayi tsaki tareda fitowa ba tareda ta kalli gurin da *Jana* take bata nufi sama danufin zuwa dakinta. Da sauri da sauri take hawa step din kamar yadda tasa ba, yayinda jikinta yake Wani irin shaking na daukar hankalin duk wani lafiyayyan Da namiji, tahau step na daya tahau na biyu ta hau na uku zata hau na hudu kenan sai wani mugun santsi yakwashe, saka makon bawon ayaban da *Jana* jefa mata, aikam tuni tayo baya zata fadi hakan ne yasa tasaki wani irin Kara me karfi tareda fadin wayyo Allah Hmm na zan fadi. Dai-dai lokacin *Habeeb* yashigo cikin azababben zafin nama yai sufa yatare ta wanda har saida guiwoyin sa suka bugi steps na biyu sannan suka zube gaba daya kasa, sai ya kasan ce shi yana kasa ita kuma tana saman jikinsa tabayan ta dasauri tajuya ta rukunkume shi, ajiyar zuciya suka sauke alokaci daya, sai kuma tasaki wani irin kuka me cike da tsantsanr tsoro had'e shagwaba, ido yarintse saboda yadda yaji kukan ta yadaki zuciyarsa hannun shi duk biyu yasa ya rungumeta sosai yayinda yaji kirjinsa yawani irin mugun bugawa, ahankali yafara Shafa bayanta cikin tsanani fargaba yace it's Ok my *Leemah* l'm here with u noting will happen to u by the great of God, cikin kukan shagwaba tace Hmm na da baka zo ba Da yanzu nafad'o yace hakan bazaya taba faruwaba Insha'allah kinji *Leemah* ta?...Kai ta gyada alamar to. Ahankali yamike da'ita ajikinsa tareda kallon gurin da bawon ayaban yake, wanda yakeda tabbacin shine yasa *Leemarsa* takusan fadowa ba don Allah yakawo sa ba da shikenan tafado da babu, abinda zaya hana batayi mummunan rauni ba. jiyayi ransa yai bala'in baci domin tuni fahimci cewar *Jana* ce ta haddasa faruwar hakan, Wani irin mugun kallo ya watsama *Janar* wacce tayi mutuwar tsaye domin batayi zaton

Chapter 29 of 42