kikaje danai maki rashin mutunci hararan kasan ido tayi masa tareda shigewa daki.
********
Koda su *Deeya*
suka fita basu yi wani dade wa ba tace tagaji don haka suka koma gida, dama iyakarsu titin anguwar su suka bi part din lnna tace zata don haka can *Habeeb* yakai ta, sannan yafito yafara ganawa da mutane.
Sosai *Habeeb* yake taimakan talakawa wanda haka ba karami kima da daraja yake samu agurin su ba, suna matukar kaunar shi tareda yimasa addu'ar gamawa da duniya lafiya.
Bayan ya sallami kowa sannan yashiga toilet yai wanka yafito yashirya yakoma gurin aiki, kamar karsu rabu shida *Leemarsa.*
Inda suka cigaba da zuwa school itada *Feeya* kasan cewar tuni takoma dakinta, sosai suke renon ciki *Deeya* da kuma kula da Affan wanda yai bulbul abinshi yakuma fara wayo, tunda yasan kamshi maman shi dana *Deeya* idan ba hannun suyake ba kona Baban shi sai yafara kuka,
Haka suke gudanar da al'amuran su gwanin sha'awa, har suka fara rubuta test sati biyu tsanani suka fara jarabawa.
********
*_Bayan sati daya_*
Ranan alhamis da misalin 3:00pm *Habeeb* ya'iso Bauchi", inda ya'iske *Deeya* tashirya masa lafiyayyan abinci me rai da lafiya bayan yayi wanka Wanda tare sukayi,
Sannan
ya shirya cikin kanana kaya Riga blue wando baki sunyi masa kyau ita kuma tasa wata doguwar riga blue, tayi rolling da bakin gyale akanta tayi kyau sosai,
gaskiya cikin jikin taba karamin kyau yakara mata ba,
Bayan gama cin abincin da yaita zuba mata santi tareda samata albarka, sai tara ka shi part by part ya gaida su sannan suka koma part din.
Tana kwance akan cinyar shi cike da shagwaba tace sweet Hmm na nidai gaskiya idan muka gama jarabawa, zan koma part din Hajiyarmu har saina haihu murmushi yayi yace kice zamu koma dai,ido tazaro tareda ce akai! Hmm na harda kai?..
yace "eh mana taya zan iya zama ba tareda ke ba umuh?..dariya tayi tace nimafa hakane to saida kuma Hajiyar bazata barka ba fa, yace karki damu my honey *Leemah*, idan tagana like dole ta kyaleni gurin zuma ta, dariya tayi tace kai! sweet Hmm na sai kace chingam?..
yace humm aini nafi chingam mannewa indai agurin kine ya kareshe fadi tareda yimata kiss agoshi, sannan yace yanzu yaushe zamu gama exam din?..tace ranan Monday karfe3:00pm samu shiga pepar yace ok Allah yabada sa'a tace ameen, har hutun *Habeeb* yakare suna manne da juna.
Ranan lahadi 2:30pm yafito cikin shirinsa har zaya shiga mota sai wayar sa tayi kara, ahankali ya duba sai yaga no ba suna mamaki ne yakama shi ganin cewa layin dayake amfani dashi yanzu na airtel ba kowa ne yasan shiba, amma sai gashi ankira shida wata sabon no da bata cikin layin kwatakwata don haka sai yadaga dasauri wata muguwar dariya yaji ansaki,
murmushi yayi domin yaga ne ko wanene don haka sai yakoma gefe tareda cewa ah! Kai! aboki na ina kashiga ne kwana biyu?.. inata ne ma layin ka don nayi maka godiya akan fadamun dakai Junior ba 'Dana bane, gaskiya nagode maka sosai, kai! abokina *Jana* taci amanata dayawa saidai nabarta da Allah amma bazan iya cigaba darike mata shegen 'Dan taba, shiyasa na dauke shi na kai mata ta Kai shi gurin ubansa.
Dakarfi Ado yace mekace"?..kasan cewa tunda *Habeeb* yafara magana yai mutuwar tsaye saboda tsabar mamakin jin abinda yake fadi wanda yasashi cikin rudani tareda fara tunanin to kodai yayi kuskuran lambane?..., saidai kuma babu kuskure tabbas senate *Habeeb* ne, don haka Cike da firgici yasake cewa kace ta kai "shi gurin ubansa?..wani irin murmushi *Habeeb* yayi yace "eh abokin...
kitttttt! Ado ya yanke wayar.
Fuska had'e *Habeeb* yace banza dakiki "dakai da ita" aisai kungane kurenku", dasauri yaje Saminu yabude masa mota yashiga suma sukaje suka shiga suka ja dama me gadi yabude masu get suka tafi da gudu sai ABJ.
Cike da tsananin tashin hankali Ado yashiga gida *Jana* tana kwance a falo tana bacci, sai jitayi ansheke mata wuya cike da wahala tabude ido aikam taga Ado rikeda wuyanta yana kokarin aikata lahira,
yayinda idon shi yaikamar garwa shin wuta wanda gani hakan yai mugun bata tsoro, cike da masifa yace gidan uban wakika kaimun 'Dana?...ido ta zaro cike da tsananin wahala tareda tsoro da kyar tabude baki tace....
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenat๐น
[11/9, 10:12 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
7โฃ4โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
Wani Dan kuma?...cikin masifa yace ke! mlm karki nemi raina mun hankali akwai wani 'Da ne tsanani na dake bayan Junior?... kaita girgiza alamar "a ah, yace yauwa to gidan uban wa kika kaishi?...tace ah! yana gidan *BB* m....takasa karasawa saka makon wani irin mugun tsawa daya doka mata, tareda cewa keeeeee! *Jana* banason iskanci fa kinji ko?...zaki fadamun inda kika kaimun 'Dana kosai nayi maki bugun mutuwa agidan nan?...
Keeee! hattara wlhy akan Junior Ina iya kashe mutun don haka fadamun inda 'Da na yake maza kafin na'aikaki lahira don wlhy Ina iya kashe ki, domin yanzu nafi son "shi dake kinji.. cike da tsoro tace "a ah wlhy "Junior yana gidan *B...* kyakkyawan marin da yashara mata ne yahana ta karasawa, baki tasaki cike da tsananin mamaki take kallon shi cikin masifa yace nizaki karya ta?...yanzu nagama waya dashi *"BB* ya tabbatar mun dacewa yakai maki Junior kin kai shi gidan "ubansa, dama yanada wani Uban ne bayan ni?....
Cike da tsoro tace Ado kana nufin *"BB* yasan "Junior ba 'Dan sa bane?.....
Cikin masifa yace "eh yasani domin tuni na fada masa wani irin ihu tasa tareda ture hannun shi daga wuyanta, aikan tuni yanzu be kasa sai kuma tayi kukan kura ta chakumi kwalar rigan shi, cikin masifan dabai taba sani tana dashi ba tace haka mukayi dakai?...Cike da mamaki ya kalle ta sannan yakalli kwalar rigar shi data rike fuska had'e yace keeeeee! ni tsaranki ne dazaki cimun kwalar riga?...
Cike da tsiwa tace na cidin kuma aiba haka mukai dakai ba, don me zaka fada masa Junior ba 'Dansa bane eyeee?....yace nafada din sakarmu riga tace wlhy bazan sakiba saika fadamun dalilin dayasa ka fadama "shi, yayi-yayi tasa kar masa kwalar riga takiya.
Aikam yashiga kauranta sosai yake dukanta yayinda itakuma take kaimai yakushi dacizo kamar wata karya, amma kuma bata sake shi ba shikam sai lakadarta yake tamkar yasamu jaka saida taci wuya sannan tasakeshi tana dura masa zagi ta uwa ta uba, bakinta yasake kaima naushi aikai saiga jini da majina yace bazaki daina zagina ba KO?..
Cike da azaba tace Allah ya'isa shege mugun kuma bazanyi auren ba mlm ka sake ni kaji ko?...
Murmushin mugun ta yayi yace aure kam yanzu kika farayin shi don haka zance saki ma bai tasoba, yafadi tareda kokarin zare belt din wandon shi, ido tazaro cike da tsoron abinda yake shirinyi. dariyar mugunta yayi sai kuma yahade fuska yace shin zaki fadamun gidan ubanda kika Kai mun yarona kosai nayi maki mummunan illa tukun?...cike da tsoro tace wlhy Ado bankai "shi ko'ina ba yana can gurin shi idan kuma ka nagani karyane to kaje gidan mu ka tambayi su Dija.
Shuru yayi yana kallon kwayar idon ta yanason gono da gaske take bata kai Junior ko'ina ba, cikin tsawa yace ki fadamun gaskiya fa tace wlhy yana can gurin *BB,* yace humm! wlhy *Jana* idan nagane karya kikai mun zakisha mamaki abinda zanyi maki, cikin kwantar da murya tace Allah ado bakarya nakeyi maba.
Mai da belt din yayi tareda zama cike da mamaki yace wato karya yaimun kenan KO?...tace to lallai kam yayi maka karya domin ni bai kawo mun shiba wlhy, yace kut! idanko haka ne yadauko ma kanshi dala ba gammo, tace to Kai ado meyasa zaka fada masa kaga yanzu karusa mana shirin mu.
Yace kyale shi ai akwai wani shirin da zanyi masa dasauri tace dagaske adona yace wlhy kuwa matso kinji, dasauri ta matsa kusa dashi sukayi kuskus dasuri tace da gaske?.. yace Allah tashi ki shirya kije tace to tareda tashi tashiga daki don ta shirya din.
********
*Deeya* kam su *Habeeb* na tafiya tafito tanufi part din lnna, da sallama tashiga falon atare suka amsa lnna da Baffa dake zaune suna fira, zama tayi kusa da Baffa tareda fadin sannu Baffa na yace yauwa *KYAUTAR ALLAH* sannu *Habeebun* yatafi ko?..
tace "eh yace to Allah yakai su" lafiya tace ameen sannu lnna ta, tace yauwa kema sannu amma dai kinsan ni lnnar *"Safeeya* ce ba lnnarki ba KO?...baki ta tabe tareda kallon Baffa wanda yaketa faman murmushi, cike da shagwaba tace Baffa kaji lnna KO?...cike da farin ciki yace kyaleta ai kema kinada ni da kuma Hajiya KO?..murmushi tayi me kayatarwa Sannan tace "eh kuma da sweet Hmm Na me Sona dayawa dayawa ko Baffa na?...
yace tabbas, baki lnna ta tabe tareda fadin humm! to aisai ki fada ma wanda baida me So domin nidai Ina dasu ga dayan me Sona nan kusada ke kinji.
Dasauri ta kalli Baffa cike da shagwaba tace Baffa aikafi so na ko?....murmushi yayi tareda fadin sosai ma, dariya tayi tareda tafa hannu tace eyeee Baffa na yafisona murmushi lnna tayi tareda girgiza Kai tace Allah ya shirya ki *KYAUTA* yanzu ke baki jin kunya?...kina kokarin haihuwa amma sai kina maida kanki yarinya, dasauri tace Baffa don Allah aini yarinya ce ko?...
Cikin dariya yace jagaf kuwa tareda mikewa yace bari nafita zamuje anguwa dasu Alh, lnna tace sai kun dawo *Deeya* ma tace sai kun dawo yace Allah yasa tareda fita.
Cike da shagwaba *Deeya* takalli lnna, tace lnna don Allah kidan matsa mun kafafuna ciwo suke mun, hararan ta tayi tareda fadin *KYAUTA* kin rainani KO?...tace Kai! Inna ta har abada babu rai ni tsanani mu, tace sai zallar shagwaba KO?...dariya tayi tace to lnna idan banyi maku shagwaba ba wa zanyi nawa?...
tace sai kiyi ma mijinki tafidi tareda daukar kafar tadora a cinyar ta tafara matsa mata ahankali.
Ido ta fara lumshe wa cike da jin dadi tace humm! lnna ai shagwaba nake zubawa sweet "Hmm na kamar ba gobe, lnna tace yayi kyau gobe kuma akwai ta tana nan zuwa sannan ita wannan shagwaba ai ajininki take nidai Allah yara baki da wannan ciki lafiya ciki wata bakwai amma kamar wata tara,
Ahankali tabude ido cikin sanyi murya tace ameen lnna Allah
ni kaina cikin nan yafara damu na sai nauyi, lnna dama haka masu ciki suke ji?...murmushi lnn tayi tace duk abinda kikeji hakan nan kowace uwata takeji alokacin datake daukeda cikin 'Danta, cikin sanyi murya tace lnna inason ki dayawa don Allah kiyafe mun duk abinda nayi maki kinji?..Allah kwana nan sai nayi tajin gaba na yana faduwa kamar wani abun zaya same ni.
Dasauri lnna ta kalle ta sai duk ta ga tayi kalar tausayi itama sai ta tsinci kanta dajin faduwar gaba tareda wani irin tsoro, amma sai tadanne don kar tadagawa *Deeyar* hankalin don haka sai tayi murmushi tace niba kiyi mun komai ba idan ma kinyi mun nayafe maki sannan babu abinda zaya faru, insha'allahu lafiya zaki haihu kamar yanda yar'uwarki ta haihu don haka ki kwantar da hankalin ki kinga ba'ason me ciki tana sa damuwa aranta kinji ko?... tace to lnna Allah yasa tace ameen.
Dai-dai lokacin da *Feeya* tashigo da sallama Affan yana rungume akafadar ta sai kuka yake, lnna Ce ta amsa sallamar itakam *Deeya* hankalin ta yana kan Affan dayake canyar ihu, dasauri *Feeya* tamika mata shi tareda fadin karbi yaron ki tun dazu ya dameni da shegen kuka Kai! haba.
Karban shi tayi tareda fadin Oh! Sorry my Affan boy what is wrong with you umuhh!?,sai kuma tafara hura masa iska kunne aikam take yai shuru sai yana sauke ajiyar zuciya, lnna da *Feeya* kam dariya su kayi lnna tace Kai! kaga 'dan neman da duk yacika mana kunne da kuka, *Feeya* tace humm kedai lnna bari nayi feeding din shi har nagaji shima lallashi nayi har nagaji be yi shuru ba shine nace kai! yaron nan baiji kamshi Uwata sa bane yau shiyasa ya dameni da dan karan ihu.
Dariya sukayi dukkan su
sannan *Feeya* ta zauna kasan cewar dama tana tsaye ne, bayan tagaida lnna sai kuma suka fara fira.
******
Da msalin 4:300pm *Deeya* tafito part din lnna ta nufin part din ta duk abinda tasan zata bukata tadauka sannan tanufi part din Hajiyarmu, domin tace daga yau bazaya sake koma part din taba sai bayanta haihu.
Tana shiga *Hafeez* zaya fito dasauri tace Hmm *Hafeez* don Allah ka kwasomun akwatunan kayana kaji?...yace ah! Kai har anyi tashin kenan?...tace "eh ka dauko mun don Allah, yace angama *KYAUTAR* bera, cike da shagwaba tace Kai! Hmm *Hafeez* banaso fa.
Dariya yayi tareda fadin sorry to kawo wannan nafara kai maki sama Hajiyar taki tana can, tace to tareda mika masa jakar laptop dinta da kuma wasu tarkace acikin wata jaka saida yakai mata, sannan yafita don sauko Mata akwatayyan.
ita kuma ta haye sama dakyar inda ta iske Hajiya zaune tana kallo, zama tayi kusa da'ita tareda fadin washhhh! Hajiya ta nagaji da hawa saman nan, cike da tausayi tace sannun hali dubuna tace yauwa. nidai wannan zaryar tafara isata tace Hajiya ta ai nadawo kenan nima duk nagaji wlhy tace to ai yafi.
To yakafar tana rage ciwon?..tace "eh da sauki ai nasamu lnna ta dan man matsa mun tace sannu kawo mugani, Ahankali tamike mata kafar ita kuma tadora akan cinyar ta tareda fadin sannu aima naga yau kafar ta dan sauka, tace "eh suna Cikin haka sai su kaji sallama dukan su suka amsa tareda dago kai dasauri saka makon jin wata murya,
Cike da mamaki Hajiya tace "a ah maraba yau Murjanatu ce agidan na mu?... cike da kissa tace "eh wlhy sannun Hajiya tafada tareda zama akan kushi, sannan tagaida Hajiyar ta amsa tareda tambayar ta ya me gidan ta?..tace yana lafiya, Hajiya tace shine tayi aure bata fada masu ba tace wlhy abin ne yazo akurarren lokaci, tace Allah sarki to Allah yabada zaman lafiya tace ameen.
Sannan suka gaisa da *Deeya*
cike da sakin fuska tace mata ashekin tsufa ne haka?...murmushi tayi ba tareda tace komai ba domin ita haka kawai taji gaban tana faduwa da ganin *Jana,*
Su lili ne suka shigo da sallama ganin *Jana* yasa suka ce lah!Aunty *Jana*
oyoyo suka fadi tareda karasawa gurin ta, cike da farin ciki ta riungume su bayan sun gaida ita sai Lili tace Aunty *Jana* muya ta zuwa gidan Dija bachinan, ina kikade?...
tace wani guri ne ai nazo nace idan kunzo akawo Ku, dasauri Junior yace Aunty *Jana* zan biki tace to yace Lili Daddy kema zakin bita?..baki ta tabe tareda cewa "a ah badan bita ba ni gurin Aunty *Deeya* na da Hajiya zan chaya, yace nidai zanbita Hajiya zanbi Aunty *Jana* kinji?
tace to ai badamuwa tunda kuna hutu barina dauko maka kayan kasai kaje ka kwana mata biyu,
Bayan takawo masa kayan har sunyi sallama zasu tafi sai tace da *Deeya* tabata lambar wayan ta, shuru *Deeya* tayi nadan wani lokaci can kuma sai tayi murmushi tareda cewa to kawo wayarki nasa maki,
tace lah! nabar wayar gida tana chaji saida ki rubuta mun atakarda idan naje saina sa awayar tace to Junior dauko mun paper da biro, yace to bayan yakawo mata ta rubuta tabata sannan tayi masu sallama.
Junior yana tayima Lili bye bye itama yana yimashi har suka fita, kasan cewar sun rakasu har bakin kofar fita sannan suka koma sama.
*Jana* kam Cike da farin ciki suka isa gida Ado na zaune akofar gida,
yana ganinsu yataso dasauri yatare su fuskarshi cike da farinciki yakama hannun Junior dasauri Junior yafisge hannun shi tareda hararan Ado, sai kuma yaturo baki tareda cewa Aunty *Jana* kice kar wannan Almajirin yasake tabani hannun shi akwai dotti ido tazaro cike da tsoro tace.....
*_Barkan mu da Jumma'a._*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
( Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenat๐น
[11/9, 10:12 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
7โฃ5โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
Kai! Junior shine fa Daddy ka....dasauri yadaga kai ya kwalalo mata ido cike da mamaki yace Kai! Aunty *Jana* wannan fa bashi ne Daddy Mu ba, ai Daddya yatafi abuja dazu.
Sai kuma yamaida kallon shi kan Ado ya harare shi tareda turo baki, yace ai bakai! ne Daddy mu ba kai! almajiri ne, irin wayan da Daddy yake ba sadaka yakareshe fadi tareda sake turo baki.
Dasauri *Jana* tace Kai!Junior zan mare kafa.... Shikam Ado mutuwar tsaye yayi tsabar mamakin jin sunan da Junior yakira shi da shi wai almajiri, cike takaici yafinsgo rigar Junior tareda fadin Kai! dan Uwarka nine almajiri?...dasauri Jana tafisge shi tareda nufar cikin gida dashi,
Kwaf! yayi tareda bin bayan su zuciyar shi cike da bakin ciki, tareda jin tsanan tsanan tsanar *Habeeb* aranshi fiyeda kullum.
*Jana* kam suna shiha ta zauna tareda zaunar da Junior kusada ita cikin kwantar da murya tace Junior wannan shine Daddy ka shikuma wancen Daddy Lili ne kaji?...kai ya gurgiza tareda mak'e kafada yace umuuuh! nidai ba Daddy na bane, cikin tsawa tace nafada maka shine Daddy.
Kuka yafashe dashi tareda fadin shidai ba Daddy shi bane dai-dai lokacin da Ado yashigo, cike da masifa yace dan Uwarka kokaki kokaso nine ubanka shi ba ubanka bane eheee!, ke! kuma kiyi gaggawar sanar dashi nine ubanshi ba wancan ba banzan ba yakareshe fadi tareda zama rai bace.
Junior kam sai kuka yake yafadin shi Ado ba Daddy shi bane *"Habeeb* ne Daddy shi, itakam *Jana* sai aikin lallashin shi take.
*_Nikam nace Oho! can takwaye maku, wlhy abinda ke faruwa yanzu kenan yawanci wasu ya'yan wlhy shegu ne da uwayan su suke kwaso Cikin su awaje sai suza gida su haifawa mazajen su, humm! to wlhy kusani dai-dai dakwayar zarra yaron yaci namijin ki gobe kiyama Saikun biyashi, Allah ka tsare mu da aikata wannan aiki ka kuma tsare mana imanin Mu ameen._*
*_Washegari Monday_*
********
Kasan cewar sai karfe 3:00pm *Deeya* take da exam shiyasa tunda tayi sallar asuba tayi karatun al'qurni me girma, sai takoma ta kwanta bata tashiba sai 10:15am ta tashi jika asanyaye kasan cewa dama jiya bata kwanta dawuri ba, saboda sun dade sunata fira itada *Habeeb*.
Bayan tayi wanka ta shirya cikin wata dakakkiyar shadda doguwar rigar me ruwan gwal, tasha aikin wuta tayi mata matukar kyau bayan ta kashe daurin dankwali, sai tasake feshe jikinta da turaruka masu asalin kamshi, sannan tafito don takarya kumallo.
Zaune ta'iske Hajiya afalon sama, kallon ta tayin tareda yin murmushi tace Hali dubu na antashi?.. Kaita gyada alamar "eh,
Tareda karasaw ahankali ta zauna kusa da Hajiyar tareda dora kanta akafadar Hajiyan, Cikin yanayin ta na shagwaba tace Hajiya ta yinwa nakeji.
Tace aidole kiji yinwa irin wannan bacci yanzu fa karfe 10:30 sai shiga dubaki nake amma baki tashib, sannan shikuma mijinki sai kirana yake awaya yana tambaya ta lafiya yanata kiran wayar ki akashe, nace bacci kikeyi yanzu dai kinga ga karin kumallon ki idan kiyin sai kije ki kunna wayar ki ku gaisa kinji KO?...
murmushi tayi tareda fadin to. Sannan Hajiya ta dauko wani dan karamin filas dake sama wani faranti da kula da filet harda chokali me fork, filas din tabude cikin cup din shi ta tsiyayo tea hadadde sai kamshi kayan yaji yake, mika mata tayi tace shanye bamusu takarba ahankali take sha harta shanye tamika mata cup din,
Sannan ta dauko kulan tareda filet tabude arish ne aciki soyayye dayaji kwai kasan cewar yanzu dashi take karin kumallo, zuba mata tayi afilet din tareda mika mata tace oya yimaza kicinye karba tayi cike da shagwaba tace Hajiya ta wannan din yayi yawa, murmushi tayi tace anya kina jin yinwa kuwa?...tace "eh tace to cinye kiban filet yar albarka,
Cike da farin ciki tace to Hajiya t tareda fara cin arish din.
Bayan tagama sai Hajiya tace to tashi kije ki kunna wayarki ku gaisa da mijinki, murmushi tayi tareda cewa to harda tamike sai yafasa dasairi Hajiyata kalle ta tace lafiya?..
Cikin sanyi murya tace Hajiya ta yau nayi wani mafarki dayaba ni tsoro wasu mutane suna bina da gudu zasu kama ni su kasheni, sai inata kiran "Hmm na da ke dasu "Baffa kuzo ku taimakeni amma duk baku zo ba, sai canga Hmm na yazo zaya taimakeni sai zasu kashe shi saina farka, Allah Hajiya ta dana farka tsoro yaka mani har naji hankalina yatashi sosai.
Shuru Hajiya tayi tabbas itama taji tsoron mafarkin aran ta saida bata nuna mata ba, murmushi tayi tace to ke halin dubuna inban da abinki ai Allah zaki kira bamu ba, domin shine zaya taimake ki aduk halin daki ka shiga, tace nakira shi tace to ki cigaba dakiran Sannan karki tada hankalin ki, wani lokaci mafarki baya zama gaskiya kedai ki kasance cikin addu'a akoda yaushe domin itadin takobin muminice,
koda wani abu zaya sameka sai ki ga albarkaci addu'ar da kake yi Allah yatsare ka, saidai kuma ita kaddarar mutun baya taba iya hanata kunsatar sa don haka tashi kije, tace to jiki asanyaye tamike ahankali tanufi daki tanajin Wani iri ajikinta.
******
Aban garen su *Jana* kam Junior kwana yayi yana kuka domin daga baya cewa yayi shi saidai Aunty *Jana* ta maida shi gida, don haka kafin gari yawa zazzabi yarufe shi da Ado yanata masifa dayaga masifar batayi sai yakoma lallashi, haka dai suka kwana.
bayan *Jana* tayi masu karin kumallo sukaci itada ado shikan Junior bai iya cin ba, domin bai saba cin irishiba don haka wanka tayi masa ta shirya shi sai Ado yace kinga inada dari biyu bari na kaishi chamis tace to, yadauke shi yakaishi chamis akai masa allura tareda bashi magani.
Sannan suka dawo zaune suka iske ta tanajiran dawowar su, dakyar yasha magani sai kuka yake yafadin zayaje gurin Lili da Hajiya da Aunty *Deeya,* cike da tausayin shi tace Ado kodai na mai dashi ne?...
dasauri yace ina?... tace gida kaga yaki kantarda hankalin shi, wani mugun kallo yawatsa mata tareda cewa aibaya da wani gidan dayawu nan dan haka dole za yakwantar da hankalin shi bari dai yaji sauki, Cikin sanyi jiki tace to Allah yabashi lafiya yace ameen tace gashi ma bai ci komai ba yace eh wlhy Sannan tamike tareda cewa bari naje nai wanka yace to nima zan fita nasamo masa wani abin yaci tace to..
Saida yaji motsin zubar ruwa alamar tafara wanka sannan yamike yanufi daki tareda fadin banza anfada maki ni dakiki ne irin ki jakarka kayan Junior yadauko, yafito dago Junior yayi wanda har yafara bacci yafarka yana yamutsa fuska kamar zaya yi kuka dasauri cikin kuma kwantar da murya, yace yishuru yarona kar kayi kuka zakasha ice cream da sweet?..
kai ya gyada alamar "eh tareda fadin zaka kaini gurin "Lilin Daddy mu kalli cartoon?.., dasauri ado yace "eh tareda daukan shi suka fita.
Koda *Jana* tafito bata ga Ado da Junior ba bata damu ba asalima cewa tayi Oh! tareda Junior suka fita, murmushi tayi yi sannan tashiga daki ta shirya tafito ta zauna tsawon wani lokaci su Ado basu dawoba sai tamike, tareda fadin kai tunda suka" kai har wa haka to ba yanzu zasu dawoba bari nayi sauri kafin su dawo ta shiga daki can tafito hannun ta rikeda waya zama,
tayi tareda fara daddan wayar takai kunnan ta can sai naji tafara fadi "eh yafita to saika zo amma fakayi sauri sannan ta kashe wayar, bata dade dagama wayar ba sai akayi sallama tana jin muryar tace a shigo aikam take aka shigo.
๐ณido nazaro ganin Alh Barau nace kuttttt!
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 42