Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da zatabi, saida sukai tafiya sosai domin sun kama hanyar fita gari sannan yace tayi parking agefen titi jikinta narawa tayi, cike da tsoro tace don Allah kuyi hakuri Ku kyaleni na tafi gida duk abinda kukeso hmm na zaya bak.... tsawa yadaka mata tareda fadin ke! fito jikinta narawa tafito tallabe da mara domin sosai yake murd'a mata, bakinta dauke da addu'a shima yafito sannan suma biyun dake bata suka fito, kallon su yayi yace ku rufe mata ido da wannan yafadi tareda jefama su wani bakin kyalle, bayan sun rufe mata ido sai suka turata bayan mota tareda sata tsakiya sai guda yashiga ya ja motar suka nausa cikin daji saida sukayi tafiya me nisa sannan suka tsaya bayan wani kango sufito itama sukafito da'ita suka shiga da'ita cikin kangon. ********** Caf....yau kam ado ya gwadama *Jana* boni domin tuntana ihu harta bari amma baifasa dukanta ba tareda kusantar ta, har saida yaga tabar numfashi tukun sannan yadaga ta tareda fadin shegiya karamar yar'iska, sannan yasa wandon shi tareda daukar sandar shi yafita. ya tsaya baki kofar gidan yaciro wayar shi daga aljihun wandon yakira tareda kaiwa kunnan shi, yace mangal inafata kungama aikin dana saku?...banji abinda akace daga can ba saidai naji yace yauwa aikinku yayi kyau sosai to kujirani gani nan zuwa yanzu nan, sannan yakashe wayar yatare mashi yahau nima dasauri natare mashi nahau nabishi don nakwaso maku rahoto..๐Ÿ˜œ **** Aban garen escorts din da *Habeeb* yaturo sudauko *Deeya* kam hankalin su yayi mugun tashi, kasan cewar sun duba gaba daya makarantar basu ganta ba basu kuma ga motar taba, sun tambaya ance tazo tafita sun kuma kira gida kota koma ance a ah bata koma ba, hakan ne yasa suka kira *Habeeb* suka fada masa basu ganta ba Cikin tsawa yace wani irin maganan banza suke fadamasa haka?... bayan yanzu suka gama waya da'ita don haka su duba mashi matarshi sukaita gida, idan suka bari wani abin yasa meta sai yayi mugun saba masu, tunda dagangan suka barta tafito ita kadai. Wasa-wasa basuga *Deeya* ba, hakan ne yasa suka sake kiran sa suka fada mashi sufa basuga madam ba hakan ne yasa hankalin shi yai mugun tashi kasan cewar yana takiran wayar ta ba tadauka ba don haka yafara tunanin to me ke faruwa da *Leemarsa*?.. Ado kam suna isa yabiya me mashin kudin sa sannan yanausa cikin dajin, ya'iske yaron daya sai zagayen kangon yake ganin adon ne yasashi karasawa gurin sa dasauri, yace Yauwa mangal aikin ku yayi kyau sosai cikin wannan arniyar motar kuka ganta ko?... wanda akakira da mangal yace "eh Oga tana cikin kangon tareda su jagu ga wayar ta, da muka karba saikira ake amma bamu dauka ba ado yakarba wayar tareda juya ta yace yauwa mangal gara da baku dagaba muje ciki nafara aikina. Suna shiga yace su bude mata ido bayan sun bude mata idon sai Ado ya kura mata jajayen idon shi, wanda suka sake tsoro ta *Deeya* taji kamar fitsarin daya matseta zaya zubo tsabar tsoro, Cikin tsananin tsoro tace don Allah kuyi hakuri karku cu...Cikin tsawa ado yace shittttttt! hakan yasata saurin yi shuru tareda kama bakinta hawaye kuwa tuni yagama wanke mata beauty fice dinta, wayar ta yamika mata tareda cewa karbi wayarki ki kira mun wannan banza miji naki, KO kuma yanzu na watse maki Kai yakareshe fadi tareda fisge bindigar hannun mangal, yasaita kanta kuma kibude kara naji kinji ko?...cikin tsananin tsoro tace to tareda karban wayar jikinta sai rawa yake ta lalubo layin *Habeeb,* Wanda yana gani kiranta saida ya sauke ajiyar zuciya taji yayinda yaji wani irin mugun faduwar gaba, saida ya tsinke sannan yakira ta dasauri tadauka tareda sakin wani irin kuka me ban tausayi wanda yasa *Habeeb* yaji kirjinshi ya tsanan ta bugawa don haka dasauri yace ya akayi ne?...honey *Leemah* ta kina inane?.. inata kiran ki baki daga waya ba, kuma su joy sunzo daukar ki amma basu gan kiba Ina kika shiga ne?... har zatayi magana sai ado yayi sauri karbe wayar tareda fadin ai munzo tun dazu mun tafi da'ita, sai kuma yasaki wata muguwar dariya Wanda tasa *Habeeb* mikewa tsaye a matukar razane Cikin tsananin tashin hankali yace... *_Slm masu karatu don Allah kuyi hakuri kwana biyu banda lafiya ne shiyasa_* Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน [11/9, 10:12 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 7โƒฃ8โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Wanene Kai?..mene kuma hadinka da matata?... wata mahaukaciyar dariya ado yakara saki, tareda fadin ah! haba abokina kace baka gane murya taba?.. Kai haba dai ninefa abokin nan naka...wanda ka kama da matar ka agidan ka suna jin fadin su, kayi mashi mugun dukan da har yasa narasa kafa ta daya, tabbas nasa yanzu kam kaganeni KO?.... Ido *Habeeb* yarintse domin jiyayi wani irin kululun bakin ciki ya turnuke masa kahon zuci, aran shi yake fadin taya za'ai namanta da dakai?... banza fasikin mazinaci dakiki mutu kawai, wato duk abinda nayi maka bai isheka ba KO?... Humm shine saida kasake shigowa rayuwa ta akaro nabiyu ko?..saboda kaidin dakiki ne jaki ko?...humm tabbas wannan karon kayi mugun kuskuren sake kulla halaka dani domin kuwa zanyi maka abinda har ka mutu baka manta da *Habeebullah* arayuwar ka ba daga kai ko har abokiyar watse warka. Ado ne yakatse mashi zance zucin dayake tareda fadin yadai abokina kagane ni KO?... ahankali *Habeeb* yabude idon shi aikam tuni sun kada sunyi jajir ran shi yayi bala'in baci saidai bai nuna ba, asalima Cikin matukar basarwa yace Oh! sorry abokina nagane ka to ya'akayi ne?.... Cikin matsanancin mamaki ado ya kalli su mangal wayanda suma mamakin jin abinda *Habeeb* yafada yakashe su tsaye, Cikin masifa ado ya damki kan *Deeya* aikam tasaki wani irin kara azaba wanda yasa *Habeeb* yai saurin rinte ido, aranshi yace zakaci uwar ubanka idan muka hadu jaki kawai. yace Ke! dan ubanki ba mijinki nace kiran mun ba eye?...cikin kuka tace wlhy shine nakira maka, dasauri yace kai! wai dawa nake magana ne?... *Habeeb* kam aran shi yace banza dakiki ashema bai gane murya taba jaki kawai, afili kuma cikin izza da isa yace kana magana ne da *Senate Habeebullah Hashim soro*. Ajiyar zuciya ado yasaki tareda fadin yauwa aidama shi nakeson magana dashi, *Habeeb* yace to inajin ka fadamun saidai karka cemun *Jana* batakai maka d'anka ba?.. domin kasan fa nagane shidin d'anka ne, cike da mamaki ado yace ah! ainasan kagane kuma yanzu haka d'ana yana tareda ni, *Habeeb* yace yayi kyau to amma yanzu kuma wani abin ne yarage tsakanin mu?.... Ado yace daukar fansa, *Habeeb* yace au! haba dai?...yace kwairai, yace ayya aboki na to koshi yasa ka dauke mun Mata ta umuh?..dariya ado yayi sosai sannan yace "eh fa ashe dai kagane?... yace abokina kenan to aikasan kwakwalwar ba daya bace shiyasa na gano nufin ka, saidai ba akan matata yakamata kadauki fansa ba akaina ya kamata kadauki fansar ka, to amma badamuwa dani da'ita abu daya ne yace yauwa to aisani hakan ne yasa na saceta. haka ne to yanzu fadamun mekake bukata?... kudi sunake bukata nawa?..miliyon goma yace zanbaka shabiyar yanzu fadamun inda kake saina kawo maka kudin kabani matata KO?... yace "eh to amma ba yanzu ba, dasauri yace sai yaushe?.. sai nayi shawara dasauri yace wani irin shawara kuma??.. inace kudi kake bukata "eh to nace zanbaka, "eh saidai nayi shawara sannan nakira ka da layina yakareshe fadi tareda sakin dariyar mugunta sannan yakashe wayar. Inda yabar *Habeeb* yanata faman hello hello cike da tashin hankali yamike yafito, ran shi amugun bace yake kwalama Saminu kira, Cikin girmamawa yanufo gurin shi dasauri yadan rusunna yace Sir gani.... Cike da tashin hankali yace Saminu mutafi gida anyi kidnapped din my *"Leemah,* dasauri yace subhalallahi! garin yaya haka yafaru?... suna tafiya yana fada masa abinda yafaru kasan cewar ya yadda da Saminu saidai be fada masa tsakanin shi da ado ba, don haka ba tareda wani bata lokaci ba suka shiga motoci suka nufi filin jirgi, cikin lokaci kankani akagama komai jirgin su yatashi zuwa Bauchi. ****** Agida kam hankalin Hajiyarmu ne yafara tashi kasan cewar taji *Deeya* shuru bata dawo ba, gashi tana takiran wayar ta, tana Kara amma bata dauka ba, don haka tafito ta nufi part din lnna don taji ko *Deeya* tafada mata zataje wani gurine daga makarantar?... to kuma adai-dai wannan lokacin ne motar su Abba da Baffa ta shigo sai kuma gatasu escorts din da *Habeeb* yatura su dauko *Deeya* sun shigo, hankali tashe bayan suyi fakin sai suka nufi su Baffa dasuka fito daga tasu motar, Suna fada masu Oga yace" suje school su dauko "madam suje daukota amma basugan taba.. Cike da tashin hankali Abba yace kamar yabasu gantaba basu ne suka kaita makarantar ba?...suce "a ah "ita kadai taje, sun kuma tambaya ance tashiga school din tafita. aikam nan yafara masu fada akan meyasa zasu barta tayi tuki dakanta alhalin sunsan ga halinda take ciki, nan dai suka fada mashi yadda sukayi da'ita, Hankali tashe akafara kiran yan'uwana ana tambayar su kotaje gidajen su?....saidai duk Wanda aka tambaya sai yace batazo ba gashi kuma anata kiran wayar ta yana Kara amma bata dauka ba, hakan ne yasake tada hankulan yan'uwa sosai. Nan da nan akafara cigiyarta akafafen sadarwa, saidai kome kamada ita ba'a gani ba, sosai hankulan yan'uwa yatashi duk sunzo gida yacika, Sannan duk abin nan dake faru Abba yace kar wanda yakira *Habeeb* yafada masa a tunanin su bai saniba. Saidai kuma ana cikin haka sai gashi ya'iso hankalin shi a matukar tashe, har yafada kasan cewar tunda suka taso yake kiran layin *Deeya* don yai magana da adon wayar akashe gashi yace" zaya kirashi danashi layin amma bai kirashi ba, hakan ne yasa hankalin shi tashi sosai yayinda yakeji zuciyar shi kamar zata buga, don bacin rai yanaji kamar yarufe ido yabude yagan shi inda ado yakai mashi *Leemah,* sai Addu'a yake Allah yatare mashi *Leemarsa* kar ado yacuta mata. Yayinda bai fadawa kowa yanda sukayi da ado ba sai *Harees* yafada wa, su abba kuma yace masu wayanda suka sace *Deeya* sunce zasu kirashi. Hajiyarmu kam sai kuka take tana fadin amma dai duk wayan dasuka sace hali dubunta basu da Imani, *Feeya* ma sai kuka take *Harees* yana ta lallashin ta, haka wasu daga cikin yan'uwa sai kuka sukeyi suna tuna halin datake ciki yayida masu karfin halin cikinsu suketa jimamin bacewar ta. **** Aban garen *Jana* kam tadauki tsawon lokaci kafin ta farfado domin ba karamin dakuwa tayi gurin ado ba duk yahada mata jini damajiya, fuskarta kamar tayi hatsarin mota dakyar ta'iya tashi domin gaba daya jikinta ciwo yake mata, musamman kanta da takeji kamar zaya tarwatse saboda tsabar sarawa dayake mata, yayinda kasanta yake wani irin mugun zafi kamar anzuba mata barkono, Dakyar tamike da taimakon bango tanufi bayi sai ihun azaba take tareda tsinema ado, wanka tayi tafito tashirya tanufi gida. zata shiga kenan saiga Baban ta yafito, Kallo daya yai mata yace subhalallahi keeee! Murjanatu hatsari ki kayi haka?...kuka tasaki tareda fadin "a ah baba "ado ne yaimun duka banyi mashi komai ba, Dasauri yace karya kike wlhy Murjanatu, Cikin kuka tace ba karya bane haka kawai yaka mani yanata dukana. Harara yawatsa mata yace humm Murjanatu kenan acikin karyayyakin ki babu wanda ban saniba, taya za'ayi baki mashi komai ba kawai yaka maki yai tadauka ai saidai idan yaje yai sana'arta shi ko?...wato shaye-shaye. tace "eh kilan yayi ne amma dai ban mashi komai ba yaduke ni, yace hakan yayi kyau KO ba komai kinga alhakin "Alh. *Habeebu* yafara binki, kuma kisani wannan din kadan ki kagani, badai cin amanar aure ba?...bawan Allah yarike ki amana kikai ta cutan shi?..toba baki nayi maki ba amma tabbas baki ga komai ba, yanzu dakika kwaso jiki kika zo me kike nufi?.. tace wlhy baba nafasa auren ka kirashi" kace yasake ni, harara yasake banka mata sannan yace humm yaro man kaza, ni Alh sani zan kira mijinki nace yasake ki??..saboda ga mahaukacin uba ko?.. to idan ma mafarki kike kiyi maza kifarka, domin hakan baya taba faruwa ba har abada saboda ni ba mutunin banza bane dayake kashe aure, Allah yatsare nikam ai saidai na hada shi badai kashe shiba kinji ko?, kuma bari kiji nafada maki abinda baki saniba koda zance nakira "ado dan yasake ki to bazaya taba sakin kiba domin nace mashi karya kuskura hakan tafaru tsakanin ku, kuma nasan ko ban fadamasa haka ba tabbas ado bazaya taba sakin kiba har abada, don haka ki daina tunanin rabuwar ku domin yace" mun auren ku mutu karanba takalmin karfe, na kuma jidadin haka don haka kama hanya ki koma dakin ki kije can ku karata ke dashi dama can dake dashi kukafi dacewa ba mutumin kirki "Alh. *Habeebu.* har zatayi magana yace maza wuce ko yanzu nakira yayanki "Jafaru yai maki wani dukan, wanda yafi wanda adon yaimaki dole tajuya ta tafi. gidan Shafa tanufa inda ta'iske itama mijinta yaimata dan banzan duka, baki yakunbure har bata iya magana, _nikam nace kila'a asirin da take masa yafara karyewa ne lol,_*Jana* dai bata gane komai agurin shafa ba don haka tanufi gida a tunanin ta zata iske ado da Junior saidai bata iske suba don haka tafara tunani to ina suka keja?. ****** Wasa-wasa yau *Deeya* ta kwana biyar ahannun ado amma ko filashin baiyi ma *Habeeb* balle ya kira shi kamar yanda yace, wanda hakan ba karamin sake sa yan'uwa cikin mugun tashin hankali yayi ba. musamman Hajiyarmu da *Feeya* sukam damuwar su abayyane take sabanin lnna da Baffa, tsabar kawaici irin ta Fulani yasa basu nuna damuwar su agaban mutane akan sace *Deeyar,* saidai idan sun kebe suna nunawa atsakanin su musamman lnna har kuka take shikam Baffa Addu'a yake sosai Allah yakare masa yar lilon yarshi yakuma bayyana ta. Shikam uban gayya yafi kowa sake shiga tashin hankali irin Wanda be taba tunanin zaya shiga arayuwarsa ba, idan kagan shi sai yabaka tausayi domin yarame sosai kasan cewar tun ranan da ado yasa ce *Deeya* rabon dayaci abinci saidai ruwa da coffee kawai yake sha, domin a duk lokacin da Hajiya tabashi abinci yaci dazaran yadiba zayaci sai ya tuna kila *Leemarsa* tana can bata ci komai ba don haka sai yafasa, fuskar shi babu walwala kodan domin tuni sunyi ban kwana da dariya sai uban kasinbar daya ajiye, maganar aiki kam tuni ya ajeshi gefe sai addu'a yake Allah yatare mashi *RUHINSA* yakuma bayan a mashi inda ado yaboye mashi ita, domin ya tabbatar itace rayuwar sa wanda idan har babu ita to bashi dawani anfani. Zaune yake afalon sama dake part din Hajiya kasan cewar tuni yakoma can dazama, sanye yake da bulun jallabiya me gajeren, kamar koda yaushe wayoyin sa ne zube akan tebur yatsura masu ido kozayaji Kira daga ado saidai kuma shuru kakeji wai mlm yaci shurwa, ido yarintse ya najin wani irin zafi a zuciyar sa tareda tsantsar tsanar ado, a hankali yafurta hum! donkey man _haka yanzuyake kiran ado,_ tabbas ranan damuka hadu dakai hukuncin da zanyi maka bazayai maka dadi ba, dai-dai lokacin da Lili yafada jikin shi hakan ne yasashi bude ido cikeda damuwa tace Daddy yoche ne Aunty *"Deeya* na jata dawo?... har zayayi magana sai wayarsa tayi kara, ahankali ya dauki wayar ya yaduba ganin lambar da bazaya taba mantawa da'ita arayuwa saba ne yasashi sauri amsawa kafin duk yayi magana yaji ance... Muje A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนmeenat Lufhat๐ŸŒน [11/9, 10:12 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 7โƒฃ9โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Assalamu'alaikum yallabai inayini?... aida sauri yacire wayar daga kunnan shi yakurama lambar ido yana kallon ta nadan wani lokaci sai kuma ya lumshe ido, yanaji wani iri aranshi. tabbas lambar irin dayace da wacce yake tsammani kira daga gareta saidai banbancin kwaya daya, wanda sam bai kula da hakan ba alokacin dazaya dauka sai yanzu. Jiyayi ance hello yallabai ka naji na?.. _kasan cewar yasa kara don haka anaji,_ ahankali yabude idon tareda fadin "eh inaji dawa nake magana?...ajiyar zuciya mutumin yayi, yace yallabai sunana musa ina zaune a unguwar jahun ranka yadade, taimako nake nema yace kamar name kenan?..yace ranka yadade na kudi "matata ce takeda ciki to lokacin haituwar yayi nakai asibiti, saidai likita yace bazata iya haihu dakan taba saidai ayimata aiki acire dan idan ba haka ba mutuwa zasuyi itada dan, yallabai kudin aikin dubu hamsi nikuma dubu goma nakeda shine nakeso ka taimaka mun dan Allah. Ahankali yace badamuwa kazo ka karba cike da farin ciki mutumin yace to yallabai nagode nagode nagode, Allah yasaka da alkhairi yakareka daga sharrin makiya Addu'a sosai mutumin yaita zubawa *Habeeb,* aikam yaji dadi sosai har dai inda yace Allah ya tsare matarsa yakuma bayyanar da'ita Cikin gaggawa, _kasan cewar babu wanda baisan cewar matar senata *Habeeb* tabace ba._ Cikin sanyi murya yace bakomai kazo zan sa'akawo maka yanzu, yace yallabai Ina kofar gida yace to bari nayiwa security magana su barka kashigo ka karba, to yallabai nagode. Kuri Lili tayi masa da kyawawan idon ta irin nashi Murmushi karfin hali yayi ba tareda yace komai ba, yakira layin Saminu bayan sunyi magana sai yatashi tareda cewa ina zuwa lilin Daddy kinji?.. kaita gyada sannan yanufi sama can sai gashi yadawo hannun shi dauke da bandir din kudi yan dubu-dubu, inda ya'iske Saminu yashigo yanajiran shi. Cikin girmama wa yace yallabai gani, kudin ya mika mashi tareda fada mashi wanda zayaba karba yayi yace OK" sannan yafita. Zama *Habeeb* yayi tareda daukan Lili yadora ta akan cinyarsa sannan ya kalle ta yace ya'akayi ne?.. Lilin Daddy, tabe baki tayi kamar zatayi kuka dan har hawaye sun fara taruwa acikin idon ta, dasauri yace "a ah my Lili don't cry kinji?..kaita gyada alamar to sannan tace Daddy "Aunty *Deeya* na bajata dawo bane?.. Dasauri yace zata dawo zata dawo Lili kiyi mata addu'a, tace to yoche jata dawo?.yace inaji ajikina takusa dawowa garemu kinji?...dariya tayi tareda fadin yeeeeeee! "aunty *Deeya* na jata dawo, tayi mun wanka tayi mun kwolliya da kicho tayi mun....nan dai tayi ta lissafin abubuwan da *"Deeyar* take mata yayinda yaketa kallon ta yana murmushi shirmen ta, Can kuma saita sauka daga kan cinyar shi tace Daddy zanje nafacha ma lnna "Aunty *Deeya* na, jata dawo KO?.. kai ya gyada mata sannan tafita da gudu, ahankali ya jingina bayan shi da kushin tareda lumshe ido ya naji zafi a zuciyar shi na rashin sani halin da *Leemarsa* take. ******** Aban garen *Deeya* kam acikin kwana biyar din nan idan kagan ta saita baka mugun tausayi, domin gaba daya tafita hayyacin ta sosai kasan cewar itama daga ruwa sai ruwa take sha, wanda shi suke bata a matsayin abincin ta da burodi, saidai batacin burodi sai ruwan kawai kasan cewar tunda ta samu ciki duk wani abinda yashafi fulawa batacin shi. Babu abinda take sai rokon Allah yakubutar da'ita daga hannun wayan nan mugayen mutane, shikam kuka tuni tamaida shi abokin firanta tanayi tana surutai yayinda zazzabi da ciwo kai suka samu mahallin zama a jikinta, wanda hakan ne yasata tasake fita hayyacin ta matuka. fuskar duk ta kunbura saboda tsabar kuka, garashin isassan bacci da bata samu da kuma rashin tafiya kasan cewar tun ranan dasuka kawota ko bakin kofar kangon basu sake bari taje ba fitsari da alwala duk nan takeyi, saidai tana d'an tashi tazagaya dakin koshi saida rana saboda duhun da kangon yakeda shi wanda yake bata matukar tsoro, shiyasa kafafunta suka sake bunburi sosai saboda rashi takasu da batayi yanda yadace. Kusan kullun zaune take kwana saboda kukan bera wanda yakesata taji kamar numfashin ta zaya dauke, da kuma kukan wasu abubuwan da batasan ko mene ne ba, ga sauron tsiya duk sun cijeta abuga fara jikinta yayi jajir yayi rud'u-rud'u gwanin tausayi. Sannan duk wani kayan adon dake jikinta sun karbe sumai da ita kamar me takaba, sai wani zoben gwal me masifar kyau, yanada harafi sunan ta Dana *Habeeb* shikam duk naci irin na ado saida yabarta da abinta, domin yaki fita daga yar karamar yatsarta wayar yakuma dama tun ranan dasuka gama magana da *Habeeb* yasata ciro layin yakarba yajefa abakin shi yataune yazubar a gaban ta sannan yatafi da wayar. ***** Aban garen *Jana* kam tun ranan da ado yaimata dukan tsiya bata sake ganin shiba, wanda hakan bakaramin dadi yaimata ba domin tasamu damar zuwa gidan Alh Barau suna holewarsu san ran su. Shikam ado saida ya kwana biyar suna gadin *Deeya* sannan yabar dajin, bayan ya gargadi su mangal akan sukula da *Deeyar* karta gudu, sannan yanufi gidan kakar shi don yaga Junior saida kuma ya'iske shi kwance ba lafiya sosai duk yarame, hankali tashe ya dauke shi yakai shi asibiti inda aka kwantar dashi, dole yaje yadauko kaka dan tazauna dashi. Amma sai masifa take mashi wai yarabo d'a da uwar shi maimakon yabari har yakara girma sannan yaje yadauko shi, sai beyi hakan ba saboda shidin bakin mugun d'an gaba da fatiha, bai bitakan ba saida yabiya kudin magani, sannan yace mata to kakar d'an gaba da fatiha zanje gida nadawo ki kulamun da yarona dakyau sannan yafita, cike da masifa tace shege da aisai bakaje kazakulo uwarka daga kabari, tazo satayi maka jinyarshi dakyau. *Jana* kam hankalin ta yafara tashi na rashin inda ado yakai Junior, bayan tadawo daga gidan Alh barau tana zaune afalo tana tunani, sai gashi yashigo fuska hade yace keee! zubomun abinci yinwa nakeji yafadi yana kokarin zama akojajjen kushin din falon, dasauri ta tareshi tareda fadin mlm aibaka bani kudin girkinba balle nay sannan gidan uban wa kaje yau kwana biyar kenan rabonka da gidan na, sannan Ina ka kai mun yarona eyeee?..., Cike da masifa yace gidan ubanki naje shikuma Junior saikin shakeni naji kamshi mutuwa sannan zan fadama ki indan nakaishi kinji KO?..., itama cikin masifa tace wlhy baka isaba saika fitomun da Dana du inda kakai shi tunda bakai kadai kedashi ba eheee. Cikin tsawa yace keeeee! kalleni da kyau ni ba sa'anki bane dazaki nagaya mun maganar daki kaga dama kinji KO?.. " Junior dai dana ne nakuma Kai shi inda naga dama don haka sai kiyi abinda zakiyi, cike da masifa taci kwalar rigarshi tareda fadin wlhy baka isaba saika fito mun da D'ana. Aikam cikin bacin rai yafara dukanta kamar jaka yana fadin dan ubanki ni zakiciwa kwala?..tab! zakiko ci ubanki yau agidan nan, kai! kaga mun shegiya, aikam nan yadinga jibgarta saida yai mata dukan tsiya yabarta kwance tana nishi azaba, sannan yafita abishi. _Nikam nace wayyo *Jana* kinga arkane๐Ÿ˜‚_ *_Bayan kwana biyu_* ****** Wanda yayi saidai da sati daya kenan da ba cewar *Deeya* Da misalin karfe 5:00pm, tana zaune akan dankwalin ta data mayar dashi tabarman, ta jingina bayanta da bango tun bayan data idar da sallar la'asar take tasbihi da hannu yayinda hawaye keta faman tsiya a idon ta, Dasauri ado yashiga kangon wanda yasata firgita domin mugun tsoron shi takeji, tsugun nawa yayi agabanta tareda tsura mata jajayan idon shi wanda kana gani zakasan yayi shane, jikinta sai rawa yake cikin kuka hade da tsoro tace dan Allah kakaini wajan hmm na, na tabbatar duk abinda kakeso zaya baka, hannu yasa yadamki gashin kanta kamar yanda yasaba aduk lokacin da yai sha yakoshi sai yabata wahala ta hanyar damkar mata gashi kai, kara tasaki cikin kuka tace kayi hakuri dan Allah. murmushin mugunta yasaki sannan yace kikace duk abinda nakeso zaya bani ko?...kai ta gyada alamar "eh yace yauwa haka nakeson, yau satinki daya kenan da muka saceki ko?..tace "eh yace yauwa yanzu kam nasan duk wani tashin hankali na

Chapter 37 of 42