Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zakai mata kaga ne tana dauke da damuwa, sai kamshi turare take zubawa sai sallama yake amma bata amsa ba hakan ne yasa dasauri ya'isa gurin ta, ya zauna tareda girgiza ta aikam tayi firgigit tareda sakin ajiyar zuciya. ahankali tace Hmm na sunnu da dawowa yace yauwa *Leemah* ta, tunanin me kike ina ta sallama baki amsa ba umuh?.. cikin tsananin damuwa tace?... Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenat Lufhat๐ŸŒน [11/9, 10:18 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 8โƒฃ4โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Hmm na yace na'am my honey *Leemah* ya'akayi ne?.. tace umm.. sai kuma tayi shuru tareda tsura mashi kyawawan idanun ta, masu matukar tsumashi akoda yaushe dasauri yasa hannun ya tallabo kumatun ta, yace ah! *Leemah* ta wai me ke damun kine?.. Koda yake na kula dakefa kwana biyu nan kina yawan tunani, kuma idan na tambaye ki sai kice mun bakomai, kuma kinsan yawan tunani yana haifarwa da mutun matsala, sannan kinsan banason ganin ki cikin damuwa KO?..kai ta gyada alamar "eh yace OK" ke kam na kula kinason gani na cikin damuwa ko?.. dasauri tace "a ah hmm na, yace to fadamun abinda ke damu ki kinji tawan?.. Cikin sanyi murya tace to Hmm ta damafa wani abu nakeson tambayar ka shine fa nake tunani taya zanfara, ido yazaro cike da mamaki yace *Leemah* ta Ina matsayin mijinki shine kike tunani ta yanda zaki tambaye ni wani abin to saboda me?.. tsaya ma tukun yaushe mukafara haka dake umuh?..yakareshe fadi rai adan bace tareda kauda fuska gefe, dasauri ta juyoda fuskar tashi gareta, cike da shagwa ba tace Oh! oh! my sweet Hmm na don't angry with me pls Sorry kaji hubby na?.. yace Ok nayi aikin san *Habeeb* baya fushi da *Leemarsa* to amma fa karki sakeyi mun haka, duk abinda kike so just ask me kinji ko?..tawan yakareshe tareda sakar mata lallausan dariya, itama dariyar tayi tareda fadin ok thanks yace yauwa u wlm my dear so ask me?.. yakareshe fadi tareda rungumeta. tace Hmm na yace na'am my life Ina sauraran ki fadi..., tace Hmm na dama inason nace maka ya kamata "Aunty *Jana* tadawo da "Junior haka nan tunda hutu yakar...takasa kareshe fadi saboda dagota dayayi dasauri yana kallon ta fuska had'e yace dama saboda wannan ne kike zama kina dogon tunani?... tace Hmm n...dasauri yace look *Leemah* ta saunawa nafada maki banason kinayi mun maganar *Jana* eye?.. cikin kwantar da murya tace kayi hakuri shiyasa narasa taya zan yimaka magana, kasan Aunty *Jana* tanada sakaci idan ba anyi magana tadawo dashi" ba baza tayi tunanin kawoshi ba gashi ni bansan gidan taba danaje na dauko shi.... dasauri yace gidan takam bana fata kisani kuma har abada bazaki sani ba Insha'allah, tace Kai! Hmm na meyai zafi?..yace komai ma indai akan *Jana* ne tace da harna fara tunani naje can gidan su aikaini...yace dako shine laifi mafi girma dazakiyi mun arayuwa ta, cike da tsoro ta tazaro ido yace tabbas don haka karkiyi kuskuren aikata hakan idan taga dama takawo shi idan kuma bagani ba tarike shi ai danta ne, kuma koda Hajiya tayi maki magana kice nace a bar shi nima idan tayi mun magana haka zance. Cikin kwantar da murya tace to kayi hakuri hmm na idan nabata maka rai yace baki bata mun rai ba *Leemah* ta maganar tane banaso shiyasa tace to nadai kaji?...,ahankali ya mayar da'ita kirjin shi ya rungume tareda fadin shikenan dama shine tambayar?..tace umh! "a ah yace to menene?.. tace dama zan tambaye ka ne shin wanene "mutumin nan daya sace ni, kuma menene alakar ka dashi sannan naji kunyi maganar Junior wanda gaba daya ya daure mun kai sosai, shiyasa ma tun ranan danaji maganar nakasa sukuni sai tunani nake pls Hmm na kafada mun domin wlhy tsoron mutumin nan nakeji kar yasake yimani wani abun kaji?.. Shikam tunda tafara magana gaban shi ke faduwa domin baiyi tsamanin tambayar daza tayi mashi kenan ba. Murmushi yayi yace Kai *Leemah* ta irin wannan tambayoyi haka koda yake *Leemah* ta barrister ce, dole ta iya tambayoyi, murmushi tayi tace Kai hmm na yace yes, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zaya sake yi maki yanzu haka daga police station nake, na kuma gargade shi akan karya sake kusku shiga ahalina kinji ko?..kaita gyada dai-dai lokacin da wayar shi tayi kara..dauka yayi yaduba inda yaga sunan D.p.o, ya kunna karan tanaji d.p.o yace Sir barka da war haka yace yauwa barka dai, sir ance kace asake su?.. yace "eh yace sir aimun shigar da kara kotu dasauri *Habeeb* yace wane zayayi shari'a dasu ni?.. impossible d.p.o banida lokacin da zanyi shari'a dasu akotu so ku sake su kawai, yace ok Sir amma dole sai hukuma ta hukunta su akan laifin da suka aika ta maka yace Ok tareda kashe wayar. Sannan yace yauwa *Leemah* ta bari nabaki amsar tambayoyin ki amma tsaya Ina Hajiyarmu take?...tace tana bacci yace Ok, inason ki nutsu ki saurare ni dakyau zan baki amsar tambayar ki, aciki kuma zakiji wata magana wacce bayan ni da dan'uwa da *Hafeez* babu wanda yajita kaf family Mu, so kema idan kinji banason ki fadawa kowa maganar kinji ko?..tace to tareda maida hankalin ta gareshi karanta kuma ta fadin to wannan wace irin magana ce da ba'aso kowa yaji?.. yace na farko bansan wannan mutumin ba cike da mamaki tace Hmm na ba kasan shi ba fa?..yace eh ban kuma nemi sanin koshi wane ba domin bani da lokacin sa, tace to menene alakar ka dashi da har ya sace ni yanata bani wahala, kuma yace" mun Kaine kayi masa duka har yai sanadin rasa kafarshi daya haka ne?.. Murmushi yayi me kayatarwa sannan cike da zolaya yace nadai gane aikin nan ta kaina za'a fara KO?.., dariya tayi tareda dukan shi kadan akirji tace Hmm na amsa my questions?.. yace yanzu kuwa gimbiyar *Habeeb* wato alakata dashi tasamo asaline, tun ranan da na kamashi da *Jana* suna aikata ZINA adakin ta... Wani irin mahaukacin zabura tayi cike da tsananin tsoron jin wannan mugun labarin, dasauri yamaida ita jikinshi tareda fadin easy easy my life, jikinta sai rawa yake cikin rawar murya tace Hmm na Aunty *Janar*?..yace yes kuma naji ance har yanzu data sake auren bata bari, Nan ya fada mata duk abinda yafaru har da jukan daya ma ado inda yace mata kin tuna wani lokaci da mukaje fadaman mada kikaga anfito dawani mutun?.. Kai ta gyada yace to shine wannan mutumin, tace hmm na yanzu aunty *Jana* da aure akanta ta aikata ZINA?... yace kwarai kuwa tana can tana aikata wa agidan wannan mutumin don ace shita aura, Kuma bari kiji wani abida *Jana* ta aika ta mun, nan yasake fada mata komai akan Junior ba dashi ba ne, Aikam sai tasaki wani irin kuka me cike da tsoro dasauri yace hey my *Leemah* kukan me kike?.. bata iya bashi amsa ba saidai kuka data cigaba dayi, aikam tuni hankalin shi yatashi sosai tareda tsoron kar wani yashigo KO kuma Hajiya ta farka daga bacci, ta tambayi dalilin kukan shikuma badaga gurinshi nakeson maganar tafito ba don haka dasauri ya dauke ta suka shiga daki sama bed ya'ajiye ta tareda yimata rumfa yafara share mata hawayen da harshe. Yana fadin pls ki daina wannan kukan haka mana haba my *Leemah* kinfa san banason jin kukan ki, amma shine kikeyi ko?..to meye ma nayin kuka umuh?..duk abinda tayi aikan ta tayiwa bani ba bake ba ko?.. kai ta gyada cikin kuka tace Hmm na Ina kukan cin amanar da "Aunty *Jana* tayima kane koda yake kanta tayiwa ta kuma ci amanar aure, wanda idan batayi gaggawan bari ba takuma tuba to tabbas idan har ta mutu cikin wannan kazamar rayuwa to lallai zata fuskanci mummunan hukunci gobe kiyama agurin Allah, Yace tabbas kuwa, tace to yanzu tunda kowa bai saniba saika rike Junior amatsayin Danka kaw...dakarfi yace bakida hankali ne?..akan wani dalilin zan rikeshi amatsayin Dana?.zata sake magana yace *Leemah* stop I can't, shuru tayi sai kuma ahankalin takai hannunta kan sajen shi tana shafawa cikin sanyi murya, tace pls i'm so sorry Hmm na if i hut u, amma don Allah kayafe mata kaji?...lumshe idon yayi tareda dora hannun shi akan nata yana ci gaba da shafa sajan nashi, cikin kasa lalliyar murya yace zan yafe mata amma saita fadima family ta danawa Junior ba D'ana bane, dasauri tace taya kake tunani zata fadi masu Junior ba danka bane umuh?...murmushi yayi me kayatarwa yace zata fadi ne, tace hum Hmm na kenan ta yasaza iya fadin wannan abin kunyar data aikata arayuwar ta yace aikam sai tafadi, zata sake magana yai saurin had'e bakin su tareda tura hannun shi cikin rigar ta. *_Nikam Ina ganin haka nayi saurin fitowa amma saida na labe nace Deeya karki yadda Hmm Habeeb yaimaki wayo da jariranki yan sati biyu๐Ÿ˜œ_* ******* Aban garen *Jana* kam tun da taga an kwana biyu bata ga ado yadawo gida ba saika wai ta cigaba da holewar ta, inda bata tsaya akan Alh Barau kawai ba, duk Wanda yane meta saita yarda, do haka sosai take sheke ayarta tana samun kudinta tana shagalinta dasu, ba tareda tunanin komai ba, agefe daya kuma suna tabka madigo ita da shafa, kasan cewar tuni mijinta yamai da ita gefe yayi auren shi yakuma kwace yaranshi yaba amaryar, don haka yanzu ba kar wahala kawai take sha, aguri *Jana* ne kawai takejin sanyi idan sunyi tsiyar su sannan tabata kudi. *Jana* kam wani lokaci idan ta zauna takanyi tunanin to wai ina ado yaje shi Junior ne?.. can kuma sai tace Oho koma dai ina sukaje zasu dawo su sameta ne, yayinda ta daina zuwa gidan su saboda fadan dasuke yi mata akan ta nutsu ta zauna dakin ta, ta daina yawace yawace banza, musamman Baban ta sosai yake mata fada saboda ana yawan kawo mashi maganar ta. ****** Aban garen kaka da Junior kuwa sati daya yakwashe yana jinya cikin yardan Allah yaji sauki, saida yarame sosai sannan kuma baya da aiki sai na kuka tareda kiran Aunty *Jana* tazo ta dauke shi takai shi gurin Aunty *Deeya* da Lilin Daddy da Hajiya, yayinda kaka tayi ta masifa tana fadin to ita inata san wata aunty *Jano* da aunty *Deeyo* da lilu ne kome Oho, harda wani wai daddi to koma dai suwane sai kajira shegen ubanka yazo ya dauke ka yakai ka gurin su kaji, Shiyasa duk ya karkare ramewa kasan cewar abinci ma dakyar yake ci,koshi da taimakon makociyar kakan wacce ita CE ke basu abincin. *_Bayan wata daya_* ******* Sosai *Deeya* ta samu kula wa gurin Hajiya itada twice dinta su shi shar abinsu sunyi wayo gwanin sha'awa, har sunyi arbai'n tuni ta cigaba da zuwa school dinta kasan cewar tunin sun koma, saidai bata zuwa da twice din gurin hajiya take bari su har tadawo, kasan cewar basu da rigima, *Habeeb* ma tuni yakoma gurin aikin shi dashi da *Deeya* sai soyayya suke zubawa abunsu hankali kwance, kamar su cinye juna dan so da kauna, musamman *Habeeb* duk sanda zayako ma yakanji kamar yadauki *Leemarsa* sutafi tare. Ado kam tuni aka yanke masu hukunci zama gidan yarina wata uku aranan da aka yanke hukunci saida aka nunasu t.v duk yakunna t.v arana don kallon labarai to yagan su Baba da Deja ma sun gansu har da Bintan da jafaru amma banda *Jana* wacce take can tana yawon tarubar dinta kasan cewar yanzu har daukan ta alh barau yake suna zuwa yawo duk garin da zashi aiki, Hankalin iyayenta da yan'uwan ta ya tashi sosai dasu kaga ashe ado ne yasa ce *Deeya,* koda Baban ta ya aika akira ta ba'a iske taba atunanin su anguwa taje ko kuma yawon ta da tasaba saidai kuma har kimanin sati daya ana zuwa amma batanan abin yabasu mamaki to inataje?. Aban garen kaka da Junior kuwa tuni yaji sauki garau yakuma dangana darashin su Lili, duk dadai wata rana yakan danta ba rigimar sai ankai shi gurin su, yayinda ita kuma zatayi tayi mashi masifa dole yake yin shuru domin yaga bala'inta yafi nashi. Suna cikin haka ciwo yakama kaka wasa-wasa har takai sai ankwantar sai antayar, makociyar ta mutuniyar kirki itake tafaman kula wa da'ita. **** Su *Jana* kam ansamu duniya saida suka kwana goma sha biyar a Abuja suna sheke ayarsu sannan suka dawo, anyi jan bilitin Kai yashi uban attached gawasu farce roba da takara akan nata sannan tashefe su da bulun fanti, abun dai bakyan gani agurin ta kam haduwane da wayewa, direct gidan Shafa tanufa saida suka gama badalarsu sannan, Shafa tace ke! dalin ashe su ado ne suka sace matar *BB*,ido tazaro cike da mamaki domin batayi zaton hakaba, dasauri tace ke don Allah?.. tace allah kuwa nanta bata Labarin hukunci da aka yan ke masu inda takareshe da, fadin shawar da zanbaki kije kimatsa mashi yasake ki tunda kin samo kudi sai naraka ki gurin wani boka yaimaki asirin da *"BB* zaya mai dake dakin ki, sannan yayi maki wanda zaya sashi yasaki wnn shegiyar matar ta shi me kamada aljanu ko me kika ce?..,cike da matsanancin farin ciki tace... Muje A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenat Lufhat๐ŸŒน [11/9, 10:18 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 8โƒฃ5โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ _DAGA_ _MARUBUCIYAR_ *_DA SANNU_!* *_ZUCIYATA CE!_* *_AFSANA_* *_(Labari na)_* *_KYAUTAR ALLAH CE_* *_(Labarin Sadeeya)_* _SADAUKARWA_ *_GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)_* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Kai! dalin shiyasa nake sonki wlhy haka za'ayi sai kuma ta bugi kirjinta da karfi tareda fadin tashiga uku to Ina "ado yakai mata "Junior?... kallon ta Shafa tayi cike da mamaki tace kina nufin tuntuni baki maida Junior gida ba?..cike da tsoro tace to aishi yadauke shi kuma bansan inda yakai shiba, nayi-nayi yafada mun amma yaki fadamun, tace cabbb to aisai kije yafada maki kije ki dauke shi kimaida shi" wlhy tunkafin asirinki yatonu, tace aikam yanzu bari natashi saida tabata kudi sannan ta fita daga gidan tanufi gidan ta. ***** Bayan tayi wanka ta shirya cikin wata atamfa koriya dinkin doguwar riga me hannun shimi, sannan ta daura dankwali tamkar wata tsohuwar kilaki sai tayafa wani matsiyacin gyale akafada wanda dashi da babu duk daya, Kai abinda ba sha'awa sannan ta rataya jaka ta fito gidansu tafara nufa tukun. Da misalin karfe 30:00pm ta'isa bako sallama tashiga gidan direct babban falonsu tashiga shima ba tareda tayi sallama ba, Baba da Dija ne zaune akan kushin Jafaru yayan ta da Binta yayar ta suna zaune akan kafet suna tattaunawa ne, akan yanda zasu bullowa Lamarin *Jana* na wannan kazamar rayuwar da tasa kanta ciki, Saboda sunji Labarin cewa tabi "Alh Barau ne domin sosai Jabaru yai bincike har yagano haka. Duk suka daga Kai suka kalle ta cike da mamakin shirin dake jikin ta, wanda amatsayin ta nayar musulmaj kuma matar aure bai kamata tayi irin shi ba, sai faman taunan chingam take cike da rashin kunya tace sannun ku fa tareda kokarin zama adaya daga cikin akushi din falon wacce ke kusa da dija. aikam Jafaru yadaka mata tsawa cike da facin rai yace kina hauka ne?.. sudin sa'annin kine dasuna zaune akan kushi shine ke mazaki hauki zauna saboda bakida kunya?.. fuska ta yamutsa tareda zama akasa tana dan gunguni, cikin tsawa yace daga kidan ubanwa kike?.. fuska yamutse tace ah! daga gidan mijina mana, har zayayi magana baban yadaga mashi hannun idon shi nakan ta yace Murjanatu Ina ki kake yau kimani sati biyu bake dakin ki umuh?.. gabanta ne yafadi domin batayi zaton sun sanbata nan ba to amma taya akai suka sani?..tsawan da Jafaru yadoka matane yadawo da'ita hayyacin ta, ke ba dake ake magana ba kinyiwa mutane banza cike da rashin damuwa tace Oh! ayya naje Kaduna ne bikin wata kawata, Baba yace ke! murjanatu kiji tsoron Allah wani irin bikine haka har tsawon sati biyu?.. tace "a ah baba to zanyi maku karya ne?..kai ya girgiza cike da takaici yace anya murjanatu kikason kigama da duniya lafiya kuwa?.. hum karya kam aitun kafin kikai haka kikeyi mana ita, wanda idan har baki barta bato tabbas ita zata halakaki arayuwar ki koda yake aikinma halaka rayuwar taki, yanzu ke a tunanin ki bamusan abinda kike aikata wa bako?.. hum wai ZINA! ZINA!! ZINA!!! fa Murjanatu shikika mayar abokin rayuwar ki da aure akanki mijinki nacikin wani hali, amma kika sakafa kika bi wani namijin har wata kasa kuna holewa, Kai! wa'iyazubillah!.. Kuka dija tasaki me cike da bakin ciki itama binta haka, shikam jafaru jiyake kamar yatashi yashake ta tamutu kowa yahuta, Cikin sanyi murya yace Allah ya shirya ki idan harke din me shiryuwa ce, idan kuma ke bame shiryuwa bace, ta Ina rokon Allah yayi maki abinda yadace dake murjanatu wannan ita ne Addu'an dazanyi maki domin dai babu irin abin da bama yimaki, daga nasiha har fad'a wanda daga karshema sai kika daina zuwa gidan sbd kar afada maki gaskiya KO?... to ki kwantar da hankali ki wata rana ma bazaki ganmu ba, yanzu Ina Muhammad?... jitayi gaban ta yayi mugun faduwa, cike da bacin rai jafaru yace ke! karkiyi ma mutane iskanci kinji ko bakiji ana tambayar ki Ina Junior ba?.. Dasauri tace umm sai kuma tayi shuru cike da hassala jafaru yamiki ya'isa gurinta yabanka mata wani uban shuri da kafa, aikam tasaki kara cikin tsawa yace kaji yar'iskar yarinya anamaki magana kinayi ma mutane banza, cikin kuka tace to ai ado ya dauke shi kuma bansan inda yakai shiba, cike da mamaki baba yace kamar ya yadauke shi akan wani dalilin eye?.. shuru tayi har jafaru zaya sake kai mata wani shurin sai Baba yace kyale ta tafadan mana dalili dayasa yadauke shi alhalin ba danshi bane don haka uhum muna jinki?. Dija kam jitayi gaban ta yafadi, cikin kuka tace niban dalilin shi nayin haka ba, Baba yace kar kike Murjanatu Dija ma tace wlhy karya kike, baba yace barta yanzu abinda nakeso dake maza kitashi kije ki sa "shi yafada maki inda yakai yaron mutane kidauko shi kikai shi gidan su kinaji ko?..dasauri tace to tareda tashi tafita. ********* Koda *Jana* ta'isa gidan yarin tafadi gurin wanda tazo bayan sun tambaye ta meye matsayin ta agurinshi, tafada masu sannan akafito mata dashi, gaba daya yafita hayyacin shi saboda tsabar wahala kallo daya tayi mashi yabata tausayi, sai kuma ta had'e fuska tareda kauda tausayi shi azuciyar ta, shi kam ado kallon mamaki yake mata naganin yanda ta koma lokaci kankani, yace ah! *Jana* ce sai yau kika tuna dani kenan?..tace umuh! yace gaskiya kin kyauta ashe kina nan?..fuska ta yamutse tace ga zahiri kagani, yace aikam naganki to ya'akayi ne meke tafe dake?..tace nazo ne kafada mun inda kakai Junior naje nakarbo shi, domin ina bukatar ganin d'ana kaji sannan kuma kabani takardan sakina dan bazan iya zama da marawo ba ehe yace ah! kai! haba?..tace kwarai kuwa aini bansan cewa dan hali ka koma yiba, kai girgiza tareda fadin saiga shikuma yanzu kinsani, tace ai shiyasa nazo kabani takardan sakina, yace aikam zaki samu yanzu, sai kuma yasaki wata muguwar dariya saida yayi me isarshi sannan ya had'e fuska tareda watsa mata mugun kallo, yace kedai kam muguwar dakikiya ce wlhy d'if-d'if-d'if kwakwalwar ki take sauna ina fada maki babu saki tsakanin mu amma bakiji ba, saboda kedin dakkwala ce to yanzu ma bari nasake fada maki idan duk mutanan duniyar nan zasu taru wlhy bazan sake ki ba, domin sunan auren mu mutu kara ba don haka saiki sake sabon shirin zama da barawo kinji kinji?..Junior kuma bazan fada maki inda yakeba, har zaya wuce tafisgo rigarshi tabaya dakarfi, cike da masifa tace ai wlhy baka isa ba, fuska had'e yajuyo yawatsa mata wani irin mugun kallo wanda yasata tasaki rigar dasauri domin wani irin tsoron shi ne yaka mata, murmushin mugun ta yasaki sannan yakwantar da murya yace aikam na'isa sosai kuma kisani idan nafito fashi da makami zanyi, ido tazaro cike da tsoro yace tabbas kuma takan wannan shegen tsohon mijin naki zanfara don wlhy duk wannan kurarin nashi basu shigeni ba saina rama, sannan yawuce yabar ta tsaye baki bude, da tagaji da tsayuwa tajuya jiki asanyaye ta nufi gida. ******* Wasa wasa saida *Jana* ta kwashi sati uku tana zuwa gurin ado akan yasake ta ya kuma fada mata inda Junior yake, amma yakiya daga baya ma sai yace da masu tsaran su suhana ta zuwa, don haka hankalin ta yai mugun tashi domin batason kowa yasan Junior ba dan *Habeeb* bane, tunda ado yace mata karya ne be fada mashi cewa Junior badan shi bane, haka ne yasa duk tafita hayyacin ta, dataga sun hanata shiga sai takoma basu kudi suna barin ta ganin shi saidai kuma tayi rokon tayi masifa tayi lallashi be fada matan ba, sannan beyi sakin ba kamar yanda takeso don haka duk yan kudin ta yakare gashi yanzu Alh Barau yace ta daina zuwa gurin shi, kasan cewar Jafaru yaje har gidan shi yamai gargadin ya rabuda ita kosu kaishi kara kotu, don haka komai yakwabe mata domin yanzu babu me kwasarta saboda wani al'amari da yasame ta, wato idan ta tsugunna tayi fitsari sai wani irin ruwa yana fitowa ta gaban ta me masifar wari, gawani mugun mafarki da takeyi wani koton mutun baki yana binta da gudu hannunsa rike da sharbebiyar wuka zaya caka mata, idan tana gudu sai taga zata fad'a wani katon rami yana ci da wuta, gashi kusan kullun sai yaya Jafaru yazo yaima fadan akan saita karbo Junior tunda shida kansa yaje gurin adon don yafadi inda yakai Junior sai cewa yayi atambaye ta tasan inda yake, shiyasa abubuwa sukai mata yawa ta koma kamar mahaukaciya. ***** Aban garen kaka da Junior kuwa abin gwanin tausayi domin suna cikin wani hali yayinda sosai jikinta yatsanan ta, danma makociyar ta na kula da'ita ba tareda gajiyawa ba yanzu kam ko abinci bata iyaci balle magana, sannan bata gane mutane abin sosai yadami matar kasan cewar batasan kowa nata ba, tsoron ta daya ma karta mutu ta barta da Junior Allah sarki wanda yanzu ya dangana darashi su Lili, bawon Allah saidai yakan zauna yayita kuka, wata rana sai matar nan me suna iyale ta lallashi tukun. ******* Aban garen su *Deeya* kam komai yana tafiya yanda yakamata, sosai suke gudanar da rayuwar su hankali kwance yayinda suka tsanan ta addu'ar neman tsari, ga makiya da dukkan wani abinki hakan ma iyayensu sosai sukeyi masu addu'a, don haka yanzu sunaji babu wani abinda zaya same su saidai kaddaran ubangiji wanda babu wani mahalukin daya'isa ya kauche mata. Yau juma'a tunda *Deeya* tadawo daga school bata zauna ba, saida ta tabbatar ta gama hadama *Habeeb* kalolin lafiyayyun abinci masu jida lafiya tareda abin sha Bayan ta shirya komai akan dinning table, sannan tashiga, wanka bayan tayi kwalliyar ta me tsari sannan ta shirya cikin wata bakar abaya me asalin kyau da tsada, Sannan tayi rolling kanta da gyalan abayar bayan ta feshe jikinta da turaruka masu asalin kamshi sannan tafita tanufi part din Hajiya. Tana shiga ta'iske hajiya na jijjiga *Haleem* dayake ta kuka, kallon ta hajiya tayi me dauke da harara fuskar hade ta tace... *_Second to the last page Insha'allah nagode sosai ,da kaunar ku gareni ALLAH yabar zumunci ameen๐Ÿ‘๐Ÿฝ_* Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenat Lufhat๐ŸŒน [11/9, 10:19 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 8โƒฃ6โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ _DAGA MARUBUCIYAR_ *_DA SANNU_* *_ZUCIYATA CE_* *_AFSANA_* *_(Labarin na)_* *_KYAUTAR ALLAH CE_* *_(Labarin Sadeeya)_* SADAUKARWA

Chapter 40 of 42