Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abin diban jini yadibi jinin *Habeeb* dana Junior Lili kam da kyar aka diba domin sai kuka take tana zagaya office din, tana fadin ita batason allula๐Ÿ˜€ saida *Habeeb* yadaka mata lafiyayyan tsawa tukun na, tareda rike ta aka diba sai kuka take tana kiran Aunty *Deeyan* ta, bayan ya diba yafara gudanar da aikin sa. Cikin lokaci kankani *Harees* yagama duka yafitar da results ahankali yake duba wa, hankalin shi yai matukar tashi da ganin saka makon hakan ne yasashi dago kai dasauri yakalli *Habeeb,* wanda shidin ma kallon *Harees* yake kallo me dauke da kainake saurare.... Ahankali yace Dan'uwa l'm sorry to say result yanuna Junior ba jininka bane ma'ana ba 'Dan" ka bane, wani abin mamaki kuma result din Lili yanuna cewa ita din jinin kace wato yar kace, ajiyar zuciya *Habeeb* yayi tareda fadin ainasan haka zata faru, cike da mamaki *Harees* yace kamar ya kasan haka zaya faru?...yace kamar yanda wancan mutumin yafada sannan nikaina zuciya ta tadade tana tunani tareda tambayar me yasa banajin Junior araina?.. kamar yanda nake jin Lili amma ban samu amsa ba, sai gashi yau Allah yabani amsa tabbas Junior ba "D'ana bane, d'an wannan "mutumin ne domi yau naga tsantsa kamar da Junior yayi dashi. Sai kuma yai shuru tareda furzar da iska taba kinsa cike da bacin rai yace Dan'uwa *"Jana* tacuceni kuma sai Allah ya'isar mun, ahankali *Harees* yace kayi hakuri Dan'uwa bakai *"Jana* tacuta ba kanta tacuta" kuma ita" da Allah *Habeeb* yace haka ne tashi muje gida, Yafadi tareda mikewa ya saba Lili akafada kasan cewar tuni tayi bacci, *Harees* yace Ok" yanzu to me abin yi game da "Junior inanufin kar maganar ta bayyana wanda hakan zaya 'iyabata maka suna?... murmushi yayi yace nafada maka tunda ubangijina be batamun suna ba to babu wanda ya'isa yabata mun, koda maganar zata fita ne bazan damuba duk da nasan wasu zasu zageni amma bakomai tunda ban zalince taba asalima "ita ce ta zalinceni don haka ita duniya zata zaka, sosai kaga yakare kanta kenan KO?.. yace haka ne yace yauwa game da Junior karka damu nasan abinda zanyi, sannan Insha'allah ni *Habeebullah* baza'a ji abakina cewa Junior ba Dana bane, saidai aji abakin ta wanda na tabbatar amana tane zayaka mata tafada, *Harees* yace hakan shine daidai sannan yakama hannun Junior suka fita suka nufi gida. Koda suka isa gida direct part Hajiyarmu *Habeeb* yanufa yakai su Lili ya'iske Hajiya tadawo, sannan yafito yanufi part din su *Harees* yana shiga *Deeya* tanufe shida kyakkyawa baby boy wanda tunda tashiga ta dauke sa yake hannun ta, mika masa yaron tayi tareda fadin sweet Hmm na sannu, yace yauwa honey *Leemah* ta tareda zama yana kallon yaron yace masha'allah wlcm to the world mah boy, zama tayi kusada shi tareda dafa kafadar sa fuskar ta dauke da farin ciki tace sauran kiris nayi fishi saboda baka zo, da wuri kaga yarona ba kallon ta yayi yasa kar mata murmushin karfin domin zuciyar sa cike take da bakin cikin abinda *Jana* tayi masa, ahankali yace thank god daba'ayi fushi dani ba, inafatan Mom din boy zatayi mun afuwa narashin zuwa da banyi dawuri naga boy din taba hakan yafarune saboda naje wani gurine. Kiss tayi masa akumatu tareda cewa anyi maka yace godia nake tawan, dariya *Feeya* da *Harees* su kayi *Harees* yana cewa Oh! su Queen of beauty agabana, fuskata rufe hannu tana dariya shima *Habeeb* dariya yayi sannan yaima yaron Addu'a, bayan yagama sai yace ma *Feeya* yajiki cike da kunya tace dasauki, yace inafata babu wata matsala?..tace "eh yace to Alhamdulillahi! Allah yaraya akan sunna suka amsa da ameen. Kuka yaron yasaki dasauri *Deeya* takarbe shi tareda tashi tana jijjigashi tana fadin sorry my boy yi shuru kaji Dad ne ko?.. Murmushi yayi tareda dafakan sa zuciyar sa cike da damu wa, Magana take tana fadin sweet Hmm na fadamun da wa yaro na yake kama tsakanin my sweet *Feeya* da Hmm *Harees?..,* shuru ba amsa tasake fadi still be amsa ma taba tayi magana yakai sau biyar amma be amsa ma taba, hakan ne yabata tsoro dasauri ta mikawa *Feeya* yaron sannan taje ta girgiza tareda fadin sweet Hmm na dakarfi aikam dasauri yadago dakai yazuba mata idon sa dasu kayi jajir tamkar an watsa masa barkono gajijiyoyin kansa sunyi rud'arud'a zaro ido *Deeya* cike da tsoron ganin yanayin sa tace.... *_Slm yan'uwana barkan muda Sallah, than barkan mu da Jumma'a Allah yakarbi lbadun mu yakuma maimaita mana ameen_*. Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [11/9, 10:12 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 7โƒฃ2โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Yah! salam sweet Hmm na meyasa me ka?...bece mata komai ba saidai yai mata kuri da ido yana kallon ta, cike da tashin hankali taje tadauko ruwa me sanyi cikin fribge agora tareda cup tazo tazauna kusa dashi, cikin rawan jiki tabude goran ta tsiyayo tabashi abaki dasauri yadora hannun shi kan nata yafara shan ruwan idon shi na kanta, saida yashanye ruwan sannan taciro cup din ta'ajiye tareda tallabo kanshi tadora akirjin ta. Tareda tura hannu ta cikin lallausan gashin kansa tana shafawa cikin sigar lallashi da sanyi murya tace it's Ok" sweet Hmm na, Ahankali ya lumshe ido tareda sauke ajiyar zuciya. *Harees* kam shuru yayi domin yasan abinda ke damun *Habeeb* din saidai kuma babu yanda za'ayi yafadi, saidai zuciyar sa cike take da tausayin halin da Dan'uwan nashi yake ciki, ahankali ya kalli *Feeya* wacce gaba daya itama tausayin halin da Hmm nata yashiga takeyi wanda tunani take aranta me yake damun shine?..cikin sanyi murya yace me darajata tashi mu shiga daga ciki mubasu guri ta lallashe sa, yakareshe fadi tareda karban yaron sannan ta tashi suka shiga daki kasan cewar dama afalon sama suke. Cikin sanyi murya *Deeya* tafara fadi duk dacewa bansan me yafaru ba bakuma zan matsamaka dole saika fadamun abinda yafaru ba domin yin hakan ba dai-dai bane, amma dai dan Allah Hmm na inason kwantar da hankalin domin komai kaga yayi tsanani arayuwa to sauki yana nan tafe musamman idan aka hada da Addu'a, don haka kadaina sa damuwa aranka kaji?.. Sannan ni nasan Hmm na jarumine kuma sadauki me tsananin hakuri dakauda kai akan dukkan wani al'amari, musamman akan abinda be shafe shi ba kai koda yashafe shine nasan yanada tsananin kawaici dazaya danne to amma meyasa, yau yakeson tada hankalin sa akan abinda na tabbatar kome ne shi zaya'iya magance shi batareda kowa yasani ba ko?..,ta kareshe fadi tareda dago da kan shi daga kirjinta wanda hakan ne yasahi saurin bude ido. Kura masa ido tayi shidin ma kallon ta yake, tace a mah correct?.. ido ya lumshe tareda gyada mata Kai yanajin tsananin kaunar ta naratsa jini dajijiyar jikinsa, murmushi tayi cikin wani irin salo nadaukar hankali ta had'e bakin su hakan ne yasashi sakin ajiyar zuciya tareda sake lumshe ido yanajin wani iri kaunar ta nasake fisgar shi aduk fitar numfashin sa, amatukar bukace ya tallabo fuskar ta yafara mayar mata da martani. Sannun ahankali *Deeya* ta kawarda damuwar dake tareda *Habeeb* wanda yasashi ya manta da tarin damuwar daya kwaso, bayan tsawon lokacin da suka dauka suna shan bakin juwa tamkar wasu tsuntsaye, cikin hakan ne yake kokarin wuce makadi da rawa aikam dasauri tacire bakinta daga nashi tana sauke numfashi cikin rikitacciyar murya tace sweet Hmm na me kake kokarin yi?... murmushi yasa kar mata cikin kasalalliyar murya me cike da zolaya yace making Love mana my honey *Leemah,* ido tazaro cike da tsoro tace kai! sweet Hmm na anan din??..yace "eh man to meye ya fadi tareda kashe mata ido daya, baki ta turo cike da shagwaba tace no! no!! no!!! sweet Hmm na nidai tashi muje part din mu kaji?.. murmushi yayi me cike da tsantsan kaunar ta yace Ok" my honey *Leemah* nagode sosai da kulawarki gareni a duk lokacin daki kagani cikin Damuwa saikin kawar da ita daga gareni, shiyasa kullun sonki da kaunarki suke sake shiga zuciya ta *Leemah* ta ina matukar kaunarki ina rokon Allah yabarni dake har gaban abada *Leemah* ta, ya kareshe fadi tareda shafa lallausan fuskarta datayi kamar kwai tsabar smooth. Cike da jin dadi tace ameen Hmm na nima ina matukar kaunar ka irin sosai sosai din nanfaaaa! ta kareshe fadi tareda yin dariyar ta me kayatarwa shima dariyar yayi yace l know my happiness to tashi mutafi part din mu sai muyi Love dinmu acan, yafadi tareda daga ta ya rungume akafadar sa. Ahankali suke taka stars din kasan cewar gaba daya jikinsu babu wani karfin musamman *Habeeb,* ahaka har suka sauka suka fito harabar gidan ta wata kofar nagasun bi sun shiga gidan nasu wacce ban taba sanin da'itaba sai yau, Ina kallon kofar sai naga ashe sabuwar koface aka bude, wacce direct zata sadaka da cikin gidan su *Habeeb* din ba tareda ka zagaya kabi ta get ba. Fitar su *Deeya* ke dawuya saiga Hajiyar su *Harees* tafito daga da kitchen hannun ta dauke da kulan abinci tahau sama tashiga dakin da sallama, *Harees* ya amsa *Feeya* na kwance saman cinyar shi yanayin mata sannu, dasauri ta'ajiye abinci tareda fadin lafiya *Safeeya?..* Yace wlhy cikin take ciwo tace subhalallahi! to ka bata magani tasha?..yace "eh nabata Insha'allah zataji sauki nan bada dadewa ba, tace to Allah sawake tashi kici abincin dakayar ta tashi da taimakon *Harees* taci abinci wanda kafin tagama cikin ikon Allah ciwon cikin yatafi. Bayan tagama cin abinci sai tace Hajiya sai anjima zan koma?... murmushi tayi tareda cewa Insha'allahu tace to, *Harees* dabai fahimci zancen ba yace Ina zata koma?..tace af na manta nafada maka zata koma part din "lnnan ta tayi jegon acan, Dasauri yace haba Hajiya yanzu Allah nan danan har sai ta koma?..kuma ma aidanan din dacan duk daya ne ko?..tace "eh haka to amma tunda tanson koma wa sai kayi hakuri takoma can din, badan ransa yasoba bayan sallar isha'i *Feeya* ta koma part din lnna inda zatayi wankan jegon ta acan. ****** Abangaren Ado kam yana gama fadawa *Habeeb* cewa ai Junior ba dansa bane ya kashe wayar, yana dariyar mugun ta tareda fadin bazan ai wlhy da sannu zan kun sa maka bakin ciki, sannan yacire wannan layin da yakira *Habeeb* dashi sai yasa wani layin still layin *Habeeb* din yasake kira, Cikin sa'a yashiga wani killed smile yayi tareda cewa yauwa l catch stupid, sai kuma yayi shuru yana kiran a picking. *Habeeb* kam yana kokarin soyewa da *Leemarsa* sai yaji wayarsa nakara, tsaki yayi tareda jawo wayar be tsaya duba wayane yake kira ba kawai yakashe, yajefa ta can gefe yaci gabada abinda yake. Wani uba tsaki ado yaja tareda fadin Oh! shatttttttt, stupid man yakashe wayar shege ai zamu sake hadu ne yafadi tareda kashe wayar. *Jana* kam tana barin gidan Ado sai kira Alh Barau tace tana son ganin shi, yace mata yana gidan hutawar shi don hata iske shi acan tace to batareda bata lokaci ba tari a dai-dai tayi masa kwatance yakaita, tabiya shiku din shi sannan tashiga gidan kwance ta isake shi afalo daga shi sai boxes yana ganin ta yawashe baki tareda tashiga tare ta daki suka shiga basuda de dashiga dakin ba nafara jin Ihun. *_Nikam nace Jana Allah ya shirya_* Tsawon wani lokaci saiga ta tafito hannun ta rikeda kudi, har bakin get Alh barau yaraka ta tafita tasake hawa adaidai ta yakai ta anguwan su Ado, yana ganinta yace gaskiya kedai *Jana* kincika jaraba yanzu kina. nufin dawowa kikai mu sake yi?.. toni kam nagaji wlhy. Dariya tayi tace gaskiya ne haka nike saidai nima nagaji gaskiya kuma bawai nadawo musake yibane, nazo kawo maka cikon kudin daza kabiya sadaki ne saboda inason gobe ka tura gidan Mu ne man aure na; cike da mamaki yace yanzu dafitar ki har kinsamo kudi *Jana* to waya baki?... dariya tayi tace adona kenan kafa sanin cikin hade rai yace ah! nasanki kam fiye da yanda iyayanki suka sanki, har zatayi magana yai saurin yamika mata hannu tareda cewa" bani dasauri tabashi kudin sannan ta tafita tanufi gida tsaki yayi yace jaka jarabbiya kawai. *_Washegari_* *********** Misalin karfe 10:30 am Ado yatura wasu makotan shi gidan su *Jana* Baban ya taresu cikin mutunci kasan cewar *Jana* tafada mashi zasu zo, ta kuma ce masa dubu ta goma tayanke masa sadaki don haka ba tareda bata lokaci ba yafada masu suka bayar tunda sun zo dashi, Aikam nan take aka daura auren Ado da *Jana* akan sadaki dubu gama, bayan an daura mutanan zasu tafi Baba yace afada mashi ya gyara guri jibi in Allah ya yarda zata tare su kace to, sannan suka tafi shikuma yashiga gida. ****** Aban garen su *Deeya* yan barka tuni suka cika part din lnna wato yan'uwa da abokan arziki, kasan cewar haihur yamman shiyasa yan'uwa basu samu zuwa jiyaba saida yau, don haka kowa ka kalli fuskar sa cike da farin cikin samun karuwar da Allah ya azurta su dashi, Su *Deeya* kam anan like da baby tunda ta sallami *Habeeb* tanufi part din lnna, tadauki yaron ta kwakume duk wanda zaya ganshi itake bashi daya gashi sai ta karbe shi aikam yan'uwa natayi mata dariya abokan wasa kuma suna fadi to Ai kema kin kusa kawo mana naki baby, tace tab! itakam ai ga baby tanan yazo wanda zaya nan ga kuma na *Feeya* ne. *Habeeb* kam yana can shida *Harees* suna ganawa da mutane kamar yanda yasaba duk ranan asabar da lahadi, saidai lokaci lokaci yana saki lallausan murmushi saboda tunawa da irin farin cikin da *Leemarsa* ta shayar dashi jiya, haka dai komai yaci gabada tafiya har ranan suna inda yaron yaci sunan Baffa Al-mustafa wanda *Habeeb* ne yai masa huduba da hakan, Amma *Deeya* tace Affan za'aringa kiran sa suna kam ya kayatu sosai inda *Deeya* da *Feeya* sukai tasa kaya iri daya, abin su gawanin sha'awa. Aban garen *Jana* kam tuni ta tare gidan ado, yau kimani sati daya kenan sai gurzan kansu suke kamar kayan wanki, sai kace wayan da basu taba sani juna ba *_Bayan wata biyu_* ******* Ranan wata lahadi da misalin karfe 11:00 am *Deeya* ce zaune akan kushin 3 siter amma kafafunta akan cinyar *Habeeb* yana dan man matsa mata, kasan cewar sun dan kumbura tunda cikinta yashiga wata bakwai amma idan kaganta saika rantse yafi wata akwai, saboda wani irin girma dayayi sosai itakan ta takara girma kirjin nan kamar yafashe tayi kyau sosai sa bani wasu masu cikin da in cikin yayi girma sai kaga sunyi muni, itakam fresh tayi abinta gwanin sha'awa. Ahankali yake matsa kafafun yana fadin sannu kinji my honey *Leemah,* itakam sai zubama shi shagwaba take kafafun tajanye sai kuma ta matsa hankali zata kwanta akan cinyar shi dasauri ya kamata ya kwantar, tareda fadi sannun murmushi tayi cike da shagwaba tace yauwa sweetheart Dina amma dai idan ka tafi yau ba sai friday zaka dawoba ko?.., hannun shi cikin suman kanta yana ya mutsawa ahankali yace wane ni aibazan iya kaiwa har friday banganki ba, don haka ranan wed zan dawo. Tace yauwa Hmm na Allah idan katafi banajin dadi bacci da kyarna keyi yace humm nimafa haka ne, yanzu tashi muje ki dan motsa jiki kinga yauda bamuje ba kafafunki sun sake kumbura sosai, tace to tareda kokarin tashi ya taimaka ta tashi shima ya tashi tareda cewa bari na dauko maki hijab bayan yadauko mata wani brown din hijab yasa mata wanda yai mata matukar kyau sannan suka fita. Aban garen *Jana* da Ado kam abubuwa sun fara kwabewa tun bayan dagara yakare wanda dama bawani me yawa bane, kasan cewar ado baya sana'ar fari balle na baki sai danbanzan shaye-shaye don haka sai tafara daukar kayan ta tana siyarwa suna cin abinci, yanzu haka sauran katifar kwanciya kawai ta rage mata. kuma ya hanata fita ko'ina ta kuma kasa komai akan haka asalima wani irin mugun tsoron shi takeji, domin yace shi bazaya dauki wannan iskanci da tayi wa tsohon mijinta ba, sannan har yanzu beyi maganar sakiba be kuma bata damar tayi masa ba saidai yau ta kudiri ajiyar yi masa magana, domin ita ba zata iya wannan zaman talauci ba gaskiya gidan *BB* zata koma wlhy. Abuge yashigo mata kamar kullum zubewa yayi akan wata kwarababbiyar kushin tareda jefarda sandar shi, cike da tsoro ta karasa gurin shi ta zauna har zatayi magana sai ta jiya yafara sakin nashari tsaki tayi tareda fadi ina nan har sai ka tashi yau sai kasake ni. Aikam tana zaune har saida yatashi baccin mika yayi batareda salati ba, fuska had'e yace mata lafiya kika tsarini da ido haka... kodai kin fara maita ne kike tunanin ta inda Zaki fara ci ajikina?...Kai ta girgiza alamar "a ah, yace aha! mlm idan makin fara garakin daina don ni nan daki kagani duk maitar mutun sai yabar ni domin bazan ciyu agare shiba eheee! , Tashiki bani abinci yinwa nakeji. tace banyi ba yace saboda me?..tace saboda baka kawo ba wani irin mugun kallo yawa tsana ta tareda fadi dama nasa ba kawo wane?.. dalla mlm tashi kibani abinci kona saba maki, tace kaga ado ni banyi ba ba kuma zanyi ba tunda ban dashi nidama takardan saki nazo kaba ni, don bazan iya wannan zaman bakin talaucin ba gaskiya, wata irin muguwar dariya yasaki sai kuma ya had'e fuska lokaci daya idon shi ya rikida yayi jajir da karfi yashako wuyan ta, cikin tsananin bala'i da masifa yace... *_Aha! Adon Jana akaftaaaaaaa!_* Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿพ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [11/9, 10:12 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 7โƒฃ3โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ _NOT EDITS_ Me kikace zan baki?...cike da tsoro tace takardan saki, yace d'an sake maimaita wa naji yafadi tareda kai kunnan shi saitin bakin ta. Sake fadi tayi hakan ne yasashi fadin aha! *Jana* anzo gurin kenan sai kuma ya saki wata mahaukaciyar dariya, saida yayi me isar shi sannan kuma ya had'e fuska tamkar be tabayin dariyar ba yayinda idon shi suka sake rikidewa da ja cike da masifa yasake shake mata wuya cikin tsawa yace *Janaaaaah,* a matukar rude tace na'am yace kinsan sunan auren mu?... Kai ta girgiza alamar "a ah, wani mugun murmushi yayi sannan yace to sunan shi mutuka raba takalmin kaza wasu kuma suce takalmin karfe, don haka ki daina wahalar da bakin ki gurin fadin na sake ki tunda hakan bazaya samu ba kinga kenan zaman talauci yanzu kika fara shi agida na, dama saboda shine kika gujeni kika ki aure na saboda kin daukeni talaka kuma matsiyaci KO?... Humm *Jana* kenan bakisan hakan daki Kai mun ya haifar da muguwar tsanarki a zuciya ta, tareda daukar fansan abinda kikai mu domin ninan daki kaganni bana yafita akan abinda akai mun, Shiyasa lokacin dakika bukaci bayan auren ki zamu ringa haduwa muna cigaba da holewar mu na amince domin shine matakin nafarko dazan fara daukar fansa, saboda nasan komin daran dadewa sai mijinki yasani kuma na tabbatar aduk lokacin da yasani sai yarabu dake rabuwa ta har abada, domin nasan babu wani jakin namiji dazaya ga matarsa dawani kawon namiji agidan shi akuma cikin dakin shi suna aikata fasikanci ba ba tareda yasake taba, shiyasa nabiye maki mukai ta holewar mu tsawon lokaci har kika haifamun 'Da ba tareda sakaran mijina yasani ba wanda nayi mamakin hakan, saidai ban damu ba na cigaba da beye maki saboda inason hak'ona yacin ma ruwa. Sai kuma sannun ahankali hakon nawa yacin ma ruwa wato "mijinki yakama mu, inda yaimun dukan da sai dana naji kamshin mutuwa gashi nan ta dalilin hakan narasa kafata daya sannan kika kaini asibiti kinka wulakantar. Sai kuma kika zomun da maganar auren kisan wuta saboda kin maidani jaki talaka matsiyaci KO?... wato na aureki saina sake ki saiki koma gidan me kudi ki cigaba dacin daula nikuma na cigaba dacin talauci ko?.. humm *Jana* kenan to wlhy baki'isa ba billahi'azin idan duk mutanan duniyar na za'a taru bazan sakeki ba, saida mu mutu cikin talaucin dakike gudu kinji?...kuma kibani wata lanba zankira wan can banzan tsohon "mijin naki saboda duk layinsa basu shiga, don wlhy saina kona masa" rai kamar yanda yakona mun nawa sosai zana ci ubansa, wannan tsohon gwamna shegu masucin hakkin talakawa, yakareshe fadi dakarfi tareda girgiza ta yace zaki bani lambar kosai nasaba maki?... Cike da tsananin tsoro tace nifa banida shi idan ma ina dashi taya zan baka?... tunda dukan lanbobi na acikin waya suke kuma ka karbe waya Sannan karya Sim card din, Tsaki yaja mtsww! tareda ture ta tafadi tabaya sannan yabita da harara, yace na kwace din kuma nakarya Sim card din, idan kinada abinyi saiki kinji ko?.. domin ni ba Jaki bane dazan barki da waya kina kiran kattan banza, kuna iskanci kinji kuma inason ganin 'Dana" don haka saiki sannan yanda zaki don naga sai wani rike shi yake kamar dan shi. Sannan yadauki san dunan shi ya mike zaya fita kafarsa yasa yatake mata yatsun hannu ta dakarfi, wani irin karan azaba tasaki yayinda shikuma yasaki dariyar mugunta Sannan yafita. Yabarta tana matsan ido hankali ta tashi tareda fadin Allah ya'isa shege mugun, sai kuma tabuga tagumi cikin sanyi murya tace Oh! ni *Murjanatu* me ke shirin faruwa dani ne wai?..sai kuma tayi shuru can tace yaka mata naga Shafa. Sai kuma ta tashi dasauri tabi bayan adon talabe jikin kofa tana kallon shi ya zauna acan gefen kwalbati, tareda Ciro wayar shi daga aljihun gaban wata kodadiyar rigar t-shirt din dake jikinsa, layin *Habeeb* yalalubo yafara kira saidai akashe wannan layin yake, don haka sai yasake kiran wani layin da'aka bashi shidin ma akashe kamar kullum idan yakira haka yakeji, tsaki yayi tareda fadin dan'iske aikwanan nan zan gudanar da kudirina akan ka sannan yatashi, yatare mashin yafada masa ya kai shi Locos. Dasauri *Jana* ta koma ciki tashiga daki tadauko gyale tayafa tafi ta gidan Shafa tanufa, tayi sa'a ta'iske ta bayan sun gaisa ta kawo mata abinci taci sannan suka shiga fira nan take fada mata abinda yafaru tsakanin Ado. Cike da masifa Shafa tace amma dai ke banza wlhy yanzu sai kika tsaya sototo "yana fada maki abinda yaga dama?..., har yana shake maki wuya baki iyayin komai ba?.. cikin sanyi murya tace to ya zanyi nifa wlhy tsoron "shi nakeji tsaki tayi tareda cewa to tsaya jin tsoron shi, shi ko yamai da ke shashasha sakarya, tace to yanzu meye abinyi umh!?.. don Allah Shafa kibani shawara wlhy bazan iya cigaba da zama da "Ado ba gaskiya gidan *"BB* na zankoma, tace da dai yafi maki wlhy tace to ya zanyi yanzu?... tace yanda zakiyi kenan kicire tsoron shi idan yakarta maki rashin mutunci ke maki karta mashi, har sai yaga jiya sakeki, sannan kuma ki cigaba da shakatar warki idan yafita kema kifita don be yi yuwa ya'ajiyeki agida shikuma yafita yana holewar sa ato. Nan dai Shafa tayi tayiwa *Jana* hudubar tsiya itako tadauka tadade gidan sannan tafito cike da kwarin guiwa tanufi gidan hutawar Alh Barau tayi sa'a yana nan, yai matukar farin ciki da ganin ta nan sukai abinda suka saba sun dade suna aikata tsiyarsu sannan yabata mutanan ta wato kudi, tafito tanufi gidan su ta dan dade Sannan ta fito tanufi gida. Ta iske ado yadawo wani irin mugun kallo yawatsa mata tareda cewa uban wane yabaki izinin fita sannan daga gidan uban wakika fito?... aranta tace ubanka ne yabani izini fita, afili kuma tace kai kabani izini mana tunda kace kanason ganin Junior shiyasa naje gidan mu na famasu idan su Junior sunzo akawosu gidana inason ganin su, tsaki yayi yace kin kuru wlhy inda yawo

Chapter 34 of 42