Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nufi part din Hajiya kasan cewar can zasu kwana, koda suka shiga babu kowa a falon kasa duk antafi gida harsu Salma, a falon sama suka iske Hajiya zaune ita kadai kasan cewar su lili mama sun bisu Salma gidansu; Da gudu suka nufi gurinta suka fada jikinta kamar yadda suka saba tareda cewa washhhh! Hajiyarmu mun gaji kuma muna jin yinwa, tace sannu ku saidai abinci da kenan na "Abban kune domin yanzu 'ya'yanku" suka cinye sauran namu abinci sannan suka tafi, don haka sai ku tashi kushiga kichin kudafa abunda zakuci, Suka ce to tareda tashi suka shiga kichin din. *Feeya* tace kin same nake jin ci?.. *Deeya* tace "eh tace ah! haba dai tace Allah tace to chanki, tace ummm! alalan kwai dasauri tace yesss! kin chanka pls muyi shi tace "OK nan da nan suka hada abun bukata, Cikin minti kalilan suka gama hada komai har da abun sha wato zobo me abarba, *Deeya* na yayyanka alalan a cikin filet ita kuma *Feeya* tana zuba zobon acikin jug bayan tafaffasa kankara ta zuba aciki, sai kawai sukaji kiran sallar magrib *Deeya* tace mukai falo mu'ajiye idan muka idar da sallar magrib sai mu zomuci kinsan ita magrib saurin wucewa take, *Feeya* tace haka ne to mu kai bayan su ajiye sai suka nufi daki don yin salla. *Habeeb* yana idar da magrib yafito daga masallaci domin wata irin yinwa yakeji, kai tsaye part din Hajiya yanufa bai iske kowa a falon kasa ba don haka sai yanufi sama, Nan din ma ba kowa saidai abinci ya gani ajiye akasa bude wa yayi, aikam take wani irin daddad'an kamshi yabugi hancin shi dasuri ya sa spoon ya dauki alalan yakai bakin shi ya tauna, take yaji wani irin dadi yana ratsa kunnu wan shi dasuri ya zauna yafara aikama cikin sa alalan kwan, ciyeke aran shi kuma fadi yake to shikuma wannan meye haka da shegen dadi?..,๐Ÿ˜‚ nikam nace lallai *BB* smart din nan fa to alalan kwai ne, saida yaci kusan rabi sannan ya tsiyayi zabon yakora, dai-dai lokacin da suka fito yana ganin su ya daure fuska domin tuni ya fahimci sune suka ajiye saboda spoons biyu daya gani, ajiye cup din yayi tareda cigaba da aikama cikin sa abun da bansan kome ne sunan shi ba, kallon juna sukayi cike da tsananin mamaki *Deeya* tace?... Muje zuwa *_Kallon DIRAMA_*๐Ÿ˜‚ *_Nidai natafi ๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€sai kunzo_* A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน[7/2, 11:47 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 2โƒฃ5โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ "Abincin mu ne fa muka ajiye muje muyi sallah mudawo shine ka zauna kanaci?..cikin karfin halin me tattareda bugawar zuciya wanda yarasa dalilin dayasa yakejin haka, aduk lokacin da suka kasan ce gurin daya, ba tareda ya kalle taba yace "eh naci din, cikin itama cikin karfin hali domin tuni kirjin ta yafara bugawa tace haba don Allah Hmm *Habeeb* yunwa fa mukeji shine zaka cinye mana abinci mu; to yanzu me zamuci tunda Wanda aka dafa yakare??, yace "eh na cinye din sai nima kucinye ni, dai-dai lokacin da yake ture filet din gefe da'alama yakoshi kenan; kallon filet din tayi taga dan kadan yarage jitayi haushi duk ya kuleta har batasan lokacin da ta watsama shi hararan kasan ido ba, aikam tuni yaganta dasauri ya mike tareda cewa ke! nikike harara?..cikin tsoro ta matsa baya yayinda *Feeya* tafece da gudu daki, cikin tsawa yace nace nacinye din sai ayi kuli-kulin kubura dani, kai ta dukar tareda ta turo baki yayinda kirjinta keci gaba da bugawa, amma ahaka kuma take tunanin abunda zatayi masa ranshi yabaci kamar yadda shima; yabata masu rai. jintayi shuru yasashi sake cewa nace ayi kuli-kulin kufara dani, yafadi tareda kafeta da kyawawan idanun shi masu firgita ta; sai kuma akayi sa'a tadago Kai suka hada ido baki ta murgud'a ๐Ÿ˜ tareda matsawa baya, sannan tace bawani kuli-kul kubura daza ayi dakai kawai kabiya mu abincin, Cike da mamaki yazaro๐Ÿ˜ณtareda cewa ke! ni kike cewa na biya ku abincin ku??.. tace "eh don beyiyuwa munyi wahala yin abun mu saboda munajin yinwa Sannan ka zauna ka cinye, yace "OK to tabari nazo nabiya Ku" yafadi tare da dunfarar ta, dasauri tafece saida takai bakin kofa Sannan ta tsaya tace ah! Mlm, to ai bani zaka biyo ba kitchen zaka shiga ka dafa eheee!, Yace eyeee!๐Ÿ˜ณ lallai yarinyar nan kin raina ni wato din ne zan shiga kitchen ko?..tace "eh mana kaga kila ma yaudin nan ka iya shikenan sai kadinga girkama kanka; kaga ka huta yawon bin part by part kana cinyema mutane abincin su tunda ita "matar ka bazata iya girka maka ba, Sannan tashige daki tareda banko kofa. Cak! ya tsaya tareda rintse ido sai kuma yadafa,๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™‚ yace Kai! wato yanzu har "yaran nan sun san cewa part by part nake bi inacin abinci; Oh! ni *Habeebullahi* Allah ka kawo Mani mafita, _*Nikam nace to ameen BB Smart*_ Jiki a sanyayye naga yasauke hannun tareda juyawa zaya fita, sai kuma naga yanufi gurin sauran abinci spoon naga yadauka tareda alalan yakai bikinsa, (Wayyo๐Ÿ˜‚ku readers ku tayani gani dama BB Smart bai koshi bane?.. kodai dadin alalan ne yasake janshi zuwa karawa)๐Ÿ˜œ Saida yatauna dadin yasake ratsa shin Sannan yace to wai shi wannan din mene ne?..gashi kamar alala amma kuma ba shi bane to mene??, (nikam dana ke gefe nace alalan kwaine dan bani nima na lasa๐Ÿ˜‹) tsaki yayi tareda cewa Oho! masu" KO" mene ne dai su suka sani marasa kunya yara kawai, kai! kaji mun yarinya har da wani cewa na biyasu" to ni ๐Ÿค”Ina nasan ma ko menene balle nasan yadda akeyi, mtww! har da cewa nashiga kitchen hmm aizan Kama kine yarinya sai kingaya mun Dani dake wazaya shiga kitchen din Sannan yajuya yafita jiki a matukar mace. *Deeya* "KO koda tashiga daki ta'iske *Feeya* saman gado dunkule sai dariya takeyi, kasan cewar tana shiga dakin sai talab'e jikin kofa tanajin duk diramar da sukeyi, Da sauri *Deeya* tahau saman gadon ta d'aka mata duka abaya tareda cewa au dariya ma kikeyi KO?..cikin dariya tace to my sweet *Deeya* idan banyi dariya ba me zanyi?.. tace "OK yayi dai-dai wato maimakon ki tsaya murama abunda yai mana shine kika gudo ki ka barni KO?.., dasauri tazaro ๐Ÿ˜ณ tareda cewa ke! sweet *Deeya* murama kodai murame, tsaki tayi tareda cewa aini wlhy saida na rama tace to aike babba ce; tace Oh! shine kika gudo kika barni wato ni yaimun zalundin da yasa bako??, tace hmm aike gani nayi kamar baki jin tsoron shi" tsaki tayi tace wlhy inajin tsoron shi fiye da yadda kikeji kawai dai karfin hali ne "KO yanzu taba kirjina kiji yadda yake bugawa, saboda tsabar tsoron shi" amma haka na tsaya nafada masa magana nagudo. tace hhh yarinya ai zakiyi bayani idan kuka hadu badai har da Ce masa" kikayi yashiga kitchen ba, ๐Ÿ˜‚ Kai! gaskiya sweet *Deeya* yaukin samo Hmm *"Habeeb* murmushi tayi tace ai shima yau yasame mu damuka dafa abinci yazauna yacinye; kuma dakike cewa zamu hadu dashi basai na tsaya ba, dariya *Feeya* tayi tareda cewa "eh kam aikin iya ballewa da gudu kamar barewa,๐Ÿ˜‚. Dariya *Deeya* tayi tare da cewa to aike ma kin iya gudun tunda da anfara magana saiki fece da gudu kibarni, ke! yanzu nidai me zamuci ne nifa yinwa nakeji sosai?..tace muje muci wanda muka 'ajiyema "Hajiyar mu, tace ayya ita kuma fa?? tace to ai guda uku ne basai mu bar mata daya ba tace "OK to muje Sannan suka fita. suka nufi kitchen suka dauko alalar guda biyu suka dawo falo, da filet din "dayaci suka ci suka sha zobon bayan sun gama ciki sai suka sakeyin alwala don suyi sallar isha'i. Shikam *Habeeb* yana fita yanufi masallaci yasake yin alwala yashiga ya gabatar da sallar isha'i, bayan an idar sai sukayi karatu kamar yadda suka sa ba sannan suka fito, shida *Harees* inda *Habeeb* yanufi part din shi shikuma yanufi part din Hajiya. *Feeya* kadai ya'iske afalon sama tana ganin shi tamike zata gudu, dasauri yace haba me Darajata kefa nazo gani shine kuma zaki gudu, ahankali yakara sa gurinta; harsunajin kamshin turaran juna ido ta rufe cike da kunya, murmushi yayi tareda cewa kina lafiya?.. kaita gyad'a alamar "eh Kai me Darajata kiyi magana mana naji sweet voice dinki; shuru ba tace komai ba, yace ok shikenan tunda bazaki ce komai ba, to amma dai kin karanta sakona KO?? kaita gyada yace to ina amsa ta, cikin daddad'ar murya ta me tsuma masa zuciya aduk lokacin daya jiyata tace yana gurin sweet *"Deeya* yace yesss! naji muryar nan me dadi, da gudu tanufi daki tana dariya, Shima dariya yayi tare da cewa pls kice takawu mun gani nan inajiran ta. yana tsaye har *Deeya* tafito gaida shi tayi tareda muka mashi takardan Sannan, tace pls Hmm *Harees* kayi hakuri da abunda yafaru dazu kaji?? murmushi yayi tareda cewa nayi musamman da'aka bani amsa ta, Ina fatan yazamo me dadi yafadi yana dariya itama dariyar tayi, tace Insha'allah yace to nagode mu kwana lafiya tace Allah yasa, Sannan kice nace me Darajata ta kwana lafiya tareda ni acikin ZUCIYARTA" murmushi tayi tace to Zan fada tareda nufar daki shikuma yafita. ******* Da misalin karfe 9:00pm *Habeeb* ne zaune a babban falon shi nakasa yana kallon labarai, sai ya tuna da sakon da "gwamna ya bayar akawo masa tsaki yayi tareda tashi zaya nufi daki, sai ga *Jana* tafito cikin wata arniyar rigar bacci wadda kallo daya *Habeeb* yai mata yaji wani irin bu, ganin zaya shiga daki yasa tayi sauri karasawa gurin shin zata farayi masa kwarkwasa yai saurin dakatar da ita dacewa" kibari anjima zan ne me ki yanzu inada aikin da zanyi kaita gyada, Saidai kallo daya zakai mata kagane ba taso hakan ba, don haka nema yasa ta zauna jagwab saman kushin tana cizon leb'e, yayinda shikuma yashige daki envelop din yadauka dake saman gado tareda zama gefen gadon, yaciro takardan yafara karanta wa kamar haka. *_Zuwa ga Hon Habeeb H Soro_* *_Dafatan kanacikin kushin lafiya Allah yasa haka_* *_Ameen,dafarko ina kara tayaka murna samun kujerar sanata Allah ya tayaka riko ameen,_* *_sanna ina neman afuwarka abisa abinda "Mustafa yaimaka don Allah kayi hakuri kuruciya ce,_* *_Sannan Mustafa yanuna mani yanason kanwar ka "Haleematus-Sadeeya_*, *_so Idan ba damuwa ina nema mashi Auren "ta agurin ka,_ _kahuta lafiya inajiran amsar ka nagode daga gwamna._* Zumbur *Habeeb* yamike tamkar ancikara mashi allura,cikin tashi hankali yace?.. Muje zuwa A *_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya) Tareda โœ๐Ÿฝ ๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน [7/2, 11:47 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ _*KYAUTAR ALLAH CE*_ _(Labarin Sadeeya)_ ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ 2โƒฃ6โƒฃ WRITTEN By ๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ OR ๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ SADAUKARWA *GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)* ___________________ ยฎ _PEN WRITERS ASSOCIATION_ ___________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ โœ๐Ÿฝ _*Bismillahirrahamanirraheem*_ Me?...Ina ai bazai yuba da sauri yafita daga daki, *Jana* tana zaune afalo yawuce ta cike da tashin hankali, tana ganin fitar shi tayi saurin bin bayan shi don taga iya yanufa, gani tayi yanufi hanyar fita gidan alamar zaya gidan *Harees* kenan; kuma tasan idan yaje yana dade wa kafin yashigo gida, don haka dasauri takoma falon tadauki wayar ta takira layin Ado, tabud'e kara tace kayi sauri kazo yanzun nan "yafita kuma nasan gidan "wannan banzan abokin nashi yaje; kuma bazaya dawo ba sai 12:00pm do haka kazo muyi abinda zamuyi kafin yadawo. yace karki damu *Jana* ta nima nakasa hakurin rashinki shiyasa ma nakamo hanyar zuwa gurin ki, yanzu haka ma nakusa karaso wa bakin kofar gidan Ku tace to shikenan bari nafito sai nashigo dakai; kasan wannan megadin yacika binciken tsiya, yace haka ne ai shiyasa nayi wannan dressing din duk binciken sa bayaza taba gane ni namiji ne ba, tace yauwa Adamcy na shiyasa nake mugun sonka yace nima haka tace amma fa kar kayi magana don kar yagane cewa kai namiji ne, idan kazo kawai dai ka kwankwasa kofa yace to, sannan ta kashe wayar. tareda fita ta'isa bakin kofar dakin megadin ta kwala masa kira baba Haladu yace na'am Hajiya tareda fitowa, yace gani Hajiya fuska ta yamutse tareda cewa Ina da bakuwa ne gatan zuwa, yace to Hajiya dai-dai lokacin da sukaji ana kwankwasa kofa dasauri Baba Haladu yace Hajiya "KO bakuwar Ce"?.. ta'iso tace "eh ita Ce", dasauri yaje yabude kofar sanye da bakin abaya da hijab har da nikaf dasafa duk kaki, da sauri yarufe kofar tareda juyowa yace sannu dazuwa Hajiya, da sauri *Jana* tace ayya Baba Haladu aibata magana da maza, yace Allah sarki aidama wasu ustazan haka suke basa magana da maza, musamman ma wayan da ba muharraman su ba tace "eh sannan suka nufi part dinsu. Direct dakin ta suka nufa dake sama, tuni Ado yacire bakar abayan da nikaf da hijab dariya suka yi gaba dayan su tareda da kokarin fara masha'arsu. _*Oh!๐Ÿค” su Jana wannan wani irin cin amana ne haka?.. abun yanzu har cikin gida ake kawo kwarto, to Allah ya shirya Ameen saidai kuma ajuri zuwa rafi watara na tulu zaya fashe ko ba haka ba readers??....*๐Ÿคท๐Ÿปโ€_ *Harees* kam koda ya'isa gidan su; direct part dinshi yanufa, zama yayi ya karanta amsar da *Feeya* tabashi yana karantawa yana sakin lallausan murmushi, bayan yagama karanta wa sai ya linke takardan tareda cewa nagode sosai me Darajata dakika karbi soyayya ta, Sannan yasa cikin aljihun jallabiya kasan cewar itace ajikinsa. Sai yanufi dinning don yaci abincin da Hajiyar su takawo mashi, bayan yagama Sannan yanufi kwanfuta da alaman akwai wani aikin dazaya yi. Yana cikin aikin ne kawai sai ganin *Habeeb* yayi yashiga dakin kamar anjefa shi wanda hakan ba karamin mamaki yaba *Harees* din ba, don shi sai mayaji kamar *Habeeb* din baiyi sallama ba yashiga, Sai kuma yaga yafara safa da marwa, ga kuma takarda ahannun shi, kallo daya yai mashi ya hango tsantsar tashin hankali a tareda shi; hakan ne yasa yai saurin karasa aikin dayake tareda rufe kwanfutar yamike yanufi *Habeeb*. Kafadar shi *Harees* yadafa tareda cewa dan uwa naga kashigo ahargitse me ke faruwa ne?..bai Ce komai ba, saidai yamika mashi takardan karba yayi tareda fara karanta wa bayan ya gama karanta wa sai ya washe baki๐Ÿ˜, yace Kai! masha'allah amma naji dadi dajin haka, kai! dan'uwa wannan "ai abun farin ciki ne "Mustapa ai na tsatsen yaro ne dazun dinma matsala akasamu yanzu Kuma komai yawuce, kaga shikenan sai hada auren danamu tunda nima me "Darajata ta karbi soyayya ta, Cikin tashin hankali *Habeeb* yace to ni kuma fa?..Cikin mamaki *Harees* yace bangane Kai kuma fa ba??..ido ya rintse tareda turo hannun shi Cikin lallausan sumar kamshi; sannan yabude idon aikam tuni har sun chanja kala, sai kuma yafurzo da wata iska mezafi ta bakin shi sannan yafurta lna *SONTA"* fa, Cikin matsanancin mamaki tareda zaro๐Ÿ˜ณyace wa "kakeso?.. harara *Habeeb* ya zabgawa *Harees* din tareda cewa aikasan kowa" nake nufi, baki๐Ÿค”yakama tareda cewa Oh! Ni *Hareesu* to ni yaza'ayi nasan kowa kakeso tunda niba allan musuru bane umm??; Dakarfi yace *"LEEMAH* nake *SO* inasonta! inasonta!! inasonta!!! sosai fiye da yadda nakeson Kai Na,duk wani abu Da kaga inayi karfin hali ne kawai amma wlhy inason ta" cikin mamaki me dauke da tsokana, domin tuni *Harees* ya fahimce shi amma sai, yace Oh!๐Ÿค” yanzu kai saboda Allah Leema ka keyima irin wannan son haka amma ka kasa mallakarta?... Cikin bacin rai *Habeeb* ya cakumi kwalar rigar *Harees* din dakarfi yace banason iskanci *"Leemah* nace ba lema ba, kuma kasani sarar cewa *"Haleematus-Sadeeya* nake nufi inaso, yace Oho! to sakar mun kwalar riga kar kayima me "Darajata hasara, sakar mashi rigar yayi tareda zama yana sauke wani irin numfashi, shima zaman yayi tareda cewa to ai sai kace mun "queen of beauty kakeso, Cikin hasala yace yesss! ai kasani i love "her since. Dariya ce takwa ce wa *Harees* aikam tuni yafara yinta har da rike ciki saida yayi me isar shi tukun Sannan ya tsaya, ya kalli *Habeeb* yace Alhamdulillahi! "anzo gurin kenan KO?..bai jira amsar shi ba, ya cigaba dacewa tabbas nasan kana sonta tun tsawon wani lokaci, Kai idan ma banyi kuskure ba tun tana cikin zanin goyon ta" ko?.. kai *Habeeb* ya gyada tamkar k'adan gare tareda tsura masa kyawawan idanun shi, *Harees* yace yauwa amma kai atunanin ka bansan kana sonta bako?.. Shiyasa naitayi maka hannun ka me sanda amma sai kanata basarwa tareda bonewa, wai kai adole sarkin yan *ZURFIN CIKI*, to aiga irinta nan wanda shinake ta gudar maka tun tuni amma kakiya sai kana tafaman kunshe abu acikin ka, kai! "ai kama gode sakon bata hannun su" Abba yazo ba; tabbas in data hannun su" yazo da sunan ka sorry domin kasan su sarar cewa su" din mutane ne masu alfarma. Cikin sanyi murya *Habeeb* yace to yanzu meye abun yi?..wlhy inason ta irinson da bansan adadin shiba bana kuma son narasa ta, yace yanzu bari na dauko maka biro da takarda ka rubuta masa "amsar anyi mata miji, sannan ka rubuta ma "Queen of beauty kana son ta kamar yadda nayima me Darajata" wanda dama nadade inafada maka lokaci nake jira, so lokacin yayi kuma nafada "mata ka gama amsar data" bayi yafadi tareda ciro takardan. Yamika mashi bamu su *Habeeb* yakarba yakaran Sannan yamika mashi, ido ya yarintse sai kuma yabude cikin sarkewar murya yace bani dai na rubuta ma "gwamna amsa, amma bazan iya rubuta ma taba domin yin hakan raini zanjama kaina, tsaki *Harees* yayi dai-dai lokacin da dayake mika mashi takarda da biro, yace matsalar ka kenan saikace wai zasu" raina ka nikuma banga wani rai ni dake tsakanin ka dasu" ba, su" da suke tsoron Kama. yace haka ka kegani amma *"leemah* tarena ni rashin kunya ma fa take mun, dazuma fa ce" mun tayi wai nashiga kitchen daga kawai sun ajiye abinci naci, nan yafada mashi abunda yafaru. dariya *Harees* yayi tareda cewa ah! to kai kuma aiba'a haka, yace yinwa nakeji so nikam naga abinci shiyasa naci. murmushi yayi yace to shikenan nidai yanzu kafa da mata kana son ta; *Habeeb* yace nifa bazan iya fada ma taba, yace to ni gobe zan fada ma Abban mu kaga sai atsayar da maganan agurin mitin KO?.. dasauri yace a ah! karka fada, nan dai suketa faman jayayya yana cewa zayafadi shikuma *Habeeb* yana cewa kar yafadi, cikin bacin ran *Harees* yace to wai kai yakake son ayine?.. bai ce masa komai ba saidai yadauki ta takardan da yarubuta ma "gwamna amsa, yafita alokacin karfe 10:30pm. ******** Su *Jana* kam saidai11:30pm sannan ta sallami Ado saida tabbatar *Habeeb* yashiga daki ta kuma tabbatar ya kwanta, sannan tarakashi bakin get. tana kokarin bude mashi kofa yafita sai baba Halidu yajiyo motsi don haka dasuri yafito yana cewa wanene?.. Cikin kwantar da murya tace baba nice ba kuwa tace zata tafi gida, cikin mamaki yace ah! Hajiya ai nace ko nan zata kwana; tace a ah zata tafi gidane yace Allah sarki tareda bude kofar yafita, ita kuma tajuya cikin gida shikuma Baba yakoma daki. Shikam *Habeeb* koda yakoma bai kwanta ba asalima daki yanufa yahau kwanfuta yafara aiki, saidai kuma wani abun mamaki baya game abun dayake saboda tsabar tunani dayake, yayinda *ZUCIYAR* shikam sai bugawa take wanda yarasa dalilin dayasa yake jin haka, Sannan kuma aranshi sai yana jiyake kamar zayarasa *Sadeeya*. Har misalin 1:00pm *Habeeb* baiyi aikin komai ba gani yai yana shirin yin barna, don haka saiya kashe kwanfutar yashiga toilet yadauro alwala yazo yafara gabatar da lafila inda yaita rokon Allah yazaba masa abunda yafi zama alkhairi tsakanin shida *Leemah,* saida yaji ankira sallah asuba sannan yanufi masallaci. ****** Washegari da misalin karfe 10:30Am *Deeya* Da *Feeya* ne zaune a falon kasa, fito wansu kenan da'alama sun fito gurin mitin din kenan, sai zuba dadda'dan kamshi suke suna sanye da wata farar atamfa me ratsin bulu, anyi masu irin dinkin da'ake yayi yanzu wato me fadin hannu wanda tsawon rigar yakusa kaiwa guiwa basu daura dan kwalin kayan ba, sai suka dora gyale bulu akai wanda yasauko kafadar su sunyi kyau sosai yan biyun Hajiya. Sai fira suke abun su gwanin sha'awa, inda naji *Deeya* tana cewa yau su" Adda Mamu basu zo dawuri ba *Feeya* tamike tareda cewa "eh fa sweet *Deeya* bari naje nayi fitsari tace "OK, tareda jingina bayan ta da kushin tarufe ido tana saurare kira'a. Kasan cewar idon ta rufe yake don haka batasan shigarsa falon ba, saidai taji kamshi turaran shi wanda yasa tayi sauri bude ido, gabanta ne yafadi sosai saka makon gani *Habeeb* tsaye a gefan kushin din da take zaune yakafeta da idanu, yana sanye dayadi baki wanda akayi masa aiki dazare yalo irin dinkin nan ne me kama jikin mutun, kanshi ba hula hannunshi daure dawani tsadaddan agogo kafarshi sanye cikin irin takalmi nan me rabin shi abude, gaskiya yayi kyau sosai. Dasauri tamike zata gudu yace kina ma tsawa daga gurin nan Zaki sani,don haka ta tsaya cak! saidai jikinta sai rawa yake matsawa yayi kusada ita har suna jin daddad'a kamshin turarensu wanda yasa zuciyoyin su bugawa a lokaci daya, dasauri ta daga kaita kalle shi shima ita yake kallo hakan neyasa tai sauri dukar dakai kirjinta yana cigaba da bugawa, yayinda shikuma yahade fuska yace dani dake wanene yaka mata yashiga kitchen?.. Cike da tsoro tace nice, yace amma shine jiya kika ce nashiga kitchen nayi girki saboda kin raina ni ko?..dasauri tace don Allah kay... katse tayayi dacewa shittttttt! banaso ina magana a nayi, Cikin rawar murya tace to kayi hakuri bazan sake cewa ba, baki yatab'e yace yasunan wannan jagwalgwalon abun nan najiya?.. Dasauri ta kalle shi da mamaki jin abunda yafada, yace malama tambayar ki nayi ba kallo na nace kiyi ba, baki taturo tareda cewa sunan shi alalan kwai, yace to naji wuce bani guri. Da sauri ta gudu saida ta hau saman, bene sannan tajuyo ta murgud'a masa baki ๐Ÿ˜sannan tace kajishi;saida ya zauna yacinye abu sannan zaice wai jagwalgwalo, saida kuma jagwalgwalo yayi Rana tunda yacika stomach tafadi tareda kyalkyacewa da dariya ๐Ÿ˜‚ ,don haka kar amanta sunanshi alalan kwai ๐Ÿ˜œ sannan takarasa hayewa da gudu tashige dakin su, Shima dariyar yayi tareda cewa yi ahankali *Leemah* ta; sarki tsokana karki fadi sai kuma ya lumshe ido yana jin *SONTA* yana ratse jininshi ahankali yabude idon, sannan yace inason wannan *DIRAMAN* _between me and U,_ sannan yayi murmushi tareda girgiza kai yashiga dakin Abba don su gaisa. ******* Koda12:00pmm babban falon yacika kamar yadda suka saba dukka family sun hadu ya'ya' da jikoki, saida sukaci abinci sannan suka zauna mitin din *Deeya* Da *Feeya* suna man ne jikin Hajiyarsu; kamar koda yaushe Baffa ne yabude taron da addu'a bayan yagama, sai Abba yai gyaran murya tareda cewa Alhamdulillahi! mungode ma Allah daya sake muna mana wannan Rana lafiya, wacce tayi dai-dai da kammala karatun yan biyu Hajiya, kuma dama kowa yasan al'adar gidan nan duk wacce ta gama secondary school, aure ake yimata saidai idan taje gidan "mijin in ya amince ta cigaba da karatu to, idan kuma bai amince ba sai tayi hakuri ta zauna tayi bautar ubangiji, koba haka ba?..yan' uwana Baffa da Baffa Al-mustapa sukace wannan haka ne. yace yauwa shiyasa muka yan ke shawarar sanar daku wani hukunci damuka yanke, tareda wani *SIRRIN* da baku saniba, don haka muka ga yaune yadace kusan dashi" Bismillah Alh Al-mustafa kasanar dasu, yace "a ah Alh kasanar da su kawai, *Habeeb* kam jiya yi kirjin sa yana bugawa Wanda yarasa dalilin dayasa yaji hakan, Abba yace to shikenan dama munasan mu sanarda ku cewa zamu hada *Harees* da *Safeeya*

Chapter 10 of 42