tabashi kudin data karba gurin *Habeeb.*
********
A haka rayuwa tamika har *Jana* tasamu ciki Wanda kusan tare suka samu da Safeena,
Saidai cikin *Jana* yariga Na Safeena, don haka itace tafara haihuwa inda tahaifi d'a naminji Wanda shi baiyi kama da *Habeeb* balle ita *Janar,* ranan sunan yaro yaci sunan mahaifinta mlm Sani,
wanda itace tanemi asa sunan don haka sai suna kiran shi Junior,
haka ta cigaba da reno Junior tareda taimakon wata tsohuwa da Hajiya tanemo mata domin ita tace bazataje gida wanka ba.
*******
Watan Junior daya Safeena ta haifi 'yarta mace kyakkyawa me Kama da'ita, saidai kuma KO" minyi biyar batayi da haihuwar ba tace ga garin kunan๐ญtarasu tabar yar jaririya,
Rasuwar data girgiza dukkan family musamman *Harees* da yafi kowa jin mutuwar, domin adan zaman dasukayi ta kyautata masa sosai, haka nan aka kaita gidanta tana gaskiya.
Bayan sadakar uku sai akace *Jana* tadauki jaririyarta tacigaba da shayar da'ita yayinda *Jana* tatuma kasa tace Ina itakam sam bazata shayar da'ita ba, kona tama yatakare da shi ballena wasu"
*Habeeb* bai nuna bacin ran sosai ba ko"dama shi ba'ason ran shiba *Janan* zata shayarda jaririyar ba,
Saboda sam batada halin kwarai saidai yanda ta muna agaban mutane baiji dadi ba, shima *Harees* bawai yayi na'am da hakan bane shiyasa ma koda tace bazata shayarda jaririyar ba bai wani nuna damuwa ba,
domin shima halayyar *Janan* bai masa ba, don haka sai kawai lnna Hafsatu ta dauke da a ka cigaba da bata madara.
*Ranan suna*
*******
"Diyar da Safeena ta bari tayi taci sunan mahaifiyarta sai su *Sadeeya* suna kiranta little Feena tayi bulbul abun fiyeda yaron dayake shan nonon uwa,
ahaka rayuwa tamike har
*Jana* tasake haihuwa tahaifi ya mace kyakkyawa me kamada *Habeeb* sak inda taci sunan Hajiya wato Rabi'atu, sai suna kiranta lili mama, kuma har wannan lokaci *Jana* bata chanja komai daga halinta ba saima abunda yakaru,
duk boyewar da *Habeeb* yake don kar afahimci zaman dasuke da *Jana*, narashin iya girki da kuma kyautata masa saida Hajiya tagane domin tuni yagaji da cin abincin saye yakoma zuwa cigurin Hajiya.
kawaye ko nabanza duk *Jana* ta tarasu don ma *Habeeb* yana mugun jamata burki, itama kuma duk iskancinta tana tsoronshi,
yawan kyatar dasu *Habeeb* keyi tareda taimakon jama'a yasa arzikisu yake ta cigaba, inda Abba ya gina wani katafaran asibiti don haka sai *Habeeb* yacigaba da kulada kamfani, shi kuma *Harees* yake kula da asibitin wanda gashi dai private ne,
Amma haka talakawa damasu kudi ke rubibbin zuwa saboda yana dauke da kwararrun likitoci, kuma akan kudi kalilan ake treatment din mutun.
Alokacin sun
*Sadeeya* da *Safeeya* sun zama cikakkun yan mata masu tsanani kyau da tsafta tareda nutsuwa uwa uba ladabi da biyayya, alokacin shekarusu goma sha hudu suna SS 2 domin kwazonsu da girma su yasa akai masu Jumping,
sun sauke al'qur'ani mai girma bayan litattafai da dama dasuka haddace, suna kuma daukar hadda gurin Baffa, sannan sun iya girki sosai dagana gargajiya harna zamani, wanda Hajiya da lnna dasu Adda Mamu sun koya masu,
sai na larabawa dana turawa shikam a t.v suka koya saboda tsabar rigima iri tasu haka suke komai tare gwanin sha'awa,
Wata rana su kwana part din lnna wata rana kumasu kwana part din Hajiya.
Ranan wata alhamis suka gama jarabawar shiga SS3 direba beko gama parking ba, *Sadeeya* tabude mota tafito da gudu tanufi part din su *Safeeya* saboda fitsari da yamatse ta, alokacin shekaransu sha biyar-biyar, bayan direba yagama yin parking sai *Safeeya* tafito tanayi mata dariya hannun ta dauke da jakarta tareda na *Sadeeya* tabi bayan *Sadeeyar* zuwa cikin gida.
Da gudu tawuce Hajiya dake zaune a falon tacewa sannun da gida Hajiyarmu cikin murmushi tace yauwa hali dubu na an dawo, tace "eh tana hawa bene dasauri, Hajiya tace ah! ya haka kuma hali dubu na bana hana shigowa da gudu ba..?, tace yi hakuri Hajiyarmu fitsarine yamatseni shiyasa, tace toh" ayi ahankali lokaci tuni tashige.
shikam *Habeeb* baki yatabe kasan cewar yashiga suna magana da Hajiya, salati tareda ihu sukaji *Sadeeya* ta nayi ai dasauri Hajiya da *Habeeb* suka mike suka nufi saman dai-dai lokacin da *Safeeya* tashiga dasauri itama tarufa masu baya,
Dukkansu suka shiga cikin dakin har da *Habeeb* yayinda ihun *Sadeeya* ke sake ka ruwa yake, cikin tashin hankali Hajiya tanufi toilet din dasauri *Safeeya* zata bita cikin tsanani bugawar zuciya *Habeeb* yadaka mata tsawa tareda watsa mata harara yace baki da hankali ne...?
tsayawa tayi jikinta sai rawa yake zuciyarta cikeda tsoro tareda zullumin abunda yasami *Sadeeya*, shikam *Habeeb* kirjinsa ne yacigaba da bugawa ga wani irin tsoro daya darsu acikin zuciyarshi,
Hajiya nashiga toilet *Sadeeya* tayi sauri ta rungumeta jikinta sai rawa yake cikin kuka tareda tsantsan tashin hankali tace...?
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ8โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Wayyo Hajiyarmu nashiga uku yau zan mutu, cikin tashin hankali Hajiya tadago da kanta daga kafad'arta tare da cewa subhalallahi!,
kul! nasa kejin kince kin shiga uku nan sannan,
kuma dama ai kullunafseen za'ekatul'mauttt! duk kan rai sai tad'and'ani d'acin mutuwa kinsan da haka ko...?, ciki kuka ta gyada Kai alamar "eh yayinda jikinta ke tafaman rawa,
tace yauwa hali dubuna toh"kinutsu ki fadamun menene yafaru...? Cikin rawar baki tace umh-umh! Hajiyarmu fitsarin *JINI* nayi kingani KO" tafadi tareda nuna mata gurin da tayi fitsirin,
shuru Hajiya tayi tareda tsurawa gurin ido can kuma sai tayi ajiyar zuciya, tareda d'aga Kai ta kalli *Sadeeya* sai kuma tayi murmushi wanda yaba *Sadeeyar* tsoro,
Sannan tace Kai hali dubu Na shine duk kika tada hankali kin Dana mu..? Cikin tsanani kuka tareda tsoro tace wayyo Hajiyarmu tunda nake ban taba fitsarin jini bafa sai yau, kingan shifa tafadi tareda sake nuna mata, kinga ko aidole natada hankali na,
Cikin kwantar da hankali Hajiya tace toh" kwantar da hankalin hali dubu na wannan nan din "aiba wani abun damuwa bane,
idon *Sadeeya* ta zaro cike da tsoro sai kuma ta shagwabe fuska da tuni tasharbe da hawaye, tace fitsarin jinifa Hajiyarmu...dariya Hajiya tayi tace ba fitsarin jini bane, da sauri tace toh" Hajiyarmu menene...?
Daure fuska Hajiya tayi alamar ba wasa sannan tace al'adarmuce ta mata wato haila, wadda duk macen data farayin shi taje tana wasa da maza shikenan saita samu ciki, Cikin tsanani tsoro tace Hajiya aimu bamuyin wasa da maza.
Tace yauwa haka nakeso don haka kiyi shuru kidaina kukun nan haka kinji KO...? tace toh", dariya Hajiya tayi tace Masha'allah 'yata tagirma Allah ka tsaremun ita daga sharrin mutun da aljani,
murmushi tayi yayinda taji wani irin kunya yarufe saboda shirmen datayi, don haka dasauri tafada kafadar Hajiya cike da jin kunya domin itakam ta manta dawani abu da mata keyi waishi haila,
dariya Hajiya tayi tareda cewa hali dubuna kenan nan dai tagwada mata yadda zatayi, tareda sake yi mata gargadin karta kuskura takula maza sannan tafito daga toilet din.
Shikam *Habeeb* tun lokacin da yaji Hajiya tace haila ce tana gama fada mata yafita daga dikin saidai yarasa meyasa kirjinshi yake bugawa, afili yace yanzu har ta'isa fara mensturation...?
Sai kuma yace _yesss! she started because she have fifteen years_("eh zata iya farawa tunda takai shekara sha shidda), sai kuma ya tabe baki yayinda yake lafiya ahankali har yafita daga part din yanufi part dinshi.
don haka koda Hajiya tafito bata ganshi ba saidai *Safeeya* dake tube school uniform tanama *Sadeeya* dariya, shirmen data kwab'a afili tace Kai! Sweet *Deeya* saikace ba'ayi mana bayanin komai a islamiyya ba, ganin Hajiya yasa tadaina dariyan tareda yin shuru.
yayinda Hajiya tace Ina "Hamman din naku...?.tace hmm! yatafi bayan yagama dokamun tsawa da harara kuma fa ban masa komai ba, daga kawai zanbiki toilet naga meya samu sweet *Deeya* take kuka shine fakawai ya hanani ta karashe fadi da turo baki,
murmushi Hajiya tayi tareda cewa toh" ai gara daya hanaki tunda baki jin magana ashe bana hanaku shiga toilet tare ba..? tace "eh toh" aimun daina dama danaji tana ta ihu ne sai tsoro yakamani, nayi zaton kotaje kashi ne tafada Cikin masai ta karashe fadi dayin dariya๐.
itama Hajiyar batasan lokacin da dariyar takufce mataba tace kai yaran nan Allah dai yashir yaku da wannan shirmen naku, zata fita sai *Safeeya* tayi sauri tace au! Hamman *Habeeb* yace" zaya shigo anjima tace Allah yakaimu sannan tafita.
Wani abun mamaki kuma shine aran da yamma itama *Safeeya* taga nata period din, nan dai Hajiya taha dasu tai tayi masu huduba mai tsoratarwa gameda period din itama lnna tayi masu nata,
******
washegari Jumma'a da misalin karfe 7:20Am *Sadeeya* tafito daga part dinsu tana sanye da school uniform, hannun ta rikeda wani littafi zata shiga part dinsu *Safeeya* saiga *Habeeb* shima zaya shiga yana rungume da lili mama aka fadarsa,
yana ganin ta yafara ke!an dubu tayi banza dashi tashige abunta, kuta yayi tareda cewa Zaki sani idan na shigo afalon kasa ya'iskesu suna rataya jakar makaranta dama ita *Safeeya* kejira yayinda Hajiya take sallamar su, gaida Hajiya yayi tareda mika mata lili Mama,
sannan yajuya ya harari su dasauri *Safeeya* tace Ina kwana bai amsaba saidai yasake watsa ma *Sadeeya* harara, wanda yasa taji gaban ta yasake fadiwa don hakan tayi saurin ce masa ina kwana tareda turo baki, domin tasan sai yaimata zalu,
aikam
bata ko rufe baki ba yamika dogon hannun shi yarantaba mata lafiyayyan rankwashi, Wanda yasa tasaki kara acikin shagwaba tace Hajiyarmu kingan shiko..?
tace toh" Allah yaida regari ya waye nidai don Allah daga yau kar kasake dukan mun yara domin yarana sun girma ka, baice komai ba yanufi dakin Abba saidai tundaga Rana ya share su domin shima yana gani idan yacigaba da meye masu zasu rainashi,
yayinda *Sadeeya* tace" tunda Hajiya tace karya sake duk kansu toh" saita rama zalu dayayi tai masu.
*****""""********
Yawan nasiyar da Baffa yakema *Jana* akan yawar fitar da takeyi ba'akan ka'ida ba wanda tuni Baffan ya fahimci cewa *Habeeb* din baida masaniya, shiyasa yake mata nasiya inda yake fada" mata cewa fitarnan fa Da takeyi ba tareda mijinta yasani ba haramun ne kuma tana daukarwa kanta zunubi megirma yayinda take kwasarwa iyayenta tsiniwa tareda la'anta,
hakan dayake fada matane yasa tadauki tsanar duniya tadora akan Baffan inda takeji kamar ta kashe shi, tasha auna yimasa rashin mutunci amma kuma saita kasa, saboda
Mugun kwarjini yake mata saidai kullum tafurta zatayi maganin sa.
********
Shikam *Harees* tun Bayan rasuwar Safeena bai sake tunanin yin wani auren ba, haka zalika su Baffa ma basu matsama saba gani yadda mutuwar ta taba shi sosai, don haka sai kawai yacigaba da aikinsa yayinda yadauki son duniya yadora akan little feena, Wanda kusan kullum yana kan hanyar zuwa ganinta shi da mutanan sa *Safeeya* Da *Sadeeya,*
Domin suma suna matukar son little feena, don haka kusan kullum tareda suke zuwa ganin ta, kasan cewa suna matukar shiri sosai da *Harees* dama shi yana sakar masu fuska,
sabani *Habeeb* da'ake yawan daure fuska domin yasha fadawa, *Harees* cewa wayan nan yaran yanda kansu kerawa idan ana sakar masu fuska sai su rainai mutun shiyasa baya sakar masu fuska,
yayinda suke yawan fada *Sadeeya* saboda ke! dakuma an dubu dayake kiranta ita kuma bata so shiyasa suke fada itakuma Hajiya tai tashari'a.
*********
Haka rayuwa ta mika aban garen *Jana* babu abunda ta chanja daga halinta yawo kam ba'a magana musamman da *Habeeb* yasiya mata mota, wanda saida Abba da Hajiya sukasa baki" tukun,
Sannan gata batasan yadda zata kyara yara ba saidai komai tasa me aiki tayi don haka rabin raino yaran duk *Safeeya* da *Sadeeya* suka yishi, *Habeeb* yayi fada akan abubuwan datake har yagaji amma a banza, ahaka harta yaye lili Mama, ranan data yayeta yadauke taya kaiwa Hajiya yace"yabata *KYAUTA*,
domin yanasan tasamu tarbiyya me kyau saboda yana tsanani son lili maman fiyeda Junior shiyasa ba yasan ta sauki munanan halin Uwata, yayinda *Jana* tace ita sam saidai abar mata yarta domin itama lili Mama tashiga ranta sosai don haka batajin zata'iya rabuwa da'ita, shi kuma *Habeeb* yace" bata'isa ba Hajiya tace" ta kwantar da hankalin ta idan lili maman ta manta da nono za'a dawo mata da'ita.
haka akayi bayan wani lokaci sai aka matar mata da yarta saidai kullum part din Hajiya take wuni, shiyasa tayi saboda su *Sadeeya* sosai,
ahakadai harsu *Sadeeya* suka shiga ss3.
Lokacin da *Hafeez* yadawo daga misira kasan cewa tun daya gama secondary yatafi karatu can Bayan yadawo ne sai shima yafara aiki a company kasan cewa shi me kazo.
*******
"A lokacin da zabe yagabato sai manyan yan siyasa sukayi meeting cewa bai kamata su sake goyama senator A B Talha baya yayi tazararce ba, tunda baimasu komai ba don haka sabon candidate zasu tsayar haka ko akayi inda suka tsayar da *Habeeb,*
domin suna da tabbacin zayayi masu adalci kamar mahaifinsa su, da lokaci yazo akai primary elections *Habeeb* yabuge abokin takaranshi yanzu haka general election akejiya yazo akafta,
Yayinda su kuma su *Sadeeya* zasu fara rubuta jarabawar su tafita ranan Monday wannan kenan.
*_Cigaba Labarin_*
*_wanda yanzu za'a fara don haka_*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart ce๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ9โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
*_WANNAN page_* *_nakune_*
*_MASOYANA_* *_nagode kwarai_* *_da irin KAUNAR KU agareni,_* *_inayiku kwarai dagaske Allah yabar zumunci tareda kauna mai d'orewa, don haka wannan page KYAUTA NE agareku kuyi yadda kukeso dashi nagode_*
*_Love yours with all_* ๐
*_my heartโค irin over din nan fah_*๐.
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Cigaba
Aunty *Deeya* Aunty *Feeya* shine abinda lili Mama take fadi harta haye bene nan, dasauri ta tura kofar daki abun sha'awa bakinta dauke da sallama, dai-dai lokacin da *Sadeeya* tanufo kofar suka hade ta amsa sallamar sannan da sauri tada gata lili maman suna kyalkyala dariya,
kiss tayi mata akumatu tareda cewa I miss u lilin Daddy itama kiss din tayi mata Cikin gwaranci hausar ta, tace mici u chuuuu Aunty *Deeya,* tace ina "Junior...?
tace chuntafi challa chida "Daddy na da "ankal chine Daddy na yace" nazo muni challa taye, dariya *Sadeeya* tayi saboda yadda lili Maman keta tabka gwarancin tace toh" lilin Daddy mutafi toilet muyi alwala sai muzo muyi sallah KO"? Kai ta gyada, har zasu nufi toilet sai lilin tace lah! Aunty *Deeya* bakince accin malance(yamma) bachau ba?...
tace "eh babu kyau, tace toh" kalli Aunty *Feeya* tana em accin malance, dariya *Sadeeya* tayi tareda cewa oh! my lili na manta ne toh" zomuje mutada ita sai tayi sallah ko?..tace "eh tace yauwa my lili toh" sauka,
tasauka tareda hauwa saman gadon da sauri tana dariya gurin kafar *Safeeya* taje tayaye bargon, yayinda itakuma *Sadeeya* taje ta gurin kanta tareda kallon lilin tace oya mufara alokacin guda naga sun fara,
tafiyar tsutsa lili takeyi mata kafa yayinda ita kuma *Sadeeya* take Shafa lallausan kashin kanta,
_kasan cewar hakasu ke tashin junansu barci._
ahankali take Jan kafarta can kuma saita bude ido ahankali tazuba su akan, *Sadeeya* daketa faman yimata murmushi, cikin sanyin murya tace lokacin sallah yayi,
yayinda lilin ta haye jikinta tana dariya, da sauri *Safeeya* tace auchhh! lilin Daddy zaki karayani kufa kinga bani da lafiya ta kareshe fadi cike da shagwaba, dariya lilin tayi tareda cewa "e akuyi Aunty *Feeya* yajiki kinji chauki...?
murmushi tayi tace naji sauki, tace toh"ki tachi muyi callah, ahankali ta tashi suka nufi toilet.
**********
Saida akayi sallar isha'a sannan su *Habeeb* suka fito daga masallaci shi dasu Baffa, Bayan sun gaisa da Baffan sai yaja hannun Junior suka nufi part dinsu,
yayin da suma su Baffa suka nufi part dinsu shida *Hafeez* suna tafe suna fira gwanin sha'awa har suka'isa, da sallama suka shiga falon lnna ta amsa tana ninke dadduma alamar itama sallar ta'idar,
Cikin shagwaba *Hafeez* yace lnna ta nadawo tace sannu *Hafeezeena* kadawo lafiya dafatan ka barosu" addan naku da yaranta lafiya, sannan Ina su" lili Mama...?
yace su addasu na lafiya su lili kuma suna can part din Hajiyarmu tace toh" masha'allah yace lnna ta saidai nikam nagaji kuma inajin yiwa,
murmushi tayi tace sannu *Hafeezee* na
bari nakawo maku abinci idan kaci sai kaje kai wanka ka kwanta ka hutu ko..?
yace yauwa lnna ta Allah yabar mun ke da Baffa na,
Murmushi Baffa yayi tareda zama akan kafet yana cewa *Hafeezu* kenan ai duniyar nan dakake gani bama tabbata bace, lnna tace kwarai kuwa Baffa yace toh" amma sun Kullum dai maganar su kenan shida *"KYAUTA* Allah yabar masu mu toh" shikuma Allah baya bari wani don wani,
yace toh" Baffa Allah yaja kwana, yace hmm! *Hafeezu* kenan kaidai kawa kace Allah yanufa muga Auren ka yace toh" ameen Baffa na lnna tace gaskiya kam toh" ameen dai-dai lokacin da tashiga kichin.
Can saiga ta tafito dauke da babban faranti da kula da filat akai dasauri *Hafeez* yakarbi farantin ya'ajiye tareda cewa sannu lnna ta tace yauwa sannu,
abinci tabude tuwan shinkafa miyar kubewa danye kamshi man shanu sai tashi yake, ahankali take ciro tuwan aleda tanasa masu kan filet, can sai *Hafeez* yace lnna ta yau naga Hajiyarmu kamar tana cikin damuwa,
Tace ashsha, dai-dai lokacin data da ta tura masu abincin gabansu tareda cewa Bismillah, sannan tashi tanufi fridge tadauko jug tareda cups guda biyu tan cewa to" ko meyake damun Hajiyar...?
yace bansani ba domin na tambaye ta tace"mun ba komai, saidai nasan tace" Mun hakane kawai saboda kar na dameta da tambaya, amma tabbas akwai abunda ke damunta,
bayan tazuba masu sobo sannan tace toh" Insha'allah gobe da safe zan shiga naji kome kefa ruwa, yace toh" Allah yakaimu dai-dai lokacin da suka faracin abinci shi da Baffa wanda da'alama sun saba ci tare.
**********
Washegari asabar tunda karfe 7:00Am su *Sadeeya* ka shirya suka nufi dama haka sukeyi sai su dawo karfe 9:00Am, sannan su shiga part din da basu kwana ba su gaida su,
kasan cewar yau partdin Hajiya suka kwana don haka suna dawowa daga islamiyya suka nufi part din lnna, Bayan sun gaida lnna da Baffa da *Hafees* sai kawai suka shiga dakinsu suka haye gado sai bacci.
Da misalin karfe 11:00Am wata hadaddiyar mota naga tashiga harabar gidan, Bayan an kashe motar sannan aka fito wani dogon saurayi nagi kwankan tarwada kyakkyawa dashi dan kimanin shekara talatin da shidda zuwa da bakwai,
yana sanye da farin suit kallo daya zakai masa kagane cikakken dan boko ne da hutu dajin dadi sun ratsa jikinsa, kai! bari dai na tsaya kafin me karatu yakosa dason sanin kowane, toh" bakowa bane illah Dr *Harees* Al-mustafa๐ Cikin nutsuwa yake taku part dinsu Safeeya yanufa,
Da sallama yashiga Hajiya dake zaune a falon kasa ta amsa, tsugun'nawa yayi ciki girma ma waya gaida ita fuskarta sake ta'amsa tana tambayar su "Hajiya yace suna lafiya, can sai yace Hajiyarmu su Queen beauty na cikine..? tace "a ah suna part din lnnarsu iskesu can, yace toh" tareda yimata sallama yafita.
part din *Habeeb* yanufa kwance take shirif kamar kayan wanki kanta ba dankwali tana sanye da riga doguwa me hannun shimi wadda ta cika ta dam,
A gaskiya kibar ta yimata yawa sosai har yasa kar mata muni, *Jana* kenan ta *Habeeb* bada kanki asare kije gida ki ce ma *Habeeb* yafadi๐,
Sai faman sallama *Harees* yake tayi tanaji amma tayi shuru sai faman daddan na waya take, daya gaji kawai saya shiga kallonta yayi tareda kauda kai sai kuma yatabe baki yace haba *Jana* bakiji sallamar dana ke tayi bane..?
wani uban tsaki taja tareda watsa masa harara tace toh" idan naji saiya zama dole saina amsa..? yace "eh toh" a matsayin ki na musulma ya zama dole ki amsa, tace toh" ban amsa din ba, murmushi yayi tareda cewa toh" ba damuwa dama 'aiba wai kinsa ba amsawa bane,
au dama kasan da haka shine ka tsaya jiran saina amsa, yace kinga bashi nazo yi ba yanzu dai fadamun dan'uwana yana ciki...?
wani dariyar tayi me cike da reni wayo tace bansa niba kai kaji, wai dan'uwashi koma meye hadin kifi da kaska Oho! kaga mlm idan zaka jeka nemi dan'uwa kaje ka neme shi can, amma banan ba domin dai mijina ba dan'uwan ka bane ehee!,
yace Allah ko...? tace kwarai yace haka ne saidai kuma dadin abun koda akaga zabuwa dazanta akagan ta, ma'ana koda kika ganmu tareki ka gan'mu don haka kuma baki'isa Kira bamu ba kinji,
cikin masifa tace ban dai ga dama ba wlhy, yace aitunda baki ganta tun farko ba toh" ko yanzu bazaki taba ganin taba har'abada, dai-dai lokacin da *Habeeb* yabudo labule sanye yake da jallabiyya fara kallo daya zakai masa ka fahimci daga bacci yatashi, da'alama hayaniyar su ce ta ta dashi sannan ga duk kam alama ransa bace yake,
ido suka hada da *Harees* yasaki labulen yakoma ciki yayinda *Harees* yabi bayan *Habeeb* din yana zabgama *Jana* harara,
itama hararan tabi shi dashi har tana hadawa da cewa banza kawai maye๐.
Dan karamin falone me kyan gaske babu wani tarkace yana dauke ne daga t.v bago sai set din kushin, can gefe kuma tebur ne guda biyu kowa ne dauke da computer, sai agogon bango shikenan.
Zama sukayi suna fuskantar juna yayinda *Habeeb* ya watsama *Harees* wani irin kallo Cikin tsanani bacin ran yace"...?
*_Don Allah kuyi hakuri da rashin ganin posting din akan lokacin munyi buki yar'uwa ta ne._*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
2โฃ0โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Wai nayi maka katanga da gida na ne..? Murmushi *Harees* yayi tareda girgiza Kai alamar "a ah, *Habeeb* yace toh" meyasa kake mun haka ne eye...?
Dariya *Harees* yayi tareda cewa yi hakuri nabari, tsaki *Habeeb* yayi tareda cewa dalla mlm aiba ba tun yau kake fadin ka bari ba amma baka bari din ba, so ni nagaji da jin haka don haka saika cigaba da yi saidai bazan fasa gaya maka ba, tabbas kanada aiki idan har sai kajira *"Jana* ta amsa maka sallama sannan zaka ringa shigowa,
murmushi yayi yace insha'allahu daga yau nabari Cikin bacin ran yace "a ah kar kabari kaji, saidai fa kasani wlhy kwanan nan zanyi maku bura'uba daga Kai har "ita domin kuna shiga hakki na baiyuwa sai Ina Cikin bacci na ku dameni da shegen surutun iskanci, ya karashe fadi tareda jan tsaki,
shikam *Harees* dariya yake sosai yayinda *Habeeb* keta hararan shi yace "OK cigaba dayin dariya ka gani idan ban dauki mataki akan iskancin da kukeyi mun ba, kuma ka sani sarai zan'iya dauka KO..?
Cikin dariya *Harees* yace tabbas nasan zaka iya yanzu dai kayi hakuri nayi maka alkawarin, bazan sake biyewa *Jana* ba musamman a iri wannan lokacin dake baccin ka me cikeda daddadan mafarkinnn..
Da sauri
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 42