An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[7/2, 11:17 PM] My Ameena: 🎁🎁🎁🎁
🎁🎁🎁
🎁🎁
🎁
*_KYAUTAR ALLAH CE_* _(Labarin Sadeeya)_
🎁
🎁🎁
🎁🎁🎁
🎁🎁🎁🎁
1⃣
WRITTEN BY
🎁 *AMEENA UMAR FARUQ*🎁
OR
🎁 *MEENAT*🎁
DOMINKU
DOMIN
_*DUK WANI MARAYAN DA YARASA UWA DA UBA, INA ROKON ALLAH YAJIKAN IYAYANKU YA GAFARTA MASU, KU KUMA ALLAH YABAKU HAKURIN DA JURIYAR RASHIN SU YA KUMA INGANTA RAYUWAR KU, A DUK INDA KUKE A FADIN DUNIYAR NAN AMEEN 👏YA RABBI*._
SADAUKARWA
_LITTAFIN SADAUKARWA NE _GA_
_*MY HABITY MY SWEETHEART HALEEMATUS SADEEYA SADEEQ (UMMU HAIDAR), KISANI INAYINKI OVER TABBAS NASAN KAUNAR MU DAGA ALLAH NE NAGODE SOSAI DA KULAWAR KI AGARENI ALLAH YABAR KAUNA AMEEN.👏*_
_ALLAH INA ROKONKA YADDA NAFARA LAFIYA KABANI, IKON GAMAWA LAFIYA AMEEN_👏.
____________________
___
_*®PEN :WRITERS ASSOCIATION*_
______________________
_~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers.~_
✍🏽
_*Bismillahirrahamanirrahim.*_
_BAUCHI_
_NEW G R A_
Ranan jumma'a da misalin 5:30 PM
NEW G R A sabuwar unguwa ce datake dauke da Kayatattun ginin zamani masu asalin kyau da burgewa, acikin gidajan ne na hango wani Katafaran gida wanda duk acikin Unguwar ta new g r a, shine gidan da yafi kowani kyau da tsaruwa gaskiya gidan ya birgeni matuka musamman danaga fantin gidan kalata ne daukar hankali wato green and white.
Kawai jinayi Zuciyata tana son shiga gidan, Don haka sai kawai nanufi gidan domin naji ajikina kamar yadda gidan yake kayatattace, "toh tabbas za'a samu kayatattace Labarin acikin sa mai nishadartar wa tareda fadakarwa, don haka mai karatu idan kanason jin👂Labari "toh biyoni muje🏃♀.
Saidai kuma koda na'isa bakin get din duk arufe kofofin suke daga karamar kofar har babban,😩"Oh! nita RASULU "toh🤔 yanzu ya zanyi na shiga?...
Shuru nayi Ina tunanin ta yadda zanyi nashiga wannan gida me matukar kyau da burgewa, saidai kuma bansan yadda zanyi ba don haka sai kawai nakoma gefe na raku'be🙇♀.
Chan saina ga wasu motoci masu asalin kyau guda biyar sun jero da gudu, mota uku ba komai jikinsu sabani mota biyu da aka manna masu foster wani kyakkyawan mutun fari Wanda naga an rubuta sunan sa kamar haka, *HON HABIBULLAH HASHIM SORO*
*(BB SMART)*
A matsayin dan takarar Senetar,
ga mamakina gidan naga motocin sun nufa dagudu .
Dasauri nasake makurewa don kar wani yagan'ni,
horn daya sukayi maigadin yabude masu kofa da sauri suka shiga daya bayan daya, ganin maigadin yana kokarin rufe kofa nayi saurin afkawa "KO antayawa nema ake cewa Oho! 😂 nidai nashige lol😜.
Masha'allah shi kam Mrs bature saboda tabar salo sai yace Wowww!😉 gaskiya duk yadda nadauki gidan yawuce haka, mai karatu gidan kam yahadu karshen haduwa musamman flowers din dasuka kawata gidan ta'ko'ina, masu kyau wanda kamshisu kawai yanasa zuciyar mutun tasamu nutsuwa. Part Uku nagani sai masallaci part biyu iri daya wanda ginin bene ne mai matukar kyau da tsari, shi kuma dayan ba ginin bene ba ne sannan baikai biyun girma ba, saidai daga tsarin ginin wanda inka cire bene "toh komai iri daya ne harda fanti.
Motar farko naga direba da sauri yafito ya bude gidan baya ahankali naga an zuro santala-santalan kafafu kasa masu sanye Da bakin takalmi, sai shainin sukeyi Cikin nutsuwa yafito kunnan sa manne da waya yajuya baya don haka banga fuskarsa ba, saidai shidin farine wanda nagane hakan ne ta hannunsa dayake daure da tsadadden agogo, kuma dashi ne yake rikeda waya.
Dogone shi sosai dan har ya rankwafa kad'an kuma yanada faffadan kafad'u wanda yai matukar karafito da cikar zatinsa, sosai saidai bayada kiba kasan cewar kirarsa irinta zakine domin cikinsa ashafe yake tamkar baya cin abinci, shekarunsa zasu kai 36 zuwa 37.
Sanye yakeda wani irin bakin yadi mai kyau wanda kallo daya zakai masa kagane tsadadde ne, kansa ba hula saida tarin suma baka kirin acukur kude tamkar ta jariri sai walkiya takeyi domin dai kam tasha gyara, ahankali yajuyo da kyakkyawar fuskarsa mai daukeda lallausan murmushi dai-dai lokacin da sauran mutanan suka fito daga cikin motocin daya bayan daya.
Tubarakalla shine abunda nafadi domin tuni nagane shine mutumin dake jikin foster nan masha'allah, gaskiya afili yafi kyau, tabbas shidin kam kyakkyawa irin ajin farko nan fuskarsa dauke takeda dogon hanci, da idanu masu kyau gawani kyakkyawan sajen da yabari wanda yakarawa fuskarsa kyau da kwarjini kallo daya zakai masa kagane hutu dajin dadi sun zauna ajikinsa. Saida yaga fitowarsu duk sanna yajuya Cikin takun isa da kasaita yanufi daya daga Cikin part, din still wayar tana manne akunnan sa yayinda sauran mutanan suka rufa masa baya.
Dasauri nabi bayansu saidai kafin duk Na karasa har an rufo kofar, tsaye nayi sun sauki tsawon wani lokaci sannan suka fito motocin nan biyu masu fosta naga sun shiga sun tafi, sannan shi kuma yakoma ciki tareda sake rufo kofar dan haka dole najuyo nanufi karamin part din domin shi abude yake.
Sautin karatun al'qur'ani ne ketashi cikin wani dan madaidaicin falo me kyau da tsari, wani farin kyakkyawan Dattijo
nagani zaune akan dadduma zubinsa irin Na fulanin asali, tsoho neshi sosai sanye yake da fararan kaya da hula fara, tareda karamin rawani idonsa manne da farin glass, wanda ga dukka alama medicated glass ne, hannunsa rikeda alqur'ani mai girma irin mai falle-fallan nan wanda ake kirada warash, ga bansa kuma wata yarinya ce zaune itama rikeda alqur'ani saidai nata Qurani hafse ne, kanta duk'e tana sanye da abaya baka sai tayi rolling da d'an kwalin abayar fara ce yar kimani shekara goma sha biyar zuwa sha shidda.
Ahankali Dattijon ke karantawa ita kuma tana amsawa cikin siririyar murya mai dadin gaske, Chan gefe kuma wata kyakkyawar Dattijiya ce zaune akan kushin tana sauraren su tana sanye da atamfa ja da ratsin yalo, kallo daya zakayi mata kane bafullata ce, ahankali suketa karatun sun dauki tsawon lokaci hardai suka Kai karshen suratul ankaboot sannan yayi masu addu'a, suka shafa tareda rufe al'qur'anin alokacin daya, ahankali tadago Kai suka hada ido sukayi murmushi yace inafata kin karanta suratul khafi?.. tace eh na karanta yace to masha'allah.
Nikam Kallon daya nayi mata nagane cewa wannan Dattijo da Dattijiyar nan mahaifanta ne saboda Kamar dasukai da'ita,
Masha'allah tabbas itadin kyakkyawa ce sosai tamkar Yar larabawa tanada manyan idanu amma ba sosai ba, suna dauke da zara-zaran eyelash tareda gashin gira wanda yakusan hadewa, sannan yanayin idanunta kamar ta najin barci, tana da dogon hanci da dan karamin baki pink colon wanda naga tana tsotson sa tamkar tana tsotson sweet Kai! gaskiya yarinyar tanada matukar kyau nadaukar hankali.
Cikin sanyin murya tace Baffana zanje naba, my sweet *FEEYA* magani dan nasan yanzu haka bata sha na yamma ba.
Kayatattace murmushi yayi tareda cewa "toh aidake da yar'uwan naki halinku daya bakuson shan magani, sannan idan baku kukaba junanku ba duk wanda zaya baku bazaku shaba, saiko Hamman ku idan yaimaku Jan ido sannan kusha, baki ta turo cike da shagwaba tace Baffa shifa *Hamman Habeeb* zalu yakeyiwa mutun murmushi yayi yace kodai menene shine dai maganin ku,
dan haka ta shikije kibata" maganin tasha Ina gaida ita da"Hajiyar taku yauma ban samu shiga mun gaisa ba, tace "toh sannan tamike ahankali tanufi wani table mai daukeda littafai ta'ajine al'qur'ani, nan naga kirar jikinta mai kyau da daukar hankali musamman kirjinta dayake cike da dukiyar Fulani, kasan cewar abayar mai shap ce wanda tayi dai-dai da yanayin jikinta dan haka saiyai mata kyau sosai, juyawa tayi ta kalli yar dattijiyar matar nan tace Innata zantafi tace "toh ki gaida *SAFEEYA* din tareda Hajiya tace "toh tareda fita daga part din.
Dayan part din tanufa ba wanda mutanan suka shiga ba, cikin nutsuwa take tafiya tamkar bataso taka kasa yayinda jikinta ke kadawa tamkar bishiya, Cikin wata murya mai sanyi naji ance.. ke! ahankali najuya don naga wanene mai wannan zazzakar murya mai dadi, kyakkyawa mutumin nan nagani sanye da brown din jallabiya da alama yayi wanka ne yacanja kaya, saidai wannan Karon fuskarsa daure take sabanin dazu dayaketa sakin kyakkyawan murmushi, cikin dakewa yasake cewa..
Ke! *KYAUTA* fa wai ko an *DUBU* bataji ne?.. tabbas wannan yar kyakkyawar budurwar yake kira saidai kuma ga mamaki na ko juyowa batayi ba balle ta amsa kiran asalima tafiyar ta kawai takeyi Cikin wani irin taku mai ban sha'awa wanda idan kagani saika rantse yanga takeyi, saidai kuma ga dukkansu alama ba yaga bane yanayin tafiyar ta kenan.
Cikin bacin rai tareda daga murya yace Ke! *SADEEYA* ahankali tajuyo cikin sanyi murya tace Na'am tareda taduk'ar da kai kasa domin jitayi kirjinta yana halbawa, dai-dai lokacin da yakarasa gurinta daddad'an kamshin turaran sa yadaki hancinsa, haka nan shima kamshin turaran tane yadaki hancin saidai shi dasauri ya kauda kai gefe ko mene dalilin sa nayin haka Oho!.
Ba tareda ya kalleta ba Cikin bacin rai yace ke! wani irin iskanci ne haka Ina kiran ki shine zakiyi banza dani?.. baya taja kadan kilan tana tsoron karya sanbada mata Mari ne😂, ahankali tadaga Kai ta kallesa still kirjinta yana cigaba da bugawa, fuskata yamutsa sannan tace "toh aini banji kaba ne, (kut😳 wai bataji shiba? lallai wannan taci abinci 😂to aikoni naji😜) shikam dasauri ya kalleta fuskarshi daukeda matsanancin mamaki yace...
_*Comments dinku shi zaya bani Kwarin guiwan sambad'o maku Labarin*_
👇
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
(Labarin Sadeeya)
_Wanda zayazo ta_
_Alkalami_
✍🏽
🌹Lufhat🌹
_Insha'allah_
[7/2, 11:17 PM] My Ameena: 🎁🎁🎁🎁
🎁🎁🎁
🎁🎁
🎁
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
🎁
🎁🎁
🎁🎁🎁
🎁🎁🎁🎁
2⃣
WRITTEN
By
🎁 *AMEENA UMAR FARUQ*🎁
OR
🎁 *MEENAT* 🎁
SADAUKARWA _*ga Sadeeya Sadeeq Ummu (Haidar)*_
___________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
✍🏽
Ke! kina nufin duk ihun kiran sunanki danayi bakiji ba?..cikin yatsina fuska tace ah! *yah Habeeb* da farko baka fa kira sunana ba, cewa kayi ke! sannan kace *KYAUTA* koda yake "eh nidin *KYAUTAR ALLAH CE* dayaba "Innata da "Baffana, don haka suka d'ai nakeso sukirani da *KYAUTA,* ita kuma Hajiyar mu ai *HALI DUBU* wan kyawo take kirana, amma kai kuma sai kace wai ke! an *DUBU*, kuma kasan cewa *HALEEMATU SADEEYA* "Abba yasamun idan kaga sunan yaimaka tsawon fadine basai kace *HALEEMA* ba ko *SADEEYA* amma sai kai takir...
Uban tsawa da yadoka mata ne yasa tashi shuru, cikin bacin rai yace Ke! nikike fadawa wannan dogon sharhin?.. "Ok wato kece ma zaki fadamun yadda zankira ki KO?... "toh idan bankiraki da yadda kike soba me zakiyi eye?..yafadi yana matsawa kusa da'ita,yayinda itakuma cikin tsoro takeja da baya, dakarfi yasake cewa nace me zakiyi?..dasauri tajuya da gudu tanufi part din.
Cikin takun kasaita mai dauka da sauri yabi bayanta yana cewa kai! kaga mun maras kunyar yarinya, daki tsaya kigani idan ban ballaki agurin nan ba wato dan kunga kwana biyu na kyaleku shine zakuyi mun iskanci ko?.."toh wlhy kwanan nan zan gyara maku zama.
Dai-dai lokacin da yashiga katafaran falon dayaji kayan more rayuwa wata kyakkyawan mace ne zaune saman kushin, sanye take da wani ratsattsen less mai ruwan brown da ratsin ruwan hoda, tasa hijab shima mai ruwan hoda hannun ta rikeda casbi tana ja kallo daya zakai mata kagane cewa mahaifiyar sace saboda kamar dasu kai.
Kyakkyawar yarinyar nan ce nagani sai boyewa take abayan wannan matar, ahankali matar tace a ah! Hali dubu na meya faru?.. sake kwakumeta tayi tareda tadora kanta akafadar matar (ga dukkan alama dama tasaba yin hakan) cikin shagwaba tace Hajiyar mu ba *Hamman Habeeb* bane ya biyoni zaya dakeni, dasauri tace daki kai masa me?.. bakita turo tareda cewa ban masa komai bafa, dai-dai lokacin da ya zauna yana zuba mana harara.
Kallon shi hajiyar tayi cikin hade fuskata tace waikai meke damunka ne?..rai bace yace Hajiyarmu meke damuna kodai meke damun wayan nan marasa kunyan yaran naki, tace "toh nidai ban haifi marasa kunya ba kuma ban koyamasu rashin kunya ba balle suyi maka, sannan akan wani dalili ne zaka biyo mun yarinya ka doka, waima bana hanaka doke-doken nan ba?.. shin Kai bakaga yarana sun girma ba ne umh?.. "toh don Allah kara basu da doke-doken nan haka.
Dasauri yace "toh don sun girma shine zasu ringa yiwa mutane rashin kunya kiranta fa nake zan tambaye ta kokin dawo, amma saboda tsabar iskanci tanaji shine tayimun banza, amma dayake batada kunya shine ta tsaya yimun wani dogo sharhi saboda tarenani. Hajiya tace a ah Hali dubu na ya haka kuma meyasa kinajinsa yana kiran ki kikai banza dashi?..baki ta turo tareda cewa Hajiyarmu baifa Kira sunana ba sai cewa yake ke! ke! an dubu, kuma gaskiya Hajiyarmu ni banason yana kirana an dubu, dasauri yace ance an dubu din kiyi abinda zakiyi yakarashe fadi tareda zabga mata harara.
Cikin shagwaba tace Hajiyarmu kingansa KO?..murmushi tayi sannan tace "toh yanzu dai ya isa haka tunda dai kun maidani alkaliyar Ku kullum nike nan cikin yimaku Shari'a, kuma Kaine mesani yinta tunda nasha fada maka kadaina kiranta da sunayen da bata so, da sauri yace toh" aida sunanta na kirata, tace a ah inda kakirata da sunanta aiba zata kyale kaba, yace harda *SADEEYA* ba sunanta bane?.. Murmushi tayi tace aikafi kowa sanin cewa sunanta kenan saboda haka kaci gabada kiranta da sunan ta, sannan kuma neman me kakeyi mun?..
gurin da *SADEEYA* take ya kalla tana nan labe abayan Hajiyar, tana kallonsa. harara ya watsa mata tareda kauda kai gefe yace "toh Malama aisai kizo kifita kiba mutane guri "KO...baki ta turo tareda mikewa tace Hajiyarmu su" Innata Na gaida ke, murmushi tayi tace "toh Ina amsawa kije *Safeeya* nacan tana jiranki kiba ta magani tace "toh.
Cikin sanyi jiki tafara tafiya kallonta yayi dai-dai lokacin da take watsa masa harara harda murguda baki😏, da karfi yace ke!. ni tsaranki ne?.. aikam da gudu tanufi sama cikin kwarewa take taka step din,
wani katafaran falo tafad'a shima dauke yake da kayan more rayuwa kamar wannan Na kasan, da gudu tashi gawani daki ta turo kofar tareda saka makargami, sannan tajingina bayan ta ajikin kofar tana sauke numfashi saikace tayi gudun kilominta dubu lol.
wata kyakkyawar yarinya ce kwance saman faffadan gado ta kudindi ne da wani lallausan bargo, ahankali tadago Kai cikin sanyi murya irin tamarasa lafiya
tace my sweet *DEEYA* meya faru wanene ya biyo munke?..dariyar tayi sannan tace tsokana nayo, itama dariyar tayi tareda cewa aikin saba "toh yau kuma wakika tsokano? cikin takunta mai daukar hankali tanufi gurinta tana warware rolling din gyalen dake kanta, aikam take lallausan kashin kanta mai santsi da tsawo ya baiyana wanda yasauka har gadon bayanta, cikin cool voice dinta tace hmm! kedai bari yau malam zalimun na tsokano, dasauri tace _what_ *Hamman Habeeb* fa?..
tace "eh dai-dai lokacin da ta zauna bakin gadon tadauki hannun *Safeeya* tadora asaitin kirjinta, tana cewa my sweet *Feeya* taba kirjina kiji kamar zaifad'o saboda tsabar bugawa, tace hmm! nima aihar kinsa naji kirjina yabuga, "toh waima meyasa kika tsokane shi?.. nan tafada mata abinda duk yafaru murmushi tayi tace hahaha yarinya sunan ki Sorry wato ma harda murguda masa baki tab! ai, idan yaka maki zakiyi bayani sala-sala, murmushi tayi batare da tace komai ba saidai tamike tana kokarin cire riga.
Shi kam *Habeeb* kallon sa ya mayar kan Hajiyar wadda itama shi take kallo, yace Hajiyarmu kina ganin yarinyar nan fa harara ta tayi harda murguda mun baki saboda tarenani KO?.., tace "toh yi hakuri, yace haba ai idan na kamata tabbas sai bakinta yayi jini. da sauri tace "toh kar kafara shi wlhy, nikam narasa yadda akai kazamo mutun mara hakuri abu kad'an saika kama fada.
wai tsaya tukun kai ba kasan Kai babban mutun bane?..yaranka fa biyu sannan gawani girma yana kokarin sake hawa kanka ko ka manta ne ummh?.. baice komai ba saidai ya tsura mata kyakkyawan idanunsa cikin sanyi murya me cike da tausayi kansa yace, Hajiyarmu shikenan nikuma dan Na kasan ce babba sai aita yimun abubuwa kala-kala anaba tamun rai idan nai magana kuma ace nayi hakuri, wato shikenan nikuma rayuwa ta acikin hakuri zata dauwa ma kenan ko?..
Murmushi Hajiya tayi sannan tace tunda kashigo na fuskanci cewa "matar ka tabata maka rai shine zaka huce akan yarinya ta, wanda kasan cewa bazan taba lamunta da hakan bako?..wani irin kallo yake binta da shi mecike da mamaki, cikin sanyi murya yace Hajiyarmu ya'akai kika fahimci haka?..murmushi tayi sannan tace saboda nice na haifeka kaga duk wanda zayasan halinka a bayana yake, shi kuma hakuri dakace aiko ka dauwama akansa ba wani Abu bane domin shi mahakurci ma wadaci, bakaji masu karin magana sunce mai hakuri yakan dafa dutse har yasha roman saba?..Don haka nakeso ka dauwama akansa saboda inada tabbacin zuwa gaba zaka dafa dutsen nan har kasha romon sa.
Ido ya rintse sannan yabude aikam tuni sun canja Kala daga Fari zuwa jajajir, cikin sanyi murya yace shikenan Hajiyarmu zanci gaba da kasan ce yadda kike so, saidai kuma kina ganin idan na cigaba da hakuri da abinda *JANA"* takeyi mun bazaya zamo *ILLA* arayuwa ta ba?.. Kallon tausayi tayi masa tareda girgiza kai alamar a ah sannan cikin sanyi murya tace meya faru kuma?..
Cikin bacin rai yace Hajiyarmu nikam nagaji da abinda *Jana* takeyi mun, tace me tayi maka?.. yace yanzu kiduba fa kigani tun safe mukabar gidan nan kuma wlhy Hajiyarmu ruwan _coffee_ ne kawai acikina wanda nayi-nayi Da *Jana* ta tashi hadamun amma takiya, dole natashi na hadawa kaina nasha yayinda ita kuma take nan kwance ta wannan matsiyacin barcin nata na hasara, sannan kuma still yanzu ma nadawo na'iske tana barci batare da tayi girkin rana ba saidai tasa mai aiki tayi saboda tsabar iskanci da walakancin kuma tasani sarai bana cin abinci mai aiki,
tace "toh bana ce idan batayi ba kazo nan kaci?.. yace haba Hajiyarmu yaza ai inada mata kamar *Jana* amma ace sainazo nan na cin abinci gaskiya wannan bayi bane, nidai na fahmici *Jana* so kawai take taka sheni.
Cikin sanyin murya tace ai ba wanda ya'isa yakashe wani idan ba ALLAH ba, yace "toh kiduba fa kigani saboda tsabar zama dana keyi da yinwa ulcer takamani, shin Hajiyarmu wannan wacce irin rayuwa ce haka?...ajiyar zuciya tayi sannan tace..
Muje zuwa
A
*_KYAUTA ALLAH CE_*(Labarin Sadeeya)
Tareda Alkalamin
✍🏽
🌹Lufhat ce🌹
Amma Fa
_*Adadin Comments adadin typing*_ 😜
[7/2, 11:18 PM] My Ameena: 🎁🎁🎁🎁
🎁🎁🎁
🎁🎁
🎁
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
🎁
🎁🎁
🎁🎁🎁
🎁🎁🎁🎁
4⃣
WRITTEN
By
🎁 *AMEENA UMAR FARUQ*🎁
OR
🎁 *MEENAT* 🎁
SADAUKARWA
*ga SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
✍🏽
Au me?..tace aure, yace haba Hajiyarmu wani irin aure kuma?..cike da mamakin gani yanayin dayashi ga, tace ah! wai dama akwai wani aure ne bayan wanda "Manzon Allah (S A W) ya umarce mu da muyi?..
yace a ah babu, tace "auto nadauka "KO akwai ne?..yace Hajiyarmu babu tace "toh shine kace mani wani irin aure?.. sannan kuma dagayin maganar auren naga yanayin ka yachanja, kamar nayi maka wata mugunwar magana,
yace Hajiyarmu ba haka bane ke bazaki gane bane shiyasa, tace "toh yane inasan nagane ?..yace gani nayi wannan aurenma yana karedashi balle kuma na karayin wani, murmushi tayi tace "toh waini aganina idan ka karayin auren zakaji saukin abubuwan da *"Jana* takeyi maka kilama, sanadiyar auren ta chanja hali gaba daya tadaina yi maka abinda takeyi.
Yace hmm! Hajiyarmu wani chanji za'asamu agurin *"Jana* wanda yau tsawon shekara biyar kenan dayin aurenmu amma bata chanja ba sai yanzu?..hmm! chanjin nan dai agurin *Jana* lallai dakamar wuya wai gurguwa da aure nesa, don haka nidai kidaina maganar Kara aure nan, mutun baiji dadin aure ba ina zaya kara yinwani,
mikewa tayi tareda cewa haka ne "toh ai shikenan tunda bazaka karaba, da sauri yace Hajiyarmu Allah yasa ban bata maki rai ba?..murmushi tayi tareda cewa a ah dama dai inagani kamar kara auren shine mafita agareka, gameda abinda matarka takeyi maka "toh saidai kuma tunda baka ra'ayi ai shikenan.
Cikin sanyi murya yace Hajiyarmu ni wlhy gani nake kowace mace halinta irin na *"Jana* ne shiyasa kikaga bana ra'ayin kara aure, domin gaba daya mata basa burgeni, kai ta girgiza tareda cewa "toh ai ba dukka akataru akazama daya ba, yace haka ne "toh nidai Hajiyarmu kiyi mun addu'a kinji?.., tace kullum cikinta nake, bari nashiga ciki yace "toh tanufi sama yayinda yabi bayanta da kallo.
🎁🌹🎁
Su *Sadeeya* kam saida sukaci dariyar su suka koshi, Bayan *Sadeeya* ta fadawa *Safeeya* abin tacewa *Hamman Habeeb* sannan tashiga toilet dan tayi wanka, wanda tadauki tsawon wani lokaci sannan tafito daureda tawul akirjinta.
ahankali ta kalli inda *Safeeya* take kwance barcin takeyi sosai abinta, yayinda take ta sharban gumi alamar sauki na shigarta kenan, murmushi tayi tareda karasawa gurinta hannu tasa tashare mata gumin daya tsatsufo mata agoshi, cikin sanyi murya tace Allah yabaki lafiya my sweet *Feeya* sannan ta gyara mata bargon,
sannan tanufi gurin mirror zama tayi akan Wata Yar karamar kujera cikin nutsuwa tafara shafe-shafe, wanda shima saida taduki tsawon lokaci sannan tagama.
ta tashi tanufi wedrobe tabude, wata jar riga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 42