ita ma Nasrim tunda tayi wayo take son sa, amma ba ta son ko da ganin Nasir tana ganin sa za ta sa kuka kaman za ta shide yau ba Harira ta barta a main parlour ta tafi hado mata madaran ta, ta rarrafa ta fito compound shi kuma Nasir yana zaune ya juya bayansa da litafi a hannunsa dan karatu yake tuk'uru sun kusa zana jarabawan fita daga primary ya ji an rike masa k'afa yana juyowa yayi arba da ita bai gane taba dayake baya tsayawa ya kalli fuskanta sosai murmushi yasakar mata ita ko tana d'agawa ta kalleshi ai k'o ta fashe da wani irin kuka da sauri yasa hannu ya dauketa yana cewa am sorry beautiful baby girl". yana kallon ta yana shafa kwantaccen suman kanta yana murmushi ya sake cewa komai naki me kyau ne baby".
ita ko sai wani irin kuka take tana neman sauk'a ajikin sa,
Agrif da yake baya shima yana nasa karatun ya ji kukan Nasrim yayi yawa ya juya da niyar ya shiga parlour ya ganta a hannan wanda bai taba zato ba
Nasir yace ''Agrif kaga wata beautiful baby girls gashinta mai kyau komai nata me kyau dan Allah yar wacece mommy tayi bak'uwa ne"?
Wani irin dariya Agrif yasa yana tafa hannu ya ce "Ashe ka san mai kyau ce ashe za ka dauke ta, ba kai ka ce ko hanyar da ta bi ka gani ba zaka sake bi ba? Ashe duk k'arya ne''.
Ya k'arashe maganan yana cigaba da dariya, sai alokacin Nasir ya tuno da wacece a hankali ya sake ta ta yi kasa da sauri Agrif ya yi niyar ɗaukota amma ina! Har ta yi k'asa tif kafin Agrif ya sunkuya ya d'agota har Nasir ya sa kafarsa ya take yatsunta biyu yana wani irin murzawa da takalminsa sawun ciki Agrif yayi-yayi ya d'aga kafar ya kasa ga Nasrim kukan ma ta daina tsabar azaba sai wani irin d'aga ido sama take kamar za ta sume, shiko Nasir sai da yaji k'aran k'ashin alaman yatsun sun karye ya d'aga k'afar a lokacin Harira ta fito wani irin kuka Harira tasa tayi kan Nasrim ta d'agota har tasuma shiko Agrif neman abin da zai bugawa Nasir ya illata shi kawai yake nema jiyake ko bindiga ya samu zai iya harbin sa wani gilas da a kacire a window Hajja ya hango zaran gilas din yayi da wani irin gudu yayi kan Nasir da yajuya baya yana ta fitar da numfashi Baba Yakubu da sauran masu aiki da gudu sukayi kansu amma kafin su k'araso Agrif yasamu nasaran bugawa Nasir a kai
sai de Allah bai sa yai Koda k'ozani ba dan gilas din ba me saurin bashewa bane saide yadanji ciwo juyowa yayi yana kallon Agrif din yace"ni ka bugawa wannan dan wannan banzar ko".
"Eh na buga kuma Wllh bai isaba sai na sake rama mata kuma Nasrim ba banza bace gaka babban banza". yasake yin kansa za k'arfi yanda idan ya buga masa ko bai faahe ba zai illata shi dak'er aka shiga tsakanin su
shiko Nasir ji yayi ya dake tsanan Nasrim dan ba a taba zagin sa haka ba sai yau a kanta har buga masa gilas din ma bai masa zafima irin zagin da Agrif din yake masa yafi masa ciwo da sauri ya sake zaran Nasrim ahannu Harira zai bugata daidai lokacin motar daddy tayi parking daddy bai jira an bude ba yayi sauri ya fito da sauri yayi saurin k'arasawa inda suke Kabiru yana kokarin karban Nasrim a hannun Nasir amma ya hana wani irin mari daddy ya dauke shi dashi zai sake k'aramasa yaji an rike hannu sa yana juyowa yaga Hajja ce cikin b'acin rai,
Ta ce'' Abdulmajid kashe min shi za ka yi a kan wannan yar taka wadda dalilinta na rasa ubansa, tun daga yanzu Nasir zai fara fuskantan maraici akan y'arka za ka dake sa? Yaushe Abdulsamad ya mutu da har za ka fara manta shi waye ka rufe ido har kana dukar masa tilon jininsa ".?
Ta k'arashe maganan tana sakin kuka
Daddy ma cikin b'acin rai Hajja ba ta taɓa ganin sa da shi ba ya ce
"Haba! Hajja ba ki ga laifin da yayi ba inda ya jefar ta fa?"
Kafin Hajja ta yi magana Nasir ya ce
" Dan bani da ABBA ba me rama ni shi ne za ka dake ni akan y'arka kuma wllh sai na rama a kanta kashe ta zan yi wllh sai na kashe ta".?
Hajja ta ce "A'a daina wannan FURUCIN, zo mu je na duba ko ka ji ciwo Allah zai saka maka, ai maraici ba siya ka yi ba marici yana kan d'an kowa maraici ba hauka ba ne soyyayata kaɗai ta ishe ka, ni ina son ka kai da ya Abdulsamad ya bar min, kai nake gani a madadinsa ba zan yarda a cutar min kai ba a kan wata banza ba".
Ta idasa maganar haɗe da jan shi suka yi gaba.
Mommy da take tsaye ranta idan ya yi dubu ya ɓaci cikin b'acin rai ta ce
" Yanzu Alk'ali abin har ya kai haka har ta kai ka d'aga hannun ka daura akan Nasir da sunan duka kuma a gaban maaikatansa za ka k'ask'antamin shi ?".
shi ma Abba cikin nasa b'acin ran ya ce "Na daka Dr Fanna ko kin fini iko a kansa ne kina ganin kamar kin fi kowa iko a kansa ko, Dr Fanna na fa gaji da irin wannan halin! Ke wacce irin uwa ce? Idan Nasir amana Halima da Abdulsamad suka bar miki ita Nasrim amana ce kai tsaye daga wajen Allah kina shi Ya ba ki kuma amana Ya ba ki kika rik'e amanan wani bawa amma kin banzatar da amanan Allah Sam.... ".
Dakatar da shi mommy ta yi da cewa "ka gaji da irin wannan halin nawa kace ko ? Na ji ka gaji za ka iya daukar matakin da ka ga za ka iya amma inde akan Nasir ne Wllh baka isa ka ce min ba ni da iko a kansa ba ko ka fi ni iko da shi ba".
har zayyi magana yaga yanda yatsan Nasrim ya kunbura sai yanzu yakula da ashe daya yasan ma rawa yake alaman ya karye cikin wani irin razana yace "Dr Fanna ya karyata fa".
"E, na gani ya karyata naka ka sani ai, yanzu ka san halin da shi Nasir yake ciki".
Cikin sanyin murya daddy ya ce "Dr ki zo mu je a kai ta asbiti ba lokacin wannan maganan ki duba halin da y'ar nan take ciki."
Ya k'arashe maganan yana karban Nasrim a hannun Harira
"kai me zai hana ka kaita".
tana gama fadan haka tayi part din Hajja
wani irin hawaye ne ya surtowa daddy yana na kallon Nasrim da sai yanzu ya gane a sume take ga yatsa yana rawa. Ya rasa ma ya zai yi Habu drive ya ce "Alhaji mu je asbitin" Shiga yayi motar kafin driver ya ja yana cewa Baba Yakubu dan Allah
"Yakubu ka cewa Aisha ta same ni a asbiti yanzu".
********
Mommy tana cikin lallashi ta ce'' my Son ka ji mata ciwo fa sosai amma na san Abu ma sai ya yi maka fad'an dan haka idan ya tambaye ka ka ce kai ba ka sani ba ka taka kar kace wa Abunku da gan-gan ka karya ta ka ji".
cikin dafe kansa da yake jin yana masa ciwon ya ce
"No Mom ba zanyi k'arya ba ina sane na taka ta ai dama na ce kar na sake ganin ta kuma dan raini har fa kamani tayi wllh na zaci watace har daukan ta fa na yi Allah ba zanyi k'arya ba da gangan na taka ta shi ma Abun haka zan ce masa".
Mommy tace'' wannan ba k'arya bane kare kai ne nasan Abu zai maka fada ko ya dake ka kamar yanda daddy ya yi".
Cikin kawar da maganan yace mommy kaina ciwo yake min Agrif ya buga min glass Dad ya mare ni''.
"Ok sorry my son mu je hospital ko".
ya ce "Na mommy ba sai mun je ba ki ban magani kawai".
Mommy tace''ok ka sha sai ka kwanta ni kuma zanje na dubo Nasrim an tafi da ita asbiti"?
turo baki yayi yace " wllh mommy ba za ki ba ai a kanta aka dake ni".
" OK my Son ba za ni ba".
Hajja da take sauk'owa daga steps ta tabe baki tace'' au dan ita yar gata ce har asbiti aka kaita daga dan takawar ummmm gata ni Lami yar Habubakar amana yayi k'aranci har agabana Abdulmajid zai nuna bambanci ga d'an Abdulsamad dan Adam kenan mai manta alkairi".
Ummu da take kallon karfin halin su ta kasa jurewa ta ce
"Haba Hajja! ina Nasir ina Nasrim ai ba sa'annin juna ba ne kuma abinda ya yi ai....
Hajja ta ce
"Dakata Amina ni bana ciki da rashin gaskiya ai shi maraya ne ko ma me yayi ai a masa kara ko dan darajan ubansa" .
daga nan Hajja ta kama fada har da gayawa Ummu magana son ranta.
********
Agrif da Mama da Kamal ne suka tafi asbitin lokacin har an shiga da ita za a mata aiki daddy suka samu a zaune yayi tagumi Mama ce tace'' Alhaji kayi hakuri insha Allah zata..
bata k'arasa ba Dr yafito da saurin sa yace '' ranka yadade kayi sauri ka saka mana hannu za ayanke mata daya yatsar duk biyun kayara ne amma daya zai gyaru daya ba zai gyaru ba dole sai dai mu cire mata dan k'ashin ya riga yayi daga-daga".
wani irin kuka Agrif da kamal suka sa haka Mama ma shima daddy cikin hawaye yace "A'a ina da d'an uwa da mahaifiya bari na gaya musu kafin nasa hannu na ji ta bakinsu. Hajja ya fara kira yana gaya mata ta sa kuka ta ce
" Abdulmajid abin har ya kai haka wllh ban yarda a ciremin yatsar jika ba gani nan zuwa".
shide katse K'iran yayi yana kiran
Alhaji Abdulraham shima Abu ya ce"subbahanalla gani nan zuwa ina cikin makaranta".
yana kashe wayan ya dafa kai ahankali yake fitar da numfashi
Dr ya ce "sir please aikin yana buk'ara gaggawa bawani abu bane ake cire hannu ma gaba daya balle dan
Fingers".?
Takardar daddy ya karba yasa hannu
Mama tace'' Doctor please bawani hanya da za a bi dan Allah ko da waje ne a fitar da ita ba mason a yanke mata yatsa".
Dr yace "Madam nasan kunfi karfin hakan to wannan k'addara ce bayan da za a yi yatsar ya koma jikinta ya riga ya bar jikinta fatar kawai za mu cire shi yatsar ya riga ya fita ma".
Kuka sosai Agrif da kamal suke yi
Abu ne ya fara zuwa amma lokacin ma har an fito da ita har ankaita d'aki Mama tana zaune a bakin godon daddy kuma akan kujeya ya sa dan yatsar da aka mek'a masa acikin wani kwali gaba Kamal da Agrif har yanzu kuka suke Abu yace "wai me ya faru ne?"
Daddy bai yi magana ba Kamal ne ya bashi labarin komai ajiyar zuciya ya sauk'e ya ce
"Kayi hakuri alk'ali Allah ya k'addara hakan zai faru da ita shikuma Nasir insha Allah suna gama jarrabawar ba za su jona na secondary a nan ba nan da wata 3 za su tafi America kafin su gama ya yi hankali dan a nan Dr Fanna da Hajja su suke biye shi.
********
Sai da Nasrim tayi kwana biyu a asbiti aka sallame su Hajja da Mama sune a kanta ta amma mommy bata ko lek'o ba dan ita a ganinta ita aka yiwa babban lefi an yake mata yatsan y'a bata reda neman izinin ta ba tafake da wannan amma azashiri Nasir ne ya hanata zuwa
dak'er Hajja ta tarasu ta basu hakuri duka. Amma tun daga wannan lokacin Nasrim ba ta sake komawa wajen mommyn ba shi ne dalilin yaye ta
bayan wata 5 tafiyar su Agrif saura sati
yau ne aka gama tattare duk wani dukiyar na Alhaji Abdulsamad akasan yawansa yasa yayiwa daddy yawa dole aka yayyato wasu alk'alai kuma duk wannan shekarun anyisane cikin tattare dukiyar alk'alan su zaga dukkan k'asashen da marigayin yake da company ko dukiyar bayan cire tumilain mommy da hakki mahaifiya Hajja aka rabawa yaran sa guda ahudu wato Nasir da jariran mommy wanda daga baya aka hadewa mommy na yaranta.
Tabdijam ! mommy ta tashi da kaso 80 cikin dari na dukiyar daga baya tace" ita a haɗe nata da na Nasir ba abin da za tayi da wannan dukiyar itama Hajja a take ta raba nata gida biyar ta bawa danginta da na mijinta kaso daya su raba daya kuma ta baya Abdulraham daya Abdulmajid daya daya tace' a bawa Nasir ta bar masa halak malak marayane daya tace za amata aikin Allah sadakatun jari'a yan uwan ta dana mijinta dama suna wajen atake sukace saide mommy ta fansa tunda company ne dama kuma ba ma a Nigeria suke ba mommy sai da ta nemi shawaran Nasir ya yarda tace'' to ta bansa atake tatura musu kudin su ma daddy da Abu cewa sukayi ta fansa dan suke gani kamar hakan zaifi musu sauki dan company nin da Abdulsamad ya mallaka musu na ashana ma bawani iya rikeshi sukayi ba daga k'ashe shima mommy suka saidawa
Yanzu de dukiyar gaba daya yazama na mommy da d'an ta
*bayan shekara biyar*
A wannan lokacin su Nasir suna level 2 a university a k'asar Americans, Aiban kuma bana za su gama secondary shida Abbaty d'an shekara shida a duniya za su shiga primary 3.
Misalin k'afe biyar na yammacin Lahadi hadirin ne sosai yake shirin tasowa daddy kwance a bayan motarsa, ya kalli gefen islamiyar su Nasrim ya ga yara sai fitowa suke wasu an zo daukar su wasu kuma da k'afa suke gudu ya cewa drive Kabiru mu shiga mu mudu ba ko ba azo daukar su Nasrim ba ga hadiri na shirin tashi ko''.
"Kabiru yace ok sir". yayi reverse ya shige ciki.
Nasrim ta lek'o ta window tace "wai Humairah baki gama rubutun ba wllh nide zanbi motar gidan su Ameera ga hadiri kuma yaufa bro Agrif da ya Kamal zasu zo nasan ma yanzu sun zo bama nan kum....
shiru tayi jin Amira tana cewa
"La Nasrim ga motar daddy ku a dai-dai lokacin kuma Humairah ta fito da sauri suka k'arasa gun mota Kabiru ya fito ya bude musu baya suka shiga Humaira ta ce'' Daddy "Ina wuni".
"Lafiya my dear ya karatun".
Ta ce muna yi daddy yace madallah".
ya juya yana kallon Nasrim da take ta faman turo baki yace
"Ya de my sweetheart".?
cikin shagwatar ta tace'' Daddy ba suya Ya Agrif bane zasuzo amma Mama tace wai sai munzo makaranta ina ga ma sunzo yanzu".
"Come down my dota kin manta yau birthday dinki ki daina ɓata rai Agrif ya kawo miki tsaraba da yawa kuma ya ce ba zai kunce ba sai kin zo"
Ihun dadi ta fara dai-dai kwanar da zai kaisu gidan su ne suka samu wani mutum da wata yarinya dakuma wata mata a kwance an rufeta da wani yadi da buzaye suke nad'awa mutumin sai kuka yake yana sake k'enk'eme yarinyar da bazata wuce sa'ar su Nasrim ba Nasrim tace daddy ka ga wasu mutane a waje ruwa yana musu duka mu tsaya mu dauke su daddy".
Sai a san'nan daddy ya juya ya kalli gefen da take nunawa ya sa Kabiru ya tsaya daddy ya leko kai yace" lafiya malam kuke zaune anan ana ruwa wacece wannan a kwance cikin matsanancin kuka mutumin ya d'ago ya ce matata ce ta mutu..
Da sauri daddy ya ɓalle k'ofar ya fito ya ce
"Subbahanalla kuma kake zaune haka ina ne gidanka?".
Cikin kuka dan buzun ya ce
"Gidan wani Alhaji Bala muke aiki a can wani anguwa shi ne da ya rasu yaransa suka kore mu. Mu 'yan Niger ne cirani muka zo ban san inda zan je ba yanzu haka neman yanda za ayi ayiwa matata sutura nake so ".
Daddy yayi mugun tausaya masa yace "idan ka amince zaka bini gidana kafin daukewar ruwan muga abin da Allah zai yi to".
"Na gode Alhaji".
Haka suka kinkimi gawar suka saka a motar bodyguard din daddy shima mutumin ya shiga sai yarinyar ta shiga motar daddy kusa da Nasrim suka ja sai gida.
Sai washegari aka yi suturan matar nan Agrif kam yayi murnan ganin Nasrim dinsa bini-bini ya ce su zo su fita yayo Shan ice cream cin cake dade sauran su Nasrim ta kalli kyakkyawar yariyar buzuwar nan tace'' ke me yasa ba kya bin mu muna fita yawo yayana yake kai mu".
washe baki yariyar tayi tace'' ina so". dan agidan da suka zauna duk da a dakin megadi suke amma yaran gidan suna mugun kyamar su shiyasa take mamakin mutane gidan nan da suke janta sosai duk sun lika can inda suka barin kudi
zama Nasrim tayi tace'' yawwa zamu na fita tare daga yau tunda kin dena kukan mutuwar zan sa daddy ya saki a makarantar mu muna zuwa tare Mamar mu tazama mamar ki ko Mama"?.
ta k'arashe maganan nata kallon maman Mama tayi murmushi tana kallon kyakkyawar yariyar da ta gama kwanta mata dama tunda ta ganta take son temaka mata yanda za ta samu ingantaccen yaruwa ita de tana son yara musamman mata kodan Kamal namiji ne. A fili murmushi tayi tace''Eh mana
My dear ki gaya wa daddy ku kina son zama da IZZZATU zai yarda ta zauna in sha Allah".
"Lah Mama sunan ta IZZZATU".
Mama tace'' Eh ".
"Mama sunan ta yayi dadi INA SON TA".
hakan ko akayi bayan kwana biyu daddy ya gayawa Hajja yana son yasa Izzatu a makaranta shikuma Babanta a samu wani aiki acikin gidan nan a bashi ko da gyaran flour ne".
Kai tsaye
Hajja tace'' ban amince ba".
shirun kowa yayi
cikin kuka Nasrim ta buga k'afa ta tashi ta fice Agrif yace "Hajja me yasa temako ne fa bake kike cewa temako jari bane duk inda muka ganshi kar mu rai nashi".
"Eh haka ne da shi kadai ne zan iya bashi wajen zama amma tunda yazo da yarinya macce gaskiya ban abince ba macce ba ta da tambas balle wannan kyakkyawar ina tsoron wata rana wani daga cikin ku jikoki na yace yana son tsintacciyar magi da ace shi daya ne yana daga waje ba abin da zai iya mana amma ita macce tana daga ciki bazai yuwu ba".
dariya Agrif yayi tsosai yace "Hajja bari kigani yace Kamal zakaso wannan.? yanuna Izza a yatsa a wulak'ance
Kamal cikin kyma yace
"Ni mezan yi da ita *TALAKA* da ita ai ni yar gaye nake so".
ya k'arashe maganan kamar zayyi amai
dariya iyayen sukayi
Agrif yace" kai Aiban kana son ta".?
girgiza kai Aiban ya yi dama shi ba mai son magana ba ne
Y kalli Abbaty yace " Barr kai fa kana son wannan abar".? ya nuna Izzatu Abbaty yace
"a a ni ai idan na girma Faridan Mama Hadiza zan aura bana son farar macce balle wannan kod'eddiyar".
Agrif yace" tsariu daya dakai Barr nima faringa bai min ba yayi kalan tsoro
"to kinji Hajja suma basa so balle ni me NASRIM".
dariya sosai suka saka Hajja tace'' to NASARA fa?".
Agrif yace ai tun yana yaro ra'yinsa y'ar barebari yake so kuma me irin zanen mommy dan haka ba abin da zayyi da wata buzuwa ko sadaka yallace ma".
A haka suka shawon kan Hajja ta amince aka saka Azza a makaran ta primary 1 aka ajiyeta ana mata lesion sosai tunda ba ta yi nursery ba kuma sosai kanta yake ja dan haka lokacin da su Nasrim zasu gama primary daddy ya ce "ita ma asata cikin su tunda malaman sunce zata iya dan tayi girma har tafi su Nasrim sawon k'afa ga alamun girman macce ya fara bayyana ajikin ta wannan shine dalilin da yasa Izzatu ta tadda su a karatu
Izza da Nasrim sunyi wani irin shak'uwa marar misali Izza kam Allah ya bata wani irin kyau nutsuwa ga shiga rai. Bayan jarrabawar su yafito zasu shiga secondary ne bala wanda suke cewa sarkin gida ya kai su tahfizul Qur'an maimakon ya musu registration makarantar su ta da ga shi tunsafe idan aka je ba a tashi sai bayan isshai.
Ana cikin cin abincin dare tukun suka shigo duk ana main parlourn na Hajja
Mama tace '' oyoyo y'an mata na hasken rayuwa ta , amma wannan din wane irin makarantane ajen tun safe sai dare".
Humairah ta ce'' Mama muna zuwa dama aka ba mu uniform kala ukku daya na safe daya na yamma sai wannan na jikin mu muka saka bayan magariba kafin isha'i aka mana hadisi da muka yi sallan kuma aka tashe mu kuma malaman Islamic studies din duk larabawa ne na boko kuma duk turawa ne sunan makarantan LITAHFIZIL QUR'AN ISLAMIC STUIES".
Mama ta ce'' gaskiya mommy ya 'amata ku duba ai wannan karatun akwai matsi tun safe har sai daren kwanciya a a wllh shi ba day ba shi ba boding ba".
Hajja ma tace'' gaskiya yayi tsanani".
Ummu dai ba tayi magana ba daddy ya ce "to ke Aisha ai hakan yayi ba kiga yaran ba alamun wahala a jikinsu ba."
ya juya yana kallon Abu yace
"Bro yaushe aka bude irin wannan makarantan a kano?".
Cikin mamakin Abu yace "a a ban sani ba kana nufin ba kai kasasu ba".?
Daddy yace" a a."
duk suka juya suna kallon mommy a tunaninsu ita ce ta sanya su ta ce "Gaskiya ni ma ban sani ba".?
Abu ya ce wa yaran
"To ku wa ya Kai ku".?
Nasrim tace'' sarkin gida ne"
A take aka kira Bala sarkin gida
Abu ya ce" Bala jiya munyi dakai zaka kai yaran nan makaran tansu da suka gama suci gaba amma yanzu kuma sukace ka kai su wani".
"Eh Alhaji umarni ne daga sama yallabai Nasara ne yace na kai su can kuma makaranta gidan nan ce, jiya aka buɗe ta, amma ina ga bai san da zaman Izzatu ba dan ba sunanta sai ni na saya mata from a kudin wajena wanda ka bani na kai su bai ma isa ba sai da na cika dan makaranta akwai tsada sosai".
Abu ya ce
"Ok ba damuwa zan ba ka cikon".
Hajja ta tabe baki tace'' mutum sai munafirci da kulle-kulle yana can waya da computer suna kunsa masa komai na gidan nan ko ina ya san sun gama makaranta shi ba zuwa yake ba".
Abin yayi matuk'ar bawa su mommy mamakin har mommy ta ciro waya ta saka a handfee ba jimawa ya yi picking
cikin muryar sana k'asaita ya ce
"My sweet mommy barka da dare kin bude ko"?.
"E, za mu yi magana an jima ashe makaranta ka buɗe babu sani ba".
"Ok sorry Mommy ai abubuwa ne suka min yawa kuma made na so nayi surprise dinku ne, in na zo sai mu yi bikin buɗe shin aki yamin yawa ina Hajja rigima ina Abu ya daddy".
"Duk lafiya kuma suna godiya Allah yabar zumunci."
nisawa yayi yace" mommy wacece IZZZATU MUSTAPHA da Bala yake gaya min".
murmushi tayi tace'' itama k'anwarka ce a gidan take shikaran ta ukku ai baka zo k'asan ba balle ka san ta ashe kai wai wani makarantan ma kashiga bayan gama degree maimakon ka dan tallafamin shi ne wai ka koma wani dogon zango ko ".?
cikin shagwabar da ya saba yace mommy ai haka ma ina temaka wa kuma karatun fa shekara 2 ne ina son na zama likita ne kinsan ina da kishi idan na yi aure baz an bar matata taga wani namiji ba ko macce y'ar uwarta kishinta ganta tsirara zan yi shiya sa na shiga kuma naji k'arfin karatun ta online tun kafin na shiga ko yanzu zan iya yiwa macce cs da sauran matsaloli in sha Allah".
Ya yi shiru yana mai da numfashi dan bai sa ba da dogon magana ba in ba da mommy ba ma ba yayi
Mommy ta ce''
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 40